Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne ya fara danna golden din maballin dake kan table din gabansa kafin duka biyun suma suka danna nasu wanda yake irin nashi golden colour,

Cike da zumu di =Rayiys alhadath ke magana "Mashaallah =
tabarakallah,>) tah niyyahn laki yah Zawjatul Ameer (congratulations to you Zawjatul Ameer), You have passed the first bridge, (Ina taya ki murna Zawjatul Ameer), kin wuce wannan gadan kin lashe, kin samu goldn crown =Q (zaiban hulan girma) kin tsallake red ma'ana maballin gazawa wato na rashi , kika kuma wuce green wanda yake pass, wato kina tsaka stakiya ke baki fadi ba kuma baki zama tauraruwa ba."

=farin ciki ya gagara boyu wa a fuskan masoyan ta kamar yadda bakin ciki ya bayyana arara a fuskan maiya=!.

"Ba tare da bata lokaci ba zamu zayya no quality na gaba wanda yake , uhmmm!!! Shine Al SHEZA (good religious girl) Yana nufin yarinya mai kirki da rikon addini, toh bari muga yadda abin zai aya daga Sangare alkalan wasa, amma nawa lissafin ko makaho ya laluma yasan Gimbiya mai jiran gado batayi kama da marar rike addini ba , sai de bari mu bar manya suyi aikin su,"

Kamar a farko gurin ya dauki shiru aka bar alkalan wasa suna nasu nazarin na fidda gwani.

shiruuuu!!!! Kake ji kamar an jefa tsumma a randa, zaka ranste babu halittar ko uda a hall din sai karar masu televising da masu aikin daukan hoto.

Diiid diiid diiid!!!! Kake ji arar maballin da alkalan wasan ke dannawa wanda sun danna lokaci daya duka su ukun,

Zare ido =@ kowa yayi dan ganin abinda suka danna baya Rayiys alhadath wanda yake jin kansa kamar ya fashe,

">/ Jazakallahu Khairan, Mashaallah =
Zawjatul Ameer You have passed with golden crown =Q, kin wuce kin tsallake gada ta biyu, bari mu dan gana zuwa na uku, shine Al SHEENAZ (beauty) ma'ana kyau, ko wannan nasan ko mutanen dake cikin hall din nan zasu shaida hakan, don naga wata budurwa mai ji da kanta tana ganin Zawjatul Ameer tasa nikab =>#=, amma bari alkalan wasa su tan tan ce abun su ."

Cike da tsarguwa yan matan da suka rena kansu ke ta faman cika suna bastewa, wacce tasan da ita ake kuwa kasan table ta shige ganin yadda kallo ya dawo kanta =@=3=@.

An dau lokaci mai tsayi ana muhawara tsakanin Alkalai, wanda sanda aka dan gana da fashion model, an dau akalla three minutes ana muhawara.

Dan dan dan dan!!!! Cikin kowa ya dura ruwa ana jiran iran feedback,

diiid diiid diiid!!!!! Kake ji karan maballi wanda state suka danna,

Murmushi kawai Rayiys alhadath yayi don dama yasan za'a rina,

"Mashaallah li annan laha Houwa ahsanul Khaaliqin >), ko ban fada ba kunsan anan Zawjatul Ameer ta lashe, ta samu golden crown =Q, ta tsallake wannan gadan bari mu garzaya zuwa na huWu, wato SUJA (calmness and quietness) ma'ana kamun kai da shiru shiru ko ince miskila, kunsan mafi akasari an fi son Sultana ko Malikat ta kasance miskila ko shiru shiru, ba wacce ina da hira ba ko ina da ita, kar in cika ku da surutu bari mu bar alkalan suyi aikin su,"

Shiruu kamar ba'a taba yin wani halitta ba'a cikin hall din,


diiid diiid diiid!!! Kake ji karan maballi wanda alkalan wasan suka danna atare,

"Allah Allah Mashaallah =
Zawjatul Ameer ta kara lashewa a karo na hudu, lalle asar Egypt tayi Sa'an Gimbiya mai jiran gado, da alama za'a kafa tarihin da aka dade ba'a yi irin shi ba, Yan zu bari mu gangara izuwa kashi na biyar wato na biyun arshe, yana daya daga cikin abu mai muhimmanci dan gane da zaben Gimbiya, shine AL SHELLA (truly Kind hearted and beautiful), ba tare da na Jamu da nisa ba bari na sada mu da alkalan wasa ,"

Dan jimmm suka yi suka hade kowa da abinda yake nazari cikin su, sun dau lokaci mai tsayi suna abu daya,

Ta fannin Shazana Subaihat ji take tamkar ta hadiye rai ta fadi kasa macecciya tsabar takaici, na farko tayi asarar kudinta da lokacin ta wajen lalata wannan taro, tayi kokarin siyan alakalan da udi mai dinbin yawa wanda sun i karaba, wani mugun murmushin mugunta ta sake tunawa da tayi cewa ta musu barazana da rayuwar ayansu, kuma sun amince zasuyi abinda take so, duk da bata ga Alaman hakan ba sai de ta tuna cewa har yanzu akwai daman cin nasara tun da ba'a yi na biyun arshe da na karshe ba wanda akansu akan iya fasa auren gaba daya, murmushin kafirci da zallan eta da mugunta ta sake= .



An kai akalla five minutes ana jiran su , har kowa ya cire rai da samun nasara, mahassada ko sun fara farin ciki, ba zato ba tsammani aka ji arar maballin diiid diiid diiid!!!

=@=3=A Kowa ya zuba ido don jin abinda ke faruwa, cike da razana da rashin gaskata abin da idonsa ya gani ya kara ware idon na yan sakanni <=3.


With full of joy and jubilation ya ce "Subhanallah Subhanallah, I never thought Zawjatul Ameer will passed this bridge, Alhamdulillah she got golden crown =Q, "

Sauke ajiyan zuciya Malikat Nubia tayi don har ta cire rai, ba ita kadai ba hatta Malik sanda ya sauke, Dukkanin su cikin zuciyoyinsu suka godewa Ubangiji, suka kuma zuba ido don jin ya za'a kaya a gaba.

"Ba tare da bata lokaci ba zamu garzaya zuwa last step, wanda akanshi akan iya fasa auren muddin ba'a samu yadda ake so ba, wannan bridge tsallake shi da wahala, don sai anyi dogon bin cike shine AL SHAZFA (SUCCESS), ko wani ban gare na rayuwa muna da bukatan Sa'a, komai na rayuwa sai da Sa'a wanda in ka samu da kuma yardar Ubangijin ka komai naka zai tafi dai dai, anan ana bukatar dogon nazari da lissafi, za'a bincika aga wani irin Sa'a aka samu lokacin bayyanar Zawjatul Ameer, wani abun alkairi aka samu ta sanadin ta, bari na sada mu da alkalan wasa don suyi aikinsu,"

Yayi magana ne cikin sanyin jiki don har ga Allah anan bashi da ta cewa,hakan yasa jikin mutane da yawa yin sanyi, wanda suka san abinda suka taka kuwa hankalinsu kwance lubb irin su Shazana Subaihat, Wacce tasa hannu ta kama hannu diyarta Sabreena cike da hope na samun nasara , Sabreena ganin haka ne yasa ta saki zuciyar ta da ranta.
Ana zaune har aka shafe tsawon mintina talatin alkalan wasa basu ce komai ba sai ma hade kansu da suka yi suna yan kus kus, kowa ya zuba ido=@ da kunne=B yana sauraron abinda alkalan zasu ce,

Tun ana sa ran zasu ce wani abu har kowa ya buge da yin harkar gaban sa, har an so manta abinda ya sa aka ka halarci wannan taro.

Tsawon one hour Babu alamun zasu ce komai , shi kanshi Rayiys alhadath ya sare = har ya samu guri ya zauna,

Cike da karaya Sultana Najda ta Kama hannun Sultan Salahuddeen, kama hannunta yayi da kyau don ya fahimci ta sare = murmushi ya sakar mata mai sanyaya zuciya.

Ta fannin Ameer Mahbeer ya ci alwashin ko da Zawjatul Ameer bata da wannan feature shi zai zauna da abin shi a haka, ko da hakan yana nufin bazai mulki asar Egypt ba, soft hand din ta ya kama gam cikin nashi yana jin wani sonta na kara Rasta jinin jikinsa, tabbas ya yadda so dashen ubangiji ne , bai taba yadda cewa akwai ranar da zata zo wanda zai so wata mace ba , musamman irin son da yake wa Shazana Mehnoor,

A hankali tace " Zawjy am tired , Ina Jin yun wa, kuma i want to sleep my head is paining me,"

Cike da tausayi ya ce "don't worry Yan zu zamu tafi gida,"
Gyada Kai tayi ta kara je fa masa wani tambayan "Zawjy where is Pops and Ukhtie?,"

A hankali yace "shiiit keep quiet Hooriyya zasu zo yanzu,"
Dan cuno baki tayi gaba da kwabe fuska kaman mai shirin yin kuka,

Murmushi yayi don stab yana iya hango yadda ta bata fuska cike da lallashi ya ce "don......,"

Ba tare da ya kammala furta maganan bakin ba yaji karan maballi diiid diiid diiid!!! Wanda yayi nasaran tattara hankalin Waukacin jama'ar dake hall din dama wanda ke kallo a television,
Ba wanda yayi tsammanin hakan kowa ya zaro ido=@ =3=A , cike da rashin gasgata wa,

Numfashin Sultana Najda har hadewa yakeyi tana kokarin yin magana ta kasa, yayin da hawaye sukayi nasarar riga kalaman bakinta fito wa, da sauri ta rungume Sultan Salahuddeen don baza ta iya jure hakan ba,

Ni kaina Queen Mahirah nayi matuar mamaki ganin wannan al'amari, bani kadai ba hatta Rayiys alhadath kanshi har hayaki yakeyi >/,

Tohh fahh readers ku biyo next page don jin yadda labarin zai kasance .

Har ilah yau zaku iya tun tuba na ta wannan lambar a WhatsApp don na saki cikin WhatsApp group inda zaki samu cigaban page din nan.
Ko kiyi following WhatsApp Channel anan zaki samu labarin tun daga page one har inda aka tsaya.
Ban manta daku ba masu comment Wannan page din sadaukarwa ne a gare ku.

Story and written by
Queen Mahirah =Q>
The wordsmith =؊=

Comment and Share fisabilillah=

Karku manta book one free ne, book two ne na kudi game bukata ga WhatsApp number ta 09168962485.












THE TWO LIGHTS (' (RIKICIN GIDAN SARAUTA <)

The story contains the fact Royalty, Ego, Separation, disastrous love, hatred, hardship, twin flame journey...

Story and written by
Queen Mahirah =Q>
Wordsmith =؊=


Ban mamta daku ba masu comment = ina godiya =O=


Baya ku Oum Affan and bloody, na gode sosai da irin aunar kuke nuna wa Novel Dina =O=>, wannan page din sadaukarwa ne a gareku=>2.

Ongoing Book =
= Typing

FREE BOOK


BOOK 1
>36>


KANO STATE (NIGERIA)

MASARAUTAR SUHATAJ MUHD HABIBULLAH


TURAKAR GIMBIYA ZUNNURA

Kwance bisa shinfidadden Royal Bed dinta wanda aka lailayeshi da hadadden bed sheets.
Tana sanye cikin kaya mara nauyi, kallo daya zaka mata ka hango zallan damuwa dake kwance lubb a fuskanta, gashi tayi wani fari da ita irin na matasa lafiya musamman masu ciwon damuwa.

Cikin nustuwa da zallan Izza da sarauta dake yawo a jinin jikinsa, ya karasa ba tare da ya damu da rashin amsa sallamar nata ba, bai tsaya ako ina ba sai inda take kwance bisa shinfidadden Royal Bed dinta, dogon numfashi yaja da ganin yadda tarame cikin an anin lokaci, zama tsayi a kusa da ita ya kamo hannunta da nashi soft moist hand din, wani dogon numfashi yaja kafin ya fara magana cikin muryan sa na mutane masu hakuri, tausayi, yadda da kuma karfin imani,

"Nur nadan kina jina, inason kisan duk abinda ya faru Muaddari ne daga Allah, kuma su yaran yanzu ka haife su ne baka haifi bakinsu ba, kidena sawa kan ki damuwa , ba laifinki bane, addara ce kuma tana kan kowa,"

Wasu hawaye masu zafi ke bin kunci ta wani irin kunyar hada ido takeyi dashi gani take duk laifin ta ne , da bata dauki Mubeen da niyar ya girma agunta ba da duk haka bazai faru ba,

Hanu yasa ya tallafi face din ta hawaye ya sa hannu ya goge mata cikin nustuwa,

"bude idon ki , "

Ba musu ta bude idonta ta zuba su cikin nashi , Wanda suke narkakku masu daukan hankali da sanya nustuwa cikin zuciyar mai kallo su.

"I told you is not your fault, stop shading your tears for no reason, ki dena fushi da Mubeen pls, ki masa addu'a shiriya, sannan kuma ki yafe masa koda zai samu rahamar Ubangiji, yanzu addu'ar ki yake bukata, inso kisan Allah shi ya bamu su mastayin aa, haka ka zalika su amana ne a garemu, in ya karbi abinda bawai yana nufin baya aunar mu bane ko baya aunar su, sai dan yafi mu son su da sanin darajar su mastayin su na yan Adam, "

Dakata wa yayi yayin da ya yana wani dogon numfashi cikin nustuwa kafin ya fesar, sannan ya cigaba da cewa

"Mubeen ya rigamu gidan gaskiya, Allah ya karbi abun sa ,"

Cike da taahin hankali ta bude idonta atakaice Bara san lokacin da ta zauna ba, kallonsa take in disbelief, Kai kawai ya gyada mata , cike da karaya ta soma jijjiga kanta kafin ta fashe da kuka mai cin rai, kana gani kasan da iya gaskiyar ta take kukan , ma'ana daga zuciyar ta hawaye ke fitowa.

Cike da karaya da tsananta tausayi yake kallon ta, yana daya daga cikin abin da yasa yake kara tausaya mata , wato rashin haihuwar da bata taba yi ba , yau shekara talatin da auren su amma ko haram wata bata taba yi ba, shiyasa data nuna tana son daukan Wan ar uwar ta bai hana ta ba, ya dauke sa tamkar Wansa babu ban ban ci tsakanin su, yau kuma da aka ce ya bar duniya bazai iya misalta irin radadin da ya je ji a zuciyar sa ba, duk da abubuwan d ya aikata a gare sa.

Cike da tausaya wa ya rungume ta so tight ya fara petting back dinta cikin Muryar sa mai san yi da zallan nustuwa ya fara tattalin ta hade da yi mata nasiha mai Rasta jiki kamar de yadda ta kasance tana masa a duk lokacin da ya shiga wani hali na unci.


TURAKAR GIMBIYA NASHWA (FULANI)

Zaune take cikin shiga na alfarma cikin kaya mara nauyi , sai de fari ne tas hannunta dauke da carbi, tana saye da hijabi shima fari tas, princess Mobina na kwance lubb bisa kafin Fulani sai jan ajiyar zuciya takeyi, da alama tayi kuka sosai, cike da nustuwa Fulani ke shafa kanta cikin salo na lallashi.

Cikin muryan ta na sheshshekar kuka tace "yanzu kenan bazan ara ganin ya Mubeen ba Jaddatii ?
Shikenan ya tafi ya barni da kewarsa sa ?
Allah Jaddatii ya Mubeen ya nuna mun so, duk da a zuciyar sa ba haka bane, amma Ni abinda yake zahiri nake gani , ba komai tattare dashi wanda nake gani sai zallan aunar da yake mun,"

Da hanzarin ta mike zaune ta haWa hannunta guda biyu =O cikin salo na neman gafara tace "Dan Allah ku yafe wa ya Mubeen, insao ya samu rahamar Ubangiji, wallahi ba laifin sa bane, nasan wani abun sa shi aka yi,"

Cike da tausayin ta Fulani ta kama both hand dinta tace "Sabr yah Hafidatiii, ki kwantar da hankalinki,"

Fashewa taI da wani mastanan cin kuka maiona rai da zuciya tace " Jaddatii baza ku yafe masa ba ?
Dan bakwa aunata ko?,"


Fulani ganin ta riki mata be yasa ta rasa mai zata yi guda Waya, don in akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce taga jikanunta cikin wani hali na tashin hankali ba , musamman ma Mobeena da take jinta tamkar ranta.

Bata kai ga cewa komai ba sai ga Bana sarki ya shigo cikin keban ceccen farlon wanda ba'a yarje wa kowani bawa ya shigo ba,

Cike da hanzarin da ya karasa inda suke ganin halin da Princess Mobina ke ciki,
"Inna lillahi Mobina mai ya faru?,"


Tana ganin sa ta tashi ta gudu ta karasa inda yake ta rungumesa ta ce" Grandpa ya Mubeen Wan Allah ku yafe masa kar Allah ya kama shi da laifin zunubin da ya aikata,"

"Shittt is okayy Maryama mun yafe masa duniya wa lahira, yanzu ba ban shigo nan ba sanda na tabbatar da sauran bayin sun yafe masa abinda ya musu, ko ba komai shi din Wa ne a garemu kuma ya mana biyayya dai dai gwargwadon iya warsa, shi din ya zama jinin jikin mu, mun yafe masa Allah ya yafe masa shine abinda muke fata a yanzu,"

Fashewa ta karayi da wani kuka mai ona zuciya "shi ke nan yanzu ya tafi grandpa?
Bazan ara kallon shi ba ?
Bazai kara kira na a waya ba?
Bazai ara kaini makaranta ba?
=-=-=-. Grandpa Dan Allah ku dawo mun dashi, wallahi na yadda zan aure shi a haka, na yadda koda shi baya sona, inason in saka mishi da irin kulawa da tattalin da ya yi gareni, ya nuna wa duniya babu yani, tur da irin halina duk Ni na jawo hakan daban tauna masa asiri ba da hakan bazai faru ba, duk da mugun nufinsa akaina na wammace hakan ta faru da rasa kanshi da yayi yanzu , nadan Ni ce sa na di,"

ba tare da ta sani ba taji an soka mata allura, tana kokarin juyowa wani bacci mai nauyi ya dauke ta, da taimakon Dr Yusuf aka kwantar da ita bisa shinfidadden kujerar, mai taushin gaske, sauke ajiyan zuciya Fulani tayi ta ce "Allah ya kawo ka a dai dai Dr Yusuf, da naga ka shigo na zaci shine ma ,"
tayi maganan ne yayin da idonta ke cikin na
Baba sarki, "hankali na ya gagara kwanciya ne shiyasa na ce bari nazo na duba ta,"

"Hmmm tun dazu ta rikice ga jikin ta yayi zafi sosai, sai sun batu take yi shiyasa nace bari kawai na kiransa ka turo mana Dr Yusuf,"

"Hmm kinyi kyan kai, mai yake damun ta ,"

Cike da girmamawa Dr Yusuf ya ce" damuwa ne da stress, sai zazzaSi, amma yanzu na mata alluran bacci she will be alright inshaallah, and kar ana barinta ita kadai kuma ban da yawan tunani, I mean kar barta tayi stressing brain dinta,"

Gyada Kai kawai Bana Sarki yayi, yayin da yake shafa kanta cike da tausaya wa da zallan auna.



RUGAR HARDO BELLO (KANO STATE, NIGERIA)

8:00 pm

Zaune muke a falo as always kowa da abinda ya keyi muna sanye cikin light wears wato kasa marassa nauyi, Sallamar da muka ji ne yasa hankalin mu karkata in da ake sallaman, wah zamu gani ???

Commodore Fareed ne da Captain Fudhal, suna sanye cikin fararen jallabiya, dan kifta ido nayi ina juya su kafin na amsa sallamar tasu, Bismillah shine abinda nace dasu yayin a Islam tun da ta amsa sallamar bata kara cewa komai ba, cike da fara'a ya samu guri ya zauna, shine Fudhal sai cika yake yana bastewa haka har ya zauna.

Cike da fara'a ya ce "sannu ku da hutawa GENTLE ladies=,"

Kai na dago na gansawa, sai kawai ya burge ni musamman yadda yake magana cike da fara'a, ko haka kadai ya nuna cewa mutum ne shi wanda ba shida damuwa.
Murmushin ba mayar masa nace yauwa sannu ya kuke?

"lafiyan mu kalau, ya Wawainiya da mu?,"

Murmushi nayi na mai mai ta Kalmar Wawainiya,

"Ehh ai ba aramin kokari kuke yi ba,"

Wani murmushin na kuma sakewa don nima gwana ce a wannan fannin musamman inna samu wanda na sake dashi.

Ai ku bakin mu ne , bakon ka kuma annabin ka ne.

Gyada Kai yayi ya ce "haka ne, if I guess right ke ce Mahnoor ko?,"

Yaff Ni ce,

"Mashaallah, and this boss lady most be Khadijatul Islam,"

Murmushi nayi na ce You guess it right, she is the one.

"You know am good at guessing,"

Humm kaji Dadi ni kam am not good at guessing,
Dan karkata kai nayi na karewa Captain Fudhal kallo na yan sakanni kafin na ce, is he seek? Naga ya hade fuska kamar gumbar waina, cikin shi na ciwo ne?

Murmushi Fareed yayi ya ce "he is not, haka yake bashi da fara'a,"

Dage gira daya nayi na ce Maama luya, so haka yake kullum da face dinshi kamar anyi gobarar attarubu?

Wani mashiriritin dariya Fareed ya sake ya ce "You are so funny,"

Murmushi nayi na ce uhmm kaga ban ma san sunan ku ba?

"Ohh my name is Fareed and this one is Fudhal,"

Ohh Masha'allah I guess I know you, but where?
Ohh =/ I remember you are Commodore Fareed, you are Air force
, and this Mr Grumpy is Captain Fudhal, I think I guess it right,

Wani murmushi Fareed ya sake ya ce"yapp haka ne, but a Ina kika san mu?,"

Ohh come on, Commodore saninku ai is not a big deal, Kuna cikin Top ten na the most famous and handsome rich guys a fadin Africa, Ni a gurin an matan Class din mu ma na sanku.

"Wow ki ce min yi wuta,"
Yayi magana yayin da yake dan daga kwalan jallabiyar sa,

Dan aramin dariya na sake yanda yayi ya ban dariya sosai, ina dayan kuma mai danne ayan mutane ajikin gini.

Dan ware ido Fareed yayi ya ce "kai kuma acikin mu yake ,"

Zumburo bai nayi gaba na ce = ehh mana kawai daga kai mishi abinci sai ya fara wa mutum mugunta, sanda fa ya gwalmadar mun da kashin kun kumi na=.
Zare ido =3 Fareed yayi y ce"subahanallhi, uhmm am so sorry = haka yake wallahi yana da zuciya sosai,"

Dan daga gira daya nayi nace, i guess ni bani dashi shi yasa ya mun haka, wai yana da zuciya, na fadi haka yayin da na kara turbune face nawa.

"Sorry kin san yan uwan nawa sai ahankali a musu afuwa please =O,"

Kara cuno baki = nayi gaba nace uhmm, ohh na manta ga can abincin ku a dining table, tun dazu Innani ta ajiye, muje nayi serving naku,

Murmushi yayi yace "okay thanks =
,,"

Yayi magana yayin da ya mike ya bi Bayan ta, shiko Fudhal sanda ya mula dan kanshi kafin ya mike, yayin da Islam tana kare mishi kallo azahiri ko zaka ranste waya take dannawa sai de idonta yana kanshi, tana karantar halayyar sa tsaff .

END Of PAGE 36, FOLLOW FOR MORE ="=

Story and written by
Queen Mahirah =Q>
The wordsmith =؊=















































THE TWO LIGHTS (' (RIKICIN GIDAN SARAUTA <)

The story contains the fact Royalty, Ego, Separation, disastrous love, hatred, hardship,Twin flame journey...

Story and written by
Queen Mahirah =Q>
Wordsmith =؊=


FREE BOOK

BOOK 1
>37>

Fudhal ko sanda ya mula dan kanshi kafin ya mike cike da izza ya je dining area, yayin da Mahnoor da Fareed sun shagala da hira zaka ranste sunyi Shekaru tare.

Da kallo na bisa kafin na mike na fara serving dinsa, ina gamawa na mika masa abincin, komawa nayi na zauna muka ci gaba da hira ni da Commandore Fareed, sallamar Innani ne ya kaste mana hiran, cike da jin dadi ta karasa inda muke tana washe hakora kamar gonar auduga, "Mashaallah Abu yayi kyau, abinci kuke ci ashe an samari,"
Fareed ne ya ce "ehh Innani Barka da dare,"

Kara washe hakora tayi ta ce "yauwa Barka, Wan albarka, ya mai jiki?,"

"Jiki da sauki sosai, Alhamdulillah,"

"Tohh Allah ara sauki,"

"Amen summa Ameen"
Toh gwanar laste laste ke baza ki ci abincin bane, kizo kuci tare mana ai yafi dad'i, kuma zai ara muku haWin kai,"

Ba tare da ta ce komai ba ta taso tazo dining area ta zauna tayi serving kanta ta fara ci cike da Miskilanci,

Wani murmushin jin daWi Innani tayi taja wani dogon numfashi ta ce "Allah albarka ci rayuwar ku ya kuma ara hada kanku,"

Cike da zumudi Commodore Fareed ya ce "Ameen Innani, kin ga na samu anne dama nawa daya ne, in zan tafi sai in kaisu gurin Ammi na ta haWa su da Mobina sai su zama su uku, kinga mu uku suma su uku,"

wani Wan guntun walla Innani ta goge cike da tausaya ta ce "kai yah Fareedu bawan Allah Allah de ya nuna mun wannan rana, da zan mia amanar dana dauka ga masu shi,"

Cike da fara'a da warewa wajen aikinsa ya ce "Ameen summa ameen, ar tsohuwa dama ita alawari kaya ne mai nauyi musamman inka rike shi a cikin ka,"

"Hmmm wassu lokutan aikewa aciki yafi ka fidda shi sarari, kasan mahassada sun yi yawa, wai kana ta kai su kuma suna ta kai,"

"So sai ma kuwa Innani ai ni zan fada Miki hakan, kinsan fa Yan zu an dena kiwon dabba sai mutum,"

Cike da jimami Innani tace "ohh duniya ina zaki kaimu, Allah de ya kare mana ku,"

"Ameen summa ameen,"

"A'a shi mara lafiyan fah, Nuriyya zo ki kai mishi abinci,"
a dan razane na dago kaina na ganta kafin na,nayi kicin kicin da fuskana na ce = nifa Innani ni wallahi gaskiya ki tura Barira ta kai mishi abincin,

"Eyyeh wai samu ya fi iyawa hawa dokin maciji, in ce ki kai ki kice na aiki Barira, yar tselen uwa ke zaki kai,"

ukan shagwaba na fashe dashi na fara shure shure da kafa a kasa, ni ni wallahi abinci nake ci, to ke ki kai da kanki mana tunda ke kin fishi damuwa da yunwar cikin shi,

"Ehyehh kin san Allah zan zazzage Miki bakin rashin mutunci Nuriyya in baki tashi kin kai mishi ba,"

Bil hakki da

Please Login or Register in order to submit comment