Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akayi ban gani ba?" Sumayya tace "nima sai da muka shiga sannan naga shine, nayi kokarin nuna miki ke kuma kina can kina yiwa yarinyar data taka miki kafa bala'i dan haka na rabu dake kawai" Ruqayyah ta kalle shi taga har yanzu murmushi yake yi sai taji tamkar ta kama kyakkyawar fuskarsa ta goga ta akan kwalta. Ta juya ta bar gurin tana maganganu kanana kanana.

Adam yace da Sumayya "sister dinki drama queen ce" ta gyada kai tace "sosai. But she is not as bad as she always acts" yace "Allah yasa, dan nasan ke kullum tare mata zaki ke yi, kullum kina side dinta ko?" Ta sake gyada kai tace "yes, bayan Inna da Baba bani da wanda ya kaita. Komai zafinta dole ita din tawa ce, she is a side of me that I can never get rid of. In babu ita to babu ni kuma ba zan........." Ya daga mata hannu "bla bla bla. Naji, amma nasan kinsan cewa bata da kirki, wannan side of her din kinsan dashi fiye da kowa" ta fito daga mitar tana k 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ara mika masa kuWin hannunta "ga kudin ka Adam. Mun gode" ya jefa mata murmushi "ki siya wa sister dinki awara, tunda ta riga ta gama debe wa abincin gidan ku albarka ko zata cinye ba zata ko shi ba" ta rufe masa kofar sannan ta jefa masa kuWin ta window ta juya tabi bayan Ruqayyah ba tare data kuma cewa komai ba. Ta sani, tabbas tasan Ruqayyah bata da kirki amma kuma it hurts her in taji wani ya fada, kullum tana wa Ruqayyah addu'a, kuma bata taba barin tayi wani abu marar kyau ba tare data yi kokarin gyara mata ba. Kuma sosai tana ganin gyaran, gashi nan ta fara chanzawa, gashi nan ranar nan har ta kusa rasa rayuwarta saboda taimakon wani Allah.

Ta tarar da Ruqayyah tana kokarin shan kwana, har yanzu mita take yi amma kuma daga dukkan alamu ba wai mitar mai taxi take yi ba kuma, mitar wani abun ne na daban.

"Mutane yanzu basu san a kyautata musu ba, shi yasa taimako yake da wahala, in ka taimaka ma babu abinda zaka samu" Sumayya ta kalle ta tana girgiza kant cikin takaici tace "shi taimako in dai kayi shi dan Allah ai baka bukatar komai daga gurin wanda ka taimaka wa" Ruqayyah tace "ko godiya? At least dai ai yazo yace min thank you for saving my life ko?" Sumayya tace "Rukee kenan. Kina kallon dai yadda aka fitar dashi daga gidan mu cikin jini, na tabbatar asibiti za'a wuce dashi kuma na tabbatar har yanzu yana asibitin, bai kamata ace har kin fara mita ba, kuma ai yayi miki godiya tun kafin ya bar gidan mu" Ruqayyah tace "wacce godiya yayi min? Ni me yace min ma in banda kira kamar tsohon makaho, 'Hassana" ta fada cikin kwaikwayon muryar Hassan, Sumayya tayi dariya ita kuma tayi tsaki, "bai san yadda na tsani a ce min Hassana ba, Baba ne kawai yake fada shima kuma dan babu yadda zanyi dashi ne".

A lokacin suka sha kwanar gidan nasu, abinda suka gani a kofar gidan ya saka su taka burki cikin mamaki, suka rike hannun juna, Sumayya ta rada wa Ruqayyah "ga mutumin naki nan yazo godiyar" Ruqayyah tace "ni Companyn sa nake so ya bani daya".

Manyan motoci ne guda biyu a kofar gidan, irin motocin da ba a kan kowanne titi su Ruqayyah suke ganin irin su ba. Ga kuma wadansu bakaken mutane masu bakaken kaya da bakaken tabarau a tsaye a gaban motocin, twins din suka rakube suka wuce su suka shiga gidan suna masu hada baki gurin yin sallama.

Babbar tabarma ce wadda Ruqayyah ta tabbatar aro wa aka yi daga gidan su Minal a shimfide a tsakar gidan, akan ta akwai wata mata wadda idan gaskiya za'a bi zata iya girmar Inna ade amma a kamanni zata iya cewa Inna ade ta haife ta. Kana ganinta kasan cewa naira ta zauna mata. A tare da ita akwai yammata, su biyar reras, wadansu farare wasu bakake. A gaban su da tray shima da aka aro a gidan su Minal aka siyo pure water mai sanyi guda goma aka zuba akai.

Daga gefen su karamar tabarma ce wadda tasu ce ta gida, akanta Baba ne tare da Inna Ade fuskokin su dauke da faffadan murmushi. Gabaki daya jama'ar gurin suka amsa musu sallamar. Inna Ade tace "yauwa, gasu nan ma sun dawo" Aunty tana kallon yan biyun da suke karasa shigowa tsakar gidan tace "tubarkallah masha Allah, ashe suma yan biyu ne?" Inna Ade ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Hassana tace "Kai! Amma fa kyawawa ne, wacece takwarar tawa?" Inna Ade ta dago tana kallon ta tace "kuma yan biyu ne?" Hassana tace "a'a, ni suna kawai naci, yayyen mu maza ne dai yan biyun. Shi wanda kuka taimaka shine Hassan, akwai hussainin sa".

Daga dan nesa su Ruqayyah suka durkusa suna gaishe da bakin. Duk suka amsa da fara'ar su. Aunty ta miko hannunta, ku zo kusa dani ku zauna kunji yayan albarka? Wacece hassanar a cikin ku?" Da sauri Sumayya ta nuna Ruqayyah itama Ruqayyah ta nuna Sumayya. Duk aka kwashe da dariya. Inna Ade tace "Ruqayyah ki amsa mana anayi miki magana" Ruqayyah ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da tsinke a kasa tace "na'am" Aunty ta taso da kanta tazo har gabanta ta ruko hannunta tace "zuwa nayi har gida inyi miki godiya Ruqayyah. Nagode Nagode Nagode, Allah ya biya ki da gidan aljanna" duk sukace ameen banda Ruqayyah da take murmushi kasa kasa tana boye fuskarta.

Aunty tace "Allah yasa wannan abu daya faru ya zama silar zumunci a tsakanin mu daku zumunci na har abada. Dan mu kam abinda kukayi mana ba zamu iya biyan ku ba, bamu da kudin da zamu iya biyan ku fatan da zamuyi kawai shine mu hada jini daku idan kun amince. Shine kadai sakayya".

Bayan bain sun tafi, Inna da Baba sun tafi rakasu mota su kuma su Ruqayyah sun shiga daki suna cire uniform dinsu sai Ruqayyah ta daga labule tana leken waje tace "ni banga ana shigo da kwalayen ba" Sumayya ta ce "wadanna kwalaye kuma?" Ruqayyah tace "kina nufin wai hannu rabbana suka zo mana gida? Sai pure water din mu da suka shanye?" Sumayya tace "ho! Rukee. Wai duk bayanin matar nan baki fahimta ba?" Ruqayyah ta saki labulen tana kallon ta tace "wanne bayani fa? Ni ban fiye gane dogon bayani ba nafi son in ga aiki a aikace" Sumayya tazo ta kama hannun ta tace "ni abinda na fahimta daga bayanin ta shine kamar tana neman aure ne a gidan nan. Kamar tana nema wa wannan mutumin da naji sun kira da Hassan auren ki".

Ruqayyah ta saki hannunta tana kallonta dalala da baki cikin mamaki, she never thought it possible, ta dauka yana da aure sannan da jerin manyan yammatan da suke rushing a kansa, bata taba tunanin mutane irin su zasu nemi hada zuri'a da irinta ba shi yasa dam bata gane bayanin ba. Ita jira kawai take taga an miko.

Sai ta kama rawa tana juyi a dan karamin dakin nasu, Sumayya tana dariya cikin taya yaruwarta farin ciki. Har sai da hajijiy ata kama Ruqayyah ta fada kan katifar su tana birgima. Sumayya tazo tana janye kayan shanyar su data debo tana cewa "ni daga mana kaya kar kiyi masu squeezing ki kara min wahalar guga" Ruqayyah ta jawo ta ta fado jikinta tana cewa "ke ta guga kike yi? Yar uwarki zata zama matar CEO na H and H amm kina damun kanki da guga?" Sumayya ta mike zaune tana dariya tace "zata zama kika ce, ba wai ta zama ba. In banyi gugar ba ai ba zaki samu kayan sakawa ba in CEO din yazo ganin ki" Ruqayyah ta mike tsaye tana kallon kanta, ta dauko mudubi ta kalli fuskarta sannan ta ajiye tana cewa "farko aiki zan saka shi ya fara bawa Baba, Babban aiki irin wanda hatta yan Zariya sai sun san yarsa tayi babban kamu. Sannan sai in saka ya rushe gidan nan ya gina mana wani, irin gidan Alhaji Kabiru sabon kudi wanda aka saka tiles har a jikin bango. Kuma ginin hawa uku nake so, kasa su Zunnur ne zasu zauna tare da abokansu da suke kwana tare a shagon Bala, hawana biyu kuma inna ade da Baba, hawa na uku ni da Sumayya, sai im saka ayi min personal balcony a can sama inda zan ke hawa ni kadai ina kallon kowa a kasa na, ina kallon duk unguwar nan a kasa na, ina kallon kaduna a kasa na. And that, will only be the beginning"


Wannan littafin na siyarwa ne, wanda yake so ya nemi wannan numberTwelve : A Kind Suggestion
Sumayya da tun da Ruqayyah ta fara lissafin ta take tsaye a bayanta rike da kaya a hannu baki a bude cikin mamaki, tasan yaruwar tata tana da dogon biri amma bata taba sanin cewa burin nata ya kai tsahon haka ba sai yau.

Gida mai hawa uku, balcony, kallon kowa a kasa, lallai Ruqayyah ta wuce duk inda Sumayya take tunani. Tace "Ruqayyah? Duk wannan lissafin kawai dan babarsa ta nuna tana so a haWa ku? Tun shi bai ce yana son ki ba tun baku fahimci juna ba ballantana ayi zancen auren har kin fara lissafin abinda zaki samu daga gare shi? Tabbas zaki fara ginin auren ki akan tubalin toka dan kuwa shi aure ana gina shine saboda Allah ba wai saboda abin duniya da ake burin za'a samu ba"

Ruqayyah ta juyo tana kallonta, ita lissafi take yi a zuciyarta ba ta san cewaa fili tayi maganar ba amma so what? Waye baya son kuWi? Kowa fa aka bashi daWin su zaiji amma mutane da munafurci sai suke nuna wa kamar basa so.

Ta hade rai tace "shikenan kuma yanzu Sumayya mutum bashi da ikon ya fadi a binda yake zuciyarsa sai a sako shi gaba da wa'azi? Ni banga aibu dan mutum ya nemi duniya at the same time kuma ya nemi lahira ba. Shi yasa ake addu'a ana cewa rabbana atina fidduniya hassanatan wa fil akhirati hassanatan......." Sumayya tace "kyakkyawar rayuwar ake nema ba wai kudi ba Ruqayyah, kudi ba shine farinciki ba, kudi ba shine abu mafi muhimmanci a rayuwa ba Ruqayyah. Happiness. Ka zauna cikin farin ciki shine abinda ake nema, wannan kuwa baya samuwa sai da wadatar zuci ba wai wadatar aljihu ba, the more kina samun kudi da more kina kara jin cewa ya kamata ki samu wasu, amma in dama baki saba dasu ba You will be contented with the little you have. Ni wannan shine abinda na fahimta, wannan shine abinda nake so. Wadatar zuciya. Kuma su kudi a fahimtata sukan kawo rabuwar kawuna ne a cikin iyali. Idan family da basu da kuWi kamar mu din nan zaki ga sunfi haWin kai ana haduwaa rufawa juna asiri but the moment kudi ya shigo ciki sai kiga an samu rarrabuwar kawuna musamman idan wani bangare ne ya samu kudin wani kuma bai samu ba. Ni abinda nake gudar mana kenan. Ruqayyah bound din da yake tsakanin mu yafi min gida mai hawa ukun da kike buri"

Ruqayyah ta jawo ta jikinta tace "my darling sister, ba kudi ba, babu abinda zai raba tsakanin mu, duk inda zanje a rayuwa duk matakin da zan taka a rayuwa you will always be by my side, family na will always be y top priority, shi yasa a lissafin nawa Baba na fara sakawa nasan yana wahala damu" Sumayya ta zame daga jikinta tace "how can I be always by your side idan kika auri CEO na H and H? Zaku tafi ne unguwar masu kudi ya gina muku gida mai hawa biyar. Ni ma kuma dole zanyi aure, yanzu misali in na auri....... Na auri..... Na auri Adam drivern taxi yaje ya kama mana hayar gidan kasa kinga ai mun rabu kenan, banbancin yayi yawa"

Ruqayyah ta kuma jawota tace "sai in saka mijina ya gina muku gida a kusa da gidan mu ya baku kyauta dan mu zauna tare" ta hade rai tace "kuma ba zaki auri Adam ba, kar ki ma kuma saka shi a misali" ta fita ta tafi yin alwala tana mita "na tsani wannan gayen wallahi, he is so arrogant and rude, gashi shi ba kowan kowa ba amma in yana magana kamar yafi kowa" tayi tsaki "inyamuri kawai. Watakila ma ba musulmi bane ba".

Ruqayyah tayi ta saka ran taji Baba ko Inna Ade sunyi mata maganar abinda bakuwarsu tace amma sai taji shiru, in ta taso da maganar sai Inna Ade tayi saurin chanja topic saboda bata son sauran yaran su san da maganar, Ruqayyah ta cika tayi ta kumburin ta sai duk suka shareta saboda dama ta saba fushin ta ita kadai.

Sai da dare bayan duk yara sun watse sannan Inna Ade tace wa Baba "Baban biyu ka fahimci inda maganar bakuwar na ta dosa kuwa? Ka gane abinda naso na gane?" Yayi ajjiyar zuciya yace "na fahimce ta uwar biyu, kawai dai nayi shiru ne kuma kema ina son ki cigaba yin shiru akan maganar saboda bama bukatar wani yazo ya gaya mana cewa mutanen nan ba sa'annin auren yayan mu bane ba, bana fatan yiwa yayana aure a gidan da za'a wulakanta su duk da dai su wadannan naga kamar ba irin sauran masu kudi bane ba, ni nafi son suyi karatu su nemi nasu na kansu ba wai su jingina da wani ba. Sannan kuma ita matar nan zata iya yiwuwa kawai nata ra'ayin ta fada bawai ra'ayin shi yaron ba, in yaron yana so da kansa zai zo ya nema. Dan haka mu bar maganar, muyi ta addu'a,idan yazo ya nema din kuma an samu daidaito tsakanin sa da yarinyar sannan mun bincika mun tabbatar da nagartarsa to alhamdulillah sai mu bashi ita" Inna Ade tace "to Allah ya shi ge mana gaba, ni ba wai maganar auren ce ta bani tsoro ba halin Ruqayyah nake gudu,dama Sumayya suka ce da sauki"

Baba ya kalle ta kawai ya dauke kai, amma maganar ta ta tsaya masa a rai. Tabbas gaskiya ta fada, duksu biyun yayansa ne amma suna da banbanci kwarai da gaske ta fuskar halayya.

A Sangaren su Aunty bayan kuwa bayan sun koma gida su Nafisa suke ta zancen gidan. Hassana tace "Amma Aunty mutanen nan daga ganinsu suna da hali na gari, kinga yadda suka tarye mu da kulawa da karramawa? Basu da kudi amma tabbas suna da kamala" Safiyyah tace "suna kuma da addini, yanayin shigarsu da nutsuwar aan ta birgeni" Khadijah tace "da tsaftar gidan, har muka fito banga datti ko digo ba, kayan sawarsu sun tsufa amma babu datti a jikin su" Nafisa tace "gasu kyawawa, kai twins din nan akwai kyau. Wato in suka samu kulawa sai an jinjina irin kyawun da zasuyi" Zulaihat tace "a yanzun ma ni banga alamar yunwa a tattare dasu ba, basu da rama kuma basu da datti. Hoda kawai suke bukata da jambaki" duk suka kwashe da dariya. Aunty tace "nima nutsuwa da tarbiyyar yaran ta bani sha'awa. Allah dai yasa yarinyar nan rabon Hassan ce dan ni kam nayi masa sha'awar ta sosai. Gata yarinya karama yadda juya ta ya kuma tarbiyyan tar da ita yadda yake so"

Wannan yasa washegari tana tashi ta kira Hassan, Hussain ni ya dauki wayar suka gaisa sannan ya bawa Hassan da yake kwance yana ta juyi. Ya karba ya gaishe ta sannan tayi masa bayanin zuwan da tayi gidan su Ruqayyah

"Jabir ne ya karbo min address din a gurin police, gaskiya Hassan naji dadin ganin yaran nan da iyayensu. Alamu na zahiri sun nuna cewa mutanen kirki ne, badini kuma Allah ne ya barwa kansa sani" Hassan ya shafa sajen fuskarsa yana murmushi a ransa yana jin kamar an yaye masa wani nauyi yace "naji dadi sosai Aunty, naji dadi da kika yaba dasu" sai kuma ya danyi shiru cikin jin nauyin Aunty yace "kin ganta?"

Sai da tayi dariya sannan tace "na gansu, su biyu ne ita da husainar ta. Kamar su daya komai nasu daga, daga dukkan alamu basu kammala secondary school dinsu ba dan ba gansu da uniform" ya gyada kai yana tuno fuskar Ruqayyah sanda take daure masa ciwon sa,ya lumshe ido ya bude yace "Nagode Aunty" suka yi sallama ya ajiye yana kallon Hussain take ta zabga masa harara, ya dga kafada yace "me nayi?" Hussain ya gyara zama yace "sai wani murmushi kake yi wai kai nan kayi budurwa. A dai bi a hankali" Hassan yayi dariya har sai da yaji wuyansa ya amsa sannan yace "oho dai" Hussain yace "wai yarinyar da ka hadu da ita cikin mintinan da basu wuce talatin ba, sannan kuma cikin tsakiyar dare ita ce kake ta kwarara wannan murmushi saboda ana yi maka maganar ta" ya danyi dan karamin tsaki.

Hassan ya mike daga kwanciyar da yake yi ya hade rai yace "ai ba mintuna ko lokacin da muka hadu Win ne madu muhimmanci ba, abinda tayi a cikin mintinan shine abu mai muhimmanci, ni na kasa gane kan ka Hussain, yarinyar nan fa rayuwata ta ceta, I owe her my life. Amma maimakon ace ka kasance mai farin ciki da ita sai kake furuci masu daci a kanta. It hurts me wallahi, and it makes me question matsayi na a gurinka"

Hussain ya ajiye magazine din hannunsa yace "haka ne, I should be grateful to her, but bansan me yasa ba nake jin something odd about her ba, kawai ji nake sam ban yarda da ita ba" Hassan yayi murmushi yace "kamar yadda nima farkon soyayyar ku da gimbiya nake jin ban yarda da ita ba, gashi yanzu na fara sabawa da ita har muna zama muyi hira, kamar yadda na yarda da gimbiyar ka kaima one-day zaka yarda da tawa gimbiyar".


Sai da suka yi sati uku a can sannan suka dawo Nigeria, a lokacin Hassan ya warware sosai har ya maida kibar sa kuma yayi haske abinsa, Hussain wata daya yaso suyi amma Hassan yaki yarda dan shi Allah Allah yake yi su dawo yaje yaga Hassanar sa. "Kar tayi fushi, tace naki zuwa"

Ai kuwa Ruqayyah tayi fushin, tun tana kirga kwanaki har ta koma lissafin sati, gashi iyayenta sunki kwata kwata suyi mata maganar, Sumayya ma ta share ta. She became very edgy daga an taba ta sai bala'i har yan gidan duk suka share ta suka daina shiga harkarta. A haka har suka kammala neco dinsu, shikenan suna daina zuwa makaranta tunda ba waec zasu yi ba. Wannan zaman gidan shi ya cigaba da frustrating Ruqayyah, har mafarkin Hassan take yi wai ya dawo daga kasar waje ya siyo mata sabuwar waya mai kyau ar yayi.

A ranar kuwa ya dawo kasar, washegari ya taho ganin ta. Drivern da ya kawo su Aunty shi ya saka ya rako shi gidan tunda ba zai gane ba. Suna yin packing yabi katangar gidan da take rabi ta langa langa da kallo yana tuno memory din ranar nan sai ya jinjina hikimar ubangiji, ya tuna sanda ya shiga gidan ta tsakanin langa langa ya kwanta a toilet din gidan yana birgima saboda azabar ciwon da yake ji a kafarsa da jinin da yake zuba a wuyansa.

Ya tuna sanda ta shigo toilet din tayi fitsari a gabansa ba tare da tasan yana gurin ba, yayi murmushi tare da alkawarin wata rana sai ya tsokane ta da abin, ya lumshe idonsa yana misalta yadda zata ji kunya ta kifa kanta a kirjinsa tana cewa "kaga bana so, ka daina tsokana ta, Allah zan rama nima" ya sake yin murmushi shi kadai yana girgiza kai, yasan da Hussain yana kusa dashi da sai ya dungure shi yace masa "idiot".

Drivern ne ya fita ya nemo yaro sannan ya tambayi Hassan "oga Hassan wa za'a ce ana kira?" Ya sake murmushi kamar idiot sannan yace "Hassana. Kace Hassan ne yazo yana son ganin Hassana" yaron da drivern duk suka yi dariya sannan yaron ya shiga ciki.

Wanke wanken kwanuka take yi tana mitar Zunnur da ya ki cin abinci dare da Sulaiman ya zuba nasa daban ya kara mata kayan wanke wanke. Sumayya tana dora wa yara karatu akan baranda Inna kuma tana ruWa tuwo. Yaron ya gaishe da inna sannan yace
"Inji wani mai babbar mota yace wai Hassana tazo inji Hassan"

Karaf a kunnuwan Ruqayyah, ta saki kwanon hannunta tana juyo wada sauri idanuwa a waje, suka hada ido da Inna, sai ta mike da sauri tana wanke hannunta da afafuwan ta. Inna ta ajiye muciyar hannunta sannan ta bita dakin, kafin ta shiga har Ruqayyah ta birkito dukkan kayan su na cikin bagko tana neman wadanda suka fi ko wanne kyau. Inna ta tsaya tana kallonta tace "gashi kuma baban ku baya nan ballantana a tambaye shi izinin ki fita gurinsa"

Ruqayyah ta yar da rigar hannunta ta juyo idonta har ya ciko da kwalla "Inna yanzu kuma jira zai tayi a waje har sai Baba ya dawo? Baban da bamu san lokacin da zai dawo ba? Inna tunda ke kina nan ki bani izinin mana, in Baba baya nan ai ke ce wakiliyarsa" Inna Ade ta girgiza kanta tana tabbatar wa da kanta hasahen da tayi akan Ruqayyah dai dai ne, sai dai kuma abinda Ruqayyah ta fada gaskiya ne, bai kamata abar bakoa waje yana jira ba kuma ita bata da waya ballantana ta kira baban biyu ta gaya masa labarin zuwan bakon.

Sai tace "bana son ku tsaya dashi a waje, bana son kuma ku zauna a cikin motarsa, gashi kuma bamu da soro ballantana ya zauna. Abinda za'a yi bara in sallami yaran nan sai ayi masa shimfida a tsakar gida ku zauna ku gaisa, dake da Sumayya zaku je. Ni kuma zan zauna a daki. Ki kiyaye ni Ruqayyah, in kika nuna masa halinki wallahi xan saka baban ku ya gaya masa kar ya sake zuwa gidan nan" Ruqayyah tayi saurin gyada kanta, ta yarda, ta yarda da ko wanne sharadi in dai za'a bata wannan chance din. Wannan chance ne one in a million ta samu kuma ba zata yi wasa da shi ba.

Tana cikin shirya wa Sumayya ta shigo itama ta wanko fuskarta, duk basu yi kwalliya ba sai mai da suka shafa suka saka kaya da dogayen hijabs dinsu. Sannan Sumayya ta shimfida tabarmi guda biyu a kasan bishiya sannan ta shimfida sallaya a saman tabarma daya. Ruqayyah kuma ta dauko sabon kwanon shan ruwan Inna Ade ta debo ruwa ta ajiye sannan ta dora kofi akai.

Sumayya ce ta fita kiransa. Yana motar dai a zaune suna hira shi da drivern, lokaci zuwa lokaci yana kallon kofar shiga gidan zuciyarsa tana son ganin fitowarta. Sai ga Sumayya ta fito, idonta ya sauka kan motar amma da yake tinted glass ne bata hango na ciki ba amma shi ya hango ta, yaji bugun zuciyarsa ya karu, ya dakata da hirar da yake yana samun damar kare mata kallo tare da tunowa da waccan fuskar da ya gani ranar nan. Abinda ya fara fahimta a tare da ita shine yadda take tafiya cikin nutsuwa. Ta tsaya a gaban motar cikin yanayin rasa abinyi. Sai kuma tayi sallama tare da knocking window din. Yaji dadin sallamar da yaji tayi. Ya sauke glass din window din a hankali sannan ya sauke idonsa cikin nata. Tayi murmushi mai fadi, ko ba'a gaya mata ba ta san shine wannan duk da cewa ranar nan bata wani ga fuskarsa sosai ba.

Ta dan durkusa kadan tace "ina yini, sannu da zuwa" ya jefa mata best smile dinsa yace "lafiya lau....." Sai ta katse shi "ammmm an ce ka shigo ciki, Ruqayyah Hassana tana ciki" ya kankance idonsa yana kallonta cikin mamaki, sai ta danyi yar dariya tace "ni sunana Sumayya...." Yace "Hussaina?" Ta daga masa kai ya bude kofar motar ya fito ya na kallon ta yace "gwara in gane ki sosai kar aje ayi min chanje"

ta sake dariya, ya fahimci tana da fara'a sosai tace "baza ayi maka

Please Login or Register in order to submit comment