Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai tsafta sosai tunda dai babies sun hana maman su girki" ya karasa yana tsokanar ta sannan ya fita, ta zauna tana jin kalmar maman babies tana bata mata rai, sai kace ita ce Inna Ade da ake cewa uwar biyu.

Sumayya bayan ta shiga gida su Inna suka yi ta mamakin ganin ta haka da sassafe, sai tace musu kawai tayi kewar gida ne shi yasa ta dawo, amma Inna Ade ta lura da damuwa a fuskarta. Sai data bari ta shiga daki tana gyara kayanta sannan ta bita ta zauna tace "ya kika baro su Ruqayyah? Jiya da dare da muka ganta naga tayi girma sosai, kamar hankalin ta a kwance yake ko? Bata da damuwa ko?" Sumayya ta ajiye kayan hannunta ta dawo kusa da Inna Ade ta zauna tace "bana jin Ruqayyah tana da damuwa Inna, ki kwantar da hankalin ki, mijinta da surukan ta suna da kirki sosai kuma suna son ta sosai" sai kuma ta dan yi shiru idanunta a kasa, Inna Ade tace "sai dai kuma me? Akwai magana a bakin ki ki gaya min mana wani abun ya faru ne?" Sumayya tace "kawai dai ina tsoro ne Inna, kin san halin Ruqayyah tun tana gidan nan, yanzu kuma tayi aure ga kuma irin gidan da tayi auren a ciki, cikin yan kwanakin nan da auren nata har idanunta sun kara budewa sosai, ta kara chanjawa sosai, ina tsoron nan gaba kar ta kauce hanyar da kika dora mu akai Inna, so nake kiyi tayi mata addu'a Inna" Inna Ade tayi ajjiyar zuciya tace "ko sau daya ban taba cire wannan tunanin daga zuciyata ba Sumayya, kullum ina yi muku addu'a gabaki dayan ku kullum dare sai na tashi nayi muku addu'a neman tsari daga shaidan, mutum da kuma aljan. Kuma na tabbatar ubangiji ba zai jiyar da addu'a ta ab saboda yayi al™awarin amsar addu'ar uwa akan ´a´anta. In sha Allah yar uwarki ba zata tabe ba. Xan kara wata addu'ar akan wacce already nake yi kullum.

Sumayya taji dadi kuma taji hankalin ta ya dan kwanta, tasan babu abinda addu'a ta bari dan karfin addu'a yakan iya chanza kaddarar mutum gabaki daya.

Cikin kwana biyu Ruqayyah ta kuma dawo da mijinta gare ta, ta kuma fara shiga cikin yan uwansa kamar yadda Minal ta bata shawara. Idan ya fita itama sai ta shirya ta tafi part din aunty tayi zamanta acan, ba zata dawo ba sai yayi mata waya yace gashi nan zuwa sannan zata debar musu abinci ta tafi can ta kuma shirya tayi masa kwalliya kafin ya dawo. Wannan yasa shima ya wanke zuciyarsa gaba ki daya akan waccan maganar yake enjoying matarsa.

Motocin su da Hussain ya siya musu ita da Fatima sun iso kuma Ruqayyah tayi murna sosai dan bata dauka haka motar ta hadu ba sai da tagan ta kiri kiri sannan ta kuma fahimtarta. Hassan ne yayi suggesting ya kamata ta shirya taje gida ta nuna musu motar dan tun da suka dawo bata je gidan ba. Dan haka ta dauki kayan tsarabarsu sannan shima kuma ya dauki kudi masu kauri ya bata yace ta kai musu, sai ya hada ta da driver yace ya kaita tunda bata fara koyon motar ba tukuna. Dan haka hankalin ta kwance ta tafi a zuciyarta tana plan din daga can zata biya ta gidan su Minal suje gurin malamin nan mai addu'a.

Tana shiga soron gidan taga Adam yana fitowa daga dakin su Sulaiman. Yana shafa kai yace "welcome Madam" ta watsa masa harara tare da jan dogon tsaki ta wuce cikin gidan sai yayi murmushi kawai ya fita. Tana shiga Zunnur yana ta murnar ganinta amma ita da fada tafara "me wancan kedarin yake yi a gidan nan? Duk ya cika masa gida da warin karti" Sumayya da take daki suna waya da Adam yana gaya mata ya gama zai tafi ta fito tana kashe wayar ta nuna ta "kar ki kuma, wallahi Ruqayyah ki fita daga idona na gaya miki" Ruqayyah tace "in na kuma nace sai me? Me zakiyi min? Wallahi sai ya daina zuwa gidan nan ai badan irin su Hassan ya sai gidan ba" Sumayya tace "to maza, yi mana gorin cewa mijinki ne ya siya mana gida, dan ma dai ba rokar sa mukayi ba kuma daya siya din ba ke ya siya wa ba Baba ya siya wa dan haka baki da iko da gidan" Ruqayyah tace "amma dai saboda wa ya siya? Saboda ni ya siya baby girl amma ina da say akan waye zai ke shiga gidan nan yana fita kuma wancan katon kedarin baya daga cikin su"

Inna data rike baki tana kallon su tace "to kuyi dammara ku daku a gaban kannen ku kunji. Akan saurayi zaki yi fada da yar uwarki Sumayya? Ke kuma akan wata akida taki ta daban zaki yiwa yar uwarki damu iyayenki gori cews mijin ki ya siya mana gida? Ruqayyah? Har kin kai haka? Har kin yi girman da zaki yi mana gorin gida Ruqayyah?" Ruqayyah ta zauna taa magana kasa kasa "ni ba gori nake muku ba inna, ni kawai mutumin nan ne bana son yake zuwa gidan nan wallahi. Na tsane shi bana son ganin sa" Sumayya ta bude baki zata yi magana sai kuma ta kalli Inna ta juya ta koma daki tana rufo kofa. Tana ragawa Ruqayyah akan komai amma ta rasa me yasa bata iya raga mata akan Adam. Ko da wasa bata son Adam yaji irin maganganun da Ruqayyah take fada akan sa, babwai dan tana son sa a matsayin saurayi ba sai don tana sonsa a matsayin sa na wanda yayi loosing everything for islam.

Inna ta jima tana yiwa Ruqayyah fadan abinda tayi sannan kuma ta koma yi mata nasiha, daga nan kuma sai suka shiga hira. Su Sulaiman da suka tafi dauko kaya daga mota suka suka dawo suna baje kayan anan tsakiyar palo kowa yana diban nasa. Ruqayyah ta dauko na Baba ta bawa Inna ta ajiye masa sannan ta bata nata itama. Ta ware na Sumayya gefe tace "ita kuma wannan inntaga dama ta fito ta dauka to in kuma tayi fushi in kinyi bakuwa inna ki bayar" Sulaiman yayi dariya yace "babu wanda zai shiga tsakanin ku dan duk wanda ya shiga to kuwa zai ji kunya" duk suka yi dariya amma ita Ruqayyah bata ga abin dariya a cikin fadan su da Sumayya ba, ita bata san me yasa suke daukan lamarin Adam for granted ba. This is very serious issue amma su suna dariya akai.

Sai daga baya Inna da kanta ta aika aka kirawo mata Sumayya ta fito suka cigaba da hirar si tare, Ruqayyah tana ta nuna musu hotunan guraren da suka je da kuma abubuwan da suka yi, sannan tace "ohh ni na manta ma, ga mota can Hussain ya bani kyauta. Tana waje" sai murna da ihu. Suka fita waje gabaki daya har da Inna, suna ta gani suna saka albarka, Ruqayyah ta saka drivern ya dauke su ya dan zaga dasu unguwa sannan ya dawo dasu.

Anan Ruqayyah ta kusan yini har laasar, sai da Baba ya dawo ta gaishe shi sannan ta fara shirin tafiya. Inna tace "da wuri haka zaki tafi?" Tace "yace kar in kai dare ne, yace in koma gida kafin ya dawo kuma karfe biyar yake dawowa" Inna Ade ta gyada kai tana jin dadin yadda Ruqayyah take wa mijinta biyayya. Ta dauko kudin da Hassan ya bayar ta ajiye musu sannan tayi musu sallama suka raka ta har bakin mota, Baba yana sakawa motar albarka.

Suna fita daga layin ta saka driver ya dauke kan motar zuwa gidan su Minal, ta dauko waya ta kira ta ta gaya mata gasu nan zuwa dan haka suna zuwa ta fito ta shiga motar suka tafi. Basuyi wata tafiya mai nisa ba suka zo gidan malamin, sai Ruqayyah tayi mamakin ganin hadadden gida ba irin gidan malam Shehu ba dan tasa ran ganin dan karamin gida mai dakin almajirai a soro da kuma malami a zaune akan buzu a kofar gidan amma sai taga an bude musu gate sun shiga hadadden gida drive in, suka fito daga motar kamar zasu shiga cikin gidan sai Minal ta kira wani a gurin tace a gaya wa Malam sunzo.

Sannan ta juya gurin Ruqayyah tace "dama tun ranar da muka yi magana dake na gaya masa ta WhatsApp cewa zamu zo" Ruqayyah tayi dariya "wai kina nufin malamin ne yace WhatsApp?" Minal tace "to me za'a fasa, na gaya miki fa ba irin wadanda kike jin labarin su bane ba. Mu shiga ciki zaki kara tabbatar da abinda na gaya miki" suka shiga cikin wani palo suka zauna, Ruqayyah tana ta mamaki "yanzu dama ana samun irin wannan kudin a harkar malinta shine malam Shehu yake zaune a gidan kasa? Duk ilimin sa?" Minal tace "shi ya zaba. Kinga shi fa wannan yan siyasa suna zuwa gurinsa yayi musu addu'ar nasarar zabe, a haka ya gina wannan gidan ya kuma sayi motoci har biyu, ko da yake dayar ance min kyautar ta aka bashi"

Suna nan zaune malamin ya fito, middle age mutum ne mai kamala da komai, ya saka manyan kayan sa da babbar riga hannunsa rike da charbi yana ja ya zauna suka gaishe shi yace "Ruqayyah ko? Amina ta gaya min zaki zo. To madallah Allah yayi albarka. Yanzu mu fara yiwa Annabi salati kafa goma tukunna" suka yi salatin nabiy a tare kafa goma sannan yace su karanto sunayen Allah 99 a tare, suka karanta sai ya jefar da charbin sa a gaban Ruqayyah yace ta miko masa, ta dauko ta miko masa sai ya rike gefe da gefen inda ta taba ya kirga adadin beats din da suke gurin sannan ya kalle ta yayi murmushi yace

"Amina ta gaya min bukatar ki, dukiya ce ta kanin mijinki ke kuma a ranki kina so ta zama ta mijin ki. Shine kike so ayi miki addu'a Allah yayi miki jagora akan wannan kudiri naki" Ruqayyah ta gyada kai tace "haka ne"

Yace "to ai malama Ruqayyah ni dai abinda na gani a tattare dake shine arziki, naga dukiya fiye da wadda kike saka ran samu, na ga budi, indai kudi ne wadanda ake kira da kudi na gansu. Amma kuma naga kadaici. Zabi ya rage naki Ruqayyah, nan gaba kadan wata damazata same ki wadda zata barki da zabi guda biyu, ke da kanki zaki zabi rayuwa cikin dauka marar iyaka ko kuma rayuwa a karkashin masu daula marar iyaka. Zabi ya rage naki. Idan kin je gurin zaki fahimci abinda na gaya miki kuma sai a lokacin zaki biya ni kudin aikina da kanki ba tare da wani ya tuna miki ba" Ruqayyah ta mike da sauri tana jin uneasiness, wannan ai duba yake yi, malamin duba ne Minal ta kawo ta gurinsa. Ba tare da tace komai ba ta yi hanyar waje, tana zuwa bakin kofa yace "Allah ya sauke ki lafiya Ruqayyah. Ki gaishe min da Hassan da Hussainin da zaki haifa".

Babu shiri ta karasa fita tana hada hanya, tana shiga mota bata jira Minal ba tace da drivern su tafi, gabanta yana ta faduwa amma maganganun malamin suna ranta kamar yayi zane akan dutse.



Sunanan, malaman tsibbu da yan duba da suke yaudarar mutane da sunayen Allah da ayoyin Alqur'ani. Su ja su fassara maka amma su jaka ku aikata shirka tare. Mu kula, mu kiyaye, mu ji tsoron Allah.

Me zaki nema a gurin ubangiji wanda ke da kanki ba zaki iya tambayarsa da kanki ba bayan shine yace yafi jijiyoyin wuyan mu kusan ci da mu? Wacce addu'a ce da ba zaki iya yiwa kanki ko ki gayawa mahaifiyarki in tana da rai tayi miki ba har sai kinje gurin wani mai amsa sunan malami yayi miki?




Wannan littafin na siyarwa ne, in kin ganshi a wani gurin to na sata ne. In kina so ki karanta halaliyar ki to kiyi min magana ta wannan number din 08067081020*The Twins*

Sai da ta kusan zuwa gida sannan kiran Minal ya shigo mata, tana dagawa ta fara yi mata bala'i "shine dan kuturun wulakanci zaki tafi ki barni ko? Wato ke ga mai mota ko? Laifi nane ni da na dauko ki na kawo ki inda za'a taimaka miki. Kuma kinyi da yar halak in dai ni Amina kika yiwa haka wallahi zaki gane kim wulakanta ni a gaban mutane" Ruqayyah tayi ajjiyar zuciya tace "kiyi hakuri Minal, wallahi ba zan iya bane ba tsoro nake ji, kema ki daina zuwa gurin sa duba yake yi. Ko waye ya gaya mishi ina da ciki har zai gaya min abinda zan haifa? Ki bashi hakuri kawai ki ce ba zan iya ba" ga mamakin ta sai taji Minal tayi dariya tace "bai ji haushi ba ai. Yace in gaya miki kiyi kokari ki aiko masa da date of birth na Hassan da Hussain da kuma na Fatima, rana da wata da shekara, da su za'a yi amfani gurin yi miki adduar" Ruqayyah ta girgiza kai tace "ni fa babu abinda zan bashi, ban sani ba kuma ko na sani ba zan gaya masa ba. Ke da jin wannan kinsan malamin tsibbu ne irin su kuma sunfi boka hadari" Minal tace "if you say so bazan yi miki musu ba, ni dai nasan bai bani komai na binne ba kuma bai bani komai na barbada ba. Dan haka ni banga tsibbu a cikin abinda yake yi ba, besides, burika na suna ta cika tunda yanzu gashi yayi min albishir cewa Alhaji Ahmed ya kusa aikoda kudin aurena, daga na shiga gidan na haifa masa yaya shikenan gidan ya dawo hannu na matar sa sai dai ta bini da kallo kawai" suka yi dariya tare, Ruqayyah tace "Allah ya bada saa, amma nikan ba dani ba" suka yi sallama Ruqayyah ta karasa gida.

A compound din ta hango Hassan da Hussain suna tsaye suna ta magana suna dariya, daga gani suna cikin murna ne. Tana zuwa Hussain yace "yauwa gata nan ta karaso, shawara nake bashi cewa ya ke turo ki kullum kina zuwa kina gaishe ni ko Allah zai taiamake ku ku haifi yaya masu kama da ni, kin dan ni din fa kyakykyawa ne" ta tabe baki tace "Allah ko? Ni dai ban gani ba" yace "ohh baki gani ba? Zo muje in nuna miki" ya wuce gaba zuwa part dinsa Hassan yana binsa a baya yana cewa "kar kasa matata a cikin maganar nan walllahi ranka zai baci. In ka sake kayi forcing dinta tace ka fini kyau ko? Ni kadai nasan me zanyi maka" suka shiga palon Hussain, Ruqayyah ta tsaya daga bakin kofa dan bata taba shiga gurin ba sai yau. Ya juyo yana kallonta yace "common in, ki fadi kuma tsakanin ki da Allah waye ya cinye hoton nan" ta shigo tana kallon hoton da yake nuna wa.

Su biyu ne a hoton, kamar kuma a wannan palon akayi saboda taga kujerar irin ta palon ce, Hussain yana zaune akan kujera ya harde kafafunsa fuskarsa da murmushin da yake bayyana dimple dinsa, Hassan a tsaye a bayan sa, ya dora guiwar hannunsa akan kafadar Hussain looking as serious as ever. Ta danyi murmushi tana rarraba ido tsakanin fuskokin su, ita sai yanzu take kara tabbatar da kamannin da suke yi sai dai banbancin fatarsu tana boye kamannin nasu. Ta jiya tana kallon Hassan ya bata rai yace "don't say it" tayi dariya tana kama hannunsa "me zance? Ai ko makaho ya shafa yasan mijina yafi na kowa kyau" Hussain yace "kin dai so kanki kawai" ta dauke idonta daga kan hoton tana kallonsa yace "ka manta da maganar hausawa da suka ce so duka so ne amma son kai yafi?" Hassan ya zagayo tabayanta ya tsaya suka jeru shima yana kallon hoton yace "gobe za'a kawo mana namu, this is just a sample. Hussain ne ya saka aka yi mana wai za'a kafe a duk kamfanonin sa dan kowaya shiga gurin yasan su waye masu gurin" ya karasa maganar yana dora habarsa a kafadarta. "Kin san halin kanin naki". Ta dan yi murmushi a ranta tace "kai zaka fada amma ni ban isa in fada ba sai aji haushi a gaya min magana".

Bayan sun koma part dinsu ne Aunty ta aiko musu da abincin dare da kuma sakon cewa cook dinsu zata fara zuwa gobe. Suka zauna suka ci abinci yana tambayar ta ya mutanen gidan su suke, tana yi masa bayani amma hankalin ta yana kan maganganun wannan mai duban, yace dama zata same ta wadda zata iya zabar abu daya cikin biyu, ko dai ta zabi yin kudi fiye da kudin da take saka rai ko kuma ta zabi xama a karkashin masu kudi, bata bukatar amsa tasan idan lokacin yazo wanne choice din zata dauka, tabbas tasan kudi zata dauka dan shine babban burinta a duniya amma kuma abinda bata sani ba shine yadda zabin zai zo mata, yace zata yi rayuwar kadaici, wanne irin kadaici yake nufi? Indai kuwa har zata yi kudi to kuwa ai babu zancen kadaici saboda tasan mutane kamar magnet suke da kudi, duk wanda yake da kudi shine yake da mutane, misali Hussain da Fatima kullum gidan su a cike yake da mutane saboda suna da kudi, ita ma in ta samu irin wannan haka nata gidan zai ke cika irin nasu. To kuwa in dai abinda ya fada gaskiya ne then bata bukatar bata lokacin ta gurin korar Fatima ko raba Hassan da Hussain ko duk wani abu da yake on agenda din ta. But ita kanta tasan ba komai da yan duba suka fada ne yake zama gaskiya ba, kuma tasan yadda da abinda suka fada shirka ne saboda babu wanda yasan abinda gobe take tafe da shi sai Allah.

Washegari weekend, haka kawai Hassan ya tashi da aikin gyaran gida, sai yau ya gama kwashe kayansa daga tsohon dakinsa ya kuma shirya komai tsaf a dakinsa na yanzu. Ita dai tana ta binsa a baya tana yi masa hira har ya gama sannan suka yi wanka suka zauna breakfast. Bayan sum gama ne ya dauko littafi karami da biro ya zaunar da ita ya rubuta wasu adadin kudi a jiki yace mata "jiya anyi mana salary, wannan shine salary na" ta kalli numbers din mentally tana calculating abinda zata yi dasu ranar da tayi kudin da take saka rai, sannan ta kirkiro murmushi tace "masha Allah, Allah ya sa musu albarka" yayi murmushi yana jin dadi yace "ameen Precious. Yanzu kinga lissafi na shine, 50% zan ajiye, su zanke tara mana na ginin gidan mu" sai kuma ya shafa kai yana kallonta da murmushi a fuskarsa yace "though, ga babies kuma a hanya, but we can manage kudin su isa har hidimar babies din" ya cigaba da rubutu yace "20% zamu siya daily needs din mu, komai na bukatar gida da kuma personal needs din mu for a month, 10% zamu kaiwa Baba, 10% percent kuma ina so in bude miki account sai kike ajiye wa kema duk sanda kike bukatar wani abu sai dai kawai ki dauka ba sai kin tambaye ni ba. Ko zaki yiwa wani kyauta ko dai wani abu mai muhimmanci haka, kamar harkar makarantar su Zunnur zaki yi musu out of your pocket. Ragowar 10% din kuma sai mu ajiye a gida in case of emergency. Ya kika gani? Lissafin yayi?" Ta cire tagumin da tayi tun da ya fara lissafin sannan tayi murmushi tace "gaskiya baiyi ba, kusan komai a kaina zai kare? Kai kuma fa? Ni banji ka ware wasu kudade kace naka ba ne ba" ya dago kai yana kallon ta fuskarsa cike da yana yin da yake nuna yaji dadin maganar ta har cikin zuciyarsa yace "don't worry about me, kin manta all that 50% yana gurina? Sannan kuma already ina da kudade a account dina zan iya dauka inyi duk bukatu na. Ke dai kawai kiyi managing wanda zan baki. Kar kike siyan unnecessary things. Kin san yadda nake siyayya ta?" Ta girgiza kai yace "duk abinda na dauka zan siya sai in tambayi kaina "do I really need this? Can I live comfortably without this? Ko kuma da akwai wani abu da nake bukata more than this? Idan har na tabbatar bana bu™atar abin sai in ajiye shi inyi gaba. That is how I avoid unnecessary spendings" tayi dariya tace "nima na koya to, haka zan ke yi" ya shafa fuskarta yace "good girl" sai ya mike tsaye yana cewa "monday sai muje a bude miki account din ko? Bara in shirya in an jima zan kai su Hussain airport" tace "airport? Ina zasu je?" Ya juyo yana kallonta yace "Thailand zasu je, zai ji signing wani contract ne da wani kamfanin shinkafa a can" ya juya ya shiga ya barta da sakakken baki "kuturin kare! Wato mijin wata yana can yana daukan matarsa tana rakashi business kasar waje ni nawa yana lissafa min albashin sa a takarda?" Sai taji duk ranta ya baci, taji ta raina albashin nasa gaba ki daya ko da kuwa gabadayan sa zai bata.

Tana nan zaune har ya fito, yana daura agogo yana cewa "so nake in shiga gidan Aunty muyi rigima da ita, dama na gaya mata aure ba zai zaunar da Hussain a gida ba, in yayi auren ma daukan matar zai ke yi suna tafiya tare" sai kuma ya lura da chanjawar yanayin ta, yace "what's wrong?" Ta dago kai tana kallonsa, tace "babu komai, kawai dai zanyi missing din su ne" yayi mata murmushi sannan ya durkusa yayi kissing goshinta yace "kar ki damu, I will be here to keep you occupied" ya kashe mata ido, tadan dungure masa kai kadan ta juya baya tare da kwanciya akan kujera. Ya tashi yana dariya yace "sai na dawo. Please ki rubuta list din duk abinda muke bukata a gida kafin na dawo. Make sure you include everything. Ni kuma in na dawo zan biya in kaiwa Baba nashi kudin".

Yana fita taja tsaki. "Ni bansan wanne iyayin ne ma yasa Hussain ba zai dauki driver ya kaisu airport din ba sai yasa Hassan ya kai su sai kace wani yaron su" ta sake tsaki tana jin bacin ranta yana karuwa, sai kuma ta mike ta shiga daki ta dauko hijab ta saka ta fita. A part din Aunty ta same su suna ta magana suna dariya har da Fatima, ta gaishe da Aunty da take rike da hannun Fatima sannan ta gaishe da Hussain tare da yi masa fatan alkhairi. Tace da Fatima "yanzu kuma shine zaku tafi ko sallama babu?" Fatima tayi murmushi tace "ban san baki san da tafiyar ba ai, tun jiya nake ta zuba idon ganin kin shiga munyi sallama" Ruqayyah ta juya ido, wato ita ba zata shiga tayi mata sallama ba saboda ita yar sarki ce.....

Lokaci ya cigaba da tafiya, Ruqayyah ta lullube kanta da barguna na mutum mai kirki ta yadda a gurin Hassan ta zama the best wife he could have ever asked for, sometimes tana dan kwace mata ta dan saki baki haka ko tadan nuna halin ta kadan amma sai tayi saurin basarwa, shi kuma in hakan ta faru yana dangana hakan ne da maganar da Baba ya gaya masa na cewa Ruqayyah tana da zuciya tana kuma da saurin fada. Dai ya dage wajen ganin duk abinda tayi ba dai dai ba sai ya nuna mata ya kuma gyara mata ya gaya mata wanda zata yi dai dai din. Tsakanin ta da mutanen gidan kuma dai mutunta juna, duk da ita ta sani suma kuma sun san cewa ta sani sunfi son Fatima akanta saboda Fatima ta fita sakin jiki da su kuma ta fita kyauta. A tsakanin lokacin ne kuma Sumayya da Adam suka samu admission a tare suka fara zuwa makaranta, Hussain ne ya dauki nauyin komai na Adam, Baba kuma yabiya na Sumayya duk da cewa Adam ya so ya biya mata amma pride din Baba ya hana ya barshi ya biya din. Shigar su makaranta tare ta kara shakuwa a tsakanin su ta yadda

Please Login or Register in order to submit comment