Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita kan titi dan ji take kamar gawawwakin da suke cikin mota suna miko hannu zasu jata zuwa cikin sauran wutar da bata karasa mutuwa ba. Sannan kuma tana jin tamkar Fatima tana binta a baya, tamkar nemanta da tayi ra rasa ta zama fatalwa ne zata galaka ta saboda yar mata da yaron ta da tayi. A idonta take ganin kamar wulkawar Fatima ta gefenta, in kuma ta rufe idon ko da da niyyar kifta shi ne sai taga idanun Minal suna kallonta kamar yadda ta ganta a cikin mota a mace. Ga kafa ta rike, sam taki lankwasuwa sai janta takeyi ta sandare kamar wani ita ce. Duk kuma wannan da sauki akan abinda take ji a zuciyarta, wani irin feeling wanda ba zata iya misalta shi ba.

Ta fara tuno masoyan ta, aan ta guda uku, Sumayya, inna Ade da Baba, suleiman da Zunnur dan duk abinda take yi, duk wannan fadi tashin da take yi da wannan dakakkiyar zuciyar tata amma ita kanta ta san tana son su sosai sai dai kawai ita bata iya nuna soyayya ba, ga kuma Hassan , da kin ta da sonta he have come to be part of her, ba zata ce tana masa so na soyayya ba amma ta damu dashi. Ta runtse idonta tana matse hawayen daya taru a idonta yake disashe mata ganin ta amma kuma hoton fuskar Minal data gani shi ya saka ta yi saurin bude idon tana kokarin kara sauri ama kafa taki bada hadin kai. Gani take kamar gawawwakin ne suka rike mata kafar. A kunnuwan ta har ji taje yi kamar ana maganganu kasa kasa. Sai kuma taji kukan jaririn data ajiye yana amsa kuwwa a kunnuwan ta.

Kuka take yi sosai, tana kokarin yin sauri iyakacin iyawarta amma in ta waiga sai taga babu inda taje, still bata wani yi nisa da motar ba. Sai data kwashe lokacin da a gurinta kamar ya kai tsahon shekara guda sannan taji gunjin mota tana shigowa gurin, sai kuma taji hayaniyar mutane sannan taga an haske ta da fitila. Hasken da ta ji shi har cikin zuciyarta, ta sauke ajjiyar zuciya tana tunanin karshen wahalar ta yazo. But that is just the beginning.

Tana ji suka karaso inda take suka kamata suka sakata a motar da suka zo da ita sannan wasu suka tafi gurin accident din suna kokarin karasa kashe sauran wutar da take ci, tana jin su suna ta yawa suna fadar abinda ta gani, sun dan fara yi mata tambaya amma ganin yadda take a rikice yasa wani wanda take tunanin shine babban su yace su rabu da ita kawai, a lokacin wata motar ta karaso kamar ta fite service da kuma wata karamar mota again, taji suna ta maganar abin taji kuma sun ambaci mutuwar Hussain, sun kuma fahimci abinda take so su fahimta na cewa Fatima matar Hussain ce a cikin motar, sun kuma fahimci wacece Fatima dan take taji wani yana waya Kano cewa a sanar da gidan sarautar kano sunyi rashin yarsu, gimbiya Fatima.

Ta lumshe idonta tana jingina da jikin kujerar motar, the dead is now complete, ta haka ta binne sirrinta babu gudu babu ja da baya, amma kuma ina Fatima take? In kuma bata mutu ba fa? In kuma tashi tayi ta tafi fa? In kuma yanzu already tana hanyar Kaduna kuma fa? In ta fada tace ta haihu ta bawa Ruqayyah dan ya zata yi kenan? Me zata ce?

Ta girgiza kanta da sauri tana cewa "uhm uhm" a fili kamar wata zararriya. It is going to be her words against fatima's. Zata musa ne da duk iyakacin iyawarta tace ita bata karbi da ba, tace Fatima sharri take yi mata. To amma kuma in aka tambayeta game da gawar da take cikin mota wadda ta riga ta furta cewa ta Fatima ce fa? Me zata ce akan hakan? Tabbas bata haa ta binne sirrinta ba, tabbas yana nan a bude kuma yana tare da Fatima a duk inda take. But What if ta mutu da gaske wani ne ya dauke gawarta, ko matsafa, ko naman daji? There is still hope for her amma bata da tabbas, kuma tasan wannan rashin tabbas din tabbas zai ke hana ta bacci. A koda yaushe, Fatima zata iya bayyana kuma bayyanar ta yana nufin bankaduwar sirrinta.

Wannan kuma yana nufin rasa komai nata.........

Including iyayenta, dan tasan direct Baba zai tsine mata inna Ade kuma tace babu ita babu ita har abada

But for now, shin gawar Minal tayi konewar da ba za'a Iya gane ta ba? Ta tambayi kanta tana lekawa ta taga, kamar amsar tanbayarta taji wani a gurin yana cewa. "Ayi wa yanuwansu waya, sai dai a binne su anan dan ba zasu dauku ba, sun zama gawayi" ta lumshe idonta da niyyar yin ajjiyar zuciya amma fuskar Minal data gani ya saka ta bude idon da sauri.

Motar da take ciki aka bawa umarnin ta tafi, a kaita Kaduna gidan mijinta, wannan yasa taji hankalin ta ya kwanta, sai dai suna barin gurin ta juya tana kallon gurin. A nan ne rayuwarta ta kare, anan ne kuma rayuwarta ta fara. Su Kusan rai shida suka bar Kaduna a mota, amma a cikin su ita kadai zata koma garin Kaduna.

***************. **********. **********


Da taimakon maaikacin lafiyar da yake cikin ambulance din Hassan ya fara dawowa hayyacin sa, amma sai dai shi har cikin zuciyarsa bai so dawowar tasa ba, so yake ya tafi shima, so yake yabi Hussain, baya so ya cigaba da rayuwa. Wannan wacce irin jarabawa ce uban giji yake yi masa?

Ya kamo hannun Hussain ya rike "Hussain! Ka tafi dani nima mana! Hussain Fatima ta bika ka roka min ubangiji nima ya dauke ni in biku! Hussain Fatima ta tafi , ta taho tare da abinda yake cikin ta. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" duk rarrashin duniya babu wanda ba'a yi masa ba amma ya kasa yin shiru. So yake wai maybe in ya ishe su da magana su gaya masa cewa ba gaskiya bane ba, su gaya masa Fatima da abinda yake cikinta suna raye, su gaya masa Ruqayyah ba gaskiya ta fada ba ko kuma anje an tarar basu mutu ba but instead of su ce haka sai yaji suna waya da yanuwansu na can akan a gaya masa gawar Fatima ba zata dauku ba sai dai a binne ta a can.

Girgiza kansa kawai yake yi, so yake yayi kukan amma ya kasa sai magana kawai yake yi da gawar Hussain kamar wani tababbe. Tabbas mutuwar Hussain ta taba shi amma bata yi masa dukan da wannan ta Fatima tayi masa ba. Saboda dama yasan Hussain bashi da lafiya, kuma a hannun sa ya mutu. Amma Fatima fa? Hussain yana mutuwa ba abinda yake so sama da abinda yake cikin Fatima amma ashe ko ganin sa ba zai yi ba, ashe ko numfashi ba zai shaka ba. Wannan wacce irin jarabawa ce? Anya zai iya ci kuwa? Ace a rana daya babu Hussain babu family dinsa? Babu komai sai memory dinsa?

Memory mai dadi.......
Memory mai zafi.......
Memory mai tsayawa a zuciya......

Yana jin wayar Hussain tanata ringing amma ya kasa kallon ta ma ballantana yayi tunanin dauka. Ba zai wuce mutanen gidan su ba, ba zai wuce aunty ko yan uwansu ba, sun kira shi suji da gaske ne? Da gaske Hussain dinsu ya tafi ya barsu? Da gaske Fatima tare da babyn su sun bi shi inda ba'a dawowa?

Ba zai iya amsa musu ba.....
Ba zai iya kallon wayar ba.....
Ba zai iya kallon hoton Fatima hannayenta a dafe akan cikin ta tayi shape din heart da yatsunta a kan cikin ba, wanda shine hoton da yake kan wayar.

Sai ya saka hannu ya kife wayar, baya jin zai iya magana da kowa.

Ya tuno da nasihar da Adam yayi masa dazu "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya fara fada yana maimaita wa hannunsa biyu rike dana Hussain "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" sauran mutanen motar suka cigaba da tay      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  a shi har suka iso Kaduna suka je gida.

********. *********** *****

Tun tafiyar su Hussain Aunty take zarya a falo, in ta hau sama sai ta sauko sai ta kuma komawa sama ta kwanta sai ta tashi ta dawo kasa ta zauna. Ta rasa me yake yi mata dadi. Su Zulaihat suna kallo a palo ta kora su daki ta kashe kallon, ji tayi bata son karar tvn, bata son karar komai.

Ta jima a nan sai kuma ta koma sama ta saka hijab dinta ta fita da niyyar shiga part din Hussain ta duba gimbiya Fatima, dama tunda cikinta ya girma kullum sai taje ta dubata. Sai dai a compound din gidan ta hadu da maigadi wanda yayi mata bayanin cewa ai Fatima bata nan yaji Lawan driver yace tace zai kaita Abuja "tare suka tafi da Aunty Ruqayyah"

Wannan yasa a take ta dauko wayarta ta kira Hussain dan taji dalilin da zaisa ya bar Fatima ta bi bayansa da tsohon ciki. Sai dai Hussain din bai dauka ba sai Hassan, ta gaya masa abinda ake ciki sannan ta koma gida ta cigaba da zaman jiran dawowarsu.

Har magrib tayi, sai ta kuma dauko waya ta kira Hassan amma bai dauka ba, ta kira Fatima not reachable Ruqayyah switched off. Ta kira Hussain shima ba'a dauka ba. Hankalin ta yayi dubu ya tashi, ta shiga dakin Khadijah ta tarar da ita a kwance wai zazzaSi takeyi, ta dafa jikin ta taji zafi sosai, sai ta koma dakinta ta dauko mata magani ta taho da niyyar zata bata sai taga kira daga Bauchi. Babban yayan su Alhaji Lukman, tayi gyaran murya ta dauka tana gaishe shi, sai taji yayi shiru kafin ya amsa sannan yace mata "duk kuna gida tare da yara?" Tace "eh" tana mamakin tambayarsa, sai yace "shikenan ku zauna a gidan gamu nan tahowa komai dare insha Allah" sai ya kashe wayar ya barta da sakakken baki. Me zai zo yayi komai dare? Koma menene a barwa gobe mana?

Ta samu gefen gado ta zauna kusa da kafafuwan Khadijah tana cigaba da kiran number din Hassan da Hussain amma duk babu wanda ya dauka. Ta gaji ta tashi ta daga window tana hangen titi ko zata hango tahowar su amma babu alamar su.

A lokacin ne taji an rusa ihun kuka da muryar Nafisa, taji wani abu ya tsirga mata tun daga kanta har tafin kafarta. Taji wani irin daci a makwogwaron ta. Sai taji sautin kukan Nafisa yayi mata kama da sautin kukanta a lokacin mutuwar Alhaji Aminu uban aan ta.

Khadijah da take kwance ta mike da sauri ta tafi dakin Nafisa tana hardewa, a hanya suka hadu da Zulaihat itama tana dosar dakin Nafisa. A dai dai lokacin Aunty taga tsayawar ambulance a kofar gidan. Ta sandare a gurin tana kallo aka bude gate aka shigo da ambulance din sannan akayi packing aka bude baya, taga police sun fito, sannan taga Hassan ya fito amma bata ga Hussain ba sai taga an turo gado da wani abu da yayi kama da gawa akai. Ta saki labulen sannan a hankali ta zame ta zube a gaban tagar.

Hassan yabi gawar Hussain da kallo ya tabbatar an shiga da ita ciki sannan ya juya gurin limamin unguwar su da ya biyo bayan motar rasu. Ashe har sun samu labari sun zauna jira. Hussain mutumin kirki.

Liman yace "dare yayi yanzu, sai dai yayi kwanan keso sai da safe ayi masa sallah" Hassan ya gyada kai kawai. Liman din yace "da assuba zan tura aje makabarta a haka kabari, yanzu kuma zan sika a siyo likkafani, sai asa lokaci saboda yan uwanku su sami sallah" sai Hassan ya girgiza kansa yana kallon garden din gidan, inda tun suna raya suke yin shuke shuke shida Hussain har suyi rigima in wani ya tabata wani yace "anan za'a binne shi, a cikin garden din mu. Nayi masa alkawarin zanke zuwa kabarinsa kullum ina masa addu'a. Anan za'a binne shi a kusa dani"


Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta WhatsApp through wannan number 08067081020

Sorry about the typos please

Mai sharing littafi, bana ganin ki Amma *Allah* yana kallon ki kuma na barki da shi*Hidden Strength*

Sumayya yau bata tashi daga school ba sai da akayi kusa kiran sallar magrib. Ta gaji likis saboda yau sun safe suke lectures babu kakkautawa, dan yau sau daya taga Adam shima briefly yazo wai zasuyi sallama zai je Abuja tare da oga Hussain. Tana murmushi tave masa "kwana nawa zakuyi?" Yace "yau zamu dawo" tace "yau zaku dawo din shine harda sallama?" Ya langwabe kai "kika sani ko kawai so nake yi in ganki shine na fake da sallama" ta dan rufe fuska da mayafi, ya kama mayafin yana leka fuskar. Ta rufe idonta "ka bari fa" yace "ni ba zan bari ba, kallon fuskarki ma yanzu na fara" ta kwace mayafinta tana kara rufe fuskar dashi, yayi murmushi yace "kinsan wani abu?" Ta girgiza kai, yace "so nake in mun gama semester din nan inyi wa oga Hussain maganar mu, so nake a fara maganar auren mu tun yanzu ba wai sai mun gam school ba tunda kinga ai ina da aikina kuma ina samun kudi ba laifi, tunda na fara aikin kuma nake tarawa ba wani abin nke yi dashi ba. In nayi masa Magana nasan zai yi min jagora a maganar auren insha Allah"

Sai taji ranta yayi mata dadi, zuciyarta tayi fari tas, yace "kin amince da hakan?" Ta gyada kai tana murmushi, still fuskarta a boye, ita da ace amimcewarta kadai ake bukata da zata iya auren Adam ko da bashi da wannan aikin, koda sadaki kadai zai bayar babu lefe babu komai, thats how much take son shi. Da zasu rabu ya jaddada mata "you know I love you right?" Ta danyi murmushi tana kallon cikin idonsa ta gyada kai, sannan kuma kamar ba zata yi magana ba sai tace "and I love you too".

Har yanzu, har bayan ta wuni sir a makaranta ta dawo gida a gajiye da yunwa da ishirwa amma bata daina jin kaifin kallon da yayi mata a jikinta ba. Tana cin abinci tana zuba murmushi ita kadai, tayi sallah tayi wanka ta fito tama shiryawa Inna Ade ta shigo tana kallon ta. "Ke kuma fa kike ta farin ciki kamar anyi miki albishir da kujerar makka? Au ashe ba kinje, dan haka ba lallai ne ma kiyi farin cikin da kike yi yanzu ba" samayya tayi dariya, "haba Inna, farin ciki ma kuwa ai har marar misaltuwa zanyi in za'a mayar dani in sake ganin Ka'aba. Amma dai duk son da nake yiwa komawar in dai aka bani a yanzu sai dai in baki ko Baba tunda ni na sauke farali" Inna ta zauna a gefen gado tace "to gaya min abind yake saka ki wannan farin ciki haka"Sumayya ta zauna a kusa da inna tana kare mata kallo. Cikin yan shekarun nan da suka dawo gidan nan baba kuma ya samu aiki duk Inna ta chanja, jikinta ya murmure sosai babu wannan muguwar ramar fatarta tayi kyau tayi haske, kyawunta ya sake fitowa sosai. Sai Sumayya tace "kawai dai ina duba rayuwa shine naji raina yayi dadi sosai. Ina duba halin da mutanen da nake tsananin so suke ciki misali ku Iyaye na, Ruqayyah, kannena da sauran su duk kowa yana cikin rayuwa mai kyau sai naji zuciya ta tayi dadi sosai" Inna tace "banji kin lissafa da Adam ba" Sumayya ta sunkuyar da kai, Inna tace "ko shine da sauransu din?" Sai Sumayya ta rufe fuskarta, a dai dai lokacin wayarta tayi kara, ta bude idon ta tana kallon bakuwar number din da bata sani ba sannan ta dauka a hankali tare da sallama "Assalamu alaikum" daga daya barin taji muryar Ruqayyah "Sumayya nice, yar uwarki Ruqayyah ce. Accident muka yi ni da m.......... nida Fatima, Allah ya musu rasuwa ita da driver. An tafi dani asibiti ni kuma"

Sumayya ta zaro ido cikin tashin hankali "accident? Mutuwa? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ya kike Ruqayyah me ya same ki ke? Wanne asibitin?" Ta jera mata tambayoyin cikin tashin hankali. Ruqayyah tace "da sauki. Asibitin da nake haihuwa. Ki gaya wa su Inna" sai ta kashe.

Inna Ade da dama tun da taji Maganar accident ta mike tsaye tana kallon Sumayya tace "me ya samu Ruqayyah? Hatsari suka yi?" Sumayya ta gyada mata kai already hawaye yana zuba a idonta tace "hatsari sukayi wai Fatima ta mutu. Allah sarki Fatima. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ta fada tana neman hijab dinta. Sannan suka fito palo tare da Inna ita kuma tana nemna waya ta kira Baba ta gaya masa zasu tafi asibiti gurin Ruqayyah, a lokacin ne shi kuma baban suka shigo sun dawo daga masallaci tare da Suleiman. Sulaiman yana goge hawaye, Sumayya tace "kunji labarin kuma ko? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah yaji kan Fatima" Baba yace "wacce Fatima ce kuma ta rasu? Mu yanzu ake gaya mana mutuwar yaron nan dan uwan Hassan. Hussain. Yanzu aka kawo gawarsa daga Abuja"

Sumayya ta dora hannu aka Baba ya daga mata hannu, "kar kiyi, ba da haka zaki nuna wa Ubangiji godiyar ki daya baki rai shima ya bashi rai sannan ya addara saduwar ku a duniya ba" Sumayya ta sauke hannnun tana sheshshekar kuka, Inna Ade tana tayata. Sannan Inna ta gaya musu kiran da Ruqayyah tayi musu da sakon data sanar dasu. Nan take suka shirya gabaki dayan su suka hau Napep din Sulaiman suka tafi asibitin.

Asibitin da aka kai Ruqayyah dana shine asibitin da suke zuwa, dan hka suna zuwa ba tare da wani matsala ba aka karbe ta aka bata taimakon gaggawa kafin karasowar likita. Kafin likitan yazo su Baba sunzo, sun kuma ji dadin yadda suka ganta complete ba tare da ta rasa wani abu na jikinta ba a hatsarin da ita kadai ta fita da rai. Wannan babban abin godiya ga Allah ne. Bayan likitan yazo yayi mata complete check up sai ya fahimci ko karaya bata dashi sai tarkade a hannun ta na hagu wanda ita Ruqayyan ma bata san dashi ba sai kuma ciwon da taji a cinyarta, wanda karfe ne ya soke ta a gurin. Amma problem din shine complain da take yi cewa kafar ta makale, ta kuma fadi cewa farkon data tashi tana iya motsa ta amma yanzu ta kasa. Sai doctor din ya rubuta mata hoto da za'a yi mata a kafar da safe yadda za'a fi ganin komai. Daga nan ya barta aga yanuwanta.

A gurin su ne ta kuma tabbatar da labarin mutuwar Hussain. Ita kuma tana kuka tana basu labarin mutuwar Fatima "tunda na tashi dama na fahimci cewa ta mutu, nayi nayi kokarin in fito da gawarsu daga cikin motar ita da driver amma na kasa, ga wuta kuma ta kama" sai ta rufe fuskarta tana rusa kuka Sumayya tana taya ta. Tace "wuta ta kone su kurmus. Ance ma ba za'a iya dauko gawawwakin su ba sai dai a binne su a can" Sumayya ta share hawayen ta tana tuno kyakykyawar fuskar Fatima, sai kuma ta kara karfin kukanta data tuno da tsohon cikin da Fatima take dauke dashi. Dai kuma Hussain, ta tuno ganinta dashi na karshe sanda taje gidan ta hadu dashi. Cikin barkwanci irin nasa yace "Sumayya kin kuwa san gimbiya ta tsohon ciki ne da ita?" Tayi dariya Tace "na sani mana, na shiga ai mun gaisa" yace "to ki je gida ki fasa bankin ki ki tattara kudaden ki ki sayi lace dan yayi ki kai wa tailor yayi miki dinkin zamani dan suna ne za'a yi shi irin wanda ba'a taba yin irinsa a garin kaduna" sukayi dariya gaba daya. Yanzu gashi babu shi babu matar babu dan. Duniya labari, duniya zancen banza, duk wanda ya dauke ta gurin zama tabbas yana tare da babbar nadama.

Baba ne yace da Inna Ade tazo su tafi gidan mutuwar, Sumayya kuma da Sulaiman su zauna a gurin yar uwarsu a asibiti gobe sa je suyi musu gaisuwa. A gidan mutuwar ne suka tarar da abin mamaki, layin gabadaya a cike yake da mutane maza da mata daga lunguna da sakuna na garin kaduna, wasu a zazzaune wasu a tsatstsaye kowa yana addu'ar samun rahama ga Hussain da iyalinsa saboda Hussain yana da wata al'ada ta kyautata wa duk wanda ya hadu dashi dan yana cewa

"ita haduwa kaddara ce, rabuwa dole ce. Duk mutumin da ka hadu dashi a rayuwa to kayi amfani da wannan damar wajen kyautata masa dan babu tabbas din zaku kuma haduwa, ko baka bashi komai ba kayi masa magana mai dadi, ko baka yi masa magana mai dadi ba kayi masa murmushi dan shima sadaka ne"

Cikin gidan kuwa da Inna ta shiga dakunan duk a bude suke kuma duk da mutane a ciki duk kuwa da cewa yan Gombe basu karaso ba, kowa kuka, musamman ma'aikatan gidan da suke ganin ba zasu kuma samun wani uban gidan kamar Hussain Aminu Abdullahi ba.

Labarin Mutuwar Fatima ya dira tamkar kibiya a zuciyoyin iyayenta, yanuwanta da masoyansa ta. Nan take masarautar kano ta hargitse kowa kukan rashin Fatima musamman da suka ji irin mutiwar da ake tunanin tayi. Wai ko gawar ta ba zasu gani ba, wai ko sun gani din ma ba zasu gane taba saboda ta zama gawayi. Fatimah dai ta su, Fatima da suke ji da Ita tamkar kwai ita ce ta mutu kuma wuta ta kone ta. Wannan wanne irin tashin hankali ne?

Mai martaba sarki duk da cewa ya dimauce ya gigice da alhinin mutuwar yar tasa amma duk da haka sai ya hada kan ya'yansa maza gabaki daya suka hau jirgi a daren suka tafi Abuja. Da assuba suka yiwa gawar da suke tunanin ta yar uwar su ce sutura tare da ta driver aka yi musu sallah sannan aka binne su a gurin da suka mutu. Daga nan kuma sai ya juyo ya koma kano dan fara karbar taaziyya daga mutanensa, yayan sa kuma ya tura su Kaduna dan su halarci jana'izar Hussain wadda aka daka karfe goma sha daya na safiyar asabar.

Abinda yake bawa kowa mamaki a gidan gaisuwar shine Hassan. Da kansa yayi wa gawar Hussain wanka ya kuma suturta ta tare da taimakon limamin gidan tun cikin dare. Kallonsa kadai idan kayi ya isa abin tausayi amma zuciyarsa tana tsaye. Yana zaune a gaban gawar yana yi masa addu'a kamar yadda cikin gidan da wajen gidan yake cike da mutane da suke masa addu'a har gari ya waye. A lokacin yan Gombe suka karaso, dangin maman su da dangin babansu. Da gari ya waye ne Hassan ya kira Aunty, wadda duk ta gama fita daga hayyacinta, tare da dukkan yan uwansu mata su biyar yace su zo suyi sallama da Hussain. Kuka suke suna karawa, haka yahada su ya rungume duk a jikinsa in ya share hawayen wannan sai ya share na wannan yana cewa "ku daina masa kuka kuyi masa addu'a, ku ringa cewa innalillahi wa inna ilaihir rajiun zaku ji sanyi a zuciyoyin ku" sai daya kaisu sannan ya dawo ya kama Aunty da kyar ya daga ta ya tafi daita itama. Suka zagaye gawar Hussain suna ta karanta masa suratul ikhlas suna maimaita wa, yadda suke kallon Hussain a kwance a cikin likkafanin sa duk sai sukaji duniyar gaba ki daya ta fita a kansu, suna tuno da sutturu irin na Hussain wanda baya saka kaya idan ba na

Please Login or Register in order to submit comment