Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

going to miss a lot." Ruqayyah tana jin tunda akayi auren yau ne Hussain yayi addressing dinta directly.

Ta tura kujerar ta baya tana mikewa, abinda yasa Hassan shima mikewar yana tambayarta lafiya? Aunty ma tace "lafiya Ruqayyah? Ko abincin kirki baki ci ba" Tace "bana jin dadi ne sosai, wannan tuwon kamar bai karbi cikina ba. Zan dan koma gida, Aunty sai da safe" Aunty tace "ki je ki kwanta to, Allah ya baki lafiya, zan aiko miki da wani abu ki ci ko tuwon ne ba kya so".

Hassan bai zauna ba ya bita da sauri a baya, amma saboda saurin da take yi da kyar ya kamota har ta kai kofar karamin gate din da ke tsakanin part din su dana aunty. Ya ruko hannunta "Hassana" ta juyo, tun daga idanuwan ta yasan ranta a bace yake yace "lafiya wai? Menene yake damun ki?" Ta juyo gaba daya tana rike kugu, tace "me akayi min? Okay yanzu na gane inda problem din yake" ta karbe hannunta tana kara sauri. Baya son ya ja hankalin ma'aikatan gidan zuwa kansu, dan haka sai ya rabu da ita ya koma cikin gida ya karasa cin abincin sa duk da hankalin sa yana kanta. Yana gamawa ya tashi ya tafi gida. A daki ya tarar da ita tana kwance da waya a hannunta. Ya zauna a kusa da kafafuwanta yana mammatsa mata su yace "ya jikin naki? Hope kinji dadi yanzu" ta ajiye wayar tana tashi zaune tace "naji dadi, dama tuwon ne naji ya tsaya min a kirji ya ki karasa wa" yace "akan maganar tafiya honeymoon ne? In kina so sai muje, bana son mu biyewa Hussain ne " Ta girgiza kai tace "I don't care about honeymoon, in baka so muje ba zamu je ba, duk abinda kake so shi zamuyi. What i care about is you mijina. Raina ya baci ne saboda naga ana neman a gaya maka magana a cikin mutane" ya dan bata rai yace "magana kuma? Wacce irin magana kike magana akai Precious?" Ta bude ido Tace "wai baka ji abinda Hussain ya gaya maka bane ba? Mr Tsimilmila fa yace maka, it is insulting ni a ganina" sai taga yayi murmushi sannan yayi dariya yace "my dear precious wife. Ba magana Hussain ya gaya min ba kinji? Wasa yake min, tun muna yara, tun primary school yake gaya min haka, mr Tsimilmila ko mr Careful duk haka yake ce min in yana so ya zolaye ni" ta daga kafada "okay, maybe dan ni macece shi yasa naji raina ya baci akan hakan, kasan mu mata muna da daukan karamin abu mu mayar dashi Babba. Dan haka ko da ace yana gaya maka haka a tsakanin ku bai kamata ya gaya maka a gaban mu ba, musamman a gaban matarsa, wannan ai sai ta zo ta raina ka tana yi maka wani kallo da daban, ni kuma ba zan iya tolerating wannan ba in tayi min na kyaleta bazan kyaleta ba in ta taba min mijina" Hassan yace "hold it! Fatima tana yi miki wani abu ne?" Ruqayyah ta koma ta kwanta sannan tace "bana son in fiya complain ne shi yasa ban taba gaya maka ba. But dama ya kake tunanin yar sarki zata yi treating yar mai gadin kamfani? Kamfanin ma kuma na mijinta. But ni ban damu ba ......." Ya kamo ta ya tayar da ita zaune, idanunsa suna nuna bacin ransa yace " yar sarki da yar mai gadi, dukkan ku matsayin ku daya a gidan nan, duk kan ku zaman aure kuke yi a gidan nan. Daga yanzu duk ranar da ta kara miki ko da kallon banza ne ki gaya min ni kuma zan nuna mata cewa she is no longer in her father's palace"

Wannan littafi na siyarwa ne, in kina so ki yi min magana ta WhatsApp through this number 08067081020Da fatan munsha ruwa lafiya, Allah ya karbi ibadun mu ameen.

Not edited
Ruqayyah tace "uhm uhm, ni bance kayi mata magana ba, kar taga kamar na hada ta da kai, ka barni da ita kawai ni ce dai dai yin ta va kai ba" sai kuma tayi murmushi tana ratayo hannunta a wuyansa "sorry mijina, na bata maka mood dinka" ya danyi mata murmushi yana shafa gefen fuskarta, kullum kyau take kara yi masa yace "kar ki kula ta kema kinji, ki fita daga harkarta kawai bana son wani abu ya hada ku saboda Hussain. Kinji? Promise me ba zaki kulata ba, one day zaiyi realizing abinda ya auro cos na gaya masa tun dadewa. I warn him about her" tayi ajjiyar zuciya tace "shikenan, duk abinda kace shi zanyi".

Ya mike ya fita sai gashi da system dinsa ya dawo, ya zauna akan kujera tare da kiranta "Precious zo ki gani, kinga guraren da Hussain yake son muje. In kina so sai mu bi su mu tafi tare" ta taso ta zauna a gefen sa tana kwanto da kanta jikinsa, ta karanta sunayen guraren, ita ko sunan ma vata taba ji ba kuma bata san wadanne kasashe bane ba. But koma ina ne tunda har jirgi za'a shiga a bar kasar nan ai kuwa va za'a barta a baya ba. Amma sai ta boye excitement dinta tace "ba naji kace ba zamu je ba?" Yace "in kina so sai muje" tace "ina ganin muje din kawai, kar Hussain yaji babu dadi, kaga har ya kai kararka gurin Aunty" yace "ai ya riga yasan saboda menene. Ni bani da lifestyle irin nasa" sai kuma yayi murmushi yana kallon dan karamin bakinta yace "but since we are talking about a honeymoon tare da ke, I think I can make an exception" lips dinta suka bude tana murmushi, yayi murmushin shima yana kallon fuskarta, duk wata damuwarsa tana wucewa tare da murmushin ta. "I am going to enjoy this" ya fada yana jan fuskarta zuwa gare shi.

A gurin Aunty Fatima tayi hirar darenta, Hussain yai ta zungurin ta akan su tashi su tafi tana share shi. Sai ya mike yana kirkirar hamma "na gaji sosai yau din nan. Aunty sai da safe zan tafi in kwanta" Aunty tace "Allah ya bamu alkhairi" ya kalli Fatima yace "sai da safe" ta dauke kanta tana kokarin rike dariya. Yana fita Aunty tace mata "tashi ki bi mijin ki, dan ba ta ido ce dashi ba zai iya sake dawowa ya sake yi mana wata sallamar" Dole Fatima ta mike Khadijah da Nafisa suka raka ta har kofar part dinta.

Tana shiga ta amsa gaisuwar bayinta su biyar da suke da dakuna a karamin palonta na kasa, inda anan din ne dai kuma yan aiki da Aunty ta bata suke. Sai data dan yi hira dasu kadan sannan ta wuce kitchen. Yarinyar ta da taje da hakkin kula da kitchen ta bita a baya da sauri, suna shiga ta tambaye su abincin da suka dafa, ta gaya mata sai ta yamutsa fuska tana girgiza kai sannan ta bude freezer ta saka yarinyar ta dauko kaza, tace "ina irin pepper soup din nan da muke yi a gida mai dankali?" Yarinyar ymta gyada kai da sauri tace "shi za'a yi miki? Yanzu kuwa zanyi miki" Fatima tace "shi zakiyi, amma bani zaki yi wa ba in kin gama ki zuba a mazubi mai kyau ki je ki kaiwa Ruqayyah kice gashi in ji ni" da sauri ta amsa da "to ranki ya dade, an gama" daga nan Fatima batakuma tsayawa ba sai turakar mijinta.

A dakinsa ta same shi daga shi sai towel yana ta zagaye da waya a hannu. Ya juyo yana kallomta sai ya yar da wayar ya rike kugu, ta jingina da jikin kofar tana murmushi yace "da baki taho ba ko, da zuwa zanyi in dauko ki aka tun daga gaban Aunty har nan" ya fada yana nuna kan gadon sa. Ta bata rai tana kallonsa tace "na yi fushi, shine kayi wankan ka ka rabu dani ko?" Ya tako zuwa gabanta yace "waya gaya miki nayi wanka? Ni na isa? Ta yaya zan wanke baya na?" Ta dan taba gashin kansa tana dubawa ko da ruwa a jiki, yayi dariya yace "banyi ba fa na gaya miki" tace "da kayi wanka ka barni ko, da yau ba zanyi wanka ba haka zan kwanta" ta fada cikin shagwaba. Ya jawo ta zuwa jikinsa, hannunsa a bayanta yana zuge zif din rigarta yace "na gaya miki ai, ba zan sake wanka ni kadai ba" ta fara dariya kuma sai ta dauke wuta saboda hannun sa da taji a cikin rigarta.

Bayan Hassan ya gama nunawa Ruqayyah guraren da zasu je sai ta sake komawa dakinsa zai mayar da system dinsa, a lokacin ne ta jiyo maganar mutane daga waje, ta daga labuke ta leka window ta hango Fatima dasu Nafisa a kofar gidan Hussain, sai taga su Nafisa sun juya sun koma Fatima kuma ta shiga. Ta tabe baki, wayo gimbiyar ba ma zata iya tahowa ita kadai ba sai an take mata baya, amma ita sanda zata taho ai babu wanda ya rako ta duk kuwa da cewa ta nuna bata jin dadin jikinta. Ta fara kokarin cire kayanta da niyyar yin wanka, so take yau tayi amfani da rashin lafiyar da take ji ta gudu daga gadon Hassan. Tana fitowa daga wankan Hassan ya dawo dakin, shima har yayi wankan sa ya saka na bacci, ya bibta da kallo tana shafa mai a jikinta. Ya karaso yana karbar robar man. "Menene aiki na a gidan nan idan har na barki kina shafa mai da kanki" ta dan bata fuska "shafa mai ai ba aiki bane ba, zan iya da kaina" yace "akwai guraren da hannun ki ba zai kai ba. Ki kawo in shafa miki ko ina da ina, in tabbatar ko ina ya samu" ta lura da irin kallon da yake yi mata sai ta dan rike cikin ta kadan tana yamutsa fuska. Yace "ya dai? Ko cikin ne?" Tace "dazu ma sai da nayi amai, kuma yanzu yunwa nake ji. Ni tunda aiki kake nema ma da abinda zanci ka samo min" ya dan shafa kansa kadan yana kallon kirjinta "kuma shafa man fa?" Ta tura baki, ni ina jin yunwa ina zan damu da wani shafa mai" yayi ajjiyar zuciya "shikenan, let me go and get you something". Ta bishi da ido har ya fita, sannan tayi dan karamin tsaki. "Duk an bi an lugwuigwuicewa mutum jiki an bar ni da ciwon jiki".

Key din mota Hassan ya dauka ya fita, bai ma san inda zai samu abinci ba, shi ba mutum ne da ya saba da cin abinci a waje ba dan haka bai san guraren cin abinci ba. Yana fita yarinyar Fatima tana kaiwa Ruqayyah abincin da ta aika mata dashi. Tata yarinyar ta karba sannan ta hau dashi sama saboda ta ga fitar Hassan, ta shiga dan madaidaicin dining area dinsu ta ajiye sannan taje tayi knocking a kofar Ruqayyah, sai data ji tayi magana sannan tace "sako ne gimbiya Fatima ta aiko miki dashi". Sai da Ruqayyah ta gama shafe shafen ta sannan ta saka doguwar rigar bacci wadda ta tsaya a gwuiwar ta mai siririn hannu ta fito tana daure kanta da ribbon, a ranta tana mitar tunda tazo gidan kullum sai ta wanke kanta gashi har gashinta ya fara lalacewa. Ta bude warmer din abincin a take taji yawunta ya tsinke, ta saka spoon ta dandana sai ta ja kujera ta zauna ta fara ci, sai data kusa koshi sannan ta tuna ta tura Hassan neman abinci. Ta dauko wayarta ta kira shi "kina ta jira na ko? Yanzu na kira Jabir yayi min kwatancen wani guri" tace "ka bar shima, har na dan dafa wani abu ma naci" yace "ayyah. Sorry Precious. Jikin yayi sauki kenan" tace "babu laifi"

Sauran data rage yazo shima yaci "amma yayi dadi sosai, sharp sharp haka har kin gama? Kai amma yayi dadi sosai" tayi murmushi kawai. Ita bata taba ganin irin wannan abincin ba ma ballantana har ta iya. Sai kuma ya ajiye chokalin hannunsa yana kallonta, ta gane kallon dan haka ta mike zata gudu, ya jawo ta ta fado cinyarsa. Wannan dai wankan da bata son yi sai data yi shi.

Washegari yace mata ta shirya zasu je ayi mata passport. Ta roke shi kuma zata je ta yiwa yan gidan su sallama. Ta shirya sosai tayi kyanta, shima haka, sannan suka fito tare suna hirar su yana yi mata alkawarin zai koya mata mota in sun dawo. "Duk san da zaki fita ko ina office ne sai kiyi tafiyar ki kawai" a kofar gidan ne taga abin mamakin da ya saka ta tsaya ta kasa motsi. Adam ne a tsaye a jikin mota yaa goge ta, ya dan rissina ya gaishe da Hassan sannan ya mika masa key din motar. Sai kuma ya juyo yana kallon Ruqayyah yace "Madam barka da fitowa" ta nuna shi da hannu "kai! Me kake yi anan?" Hassan ya juyo yana kallon ta yace "kin san shi ne?" Bata amsa ba ta sake cewa "me yake yi a gidan nan?" Yace "Sumayya bata gaya miki ba? Let's go, zan gaya miki a hanya" ta sake juyawa tana kallon Adam sai ya daga mata kafada sannan ya juya yayi tafiyar sa hannayensa a cikin aljihun wandon sa.

Ta bude motar ta shiga shima ya zagaya ya shiga. Yana zama tun kafin ya tayar da motar tace "me Adam yake yi a gidan nan?" Yace "wai dama kin san shi ne? Da naga Sumayya tana biye miki shi na dauka baki san shi ba bata son ki sani" ta kara bata fuska tace "Sumayya? Wai kana nufin kasan shi tare da Sumayya?" Yace "a tare ma na gansu. Daga baya ba dauke shi aiki, yanzu driver ne shi a gidan nan. Yadda na fahimta kamar saurayin ta ne" ta sake cewa "Sumayyan? Lallai wannan yarinyar ta wuce duk inda nake tunani wallahi. Wato ashe Adam ne suke waya dashi, shine wanda ta karbi number dinsa a hannun ka kuka ce min wai abokin ka ne" yayi dariya, "I noticed bata son ki sani, I tot zata gaya miki kafin bikin mu shi yasa ban gaya miki ba" tace "ba zata gaya min ba ai. Ta san bata da gaskiya" ya dan bata rai yace "menene problem din? Ni a ganina kamar bashi da problem except that he was a christian sai ya musulunta, iyayensa har yanzu Christians ne. But character wise bana jin yana da aibu" Ruqayyah ta rike baki, tubabbe? Yanzu Sumayya a kan tubabbe zata kare? Amma ganin Hassan yana nuna hakan ba komai bane ba sai bata yi comment akan hakan ba. Amma sai tace "no you are wrong, yana pretending ne amma bana gari bane ba. A inda na sanshi, a inda muka fara haduwa dashi a motar sa ne taxi ya dauko mu daga school ni da Sumayya, and ge tried to touch me, a gaban Sumayyan. Shi yasa nayi mamaki da har zata kula shi har suke soyayya" Hassan yayi shiru maganar tana taba zuciyarsa, wato abinda ya dauko ya kawo musu gidan su kenan? Yace "tabbas biri yayi kama da mutum. Ranar dana fara ganin shi a kofar gidan ku ya faya min gaisawa yake so kuyi, amma sai yace da Sumayya zasu gaisa dan yasan in ya miki magana maba zaki kula shi ba. Wato wannan shine dalili" tace "tabbas. Yasan ni ba zan kuka mai dabi'a irin tasa ba". Kafin su je gidan Baba Hassan ya yanke hukuncin korar Adam. "Muna da yammata a gidan, he is a risk to them".

Sai da suka je aka yiwa Ruqayyah passport aka gama sannan suka biya ta bakery suka yiwa su Inna siyayyar kayan kwalama, suka kuma siya musu fruits da drinks da yawa sannan ya kaita gida, bai shiga ba yace zaije unguwa shima sai ya dawo zai shiga, ta turo Zunnur ya kwashi kayan ya shigar musu dashi.

Ita kanta sai data gansu sannan ta san tayi missing dinsu. Suma suna ta murnar ganinta kamar wadanda suka yi shekara basu ganta ba. Ta basu labarin tafiyar da zasuyi da Hassan da Hussain da Fatima, nan take su Zunnur suka fara jera mata list na kayan da zata siyo musu tsaraba. Anan suka ci abincin rana tare a palo, sai taji ta kasa cin abincin sosai duk kuwa da cewa babu laifi da kyansa duk da babu kaji amma akwai kifi da ganye a ciki. Amma kifin ne ma taji yana tayar mata da zuciya.

Sai da suka shiga daki da Sumayya zasuyi sallah sannan ta tayar mata da zancen Adam "yanzu dama Sumayya ashe Adam ne kuke wayar nan dashi? Duk wannan murmushin da kike yi ashe Adam kike yiwa? Yanzu ki rasa wanda zaki yi soyayya dashi Sumayya duk mazan garin nan sai inyamuri? Ina samarin hausawa? Ina fulani? Ina bare bari ina shuwa ina duk sauran kabila masu mutunci amma duk basu yi miki ba sai inyamuri? Kema kanki kinsan Inna Ade da Baba ba zasu taba karbar wannan maganar ba" Sumayya da take tsaye da hijab a hannun ta tace "kin gama? To bara in tuna miki, ni ce nake sonsa ba ke ba, in auren nema ni zan aure shi ba ke ba, ina ruwanki?" Tace "da ruwana mana, ke fa yaruwa tace, shi kuma drivern miji na ne, ba kya ganin alakar tsakanin ku kamar disgrace ne a guri na. Dama can ana min kallon wulakanci ballantana kin kara zubar min da mutunci" Sumayya tace "okay shine problem dinki? To ni babu ruwa na da kasancewar sa drivern mijin ki wannan problem dinki ne" Ruqayyah tace "amma dai ai na tabbatar kina da problem da kasancewarsa tubabbe ko?" Sumayya ta juyo tana yi mata wani irin kallo, Ruqayyah tayi dariya "ohhh kar dai kice min duk murmushin da kuke yiwa juna bai gaya miki ko shi waye ba" Sumayya ta ajiye hijab din hannunta tace "don't ever call him that again" Ruqayyah tace "in na sake kuma fa? Me zaki yi min?" Sumayya tace "zan tabbatar baki sake yiwa wani rashin kunya ba" Inna ta bude dakin ta tsaya tana kallon su "ohh ni Sa'adatu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu yaran nan kwanan ku nawa baku hadu ba, amma daga haduwarku har zaku yi fadan naku da kuka saba? Yanzu kuma me ya hada ku?" A tare suka ce "babu komai Inna".Har suka gama abinda zasu yi suka dawo gida Hussain hankalin sa yana kan maganar Adam. Yaron yaki ya gaya masa gaskiyar abindaya faru maybe daya gaya masa da yasan abinda ya kamata yayi. Shi tun farko hankalin sa bai kwanta da Ruqayyah ba, sai dai kuma a yanzu matar dan uwansa ce dan haka bibiyarta da kuma saka ido a kanta ba zai yiwa dan uwan nasa dadi ba. Dole sai yabi a hankali, dole sai ya nemi dabara yadda zai bullowa lamarin ta lumana ba tare daya taba zuciyar dan uwan sa ba.

Suna dawowa gida ya wuce part din Aunty ya gaishe ta, a can ya tarar da Hassan shima ya shiga gaisheta, Hassan ya dauke kansa yayi kamar bai ga shigowar Hussain ba shi kuma sai ya kama tsokanar sa wai yaga alamar har wani tumbi ya fara ajiyewa saboda jin dadin amarci. "Me Ruqayyah take baka ne? Zan ke aiko da kwano na nima ana sammin ko na kara kumari da kwarjini" Hassan ya kalle shi kawai ya dauke kai, Aunty tace "an kuma kenan, me ya hada ku?" Hussain yace "aunty driver na ya kora, ni kuma nace na mayar dashi bakin aikinsa shine yake fushi" Aunty tace "akan driver kuma? Hassan me yayi maka da zafi haka da har zaka yi fushi da dan uwanka?" Hassan ya mike yana daukan wayarsa yace "ya wuce aunty, laifi na ne dama, drivern sa ne shi yake biyan sa albashi, motar sa ce gidan sa ne, I should have know my place, yanzu kuma na sani dan haka zanyi minding business dina" aunty ta rike baki tana salati yayin da Hassan din ya juya ya bar gidan. Tabbas yan biyun nata suna fada, amma mostly fadan nasu yafi yi mata kama da wasa dan akan silly silly things suke yin fadan,but na yau is different. Na yau ba wasa bane ba.

Ta juya tana kallon Hussain tace "ka sallami drivern Hussain" ya girgiza kansa "Aunty ba zan iya ba. Kuma akwai dalilin da yasa ba zan iya din ba" ya dago yana murmushi yana kallonta. "Ki rabu dashi, yadda ya hau shi kadai haka zai sauko shi kadai"
Daga gidan aunty hassan gidan sa ya zarce, a palo ya tarar da Ruqayyah a kwance a kujera da packet din chewing gum a gaban ta tana kuma cin wani, tayi masa murmushi amma sai ya wuce ta ba tare daya mayar mata ba, ta bi bayansa da harara sannan ta cigaba da wayarta. "Wallahi ina gaya muki Rukee sai kin waye, in ba haka ba kina ji kina gani za'a mayar dake tsumman goge kashi" tace "to Minal me zanyi? Kin ga fa su Fatima ce tasu, sam basa ma shigo bangare na sai gurinta, saboda zata dauko abin duniya ta basu ni kuma bani dashi" Minal tace "nema zakiyi kema ai, in baki dashi ai mijinki yan dashi shine zai baki ai. Ki san me yafi so ki ringa yi masa, ki kwantar da kanki sosai kar ki sake ki nuna masa wannan zafin ran naki, ba dai shine babba ba? In dai kin kama babban yayansu ai kin kama su gabaki dayan su babu wanda zai isa yayi miki musu. Kuma suma ki shiga cikin su, ki nuna musu soyayya kamar ruwa, ai da haka ake jan ra'ayin mutane, ke yanzu ko yar kissar nan ma ashe baki iya ba? Ai nuna musu zaki yi duniya babu yasu. Ki kafa gwamnatin ki sosai sannan ki fara diban rabonki. Dakin samu kin tara ki sayi gida, in kin kuma tarawa ki kuma siyan wani. A haka in rabuwa ma tazo Allah ya kiyaye kin ga kin samu madafa, tunda dai ba wani sonsa kike yi ba nasan auren ba wani guri zaije ba" Ruqayyah ta bata rai tace "wannan ai mugun fata ne, kuma ni yaushe nace miki bana sonsa?" Minal tace "ko kima sonsa ma na tabbatar kinfi son kudinsa a kansa, ko ba haka bane ba?" Ruqayyah ta jiya ido tace "to waye bayan san kudi? Annabi ma da kansa yace mu nemi tsari da talauci dan talauci musiba ne. Duk wanda yace baya son kudi to munafiki ne" suka yi dariya tare. Minal tace "yanzu yana ina?" Ruqayyah tace "yana dakinsa ina jin. Yanzu muna wayar nan ya shigo ya haye sama, kin san fushi yake yi akan maganar drivern nan" Minal tace "amma lallai Ruqayyah sai na kai ki ina jin gurin Aunty Hafsa ta wanke min ke, yanzu mijin naki yana fushi shine kika barshi ya tafi daki shi kadai? Mijin ma kuma mai kudi irin wannan? Ai ko da baki yi laifi ba zuwa zakiyi ki ba shi hakuri. Ki lallaba kayanki in ma yaga laifin ki ya dawo yana ganin laifin wanda ya fadi laifin ki".

Da haka suka yi sallama Ruqayyah ta tashi ta hau saman itama, sai data fara shiga dakinta ta shafa turare saboda jin ta take yi kamar tana dan tashi kadan duk kuwa da cewa tayi wanka ta kuma saka turaruka iri iri, amma ta na jin kamar kalar turaren da ta saka ne bata so. Ta shiga dakinsa ta tarar ya fito daga wanka yana shafa mai, ta bi kirar jikinsa da kallo sannan ta danyi masa murmushi "yanzu ni shikenan sai mijina yazo ya wuce ni ko kula ni ba zaiyi ba, kawai sai yake fushi dani duk da bansan laifin da nayi masa ba?" Bai ce komai ba ya fara shafa man sa, ta zo gabansa ta tsaya tana shagwabe fuska kamar zata yi kuka. Ya zauna a bakin gado sai ta bishi ta zauna akan cinyarsa tana leka fuskarsa. "To ni ka kalle ni mana? Ni

Please Login or Register in order to submit comment