Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐



L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️


R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)




G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)




M͆y͆ t͆e͆l͆e͆g͆r͆a͆m͆ g͆r͆o͆u͆p͆ l͆i͆n͆k͆👇
https://t.me/+YyGNyl_PQv1iODdk




M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻


https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐


Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ


Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️




Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ


Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ


Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗






*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*


B͆I͆S͆M͆I͆L͆L͆A͆H͆I͆R͆ R͆A͆H͆M͆A͆N͆I͆R͆ R͆A͆H͆E͆E͆M͆


Ɗu͆k͆k͆a͆n͆ y͆a͆b͆o͆ d͆a͆ g͆o͆d͆i͆y͆a͆ s͆u͆n͆ t͆a͆b͆b͆a͆t͆a͆ g͆a͆ A͆l͆l͆a͆h͆ m͆a͆i͆ k͆o͆w͆a͆ m͆a͆i͆ k͆o͆m͆a͆i͆, t͆s͆i͆r͆a͆ d͆a͆ a͆m͆i͆n͆c͆i͆n͆ A͆l͆l͆a͆h͆ s͆u͆ ƙa͆r͆a͆ t͆a͆b͆b͆a͆t͆a͆ g͆a͆ M͆a͆n͆z͆o͆n͆ m͆u͆, m͆a͆s͆o͆y͆i͆n͆ m͆u͆ a͆b͆i͆n͆ a͆l͆f͆a͆h͆a͆r͆i͆n͆ m͆u͆ A͆n͆n͆a͆b͆i͆ M͆u͆h͆a͆m͆m͆a͆d͆ S͆.A͆.W͆, d͆a͆ i͆y͆a͆l͆a͆n͆ s͆a͆ d͆a͆ S͆a͆h͆a͆b͆b͆a͆n͆ s͆a͆ b͆a͆ƙi͆ ɗa͆y͆a͆...


Y͆a͆d͆d͆a͆ n͆a͆ f͆a͆r͆a͆ r͆u͆b͆u͆t͆a͆ w͆a͆n͆n͆a͆n͆ l͆i͆t͆t͆a͆f͆i͆n͆ a͆ s͆a͆'a͆, A͆l͆l͆a͆h͆ ka͆ b͆a͆n͆i͆ i͆k͆o͆n͆ k͆a͆m͆m͆a͆l͆a͆w͆a͆ a͆ s͆a͆'a͆, k͆u͆s͆k͆u͆r͆a͆n͆ d͆a͆ ƙe͆ c͆i͆k͆i͆ A͆l͆l͆a͆h͆ y͆a͆ y͆a͆f͆e͆ m͆i͆n͆, A͆l͆l͆a͆h͆ y͆a͆ b͆a͆m͆u͆ i͆k͆o͆n͆ y͆i͆n͆ a͆m͆f͆a͆n͆i͆ d͆a͆ a͆b͆i͆n͆d͆a͆ y͆a͆ƙe͆ c͆i͆k͆i͆...

Gᴀʀɢᴀᴅɪ!! Gᴀʀɢᴀᴅɪ!!Gᴀʀɢᴀᴅɪ!!!

Wᴀɴɴᴀɴ ʟɪᴛᴛᴀғɪɴ ƙᴀɢᴀɢɢᴇɴ ʟᴀʙᴀʀɪ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʏɪ ꜱʜɪ ɗᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴡᴀᴛᴀ ʙᴀ, ꜱᴀ'ᴀɴɴᴀɴ ʙᴀɴ ʏᴀᴅᴅᴀ ᴀ ᴊᴜʏᴀ ᴍɪɴ ꜱʜɪ ᴛᴀ ᴋᴏ ᴡᴀᴄᴄᴇ ꜱɪɢᴀ ʙᴀ, ʏɪɴ ʜᴀᴋᴀɴ ʙᴀʙʙᴀɴ ʟᴀɪғɪ ɴᴇ, ᴋᴜᴍᴀ ɪɴᴀ ʜᴀʀ ɴᴀ ᴋᴀᴍᴀ ᴍᴜᴛᴜᴍ ᴅᴀ ʜᴀᴋᴀɴ ᴢᴀɪ ғᴜꜱᴋᴀɴᴄɪ ʜᴜᴋᴜɴᴄɪ...



PⒶⒼⒺ 1️⃣


Anty!! Anty!! Anty!!
Mommy ta ce ki tashi daga bacci nan kafin ta zo da ƙanta.


Dogon tsaki ta ja, ƙara gyara kwanciyar tayi ba tare da ta tashin ba, ganin haka ne yasa Arya fita daga ɗakin da gudu ta nufi parlour, wata mata ce a kalla zata kai shekara arba'in, tana zaune a kujera, waya ce a hannun ta da alama magana ta gama yi a wayar, ganin yar autar tata ta dawo ba tare da wacce ta aika a kira ma ta ba ne yasa ta cikin hassala ta ke faɗin


"Arya, ina Raudar take? Ko baƙi je kin taso min ita bane"?

Bude baƙi Arya tayi a shagwabe ta ce :
To Mommy na je amma ta ƙi tashi kuma fa tana ji ina ce da ita Mommy na ƙiran ta, shine ta ƙara jan bargo bata kulani ba"

Shikenan! Go and call Saleem" cewar Mommy ta fita a parlour'n tayi hanyar dakin Raudah, ita kuwa Arya da gudu ta fice compound din gidan dan kiran Saleem kamar yadda mommy ta aike ta.


Mommy na shiga ɗakin Raudah ta hango ta nannaɗe a gado tana barci, charger ta cire a jikin socket ta nufi gaɗon, tana isa ta yaye bargon ta zuba ma ta a cinya, wani ƙara Raudah ta saki, ba shiri ta miƙe ta na sosa wajan ɗan taji zafi sosai, bacci ne fal a idon ta amma dole ta tashi ganin Mommy ce da ƙanta.


"Yanzu fisabillilahi Raudah kin ma ƙan ƙi adalci kenan? Sau nawa ina aiko Arya ta tashe ki? Duk yau aikin gidan ni nayi abu na, wallahi idan ki ka ce da wannan lalacin zaƙi je gidan miji wahala zaƙi sha dan kuwa babu namijin da zai jure wannan halin na ki"


Shiru ta yi tana shagwabe fuska ganin Mommy na ta sababi yasa ta yi shiru, ba ta ce komai ba, ita kuwa Mommy ci-gaba ta yi da fada, ɗan halin na Fauzah ya fara isar ta yarinya sai lalaci, sai da tayi mai isar ta sannan ta fice a ɗakin.


Mommy na fita Raudah ma ta fice a ɗakin, tsakar gida ta je, ganin har rana ta fito sossai yasa ta hanzar ta daukan boƙiti wankan wanƙa ta nufi kitchen, ruwan zafi ya gani a kettle an tafasa, da hanzari ta juye ta shige bayi, koda ta fito daga wankan ba ta bi ta ƙan abin ƙaryawan da a ka ajiye ma ta ba ɗan tasan zuwa yanzu ya gama sanyi, wayar ta iPhone 7 plus da ke kan gadon ta ɗauka, ganin sha daya saura minti takwas yasa ta ce


"Wayyo Allah na!! Allah yasa Bestynah bai yi fushi dani ba dan yau kwata_ƙwata ba muyi magana ba" tana fada tana kokarin kiran number BESTY ...


Sai da ta ƙira sau biyu ana uku ya daga bai ce komai ba ta fara magana cikin shagwaba


" Haba BESTY tin da kaga ban neme ka ba ai sai ka kira ni kuma ƙasan munyi da kai yau za ka raka ni wajan tela"


Shi ma daga can ɓangaren shagwabe murya ya yi ya ce
"Kiyi hakuri BESTY na ban tashi da wuri ba ne, kin ganni nan ko fitowa ban yi ba har yanzu ina daki, ban ma san wacce wainar aka toya a cikin gidan ba, tashi na kenan sai ga call ɗin ki".


Narƙe murya tayi ta na faɗin " ba mun yi alƙawarin ba zamu dinga zama da yunwa ba, though nima tashi na kenan ɗan da charger waya ma Mommy ta tashe ni", har da yin shesheƙar ƙarya kamar yana gaban ta, da sauri Besty ya riki ce sai cewa ya ke
"Kashhh!!amma dai Mommy bata ji miƙi ciwo ba ko? Ni fa da wani abu ya same ki gwara mulkin Buhari ya dawo farko, ya karshe maganar yana dariya, ita ma Rauda sai da ta ɗara jin abinda ya ce.


Waya suka ci-gaba da yi cike da kulawa ganin call ɗin Ya Noor yana ta shigowa ne yasa ta ce
" Ammm besty bani minti biyar pls, Ya Noor yana ta ƙira na ko me zai ce mun ohoo, ba na fada maƙa ba ranar, tunda ya kawo sadaki sai ya dinga min wasu abubuwa kamar iko _ iko, Ni wlh na gaji da halin shi, mutum sai shegen miskilancin masifa, mtseww",


Shiru ya yi bai ce mata komai ba sai da ta karaci mitar ta sannan ya ce ma ta " kinga malama kin dame ni da maganar mutumin nan, ai tin ba yau ba nace ki rabu dashi ƙin ki ji, oh saboda ban isa dake ba ne, hmmm ai nasan matsayi na, mutumin da ko kallon arziki baya min, ta yaya ma zan ji dadi ace bestyna tana tare da wanda baya mutunta Ni? Indai har da gaske ni better half ɗin ki ne, to ya zama dole ki rabu dashi mu nemo wani saurayin" ya faɗa in a serious tone,


Zufa ne ya fara karyo wa a jikin ta, tabdi!! tama isa ta ce ma Baba bata son Nura? Ai Wlh sai ya sumar da ita daga ita har Bestyn, gashi kuma bata son ɓacin ran besty'n na ta, ganin tayi shiru ne yana ta magana shi kaɗai yasa ya kashe wayar shi gaba ɗaya, ai kuwa sai ga kiran Noor ya sake shigowa a karo na uku wayar ta, tin da taga kiran da Noor yake ya yi yawa tasan wani abu zai fada ma ta mai muhimmanci ɗan shi Noor call daya yaƙe mata idan bata daga ba to ba zai kara kira ba har sai ta neme shi da ƙanta, ta inda BESTY ya fishi kenan sai ya mata missed call biyar ko shida koda kuwa hira kawai yake so suyi da ita.


Sai da call ɗin ya kusa yankewa sannan ta daga, bata ce mai komai ba, hakan ba karamin fusata Noor ya yi ba, lallai ma Raudah ba karamin raina shi ta yi ba, ya zama dole ya yi maganin ta...






Tana kwance a saman ƙirjin shi, wasa take da gashin da ƙe kwance a saman faffadan kirjin shi, hakan ba karamin nishadi yaƙe sa ka ta ba, kallon ta ya yi da rinanun idanuwan shi, da kyar ya ke iya kamo numfashin shi saboda wata sha'awar ta daƙe ƙara azalzalar shi, babu abinda yake so sama da ya ga ya yi sex da ita amma taƙi bashi hadin kai, tsawon watanni 5 kenan da haduwar su,kuma babu irin sabon da basu yi ba, ta yadda bata iya tsallake maganar shi, abu ɗaya ne ya kasa samu daga wajan ta, sai dai duk lokacin da suka haɗu suyi romancing ɗin junan su, a wanan lokacin hakurin shi ya ƙare,
Hannun ta ya cire daga jikin shi, ganin hakan ne ya sa tayi saurin kallon shi
"Haba mana Adnan, me yasa za ka hanani yin abinda nake matukar so da kauna" ta fada kamar zata fashe da kuka,
Wata iska ya furzar da kyar ya aro jarumtar yin magana


"Ya kike so nayi ne Fadeelah" ɗan baƙi san yadda na dauke ki bane, tin lokacin da muka fara abota har nasan damuwar ki da wancan tsohon saurayin na ki, na daukar wa kaina alkawarin share miƙi hawaye duk rintsi duk wuya, bani da burin da ya wuce na faran ta miƙi rai, amma ke kin gagara fahimta, ko da yaƙe dan kin ga na damu da ke ne shi yasa!


Tabbas taga ɓacin rai a idanun Adnan, amma kuma fa ba zata iya bashi ƙanta ba, wannan tanadin sai gidan miji, to amma ya zata yi da rigimar da yaƙe neman ɓullo ma ta?


Innaaa!! Ba abu bane mai yiwuwa, tab ai ba zata taba yadda ya aikata abinda yake so da ita ba, zina kenan fa, ta fada a ranta, shi kuwa Adnan yana nazartar yanayin ta ba tare da ya ce komai ba ya miƙe ya shiga toilet, bata yi ƙasa a gwiwa ba wajan tashi ta bi shi cikin toilet ɗin gudun kar ranshi ya ƙara ɓaci...




Toh fa reader's da alama besty zai yi halin na shi🤣


VOTE






COMMENTS






SHARE


✍️
BADAWEEYERH






💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐



L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️


R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)




G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)




M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻


https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐


Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ


Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️




Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ


Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ


Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗






*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*


Na gode da ganin comments ɗinku, Allah ya bar ƙauna...
Besty yace na gaishe ku🤪




PⒶⒼⒺ 2️⃣


Ƙo a toilet ɗin ma sai da Adnan ya ƙara rage zafi , ganin hankalin shi ya kwanta ne ya sa tayi wanka ta fita daga toilet ɗin ta koma ɗaki, tana cikin sa ƙaya wayar ta dake ƙan bedside ta fara ringing, ganin sunan Anty baro_baro yasa gaban ta dukan tara_tara, ai ba zata iya dagawa ba, sai yanzu ta tuna da aikan da Anty ta ma ta, shine ta biyewa Adnan suka zo hotel,


"Hubbey ka fito Anty nata kira na, kazo ka kaini inda ta aike ni"


Fitowa ya yi yana goge gashin kan shi da towel, ganin ta ya yi a tsaye, matsawa ya yi kusa da ita ya kamo ƙugunta, ƙara narke masa tayi a jiki sai ta juyo ta ƙarbi towel din ta ƙara sa goge mai jikin shi, yana saka kaya ya ɗauki mulkin mashin din shi suka fice a ɗakin.


A kasuwa ya ajiye ta ya wuce shagon shi bayan ya mata alƙawarin dawowa da daddare, da sauri ta shiga kasuwar, da kyar ta samu abinda Anty ta aike ta saboda yamma tayi, wajan ƙarfe biyar ta shiga gida.


Ai kuwa titsiye ta Anty tayi bayan ta haɗe rai


"Daga ina kike?"


"Daga ƙasuwa nake Anty"cewar Fadeela muryar ta na rawa

"Kasuwar ubanki!!, Awan ki nawa da fita daga gidan nan? Kin tafi yawon ta zubar ɗin ki ko? Wai Fadeelah me kike so ki mayar da kan ki ne? Ga maneman ki na arziki amma kin ƙi yadda, kin nace ma wannan shegen yaron mai kai kamar saman risho"


Ai kuwa ɓaki na zumɓura jin munanan kalaman da Anty take jifan besty Adnan da shi, wallahi banda yayata ce da yau sai na sumar da ɓakin ta.


Murfin kwanon da ke hannun ta ba tare da na lura ba ta buga min shi, ai kuwa sai da bakina ya fashe , ganin jini na zuba yasa na kwalla ihu tare da barin wajan ina tafiya ina ja mata Allah ya isa, ba baƙin da ya fashe bane ya ba ni haushi, a'a bestynah da ta zaga ne ya ƙona min zuciya, wajan rijiya na nufa na wanke bakina, bayan na gama na shige ɗaki abuna, ummahani yar Anty na gani a cikin ɗakin tana wasa da remote, ai kuwa sai da na mangare ta na ce "shegiya da ido kamar malmo, Allah ya isa dukan da babar ki tamin" ai kuwa ta sa kuka ta fita a ɗakin ganin haka yasa ni ma barin ɗakin kar Anty tazo ta kuma min wata masifar.








Raudah ganin shima Noor bashi da niyyar magana yasa ta kashe wayar, ai kuwa ranshi ya baci,


"Ba komai, zaki shiga hannuna ne" Noor ya fada yana dukan table din office ɗin shi.


Ina kashe wayata na saka riga da skirt na wata jar atampha, ban shafa komai ba kasancewar ni fara ce sol kuma ni ba mai ra'ayin kwalliya bace, ko da yake besty ne ya cusa min ra'ayin nan wai shi yafi son ganin fuska na a haka, fita nayi zuwa dakin mom, ganin bata gyara ba yasa na gyara mata sa'annan na share dakin , ai kuwa nasha yabo a wajan ta


"Iyeee!! Yau su Raudah anyi abun kai, chab da alama za'ayi ruwan sama da ƙanƙara, yau kece da gyara dakin nan?" Mommy ta fada cike da mamaki


Murmushi nayi ina wasa da zoben hannuna na ce


"Eh mom ya yi kyau ko?"


"Ah sosai ma Allah ya miki albarka", Mommy ta fada, alamun jin daɗin abinda nayi sun bayyana a fuskar ta ganin ƙamar Raudah ta fara shiryuwa.


Ɗaki na koma na saka gyale na, purse na ɗauka na fice a tsakar gida na iske Mommy na ma ta sallama ɗan zuwa wajan tela, ina fita ƙofar guda na ha motar Noor a waje a hankali na taka har wajan shi ina hu_hura hanci ɗan ban so ganin shi ba,


"Maye", na furta a raina

Cikin ɓacin rai Noor ya ce;


"Raudah me yasa kika kashe min waya"?


A dage nace mai " tambaya kake ko neman sani?


Bai ƙara yin maganar ba, mun kai minti ɗaya a haka, ganin kamar bai da abin fada yasa na ce " kaga malam!! ni ina da wajan zuwa idan kai baka da shi",


"Ina zaki je?" Noor ya tambaye ni, ko kafin na bashi amsa na hango bestyna yasha gayu cikin wasu kananun kaya jeans baƙi da jar riga yana ganin motar Noor ya haɗe girar sama da ƙasa ya samu gefe ta tsaya ya naɗe hannu a kirji yana kallona,


Noor bai ga zuwan Besty ba, ganin ban bashi amsa ba yasa shi faɗin


"Ki shiga na kai ki na ce "


"No ka barshi za mu tafi da Dee dina"


Juyawar da Noor zai yi sai ganin Dee ya yi a tsaye yana harar shi, ai kuwa a zuciye ya fito daga motar ya nufi inda yake...




Hahahaha fan's din besty yau fa da alama zai sha ɗuka a wajan noor








VOTE






COMMENTS






SHARE


✍️
BADAWEEYERH




💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐



L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️


R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)




G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)




M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻


https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐


Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ


Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️




Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ


Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ


Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗






*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



💓💓вє тнє gιяℓ уσυ ωαит тσ вє 💃 αи∂ иσт тнє gιяℓ тнαт ρєσρℓє ωαитѕ уσυ тσ вє 🙅🏻



✍️
яυвву



PⒶⒼⒺ 3️⃣


Ran Noor a ɓace ya kara sa wajan da Besty yake, ganin haka yasa Raudah tayi saurin bin bayan shi kar yaje ya yi aika_aika, yana isa ya nuna Dee da ɗan yatsa


"Wannan shine warning na ƙarshe da zan maka Kamaludeen, babu kai ba Raudah, ka fita a hanyar ta, tunda ba auren ta za kayi ba,ka bari na zauna lafiya, in kuma ba haka ba wlh!wlh! wlh! Kaji rantsuwa uku ko?za kayi dana sanin sanina!!


A yatsine Besty ya kalle shi, sai kuma ya taɓe baƙi ya ce;


"Lallai Nuradden, kana wasa da lamarin besty, to ga ka ga Raudah nan, ita ya kamata ka kafa ma wannan dokar ba ni ba" ya ƙara sa fada yana dariyar shakiyanci


Tsananin haushi ya sa Noor kasa ce ma sa komai, kawai ya juya ya fisgi mota ya bar wajan, ita kuwa Raudah da ta tsaya kallon ikon Allah bata iya cewa komai ba sai da Noor ya tafi sannan ta juyo ta kalli Besty, dariya ta tuntsure da shi cikin sigar zolaya ta ce


"Kaiii, dama Noor ya zane ka, yau da na sha dariya yadda naga ya zuciyan nan" ta fada tana dariyar kamar wata taɓaɓɓiya, hakan da tayi ba ƙaramin tunzura Besty ya yi ba, kasa ce ma ta komai ya yi a zuciye shima ya bar wajan ya juya ya fara tafiya, ai da wani irin sauri Raudah ta ke bin shi tana mishi magiya da fadin


"Haba better half wasa fa nake maka, so nake kawai na tsokane ka", ganin ya ƙi kulata ne yasa ta fashe da kuka wanda hakan ya sa shi tsayawa chak yana toshe kunne, ƙara haɗe girar sama da ƙasa ya yi kai kace an aiko masa Sarkin garin su ya mutu ne, "To Malama ai sai ki mana shiru ko kada ki cire min doddon kunne", ƙafa ta fara bubbugawa cike da shagwaba take faɗin
" To to ni ba zan dena ihun ba kuma ma .... bai bari ta karasa maganar ba ya kamo hannu ta suka tsallaka titi, da kyar suka samu abin hawa zuwa shagon tela.




Noor yana barin wajan su ya nufi babbar kasuwa, shagon da mahaifin Raudah yake sigar da takalma da yadin maza gami da shadodi ya nufa, a kofar shagon ya ga Abba zaune da abokan shi suna hira, cikin girmamawa da kunya ya tsuguna ya gaishe su , ganin yanayin shi yasa Abba tashi yace su shiga shago


"Nuru me yake damun ka na ganka wani iri, ko baka da lafiya ne?" Abba ya tambaya yana tsare shi da ido


"A'a Abba , kawai na kasa hakuri ne ma shi yasa na ga ba zan iya jira ba har sai nazo na fada maka abinda ya faru yanzu, saboda banji daɗin abin ba"


"Subhanallah, Nuru faɗa min mene ne ya faru ɗan Allah"


"Abba dama ba wani abu bane so nake kawai ka ma Raudah magana akwai wani yaro sunan shi Kamaludeen tana ce masa Dee, to abokin ta ne, sam Abba bana son alaƙarsu kuma nasan da wuya idan kana da masaniyar suna tare, shi yasa nace bari na faɗa maka domin ayi wa tufkar hanci" cewar Noor yana kara russunar da kanshi ƙasa.


Ran Abba ba ƙaramin baci ya yi ba kuma Noor ya kula da hakan , ƙara kwantar da murya ya yi


"Abba ba wani abu bane fa kawai dai magana zaka ma ta" ya fadi haka ne ɗan ya ga Abba ya dauki abin da zafi dama yasan halin Alh Adamu mahaifin Raudah baya ɗaukar raini kuma mutum ne da yaƙe tsaye tsam akan iyalinsa, sa'annan baya magana biyu idan yace eh to eh ne haka idan yace a'a to fa a'a nan ne, shi ya sa mutane su ke ganin girman shi da kimar shi"


Abba ya ce


" Kar ka damu Nuru, ai kai da Raudah duk ɗaya ku ke a wajena, insha'Allah zata gane ƙuskuren ta, kayi hakuri, ina ga ma zan kira mahaifin ka, idan ya shigo ƙarshen satin nan mu zauna a saka ranar auren kawai hankali na zai fi kwanciya"


"To shikenan Abba Allah ya ƙara girma"


"Amen Nuru, Kai kuma Allah ya maka albarka"


"Amen Abba"


Ganin ba wanda ya ƙara cewa komai a cikin su yasa Noor tashi ya ma Abba sallama, ya koma office.






Ko a cikin adaidaitar hira suke cike da nishadi, tabbas suna jin daɗin kasancewar su tare a lokuta da yawa, koda suka sauka Raudah ce ta biya kuɗin, kasancewar shi Dee ba wani kudi ne da shi ba, ɗalibi ne ya na ajin karshe a jami'ar ATBU Bauchi, jakar hannun Raudah ya karba ya riƙe har suka karasa shagon tela, kai idan ka gan su zaka ɗauka masoya ne, dama telan abokin Besty ne haka suka zauna suka sha hira sai wajan ƙarfe uku na rana suka bar shagon a tare suka tafi, sai da ya rakata har ƙofar gida sannan ya juya ya tafi yana ta wurgo mata kiss da hannu, wasu samarin anguwan ne da su ke zaune a saman dakali su ke gulmar Raudah ƙasa_ƙasa, kallon su Raudah ta yi ɗan tabbas taji me suke faɗa a kanta, harara ta galla musu ta yi shigewar ta cikin gida.


Gidan su Raudah matsakaici ne dai_dai zaman mutum daya, akwai flowers wanda aka ƙawata gefe da gefe compound din gidan, sai rijiya da pampo duk a waje ɗaya, daga chan gefe wajan ƙarshen gidan a nan toilet yake, flat biyu ne a gidan sai daƙin tsakar gida da kitchen madaidaici, a gefen kitchen ɗin store ne da yawanci tarkacen su suke ajiye wa, ba za'a ce da gidan su Raudah gidan masu kudi ba, amma suna da rufin asiri ɗan ba abinda suke nema su rasa a wajan Mommy da Abba, kasancewar Abba ɗan kasuwa, Mommy kuma malamar makarantar primary'n gwamnati ce.




Raudah ce ƴa ta farko a wajan Alh Adamu sai Mubasheer da ke binta, sai Salem sannan auta Arya, Raudah nada shekara ashirin, tana zuwa school of nursing, shi kuma Mubasheer shekarar shi 17 yana SS 3 , sai Saleem ɗan shekara goma sannan auta Arya mai shekara biyar ta na nursery three, suna samun kulawa da tarbiyya yadda ya kamata kasancewar mahaifin su da mahaifiyar su basa ɗaukar wargi, suna da wasa da dariya da yara amma kuma hakan baya hana su tsawatar musu idan su ka yi ba dai_dai ba..





Wajen ƙarfe takwas na dare a lokacin Raudah ta iddar da Sallah, tana zaune suna chart da Besty, sai ga Salem ya shigo dakin ta


"Anty Abba yana kiran ƙi"
Damm gaban ta ya faɗi na ce "na shiga uku Salem me nayi?"

Dariya Saleem ya sheke da shi ya na tafa hannu tare da faɗin


"Kaiii Anty!! Kinga yadda kika zaro ido kuwa, sai kace an ka ma kaza za'a yanƙa" yana fadar haka ya fita ya bar ma ta ɗakin, jiki a sanyaye ta tashi bayan ta kashe data ta ajiye wayar a kan daddimar salla ta fice, a hankali ta ke tafiya kamar wata munafuka, kasancewar ba wuta, a haka ta karasa falon Abba.


Da sallama ta shiga, ganin Mommy a wajan yasa gabanta kara faɗuwa, gefe ta samu ta zauna ta raƙube tare da cewa


"Sannu da dawowa Abba"


"Ba abinda na kira ki kimin ba kenan" Abba ya fada a hasale, ya cigaba da faɗin "dan ubanki waye Kamaludeen?"


Cikin In inaa Raudah ta ce


"A...a Abba ɗan makarantar mu ne, tare mu ka gama secondary" ta karashe zancen baƙin ta na rawa


Mommy ta ce


"Makarantar ubanki, yanzu Raudah kaf a cikin ƙawayen ki mata ki tasa wacce za kiyi ƙawa da ita sai namiji? Kisa mahaifin ki yana ganin kamar da haɗin bakina?"


"Mommy dan Allah kuyi hakuri"


Abba ne ya tashi a fusace ɗan jin zuciyar shi yaƙe kamar zata fashe saboda baƙin ciki ya kalle ta ya ce
"Raudah abota!! Abotar ma da namiji", girgiza kai ta shiga yi ganin Abba na matsowa da bulala yasa ta fara

Please Login or Register in order to submit comment