Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alamun ya karye kenan, a gigice Raudah ta nufi inda Noor ya ke ganin dukan da ya ke mai kamar baya cikin hayyacin shi, ai kuwa idon shi ya rufe ba ya ji ba ya gani, kamo hannunsa Raudah ta yi tana cewa:


"Yanzu Noor so kake yi ka kashe shi? Haka kawai babu abin da ya maka ka rufe shi da duka? Wannan ai zalinci ne.."


Ai ko kafin ta ƙarasa sai jin duka ta yi, dukan ta ya ke ba ji ba gani yana faɗin:


"Ni ne azzalumin? A kan wannan ɗan iskan ki ke kira na da azzalumi? Oh wato bai min komai ba na dake shi? To ki rama mai, na ce ki rama mai"!


A zafafe ya ƙarasa maganar yana ƙara marin na ta, ihu take yi iya ƙarfinta amma ba mai ceto, sai da ya yi mai isar shi sannan ya zauna ya na mayar da numfashi, shi yasa baya so ranshi ya ɓaci saboda bai iya ɓacin rai ba, duk abin da aka mai yana ƙoƙarin danne fushinsa, saboda idan ya yi fushi shi kanshi yana shan wahala, da ƙyar ya iya tashi ya je wajen fridge ya sha ruwa sannan ya dawo ya kwashe su zuwa asibiti....


*** *** ***


Zeenat amarya sai chushe-chushe ake yi, ga wani rashin kunya da ya ke ƙaruwa a kanta, sai rawar kai ta ke yi ita ga amarya, ita da ƙawayenta sun haɗa party a ɓoye, wanda za a fara tun takwas na dare har safiya wanda suke kira (till down), a ɓangaren ango Adnan ma sai rawar kai ya ke yi shi da su Farouk da sauran abokansa, iyayensa kuwa sun saki bakin aljihu sun haɗa lefe na gani na faɗa an kai gidan su Zeenat, iyayen Zeenat irin masu son abin duniyan nan ne kuma ba sa ma Zeenat faɗa, sosai iyayenta suka gwangwaje ta da furniture's na gani na faɗa, sosai suke shirye-shiryen bikin.


Ranar Asabar da misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi dubanin jama'a suka shaida ɗaurin auren Adnan da Zeenat a kan sadaki naira dubu ɗari, farin ciki ne kwance a fuskar Adnan, sai dariya ya ke yi domin kuwa yau mafarkin shi ya zama gaskiya, Zeenat ta zama mallakinsa, Allah ne kaɗai ya san yawan son da ya ke wa yarinyar domin tana da nutsuwa da kamun kai abin da ya fi fisgar shi a wajen mace kenan, shi kam ya gama dacewa da mace a duniya.


Ƙarfe biyar na yamma aka raka amarya Zeenat zuwa ɗakin mijinta tare da rakiyar manyan gogaggun ƙarshen ta, sai santin gidan su ke yi tare da ma ta lakca da huɗubar banza wanda ta hau kai ta zauna to dama abu ya haɗu da halinta, ba su bari an rako ango ba suka watse bayan sun ja gefe da wata babbar ƙawar ta ta bata kwalli da wasu ƙwayoyi, daga ita sai cousin's ɗinta aka bari saboda Adnan bai san ta da ƙawaye ba. Basu wani ɓata lokaci ba aka tafi kai ango domin ya matsa musu ayi a raka shi wanda zumuɗin da yake yi sai da ya ƙular da Farouƙ, tsaki kaɗai Farouƙ ɗin ya ke ja yana faɗin:


"Dalla Mallam kar ka dame mu! Ai ba a kanka aka fara aure ba ka zo sai wani rawar kai kake kamar kwaɗo".


Cikin haɗe gira da jin haushin abin da ya faɗa Adnan ya ce:


" Kawai ka ce haushin rashi ne, ko da ya ke yau kai ba sa'a na ba ne, i pass Ur level so I don't have Ur time, ai ban ce dole ka raka ni ba ko?"


Farouk bai sake magana ba ya tashi ya shiga mita sauran abokan suka rufa musu baya, hira suke yi cike da nishadi har suka ƙarasa gidan Adnan, bayan raha da barkwanci a tsakanin su da yan'uwan Zeenat, kuɗi suka basu sannan suka mayar da su gidan iyayen Zeenat ɗin kasancewar a can za su kwana, Adnan na ganin tafiyar su ya rufe get, ya koma ciki, har yanzu Zeenat na zaune a kujerar da ya bar ta, bakinsa ya ƙi rufuwa, cike da jin daɗi ya ke faɗin:


"Amarya ba kya laifi, to ki tashi ki shiga toilet ki canja kaya mana na ga waɗannan sun miki nauyi, ni ma bari in je ɗakina in shirya kar na takura miki ko?".


Kai ta ɗaga ba tare da ta ce komai ba shi kuma ya juya ya fice, tana ganin ya fita ta shiga toilet ta gama abin da za ta yi gudu-gudu ta shafa kwallin da ƙawarta ta ba ta sannan ta fesa wani farin abu a gabanta, fitowa ta yi ta ƙara buɗe jakarta ta ciro wani garin magani ta zuba a cikin humra ta jijjiga sannan ta bi kowanne lungu da saƙo na jikin ta da humrar, wasu fingilalun kayan bacci ta saka, komai na jikin ta ana gani sannan ta ɗora hijabi a kai, zama ta yi a bakin gado tana dakon jiran ango Adnan.


Ko da Adnan ya gama abin da zai yi, ɗakin Zeenat ya koma cike da murmushi, a bakin gado ya tarar da ita tana danna waya, cike da kulawa ya ƙarasa gefen ta yana kamo hannunta haɗe da shafa cikin ta yana faɗin:


"Baby babu komai a cikin nan na ki, farin ciki ya hana ki cin abinci ko?" Ya ƙarasa maganar yana lakuce ma ta hanci.


Murmushin jin daɗi Zeenat ta yi domin kuwa yadda ya ke ma ta yawo da hannayen shi a cikin ta ba ƙaramin daɗi ta ke ji ba, tun daga tsakiyar kanta har tafin ƙafarta saƙon yake isa, zamewa ta yi ƙasa ta zauna ganin haka ne ya sa ya sakko shi ma ya fara bata abinci ita ma tana bashi, ko kunya ba ta ji ba, a nata ganin ai anyi mai wuyar tun da an yi auren, sai da suka ƙoshi sannan ya kwashe plates din zuwa kitchen ta shiga toilet ta kuskure baki, yana shigowa shima ya je ya wanke baki, kafin ya fito ya iske har ta kwanta, wutar ɗakin ya kashe ya kunna mara haske sosai sannan ya haura saman gadon ya janye bargon da ta rufa, hijabin jikinta ya cire ai kuwa idanun shi suka ci karo da ƙirjinta, tuni idanunsa suka kaɗa, kuma turaren da ta shafa ya fara fisgar shi, lumshe idanu Zeenat ta yi cike da jin daɗi, Allah-Allah ta ke yi ya jefa ƙwallo a raga ta ji ya yake, shima gaba ɗaya ya gigice a haka ya rabata da komai na jikin ta ya ci-gaba da ma ta wasanni masu tada hankali, ganin ba za ta iya jurewa ba ya sa ta fara mayar mai da martani, bai ma kula da abin da ta ke mai ba saboda gaba ɗaya ya fice a hayyacin shi, ga wani soyayyarta da ke ƙara ƙaruwa, a haka ya samu ya shige ta, sai dai ya tsaya jimm jin ƙofar a buɗe, ko da an yi wasu kwaskwarima hakan ba zai hana shi gane macen da aka taɓa buɗewa ba, wani nauyi ya ji a zuciyar shi, ji ya ke kamar ya fasa ihu amma ina ya kasa ƙarasawa, haka ya zare jikin shi, kamo shi ta ƙara yi suka haɗa ido, nan da nan- ya ji komai ya gudu a ƙwaƙwalwarsa, ci gaba ya yi da sarrafa ta yadda ya ke so ita kuma sai jin daɗi ta ke yi na ganin komai ya tafi yadda ta tsara..












Taimakon gaggawa likitan ya fara ba ma Fadeelah, sai da suka kwashe tsawon awa ɗaya sannan aka samu numfashinta ya dawo, ban da kuka ba abin da Anty ta ke yi tana faɗin:


"Shikenan Fadeelah kin cuce ni, yanzu sakayyar da za ki min kenan? Duk irin yadda na ke faɗi-tashi a kanki amma sai da kika ɗauko mana abin kunya? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah na tuba ", haka Anty ta ke ta maimaitawa cikin baƙin ciki da ƙunar zuciya, ita kaɗai ta san me ta ke ji a cikin zuciyarta, da ƙyar wata nurse ta ja ta gefe ta rarrashe ta sannan ta tsagaita da kukan, jira kawai take yi Fadeelah ta farka ta faɗa ma ta wanda ya aikata ma ta wannan aika-aikar, ko da ya ke ai ba laifin shi ba ne, da ba ta ba da kanta ba ai hakan ba za ta faru ba, ga shi yanzu ta ja musu masifa suna zaman-zaman su cikin rufin asiri. Sai da Fadeelah ta kwashe awanni wajen biyar sannan ta farka, cikin firgici da ihu, bubbuga gadon take yi tana miƙewa jin hakan ya sa Anty da ke bakin ƙofa ƙarasowa da sauri, tana shiga ta tarar da ita a wannan yanayin tsawa ta daka ma ta tare da faɗin:




"Dalla ki mana shiru munafuka, koma mene ne ai ke kika jawo, tun da kin zama ballagaza jaka, wallahi Fadeelah kin cuce mu", ta ƙarasa maganar kuka na kufce ma ta, ita ma Fadeelah kukan take yi ta na cewa:




"Tabbas Anty na cuci rayuwata, Adnan ya cuce ni, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun wannan wace irin masifa ce?" Matsowa Anty ta yi gadan-gadan kamar zata dake ta ko me ta tuna kuma sai ta fasa, juya wa ta yi ta tsaya a dai-dai saitin window hawaye na zubowa a idanunta, yadda take ji a zuciyarta ko ta daki Fadeelah ba hucewa za ta yi ba, babban abin takaici ma wai wannan ɗan iskan yaron mai ido a tsakar ka, yaron da ba ya ganin mutuncin mutane, ita kam ina zata saka rayuwarta? Haka dai ta yi ta saƙe-saƙe a cikin zuciyarta, ganin ta rasa mafita ya sa ko kallon inda Fadeelah take kuka ba ta yi ba ta fice gaba ɗaya a ɗakin.


Waya ta ɗauka ta kira mijinta kasancewar ba mazauni ba ne ta faɗa masa abin da ya faru, cikin kuka take faɗin:


"Yaya Fadeelah ta cuce mu, ta kasa riƙe mutuncinta, ciki fa ta yi, ina zamu kai wannan abin kunyan? Ni wallahi na rasa yadda zan yi ma".


Daga ɓangaren shi shiru ya yi sai da ta gama bayani sannan ya ce:


"Ki yi haƙuri ki daina kuka, ƙaddara ce amma kuma duk da ganganci, ki kwantar da hankalin ki insha'Allah gobe ko jibi zan taso sai mu san yadda za a yi, amma kafin nan dan Allah kar ki ce ma ta komai", sai da ya tabbatar da hankalin ta ya kwanta sannan ya ma ta sallama ya ajiye wayar cike da mamakin abin da ƙanwar matar ta shi ta aikata, yana ma ta kallon mai wayo ashe shashasha ce...


Kwanan Fadeelah uku a asibiti a ka sallame ta a ɗan wannan lokacin jikin na ta ya yi kyau sai dai damuwa da ya ramar da ita, tsakanin ta da Anty kuwa sai dai kallo don ko ta ma ta magana ba amsawa ta ke ba, a haka dai suka tattara suka koma gida, kuma har a lokacin mijin Anty bai dawo ba, rayuwa ta ma Fadeelah tsauri, ko kaɗan Anty ba ta raga ma ta...


Ango Adnan kam sai zuba soyayya a ke yi da Amarya Zeenat, ba ta bari ya fita ko nan da can, gaba ɗaya gajiyar da shi take amma ya kasa ce ma ta komai, tsabar tsanar ta ce a kwance a ƙasan ranshi amma bakinsa na mai nauyin furta ma ta, ga shi bai isa ya sa ta abu ta yi ba sai dai ta balbale shi da masifa ta na faɗin ita fa ba 'yar aiki ba ce, ko girki ba ta yi sai dai kullum ya siyo musu, ga ƙazanta kamar me, cikin wata ɗaya da aure Adnan ya rame, sai idanu, kana ganin shi ka ga mai damuwa amma ba zai iya furta wa ba, wani sabon abu ma da Zeenat ta tsira shine fita da ta ke yi kullum ba tare da izinin shi ba, ga shi bai isa ya ma ta magana ba sai ta hau shi da masifa wai yana takura ma ta, tsakanin shi da ita yanzu sai idanu...








Noor na isa asibiti ya kira Abba ya sheda mai abin da ya faru sannan ya ƙarasa ya kira nurses, ba ɓata lokaci aka karɓe su kasancewar asibitin mahaifinsa ne, cikin ƙanƙanin lokaci aka ba su taimakon gaggawa, Besty kam ya jigata sosai kasancewar ya bugu da gefen kujera ga kuma karaya a hannun shi na dama, naɗe wajen aka yi da bandeji bayan an gyara karayar hannun da ƙyar, sannan aka mai allura ya koma baccin wahala, ita kuwa Raudah allura kaɗai aka ma ta kasancewar suma kaɗai ta yi, Noor ya na ƙofar ɗakin da Raudah ta ke a tsaye, haushin ta yake ji sosai, gani yake kamar wani abu ya shiga tsakanin ta da Dee, sam ya ji ba ya ƙaunar ganin ta, ana cikin haka Abba da Mommy suka ƙaraso asibitin a tare, don Noor na gama faɗa wa Abba a lokacin ya na kasuwa shi ma ya kira Mommy hankali tashe, a bakin titi Mommy ta jira shi ya zo ya ɗauke ta suka wuce cike da fargaba, ran Abba ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, wato Raudah ba ta jin maganar shi kenan, duk faɗan da ya ma ta a banza ta yi auren ma ba ta rabu da wannan tantirin yaron ba, haka su ka tsaya cirko cirko a asibitin ba wanda yake iya magana, sai bayan isha'i sannan Raudah ta farka, ƙin shiga ɗakin Noor ya yi sai mommy ce ta shiga a lokacin Abba bai dawo daga masallaci ba.


Ko da Mommy ta shiga ta tarar da Raudah a kwance idanunta biyu amma hawaye na tsiyaya a fuskarta, ko a mafarki ba ta taɓa zaton Noor zai iya dukan ta ba, lallai ta san ta kai shi maƙura, tsinkar muryar Mommy ta yi ta na cewa:


"Ai ba ki ma yi kuka ba, bari Abbanku ya shigo za ki faɗa mana uban me wannan yaron ya je yi gidanki na aure",
Ƙara sautin kukan Raudah ta yi don ta tabbatar yau kashinta ya bushe, babu abin da zai hana Abba dukan ta, ita babbar damuwar ta ma Noor ganin ba ta gan shi a ɗakin ba, tunowa ta yi da abin da ya faru sai ta ji duk duniya ba wanda ta tsana kamar Dee don ko sunan shi sai ta ji ya ma ta ɗaci, yau a kan shi mijinta da take matuƙar so kuma yake son ta, mai haƙuri da kawaici ya sa hannu ya dake ta? Ko da ya ke ba ta laifinsa ba ne, don ko ita ce abin da za ta yi kenan ko zuciyarta za ta ji sanyi, babbar damuwarta ma shi ne kallon da Noor zai ma ta, ba ta da wata mafita, kuma duk abin da za ta faɗa ba lallai su yarda da ita ba, ita yanzu babbar matsalar ta ma bai wuce Noor ba ta ga har yanzu bai shigo ba, numfashi mai ƙarfi ta ƙara ja tana mai kallon Mommy, ganin Mommy ta ƙi kallon ta ne ya sa ta rufe ido tamkar mai bacci.


Ko da Besty ya farka ba wanda ya zo ya duba shi sai nurses da ke sintiri, kanshi har yanzu bai daina sara mai ba, ya yi nadamar kasancewar shi Besty, a ranshi yake faɗin "me ma ya kai ni gidanki Raudah? Ga shi nan na ja ma kaina" ganin ya kasa ɗaga hannun shi ne ya duba ya ga hannu a nannaɗe hakan ya tabbatar mai da har karya shi Noor ya yi, nurse ce ta shigo ta ƙara duba shi sannan ta ƙara mai allura, roƙon ta ya yi ta kira mai mahaifiyar shi, bayan ta kira ne ya shaida ma ta yana asibiti, ba shiri ta tashi ta yafa gyale ta taho wajen Dee kasancewar shi ne yaron su ɗaya tal da Allah ya ba su, ko da ta iso ta ga yadda jikin nashi ya yi bayan ya labarta ma ta abin da ya faru faɗa ta hau shi da shi tana faɗin:


"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!! Kamaludeeni yaushe ka zama kwarto?" Ta tambaya cike da mamaki, da ƙyar Dee ya iya ɗago idanunsa da suka kumbura saboda yadda kan shi ya ke mai ciwo ya ce:


"Haba Mama kwarto kuma? Kawai ƙawata ce fa shi ne na je na gan ta" ya faɗa yana juyar da kan shi gefe domin ba ma ya son ƙara tunawa, faɗa sosai Mama ta dinga mai kamar ta aro baki sannan ta fita waje ta kira mahaifinsa ta sanar da shi, shima ba shiri ya bar aikin ginin da ya ke yi ya taho asibitin, ko da mahaifiyar Dee ta labarta mai abin da ya faru tashi ya yi ya fice daga ɗakin yana cewa "Allah shi ƙara" tun da shi ya ja wa kan shi.


A haka suka kwashe tsahon kwana uku a asibitin kuma har yau Noor bai shiga ya ga jikin Raudah ba, Abba dai ya duba ta sau biyu amma har yanzu bai ce komai ba, babu wanda ya san tana asibiti a cikin familynsu saboda Abba ya ce wanann labarin ba abin sanarwa ba ne, Mommy na kula da rashin shigan Noor duba Raudah amma ba ta ce mai komai ba, kullum a asibitin yake wuni kuma duk abin da ake buƙata shi yake yi, shima a ɓangaren 'yan gidansu bai sanar da kowa ba, kullum Raudah sai ta yi kuka tana ce ma Mommy dan Allah ta kira ma ta Noor amma ko kallo ba ta ishi Mommy ba sai dai ta bata amsa da cewa "ai ke kika ja ma kanki ba wani ba" .


A zaman da suka yi a asibitin ne mahaifin Raudah suka haɗu da mahaifin Dee har suka tattauna sosai, ɗan zaman da suka yi har sun saba tare da samar wa da kan su mafita, mahaifiyar Dee ce ma ta lura da shige da ficen su Abba a asibitin shi ne ta tambayi wata nurse, yadda nurse din ta ma ta kwatance cewa tare wani ya kawo su da wata mace hakan ya tabbatar ma ta da ita ce matar da Dee ya je gidanta, shi ya sa ta faɗa wa mahaifinsa shi ne ya nemi Abba suka yi magana kuma alhamdulillah domin kuwa sun fahimci juna yadda ya kamata, mahaifin Dee ya so su haɗu da, shine Abba ya sanar wa da Noor din amma da ke har yanzu bai huce ba, ya na ganin mahaifin Dee sai ya canza waje .


Ko da aka sallami su Raudah gidansu Abba ya mayar da ita da kan shi, ta ji sauƙi ba laifi, a ranar shi ma Dee mahaifinsa ya ce a sallame su saboda sun gaji da zaman asibitin shi dama karayar da ya yi ne da buguwar da ya yi a kai ba su warke ba wannan kuma sai a hankali, Abba ne ya biya ma Dee kuɗin asibiti saboda Noor ƙin biya ya yi na matarsa kaɗai ya biya ya juya ya bar asibitin, shi kaɗai ya san yadda yake ji a zuciyarsa. Yana son ganin Raudah amma fushin da yake yi da ita ba zai bar shi ya iya ganin ta ba...




Bayan kwana biyu da dawowar su iyayen Dee suka zo tare da Dee gidan domin yin zama na musamman a tsakanin su, da ƙyar Noor ya yarda ya zo don ma yana jin kunyar Abba ne, a babban falon Abba suka zauna, bayan zaman su da kamar minti goma sai ga Raudah ta shigo sanye da farin hijabi har ƙasa, suna haɗa ido da Noor gabanta ya faɗi ganin yadda ya rame sosai kamar ba shi ba, sauke idanunwan ta tayi ƙasa tana tafiya a hankali har ta kai gefen da Noor ya ke ta zauna a ɗan gaba da shi, juyawa ta yi ta hango Dee a ƙasa a gefen ƙafar mahaifin shi dama ta san iyayen shi domin yana saka su a status, kallo ɗaya Noor ya ma ta ya ɗauke kai kamar bai ganta ba, haka kawai sai ya dinga jin haushin ta, Uncle Babangida ne ya buɗe taro da addu'a sannan ya fara da musu nasiha tare da nunar musu yadda addini ya tsara macen da ya kamata ka yi mu'amala da ita da kuma namijin da ya kamata ka yi mu'amala, da haramcin kula wadda ba muharramarka ba da kuma wanda ba muharraminki ba, kuka kawai Raudah take yi saboda jin yadda Allah ya tanadar ma da masu irin halayen ta azaba amma ta biye wa son zuciya, jikin Dee ya mutu murus kuma tun ba yau ba ya yi nadamar abin da ya yi, Abba ne ya katse Uncle Babangida da faɗin:


" Raudah kin ba ni kunya, tun da ki ka taso a gidan nan har kika mallaki hankalin kan ki kin taɓa ganin wani wanda ba ki sani ba ya zo da sunan shi abokin mahaifiyarki ne?"


Girgiza kai Raudah ta yi ba halin magana Abba ya ci-gaba da cewa:


"Ko kin taɓa gani na da wata da sunan ita ɗin ƙawata ce?" Nan ma dai girgiza kai ta yi sannan ya ce:


"Oh to sai ke tsabar shashasha ce ke, ba ki san inda yake miki ciwo ba shi ne za ki biyewa son zuciya da wata shegantaka da sunan wayewa wai Besty ko? To ai gashi nan kina nema ki ɓalle auren ki da hannunki, kuma wallahi wallahi wallahi kin ji rantsuwar musulmi in dai Nuruddeen ya rabu da ke to sai dai wani gidan ba nawa ba". Yana gama faɗar haka ya ja bakinsa ya yi shiru ai Raudah na jin kalmar rabuwa ta ƙara fashewa da kuka ba wanda ya ce mata komai sai da tayi mai isar ta sannan ta yi shiru, mahaifin Dee ya ɗora da faɗin:


" Ni na rasa me zan ce ma wallahi, Alhaji, Hajiya dan Allah kuyi haƙuri dama shi ya sa na ce gwara mu taru mu yi magana ta fahimta, waɗannan yara sam ba su kyauta ba sun yi rashin hankali kuma wannan ba tarbiyyar musulmi ba ne kuma ni wallahi abin da mijin yarinyar nan ya yi ya min daidai domin kuwa ko ni ne zan yi fiye da haka ma" sai ya juya wajen da Dee ya ke ya ce " kai kuma na dawo gare ka mutumin banza mutumin wofi, wallahi wallahi idan baka fita a harkar 'yar mutane ba sai ranka ya ɓaci kai kasan karon mu da kai ai, ba kai ba ita na faɗa maka, ko da wasa na sake jin makamanciyar hakan kai ko ba a kan ta ba ko a kan wata ce na haramta maka zama Besty idan ka ƙi kuwa za ka gane ba ka da wayo".


Share hawaye Dee ya yi sannan ya ce " don Allah don Annabi ku yafe min insha'Allah ba zan sake ba tun daga ranar da abin ya faru na yi nadama kuma insha'Allah ko a kan wata ma ba zan ƙara zama Besty ba domin a "SANADIN BESTY" aka karya min hannuna, hannun da har yanzu ya ki ɗauruwa", ya ƙarasa zancen hawaye na ƙara zubo mishi, rarrafawa ya yi ya je wajen Noor ya roƙe shi gafara a taƙaice, ya amsa mai sannan ya nemi yafiyar Raudah da iyayenta, shi da zama Besty har abada, haka aka musu katangar ƙarfe mai ƙarfi tare da gindaya musu sharuɗa na musamman, sannan ita ma Raudah ta nemi yafiyar iyayen ta da mijinta saboda ta san ta kai su bango tun da har suka iya jure yin fushi da ita, tana hango fushin da Noor ya ke yi a cikin ƙwayar idanunsa amma ya ta iya? Ba ta ankara ba ta ga ba kowa a ɗakin daga ita sai Noor ashe duk sun watse, gefen Noor ta je ta kamo hannunsa tana kuka a lokaci guda ta na cewa:


"Ka yi haƙuri mijina sharrin shaiɗan ne ba zan sake ba, Please forgive me" kallon ta ya yi da rinannnun idanunsa ya ce:


"Why Raudah? Why? Me na miki haka da za ki saka min da wannan? Na dawo gida na na ganku da wani, wani fa Raudah?" Fashewa Raudah ta yi da matsanancin kuka

Please Login or Register in order to submit comment