Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lapiya Mommy ta ma ta, Arya ce ta ajiye littafin da ke hannun ta, ta je kusa da ita ta na cewa


"Anty zan biki", ba tare da Raudah ta ce komai ba ta kama hannun ta suka fita waje, yana tsaye a jikin motar shi ya saka kaftan Black colour, ba karamin kyau suka mai ba, saboda shima Noor kyakyawa ne, jingina ta yi da jikin motar ita ma tana gaishe shi, amsa wa ya yi ya miƙa ma Arya hannu yana faɗin


"Little zo mana mu gaisa", da sauri Arya ta karasa kusa da shi, hirar su suke ta yi da Arya, hirar ba ta komai ba ce face school, satar kallon Raudah ya yi, yaga tana ta lanƙwasa ƙafa alamun ta gaji, motar ya buɗe ya ciro chocolate ya ba Arya, cike da farin ciki ta ce


"Thank you uncle" tana gama faɗar haka ta shige cikin gida da sauri tana ƙwalawa Saleem kira.


Juyowa ya yi ya kalli Raudah, ba karamin kyau ta mai ba, murmushi mai sauti ya yi, bai ce mata komai ba, kuma a irin yanayin shi ba zai ce ta yi kyau ba, dama ta saba in dai Noor ne, da wuya kayi abu ya yaba, shi yasa ta ke jin daɗin Dee komai ya gani ya yi ta koɗawa kenan, koda abin bai ma ta kyau ba har sai ta ji ya shiga ranta, gaishe shi ta yi amma sai da ya ja wasu seconds sannan ya amsa, shiru ne ya biyo baya daga bisani ya ce


"Amarya ba kya lefi, ko kin kashe dan masu gida inji hausawa", murmushi Raudah ta yi da jin maganar da ya faɗa sannan ta ce


"Uhmmm su ango manya", dariya ya yi sannan ya ci-gaba da faɗin


"Dama nazo ne muyi magana na ji mene ne shirye-shiryen ki, kwana biyu ban samu zama ba ne, tunda daddy ya zo, sai da ya tafi yau da safe sannan na dawo dai-dai, kin san daddy sai a slow, sai ya saka ni a gaba ya ce duk inda za shi sai na raka shi, bayan ya san ina da schedules ni ma"


"Allah sarki ashe daddy ya zo, ban ma sani ba, ko da yake na ma manta yaushe rabon da muyi waya da kai", Raudah ta faɗa cike da damuwa


"Kiyi hakuri Amarya, abubuwan ne sai a hankali kema kin sani" Noor ya bata amsa cike da ƙwarin gwiwa, da uhmmmm kawai ta amsa daga nan bata ƙara cewa komai ba, shima shirun ya yi, sai da suka kwashe wajan minti biyar a haka sannan Noor ya katse shirun da cewa


"Raudah mene ne shirye-shiryen ku? Ina so na sallame ki ne gaba ɗaya tunda kinga yadda abin ya zo, ko da ya ke ai dama chan exams din ki ne ya ke ja mana delay, amma komai ya zama ready, amarya kawai na ke jira ko da yake inaga da yanzu kin aihu"


Mamaki ne ya kama Raudah ganin irin zumuɗin da ya ke yi, tunowa ta yi da wani lokaci da suka taɓa hirar event da Besty ya ke faɗa ma ta abinda ya ke so ta yi a bikin ta, murmushi ta yi sannan ta ce


"Anko za mu cire jibi, za muyi henna party, friends of honour, kamu shikenan, kai mene ne shirinka?"


"Ah ni ba abinda zanyi, friends ɗina ne za su haɗa mana dinner, daga nan shikenan, amma ba damuwa ki tura min list ɗin abubuwan da kike so sai na tura miƙi kuɗin, shikenan"?


Bata ce komai ba ta illa ɗaga kai da ta yi, daga nan suka ci-gaba da hirar su, sannan ta mai sallama ta shigaa gida ganin dawowar Abba tun dazu.






Fadeelah bata farka ba sai karfe uku, salati ta yi sannan ta miƙe zumbur kamar wacce aka tsikara da allura, kallon ɗakin tayi bata ga kowa ba, tashi ta yi sai taji wajan ya ɗan rage zugi amma dai tana ɗingisa ƙafa, toilet ta shiga ta ƙara gasa wajan kamar yadda taga ya mata dazu sannan ta yi wanka, a ranta tana tunanin a haka zata koma gida? Kar fa Anty ta gane, da wannan tunanin ta gama wanka ta fito, ganin Adnan ta yi a kujerar da ke chan gefen ɗakin, ba ta ce mai komai ba sai ya taso ya nufo inda ta ke


"Besty har kin tashi? Nima na gangara ƙasa siyan kati"


"Eh na tashi ka mayar da ni gida kaga yamma tana yi"


"To shinkenan shirya mu tafi"


Bayan ta gama shirya wa ne suka fito, duk da haka tana ɗingishi, kallon ta ya yi sannan ya ce


"Sai fa kin gyara tafiyar ki Fadeelah kada Anty ta fahimci wani abu" da kyar ta saita ƙafar saboda ko yaya ta haɗa su sai wajan ya ma ta zafi, amma haka ta daure suka tafi, suna isowa junction ya ajiye ta kamar yadda ya ɗauke ta, godiya ya mata tare da kalamai na soyayya sannan su kayi sallama ya tafi, da kyar ta iya karasa wa gida. Da sallama ta shiga, a tsakar gida ta iske Anty na wanke-wanke, karasa wa tayi ta ƙarba, taba faɗin


"Sannu da gida Anty"


"Sannu Fadeelah kin dawo?"


"Eh na dawo", ta bata amsa suka ci-gaba da wanke-wanken, suna gamawa Fadeelah ta tashi ta nufi hanyar ɗakin ta, kamar daga sama ta ji muryar Anty tana cewa


"Keee Fadeelah me ya same ki? Wacce irin tafiya kike yi haka?"....






Fan's yau fa asirin Fadeelah zai tonu, chabb ko yaya zata kaya gashi Anty kamar ta gano an ɓarar da darajar......
















VOTE






COMMENTS






SHARE


✍️
BADAWEEYERH
💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐



L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️


R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)




G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)




M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻


https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐


Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ


Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️




Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ


Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ


Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗






*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




PⒶⒼⒺ 1️⃣3️⃣


Kiɗimewa Fadeelah ta yi cikin in ina ta ce


"Anty ogan mu ce ta sani mopping shine na zame a kan tyles na faɗi" gaba ɗaya ta ruɗe da kyar ta iya haɗo ƙaryar ta bada amsa, kallo Anty ta bita da shi cikin tausayi ta ke faɗin


"Subhanallah!!! Sannu Allah ya ƙara sauki, akwai pain relief a ɗaki ki ɗauka ki sha sai ki kwanta".


Da to ta amsa ta wuce ɗakin Anty ta sha maganin, fitowa ta yi ta koma ɗakin ta, ta chanza kaya, sai da tayi sallar la'asar sannan ta kwanta nan da nan wani baccin ya kuma kwashe ta.




Adnan yana kan hanayar shi ta koma wa gida ya haɗu da wata yarinya sanye da hijabi har kasa, yarinyar Black beauty ce tana goye da jakar baya, kallo ɗaya Adnan ya ma ta ya ji zuciyar shi ta kamu da sonta, tafiya ta ke cikin nutsuwa wanda hakan ya ƙara jan hankalin Adnan, kokarin tsayar da ita ya ke yi amma sam ta ƙi tsayawa, a haka ya dinga bin ta a baya har ta iso wata unguwa ta masu rufin asiri, dai-dai wani matsakaicin gida ta tsaya, knocking ta yi aka buɗe ma ta, ta shiga, duk da ta ga wannan mai mashin ɗin yana bin ta hakan bai sa ta tsaya ba, wani yaro Adnan ya gani ya kira shi yana tambayar shi,


"Ɗan samari wannan yarinyar a anguwar nan ta ke?"


"Eh nan ne ma gidan su" yaron ya faɗa yana nuna gidan da ta shiga,


"Mene ne sunan ta"? Adnan ya ƙara tambaya


"Zeenat" yaron ya faɗa har a lokacin yana wasan shi, godiya Adnan ya ma yaron, sannan ya juyar da mashin ɗin shi ya tafi, a zuciyar shi yana ta murna da zumuɗi, shifa ya samu matar aure, ɗan gaskiya wannan yarinyar yaga alamun tana da tarbiyya kuma irin macen da ya ke so ce, cikin farin ciki ya karasa gida ba tare da ya anƙara ba.




Washe gari da safe Noor ya tura ma da Raudah ƙuɗaɗe masu yawa, sai da ta faɗa ma Mommy dukkan shirye_shiryen su ita da ƙawayen ta, Mommy ta ƙara bata wasu shawarwari, Hajiya Salimah bata samu zuwa a ranar da ta ce zata zo ba, washe gari sai gata niƙi-niƙi da kayan mata ingantattu da magungunan sanyi masu kyau da inganci,wanda ta saka a ka haɗo musu a wajan shahararriya kuma ƙwararriyar likitar mata, wadda ta shahara wajan sanin duk wani magani mai saka ni'ima da kuma ɗanɗano,gwana ce sosai a fagen sanin sirrin kula da jiki ciki da waje ma'ana mai kara mayar da mace cikakkiyar mace ta hanyar ƙwato ma ta daraja da ƙima a wajan oga, a gefe guda kuma maganin sanyin ta ma ba'a bar shi a baya ba wajan magance ko wanne irin nau'in sanyi, sanyi na ciki da na waje duk tafiya su ke yi su bar ki ki shana, ba wata bace face MAMAN YUSUF wacce ake ma laƙabi da (Dr mata ko kuma likitar Mata) ƴar mutan sokoto, (duk mai bukatar kayan ta ya tuntuɓe ni).

Cikin kwanaki ukun da Raudah ta yi tana amfani da maganin sanyi ba ƙaramin daɗin jikin ta ta ji ba, ita ƙanta ta ji chanjin da bata sani ba a tattare da ita, dama da maganin sanyin zata fara amfani kafin tayi amfani da sauran, a cikin satin suka je cire anko ita da fa'iza da kuma Maryam, fa'iza ƙawar ta ce Maryam kuma cousin ɗin ta ce, sun ciro anko masu kyau sossai, ko a cikin group ɗin bikin ta da suka tura ma freind's din santi suka dinga yi, dama kwata-kwata su goma ne ƙawayen, cousin's din ta huɗu sai sauran kuma freind's ɗin ta, duk abinda ta ke yi sai ta tuntuɓi besty sun yi magana, ko da Noor ya turo ma ta da outfit ɗin dinner sai da ta tura ma Besty, amma Besty na gani ya ce basu mai kyau ba, haka ta kira Noor ta ce a chanza basu ma ta kyau ba,


"Haba Raudah basu miki ba fa ki ka ce? Ai naga is one of Ur best colour" Noor ya faɗa cike da ɓacin rai


"Eh kawai bai min ba ne" ta bashi amsa a taƙaice, bai ƙara ce mata komai ba ya kashe wayar, wayar ta bi da kallo sai chan kuma ta girgizar kai tana faɗin


"Ohoo dole a chanza min ɗan bai ma Besty kyau ba, tunda bai mishi kyau ba nima bai min ba", chatting ta ci-gaba da yi chan ta ji massage ya shigo tana buɗe wa ta ga wasu colours ɗin Noor ya turo ma ta, ba ta mai reply ba kawai ta tura ma Besty ta ce ya zaɓar musu duk wanda ya mishi...








Sai da Fadeelah ta kwashe kwanaki biyu ta na jinyar jikin ta tukunna ta dawo dai-dai, tunda wannan abun ya faru Adnan sau biyu ya kira ta, ba kamar da ba, da a rana sai ya kira ta sama da sau biyar, wannan abu ba ƙaramin ɗaga ma ta hankali ya yi ba amma ta daure bata mai magana ba.


Yau bayan ta gama aiki da safe ne ta kira shi, sai da ta kusan katsewa sannan ya ɗaga


"Besty wai me na maka ne ka share ni? Tun ranar da abin nan ya faru sau biyu ka kira ni"? Fadeelah ta faɗa tana fashewa da kuka, shiru ya yi bai ce komai ba, sai da ta yi mai isar ta sannan ya bata haƙuri ya ce idan ta fito ta kira shi za su haɗu, ai kuwa jiki na ɓari ta shirya, Anty tayi ma sallama ta ce ta tafi shago, tana fita ta kira Adnan, nan da nan ya zo ya ɗauke ta zuwa hotel kamar yadda suka saba, wannan ƙaron ma sai da ya ƙara yin sex da ita, sai dai bataji zafi ba kamar na farkon, haƙuri ya bata na rashin kiran ta da bayayi saboda aiki ya mai yawa a yan kwanakin nan, sai yamma ya mayar da ita gida tare da alƙawarin zai zo gobe da daddare.


Washe gari ne Fadeelah ta koma shago gudun kar Anty ta je shagon watarana bata ganta ba ko a ce bata zuwa, dan ta san Anty da bin ƙwaƙwafi, ai kuwa ta sha faɗa a wajan Madam Cynthia, aikin ranar gaba ɗaya ita ta yi shi, sai karfe shida ta koma gida, gaba ɗaya a gajiye ta ke, da kyar ta iya yin sallar magriba ta ci abinci, Adnan ta kira ya tabbatar ma ta da zai zo bayan isha'i, har zata katse wayar ya ce


"Emm Baby yau kar ki saka kaya, hijab kaɗai za ki saka ɗan yau a matse na ke" Adnan ya faɗa har da kashe ido kamar tana gaban shi, da to kawai ta amsa mai sannan ta yanke kiran, tashi tayi ta nufi daƙi ta gabatar da Sallar isha'i, sannan ta saka wasu pant da bra masu kyau da ɗaukar hankali, katon hijab ta saka ta fesa turare a jikin ta.


Misalin takwas da rabi Adnan ya kira ta ya sanar ma ta yana waje, sallama ta ma Anty ta fice, wajan rumfar shanu suka nufa ganin anguwar ba mutane kamar kullum, ciki ta shiga shi kuma ya tsaya ta waje, matsowa ta yi ta ɗaga hijabin, ai kuwa yana kyalla ido ya ganta hankalin shi ya tashi, wasanni suka fara yi sai da ya samu nutsuwa da ita ya ma ta sallama ya koma gida, itama gida ta koma cike da farin ciki domin tana son kasancewar su a irin wannan yanayin...














VOTE






COMMENTS






SHARE


✍️
BADAWEEYERH




💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐



L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️


R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)




G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)




M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻


https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐


Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ


Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️




Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ


Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ


Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗






*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




PⒶⒼⒺ 1️⃣4️⃣


Yau ya rage saura sati ɗaya bikin Noor da Raudah, kuma a yau ne aka kawo lefen Raudah gidansu, lefe ne na gani na faɗa, sosai Raudah ta ji daɗin kayan domin Noor ya gwangwaje ta, a waya ta kira shi ta mai godiya, ko da ta nuna ma Besty bidiyon kayan ta waya shima ya taya ta farin ciki ga shi dama duk wani kayan da ta ɗinka sai da ta siya ma Besty shadda colour ɗin kayan, wasu kuma ƙananan kaya ta siya mishi saboda ta ce bikin nasu ne.




Ranar Laraba aka yi henna party inda ƙawayen suka saka lifaya bayan an kammala musu lalle ja da baƙi, sosai suka yi kyau cikin lifaya kalar sararin samaniya, ita kuma amarya ta saka baƙa, musamman aka kira Bebeji mai hoto ya zo ya musu hotunan, Masha Allah don duk wanda ya ga hotunan sai ya yaba domin sun yi komai cikin tsari da wayewa, a gidan Anty Salimah suka yi henna party ɗin, tun da Besty ya ga hotunan Raudah ya ke koɗawa cewar tayi kyau, ba abin da ta ke yi illa murmushi da jin daɗi ko ba komai ya wanke mata baƙin cikin Noor domin shi da ta tura masa emojin murmushi kawai ya aiko mata wanda hakan ba ƙaramin baƙanta ranta ya yi ba, washe gari Alhamis su kayi freind's of honour, nan ma amarya da ƙawayenta sun sha kyau har sun gaji, kuma Besty ya halarta, ko da Noor ya ga hotunan su tare da Besty ran shi ba karamin ɓaci ya yi ba amma ya danne a cewar shi kwana nawa ne ta zama mallakinsa.


Ranar Juma'a suka yi kamu a flourish event center, amarya Raudah da angonta Noor sun sha kyau sosai, duk motsin da Noor zai yi sai ya galla ma Besty harara, shi kuma sai ya yi murmushi ya waske, Raudah na kula da yanayinsu amma ba ta ce komai ba, a haka aka saka Raudah a lalle, sai a lokacin ne gabanta ya fara faduwa ganin fa da gaske gobe ne auren, nan da nan jikin ta ya yi sanyi, a haka dai aka yi kamun aka gama amarya ta koma wata shiru-shiru, ai kuwa dangi suka saka ta a gaba da tsokana wai munafurci ne ita dai bata iya cewa komai, sai wata matar abokin Abba ce mai tare ma ta.
Washe gari ya kama Asabar da misalin ƙarfe biyu da rabi dubanin jama'a suka shaida ɗaurin auren Nuradden Mukhtar Baba tare da amaryar sa Raudah Adam a babban masallacin ƙofar fada, a kan sadaki naira dubu ɗari da hamsin, bayan an gama ɗaura auren ne ango ya dinga gaisawa da jama'a yana washe baki kamar wanda aka ma gafara, can na hango Besty shima ya sha shadda blue sai ɗaukar ido ta ke yi yana ta hura hanci, a lokacin ne kuma Besty ya kira Raudah ya sanar da ita an daura,


"Amarya ayuriri!!! Yau kin zama matar aure" Besty ya faɗa cike da zolaya, kuka Raudah ta fashe da shi hakan ya sa ya kashe kiran saboda ba zai iya jurar jin kukanta ba, daga nan wajen cin abinci aka nufa inda aka ci aka sha aka yi hani'an....






Misalin ƙarfe biyar na yamma jerin motocin ɗaukar amarya suka tsaya a daidai ƙofar gidansu Raudah, a lokacin tana tsugunne gaban dangi tana rusa kuka, addu'ar zaman lafiya mai ɗorewa ake mata daga nan Anty Salimah da Anty Hassana ƙanwar Abba suka kama ta suka kai ta ɗakin Abba, shi da abokansa da kuma yan'uwansa ne a ciki, nasiha mai ratsa jiki suka yi mata sannan aka fito da ita aka nufi wajen Mommy, addu'ar zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba Mommy ta bi 'yarta da shi, da ƙyar aka ɓamɓare Raudah daga jikin Mommy zuwa cikin mota, har aka dangana ta da katafaren gidanta da Noor ya gina mata ba ta daina kuka ba, kowa sai santin gidan ya ke yi, a haka aka shigar da ita, daga nan kuma aka fara shirin sallar magriba saboda daga gidan za a shirya tafiya wajen dinner.




Wajen dinner ya cika da yan'uwa da abokan arziƙi ta kowane ɓangare, ango da amarya sun sha kyau har sun gaji, ranar kam an yi rawa da kuma watsi da kuɗi, da gangan Noor ya taka ma Dee ƙafa lokacin da ya shigo yi ma Amarya manni, shi har ga Allah ya tsani yaron, amma ba komai ai ya zo ƙarshe, abinci serve your self ne, can na hango Sanadin Besty Fan's 1 sun sha anko suna ta ɗibar kaza har da masu sakawa a leda nace to! Su kuma waɗannan gayyar wa? Ban gama mamaki ba na hango Sanadin Besty Fan's 2 suma an ba su fili suna taka rawa na ce yau kam Raudah'n Besty an sha gata, ta ba da Sanadin Besty Fan's sun miki kara, sai dai fa sun kwashi gara.
Ba'a tashi a dinner ba sai ƙarfe shabiyu na dare daga nan kowa ya watse ya koma inda ya fito, ƙawayen amarya kuma aka mayar da su gidansu Raudah saboda Abba ya ce babu mai kwana ba ya son wanan ƙaƙalen kawai a bar ango ya shiga gidanshi...




Adnan kam soyayya mai ƙarfi ce ta ƙullu a tsakanin shi da Zeenat, domin har ya kai kuɗin aure an saka rana, bai da wani buri da ya wuce ya same ta a matsayin mata, ya ma manta da wata Fadeelah don ko ta kira shi a waya ba ya ɗagawa, shi ya sa ta ɗan daga mai ƙafa kwana biyu.




Yau Fadeelah ta tashi da matsanancin ciwon kai, ga zazzabi, ko'ina a jikinta rawa yake, ga shi komai ta ci sai ta amayar, gaba ɗaya ta galabaita, ganin zazzaɓin ya ƙi sauka ne ya sa Anty ta shirya ta suka tafi asibiti, bayan likita ya gama mata aune-aune ya miƙa ma Anty result yana faɗin


"Congratulations, tana ɗauke da ciki tsawon sati shida"


"Ciii meee?" Cewar Anty ta faɗa tana zazzaro ido, tabbatar mata da cewa Fadeelah na da ciki likita ya yi, jin haka ya sa Fadeelah ƙwalla wani uban ƙara ta faɗi ƙasa sumammiya...


**** **** ****


A daren da aka kai Raudah Noor bai mata komai ba saboda kulle ƙofar ɗakinta da take yi kamar yadda Besty ya ba ta shawara, ai kuwa ba ƙaramar ƙuluwa Noor ya yi ba, amma ya tabbatar da cewa duk randa ta shiga hannunsa za ta gane ba ta da wayo, a haka sai da ta shafe sati ɗaya tana kulle ƙofar idan dare ya yi, ranar kuwa da ya sace ta ya riga ta shiga sai da ta faɗa ma masu anguwan garinsu, don sai da ya sauke ma ta sannan ya samu nutsuwar, kwana Raudah ta yi tana kuka, daga bisani kuma ta warware suka ci gaba da shan soyayyarsu kamar za su mayar da juna ciki, sai yanzu ne ta kuma tabbatar ma da kanta cewa tana ƙaunar Noor fiye da tunaninta, duk da halayen shi na i don't care ba wai ya daina ba ne, ganin shi ba mai irin wannan ra'ayin ba ne ya sa ta rage damun kan ta....




Satin su uku da aure kullum sai ta yi ma Besty ƙorafin ya ƙi zuwa, yau dai ya yanke shawarar zai zo, bayan ya sanar da ita, murna fal a ranta ta tashi ta hau gyare-gyare da soye-soye, wanda tun da aka kawo ta ba ta taɓa yi ba, bayan ta kammala komai ne ta sakawa gidan turaren wuta ai tuni ya baɗe da ƙamshi, wanka ta yi a gurguje sannan ta shirya cikin wani material, ɗinkin gown ne amma ya mata kyau sosai, ba ta daɗe da zama ba sai ga kiran Dee a wayarta, gate ta je ta buɗe mai kasancewar har yanzu ba su da mai gadi, tun daga wajan gate ta fara zuba mai shagwaba har suka yada zango a parlour'n, bayan ya huta ne ta zuba musu abinci suka fara ci a tare, a dai-dai lokacin ta ji kar'ar buɗe gate, dammm gabanta ya faɗi ta ce


"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, na shiga uku Noor ya dawo" gaba ɗaya ta rikice domin zuwan ta da kwana biyu a gidan ya ji tana waya da Besty, ai kuwa ya zaunar da ita ya zana ma ta serious warning, kuma ta masa alƙawarin ba ita ba Dee, wannan dalilin ne ya sa hankalin ta ya tashi saboda ba ta yi tsammanin zai dawo da rana ba tunda sai biyar suke tashi a office .


Shi kam Dee bai ma san tana yi ba kazar shi kawai ya ke ci kamar wani sabon mayunwaci, ci ya ke cike da kwanciyar hankali, cikin siririyar murya Noor ya yi sallama ya buɗe kofar parlour'n ya shigo, kasa ko da ƙwaƙwaran motsi Raudah ta yi jin har ya gama shigowa, bin inda ta ke Noor ya yi da ido ganin ko sallamar tashi ma yau ta kasa amsawa, kallon gafenta ya yi ai bai san lokacin da ya yar da jakar hannun shi ba, ƙarawa ya yi bakin shi na rawa ya ce


"Kai me ya kawo ka gida na wajan matata"? Noor ya tambaya yana nufar inda Dee ya ke, bai tsaya wata-wata ba ya shaƙo wuyan shi yana ci gaba da faɗin:


"Oh ƙawancen naku bai tsaya a waje ba har sai ka biyo ta cikin gidanta na aure? Ko da ya ke ba laifinka ba ne laifinta ne da ta ba ka wannan damar" nufar inda Noor ya ke Raudah ta yi, tana ƙoƙarin cire hannun shi a wuyan Dee da ya shaƙe saboda ta lura Besty'n ma ya kasa magana sai numfashi da ya ke fitarwa sama-sama, tsoron kar ya illata shi ne ya sa ta je ceton shi, ai kuwa tana saka hannu Noor ya wanka mata mari, sannan ya hankaɗa Dee saman kujera ya fara jibgar shi kamar wanda Allah ya aiko, sai ihu ya ke kwararawa sai da hannun Dee ya bada sautin ƙas

Please Login or Register in order to submit comment