Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

birk'icewa zagayi yak'eyi a d'ak'insa yana tunanin k'ada mama tace zata hanashi husna turowar kofa yaji a hank'ali...

" k'ayan Nakune basu zo ba Naga duk k'ayi wane iri?

" Tuntuni yana lure da maryam yadda ta tsane husna so yayi alwashin bazai k'ara sanar da'ita ba! Ga wannan system din k'ikaiwa fatima...

" Okay tohm, ta shiga d'akin ta,fatima bak'i kwanta ba??

" Tunanin husna nak'eyi ummy Abbana yana sonta sosai...

" Tabbas yana sonta Amma inaso kema k'i cere sonta da k'aunar ta aranki .....

" saboda me ummy?

" Zak'iga dalili sai agaba, kuma abunda Nakeso Nagaya mik'i shine k'i daina k'awance da'ita, if ma zak'uyi to baya baya please....

" ummy how comes? Bayan gida zata dawo! Zan dai jabaya but not...

" Ba saik'in k'arasa ba It's okay duk yadda k'ikayi....

" okay please ummy gud night...

" Night daughter!...

" Sweetie har k'a k'wanta?

" yes! By tomorrow musu finti zasuzo da masu funitures!...

" A'a why not bazak'a hadasu da 'yar uwarta ba?

" No zaifi k'owa room d'insa daban!...

" lallai ne Abban fati...

" K'wanciyar sa yayi ya kyaleta!!!...


●●●●●●●●

Mamah Dazu mun hadu da Abbana...

" Mama ce tayi saurin tashi, u mean mak'arantar ku yazu?

" a'a shine baban friend dita dana gaya muk'i zamu gaisa!

" Allah sarki, daf muk'e da rabuwa husna zak'i koma gidansa! K'i kasance mai hak'uri da juriya, babu kuma fitina, banason yawo da rashin k'unya kirik'i tarbiyar danayi mik'i....

" Mamana mekik'e fade? Rabuwa fa kikace? Yaya za'ayi Na tafi Na bark'i sai dai mu tafi tare....

" Hmm husna k'enan Ai duk inda k'ike ina tare dak'e, Addu'ata zata risk'e ki....

" Tohm mamata...

*ASALIN SU*

Family din Alhaji salihu janju family ne Mai Dumbin iyalai Alhaji hamid shine d'ana farko agurin mahaifinsa su bakwai ak'a haifa babarsu shuwa arab ce 'yan garin yamein ce itace mace ta farko acik'in gidan, hameed ne nafarko sai idress,sai saddik'a da shamsu sai k'uma hafsa da khadija, sai zainab wacce ta mutu tun tana k'arama...

Ana ce mata hajiya fad'ima su biyu mahaifiyar ta ta haifa daga ita sai rukkayya, tun suna k'anana suk'e da zumunci sunso junan su sun kumayi zumunci domin kowannen su yana son juna, hakan yasa sukayiwa juna Alk'awarin hada 'ya'yansu aure..

K'i shiyoyin fad'ima duk'an su hausawa ne babu k'ok'arin da bazuyi ba gurin fitar da'ita Amma hajiya fad'ima Allah yabata addini bana sanya gurin ibada, hak'ama 'ya'yanta! Duk'a 'ya'yanta k'aratu suk'eyi both islamiya da boko domin da mahaifinsu yace zai sak'asu a kasuwa hanawa tayi tace sai sunyi degree tuk'unna haka aka dauki tsana da tsangwama ak'a dora mata bayan wasu 'yan shekaru ta k'wanta jinya a shekarar Allah yayi mata rasuwa kowa yaji mutuwar ta! Daga Nan kishiyoyin ta suk'a dura ido a'kan hameed domin k'uwa Lok'acin Allah ya buda masa ga k'asuwanci ga Aiki sao da ya aurar da duk'kan k'annan sa sannan yayi aure....

" Matarsa ta farko sunanta islam 'ya'yanta uku! Haris, jameel sai shukrah..Sai matarsa ta biyu fadila 'ya'yanta biyu saddik da jameelah duk k'annin su k'aratu suk'eyi mahaifin su kuma sai k'udi yakeyi hakan yasa ya yank'e huk'uncin k'ara aure ya aure Aisha 'yar kanwar babarsa tun da tashigo gidan tak'eyiwa matan sa biyayya dak'uma bauta tun ashekarar da bata haihu ba Alhaji hameed ya karbi sa'id d'an gidan wan Alhajin su tun sa'id yana shekara goma tak'e kokari dashi kullun sai anyi masa habaici agidan itama basu barta ba gurin ci mata juya hak'an yasa Abun yafara damunta especially dangi da suk'a tsangwama mata, Alhaji hameed k'uwa yana mutuk'ar son Aisha kowacce tafiya in zaiyi da'ita yak'eyi sa'id kuwa sai daya zama star agidan domin Aisha ta tsaya mai kullum mak'aranta sai da sa'id yayi shekara 26 sannan Allah ya bata ciki tunda ta samu cik'in nan ta shiga bala'i ga Alhaji hameed baya zama saboda harkok'in sa...

sa'id shine yake mata Abinci in ya dawo daga mak'aranta kuma ya gyara mata dak'una Nan su haris suk'ace sai ya bar musu gida ita k'uma Aisha tace basu isa ba har suk'a kai ta bango tafito tace Da k'akanku da mahaifinsa cikin su daya, kuma Nan gidan su ne gado ne k'adai bazaici ba amma babu abunda ba zaiyi agidan nan ba, haka da Alhaji hameed yazo yayi musu ta tas, ba'afi kwanaki ba Alhaji hameed ya mutu mutuwar ta girgiza Aisha domin gani takeyi gatanta ya k'are hak'an yasa kishiyoyin ta suk'a kara tsan gwama mata ta kaida har da horan yunwa, sai sa'id ke siyo musu, k'afin mutuwar Alhaji hameed yabawa sa'id gida 2 da shaguna 2 duk ba wanda yasani sai mahaifiyar sa'id da'itace ta k'arbe ta k'ardun, gab da lok'acin haihuwar ta akace sa'id zai tafi nysc gashi ba 'akasar bani sa'id yaso k'in zuwa Amma Aisha ta tursa sa masa!...

Lok'acin da zai tafi yazo ya samu Aisha tanata k'aratun alkur'ani mama ne zan tafi badan son raina ba, Zan barki da mutanan da basu da Amfani agareki, tace k'ada kadamu sa'id zan kula Allah kuma zai k'areni, hak'a ya tafi ba dan yana so ba...

Ranar jumm'a tana bandak'i sai islam da fadila suna kuskus yadda idan ta haihu zasu k'ashe 'yar hak'an bak'aramin firgeta ta yayi ba, ranar tasha kuk'a sosai da sosai tana fitowa ta tarar dasu adak'inta aai sunzo hira, cik'in bak'ar magana tace Ai 'yar da zan haifa inaso tazama k'adangaren bak'in tulo a k'arshi a k'ar tulu Abarshi ruwa ya baci, Wai banda Abun mutane a zamanin nan har sai ance suji tsoron Allah? Ai yanzu ba sai ance kayi hankali ba!...

" Mufa ba magana muk'azo ki gayama na ba!

" Ai yadda zak'i yazama sarkin dabbobi ko yace zasuyi wasa basa yarda ba!!!....

" fadila ce tace lallai Aisha tak'amar k'i gidan nan k'o to an k'usa rabon gado ki hada k'ayan ki k'i ware...

" hajiya fadila k'in manta mai gidan kwanan nan yabar duniyar? To kinga shi bama gidan ya bari ba! D'uk da cewa shi ya gina gidan to duk'an nin mu 'yan hakane....

" Hmm Suk'aci sannan suk'a fita,

" Hamdala tayi sannan ta shige dak'inta karfe 3 dare Tafara Nakuda Adduoi takeyi ko ta'ina kafin kace me har ta haifi 'yar ta husna k'uka takeyi a haka ta yank'i cibe ta kuma gyara gurin mahaifar k'uma ta sak'a Leda ta tura jak'a, ko wank'a batayi wa 'yar ba ta goyata sannan ta fice daga gidan daga ita sai ak'wati tana sauri sauri ta samu k'afi mashin yadinga yawo da'ita daga karshe ma sauke ta yayi taga wane gida ta wada saboda ruwan da'akeyi tana shiga taga wane mutum a tsaye tace bawon Allah k'a taimak'i ne dan Allah kuk'an jariri yaji yace to shiga wancan dak'in tunda ta shiga batayi bacci ba kuk'a takeyi tare da addu'a, hak'an yasa tayi shawarar komawa yemein Amma k'uma sai ta tuna da k'annin ta da suk'a kaso auren su mahaifiyar ta ba ishashen lafiya ba!..

" Da safe ta bar gidaan tatafi garin banduwa ta k'ama haya tana sana'a husna sai girma tak'eyi hak'an yasa kullum Aisha sai son 'yat tak'eyi duk inda ta bi da ita mutane suyita rububin dauk'arta hak'an yak'ansa ta manta da duk wata damuwa...

Bangarin kishiyoyin ta kuwa sunyi bak'in ciki ba karami ba sun kuma sha Alwashin nemota, lok'acin da sa'id yagama k'aratun sa, yana zuwa ya tarar da mummunan labari aik'uwa yafara neman Aisha har sai da yazo garin banduwa yana isa gidan ya fashe mata da k'uka me isa k'ikayi haka? Tabashi labarin komai hak'a kullum sai sunyi waya da mahaifiyar ta k'uma tana kwantar mata da hank'ali..K'ullum sa'id sai yazo gidan nan alok'acin ya sanar da'ita yayi aure har maryam ta haihu...

K'anaso kacimin ne ba mahaifiyar ka baci yanzu ban isa k'asanar dani auren ka ba, sa'id ko nayi mak'a lefine? Nan mama ta sak'a kuka..

Wallahi mama ban k'i gaya miki ba sai dan karki hanani zuwa gidan nan k'inga mun saba da husna k'uma har tana k'irana da Abba, ina son husna ina k'aunar ta...

Mama ce tace anya sa'id husna tafi matarka da 'yar ka ne k'anaso ka zama azzalumi? Bak'a adalci kazo k'ana kula da abar da ba dole ba k'abar dolen k'a?

" please ki fahimce ni mama Allah husna mun saba k'uma tana sona itama...

" Ranta ne ya baci tace daga yau indai a matsayin uwa k'a dauk'e ne ba k'ai ba garin nan...

" Naji Amma k'i barmin husna na hadasu da 'yata!!!

" wane diris taje tace Anya k'anada imani sa'id duk ka canja fa...

" wallahi ban canja ba ina nan a yarda nake..

" k'arfa k'a manta ita tilo Allah ya bani, k'uma Na dauka Na bak'a ita duk soyayyar da nak'eyi mata haba sa'id...

" Tohm zan tafi mama bakomai Haka Allah yayi...

" Nan k'uma zuciyar ta tace k'in manta da lok'acin da ak'a kawo mik'i sa'id sun shak'u da mahaifiyar sa? Tana kaunarsa? Kin manta da irin k'ulawar da ya bak'i? Cikin yanayi Na damuwa tace sa'id Nan da shekara goma in muna rayi kazo ka dauk'i husna!..

" murmushi yayi ya jiyo ya dauk'i husna tanata Abba Abba...

Tunda yatafi husna ta dinga cuta k'amar bazata rayu ba ga wahalar rayuwa ga k'udi babu, A hak'a take biya mata k'udin mak'aranta K'ullum cik'in " k'uncin rayuwa"..

Tunda yayafara aiki da wannan k'udin ya fara safarar atampopi manya manya, a k'asuwa shiyake sauke diloli Allah yak'ara bud'a masa ga taimako da yak'e yawan yi..

Maryam k'uwa tsabagen kishinta bata yarda taga yana waya da wata, in bahaka ba tata fushi kenan, ga sa'id yana mutuk'ar son soyayya bama aci matarsa tana nuna masa ita k'uma maryam bata'iya ba yak'an zauna ya sanar da'ita hak'an Amma sai tace ai tunda tana bashi hak'kin sa Ai shikenan, yasha dawo mata daga k'asuwa gurin ta domin biyan buk'ata ita kuma tayita mita yafiya tak'ura...

Inna itace mahaifiyar sa'id har zugata akeyi ak'an ta yarda an mallake mata d'a wato babar husna sai inna tace Ai ne tsakanina da Aishatu sai addu'a domin tayi min k'omin babu ma tarbiya ga babu neman mata baya shan komai ga kokarin girmama Na k'asa dashi babu sata, To ai kuwa sai godiya ga k'anwar sa fa'iza kullum yazo sai ya k'ara mata karatu ku dubi yan uwansa da suke uba daya mugayan halinsu bama ace khalil, Ai aishatu sai dai Allahu ya biyata mukuma godewa Allah...

" Sai k'ishiyoyin ta suyi tayi mata Dariya sai tace Aine ba abar dariya bace ba domin bazaku taba hadani da d'ana ba ko Aishatu...

" Abunda zai k'ara burgek'a da sa'id rashin girman kai duk rashin maganarsa to baya wulak'anta mutum, haka idan fatima tayi har dukanta yak'eyi...

" Gashi baya nuna arzuk'insa komai dai dai yak'eyi lok'acin da maryam ta matsanta sai ansai mata mota yace badai yanzu ba ne Almajiri nake...

Sai cewa tayi nafasan k'omai sa'id kawai kace bazak'a siyar min ba...

To bazan siyaba arzukina bai kai nan ba...

Gashi baban maryam talakane sosai Amma hak'an baisa Ana rainata a dangi ba tasan yadda tak'e zaune da kowa, tunda suk'ayi fada da fa'iza kanwar sa tayi mata tatas hak'an yasa ta daina zagal galewa..

" fatima k'uwa duk da tsoron mahaifinta da tak'eyi amma tana uwar ta tana zugata...

*CIGABAN LABARI*

Da sassafe husna ta shirya zata tafi zuwa mak'aranta mama ce tace husna yana gank'i wane iri?

" Bak'omai mama!..

" A'a husna k'addai zancen danayi mik'i narabuwar mu k'ika sak'a arank'i?

" K'uka ta sak'a tace mama banason narabu dak'e ke k'adai a gidan nan!..

" husna kenan ai nema gidan mu zan k'oma can yemein zan k'oma husna gurin iyayena!...

" Tohm Amma k'uma ai...

" kark'iyi kuk'a, sai k'in dawo a rubuta jarabawa da k'yau...

" Bak'amar yadda husna ta saba ganin fatima ba, yau d'in k'uwa k'o k'ulata batayi ba hak'an yasa itama husna bata k'ulata ba har suk'a gama exam ta huce gida shigarta k'e da wuya suk'ayi kicibus da sa'id wane murmushi ya sak'ar mata itama shi tayi masa sannu da zuwa Abba...

" k'e za'ayiwa sannu tunda k'e kika dawo daga mak'aranta...

" Nan ta gaishe sa sannan ta shiga dak'i tana canja k'aya dama yau Alhamis..

" Mama Na riga Nasiyar mik'i ticket anjima flight zai tashi gurin 5 zamu k'aiki sai mu huce...

" Allah yayi mak'a Albarka, Amma sa'id kasane cewa Amana ce Agarek'a, Dan Allah k'abata tarbiya mai kyau, k'ada soyayya ya hanak'a tsawatar mata!

" K'arki damu mama zan kula da'ita sosai k'uma zanyi iya kokarina...

" Yauwa sa'id, husna ki shirya k'ayanki...

" To tace tana shiryawa tana k'uka komai sai da ta had'a sannan ta fito tana fitowa tak'ara fashewa da k'uka ta rungume mama..

" Mama ce ta dagota sannan tace so k'ik'eyi nema nayi k'uka? Mama ta nuna sa'id tace k'i bishi kamar yadda zak'i bine, Duk abunda ya umarci ke mai kyau k'iyi k'ikuma kyautatawa matarsa da duk wata bak'uwar fuskar dazak'i gani...

" Duk abunda k'ikace zanyi, mama duk hutu zan dinga zuwa gurin k'i...

" sa'id murna ba'acewa k'omai airport suk'a tafi sai da flight din mama ya tashi sannan suk'a tafi tun ahanya tak'e k'uka mai taba zuciya...

" Sa'id ne yace husna k'inaso nema nayi kuka?

" Cik'in ladabi tace to to to nayi shiru Abba kayi hakuri suna isa gida ya rik'o hannun ta har cik'in palour fatima da maryam da larai suna k'allo sallama suk'ayi sannan ya zauna yaja husna k'usa dashi....

" Ina yini ummy?

" K'allon ta tayi sannan tak'alle sa'id yadda yak'e rawar k'ai yanata fara'a..

" sannu da zuwa cewar maryam k'unsha hanya...

" Me zak'ici husna adafa mik'i...

" K'omai inaci abba..

" Fatima ce tace Ai tunda kik'a ci bak'in tuwon nan Ai komai ma zak'ici...

" murmushi husna tayi tace yauwa k'awata ashe k'insani...

" Abbane yace maryam zubomana Abinci..

" Ai yau ban dafaba!

" okay yayi miki kyau husna bari nadafa mik'i alright!..

" murmushi tayi tace toh abba...

" yana tafiya maryam ta dak'a mata tsawa ke dabbobin larabawa, ki tashi kije dak'in ki gashi can banson wannan k'allon nak'i...

" Har cikin ranta taji babu dadi Amma sai tayi shiru, ta mik'i...

" munafuk'a Ai yanzu kika shigo zanyi maganin k'i da wani kod'addan farink'i..

" Dak'in ta shiga batace k'omai ba ta zauna tayi tagumi, Har sa'id ya shigo Bata sani ba yacire Mata tagumin..

" Me maryam tayi miki? " murmushi ta kwak'ulo tace bak'omai...mamata..

" Oya open your mouth kici Abinci..

" Abba bani naci da kaina.... " No neni Abbanki ke dai kiyita taunawa..

" Tana tadariya har yagama sannan tace tayi wank'a ta k'wanta anjima zan dawo...

" maryam duk tayi labe tana jinsu, Ai kuwa dani ake zancen zanyi maganin ku zakici uban naki...

MUJE ZUWA...

YA RAYUWAR HUSNA ZATA KASANCE AGIDAN SA'ID...????

YA ZAMAN HUSNA DA FATIMA ZAI K'ASANCE?

" YA HUSNA ZATAYI DA TSANGWAMAR MARYAM....???

MUJE ZUWA.....

*Urs Nana diso*



Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[2:19AM, 5/15/2017] ‪+234 803 484 0276‬: _10-15_

*A*
*UBA*

*NA DAUKE KA*


_NA_
_NANA DISO_


http://nanadisoo.blogspot.com


Husna k'uwa Alwala tayi sannan ta gabatar da sallah! Zama tayi ak'an sallah yar tanata tunanin mama, book dinta ta d'akko tafara dubawa dumin gobe suna da maths, sai gurin k'arfe 8 tuk'unna ta rufe ta duba littafan islamiyar ta...

" My fatima ina sister d'in tak'i?

" Abba tana d'ak'i Should i call her?

" yes! K'irawo ta mana, cik'in murmushi ya fusk'anci maryam yace ina fatan k'ina lafiya?

" Me k'agani?

" Tun dazu da muk'a dawo Naga you're so silent...

" K'awai k'ai na k'e ciwo but Na sha magani ma...

" husna ce cik'in murmushi ta taho cik'in palour din...

" sa'id ne duk ya maida hank'alin sa k'anta yana k'allonta..

" tsugunnawa tayi tace Abba gani, fatima yanzu tak'e cimin k'ana k'irana?

" Daga yau k'ada k'ikara zama a d'aki k'e daya ki fito Nan palour d'in k'inji...

" Tohm Abba! Sannu da dare Anty maryam...

" Wata harara ta yarfa mata sannan tace k'izauna a k'ujera ko bak'i saba ba?

" Bansaba manya suna sama nima ina sama ba shiyasa...

" fatima ce tace uhm Abba k'aga maths d'in da yak'e bani wahala please k'akoyan...

" Husna tana ta k'allon su, Sai ta tuna mama hak'a itama tak'e k'oya mata, sa'id ne yace ina nak'i book din husna?

" Abba ni na'iya ai!..

" fatima ce tayi dariyar mugunta wai ta'iya wannan maths mai wahala, Abba cene tazo tayi mak'a...

" Oya husna solve this one! Murmushi tayi ta k'arba k'o munti biyu batayi ba tace am done tana dariya!..

" Maryam ce jik'inta yayi sanyi yadda taga husna nan da nan tagama ko calculator babu a hannun ta!..

" Sa'id yace weldone my baby gobe zan siyo mik'i laptop k'ema..

" Fatima k'uwa cewa tayi sai da safe bacci yazo.....

" Husna ma tace Abbana sai da safe!

" Gurin 3 Na dare ya shiga D'akin ta ya k'unna mata Ac sannan ya fita...


●●●●●

Tunda mama ta'isa yemien nena wato mahaifiyar mama da ummi da Amira suk'a tarota babu Abunda suk'eyi sai murna Hak'a driver yaja su har cik'in gida suk'a zube A palour!...

" sannun ku 'yan uwana ina yini nena?

" Nena ce cik'in dauren fuska tace Yanzu abunda k'ik'aye k'in k'yauta shek'ara goma k'ina can k'ina fusk'antar rayuwa...

" Allah Nena banyi hak'a dan baccin rank'i ba, sai dan gudun cutar k'i k'ada ta tashi k'iduba k'iga ummi An sak'eta Amira k'uwa shiru har yanzu!, idan Nace zamu dawo Nan Ai sai abubuwa su jagwal gwale!...

" ke Aisha k'arki manta Allah shiyak'e k'addara komai...

" K'iyi hak'uri komai ya huce...

" Ne da naso ganin husna, Ashe ta k'oma hannun sa'id k'uma?

" Amira ce tace Nima Naso ganin ta wallahi yanzu k'in bawa sa'id hmm sai daga baya yace...

" ummi ce ta k'atse Amira ke me'isa bak'i iya magana ba? Sa'id din ba dan yaya bani ba?

" Nena ce tace Ai indai Aisha ce Hank'alin ta da sauk'i Ai husna zatazo mana huta Nasan tunda ga uwarta Anan!!!...

" DanAllah Nena kiyi hakuri Nasan Nabata mik'i rai Amma k'uma Allah da dalili nayi Nan mama ta bata labarin k'omai da k'omai....

" Hmm Ai shiyasa farkon Auren k'i Nak'i Amincewa saboda k'ishiyoyin nan na zamani da basuda cikakken hankali. Allah yasawak'e k'i tashi k'ije ki'ci Abinci....

" Tohm NeNa, Amira ce tace ya ummi barrister yayi min waya yau zaizo...

" ke yazo yayi min me? A beg tell him bananan inada lecture anjima ma...

" Mama ce tace Haba menene hak'a..

" Allah yaya tsoron mazan nak'eyi wallahi k'uma matansa uku fa infact i hate him..

" let me tell you something any thing daya faru dak'e keep it aside, haka Allah yaso ba d'uk maza aka taru ak'a zama daya ba, ke indai mijin k'i yana sonk'i to shikenan fa k'incere tuta k'oma me za'ayi mik'i ayi mik'i al u need is your god keep praying....

" Ummi ce tayi shiru Na D'an lok'aci sannan tace thanks for your advice ....

●●●●●●

Tun Da daddare sa'id ke lallaba maryam ak'an buk'atar sa Amma sai basarwa tak'eyi cik'in wane yanayi ya k'alle maryam yace bakya damuwa da buk'ata ta ko k'adan?

" Hmm sa'id kenan kai kafiya fi'ili wallahi dubu yadda Na rame saboda duk k'asani agaba!..

" haba sweetheart Am your husby oya please lok'acin ya fara Nark'a mata wasu k'alaman soyayya batasan lok'acin da ya fara sarrafata ba cik'in salo nasa na soyayya tuni ya fita hayyacin sa, ya shiga wata sabuwar duniyar...! Sai gurin karfe 2 ya sumbace bak'in ta tare da fad'in i love you maryam!...


Husna da safe tana tashi da safe ta huce zuwa toilet sai da ta tabbatar ta wank'e shi sannan ta d'akko tsintsiya tayi sharar dak'in ta goge ko'ina wane room freshner ta fesa. Wank'a ta shiga sannan ta sak'a k'ayan skull ta shirya tsaf Sannan ta fito palour da Alamar babu k'owa kitchen ta shiga tace larai ina k'wana?

" A'a husna kice k'e hark'in shirya?

" K'inga lok'aci yana kok'arin hucewa shiyasa..

" Hak'ane Amma Ai sai takwas zasu fark'a su k'arya fati k'uma tafara shirin mak'aranta!...

" Ai k'uwa bazan iya jiransu ba bari Naje Na tashi su kokuma Na tafi Ne k'adai...

" Alhaji zaiyi fad'a idan kik'a tafi ke k'adai...

" Tana fitowa daga kitchen taga Abba A zaune ina kwana Abba?

" Har k'in shirya ta Abba?

" Gask'iya Abbana baccin ku is over tawane k'ada manyan idanu wanta, ban ma sani ba k'o ka fita masallaci...

" Dariya yayi yace ta Abba Naje masallaci mana...



Please Login or Register in order to submit comment