Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kedai fad'i buk'atarki kawai 'yammata kiga aiki da cikawa.
Cikin tsoro Safna ta ce, "malam dama inaso shi wannan saurayin yazo dakansa gidanmu ya ce, " yana sona, kuma yasaki matarsa Dan wlhy inada kishi sosai malam, kuma inason sa sosai har inaji idan ban sameshiba zan iya mutuwa wlhy, Dan ALLAH malam ataimaka mini.
Malam da'u ya ce, "babbam taimako aljihunki 'yammata.
Baseera da dama tasaba indai bin malamine, hankalinta kwance ta ce, " malam kaima Kasan kud'i ba matsalarmu bace aii, inhar buk'ata zata biya to kad'auka kasamu kud'i konawane.
Malam da'u ya wangale bakinsa dake cike da damzar goro, wasu hak'oranma sun fita, ya ce, "baseera indai kece aii saidai nafad'ama wani, Dan haka kisanar da k'awarki tagama samun abin sonta.
Wani faranti yajawo dake cike da k'asa, yafara Zane Zane yana motsa baki, bayan yagama yamaida kallonsa Kansu, kince ya sunansa?.
Safna ta CE, " nidai bobo nasani, amma Wanda nasaka yamin bincike akansa ya ce, "Abdulmaleek.
Malam da'u yakuma maida kansa k'asa, shiru yayi Dan shikad'ai yasan miya gani, to ammafa yana fad'a mata gsky bazata sakar masa nairoriba, gata kallon d'aya zaka mata kagane kud'i sun jik'ata, Dan haka ya canja shawara, ya ce, " zaki gansa anan kusa kam, saidai bazan fad'a miki ranarba, sannan kuma saikun had'u zan fara aiki akansa, ga wannan yazama kwallinki, wannan kuma hoda.
Kar6a Safna tayi tai godiya.
50k suka ajiye masa suka tafi suna godiya.

Na ce, "hummmm.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Bobo har police tetion yaraka 'yan sanda, saida aka gark'ame Haneef Wanda tuntini hankalinsa yafara tashi, yaza'ai kamarshi d'an gata ace anakawoshi nan gurin?, gashi sun kar6e masa waya bare yakira dad nasa yasanar MASA halin dayake ciki.
Yad'au alk'awarin Indai yafita agurinnan saiya wulak'anta yan sandar nan da saurayin nan.

Saida yayama police d'in nanan gargad'i sosai akan wlhy kowaye yazo karsu bada belin Haneef, sannan yawuce yanufi office d'insa, yanason fara shirya yanda zasu shiga kotu.

+
Yaduk'ufa sosai wajen latsa lap-top, gaba d'aya hankalinsa yana wajen binciken family d'in Alh Sunusi Dala, da sauri yad'ago danjin an ta6ashi, jar uban nanan kai yafad'a cikin ihun farin ciki, rungume juna sukayi shida bak'on nasa.
Ammar yaushe a k'asar?.
Ammar yay dariya wlhy mutumin jiya da daddare, shiyyasa yau naimaka sakko amma natarar kafita.
Kabari kawai wlhy naje wajen yaranka ne sukamamin wani d'an iskan mutum.
Kai Bobo kana nandai baka canjaba?, yanzu kuma wa'aka kafama tarko ne?.
Wani murmushi bobo yasaki, kamar mai rad'a ya ce, d'a gurin Alh Sunusi Dala!.
Ammar yad'an zaro ido, Bobo Kasan kuwa sunanwa ka fad'amin?.
Kwarai kuwa nasani, ni kam ainafi kowa farincikin dawo warka wlhy, inason kaima yaranka magana su k'ara gark'ameminshi sosai, Dan ranar litinin nakeson mufara sharia.
Baka da damuwa da hakan abokina.
Yes sir!, Bobo yafad'a yana sarama Ammar.
Dariya ammar yayi yace d'an iska, ALLAH dai ya shiryaka, duk kabi katakurama 'ya'yan manyar garinnan, ina baby Nawal da amarya?.
Saida ya sauke numfashi sannan ya ce, "suna lfy.
Masha ALLAH, kasanar da amarya zanshigo weekend cin abincin amarci, daganan naga amaryar tamu, tunda ALLAH baisa ansha biki daniba.
ALLAH ya kawoka Bobo yafad'a.
Daga nana hirarsu suka cigaba dayi, dagani kasan sunyi bala'in shak'uwa da juna.

*Waye Ammar?.*
Ammar Khaleed Adam, d'ane ga Alh Khaleed Adam, abokin Appa na k'ut da k'ut wanda yayma Rahma k'yautar mota ranar walimar makaran tarsu, su 7 mahaifansu suka haifa, shine na biyar agidansu, yanada yayye maza da mata su hud'u, sai k'anne biyu mata, Ummy matar ya Hamza dakuma autarsu Lubna ita sa'ar su khairiyyace.
Tare sukayi karatu da Bobo tundaga primary har secondary, daganan kowa Yakama inda yafi wayau, Bobo yatafi karatun lauya, shikuma yafad'a aikin 'yan sanda, ayanzu haka shine Qumissioner of police na jihar kano, sun shak'u sosai da Bobo, bashida wani aboki sai Ammar da yayyensa.
Duk wani aiki da Bobo yarikito Wanda yake buk'atar tsaro to Ammar ne ke taimaka masa, yanzuma yayi wata 'Yar tafiyane ta wata biyu, shiyyasa baisamu damar halartar bikin Bobo ba.
Shima matarsa d'aya da yara biyu duk maza.
Wannan kenan.............







*_luv u oll my fan's_*
*_(((S)))...........2017_*
[14:23, 10/09/2017] hm: ����‍��typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


3⃣9⃣=4⃣0⃣

_washe gari_
Rahma tatashi tayi duk abinda tasabayi dukda tasan yau weekend Bobo bazai fitaba, tana cikin saka turare a falo bobo yafito sanye da jallabiya ruwan toka mai gajeren hannu, rissinawa tayi ta gaidashi, kamar yanda yasaba ya amsa da lfy.
Amsa gaisuwar nan nabama Rahma haushi, amma babu yanda zatayi.
Yad'anbi falon da kallo komai tsaf, gawani k'amshi na musamman, yana jin dad'in kasancewarta mace mai tsafta.
Itadai cigaba tayi da abundan takeyi. Ya ce, "bari nad'anje wani waje nadawo.
Aranta tace kofa wanka bakayiba, amma afili ta ce, " to ga Break.
No barinaje nadawo, aiba dad'ewa zanyiba, yafad'a yana ficewa.
Itama ta ce, "ALLAH ya tsare.
Dukda yafita amma yajiyo addu'arta.

Bayan takammala saka turaren zuciyarta tabata shawara dataje ta gyara masa d'akinsa, kamar bazatajeba saikuma tatuna nasihar mahaifiyarta da ummansu Basma.
d'akin tanufa da tunanin ALLAH yasa bai rufeba, tana tura k'ofar tabud'e, k'amshinnan yana nan kamar kullum, yau tanutsu takalli ko ina na d'akin, komai farine tas, aranta tace farin Abu name tsaftane.
Sai manya manyan hotunanan Ni'ima Maman Nawal, bani gurin ita kad'a, wani gurin kuma shida ita.
Ko kad'an bataji haushiba bare kishinta, Bata 6ata lokaciba tafara gyara ko ina, Dan danan tagama d'akin yak'ara d'aukar haske komai yana d'aukar ido.
Bathroom tashiga zata wanke saitaga kaya ajik'e abokiti.
Shiru tayi tana tunanin ta wanke kota barmasa abinsa, wata zuciya ta ce, " ki wanke, kobabu komai zaki samu lada aii.
Haka tazauna tahau wankin gajerun wandunansa da vest, akunyace take wankin tamkar tana gabansa, gudu gudu sauri sauri tagama bataso yazo yataddata tanayi.
Dandanan tagama tawanke bayin, tad'auki kayan tafito waje, acan baya taje tashanyasu sannan tadawo d'akinta tashiga wanka, Dan Nawal bata tashiba.

Shigarta wanka babu dad'ewa yashigo gidan, d'akinsa yanufa kai tsaye, baki da hanci da ido yasaki yana kallon d'akin NASA, yalek'a bayi nanma fes, bokitin daya jik'a kaya wayam, wani lallausan murmushi yasaki, labulen window d'insa yad'aga, can yahango kayan ashanye.
Jiyay wani Abu nata6a zuciyarsa, afili ya ce, ''ALLAH yaymiki albarka.
Fitowa yayi yanufi d'akin Rahma, hakan yayi daidai da fitowarta daga wanka, daga ita sai guntun tawul iya cinya.
Wata tsayuwar sojan badakkare bobo yayi, sai Raba idanu yake akan Rahma, da wannan munafikin kallon nasa k'asa k'asa.
Itakam dukta rikice, waige waigen abinda zata rufe jikinta kawai takeyi, can ta hango hijjabin sallarta, amma dole saitabi tagabansa zata d'auka, ganin haka saikawai takoma cikin bayin da sauri.
Murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya, yak'arasa inda hijjabin sallarta yake yad'auka, ahankali yak'arasa har k'ofar bayin ya kwankwasa, Rahma dake jingine da k'ofa tagwalo ido waje, k'irjinta sai dukan Tara Tara yakeyi.
Yak'ara kwankwasawa.
Muryarta narawa tamkar zatayi kuka tace yes, yanda tayi maganar tabashi dariya amma saiya gimtse ya ce, "bud'emin k'ofar.
Innnalillahi tace azuciyarta, wai mi mutumin nan yake nufi.........maganarsa ta katse mata tunani, " wai kobaki jinane?.
Bayan k'ofar takoma tala6e sannan tabud'e, gaba yay tamkar zai Shiga, saikuma yamik'a mata hijjabin, dasauri takar6a tamaida k'ofar burum tadatse.
Girgiza kai yayi yanad'an ta6e bakinsa, yazauna bakin gadon yana shafa kan Nawal daketa barcinta hankali kwance, shi mamakin kansama yakeyi, wai miyake jirane?, zuciyarsa ta ce, "kanason sake kallon Rahma ne.
d'an tsaki yaja yamik'e yafice, shi adole zuciyarsa tayi k'arya.

Saida taga yafita sannan tafito, taje tasakama k'ofar key, sannan tazauna tagyara jikinta, tasaka Riga da wando na Pakistan, nakula tana son irin kayannan sosai.
Nawal ta tashi itama tayimata wanka tashiryata cikin wandon Jin's da pink d'in T shert mai k'yau.
Falo suka fito, fitowarsu babu dad'ewa shima ogan yafito, haryayi wanka yashirya cikin jins blue da farar Riga sai zabga k'amshi yakeyi.
dinning suka nufa, Rahma sai sinne kai takeyi Dan kunya, shikam ko'a kwalar rigarsa, yanacin abinci Nawal namasa surutu, iyakarsa Yamata murmushi koya d'aga kai.
Rahma ta ce, " azuciyarta, muskili kafi mahaukaci ban haushi.
Suna kammalawa Nawal taja hannun Rahma wai suje tamata lilo, fitowa sukai sukabarsa kwance saman doguwar kujera yana kallon film.

Sunacan a lambu Rahma NATA biyema Nawal suna lilo, jiyay falon babu dad'i Dan haka yafito, jiyo dariyarsu alambu yasashi nufarcan, Rahma na zaune akan lilo, Nawal na shillata suna dariya, k'arasowarsa yasa Nawal cewa lah papa kaima zona lilaku.
Kai ya girgiza mata alamar A'a.
Takwa6e fuska zatayi kuka, cikin takun k'asaitarsa yak'arasa wajen lilo d'in, Rahma tayi yunk'urin sauka Nawal ta ce, "momy kubiyufa zanyimawa, sandarewa Rahma tayi azaune, kafin ta farga Bobo ya haye lilo d'in amma d'an nesa da ita.
Da k'arfi Nawal ta hankad'a lilo d'in, aiko sukayi gaba kamar zasu fad'i, da Sauri Rahma ta ruk'unk'ume Bobo, shima yarik'eta.
Nawal Yar kwal uba tacigaba da lila lilo da k'arfi, basuda za6i bayan rik'e junansu dak'yau, Nawal dai sai dariya takema iyayen nata, saida tagaji Dan kanta sannan tadaina lilasu.
Bobo yabud'e idanunsa ahankali danjin lilo ya tsaya, ga Rahma na mutsu2n kwace kanta, yana sakinta tasauka, da Sauri tabar wajen, binta da kallo yayi yana murmushi, Nawal takatse masa tunani, baby d'orani muyi tare tunda momy tagudu.
daukarta yayi yad'ora sukacigaba da lilonsu zuciyarsa cikeda tunani kala kala.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Safna zaune gaban Abba da ummi da alama fad'a ake mata, Dan fukarnan adagule take.
Abba ya ce, " wlhy nabakinan da wata uku zuwa hud'u kifito da miji a had'a aurenku keda amira, inbandama auren ameerar da sati biyu zan baki, amma Abubakarne yaceceki ya ce, "abari ahad'a bikin dan a samu sauk'i."
To saikiyi gaggawar sanar da Wanda kikace kinason harkikaso wulak'antamu akansa.
Insha ALLAHU Abba zan kawoshi, nidai kuyi hak'uri kubar ganin laifina, ALLAH yariga yarubuta Dama shid'in Mijin k'anwatane baniba...
Dallah yimana shiru!!, ummi takatseta atsawace, Mara mutunci kawai, Indai duniyace aigaki gata nan, kuma koyaya Wanda kikace kinason yake wlhy haka ZAMU aura miki shi, kijecan kiji da bak'in halinki, tashi kibamu waje mu.
Mik'ewa Safna tayi tabar falon tana k'unk'uni.

Na ce, " ALLAH ya shirya to.


.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Ad'an hanzarce takeyin aikin gidan, Sauri take tagama dawuri taje tayi girki Dan maigidan ya ce, "mata yau abokinsa zaizo da iyalinsa, tagama komai tsaf har girkin ta kammala d'akin bobone kawai yarage mata shima Dan yana kwance ad'akinne.
Saiwajen 12 yafito daga d'akin yafita danufin siyo ruwa datace masa babu.
Yana fita tashiga d'akin Dan gyarawa, tagama aikinta lfy lau, tsautsayi yasa takai hannunta kan wani hoton Ni'ima datayi bala'in k'yau, Ashe bai zauna da k'yauba aiko yafad'o jikake taratsatsa!!! ya tarwatse ak'asa abinka da gilas.
Hakan yayi daidai dashigowar Bobo falon, da hanzari yanufi cikin d'akinsa, aiko abinda yake zarginne yagani, dandanan fuskarsa ta canja kama idonnan sukayi ja danshi aganinsa da gangan Rahma tayi saboda batason ganin hotunnan tunda dai yasan mata da kishi.
Tunda yashigo jikinta ke rawa, tabud'e baki arazane zatayi masa magana yadaka mata tsawa.
Dallah yimin shiru, dama kina shigowa gyaramin d'akine danki kashemin hotuna?, to wlhy idanma kishi kikeyi da ita kidaina Dan babu yanda kika iya da ita, wannan dakike gani itakad'aice nabawa zuciyata, daga itakuwa babu wata mace dazata samu haka daga gareni, wlhy akan wad'an nan hotunan sainayi mugun sa6a miki, banason cikin da iskanci.
Rahma tamatso danufin tsugunnawa tabashi hak'uri amma abisa tsautsayi ta taka gilas ak'afa, runtse idonta tayi saboda azaba, dama ga hawaye tuni sun wanke mata fuska.
Tsawa yasake dama mata, dallah malama fitarmin ad'aki, kuma karna sake ganin k'afarki ad'akina.
Ran Rahma ya6aci sosai ganin yanda yake cimata mutunci akan hoto, Wanda inyanzu yaso zaikai amaida gilas d'in daya fashe, haka tataka k'afa tabar d'akin tana kuka, tanazuwa tazube akan gado, ga azabar da k'afarta take mata amma bata kulaba, sai kuka maicin rai data saki.
Duk abinnan yake faruwa Nawal tana can baya tana wasa, Rahma taturata wajene dantabarta tayi aiki, batason surutu.

Bobo kam tana fita yadurkushe agaban hoton, d'agosa yayi yana gogewa tamkar zai fasa kuka, muryarsa na Rawa ya ce, "kiyi hak'uri Ni'imana bada sanina tayiba, ALLAH ya gafarta miki ya yafe miki kinji.

Nawal tashiga d'akin Rahma tana kwala mata kira momy! Momy!!, tak'arasa cikin d'akin da murnarta, amma ganin jini ahanyar sai jikinta kuma yay sanyi, tak'arasa har bakin gadon tana kallon k'afar Rahma da gilas ke jiki ga jini yanata zuba ak'asan wajen.
Fitowa tayi da gudu tanufi d'akin Papan ta, har yanzu yana gaban Hoton adurk'ushe, papa papa zokaga k'afar momy jini yanata zuba dayawan tsiya.
d'agowa yayi yana kallonta, yanda tabirkice shima sai jikinsa yay sanyi, mik'ewa yayi suka nufi d'akin Rahma d'in, gsky shima abin yabashi tsoro ganin jinin dad'an yawa, ga gilas babba kafe ak'afarta, tana kwance rubda ciki tana darzar kuka.
Tsugunnawa yayi Kusada k'afar yakama gilas d'in zai cire tasaki wata k'ara wadda tasaka Nawal fashewa da kuka itama, ga gilas d'in yakafe dayawa, ganin karya k'ara jimata ciwo yasa yamik'e dasauri yaje d'akinsa yad'akko key d'in mota.
Dawowa yayi ya ce, " tashi muje asibiti acire miki wannan kwalban.
Banza tayi masa tacigaba da kukanta, wani haushi yak'ara turnik'eshi, baisan lokacin daya sungumetaba yay waje da itaba, Nawal nabinsa abaya, Nawal tabud'e masa k'ofar motar yasakata aciki, suma suka shiga sai asibiti.........





_kuyi hak'uri da wannan yau kaina namin ciwo._



*_luv u oll my fan's_*
*_(((S)))..........2017_*

����‍��typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


4⃣1⃣

Asibitin ya sulaiman sukaje, ALLAH yasosu sun tarar dashi.
Aiko ansha fama wajen cire gilas d'in nanan, Rahma tasha kuka dukta fita hayyacinta, ga k'afar harta d'an kunbura.
Shikansa Bobo ya tausaya mata, saiyanzu yake ganin abinda yay mata bai k'yautaba, to amma idan yatuna miyakai hannunta wajen hoton saiyaji ransa ya 6aci.
Da hakadai aka kammala, ya Sulaiman yamata allurai tad'an samu nutsuwa.
Bayan an kammala bobo ya ce, "ya yarinyar nan kuwa?.
Jikinta kam saidai muce alhmdllh, ammafa yakamata asan iyayen yarinyar nan Abdulmaleek, gashi kace zaku fara shiri'a ranar talata, kasanfa Alh sunusi dala mutumne mai had'arin gsk, sarai zai iya bincike akan yarinyar, kuma zai iya aikata kimai Dan ganin d'ansa ya ku6ta.
Hakane Yaya, amma inata iya k'ok'arina wajen Neman iyayenta, saidai kutayamu da addu'a kawai.
To ALLAH ya taimaka.
Amin dai, bari mubiya muganta saimu wuce gida.
Okey, kardai kamanta kusiyi maganin.
Babu damuwa, k'arasawa yay inda Rahma take fuskarsa babu walwa, yakama hannunta ta sakko.
Ya Sulaiman dake kallonsu ya ce, " saidaifa kad'auketa kamar d'azu, Dan babu yanda za'ayi ta iya taka wannan k'afar.
K'ara 6ata rai yayi, kamar bazaiyi maganaba, saikuma ya ce, "Yaya ba ancire ba?, eh ancire, amma karfa manta yanda gurin yake a yanzu, idanmma kunje gida ad'an gasa k'afar da ruwan zafi.
Baice komaiba ya d'auketa, saiwani kauda kai yake daga saitin fuskarta, itama saita runtse ido Dan bata son ganinsa.
d'akin da yarinyar nan take yakaita, yadireta saman kujerar gaban gadon, lahh Muheebat! kece?, Rahma tafad'a tana kallon yarinyar.
Itama tashi tayi zaune tana dariya Dan ganin Rahma.
Bobo ya ce, " kinsanta ne?.
Eh nasanta, K'anwar direban muce idris, dama sunata nemanta tun tuni wlhy.
Ajiyar zuciya bobo ya sauke ya ce, "Alhmdllh, yaciro wayarsa yakira Ya Sulaiman, babu dad'ewa kuwa ya iso, shima yaji dad'i sosai dajin labarin.
Sun ajiye magana akan anjima zasuje gidansu Muheebat, dukda bata iya magana to tanajin abinda suke fad'a, Dan haka taita murmushi.

Bobo Yakuma d'aukar Rahma zuwa Mota, daganan sukayi gida, motar tsit babu mai magana kamar wasu kurame, Bobo sai shan k'amshi yakeyi, itama ganin haka saita d'auke kanta, dama can suka baro Nawal zatabi ya Sulaiman gidansa.
Koda suka shiga harabar gidan saiya bud'e motar yay tafiyarsa ciki yabarta.
Rahma tayi wata dariya azuciyarta ta ce, " kama dawo wlhy, dan babu inda zan motsa.
Aiko tayi zamanta amotar, shikam haryaje k'ofar falon saiyaji babu motsinta abayansa Dan haka ya waiga, can ya hangota cikin mota ko motsawa batayiba, afili ya ce, "wai mi waccan abar take nufi da nine?, koni bawantane dazanta d'aukarta ina ajiyewa mtsooow, yak'arashr maganar dajan tsaki.
Komawa yayi wajenta sai wani d'aurewa yakeyi, Rahma ta hangoshi yana tahowa, tayi murmushin mugunta tana fad'in kadaiji dashi.
Bemata maganaba yabud'e motar ya d'auketa, itako ta lumshe idonta kamar mai barci, haushine yak'ara turnuk'e zuciyar bobo, gani yake tana k'ara langya6ewa ne kawai.
Koda yadireta a gadon bai kalletaba yajuya ya fita.
Ita kuma taimasa gwalo��, wai dole dai ad'auketa. lol.

Tana nan zaune har kusan minti talatin, harta fara tunanin yanda zata fita taci abinci Dan yunwa takeji sosai, tayunk'ura zata tashi taji wani azababben zafi, danhaka takoma ta zauna, wai miyasama tabar Nawal tabi ya Sulaiman ne?, yanzu da tananan ai data rage mata wani abun.........bata rufe bakiba taji anturo k'ofar.
Kamshinsane ya tababbatar mata dashine, Dan haka tak'i d'agowa danko sallama bataji yayiba.
Tire yadire ak'asa na kayan break, Rahma tayi kamar bata ganshiba, shima ko kallo bata isheshiba yad'akko kofin tee ya mik'a mata.
Kamar bazata amsaba saikuma ta amsa Dan ganin yayi tamau da fuska kamar bai ta6a dariyaba, yamik'o mata filet d'in soyayyar doya.
Saman kujerar dake d'akin Yakoma ya zauna yana danna waya, ganin haka yasa tadake taci abincinta Dan yunwa takeji sosai.
k'asa² yake kallonta, aransa ya ce, "k'aryar ciwo kikeyi yarinya, tumda har kika iya share filet guda na doya, Rahma ta kalleshi ta ce, " nagama.
Banza yay mata yacigaba da danna wayar, saida ya mula Dan Kansa sannan yataso yazauna saman durowar gefen gadon, maganin yacira yabata.
Tofa anan akeyinta, Rahma tayi kwalkwal da ido zatayi kuka, tsak'i yayi yana harararta, idan bazaki amsaba kibarsa kece zakisha wahalarki ke kad'ai wlhy, danni yanzuma zanbar miki gidan.
Yanda yake zabga ruwan masifa yasa ta k'ar6a, saidai tana hawaye tana sha, idan tasha d'aya saitayi kamar zatayi amai saikuma ta daure, shidai yana kallonta ta gefen idonsa Dan yacigaba da latsa waya, hakadai tadaure tasha maganin.
Tashi yayi ya d'auki kwanukan yafita dashi, babu dad'ewa yadawo da k'aramar roba da ruwan zafi aciki, sai k'aramin tawul.
Baiyimata maganaba yajawo d'ank'armin tebir na gilas dake kusada kujera ya zauna, Rahma ta ce, "kasada aranta.
K'afarta yad'auka yad'ora saman stool na madubi, itadai ikon ALLAH take kallo kawai.
Dukda yaga kallon datake masa bai kulaba yafara aikinsa batareda yabi takantaba, yasaka tawul d'in aruwan zafin yad'an yamatse, daganin yanda yake matsar tawul d'in kasan ruwan da zafi, amma Dan bak'ar mugunta ahaka ya nanama Rahma akan k'afar, wani wahalallen ihu tasaki, yay saurin rik'e k'afar yana harararta, kawai saitaji hawaye nabin kumatunta.
Raguwar banza yafad'a afili.
Itama ta ce, " ruwanfa da zafi wlhy, yanda tayi maganar ashagwa6e saiya tsaya yana kallon bakinta, ta kauda fuskarta tana tura Baki gaba.
Shima bakin yata6e yacigaba da aikinsa.
Da zame zame da mazurai aka gama wannan gashin k'afar, yad'auki maganin shafawar ya shafa mata sannan yakwashe kayan yafice itakuma ta kwanta tana sauke numfashi.

Bai sake shigowa d'akinba harsu Ammar suka iso shida matarsa da yaransu biyu duk maza.
Cikin farinciki yataresu, yanda yaketa murmushi saika d'auka bashibane yagamawa Rahma mazuraiba yanzu.
Cikin falon suka k'araso, Sumayya matar Ammar ta ce, "nibanga amaryarba ko ka sakata ta 6uyane?.
Murmushi yayi ya ce, " 6uyan lfy, tana d'aki kwance batada lfy.
Ammar yashek'e da dariya mutumina komun samu k'annen Nawal ne?.
Harararsa yayi kaifa bakada kirki wlhy, to Abu ta taka ak'afarta d'azu da safe.
Ammar ya ce, "ayya ALLAH yakiyaye gaba, amma yanda na sanka d'innan ai yanzu munsami baby duk wani zame ²n ka.
Kadaiji dashi d'an iska, bobo yafad'a yana nufar d'akin Rahma.
A zaune ya Tatar da ita tagama saka kaya, Dan k'afar tad'an saki shine taje tayi wanka.
Ki taso su Ammar sunzo.
To. tafad'a atak'aice, haryaje k'ofa takatseshi dafad'in bafa zan iya fitaba.
Cak yatsaya kuma bai juyoba, yakai minti uku ahaka saikuma ya waigo, yawani saki murmushin mugunta danyasan maganar dazaiyi, okey kinaso nad'aukeki Dan kinji Ammar ya ce, " namiki ciki ko?, kinaso su tabbar kenan?.
Ido Rahma ta gwalalo waje ta ce, "nid'in?.
Baki ya ta6e tareda takowa har inda take, taho na d'aukeki nikuma namiki alk'awarin tabbatar musu da hakan.
Matsawa tayi gefe, ta ce, " kabarsa kawai zan iya.
Dariya yayi ya ce, "Yar rainin hankali, yana gama fad'a yafice yana cigaba da dariyarsa.
Rahma tarike baki o ni Rahma dama haka mutumin nan ya ke?, barikiga natashi kafin yaje ya nafkamin wani sharrin.
Haka ta d'ingisa har zuwa falon, ta zauna suka gaisa sunata tsokanarta, itadai bata iya cewa komai sai murmushi, mik'ewa tayi danufi basu ruwa da abin motsa baki, ya ce, " ina zaki?.
Ruwa zan basu tafad'a tana tafiya da d'ingishi.
Sumayya ta ce, "kinga dawo kizauna amarya, bari na d'akko mana aimu ba bak'i bane, Rahma ta ce, " haba daga zuwanku sai asaka ki aiki?.
Karki damu kinji, idanma kika kusa haihuwa nan gidan zan dawo, hannu tasa tarufe fuskarta Dan kunya, Ammar Kuma yayi dariya, Bobo ya ce, "Ashe na huta nikam?.
"Aiko ka huta."
Sumayya ce tamusu komai daya dace Rahma tayi, abincima atsakar falon sukaci, mutuminku sai wani kaffa² yakeyi da Rahma, ita abunma kunya da dariya yaringa bata, idan kukaga kulawar dayake bata saika d'auka haka suke kullum.

Har dare su Ammar suna gida, sai bayan isha'i suka tafi, bobo kuma yatafi d'akko Nawal Dan gobe zasu koma makaranta.

Rahma tad'an daddogara kamar gurguwa tad'an gyara abinda yadace sannan tayi wanka, shirin barci tayi tazauna jiransu.
Bayan wasu 'yan mintuna da zamanta saigashi ya iso da Nawal akafad'a tayi barci.
Saman gadon ya kwantar da ita, Rahma ta ce, " sannu.
Yauwa, tafad'a atak'aice.
Batabi ta kansaba harya sauyama Nawal kayan barci,

Please Login or Register in order to submit comment