Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saikuma suka dawo da kallonsu kan Nawal.
Baby ka ajiye jaka ka goya momy kawai.
Da sauri Rahma ta ce, " nikam Nawal na yafe.
Nawal ta k'ya6e fuska tana fad'in um um nidai sai yayi miki goyon, saikitacewa kin yafe kullum kullum.
Kan Rahma ak'asa ta ce, "toki bari yahuta kinga yazu yadawo daga aiki, tajawota jikinta tana lallashi.
Bobo yawuce d'akinsa yana murmushin darun Nawal.

Bayan yayi wanka yafito sanye da wando iya guywa da Riga k'arama, Rahma tamik'e kanta ak'asa ta ce, " ga abincifa.
Baice mata komaiba yanufi dinning, itama baya ta take masa, bayan ya zauna tafara had'a masa komai, sai satar kallonta yake k'asa k'asa, tagama takoma falo taja Nawal suka koma tsakar gidan dansu sha iska.
Bayan kamar minti 30 suka dawo, sannan bobo ya kammala yanazaune da jaridar tasa ta fama.
Nawal ta ce, "yauwa baby tashi kagoya momyn to.
Da sauri Rahma tanufi d'aki dantaga rigimar Nawal bazata k'areba.
Bobo yajawo Nawal yad'ora kan cinyarsa, kinga babyna kibari zan goya momynki amma ba yauba, kinga yau nagaji, yak'are maganar da sumbatar kumatunta.
Nawal ta k'ya6e fuska ita adole bata yardaba.
Ganin zata takura masa, shikuma soyake yahuta saboda yagaji sosai, ya ce, "to tashi muje na goyata, tamik'e yarik'e mata hannu suka nufi d'akin Rahma.
Tana zaune bakin gado tana wasa da wani d'an babyn Nawal, suka shigo, ta d'ago kai tana kallonsu, suna had'a ido da bobo ta kauda idonta.
Nawal ta ce, " momy tashi baby yamiki goyonki.
Rahma tabud'e baki zatayi magana Bobo yad'aga mata hannu, karki damu yarinyar nan taki ba k'yalemu zatayiba inhar ba'ayi goyonnanba, Dan haka taso kawai nayi muhuta.
Da sauri Rahma takallesa danjin furicin bakinsa, yama za'ayi harta iya yarda ya goyata saikace wata yarinya.
Bata ankaraba taga ya tsugunna yana jiran tahau kenan.
Cikin sanyin murya ta ce, "Dan ALLAH kayi hak'uri bazan iyaba.
Juyowa yay yana kallonta fuska a d'aure, ya ce, "amma dai kinsan Nawal dashegen naci, indai ba goyonnan nayiba ba barina zatayi na hutaba, nikam natsani adameni da hayaniya.
Ganin yanda yake magana cikin fad'a amma hakan baihana muryarsa fita cikin nutsuwa da taushiba yasa dole tasakko daga gadon, amma tayi tsaye takasa hawa saboda tana matuk'ar jin kunyaarsa.
Momy kihau baby yana jiranki Nawal tafad'a tana kallonta.
Hararar da Bobo ya watso matace tasata saurin d'anewa bayansa.
Shikuma yamik'e yanufi falo da ita, Nawal nabiye dasu tana dariya.
Yajuyo yana kallon Nawal to nagama ko baby?.
Lah baby saikaje d'aki da'ita sau uku kana dawowa, haka yayta zarya daga falo zuwa d'aki harsau uku, ana ukunne yadireta saman doguwar kujera yana fad'in wash bayana, wlhy momyn Nawal kincika nauyi.
Rahma tayi k'asa dakai cike da kunya, yabata dariya wlhy, sai wani yatsine fuska yake da rik'e k'ugu tamkar zaiyi kuka, amma saita gimtse, wai yau itace namiji yagoya, da gudu tabar wajen tanufi bedroom.
Shikam dariyama tabashi Dan haka yad'an murmusa tareda zama saman kujerar, wani nishad'i na musamman yatsinci kansa aciki, yajingina kansa da kujera tareda lumshe fararen idanunsa yana cigaba dasakin lallausan murmushi.

Har aka kira sallar magriba yafita Rahma bata sake fitowaba, gani take bazatama iya had'a ido dashiba aii.
Saida akayi isha'i yashigo gidan dakayan kwalam da mak'ulashe, Rahma najin motsin dawowarsa ta tura Nawal itakam tayi kwanciyarta tak'i fita.
Nawal taje tafad'a jikinsa tana masa oyoyo, shima rungumeta yayi yana fad'in babyna kinyi sallah?.
Eh nayi nida momy, harta koyamin karatu.
Ya ce, "iye kaga 'Yar gatam momynta, ina momyn taki to?.
Tana d'aki wai zatayi barci, nikuma nazo wajenka nayi fira.
Murmushi yayi Dan yagano tanajin kunyane dankarsu had'u, ya ce, " jeki kiramin ita.
Da gudu tanufi d'akin, tafad'a saman Rahma dake kwance kan gado, momy kizo baby na kiranki.
Rahma tadafe kai banace kice masa ina barciba?, kuma daga yau kiringa cemasa dady ba beby ba kinji babyna.
To momy zandinga fad'a tashi muje to.
Badan Rahma tasoba tasakko suka nufi falo itada Nawal.
Yana zaune idonsa akan Tv yana kallon labarai ta ce, "sannu da dawowa.
Yauwa yafad'a batareda ya kalletaba, ya ce, "ga wannan yamik'a mata ledan kayan motsa bakin.
ALLAH yasaka da alkairi tafad'a tana kar6a, kicin tanufa itada Nawal suka juyo afilat, wad'anda bazasu ciyuba tasaka afirij.
Takawo masa nasa itakuma tad'auki nasu danufi sutafi d'akinta suci, ya ce, " ina zakuje kuma?.
Kanta ak'asa ta ce, "d'aki.
sabodani zakuje d'aki cin abinci?.
Dawowa tayi tazauna batareda tabashi amsaba, saidai akunyace takeci, shikuma yana satar kallonta har suka gama tashige d'aki tabarsu shida 'yarshi.
Shirin barci tayi tai kwanciyarta, dama kayan barcine ajikin Nawal.

Yana gama kallon labarai shima yamik'e da Nawal ajikinsa datai barci, yakashe komai sannan yanufu d'akin Rahma.
Ahankali yasauke Nawal akusada ita, yay musu addu'a sannan yaja bargo yarufesu idonsa akan Rahma, yanda take barci hankali kwance sai fuskarta tayi wani wasai.
Jiki asanyaye yanufi d'akinsa yay shirin barci shima yakwanta...............
[14:23, 10/09/2017] hm: ����‍��typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


3⃣5⃣=3⃣6⃣

Hankali tashe Alh sunusi ya iso gidansa, ko fakin bai bari direbansa yagamaba yafice.
Matarsa na zaune afalo itada k'annen Haneef d'in yafad'o ko sallama babu.
Arazane suka mik'e suna binsa da kallon mamaki, dukda ba yaune rana tafarko daya fara shigowa gida ahakaba.
Ina my son?, yafad'a aburkice.
Cikin mamaki haj Falmata ta ce, "Haneef?.
"Eh," ya bata amasa afusace.
Yanzu babu dad'ewa yafita aii, wani abune yafaru?.
Wata uwar harara yasakar mata, waike wace irin shashashar uwace?, wai kina nufin bakisan 'yan sanda sunzo har gidannan sun kamamin yaroba?.
Afirgice ta ce, "naga takaina ni Falmi, yaushe hakan tafaru?, yanzufa Haneef d'in yashigo gidannan ya sauya kaya yafita.
Bai sauraresuba yafice yabarsu cike da tashin hankali.
Abin kamar wasa Alh sunusi har dare yana Neman Station d'in da akakai Haneef amma babu ko Alamarsa, ransa yak'ara 6aci da harzuk'a, aiiko wlhy saiya d'auki mataki akan 'yan iskan police d'in dasukai k'arfin halin shigar masa gida harda kama masa tilon d'ansa namiji.
Gida Yakoma danufin zaije ga Qumissioner of police gobe idan ALLAH ya kaimu, saidai zuciyarsa namasa rad'ad'i idan yatuna Haneef zai kwana a Station yau.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
*_9:30pm_* ya isa gidansa duk agajiye, jinsa yake yau fes tunda ankama masa d'an iskan nan, bayan sun gaisa da mai gadi yashige cikin gidan.
Babu kowa afalon, har TV akashe yake ga gidan tsit kamar babu kowa, da alama masu gidan har sunyi barci.
K'ofar yamaida yarufe sannan yanufi d'akinsa, yazube kayan hannunsa cike da gajiya, babu 6ata lokaci yacire kayansa ya fad'a bayi domin yin wanka.
Bayan yafito yagabatar da shafa'i da wutiri, 'yan dube dube yafayi da alama akwai abinda yakeson gani, amma babu, d'an k'aramin tsaki yayi tareda mik'ewa yafice.

Cikin barci Rahma taji ana bubbugata, afirgice ta tashi, Dan dama tsorace takwanta, saboda rashin dawowar mai gidan.
Ganin shine atsaye yasa ta sauke ajiyar zuciya, ahankali ta ce, "sannu da zuwa.
Bai amsaba ya ce, " ina shayina?.
Tad'an dafe kanta, wlhy na manta ne.
Aii yanzu na tuna miki, yafad'a yana ficewa.

Asanyaye Rahma tasakko daga gadon, Dan barcin data fara yasa jikinta yin lakwas, haka ta k'arasa kicin tana jan k'aramin tsaki, idonta cike da barci tadafa masa shayin, tajuye akofi tareda yanka lemon tsami ta matsa aciki, tad'ora akan k'aramin tire tafice.
Ganin baya falo gabanta yafad'i, kenanfa d'akinsa zata kai masa?, tai shiru kamar mai nazari, zuciyarta ta ce, "kije kikai karya huce Rahma ki k'ara jama kanji wani laifin", tunda tazo gidan yauce rana tafarko dazata Shiga d'akinsa, Dan haka k'irjinta keta dukan uku uku, haka tadaure ta kwankwasa, saida tayi kusan Monti biyu sannan ya ce, " tashigo.
Ahankali ta tura k'ofar tashiga, wani k'amshi yadaki hancinta tashak'a talumshe idanunta, saikuma ta bud'e ta sauke akan Bobo dake zaune abakin gado yana latsa laptop, k'afarsa d'aya ak'asa d'ayar kuma ya tank'washeta a gadon, sanye yake da kayan barci ruwan ganye mai turuwa, tana mamakin yanda yakeson latsa laptop da karatun jarida.
Jin shiru bata ajiyeba, bakuma tayi maganaba yasashi d'agowa ya kalleta, shima baiyi maganaba saidai tura mata k'aramin tebir na gilas dayayi.
Ganin haka yasa itama tad'ora batareda ta ce, "k'alaba.
Bayan ta ajiye saikuma tayi tsaye takasa tafiya.
Yana danna laptop d'insa yana shan shayi, tsawon minti 7 ita batayi maganaba shikuma ya shareta yanata aikinsa, yakula bazatace komaiba, kuma akwai magana abakinta, Dan haka shi ya daure ya ajiye NASA shan k'amshin ya ce, " kinada matsalane?.
Kad'an ta kalleshi taga har yanzu idonsa nakan laptop d'in.
gyara tsayuwarta tayi, muryartan nan mai kasheshi ta daki kunnensa, dama sonake naji yau ko lfy Baka dawo da wuriba?.
Cak ya tsaya da abinda yakeyi, yad'ago fararen idanunsa ya sauke akanta, sanye take cikin dogon hijjabinta har k'asa, sa6anin d'azu daya Tatar da ita da kayan barci.
Ahankali yasauke ajiyar zuciya, koba komai yaji dad'in kulawarta agareshi, cikin miryarnan tasa ya ce, "babu wata Marsala aikine yamin yawa a office.
" okey saida safe."
Harta kai k'ofa yana binta da kallo, yadaure ya ce, "incedai babu wata damuwa daga babyn taki?.
Bata juyoba amma ta tsaya, Dan furucinsa na k'arshe yaymata dad'i, muryarta araunane ta ce, " a'a babu Marsala, saidai tata jiran dawowarka, harta gaji tayi barci..... Bata jira amsarsaba tafice.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe idanunsa, zuwa wani lokaci ya bud'e idon, d'an murmushi naga yayi Wanda bansan da liliba, saikuma yacigaba da aikinsa yana shan shayi.

Itakam Rahma tana komawa d'aki tahaye gado ta kwanta abinta sai barci.

::::::::::••••••••••••:::::::::
Washe gari Rahma ta tashi kamar yanda tasaba ta had'a break fast da gyaran gida, taima Nawal wanka itama tayi, kwalliya sosai taima yarinyar tai tsaf da ita, Dama ga ruwan k'yau d'an Asali, kan baby Nawal yasha gyara Dan jiya da yamma Rahma tayi mata kalba, kasancewar yau juma'a.
Tana cikin saka mata janbaki yaturo k'ofar yashigo da sallama ciki ciki kamar Wanda akaima dole
Da sauri Nawal ta hantsilo daga kujerar madubi danta hango daddynta ta madubi, oyoyo papa na tafad'a cike da farinciki tana rungumesa, shima d'aukarta yayi yad'aga sama yana dad'in "I luv u my child," yasumbaci kumatunta.
Ta shagwa6e fuska, papa shine jiya kak'i ka dawo ko?, lah nadawo mana, saidai kinyi barci sannan kitanbayi momy kiji?.
Nawal takalli Rahma dake kallonsu cike da sha'awa, wai haka momy papa yadawo jiya?, kai Rahma tad'aga mata tana murmushin daya kusan narkar da Bobo atsaye, hakane babyna yadawo kina barci.
Nawal tasunbaci kumatun babanta da k'asunba ta kwanta luf tanata shek'in gara.
Shikam hankalinsa nakan Rahma yana mata wannan munafikin kallon NASA k'asa k'asa.
Talura dashi tsaf dan haka tatsargu, rissinawa tayi ta ce, "INA kwana?."
Lfy, yafad'a cike da basarwa shi adole ba ita yake kalloba.
Rahma ta d'an ta 6e baki, dukda ta fahimci salon amsa gaisuwarsa kenan...... Muryarsa ta katse mata tunani, kushirya idan mungama break gida zamu wuce, Dan duk juma'a a can kowa yake yini.
Ahankali ta jinjina kai kamar wata k'adan garuwa.
Shikam yajuya yafice da Nawal ahannu.
Itama fitowa tayi tahad'ama kowa abinci agabansa, hankalinsa kwance yakecin abinci shida d'iyarsa, amma Rahma duk atakure take, haka kullum take cin abin ci atakure, bakuma danwai bata saba da ahakan bane, saidai kawai nauyinsa datakeji, tunda agidansu gaba d'aya suke had'uwa suci abinci tuntana yarinya.
Tananan tana juya cokali haryagama shida Nawal, yad'auketa suka koma falo suna jiranta.
Ganin yatashi yasata sakin jiki taci abincinta sannan takwashe kayan taje ta d'auraye.
d'aki takoma tacanja shigarta cikin wani had'ad'd'en doguwar rigar shadda pink colour, kayan sunmata k'yau sosai, tasaka k'aton farin hijjabinta sannan tafito, babu kowa afalon, danhaka takashe komai na kayan wuta, gamawata keda wahala yafito shida Nawal daga d'akinsa, hannunsa rik'eda jakar aikinsa.
Kallo d'aya yaymata yad'aukekai, saidai har azuciyarsa yaji dad'in hijjabin data saka, yanason kamilar mace arayuwarsa, gaba yay suka bishi abaya.
Tashaya kulle k'ofar falon shikuma sukai gaba cikin mota shida Nawal.
Ganin Nawal abaya itama tabud'e bayan zata shiga, ahankali yay maganar tamkar mai ciwon baki.
"Halan ni direban kine?."
Cak tatsaya tafasa bud'ewa, kuma tak'i dawowa gaban.
Yakuma cewa kina 6atamin lokacifa, kuma wajen aiki zanje, jiki a sanyaye tabud'e gaban tashiga, shima baisake cewa komaiba yatada motar suka fice bayan sun gaisa da baba mai gadi.

Karatun Alkur'ani yasaka musu, cikin k'ira'ar shiek Abdurraham sudes, ahankali Rahma kebin karatun, yana kallonta ta gefen idonsa, jiyay tak'ara girma a idonsa.
Har sukaje gidan Appa babu Wanda yay magana, garama Nawal takanyi jefi2.
Saida yatsaya suka gaisa da baba mai gadi, yaymasa alkairi kamar yanda ya saba sannan yashige ciki.
Yana faka motar Nawal tafice da gudu zuwa cikin gidan, sukuma suka fito cikin nutsuwa, da gudu khairiyya da khursiyya suka fito, rungume Rahma sukayi suna farin cikin ganinta.
Ta ce, "aini nayi fushi, daga zuwa d'aya baku sakeba.
Kiyi hak'uri auntyn mu, Ammi ce ta ce, " mubari sai nan gaba.
Bobo yak'araso yana harararsu to maganannu ai kwabari kushiga gida dai ko?, yay gaba abinsa.
Khursiyya ta ta6e Baki, aifa yau munga banu jarabatu yazo, ALLAH yasa aiki zai wuce cewar Khairiyya.
Rahma najinsu dai tayi murmushi kawai.
Cikin gidan suka shiga, hakan tayi daidai da sakkowar Ammi daga saman Appa, Dan Nawal nazuwa canta haura.
Ta rungume Rahma tanamai jin dad'in ganinta, cike da kunya Rahma ta rissina ta gaida Ammi, ta amsa cikeda fara'a, da tambayarta ya zaman babudai wata Marsala ko?.
Kan Rahma ak'asa ta ce, "Ammi babu matsalar komai, to Alhmdllh d'iyata haka nakeson ji.

A'a mukarram d'ina lfy dai ko?, Ammi tafad'a tana kallon bobo dayay tsaye yana kallonsu tun d'azun.
yaturo baki gaba kamar wani yaro, yo Ammi sai yanzu kika san dani?.
Ammi taje takama hannunsa, o ni na isa namanta da babana, kawai ina murnar ganin d'iyatane.
Yakuma turo Baki, Toni bari nakoma tunda bak'ya murnar ganina, yanda yay maganar ashagwa6e yasa su khairiyya kwashewa da dariya.
Harara ya watsa musu suka bar wajen, itadai Rahma murmushi takeyi da mamakin Bobo, irin wannan shagwa6a haka kamar wani d'an shekara 5, anace mata tanada shagwa6a toga Wanda yatakata iyawa.

Ammi ta lallashesa suka haye sama domin gaida Appa.
Appa yaji dad'in ganinsu sosai, Dan haka yaymusu nasiha sosai sannan bobo yamik'e yaymusu sallama Dan wucewa aiki, saikuma antaso.
Yakalli Rahma k'asa k'asa ya ce, "saina dawo.
Kanta ak'asa ta ce, " ALLAH yatsare yabada sa'a.
Yaji dad'in addu'arta Dan dama ita yake son ji.
Ammi taji dad'in addu'ar da Rahma taima bobo, hakama Appa, suma sukai masa yatafi.

Zuwa 10:30 gidan yagama cika, aunty Rasheeda da 'yayanta, aunty Sameera ma da NATA, aunty ummy ma haka, mazan kuma suna ajiyesu suka wuce wajen aikinsu.
Dan danan gidan ya haukace da hayaniya, yaran duk suna falon sama wajen Appa, sukuma iyayen suna falon k'asa sunashan hira kamar wasu k'awaye, babu wannan shegiyar ak'idar ta kishin Sauri, hirarsu suke sosai, Dan danan Rahma tasaki jikinta dansu, su aunty Rasheeda akwai saurin shiga rai, gasu khursiyya iyayen shafta............






*_luv u oll my fan's_*
*_(((S))).........2017_*
[14:23, 10/09/2017] hm: ����‍��typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


3⃣3⃣=3⃣4⃣

"K!, ina zakije da sassafennan?.
Safna ta kwa6e fuska, ummi munafa da Lectures k'arfe 7:30am kuma malamin baida kirki wlhy, gashi ya CE, " test zai mana, tak'are maganar da turo baki gaba.
Ummi ta ta6e Baki, ta ce, " shikenan jeki, amma idan kin dawo inason magana dake nida mahaifinku.
Gaban safna yafad'i ta ce, "ummi magana kuma?, tami to?.
" idan kindawo k'yaji, Dan inama son aikenki gidan Rahma.
Kai ummi gidan Rahma fa kikace?, saikace wata k'anwarta.
To tunda tarigaki aure aikin zama k'anwar tata aii, ko kina nufin dankince bak'yason mijinta bazakije gidantaba?.
Nifa Bahaka nake nufiba ummi, kawai INA dai ganin da kunya.
Harara ummi tasakar mata, o sai yanzu kika San kunyar?, alokacin dakikai shirin wulak'antamu kin manta da kunyar.
Nidai ummi ALLAH yabaki hak'u, ALLAH fa yariga yarubuta itace matarsa kawai, amma ni ban wulak'antakuba, kawai ina gudun kar asakamin kaina atunkunya ne, saina dawo, tayi saurin ficewa, Dan batason jin amsar ummi, tasan halinta sarai, yanzu saita hau sama ta 6ata mata shirinta, itako awannan lokacin bata fatan abinda zai hanata fita.
Ran ummi yak'ara 6aci, duk cikin 'yayanta babu Mara kunyar irin Safna, ita bata iya tauna magana ga mahaifaba, ta maidasu tamkar wasu k'awayenta, kodan gatan dasuka nuna matane abaya?.

Tana fita taci karo da Baseera ak'ofar gida.
A'a kice kina nan?, dafa shirin shiga gidanku nakeyi, to waima inbanda iskanci miye natsayawa anan?, gidan bak'onkine?.
Baseera tarufe murfin motar tana fad'in Bahaka baneba, banason nashiga mu 6ata lokacine kawai.
Dariya safna tayi, haba k'awata aganinki zan 6ata lokacine?, kenifa k'agara nayi gari ya waye, yanzun haka jinake tamkar nayi tsuntsuwa na ganni agaban malaminnan.
Baseera ta tuntsure da dariya kai k'awata kemafa bakida dama akan abinda kikeso, lallai guy d'innan yayi babbar sata.
Safna tak'ara dafe sitiyarin motar, ai wlhy Basee guy d'innan ba k'aramar sata yayiminba, wlhy gaba d'aya ya haukatani, saidai idan natuno kafinni harya zauna da mata biyu nakanji raina ya 6aci, badan ina sonsaba sosai da watsar dashi zanyi.
Shiyyasa Nima na d'auki alk'awarin saina mallakesa amatsayin miji kota halin k'ak'a, ke namiki mai kankat wlhy har yarinyarsa saina rabashi da ita, Dan dagani sai 'ya'yana nakeso mu zauna dashi.
Hummm 'yammata ace insha ALLAHU dai.
Safna ta gallama baseera harara, to aii dama komai insha ALLAHU ne, koko insha Baseera ne?.
A'a Dan ALLAH karki mana sa6o mudai kisa akifar damu, kefa wani lokacin kamar bakiyi islamiyyaba haka kike.
Banza Safna tai mata, Dan idan tabiye mata fad'a zasuyi, itakam lalla6ata takeyi tasamu arakata gun malami.
Sun isa gidan malam amma da mutane, Dan haka suka jira a mota.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*
Bobo a police tetion yasaka 'yan sanda gaba sai masifa yake musu, wai basu san aikinsuba.
Haba Dan ALLAH wai mikuka maida kankune?, yau sati nawa ace angagara nemo mai laifi, hanyafa mai sauk'ine gano koma wane d'an iskane, saboda anbaku no. d'in motarsa, wlhy nabaku nanda gobe idan ALLAH yakaimu inhar baku zomin da mai lafinnanba zan d'au mataki, Dan saina saka anta6a aikinku, tunda bakusan abinda kukeyiba...
Sudai 'yan sanda cikinsu ya d'uri ruwa Dan sunsan kowaye Abdulmaleek, tunda bayau yafara d'ora su akan aikiba.
Tsaki yaja yafice, afusace yashiga mota yafigeta.
Yayi nisa atafiyarsa sai masifa yakeyi shikad'ai amota, tamkar zai ari baki.
Wani haushine yak'ara turnik'eshi Dan ganin wani banzan Go slow mara dalili, kamar ance ya waiga idonsa yasauka akan number motar guy d'in dasuke nema.
Jikinsa har rawa yake yad'auki waya yakira 'yansanda, saidai yana yanke wayar ana sakin Go slow d'in, da hanzari yatakema motar baya, binsa yake cikin dabara har zuwa wani kantamemen gida, ya sauke numfashi afili ya ce, "gidan Alh Sunusi Dala kuma?, kenan wannan motar tanada alak'a da gidan?.
Wayarsa ya d'auka dake wringing 'yan sandane suke tambayarsa yana ina?.
Kusameni gidan Alh Sunusi dala.
Kansa ya kwantar jikin kujera, saiyanzu yagane abinda yasa 'yansandan suka kasa kama mai laifin, tabbas sunsan yanada alak'a da wannan gidan.......
Tunaninsane yatsaya alokacin da motar 'yan sandar ta iso, bai fitoba amma yabud'e murfin motar.
'Yan sanda biyu suka k'araso inda yake, fuska ad'aure yakallesu, nan gidan motar nan tashiga, Dan haka saikuyi aikinku.
Cikin d'an sanda d'aya yabada wani k'ululu, baki narawa sukace nan gidan kuma?.
Cikin daka tsawa ya ce, "e nan gidan, dama nasan kunsan Wanda ya aikata, amma kwad'ayi irin naku yasa kuka kasa d'aukar mataki, to yanzu saiku za6a, kamashi kokuma asarar aikinku......
Kafin yarufe baki sunnufi k'ofar gate d'in gidan, dak'yar maigadi yabarsu suka shiga.
Daidai nan Haneef yafito cikin sabuwar shiga danufin sake fita, harya fara k'ok'arin bud'e mota yadakata Dan ganin 'yan sanda.
K'arasowa sukayi har inda yake tsaye, sallama sukai masa, ko amsasu baiyiba, saima kallon banza dayake bisu dashi.
d'an sanda ya had'iyi wani yawu sannan ya ce, " yalla6ai u onder arrest.
Me!, Haneeff yafad'a cikeda rainin hankali, yacigaba da fad'in Ku harkunkai matsayin dazaku shigo cikin gidanmu kuce kunzo kamani?, toma awane dalili?.
Kayi hak'uri yalla6ai zamu maka bayani idan munje can, Dan duk abinda kafad'a anan zai iya zama hujja agareka a kotu.
Kan uba...... Saikuma yay shiru yakasa k'arasawa, yaja numfashi kumuje zan biku abaya, yayi hakane danya kafa musu tarko.
A'a kamuje kawai aiiba dad'ewa zakayiba.... Maganar Bobo tadaki kunnuwansu.
Kai kuma awa?, haneef yafad'a yana kallon Bobo.
Karka damu da matsayina, kaidai kadamu da kanka kawai my friend.
Cikin 6acin rai Haneef ya ce, "kadai iya bakinka k'aramin k'waro.
Wata banzar dariyar rainin hankali Bobo yasaki, wadda zan iya cemuku yauce rana tafarko danaga dariyarsa, ya kalli 'yan sandan ya ce, mikuke jira?, yana gama fad'a yafice daga gidan.
Cikin 6acin rai haneef ya ce, "kumuje to, ammafa yak'udiri aniyar wulak'anta d'an saurayinnan da 'yan barandarsa.
Haneef yashiga motar 'yan sanda, bobo kuma yashiga motarsa.
'Yan unguwar sai dad'i sukeji da ganin Haneef amotar 'yan sanda, yayinda agefe kuma tuni magulmata sunkira Alh Sunusi sunkai masa rahoton kama Haneef da 'yan sanda sukayi yanzu.
Hankalinsa atashe yabaro office yanufo gida.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Suna nan zaune har layi yazo kansu, sannan suka shiga.
Bayan sun gaisa da malam da'u safna ta ce, "malam......
Da sauri yad'aga mata hannu karkice komai, tunkafin kizo sud'an tsito sun sanar dani komai.
Kin kamu da son wani saurayi, kinkumasa ayimiki bincike akansa, yanada mata ba'a dad'e dayin aurenba, kuma yata6a aure matar tamutu harda 'ya atsakaninsu, koba hakaba?.
Cikin mamaki da rawar jiki Safna ta ce, " to amma ALLAH ya gafarta malam ta INA kasan wannan?.
Malam da'u yatuntsure da dariya, kai yaro yarone dai,

Please Login or Register in order to submit comment