Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sharri zuciya dana k'awa, Dan baseera ta taka rawar ganin wajen zurma rayuwarta ga halaka.
ALLAH sarki zeenat dama kin fad'amin zanyi nadama, amma na k'aryataki, nak'i yarda da zancenki lokacin Sharrin shaid'an Dana zuciya suna d'awauniya dani, sai yanzu nagane ke mai k'aunatace da gsy, kece k'awa abar alfahari agaren......tarushe dawani kuka maiban tausayi.
Da sauri ummi tak'araso gareta tana fad'in Safna lfy kuwa?.
Tashi tayi zaune da sauri tak'ank'ame ummi tana kuka, ummi wlhy nayi nadama, yanzu zan canja, dan ALLAH ki gafarceni keda abba dasu ya munner, wlhy nayi nadama bazan sakeba........
Takuma rushewa da kuka yayinda numfashinta ke sama yana k'asa, k'irjinta tadafe tana fad'in wash ummi zan mutu, ummi k'irjina zai fashe..
Arazane ummi take girgizata tana kwala kiran Safna! Safna!!, ke Safna!!!.
Ina Safna tayi nisa batajin kira, numfashinta yatsaya cak da aiki, afirgice ummi ta ce, " nashiga uku ni sa'adatu mizan gani haka?, wayar safna ta raruma jikinta sai rawa yake takira abba, yana d'agawa tafashe dakuka mai tsuma rai, abban shaheed ka taimakeni kada safna tamutu dan ALLAH.
SHIMA cikin mamaki ya ce, "safna kuma?, miyafaru da safnar?.
Abba Shaheed nidai kataho gida wlhy safna bata numfashi gabad'aya wayyo ALLAH na safna karki mutu, munyafemiki dan ALLAH karki tafi kibarni wayyo safna....
Surutai da sambatu kawai ummi ke zubawa.
Cikin lokaci k'alilan saiga abba da likita harda ya munnir, ai ganin Safna sharaf kamar gawa doctor ya ce, " sud'auketa kawai atafi asibiti, jikinta yawuce adubata agida.
Ya munnir yasa6eta batareda yabarima likita ya k'arasa fad'aba.
Agaggauce suka isa asibiti.
Taimakon gaggawa aka shiga bama safna wadda saidai abinda ALLAH yayi kawai, dan kwance take sharaf babu alamar numfashi.

Masu karatu nimafa atsorace nake😟, safna saidai wani abu ga ALLAH.

Su Abba sai safa da marwa sukeyi ak'ofar d'akin da'aka sakata, ummi kam banda hawaye babu abinda take shar6ewa, Abba da ya muneer sai hak'uri suke bata.


*................................*
Awanan lokacin kam Rahma nagida itada Nawal da direba yad'akko yanzu Daga school.
Bayan Tamata wanka sukadawo falo, Nawal nagefenta zaune tanacin abinci itakuma tana duba buks d'inta taga ko anbasu homework
Nawal ta ce, "momy!.
Na'am babyna, miya farune?.
Nawal tayi 'Yar dariya, momy auntynmu ce ta ce, " wai bankai mata kayan bikiba, shine nace gobe zan kaimata, aizaki bani nakai mata ko?.
Murmushi Rahma tayi tareda d'agamata kai, zan baki my sweety na insha ALLAH.
murna Nawal tafara, itakuma Rahma tana kallonta tana dariya.
Bayan takammala cin abincin ta koya mata homework, suna kammalawa suka fito harabar gidan suna shan iska, Nawal tanata wasanta cikin 'Yar motarta, ita kuma tana zaune tana karatun book awaya dansu Basma sun sakata groups na Novels.
Jin k'arar bud'e gate yasa tad'ago tana kallon hanyar gate d'in dukda basosai take hangowaba amma taga kamar motar bobo.
Agogon dake manne ahannunta ta kalla _4:15pm_ afili ta ce, "lfy kuwa Nurulk'albi?.
Bobo yay farking a inda yadace sanan yafito, sanye yake cikin k'ananun kaya, blue d'in wandon jins da farar Riga mai dogon hannu, yayi k'yau tamkar yanzu yay kwalliyar, jakar aikinsa yad'auka ya rataya sanan yakwashi wayoyinsa, harya nufi hanyar falon saiya jiyo dariyar Nawal da Rahma abaya.
Dawowa yayi yanufi inda yakejin dariyar.
Nawal naganinsa ta tashi da gudu ta taroshi, rungumeta yayi yanamai farincikin ganinta, ya ce, " baby ya school?.
Lfy lau papana.
Masha ALLAH, amma yau ba'aje islamiyyaba?.
Kanta ta d'aga.
Ya ce, "miyasa?.
Shiru tayi Dan tama manta abinda yasa yau bazasu islamiyarba.
Ganin haka yasaka bobo d'agowa yana kallon Rahma, sauke idonta tayi daga satar kallonsa, idonsa yalumshe yana murmushi, afili ya ce, " gulma.
Kallonsa tayi tana turo baki Dan tasan da ita yake, fuska akumbure ta ce, "sannu da zuwa".
Bakinsa yata6e ya ce, " bazan amsaba, aiba haka ake tarar mijiba.
Idanu tad'an zaro tana kuma satar kallon Nawal.
Shima Nasal d'in ya kalla saikuma yamaida kallonsa ga Rahma, gira yad'aga mata yana wani murmushin gefen baki.
Tashi tayi tak'araso gareshi, tamik'a hannu nufinta yabata jakarsa, maimakon yayi haka saiya mik'a mata kafad'arsa duka.
Nawal takuma kalla taga takoma wajen motarta, d'an kad'a idanunta tayi sanan tasaka hannu tazare jakar.
Bak'aramar kasala tasakarma boboba data kad'a idanunta, yalashe la66ansa sanan yamatso daf da ita ya manna mata kiss akumata.
Ja baya tayi da Sauri, harma taso bama bobo dariya saboda yanda ta razana kamar wani maciji ya ta6ata amma yadake.
Ra6awa tayi ta gefensa tawuce, binta yayi da kallo harta shige.
Yakalli Nawal daketa wasanta da mota, ya ce, "baby kijirani yanzu zanyi wanka nadawo.
To my papa, Nawal tayi maganar hankalinta awasa.
Ciki shima yanufa.
Yana shiga d'akinsa Rahma na niyyar fitowa, Ra6awa tayi tagefensa zata fice yay saurin shan gabanta, k'ara kaucewa tayi nanma ya tareta, tad'ago ido tana kallonsa saitaga fuskarsa ta canja yakomamata ainahin bobo nada data sani ada.
Jada baya yayi yajingina da k'ofar, ya hard'e hannayensa ak'irji yazuba mata mayun idanunsa, k'asa tayi dakanta gawani tsoro yana shigarta, jitai miyasama take masa haka?, kodan taga yanzu ya sake mata yana wasa da ita?.
Kallonta yake daga sama har k'asa, shifa ganin yakema tak'ara MASA k'yau da haske, yad'an lumshe idanunsa yabud'e, murya a tausashe ya ce, " Rahma!."
Kanta tad'ago ahankali tana kallonsa, ganin ya zuba mata idanunsa da awanan munafikin kallon NASA k'asa k'asa yasa tamaida idanunta tana wasa da zoben hannunta.
Yakuma fad'in Rahma!.
Na'am ta amsa kanta asunkuye kuma muryarta tana rawa.
Ya ce, "miyeni awajenki?.
Tambayarsa tabata mamaki Dan haka tad'ago tad'an kallesa ta maida kanta k'asa sanan ta ce, " mijinane.
Ajiyar zuciya ya sauke sanan ya warware hannayensa yatako ahankali zuwa gareta, jin k'amshin turarensa yak'ara kusantota yasakata rumtse idanu, nanma tsayawa yayi yana k'are mata kallo, saikuma yasaka hannunsa yad'ago ha6arta, kalleni yay maganar akasalance.
K'ara rumtse idonta tayi Dan bazata iya kallon nasaba.
Yakuma cewa My Nusfulhayat kalleni.
Girgiza MASA kai tayi alamar a'a.
Ya ce, "miyasa?.
Batace komaiba amma tagyara tsayuwarta.
Bobo Yakuma narke murya can kasa tamkar mai rad'a ya ce, ''kina fushi da mijinki ko?, saboda kina zarginsa dacin amanarki yakeyi?.
Hawaye suka ziraro daga idanunta, ahankali suke silalwo visa kumatunta, yad'an cije le6ensa yanamai k'ara tsura mata idanu.
Matsota yakumayi, yasak'alo d'ayan hannunsa kan k'ugunta, ahankali yad'ora bakinsa visa nata, cikin Sauri da rawar jiki tabud'e idanunta saidai tamakaro Dan haryayi nasarar zira harshensa aciki, kissing nata yake cikin kwarewa danuna zalama.
Itakam tun tana yunk'urin kwacewa harta hak'ura tamik'a wuya Dan tuni ga6o6in jikinta sun saki, da wanan damar yayi amfani wajan cud'anyata San ransa, ganin tsayuwa tana Neman gagararsu yad'auketa can sukayi gado.

πŸšΆπŸ»β€β™€sum sum nafito wajen Nawal.

Soyayya sosai Bobo yasha, saida nutsuwa tazo musu sanan Yakuma jawota jikinsa yarungume, muryarsa can k'asan mak'oshi ya ce, "Rahma da gsk kina zargin mijinki da cin amanarki?.
K'ara kwanciya tayi luf visa faffad'an k'irjinsa tana shak'ar daddad'an k'amshinsa, muryarta nad'an rawa ta ce, " nifa ba zarginka nakeyiba.
Ya ce, "to miyasa kike 6ata rai idan kinganni?, miyasa kuma Safna tatafi gida batareda nasaniba?.
Idonta ta rumtse tareda sauke sassanyar ajiyar zuciya, wlhy bani nakori aunty Safna ba, kuma bansan abinda akai mataba tatafi, nidai naganta da kaya kawai.
To miyasa baki hanata tafiyaba?, Ko kuma ki sanarmin?.
Inatsoron kartamin masifane, kuma gashi acikin mutane Muke.
Huci yafitar daga bakinsa, yasaka hannu ahankali yana shafa kanta, suduka sukayi shiru nad'an lokaci, jin shirunta yayi yawa yad'ago yalek'a fuskarta saiyaga barci yakwasheta.
Maida kansa yayi ya kwanta shima ya lumshe ido amma ba barci yakeyiba yafad'a duniyar tunanine kawai, tundaga randa Appa yay masa maganar auren Safna harzuwa canjamasa da akayi da Rahma, bikinsu, rayuwarsu tanesa nesa, har zuwa yau dasuka zama Abu guda, yad'anyi murmushi dantuna darun Rahma, yasan kishine kawai kecin zuciyarta, jiyayi yak'ara k'aunarta nikin baninkin, yad'ago ahankali yana kallon fuskarta, ahankali take sauke numgashi ak'irjin nasa, fusakarta tayi fayau gawani annuri namusamman datake fitarwa, shiru yayi yana sauraren yanda Nawal take buga k'ofa tana kiran momy! papa!.
Tashi yayi ahankali da Rahma ajikinsa, cikin hikima yazameta daga jikinsa ya kwantar da ita tareda kara mata filo, kafin yagyara mata kwanciyarma harta gyra kanta tareda jawo filo tarungume.
Murmushi yayi yana mai kallon k'yak'yk'yawar fuskarta, azuciyarsa ya ce, "ragguwa da anta6aki sai barci.
Jin Nawal takuma bugawa yamik'e yad'auki tawul yad'aurama k'ugunsa sanan yanufi k'ofar yabud'e.
Tana tsaye abakin k'ofar, ya ce, " baby miya faru?.
Papa ina momyna?.
Saida yajuya yakalli Rahma sanan yadawo da kallonsa kan Nawal, momynki tana aikine jeki kijirata afalo kinji d'iyar albarka.
Kanta ta jinjina, ta ce, ''papa nakalli cartoon?.
Eh babyna jeki saka MBC 3 kigani, muma yanzu zamu fito.
Tafiya tayi abinta tana murna, shima yamaida k'ofar yarufe harda saka key.
Bathroom yashiga yay wanka, dama Rahma tahad'a masa ruwan wanka, bayan yagama k'alk'ale k'alk'alensa yafito.
Kujerar madubi yaja yazauna, yana cikin shafa mai yaga Rahma yatashi afirgice tana sambatar aunty Safna! Aunty Safna!!, Dan ALLAH karki mutu, A'uzubillahi minashshaid'anirrajim!, sai jikinta ke rawa, da Sauri. Bobo yamik'e yaje yajata jikinsa yarungume, yana kiran my Nusfulhayat nutsu kinji, mafarki kikeyi ba gske bane, nutsu.
Hawaye tafara zirarwa, a'a my Nurulk'albi Dan ALLAH ka kaini na ganta, kacemin bata mutuba, wayyo aunty Safna karki tafi ki barni.........
Kafin tarufe baki wayar bobo tafara wringing, dak'yar tayarda ya janyeta daga jikinsa yatashi yad'auki wayar, gabansane yafad'i shima Dan ganin sunan ya Shaheed 6aro 6aro akan screen d'in wayarsa.
Haka kawai yasamu zuciyarsa dayin rawa, dakuma k'ok'arin gaskata mafarkin Rahma, shiyyasa ba'ason barcin la'asar yafad'a azuciyarsa yana kallonta.
Ganin kallon dayake mata saita sake fashewa da kuka, cikin muryar kuka ta ce, "yan gidammune ko?, namasan zasu fad'amin aunty Safna na tarasune kawai...... Tasaki kuka maiban tausayi da tsuma zuciyar mai saurare.
Kiran ya Shaheed ne yakuma shigowa, jiki a sanyaye yad'aga yakara akunne, muryar ya Shaheed kawai dayaji yasaka zuciyarsa karaya, bayan sungaisa ya Shaheed yasanarma bobo abinda nikaina banjiba.
Cikeda tashin hankali ya ce, "ya Shaheed gamunan zuwa, koda suka yanke wayar.. Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kawai bobo ke iya ambata, Rahma tataso ta warce wayar, ganin sunan Wanda yakirashi yasakata fashewa da kuka, matsowayayi Kusada ita ya ce, " addu'a Safna take buk'ata yanzu agaremu Rahma, kinga tashi kiyi wanka muje.
Kasa tashi tayi, saishine ya d'auketa yakai bathroom yaymata wankan dakansa, dak'yar yasamu tayi wankan tsarki sanan suka fito, d'akinta yaje yad'akko mata wasu kayan, babu zancen shafa mai zirawa kawai tayi, shima yasaka doguwar riga kawai yakama hannunta suka fito.
Afalo suka d'auki Nawal sai gidansu Rahma.
Amotama sai kuka take, shima yakasa lallashinta Dan duk arud'e yake, tuk'i kawai yakeyi cikeda damuwa..............


πŸ€”πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­


*_"Hummm masu karatu akwai damuwafa, mikuke tunani gameda Safna??????."_*









*_Luv you oll_*
*_(((S)))........2017_*g




πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_β€’πŸ…±πŸ…ΎπŸ…±πŸ…Ύβ€’_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


6⃣6⃣

Ganin yanufi wata hanya daban yasa Rahma tsura masa idanunta dasuka k'ank'ance saboda kuka, yana kallonta tagefen ido kuma yakula magana takesonyi amma takasa, shima bai iya cemata komaiba, gudu kawai yake shararawa, ganin sunshigo cikin asibitin Rahma takuma yarda mafarkinta ya tabbata, guri bobo yasamu yay fakin kowa yafito jiki a sanyaye, banda Nawal dabatasan wainar da'ake toyawaba, cikin asibitin suka shiga kowa da abinda yake sak'ama zuciyarsa, Rahma takan share hawaye lokaci lokaci.
A Reception suka tsaya bobo yakira ya shaheed.
Babu dad'ewa saigashi yazo, Rahma tana ganinsa tafad'a jikinsa tana kuka, cirota yayi daga jikinnasa yana fad'in haba Autar Ummi bakisan kin girma bane?, kinga share hawayenki kinji.
Cikin shashshekar kuka ta ce, ''yaya waye bashida lfy?.
Ya ce, "safna CE."
K'ara share hawayenta tayi ta ce, "yaya nasamma aunty Safna tarasu ko?.
Idanunsa yazaro ya CE, "haba auta wayace miki tarasu?, a'a tana nan da ranta har yanzudai tana tareda doctor's ne.
Ta share hawayenta tana kallonsa, to yaya miya sameta?.
Muma bamu saniba Rahma saidai idan likitoci sun fito muji.
To muje kokin manta bake kad'ai baceba?.
Ita saima yanzu ta tuna tare suke da bobo Dan haka takalli Inda yake tsaye rik'eda hannun Nawal dake kuka tunda taga Rahma na kuka.
Da sauri tazo taja Nawal jikinta ta rungumeta tana lallashi, bobo dai da ya Shaheed suna tsaye suna kallonsu.
Ganin abun bana k'are bane yasa bobo matsawa kusada ita ya CE, " yakamata mu k'arasa ko.
d'agowa tayi ta kalleshi saikuma takama hannun Nawal suka shiga ciki.
Acanma tana ganin su Abba taje tafad'a jikinsa tana kuka, dak'yar ya lallasheta tayi shiru, bayan sun gama gaggaisawa suma sukabi sahun 'yan zaman tagumi.


.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Har akayi sallar magriba likitoci nakan Safna, su bobo dasu Abba suka nufi masallacin cikin asibitin, sudai su ummi da matansu ya Shaheed duk suna nan zaune jigum jigum, Nawal kam tuni tayi barci, ummi taciro d'ankwalin kanta dayake yanada girma tabama Rahma ta ce, "ta Goya Nawal, amsa Rahma tayi tacika umarnin ummi, gama goyon babu dad'ewa saigasu ya Muneer sun dawo daga masallaci, hakan kuma yayi daidai dafitowar doctors d'in kowa yana yarce gumi, da Sauri kowa yanufesu yana tambayar halinda safna take ciki, duk zame jiki sukai suka gudu akabar doctor Kaleel kawai, kallonsu yayi d'aya bayan d'aya yana share gumi, ganin duk 'yan gidane ya sauke ajiyar zuciya, ya ce, " Alhmdllh munsami nasarar ceto ranta, yanzu haka tasamu barci, yanzuma za'a wuce da'ita d'akin Hutu danhaka Ku kwantar da hankalinku alhaji, komai yazo da sauk'i aii alhaji, sauran bayani kuma sai zuwa gobe idan ALLAH yakaimu.

Alhamdllh suka fad'a gaba d'aya, godiya sukaima doctor Kaleel sannan yawuce office d'insa.
Tafiyarsa babu dad'ewa aka gunguro Safna a d'an gadon marasa lfy, kwance take sharkaf tana barcin wahala, cikeda tausayi da addu'ar samun lafiya suka bita.
Zuwa yamzu fuskokin kowa garage damuwa bakamar d'azunba.
Bobo yamatso kusada Rahma ya ce, "My Nusfulhayat ki sauketa mana, aii yanzu Nawal tawuce goyo karkizo k'irjinki yana ciwo.
Girgiza MASA kai tayi ta ce, "bafa tada nauyi ALLAH.
YA munnir dake kusadasu yana jinsu ya ce, "aidama gida kuka tafi tunda anga yanda jikin NATA yake.
Abba ya ce, " gaskiyarka muneer, Abdulmaleek kutafi gida hakanan, kuma su Muneer kud'auki iyalanku Ku tafi gida saboda yara dakuka bari..
Rahma ta turo baki gaba cikin shagwa6a ta ce, "Abba nidai anan zan kwana gsky.
A'a auta bazai yuwuba, idan anbarki kin kwana anan mijinkifa, bobo yad'an shafa Kansa idonsa ak'asa ya ce, "Abba abarta ta kwana Indai Dan tanine babu wata matsala.
A'a a aiba hauka akeba Cewar ummi dake Harar Rahma.
Abba ya ce, "kutafi gida kinji auta, ALLAH yay muku albarka gaba d'aya, gobe idan ALLAH yakaimuma aii ranace ko.
Bobo ya ce, " to Abba bara muyi sallar isha'i, Dan komun tafi a hanya zata riskemu.
Eh gsky ne to kubari ayid'in.

Bayan sallar isha'i badan Rahma tasoba suka fito gaba d'aya harsu ya Shaheed da matansu domin tafiya gida.
Abba da ummi kad'ai aka bari a asibitin zasu kwana.
Har yanzun Nawal tana bayan Rahma agoye saida zasu Shiga mota bobo ya taimaka mata ta sauketa ya kwantar da ita a sit d'in baya sannan suka Shiga mota kowa yanufi gida.
Babu maima wani magana harsuka Shiga cikin gidan, bayan mai gadi yabud'e musu suka Shiga, bobo yay fakin suka fito, harzata d'auki Nawal ya ce, "tabari ya d'auketa, bata Musa masaba tabari ya d'auketa suka Shiga cikin gidan.
Har d'akinta yakai Nawal ya kwantar, ita kuma tashiga wanka.
Shima d'akinsa yanufa yacire doguwar rigarsa yasaka kayan barci, fitowa yayi yanufo dinning Dan yunwa yakeji.
Rahma tafito wanka ta rama sallolinta sannan tanufo falo domin d'aukar Abu.
Ganin bobo zaune a dinning yatuna mata dabaifa ci abinciba Ashe, jitayi yabata tausayi, tak'araso Inda yake tana fad'in sorry Nurilk'albi muntafi ko abinci bakaciba.
Murmushi yay mata ya ce, " karki damu o, kina arikicannan ta'inama zaki tuna da cikina.
Marairaice fuska tayi tamkar zatayi kuka, ta ce, "pls kamin afuwa.
Ayya my Nusfulhayat karki damu ai nasan bakiyi da niyyaba.
Itama murmushin tamasa.
Ya CE, " babynkifa?.
Tana barcinta har yanzu.
OK tom zoki zauna muci abinci, Nima yunwace ta addabeni shiyyasa ban nemekiba.
d'an yatsine fuska tayi tareda ta6a cikinta ta ce, "nikam na k'oshi."
Kamo hannunta yayi, yajawota ta zauna saman cinyarsa, shima hannunsa ya d'ora akan cikin nata yana shafawa ahankali, haba my Nusfulhayat kinaso ki haifamin babyna d'an k'aramine?, nifa k'atoto nakeso Wanda Nawal zata d'auka da k'yar.
Kallonsa tayi tad'an juya idonta dasuka kummbura saboda kuka, tasaka hannu tarufe fuskarta tana fad'in Nurulk'albe baby kuma?, a INA?.
Hannunta ya janye ya d'aga mata gira, ya ce, "acikinki mana.
Tad'an zaro ido tana tura baki gaba ta ce, " nidai kabar fad'a.
Ya ce, "miyasa?."
Since kanta tayi ak'irjinsa cikin sassanyar murya ta ce, "wlhy inajin kunya.
Tabashi dariya Dan haka yay murmushi mai sauti tareda d'agota yana fad'in Ashe kunyarnan har yanzu ban gama fiddataba?, shikenan nadaina tashi muci abincin.
Girgiza masa kai tayi.
Ya ce, " pls ko kad'an kici.
Yunk'urawa tayi zata tashi, ya maida ita ya zaunar, no yizamanki kawai.
Badan tana son cin abincinba ya matsa mata, dakansa yarink'a bata shima yanaci, tana zame zame damasa ta6aradai har sukaci da d'an yawa sannan suka mik'e, ya taimaka mata suka gyara wajen tsaf sannan kowa yanufi d'akinsa.
Harta kwanta ta rungume Nawal taji motsin shigiwarsa shima gadon yahawo, suka saka Nawal a tsakkiya, yamusu addu'a ya shafama kowa sannan yahad'asu yarungume sai barci..

Nima dai homajeep d'in k'afafuna naja natafi wajen my Abdul d'ina nabar Rahma Dana itama.😜


.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Washe gari bayan sunyi breakfast Rahma tabisu, yasauke Nawal A school sannan suka nufi asibitin.
Har cikin yashiga shima, yatayata d'aukar kulolin kayan breakfast d'in Data had'o musu, ahanya suka had'uda Abba zai fita, suka rissina suka gaisheshi, cikeda fara'a ya amsa musu, Yakoma yimusu bangajiyar jiya, suma suka tambayeshi yamai jiki?, ya ce, "a dasau kam Dan tana nanma zaune yanzu haka.
Alhmdllh suka fad'a atare.
Ya ce, "kuk'arasa ciki to, nima zanje gidane na shirya nawuce kasuwa.
Saika dawo.

Da sallama suka shiga d'akin, Safna tana zaune akan gado tajingina bayanta da filo, hannunta manne da k'arin ruwa.
Ummi na zaune agefenta tana had'a shayi, d'agowa sukayi gaba d'aya suna amsa sallamar, Safna kallo d'aya tamusu ta kauda kanta.
Ummi ta tashi tareda turama bobo kukerar tace ya zauna.
A'a ummi kiyi zamanki, zanma wuce wajan aikine, rissinawa yayi ya gaidata da tambayar maijiki, ta ce, "jiki Alhmdllh tunda gata azaune hartana magana.
Ya ce, "ALLAH yak'ara sauk'i.
Ameen ummi tafad'a tana fita.
Rahma dake Kusada Safna tsaye tana tambayarta yajikin?, da k'yar ta amsata, Rahma dai bata kawo komai arantaba duk zatonta zafin ciwone.
Ummi nafita bobo ya kalli Safna, ya ce, " antynmu ya jikinki?.
d'ago manyan idanunta tayi ta kallesa, ahankali ta ce, "da sauk'i.
Ya ce, " ALLAH yak'ara sauk'i, yasa kaffarane.
Amin tafad'a a saman la66anta.
Shiru nawani d'an lokaci, bobo yakalli agogon hannunsa sannan yakalli Rahma, my Nusfulhayat bara nawuce ko, kinsan yau k'arfe 10 zamushiga shari'armu dasu Alhaji Abdurrazaq.
Itama kallonsa take tana d'an murmuahi ta ce, "to Nurulk'albi ubangiji ALLAH yabada nasara, yakuma d'oraka akansu.
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi, ahankali yabud'e akanta ya ce, " ngd sosai da addu'arki gareni my Nusfulhayat.
Murmushi kawai tamasa batareda tace komaiba.
Yamatso daf da ita, bata ankaraba taji kiss akumatunta, d'an zaro ido tayi tana kallonsa, shikuma yad'aga mata gira sannan yamik'a mata kumatunsa wai tamasa kiss, hannu tasaka tarufe fuskarta tareda fad'in kai Nurulk'albi nidai a'a gsky.
Dariya yayi ya ce, " shikenan aii, ya kalli Safna da bak'incikin abinda sukeyi agabanta tamkarma sun manta da ita ya tokare mata mak'oshi.
Auntynmu ALLAH yak'ara lfy fa, bara natafi office time natafiya, sai dai ganinki yasa matana takasamin adawo lfy.
Murmushin yak'e Safna tayi Wanda duk Wanda yagani yasan tabbas na yak'ene, ta ce, "a'a nikam babu ruwana..
K'ofar yabud'e zai fita sannan yajuyo ya kalli Rahma yakashe mata ido d'aya yafice.
Murmushi Rahma tayi tana girgiza kai.
Safna tazame ta kwanta idanunta cikeda kwalla.
Ahaka ummi tashigo ta samesu, sai yanzu Rahma tasami damar gaida ummi.
Ummi takama hannu Rahma suka zauna ta ce, " autana ina d'iyar takine?.
Tana makaranta ummi, saida mukama ajiyeta sannan muka wuto nan, ALLAH sarki aii yarinyar tanada Shiga rai wlhy, gatada wayonta masha ALLAH.
aii ummi saima kin zauna da Nawal wlhy, yarinyar batada damuwa ko kad'an.....
Haka sukaita hirar Nawal, Safna tana kwance tana jinsu amma tayi shiru, da k'yar ma ummi tasata ta tashi tayi breakfast da kayan Rahma data kawo.
Ummi saiyabama girkin Rahma takeyi itakuma tanatajin dad'i, Safna dai batacemusu k'alaba har doctor yashigo yaduba jikinta yacire k'arin ruwan.
Fitar doctor babu dad'ewa saigasu ya muneer da matansu, suma basu dad'e dazuwaba saiga 'yan gidansu ya Kamal, harma dashi ya Kamal d'in, saikuma ga Appa Ammi da inna, nanfa akashiga gaishe gaishe datambayar mai jiki.
Zuwa azuhur asibin yacika da dangi, sunata tururuwar zuwa ganin Safnar, haka suka kasance da dangi, kowa yaga Rahma saita burgeshidantakuma yin bul bul da ita, ga wani k'yau da murjewa data k'ara na musamman.
Aunty yahanasu Maman Basma ma

Please Login or Register in order to submit comment