Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rahane ta ga cewa kuka ba zai mata ba, gara ta roke shi ya yiwa Allah ya rabu da ita ko kadan ba ta son shi. Ba tun yau ba, haka nan ko ganinshi ba ta son yi saboda kamanninsa.
Ta ce, “Don Allah don Annabi ka yi hakuri ka nemi wata, ni makaranta nake so na yi...” Ta ci gaba da kuka.
Ya ce, “In don wannan ne Rahane daina kuka, zan barki ki ci gaba da makaranta amma bayan anyi auren mu”.
Ta zaro ido ta ce, “Ni ba zan yi aure ba, yoyon fitsari yake sawa”.
Ya bushe da dariya ya ce, “Duk karyar nasara ce Rahane, iyayenmu da kakanninmu basu kai ki ba duk aka yi musu aure, me ya same su?”
Cikin kuka ta ce, “Nifa bana sonka, ko dole ne?”
Ya yi fuska sosai, sai kuma ya ce, “Ayya! Kin makaro, zamanki lafiya da matsiyacin ubanki kawai shine ki yarda ki aure ni, wanda daga ana bashi ‘yar dari biyar ya yarda ya bani aurenki. In ke baki sona, ni ina sonki, dama ba son na zo nema ba tunda baki da kunya, har ki dubi tsabar idanuna ki ce bakya sona, ba ki yi tunanin cewa ina da kamar ki a gida ba.
Aure kuwa nan da sati biyu tunda kin bullo min ta nan. Makarantar ma na fasa barin ki kiyi, shashashar wofi!”
Ya karkace ya zaro kudi a aljihunsa ya haska da cocilan ya ce, “Ungo nan, ki raba ke da kakarki”.
Ya kuma turo mata wata katuwar leda, “Amshi nan ki sabunta tufafinki kafin a kawo lefe shashashar yarinya da ba ta san abin arziki ba”.
Juyawa ta yi tana kuka sosai ta nufi cikin gidansu bata karbi kudi da ledar da yake tura mata ba.
Ya bi bayanta ya kira wata yarinya dake sai da gyada a nan gefensu, ya ba ta kayan da kudin ya ce ta kai mata. Shi kuma ya saki wani matsiyacin fito ‘fiii-fiii....’ ya yi gaba yana cewa,
“Kwanan nan zan farke santaleliyata, Rahane!”.
Rahane na shigowa gida tana kuka ta yi ido hudu da Babanta a tsakar gida yana dakon shigowarta.
Kofar dakinsa ya nuna mata, wato ta shiga. Shi kuma ya tashi ya bita. Ya zauna a kan tabarmar shi ta kaba dake shimfide a dakin ya dubi Rahane wadda ke ta kokarin hadiye kukanta karfi da yaji.
Ya ce, “Rahane!” Ta cira kai ta dube shi idanunta jawur.
Ya ce, “Ni Babanki ne, ni na haifeki, kin san kuma ba zan cuceki ba. Ko baki son auren Ado ki yi hakuri ki tusawa zuciyarki son.
Na samu kaina da talauci mai yawa, kada ki manta gidan nan ma da muke ciki na Ado ne, amma yau tsayin shekara goma sha daya tun haihuwarki Ado bai kara karbar kudin haya na ba.
Idan na ce zan gaya miki irin taimakon da Ado yake mini ba za ki taba yarda ba. Ya sha siye kayana don in samu abin da zan baku ku ci, ba don yana da bukatar su ba.
Duk halin banzan da ake kira mishi ni na yi bincike kansu ban gani ba, zancen nan da nake miki yanzu haka ya samo min aikin kula da dawakin Hakimin Takai, na daina wahalar shan rana a kasuwa, babu wani cinikin arziki. Idan kika ki auren Ado me kike so in ce masa, ko in masa na biyashi alherin da yake yi min?
Don haka ki kwantar da hankalinki, ki kwantarwa Iya. Idan har kina kaunata Rahane ki nunawa Iya kina son auren nan kin ji Rahane? Don Allah ki fitar dani kunyar Ado”.
Rahane ta daga kai. Ta yarda kawai da kudi Ado ya saye Babanta. Abin da ba ta taba tsammani ba, kwadayi daga Babanta!
Ya ce, “Shi kenan Rahane jeki. Allah ya yi miki albarka”.
Ta mike hawaye na mata ambaliya ta fita ta samu Iya na sallah mai tsayi, sai ta hau ‘yar yaloluwar katifarsu ta kwanta.
Barci ya kasa dauke Rahane, duk iya satarsa kuwa. Duk da kasancewarta karamar yarinya ‘yar shekaru goma sha daya tana da zurfin tunani da hangen nesa.
Tana son Babanta fiye da yadda shi yake sonta, ta san Babanta ba shi da kwadayi, don haka ta yi matukar mamakin yadda ya yi hakan, kamar ma tsoron Adon yake ji.
Ta tuno wai ya samo masa aikin kula da Dawakan Hakimi, kuma baya karbar kudin hayarsa. Wannan ne dalilin da yasa zai bashi ita. Abune da take da yakinin cewa, Iya ba za ta taba yarda ba, wato ayi mata aure yanzu, don haka ta dan samu salama a cikin ranta.
Har barci ya dauke ta, kayan da Ado ya biyota dasu suna nan a gefe ko daga su Iya ba ta yi ba.
Da asubahin ranar Iya ta tashe ta don ta yi sallah. Ita kuma tana hada kayan su cikin Ghana must go. Kaf ta hada kayansu bata rage komai ba.
Rahane na sallah tana jin Iya da Babanta na fafatawa. Iya na cewa, “Gidan Ado ko? To daga yau bamu kara kwana cikinsa ni da Rahane, in dai a kansa ne za ka ba shi auren yarinya mai daraja irin Rahane. Sai ka san yadda za ka yi da shi da kudinsa da kake ci.
Ba aikin gidan Hakimi ba, Allah yasa aikin Hajji ya samo maka. Sai ka ganmu, sannan ka yi mata auren”.
Iya gigicewa Malam Rashidu ya gigice, don ya san halin Iya kwarai in ta furta abu, to wallahi ba mai iya hanata.
Shi ba wani abu bane don sun tafi, bai san ya zai yi da Ado ba wanda ko mahaliccinshi baya tsoro, yadda yake tsoron Ado a kwanakin nan.
Ya yi magiyar ya yi lallashin amma Iya ta yi banza da shi. Da ya gaji ya mike jiki babu kwari ya fita, ya kasa zuwa ko’ina yana zaune a dakinsa ya saka wannan ya kwance. Bai ma san sanda Iya tasa Rahane a gaba ba suka fice. Rahane dauke da dakon kayansu zuwa tashar motar Rake suka hau bayanta suka bar Takai baki dayanta.
****
[12/24/2019, 17:56] Takori: Tunda suka hau titi Rahane kuka take tana tunanin Babanta da abin da ka je-ya-zo. Shi kenan yanzu ta rabu da Babanta? Shima ta raba shi da mahaifiyarsa dake matukar son shi? Ina za su? Yaushe zasu dawo? Ko dai ta hakura ta ce da Iya su koma ta auri Adon?
Ita kanta Iya kuka take ranta cike da tunanika masu yawa. Ko dai su koma ne? Ta fishi iko da diyarsa ne? Ko ta fishi sonta? Ta daure mata gindi kenan ta ki yin biyayya ga mahaifinta. Ita ba aure ne ba ta son a yiwa Rahane ba, mijin ne bai yi mata ba, da shekarun Rahanen.
Mummunan hatsarin ya faru ne a kwanar shiga garin Tsangaya. Inda wata motar haya peageout irin masu mugun gudun nan ta karawa Akori-kurar raken da su Rahane ke ciki ta kife.
Wasu suka zubo kan titin, wasu suka fada cikin ramuka motar ta danne su. Tsirarun motocin dake gabansu da bayansu suka tsaya don kawao agaji. Ga shi babu jami’an tsaro a kan titin baki daya.

****









Cikin wadanda aka kwasa zuwa asibitin koyarwa na Kano, cikin masu hatsarin da suka tsira da numfashinsu har da Rahane. Cikin gawarwakin da aka kai mutuware kuma har da Iya Bilki.
A hankali Rahane ke bude idanunta tana kallon likitan da ke tsira mata allura cikin jijiyoyin hannunta.
Abubuwan suka soma dawowa Rahane tar-tar a idanunta. Da sauri ta juya gefenta inda Iya Bilki ke zaune, babu kowa. Kai dakin ma da take ciki ba ta taba ganin irinshi ba. Haka mutanen da take gani suna gilmawa ba ta saba ganin irinsu ba.
Wadannan fes-fes suke cikin fararen kaya masu tsabta, ba irin kalar jama’ar da ta saba gani bane.
Dr. Mansur, ya manyanta sosai, shine babban likita yau a emergency, yana daga zaune yake bai wa dalibansa dake tsaitsaye lacca na taimakon da za su yiwa Rahane, wadda goshinta ya fashe ko’ina kaca-kaca da jini a jikinta, ba za ka iya tantance iyakacin raunin da ta ji ba.
Dinke nan, like nan haka suka yi ta yi, yayin da kuka ya gagari Rahane saboda azabar da take ji a cikin gangar jikinta tayi azaba. Ta suma ya fi sau uku suna kakaba mata oxygen tare da bata taimakon duk da ya dace.
Washegari da ta farka karfe takwas na safe da dan sauki jikin nata. Don haka ta fara kuka a hankali. Dai-dai da shigowar Dr. Mansur da tawagar kananan likitoci dake binsa a baya.
Cikinsu har da photocopy na Dr. Mansur wato matashin likitan da ke (housemanship) mai amsa sunan I.M Takai, wato IBRAHIM MANSUR TAKAI.
Da gani babu tambaya ka ga uba da dansa. Duk da yanayin halayyarsu a fuska ya nuna ba daya bane, domin shi Dr. Mansur mutum ne mai sakin fuska sosai, sabanin Ibraheem da yake mutum mara walwala sam-sam. Duk abin da Dr. Mansur ke yiwa Rahane suna jotting ne.
Dr. Mansur ya matsa dai-dai kan Rahane ya dora hannunshi a kanta ya ce, “Daina kuka kin ji? Insha Allah za ki samu lafiya”.
Ta cira idanunta da suka kada suka yi jawur a hankali ta dube shi, bakinta na motsi amma ta kasa magana.
Ya dubi Ibraheem ya ce, “Dagata ta zauna”. Ya cirata ta zauna ya tusa mata filo a bayanta ta zauna sosai.
Dr. Mansur ya ce, “Me sunanki?” Bin shi ta yi da ido kawai ba ta yi magana ba. Ya ce, “Ku rabu da ita ta warware a hankali”.
Nurse din da suke tare ta mika mata kofin tea. Dr. Mansur ya ce, “Bata shayin ta sha Ibrahimu”.
Ya yi kamar bai ji ba, ya yi baya kadan ya dan tura Eric Ipatobe abokin karatunsa dake gabansa yayi baya. Shima Dr. Mansur sai ya yi kamar bai ga abin da ya yi din ba. Cikin girgiza kai ya karbi kofin ya matsa sosai ya soma bata da kansa. Yana fadi cikin ransa, dani kake zancen, wallahi sai na kwashe maka maki (marks).
Mamaki ya kama su dukkansu, Doctor Mansur da kansa! Da sauri Nurse din ta karba tana bata. Ya dan ja baya ya sarke hannun shi a kirjinsa bai kara kallon Ibrahim ba. Ya ci gaba da feso musu lacca kamar Obama ya diro Nijeriya.

Kwana uku Dr. Mansur na kula da Rahane, ta ji sauki sosai amma ta ki magana. Don haka ya soma tunanin akwai wani abu. “There must be something wrong beneath!” Ya fadawa su Ibraheem.
Ya girgiza kai ya juya gare su, “Tana bukatar ganin likitan kunne da makogaro yayi examining dinsu, wanda wannan ba shine darasin da muke a kanshi ba tukunna, muna neman lafiyar gangar jikinta ne gaba daya”.
Cikin sati biyu Dr. Mansur ya ba da hankalin shi da kwarewar shi gaba daya a kan Rahane da shi da Dr. Imam, kwararren likitan kunnen da ake ji da shi a AKTH. Duk wani taimako da ya kamata ya bata sun bata, amma Rahane sai da aka dangana da hearing test wanda ya nuna ta gamu da very unusual hearing issue, wanda ke bukatar ayi CT Scan da MRI Scan, dake bukatar kudi na fitar hankali wanda zai nuna hakikanin menene matsalarta daga inner and outer zones na kunne da kwakwalwarta, a dalilin rashin sanin daga inda ta bullo da kuma rashin sanin kowa nata, suka samar da occasional hearing Aid gareta, sannan ta ji abin da suke cewa. Amma idan aka cire bazata ji ba. Duka daga aljihun Dr. Mansur Takai, wanda Allah ya sakawa kaunar Rahane da tausayin ta,
Yau Asabar ba shine on call ba, Dr. Hashim ne, amma sai da ya shigo asibitin musamman don yaga jikin Rahane. ‘Yar shi karama AZiza na rike da hannun shi, caftan na shadda milk colour ne a jikinshi da hular da ta dace dasu ba suit da lab-coat ba.
Rahane na hangoshi ta soma murmushi, shima murmushin yake mata. Ganin ta zauna ras alamun lafiya na samuwa, ya ja kujerar dake gabanta ya zauna.
“Yar Doctor, lallai lafiya ta samu”.
A sanyaye ta ce, “Alhamdulillah!”
Lokaci na farko da ya ji furucin bakinta, tun ranar da su kai hatsarin.
Shima ya ce, “Alhamdulillah ‘yata ya ya sunanki?”
Ta ce, “Rahane”.
Ya bushe da dariya, “RAYHANAH kenan ko?’
“A’a, RAHANE!” Ta sake gyara masa.
“To na yarda Rayhanatu, ni ba zan iya fadar wancan din ba, saboda ba shi da ma’ana kwata-kwata”.
Dr. Hashim na jinsu yana dariya yana auna patient din gadon kusa da ita. Lokaci guda Rahane ta soma kuka. Duka likitocin suka tsaida dariyar suka yi kanta.
“Kuka Rayhanah? Daina kuka har gida zamu kai ki. Fatanmu shine Allah ya baki lafiya mu tambayeki ke da waye kuka taho? Kuma ina ne garinku?”
“Ni da Iya ne, kuma ban ganta ba tun ranar”.
“Za ki iya gane ta cikin kowanne hali?”
Ta ce, “Eh”.
“Daga ina kuke?”
“Takai, zamu Tsangaya”.
“Takai? Ikon Allah”.
Ya yi dan shiru yana kallon ta. “Sunana Dr. Mansur Balarabe Takai....”
Ta dube shi da sauri. Ya gyada mata kai yana dariya. Dr. Hashim ya juyokadan ya ce, “Dr. Takai, ashe ‘yar taka ‘yar garinku ce, dole a bata extra kulawa, kyakkyawa da ita, ina kamu Doctor”.
Murmushi ya yi, ya ce da Nurse dake gefe a kawo Rahane ‘matuary”.
A kujerar daukar marassa lafiya nurses biyu suka turata zuwa mutuware.
Aka soma zarowa Rahane akwatunan gawarwaki abin babu kyawun gani. Rahane ba ta taba ganin gawa ba sai yau a idanunta. Iyakacin firgita ta firgita, amma da aka zaro Iya Bilki, ba ta san sanda ta fada kanta ta rungumeta ba. Kuka take na fitar hankali, domin Iya sumul take babu ko kwarzane a jikinta. Idanunta ne kurum a rufe kamar mai barci, kamar ta ce “Iya”. Ta bude ido ta amsa mata.
Da kyar Dr. Mansur ya janyeta, aka hada Iya cikin motar daukar gawarwaki na asibitin. Motar Dr. Mansur na biye dauke da Rahane da I.M a gidan gaba, suka dauki hanyar Takai.

Rahane na baya ta kankame jikinta tana kuka mai cin rai, sai dai daga Doctor har dansa Ibraheem babu mai jin ta sakamakon kira’ar Ahmad Sulaiman da Dr. Mansur ya saki a motar har suka isa garin Takai.
Rahane ke nuna musu hanya da aka shigo Takai har kofar gidansu. Tana hango Akori-Kurar Ado a kofar gidansu gabanta ya yi mugun faduwa. Hakan bai hanata fitowa daga motar ba a lokacin da Ibraheem ya bude mata, yana ta zabga mata harara kamar ya hankadata.
“Shiga ki karawo shi Rayhanah”. In ji Baba Dacta (kamar yadda take kiranshi)
Da addu’a tasa kai cikin gidansu. Ta yi sallama ba a amsa ba. Sai kawai tasa kai. Caraf! Ado ya cafke ta ya danneta a dakin Iya, nan ta ga babanta a makure a gefe daga shi sai gejeran wando, ko’ina a jikinsa shatin bulala ne, jini ya bisu ya kwanta.
Ado ya ce, “Munafiki! To gata ta dawo da kafafunta, auren ma na fasa a gabanka zan yi kaca-kaca da mutuncin ta in fanshe wahalata ta shekara da shekaru”.
Bai yi la’akari da halin ciwuwwukan da ke jikinta ba ya hadata da bango ya keta rigar jikinta tun daga sama har kasa.......!

Ihun da Rahane ta zabga ya amsa kuwwa har sauran gidajen da ke makwabtaka dasu suka jiyo. Dr. Mansur na waya, dansa Ibraheem ya yi saurin dagowa ya ce,
“Daddy.....yarinyar nan ihu fa take yi”.
Da sauri Dr. Mansur ya juyo, shima kunnuwansa suka jiyo masa kururuwar da Rahane ke zabgawa. Shi da Ibraheem suka runtuma cikin gidan ba tare da sunyi wata maganar ba.
A lokacin Ado ya kaita kasa, dan kamfai ne kawai a jikinta. Ga Malam Rashidu a gefe dunkule wuri daya yana ta kwararar da hawaye sai tsima yakeyi ko uffan bai ce ba.
Ibraheem ya danko kwalar rigarshi ya finciko shi ya hada shi da bango, ya dunkule hannu ya sauke a bakin Ado, sai ga hakora biyar sun zubo, jini ya biyo bayansu. Ya tankada shi tsakar gidan da doguwar kafarsa.
A lokacin jama’a makota har sun cika gidan, shi kuma Daddy waya ya yiwa ‘yan sanda nan da nan sai gasu a (shiga-ba-biya) suka danna Ado a ciki, jama’a na ta sallallami ganin Malam Rashidu daga shi sai gajeran wando gaba daya ya fita hayyacinsa ya zama dan tsurut. Jikinsa ba masaka tsinke da tambarin bulala. Rahane na gefe ta kankame jikinta tana ta kuka.

I.M Takai, ya ciro suit din dake jikinsa ya rufa mata, don ta kare tsaraicinta.
Nan Malam Rashidu ya matsa gaban Rahane ya saka kuka. Cewa yake

“Ina Iya Rahane?”

Jama’a makota suka soma cece-kuce kan cewa yau sati biyu kenan basu sa Malam Rashidu da Rahane a idanunsu ba, sun dauka ma barin garin suka yi ba tare da sun yiwa kowa sallama ba.
Dr. Mansur ya ciro malun-malun din da yake snaye da ita ya sanyawa Malam Rashidu. A nan ya soma gaya musu yau sati uku kenan Ado ya kulle shi yana azabtar da shi a kan sai ya fada masa inda ya kai Rahane don kar ya bashi aurenta. Bayan shima bai san inda suka tafi ba ita da Iya.
Kowa ya ce, “Ado zai aikata fin haka. Allah ya saka masa”.
Dr. Mansur ya ce, “Sunyi hatsari ne ita kadai ta sha aka kaita asibitin su, Allah ya yiwa Iya rasuwa tare suke da gawarta”.
Malam Rashidu ya rikice da kuka shi yana yi Rahane na yi. Jama’a na ambaton “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Allah ya ji kan Iya Bilki, Allah ya yi mata rahama”.
Kan ka ce meye wannan jama’ar Takai ma’abota kara da hadin kai sun cika kofar gidan. Tare da Dr. Mansur da I.M aka sallaci Iya Bilki, aka dauketa zuwa gidanta na gaskiya. Dacta da I.M suka wuce gidan Hakimin Takai.

Dr. Mansur dan asalin garin Takai ne. Da shi da Mai-Martaba Hakimin Takai cikinsu daya, sai dai shi Mansur dan boko ne na a buga a jarida, kwata-kwata baya sha’awar sarautar tasu, ko zaman garin su sai dai ya zo da ziyara, yana Kano tare da iyalinsa. Shekararsu goma a kasar Ireland suna karatu shi da mahaifiyar su Ibraheem (Asma’u) wadda ‘ya’yanta suke kira (Mami).
Mami ‘yar asalin garin Jos ce, (arnan Jos), a da, bata da addini, sunanta (Anita Shiyana). Sun hadu da Dr, Mansur a jami’ar TRINITY dake (Dublin). A hannun Mansur ta karbi musulunci ta kuma rike shi da kyau, ya sanya mata sunan mahaifiyarsa (Asma’u) wadda ta dade da rasuwa, don haka shima Mamin yake ce mata.
Mami cikakkiyar likitar yara ce (paediatrician) da ta san aikinta. Duka yaransu biyar, kowane da rata sosai tsakaninsa da wanda yake bi a haihuwa.
Rayuwar Mami zallanta na (Irish) wato na mutanen Ireland ne, ga masifar son ‘ya’ya. Ba ta son kowa ya rabe su, daga ita sai ‘ya’yanta sai mijinta. Sabanin mijin, Dr. Mansur mutum mai kara da kawaici, ga faram-faram da mai da kowa nasa, ga son zumunci da muhimmanta shi. Ga son mutane da saukin kai,

Tunda ya shigo gidan Hakimi tunanin Rahane da Babanta yake, da yanayin ban tausayin da ya baro su a ciki. Suna hira da dan’uwansa Hakimi Abdullahi Takai, amma ya lura sam hankalin dan’uwan nasa baya tare da shi.
Ya yi gyaran murya “Wani abu ya faru ne Mansur?’
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, “Wani abin tausayi nake tunani, Allah ya ja da ran Hakimi”.
Ya warware masa komai. Shi Hakimi bai san su ba. Ya ce, “Yanzu da kasa kanka cikin dogon tunani irin haka me kake ganin za ka iya yi a kansu? Talakawa fa na da yawa a kasar nan, ba su kenan ba, kuma ba za su kare ba”.
Dr. Mansur ya girgiza kai ya ce, “Allah shi ya hada jinina da wannan yarinya, zan tafi dasu Kano. Shi ya yi min aikin gadi, ita kuma yarinyar zan hadata da su Abida in dau nauyin iliminta, don da ganinta ba haka Allah ya yi nufin barinta ba!”.
Hakimi ya girgiza kai, jin yadda yake maganar (with confidence) kuma tun daga karkashin zuciyarsa “Ka tafi da yarinyar kawai, ka bar min uban a nan za sa a kula da shi. Daman kuma sarkin Dawaki ya rasu, ina neman nitsattsen mutum wanda zai jure hidimar Dawakai na babu lalaci har na baza cikiya a cikin gari.
To ka san halin talakawan namu basu yarda su rabemu saboda gudun wulakanci, na shaidi jama’ar Takai a nan”.
Dr. Takai ya ce, “Hakan ya yi, na ji dadi sosai Yaya. Bari in tura Ibrahimu ya zo dasu”.
Ya dauko waya ya kira I.M ya ce, “Daddy ina barga tare da Dawakan Mai Martaba”.
Ya ce, “Daure ka zo maza, ko da yake ba sai ka dawo ba, ka je ka zo min da yarinyar nan da mahaifinta yanzu. Ina tare da Hakimi”.
Ya rausayar da kai ya ce, “Daddy why me (me yasa sai ni)?”
Doctor ya ce, “To wa ya san gidan idan ba kai ba?’
Yana daga cikin mota yana kallon yadda jama’a ‘yan zaman makokin Iya suka cika harabar gidan, yana daga cikin motar bai fito ba yana ta shan kamshi da jan numfashi.
Can kuma ya yafito wani saurayi ya ce don Allah ya daure ya zo masa da Malam Rashidu da ‘yarsa, ya sanar

Please Login or Register in order to submit comment