Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta karkaro ta zuba masa sannan ta ɗebo gishiri mai ɗan dama ta ƙara masa ta yanda ba zai iya ci ba, ta ɗauka ta fito. Ko da Baba Ladi ta haɗu da ita a kofar fitowa daga kitchen din ta ce mata "Hanne wa zaki kaiwa wannan ƙanzon? Ba dai bil adama zaki bawa wannan abincin ba?"
Sai ta ya mutsa fuska ta ce "Almajirai zan bawa ai su suna so ya fi a zubar."

Girgiza kai Baba Ladi ta yi ta shige kicin ɗin abunta tana yiwa Hanne fatan shiriya don yanzu ta sani tana ƙara magana zata iya zaginta.

Ita kuwa Hanne tsaki ta ja tana faɗar "Gulmammiyar tsohuwa kawai 'yar sa'ido. Wallahi kowa ya shiga gonata a gidan nan sai na aske shi tas, bari dai na gama da wannan mummunar halittar na dawo kanki daga baya." Ta faɗa ƙasa-kasa tare da wucewa zuwa sashen Mahmud don kaiwa Abdul abunda take kira da abincinsa.


To fah readers? Me Hanne ke shirin aikatawa..
Wannan fa shi ake kira da rijiya ta bada ruwa guga ta hana.


Mu je zuwa dai don ganin ya za'a garƙe.

More comment more typing












Follow me on Wattpad @Ruky_i_lawal

Instagram: Rukayyarh_ibraheem












UMMU INTEESAR CE


*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*


*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*

DEDICATED TO ALL MEMBERS OF HALITTAR ALLAH CE FANS GROUP.

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
PAGE 57-58


Ƙofar Sashen a buɗe take don haka ta shige kai tsaye.

Lokacin Abdul na kwance kan doguwar kujera fuskarsa har ta kumbura ɗayan idonsa ya yi ja, da alamu ya ci kuka har ya ƙoshi.

Jin an banko kofar da ƙarfi ya saka shi zabura, ya tsorata sosai.

Hanne ta ƙaraso gabansa tana tamke fuska, sannan ta miƙa masa abincin.

"Kai Dabba tashi ga abincinka." Ta faɗa.

Baki na rawa ya ce "to." Tare da amsar kwanon don tun ranar farkon zuwansa gidan yake tsoronta.

Fara ci ya yi hannu baka hannu ƙwarya saboda matsananciyar yunwa da ya jima bai ji irinta ba.

Lomar farko da ya yi ya fito da idonsa waje, kamar zai dawo da abincin waje. Sai kuma ya tuna ai ya saba da irin wannan, tunda ya ci wanda bai ma kai wannan tsafta da daɗi ba.

Tsawa ta daga mishi "Ubanwa kake fiddowa ido? Nakasasshen banza maza ka cinye shi tas. Kuma wallahi idan ka sake ka gayawa wani a cikin gidan nan kalar abincin dana baka sai na ƙwaƙule ma ɗayan idon da kake da kowa ya huta. Dama miye amfanin ka?"

Ɗaga mata kai ya yi alamar to. Ya ci gaba da tura abincin yayin da ta yi ƙwafa ta juya ta fice daga ɗakin.

Hawaye ne suka ci gaba da bin kuncin yaro Abdul. Kukan zuciya yake tare da kuka na sarari. Maganganu Hanne sun tsaya masa a rai, haka sun zauna a kwanyarsa daram.

"Dama ashe bani da amfani shiyasa mutane basa sona?" Ya faɗa a ransa.

Nan fa zuciyarsa ta yi ta masa saƙe-saƙe akan rayuwarsa.

"Tabbas banda amhwani ga kowa, don ga shi sauran yara dut suna makaranta wanga lokaci amma ni gani nan kulle cikin ɗaki saboda kowa tsoro na ya kai."

Ya faɗa yana daɗa fashewa da kuka.

Bayan kwana biyu gidan ya gama yiwa Abdul zafi don nan ɗin ma dai kamar gidan Kande, ya zame masa inuwar bagaruwa ga sanyi ga ƙaya.

Don haka ya fara tunanin guduwa sai dai ba hali tunda ƙafafunsa basa tare dashi (sanduna). Dole ta saka ya haƙura don ba zai iya guduwa da rarrafe ba.

Haka ya cigaba da addu'ar neman mafita, dama yaron akwai son ibada ko wacce sallah bata wuce shi. Ko lokacin da yake jeji da ya kwatanci lokacin sallah ya yi koda bai samu ruwan alwala ba a haka yake sallarsa don bai ma san da zama taimama ba bare ya iya ta.

Allah maji roƙon bawa, a kwana na uku da tafiyar Mahmud Likitansu ya samo sandunan bayan shafe tsawon makwanni yana nema. Don haka ya kawowa su Hajiya har gida kamar yanda ya alƙawartawa Mahmud.

Haka ma ya nemi akai shi ga Abdul don ya gwada sandunan ya ga ko zasu ma yaron.

Hajiya ce ta masa jagora har sashen a karo na farko da ta leƙa sashen tun bayan tafiyar ɗan nata. Wannan ma don bata son likita ya zargi wani abu har ya faɗawa Mahmud ne.

A bedroom suka same shi zaune akan tiles ya buga tagumi sai sana'arsa yake ta hawaye.

Da sauri Hajiya ta dube shi "Subhanallah! Abdul me ya same ka kake kuka? Ya ma aka yi ka rame ko baka cin abincin da ake kawo maka ne?"

Kallon zargi likitan ya mata, sannan ya dubi yaron ya ga alamun tsoron hajiyar tattare da shi.

Girgiza kai kawai ya yi alamun tausayawa da mamaki ya ce "Yaro karɓi waɗannan mu gani ko za su maka." Ya miƙa masa.

Karɓa ya yi ya miƙe, sai dai sun masa tsayi kaɗan. Cikin Sa'a kuwa aka yi dace da irin sandunan nan ne masu maɓallai da ake iya ƙara tsawonsu ko ragewa.

Don haka likitan ya rage masa su ta yanda zasu masa dai-dai.

Daga nan ya yi Sallama da Hajiya ya fice daga gidan yana tausayawa wannan yaron da masa addu'ar samun lafiya.

Amma ya ƙudurce a ransa zai faɗawa Mahmud gaskiyar halin da yaron ke ciki, don ga dukkan alamu bai sani ba.

Hajiya kuwa tana ganin tafiyar likitan ta fara tsara yanda zata kori yaron daga gidan ba tare da kowa ya sani ba bare a samu mai bawa ɗanta labari idan ya dawo.

Washegarin ranar tun sassafe ta tashi da shirye-shiryen taron baƙuwarta (Anty Habi) yayarta da zata zo daga Taraba state. Don haka ta yi amfani da damar ta aiki duka ma'aikatanta nesa, yanda zata kori yaron cikin sauƙi.

Hanne kawai ta rage don haka ta ce "Yawwa Hanne zamu yi wani sirri kada ki sake kowa ya ji ko ya ganki a lokacin da kike aiwatar da shirinmu, don ko tun za'a tafi ake shiri ba sai an dawo ba."

Hanne ta ɗaga kai tare da faɗar"Na fahimta aikin sirri ne za'a yi ko?

Eh, yanzu ki je Sashen Son ki tattare duk abinda yake mallakin wannan halittar sannan ki fito da shi a sirrance ki je ki hau abun hawa ku yi nesa sosai da unguwar nan, ta yadda ba zai taɓa gane ta ba bare ya dawo. Kin ji ni koh? Bana son a samu kuskure, ki tabbatar angama da wannan matsalar kafin yaya Habi ta ƙaraso, dama sanduna nake jiran ya samu."

"Haka ne ranki ya daɗe kin ga sai mu gayawa Boss cewar guduwa ya yi ba da sanin kowa ba." cewar Hanne.

Hajiya ta yi murmushi tace "Maza ki je lokaci na tafiya, ki kula bana son a samu kuskure."

Kuɗin abun hawa Hajiya ta miƙa mata sannan ta tsaya don ganin fitowar su.

Cikin zumuɗi Hanne ta nufi sashen tana murnar burinta ya cika.

Duk yanda Hajiya ta faɗa mata haka ta aikata.
Janyo shi ta yi har gaban Hajiya.
Abdul na kuka yana roƙon Hajiya faɗar yake "Don Allah Mama ki temake ni ki banni in rinƙa kwana nan, in yasso da rana in tahi inyo Bara cikin gari in samu abinci amma kat ki kore ni ina son ƙara ganin yayana ina son shi matuƙa."

Hajiya takai ƙololuwar ƙuluwa ta daka mashi tsawa tana faɗar "Yi mun shiru, wato dai so kake ka tona mun asiri a nan unguwar ma kake tunanin yin Bara?

Mai da dubanta ta yi ga Hanne "Zaki fice mun da shi ko sai sun dawo tukunna?"

Ganin yanda ran Hajiya ya ɓaci yasa ta tungume shi ta fita ta ƙofar baya ta tare abun hawa.

Sai da suka yi tafiyar awa ɗaya da kusan rabi a abun hawan, har sai da mai abun hawan ya gaji ya ja ya tsaya tare da faɗar "Malama na gaji da yawo ina zan sauke ki ne wai?"

"Nan ma ya yi ai.' Ta faɗa tana fitowa daga abin hawan fito da Abdul ta yi ta ɗauko masa kayansa ta ajiye masa.

Ta sallami mai abun hawan.
Abdul sai faman kuka yake, dariya ta yi tace "To dodon gidanmu ni na tafi Allah ya kawo wani mai rabon wahalar kamar Boss."

sannan ta taka da ƙafa ta nufi titi don neman wani abun hawan. Ta yi hakan ne don kada a samu wata matsala.

Da dai Abdul ya ga tabbas ta tafi, ga shi gurin shiru-shiru ba kowa, irin bayan garin nan ne ba kowa sai wanda hanya ta biyo da shi.

Ɗaukar kayansa ya yi cikin ƙarfin hali ya matsa gaba, nan ya samu ɗan wani ɗakin langa-langa da gani irin na masu gadi ne ko 'yan ci rani da basu da muhalli.

Don haka ya shige ciki tare da ajiye kayansa ya bazama cikin gari don yin Bara ko ya samu abinci don yunwa yake ji sosai.

@@@@@@@@

Bayan barinsu gidan da kamar awa Uku Anty Habi ta ƙaraso.

Da murna Hajiya ta tare ta tuni ta manta da wani Abdul kowa ya dawo sai shagali ake.

Anty Habi na tsaka da cin abincin taron baƙin da aka mata.
A hankali suka fara jiyo-hayaniya da iface-iface abun sai ƙara daɗuwa yake da kaɗan-kaɗan.

Nan fa hankalin Hajiya ya fara tashi dama gata da ɗan banzan tsoro kuma tana da hawan jini.

Zuwa can aka callara wata ƙara mai Masifar ƙarfi da take barazanar fasa masu dodon kunne......


Hmmm! Tofah readers meke shirin faruwa a gidan Hajiya ne?🤔🤔

Ina Abdul ya nufa, rayuwar Bara zata riƙe shi kuwa?

Waima shin ina labarin Hajiya Hasina da yan uwan Alhaji Munir?

Shi kanshi Alhaji Munir ɗin meke faruwa da shi?🤔🤔

Don samun wadannan amsoshin ku juri bibiyar alƙamin Ummu inteesar don jin ya zata kaya.



Kada ku manta more comment more typing.










UMMU INTEESAR CE😍🥰❤️❤️


*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*


*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*


Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram, whatsapp, telegram, facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number __08109634202__

Kowacce irin haja je gareka zamu tallata ma cikin rahusa insha'allah.

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


PAGE 59-60

Nan fa mutanen dake gidan suka birkice, yaya Habi ta ajiye cokali tana neman guduwa amma ina! Kafin ta gudun abun ya ƙaraso.

A kiɗime Hajiya ta ɗaga kanta don ganin menene ke wannan Masifar ƙarar. Wani curin dunƙulallen abu ne a hankali yake ƙara girma har faɗinsa ya mamaye ilahirin inda yake. Zuwa can kuma ya rabu gida goma.

Hanne da tashin hankali ya korota daga kitchen ta nufo falon, a nan ta tarad da sabon tashin hankali. Amma duk da haka bata yi kuskuren komawa kitchen ba, domin kuwa duk abinda ya koro ɓera har ya faɗa wuta ba ƙaramin abu ba ne.

A hankali waɗannan curin suke mulmulowa sai hayaƙi suke fitarwa ga wasu sautukan Muryar yara iri-iri dake fitowa daga curin. Suka nufo inda yaya Habi, Hajiya da Hanne suka manne waje ɗaya don tsoro..


Wani tsalle yaya Habi ta daka, tana yin sa'ar ƙetare abun ta yi wuf ta faɗa ɗaya daga cikin ɗakunan dake falon ta rufo da makulli tana mayar da ajiyar zuciya.

Hajiya kuwa ganin curin na nufo ta, tun bai ƙaraso gare ta ba hankalinta ya gushe ta fadi a gun kafin ta kai ga suma ta ji wata mummunar murya na faɗar "Kin tsani ganin Musakai a rayuwa koh? To kishirya don kina dab da tsanar kanki." Daga haka aka bushe da matsananciyar dariya mai ƙara birkita birkitacce.

Kafin idonta su ƙarasa rufewa ta hango bayyana wata mummunar halitta a gabanta mai ido ɗaya saman hanci da wani wagegen baki. tsaya faɗa maku munin halittar bata lokaci ne don tafi Abdul muni nesa.

Haka halittar ta ƙarasa ga hajiyar ta rungume ta. A take idon hajiyar ya rufe ruf alamun ta suma.

Hanne kuwa yau taga tashin hankali da bata taɓa ganin irinsa ba. To wai duk me wannan abun ke nufi? Me ya janyo musu wannan masifar? Tana tsaka da wannan tunanin ta ji an sure ta anyi sama da ita.
Waige-waige ta hau yi tana ƙwala ihu amma bata ga abinda ke riƙe da ita ba. Kawai ta ganta a sama.

Can kuma aka makata ga ƙauren ƙofar falo ta faɗo a galabaice.

Zahirin siffar Abdul ce ta bayyana a gabanta, amma wannan ba Abdul bane don ya ninka tsawo da kaurinsa sau biyar.

A haka ya nufota ya shiga yin Ball da ita tun daga ƙofar falon har zuwa harabar gidan.

Sai ihu take amma a banza banda Ƙasimu mai gadi ba mai jinta. Sauran ma'aikatan gidan duk barci suke.
Shima Ƙasimun ashe rabon ya girbi abinda ya shuka ne.

Don haka aljani Mazkud da ya zo a siffar Abdul ya haɗe su gu ɗaya shida Hanne ya ci gaba da wahalar da su har zuwa lokacin da ya tabbatar sun karɓi saƙo sannan ya ɓace yayin da suke jiyo kakkausar muryarsa na faɗar "Sai ku kiyaye gaba, ko wane mai kama da Abdul kuka kuma wulakantawa zamu gamu ne." Daga haks suka ji tsit kamar Muryar bata taɓa wanzuwa a gidan ba..

Ai da gudu suka watse kowa ya nufi maɓoyarsa.

@@@@@@@@@@@@

A bangaren Abdul kuwa haka ya cigaba da yawo cikin gari yana Bara, ko kwano baya da daƙyar aka samu wata mata ta taimaka ta ba shi kwanon. Haka ya yi ta yi, wani lokacin idan mutane suka gan shi su gudu musamman yara. Masu ƙarfin halin cikin mutanen ne ke tsayawa su ba shi haƙuri, masu abin ba shi su bashi.
Idan yamma ta yi ya dawo malaɓarsa ya zauna.

Haka ya ci-gaba da aikatawa tsawon shekara biyu zuwa uku, har wasu daga cikin mutanen yankin suka fara sabawa da shi suna saka shi aiki kamar wanki,wanke-wanke suna biyan shi. Don a lokacin ya kai shekaru 16 a rayuwa.

Ɓangaren Mahmud kuwa har zuwa lokacin yana waccan ƙasar bai san halin da ake ciki ba. Don kuwa tun bayan fitar Likitansu daga gidan ya samu kiran gaggawa zuwa ƙasar Turkiyya, wannan dalilin ne ya mantar da shi kudurinsa na sanar da Mahmud halin da ya samu Abdul ciki.
Shiko Mahmud duk sanda zai kira Hajiya sai ya nemi ta haɗa shi da Abdul su gaisa amma sai ta samu karyar data masa. Daga ƙarshe ma tace masa ta maida yaron boarding school ne. Sosai ya ji daɗin ganin Hajiyarsa ta karɓi yaron. Bai san cewa ta ɗinke shi a bai-bai ba ne.

@@@@@####

A gidan Hajiya bayan ƙura ta lafa yaya Habi ta buɗe ɗakin ta fito. Nan ta samu Hajiya a some, kinkimarta suka yi zuwa asibiti. Sai da likitoci suka kwashe tsayin wasu awanni a kanta kafin ta dawo hayyacinta, amma jininta ya hau sosai.
Kuma tun tashinta take jin ƙafarta ɗaya wani iri. Sosai ƙafar ke ciwo, likitoci sun yi iya ƙoƙarinsu ba su gano komai ba. Daga ƙarshe suka yi tunanin ko hawan jinin ne ya taɓa ƙafar don haka suka ɗora ta akan magani.

Tun a lokacin Hajiya ke fama da matsanancin ciwon ƙafa, anyi maganin har an gaji.

Bayan dawowar su gida yaya Habi ke tambayar musabbabin wannan tashin hankalin.
Cikin damuwa Hajiya ta dube ta tace "Wani nakasasshen yaro ne Son ya zo da shi nan gidan, da zai tafi ya ban amanarsa, shine na saka aka jefar da shi. Dalilin haka aljanu suka zo mana a siffarsa suka tsorata mu don ɗaukar masa fansa. Wannan shine tunani na."

Girgiza kai yaya Habi ta yi tace "Meyasa kika kore shi?"

"Halittarsa nake tsoro, don wannan bai yi kama da mutane ba,rabin fuskarsa fa a shafe take."

Zaro ido ta yi tare da nisawa ta ce "Tab! Wannan yaron sai kace yaron da Zulaihar Baba ta haifa? Kinsan lokacin da ni aka je Sokoto suna, amma a ƙagare na yi sati ɗayan ni da na je da zimmar zaman jego."

Ita ma Hajiyar fiddo ido ta yi tace "Yaya dama ƙanwata da nafi so kalar abinda ta haifa kenan shine baku sanar mun ba? Kin san fa lokacin Alhaji yana ciwon ajali shiyasa ban je ba. Amma kuka ce mana yaron kyakkyawa ne kuma yana ƙalau?"

Shiru yaya Habi ta yi kamar ba ita aka tambaya ba.

Nisawa ta yi ta ce "Allah sarki ƙanwata mai yawan sona, kin mun rana, kin zame mun lema a lokacin da rayuwata ta shiga wani yanayin ƙunci. Ina ma ace a lokacin da kika mutu na san wannan, da duk tsanata da Musakai sai na riƙi wannan yaron naki hannu biyu na masa gata, da ban wulaƙanta ko da mai irin siffarsa ba..."

Ta faɗa tana hawaye.

"Allah ya jikanki da Rahama ƙanwata. Na miki alƙawarin zan je har Sokoto don karɓo yaronki daga hannun dangin ubansa, ba wanda zan bari ya wulakanta jinina. Ko waye kuwa ya yi kuskuren aikatawa sai na yi Shari'a da shi."

Haka ta yi ta sambatu har sai da yaya Habi ta dakatar da ita da faɗar "Ya isa haka, haƙuri zaki yi, ki ci gaba da masu addu'a."

@@@@@@@@@@@@@@

Bayan kamar watanni bakwai da wannan maganar Hajiya ta shirya zuwa Sokoto don karɓo yaronta.

A da taso ta bari har ta ji damar ƙafa, amma da taga ba alamun haka, ta ce "Ina amfanin baɗi ba rai?" Gwanda ta je tun lokacin da take da abun yi.

A ranar wata Assabar Hajiya tare da wani kawunsu (dake zaune a nan Kaduna) suka yiwa Birnin shehu dirar mikiya.....


To fah! Readers Hajiya na neman yaronta, wanda ta wulakanta fa waye?

Ya zasu kwashe tsakaninta da a halin Alh Munir dama Hajiya Hasina?

Ya rayuwa Abdul zata ci gaba da wakana?.

Ku biyo alƙalamin Ummu inteesar don ji ya zata kaya.



More comment more typing



Ummu inteesar ce.❤️😍
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment