Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

*GODIYA* Ina ƙara miƙa godiya ta ga Allah madaukakin sarki wanda ya bani da ma da ikon sake zo maku da wannan ƙayataccen labarin, cikin hikimarsa da iyawarsa ya aramn damar dasa alkamina domin na yi nuni tare da ishara ga wani abun da ba dai-dai ba.

Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu (s.a.w) haka ga sahabbansa da iyalan gidansa.

*GARGAƊI* Wannan labarin gaba ɗayansa ƙirƙira ne, na kuma samar dashi ne don yin nuni tare da faɗakarwa akan wasu mutane masu irin halayyar da zata zo a labarin, idan hakan ya yi dai-dai da rayuwarka/rayuwarki, to hasashe ne kawai.


DEDICATED TO: ALL MEMBERS OF AREWA WRITERS ASSOCIATION
Ina fatan Allah ya ƙara haɗe kanmu, much love🥰🥰


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

*Page 1-2*

Da misalin karfe 7 na safiyar ranar talata wata daleliyar mota ce ke sharara gudu akan titi, yayin da wata motar 'yan daba ke binsu a baya da alama hari suka kawo masu.

Tuƙi yake hankalinsa a tashe yayin da yake hangensu ta jikin madubin gefen motar, sai gudu yake shararawa kamar ba gobe, fatarsa shine ya isa makarantarsu yaron ya sauke shi lafiya, idan ya so ko miye shi ya faru akansa, amma ya na so ya kare rayuwar ɗan talikin yaron nan.

Gudun kawai yake yayin da hankalin ƙaramin yaron da ke zaune bayan motar [wanda ba zai wuce 11 – 12 years ba ] yay matukar tashi.
Abdul ya ja nakasasshiyar ƙafarsa tare da juyawa baya ya na hangensu ta cikin glass da idonsa wanda ya kasance kwaya ɗaya jal.
Ganin baƙar motar na cigaba da biyo su ya sanya ya juyo cike da firgici; ya buɗi bakinsa da ya kasance rabi, ya ce ‘’Dan Allah baba direba ka ƙara sauri, in sunka kama mu kashe mu za su yi.’’
Ya faɗa cikin muryarsa da bata fita dai-dai, saboda tawayar dake ga halittar bakinsa.
Idonsa kuwa sai tsiyayar da hawaye yake.
Nan fa hankalin baba direba ya kai ƙololuwa gun tashi.
A dai-dai lokacin ne kuma suka iso Abuja Road,titin da ya kasance tsit,saboda rashin hayaniyarsa.
Anan suka yi yunƙurin shiga gabansa da motarsu, har ma motarsu tana zozar tasa.

Cikin zafin nama Baba Direba ya ture motarsu tare da shammatarsu ya zubawa motarsa speed, kafin su ankara ya kai ƙarshen titin.
Ganin hakan yasa suka karo gudu, ba su kuma haɗuwa ba sai a round ɗin da zai sadaka da (Government house) gidan gwamnati na jihar Sokoto.

Saboda haka sai suka daina gudun, suna dai bin shi baya a hankali, kasancewar gun babbar hanya ce suna gudun jama'a su ankara da nufinsu.

Shi kuwa Baba Direba ya na ganin ya samu dama, sai ya miƙe hanya samɓal ta kan babban titi, su kuwa sai suka kewaya ta ɗaya hanyar, da zimmar su haɗu da shi ta hanyar da bata da hayaniya sosai don su samu damar sace yaron cikin sauƙi.

Da wannan damar Baba Direba ya yi amfani ya ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali har ya isa *Abdulrashid Adisa Raji special school sokoto* ya sauke yaron.

¥¥¥¥¥¥¥¥
'yan daban kuwa, da suka tabbatar sun rasa shi, sai suka nemi guri suka faka motarsu.

Ogansu ne ya fito ya na neman wani layi a wayarsa, ringing biyu ana uku aka ɗaga kiran.

A can bangaren Kulu mai adashen sharri ce ta ɗaga wayar ta na masa kirari da cewa "An gaida Gumush, sannu sikelatu mai magana ƙahwahu masu tahiya da kansu, ka ga hitilar sheri, koy-yada ka ya yadama kai nai hitina, ga ka ranke-ranke amma sherinka ya hika yawa, yaya aiki ya yi kyau dai koh." Ta ƙarashe zancen da tambaya.

Shi kuwa Gumush tunda ta fara masa kirari, yake hura hanci, sai da ta dasa aya, sannan ya ce "Hajjiya an samu matsala, wallahi Direban nan shegen gudu ga rai, amma kat ki damu na rantse da takobina *Zarta* nan gaba bai isa ya hana mu ɗaukar yaron nan ba."

Wani uban tsaki mai adashen sharri ta ja, sannan ta ce "Amma wallahi ka ba ni kunya Gumush, ganin ƙwarewarka da can-cantarka yassa nit baka wanga aiki, amma shina kaka hwaɗamin wai an samu matsala?"

Cikin rangaji irin na 'yan maye ya ce "Ya isheki hwa to, ni dai yanzu ki hwaɗamin inda zan cimmiki in kai miki motakki, ki bamu 'yan canjinmu mu ware."

Wata uwar ashar ta lailayo ta ce "Kutuma! Kama raina ma kanka hankali wallahi, har ma wasu kuɗɗi kaka magana bayan ka ɓata muna plan?"

"Haba dai Hajjiya! Ke san dai dole ki bada na chaji, saboda wagga wahala da mun ka sha ni da yarana bai yiwuwa ta tashi ga banza."
Ya faɗa cikin Muryar 'yan ƙwaya da alama ya yi mankas ne, duk suma sauran yaransa a make suke.

Akan haushi bata samu damar sake cewa komai ba, kwatance kawai ta musu ta kashe wayarta ta na tunanin yanzu me zata gayawa Hajiya?

Cikin motar suka koma ɗaya daga cikin yaran ya ja motar suka nufi gun da ta kwatanta masu.

Ƙarfe ɗaya da rabi na rana aka tashi yara daga makaranta dama can Baba direba tun ƙarfe ɗaya ya nufi makarantar, don haka koda yara suka turo Abdul akan keken guragunsa sun tarar da Baba Direba a gate ya na jira, buɗe motar yayi ya sunkuci yaron ya saka shi a ciki, sannan ya juya ya ɗauke keken ya saka a Boot ɗin motar, ya kewaya ya shiga ya ja sai Sama-road unguwarsu Abdul ɗin kenan.

%%¥¥¥¥¥¥

Wata mata ce wacce ba za ta haura shekaru talatin da bakwai zuwa da takwas ba, zaune take akan kujerar falo ta miƙe ƙafarta akan table dake gabanta, sai kallon makekiyar screen tvn dake manne a bangon ɗakin take, gefe ɗaya kuma ga juice a gabanta tana kurɓa, hankalinta kwance, kallo ɗaya zaka mata ka fahimci tana cikin nishaɗi, don kuwa murmushi ne kwance akan fuskarta.

Turo ƙofar falon da aka yi ne ya dawo da ita daga duniyar nishaɗin da ta afka.

Zumɓur ta miƙe ganin Baba Direba ne ya turowa Abdul kekensa suka shigo falon, nan da nan fuskarta ta bayyanar da mamaki ƙarara ga kuma tsabar ɓacin rai kwance akan fuskarta, me hakan ke nufi? Ya ta ga Abdul anan ita dake zaman jiran gawarsa?

Baba direba ne ya tsinke mata tunani da cewa "Hajiya Barka da rana, ya gida?"

A hargitse ta juyo cikin murmushin yaƙe ta ce "Alhamdulillah! hak-kun dawo?"

"Eh, Hajiya." Ya bata amsa.

Murmushin yaƙe ta yi a karo na biyu ta ce "Sannunku da zuwa kun sha hanya, in ce dai babu wani abu da yas-same ku a hanyar tafiyarku da dawowarku?"

Ta ƙarashe zancen a lokacin da ta isa gaban Abdul ta tura kekensa zuwa tsakiyar falon.

Baba Direba ya ce "Babu komi Hajjiya, ƙila wani mummunan abu ya tashi hwaruwa, amma da yake Allah ya na kare salihan bayinsa waɗanda basu da haƙƙi a kansu, sai gashi mun dawo lahiya."

A firgice ta juyo ta kalle shi domin a zatonta ko ya gano shirinta ne, kun san an ce mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi.

Murmushi kawai Baba direba ya yi ya juya ya koma bakin aikinsa, zuciyarsa na masa saƙe-saƙe akan uwar ɗakinsa Hajiya Haseena.

Ita kuwa tura keken da yaron ke kai ta yi zuwa ɗakinsa, ta na buɗe ƙofa ta wawwaiga ta ga ba kowa, kawai sai ta ta tura keken da ƙarfi, ta juya abinta cike da jin zafi da raɗaɗin abinda ƙawarta Kulu ta mata.

Keken kuwa sai da ta haɗu da jikin gadonsa sannan ta tsaya sakamakon to kare tan da gadon ya yi, bawan Allah Abdul kuwa tuni ya faɗo ƙasa ji kake tim! Kansa ya ƙumu a ƙasa.

Ba ya da wani ƙarfi ko kuzarin da zai iya miƙewa da kansa, kasancewarsa gurgu wanda ƙafarsa take a lanƙwashe, gashi tun asali shi ba lafiyayye ba ne, hakan ta saka ya kasa tashi daga gun, ya na nan kwance sai kuka yake shi kaɗai, gashi kuma Mamma ta rufe ƙofar ɗakin bare wani ya hango shi ya zo ya taimake shi.

Ko da yake ba mai shigowa cikin falon nasu kai tsaye sai Abbunsa kuma yanzu ya tabbatar ya na kasuwa, saboda haka ya ci gaba da kukansa tare da yunƙurin taimakon kansa da kansa.

¥¥¥¥¥¥¥
Hajiya Haseena kuwa ta na shiga ɗakinta kai tsaye gun da wayarta take ta nufa, cikin fushi ta kira layin ƙawarta Kulu mai adashen sharri, sai dai har kiran ya tsinke bata ɗaga ba, kira biyar ta jera mata amma ba'a ɗaga ko ɗaya bs, a zuciye ta ajiye wayar ta koma kan gadonta ta kwanta ta na famar jijjiga ƙafa tare da ƙissima irin rashin mutuncin da za ta yiwa ƙawar tata, a ranta ta ce "Lallai Kulu ke raina ni, ni zaki yiwa haka?"

A bangaren mai adashen sharri kuwa, ba komai ne ya hana ta ɗaga wayar ba, sai tsoro da fargaba da suka gama mamaye ta, tasan yanda Hajiya ta ɗau zafi a maganar nan, ga shi ta yiwa hajiyar alƙawarin yau za'a gama da wannan matsalar, amma sai ga shi wancan banzan ya rosa masu plan, tun bayan da ya kawo mata motar ya juya take son ta kira Hajiya Haseena a waya amma ta kasa, sai ga shi yanzu ta kira, tabbas kuwa yaron ya koma gida shiyasa take nemanta, ta na ɗaga wayar kuwa tasan kan zancen shiyasa ta ƙi ɗagawa a nufinta bari zata yi sai hajiyar ta huce sannan ta kira ta ta lallashe ta.....


Tofah! Readers ku dagajin wannan labarin kunsan akwai sarƙaƙiya acikinsa.

Shin ya matsayin Hajiya Haseena ya ke agun Abdul?

Ina mahaifinsa?

Wace rayuwa yake fuskanta a cikin gidansu?

Shin wace iriyar halitta ce wannan ga Abdul?

Don cin cigaban wannan labarin ku biyo alƙalamin Ruky don jin ya za'a ƙare.

Adadin Comment naku shi zai bani damar ci gaba ko akasin haka.

Follow me on wattpad @ummu inteesar



Vote share Comment

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*



________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*


Page 2-3

Hakan aka yi sai da yamma liƙis, sannan Kulu ta kira hajiya ta rarrashe ta sosai tare da bata haƙuri, ta kuma yi mata alkawarin za ta sake sabon shiri, kuma Insha'allah a shirinta na gaba sai sun yi nasarar sace Abdul, su nisanta shi daga gidan babansa har abada.

Ba laifi ta yi nasarar shawo kan hajiyar, amma sai hajiyar ta ce mata ‘’na ji batunki kulu, amma kin sanni sarai ban son wasa ga lamarina, ba gidan ubanai ɗai ba, so ni kai a nisanta shi da duniya gaba ɗai, na tsani ganin yaron nan tsoron huskatai ma ni kai, baƙin nakasasshe, ya shiga tsakanina da burina da yasshigo da ni gidan Alhaji, don haka dole a kau da shi.’’
Tana dire zancenta Kulu ta ja dogon numfashi ta ce ‘’Hajjiya in har za ki ɗoki shawarata kak-ki sa a kashe Abdul, don ko in har an ka gaya mutu haka kwatsam, dole Alhaji ko danginai su zarge ki, amma ke ga in har ɓacewa ya yi basu san duniyar da ya shiga ba, dole zuwa wani lokaci su hanƙura da shi, kuma kahin Alhaji ya mutu sai kisa a biɗo miki Abdul a kashe shi, daccan, sai a kawo gawatai a ce wani gari aka tsinto gawar.’’

Ta na dasa aya hajiya Haseena ta ƙyalƙyace da dariyar mugunta ta ce ‘’Kai amma shiyassa ni ka sonki abokkiyata ke san kan tsiya da sheri, shiyasa sunan mai adashen sheri ya dace dake.’’
Dukansu dariya suka saka a tare, a ran kulu ta ce ‘’Har akwai wata muguwa, 'yar sheri bayanki haseena?, ke da kike neman ran karamin yaro bawan Allah nakasasshe ma baki bari ba,ina gani in na sabawa umurninki?.

Sai da Haseena ta yi dariya mai isar ta, har ta buɗi baki za ta kuma cewa wani abu, ta jiyo sallamar Alhaji ya na shigowa ɗakin, da sauri ta katse kiran ba tare da ta tsaya yiwa Kulu sallama ba.

Da fara'arta ta nufi Alhajin tana Faɗar ‘’Sannu da dawowa alhajina.’’
Yawwa sannu da gida hajjiya, ya yaron na ki fatan yana lafiya?.

Ai ji ta yi kamar ya caka mata wuka a ƙahon zuci, can cikin ranta ta ce’’ Yaronka dai, amma ni wannan nakasasshen ba ɗana ba ne, Allah ma ya sawwake na haifi nakasasshe.’’ Amma a fili sai ta ce ‘’Yana nan lahiya, tun ɗazu ma ya dawo makaranta.’’
‘’Madallah." Alhajin ya faɗa ya na nufar hanyar ɗakin Abdul ɗin.
Saurin shan gabansa ta yi tana fadar ‘’Alhaji ina ka yi ko hutawa baka yi ba?.’’

Da murmushi a fuskarsa ya bata amsa da cewa ‘’Zuwa zan yi inga amanata, ke san shi ɗai gare ni duniya yanzu, kuma kafin mutuwar mahaihiyartai sai da ta bammin amana tai,shine kuma wasiyyarta ta ƙarshe da tabammin, ta roke ni na zaɓa mai uwa ta gari bayan ranta, shiyassa nid-daɗe banyi aure ba, sai da nissame ki, na tabbatat kina da amana kuma za ki iya.’’

Murmushin yaƙe ta yi ta ce ‘’Hakane alhajins ai ɗa na kowana,don ba'a san mai cin unhwaninai ba, yanzu dai zauna ka huta bari na kira maka ɗan Baban, dannan sai in kawo ma abinci."

Ta yi haka ne don ta hana Alhajin sanin abinda take aikata ma ɗan nasa bayan idonsa, domin muddin ya je ɗakin nan yanzu, asirinta zai iya tonuwa.

Zama yayi kan kujera ya na murmushi, ya na jin dadin yadda Haseena ke kula masa da yaron da yafi so akan komai a rayuwarsa.

Ita kuwa wucewa ta yi,zuciyarta na soya, wannan na ɗaya daga cikin abinda yasa ta ƙara tsanar Abdul, saboda Alhaji ya fi muhimmanta shi akan komai na rayuwarsa, da alama sanda uwarsa na raye ta na da babban matsayi a zuciyar Alhajin shiyasa.

Ko da ta shiga ɗakin Abdul na zaune kan kekensa har ya yi barcin wuya, don tun lokacin da ta fita ɗakin bata kuma waiwayo shi ba sai yanzu, bare yasa ran za'a kawo masa abinci, da yake ya saba da horon yunwa, shiyasa da ya samu daƙyar ya miƙe ya hau kekensa, ya je ma'ajiyarsa, ya ɗauko biscuit da nutri-milk ya sha, shine har ya samu damar yin wannan barcin.

Hakika da hajiyar tasan da wannan ma'ajiyar ta Abdul, da tuni ta yashe shi, amma da yake yaron mai wayo ne bai bari ta sani ba, tunda yasan bata son shi.

Fuskarsa ta kalla, cikin hanzari ta kawar da kanta ta na runtse ido da ƙarfi, hakika siffar wannan yaron ita ce siffar ɗan Adam mafi muni da ta taɓa gani a rayuwarta. Rabin fuskarsa a shafe take sumul bako alamar yankan ido ɗaya ko hanci da baki a gefen fuskar na hagu, a bangren dama ne kawai yake da ido ɗaya,rabin hanci, rabin baki.

Saurin kauda tunanin halittarsa ta yi daga ranta, domin ya na gaf da ɗarsa mata tausayinsa a ranta ga shi bata fatan haka, acewarta ɗan kishiya ba ɗa ba ne, ɗan kunama ne, ka sake ka goyasa to tabbas zai harbe ka a baya.

Rangwashi ta zuba masa a tsakiyar kai, firgigit ya farka daga barcin, har ya buɗi baki zai zunduma ihu, ta yi saurin rufe masa baki ta na Faɗar ‘’Karka muri inji shegiyar muryan nan taka, Babanka na falo karka yarda ya gano baka ci abinci ba ko na maka wani abu, in ba haka ba wallahi sai na kusan yanke ka, cikin gidan ga in yat hita.’’

Ta na gama faɗa ta tura keken Abdul zuwa falon ta na murmushi.

Ko da suka fito Alhaji ya na zaune ya na jiransu dama.

Kallon Abdul ta yi yayin da suka kusa ƙarasowa gun babansa, ta ce ‘’Abdul ɗana ga Babanka ya dawo, ko ka na yammin abinda ya kawo maka.’’ Ta ƙarashe zancen ta na masa murmushi.

Shi dai Abdul bai ce komai ba, tsoro ne fal aransa, domin ya na tsoron Mamma bada wasa ba, saboda shi kaɗai yasan irin uƙubar da ya ke sha hannunta, Abbunsa bai san cewa kura ce da fatar damisa ba, shiyasa kullum yake yabon ta.


Alhajin ne ya ce ‘’Iso gare ni ɗana.’’

Dai-dai lokacin ne kuma suka iso daf da Alhajin, ya jan yo shi a jikinsa ya rungume shi.

Har ya buɗi baki zai yiwa ɗansa Magana, suka jiyo sallama a ƙofar falon.

‘’shigo shine kaɗai abinda Alhajin ya ce, kasancewar ya riga ya ɗau muryar mai sallamar.

Yayansa sunusi ne ya shigo falon tare da neman guri kan ɗaya daga cikin kujerun falon, ya zauna.

Gaisawa suka yi da hajiyar, sannan ta juya ciki don kawo musa abinci.

Sosai suka gaisa da ƙanin nasa, sannan ya kalli Abdul ya ce ‘’Ɗana taho nan, taho ka gani ga alewa na kawo ma.’’

Ya faɗa ya na ciro wata bakar leda daga aljihun rigarsa.

Ba musu yaron ya zo cikin hanzari ya karɓi ledar daga hannun Alhaji Sunusi, sai dai bai sha ba, ya riƙe ta dai a hannunsa ya na dariyar murna.

‘’Ka sha alewarka ɗana.’’ Alhaji Sunusin ya faɗa.

Yaron ya ce ‘’Sha zan yi ai Baba.’’

Har ya buɗe ledar ya dauko alawar zai buɗe ya sha kenan, ya jiyo muryar Abbunsa na Faɗar ‘’Ɗan Baba ajiye alewar nan sai mun ci abinci sannan ka sha ka ji.’

Ba musu ya mayar da alawar cikin ledar da ta fito.

Shi kuwa alhaji sanusi tun lokacin da Abdul ya ciro alawar daga leda yake zuba murmushin mugunta, jira kawai yake ya ga yaron ya sha alawar har ya hango kabarin Abdul ɗin, kwatsam sai gashi Alhaji ya hana masa sha, ba ƙaramin haushin ƙanen nasa ya ji a ransa ba.

Kallon ƙanin nasa ya yi ya ce "Da ma maganat kasuwancinmu ta tak-kawo ni, muna so za'a yi sabuwar oda, ya ya za'a yi kenan? don kuɗin hannunmu ya yi ƙaranci."

Murmushi Alhaji Munir ya yi ya kalli yayansa ya ce "Karka damu yaya, an jima zan shigo gida sai mu haɗu can mu yi manat."

To kawai ya ce, ya miƙewa ya na Faɗar "Ni zan tahi, Abdul yaron kirki ka tabbatar ka sha alewarka bayan gama cin abincin ka ji."

Daga haka ya juya, juyin duniyar nan Alhaji Munir ya yi yayansa ya tsaya ya ci abinci, amma ya ƙi, acewarsa ya na sauri ne.

Ficewa ya yi aransa ya na Faɗar "Ga abinda nake so nan ka hanani ci, sai wani abincin banza zaka ba ni?, ka ga shege mai ɗan banzan wayon tsiya duk lokacin da muka yi yunƙurin kashe ɗan neman yaronga sai ka ga kamar ana hwaɗa mai."

Daga haka ya bar gidan gaba ɗaya, sai da ya yi nisa da gidan ya fita layin gaba ɗaya sannan ya faka motarsa gefe, tare da janyo wayarsa ya kira yayansa Sani ya shaida masa abinda ya faru.

Buɗar bakin sani sai cewa ya yi ".......




RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*



________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

Page 5-6


Buɗar bakin Sani sai cewa ya yi ‘’Ka ga shegen mutum koh?, to ko ya ƙi ko ya so sai mun ga bayansa shi da wannan mummunan ɗan nasa.’’
Huci ya yi, sannan ya rufe zancensa da cewa ‘’Mu haɗu gida anjima da dare, sai mu tattauna maganar tare dasu yaya Bily don ko bata taɓa saɓuwa bindiga a ruwa.’’ Ya na gama faɗa ya kashe wayarsa a hasale, da alama shi yafi sunusi saurin zuciya da ɗaukar abinda ya faru da zafi.

Alhaji sunusi na ganin ɗan uwansa ya sauka a layi, kawai sai ya juya cike da baƙin ciki ya hau motarsa ya wuce, amma ya ɗau alwashin sai ya ga bayan ɗan uwansa Munir da ɗansa kwaya daya jal a duniya, domin kuwa su suka fi dacewa da cin gadon wannan dukiyar ba wannan nakasasshen ba.

A can gidan Alhaji Munir kuwa, bayan sun gama cin abinci shi da ɗansa, sai ya tashi ya shiga ɗakinsa don hutawa, bayan ya kai Abdul ɗakinsa ya ba shi tsarabar da ya zo masa da ita.

Bayan fitarsa ne Abdul ya fiddo alawarsa da wan mahaifinsa ya kawo masa da zimmar zai sha, kawai sai ya ji kamar an fisge alawar daga hannunsa an yi jifa da ita ƙasa.
Akan dole ya haƙura, domin ka'idarsa ne da abu ya faɗi ƙasa haƙura yake da sha ko cinsa, ba don komai ba, sai don baya iya durƙusawa ya ɗauko shi.

Faruwar hakan ke da wuya Abdul ya gyaɗa kansa alamar rashin damuwa, ya buɗe ledar da Abbunsa ya kawo masa ya ciro ice-cream ɗinsa ya na sha.

Da dare Alhaji Munir ya shirya ya hau motarsa ya nufi unguwar miyatti Allah, da yake a can gidan iyayensa yake.

Ko da ya je gidan ya tarad da sauran yayyensa su biyar a gidan, kasancewar kusan wannan lokacin shine lokacin zuwan kowannensu gida domin su gaida mahaifiyarsu.

Bayan sun gaisa da hajiya Inna ne, ya fito tsakar gidan ya samu yayyensa suka ƙara gaisawa cikin mutunta juna da nuna ƙaunar junansu.

A nan ya kalli Alhaji Sunusi ya ce ‘’Yawwa yaya Sunusi, ɗazu ka je da magana na ce ka bari sai mun haɗu gida koh?."
Ya fada da sakin fuska.

Sunusi ya kalle shi fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce ‘’Hakane, mu je waje mu yi maganar.’’
Alhaji Munir ya shiga gaba, Alhaji Sunusi na binsa a baya, ya na masa wani kallo mai cike da tsana, a ransa ya ce ‘’Na tsane ka Munir, me yasa duk wani buri nawa da duk abinda nake so kai Allah ya tattara ya bawa?, dole sai mun ga bayanka, bari dai mu gama da wannan ƙaramin ƙwaron.’’
Haka ya ci gaba da sake-sake da zancen zucinsa, har suka isa wajen suka nemi guri suka zauna don tattauna maganar.

Bayan ya gama shiryawa Alhaji Munir zance, suka ajiye Magana akan gobe ya je ya same sa a inda yake siyar da motoci, don karɓar wasu daga cikin kuɗaɗen.
Daga nan suka miƙe, Sunusi ya je ya tarar da sauran yayyensa kuma abokanan makircinsa suka ci gaba da ƙulle-ƙullensu na yanda za su yi nasarar hallaka ƙanin nasu tare da ɗansa domin su mallaki dukiyarsa, yayinda Alhaji Munir ya je ya tarar da yaya Mizbahu suka ci gaba da hirar zumuncinsu, da yake shi Mizbahun kwata-kwata ba halinsu ɗaya da sauran 'yan uwansa ba, shi kam ya'na son ƙaninsa Munir da zuciya ɗaya, sabanin yayyensa da suke zaune da Munir ɗin da biyu.

Da misalin ƙarfe tara da rabi na dare suka watse, ko wannensu ya nufi gidansa, amma shi Alhaji Sunusi ya tafi da tunanin ko Abdul ya sha alawar? Shin ya mutu ko yana raye?

A haka ya ƙarasa gidansa cike da jiran tsammanin ganin wayar ɗan uwansa domin ya shaida masa labarin mutuwar ɗan nasa.

¥¥¥¥¥¥¥¥

Bayan kwana biyu, Hajiya Haseena ce zaune a falo ta na ta famar tunani, to me Kulu ke nufi, kar dai ta manta da zancensu?, ta ji shiru har yanzu, hakurinta ya kusa ƙarewa, ita fa ta tsani wannan yaron kamar yanda ta tsani mutuwarta, shi yasa take jin daɗin rashin haihuwarta a gidan nan har yanzu, domin bata so ta haifi ɗan da zai kalli wannan nakasasshen ya ce masa yaya, ta fi son sai ta ɓatar da shi sa'annan ta zuba tata zuri'ar, yanda za su mori dukiyar da kyau.

Ganin wannan ba zai fitar da ita ba, ya saka ta ɗaga waya ta kira Kulu mai adashen sharri.

Bayan sun gaisa ta ke cewa ‘’Wai Abbukiyata mi kika nuhi halam?, kwana biyu na ji shiru bayan kesan na riga na biya kuɗɗin wanga aikin, to in baki iyawa na, ki dawo min da kudɗaɗena, in biɗi wanda ka iyawa.’’

Ta na gama faɗa ta kashe wayarta, ba tare da ta jira cewar Kulun ba.

Har za ta shige ɗakinta ta jiyo sallama a ƙofar falon, juyowa ta yi ta na faɗar "Wa'alaikumus salam, shigo."

Yayarta

Please Login or Register in order to submit comment