Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gasu nan,

Abban amal bazai iya musawa abban afham ba amma baason ransa ya aminceba,
Anan abban afham yazare kudin sadaki, kamar yadda addina yatanada yabawa mahaifin amal,

Mahaifin amal yace abari yafita waje yakira koda limaman unguwane,

Abban afham ya amince da hakan,
Mahaifin amal yafita yaje yakira limaman unguwa da dattjiwan unguwa suka fita a harabar gidan su amal anan aka dauka auren AFHAM DA AMAL..

Na:-?Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[7:49PM, 5/12/2016] Mr, Smiles??: [7:56PM, 5/10/2016]
????Amanar aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??75 and 76??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Bayan angama daurin auren, abban amal yacewa abban afham to yanzu ya zaayi maganar kai amarya amal gidanta "

abban afham yace "kowane lokaci suka tashi sukaita domin yasan komai daren dadewa afham zai dawo, abban afham yaci gaba dacewa "zan dafe duk wata kafa tafitar da kudina, tayyada bazai iya fitar da koda sisi bane daga cikin kudina sobada haka idan yaji matsuwar rashin kudi zaidawo"

Abban amal yace "to shikenan ajirashin harya dawo sai a kai masa matarsa"

Abban afham yayi godiya sosai, sannan sukayi sallama ya wuce office dinsa, yau daikam yacika burinsa,
Har bayan yazauna yafara aiki, yatuna dabai gayawa umman afham batun auren ba wayarsa yadauko yakirata yasanar da ita komai dayake faruwa, saida tamsa kuka a wayar,
Ransa yasoma baci da sauri ya kashe wayar,

Aneesah tana zaune a falo tatayar da kanta sama, momy tafito daga cikin dakinta tana hawaye takaraso gurin aneesah,

Ganin da aneesah tamata yasa tatashi zaune tana tambayarta " momy lafiya kuwa "
Momy tace "an daura auren afham da amal, yanzun nan abbanki yakirani yasanar dani"

Aneesha taji gabanta yafadi, kafin tafara magana hawaye suka soma sauka kan kuma tunta tace " taya za a daurawa mutum aure baya gari, wannan wlh amal aka cuta, Allah sarki amal" takarasa maganar tana kuka,

Momy ta katse mata kuka dacewa "kitashi kije kikara afham kiji koda ke zaki samesa, domin ni tun jiya nake kiraan wayarsa a kashe,"

Aneesha ta share hawayenta tace "nima tun dazu nake neman wayata bansan inda na jefa taba"

Momy tace "tashi kishiga dakinki mana kiduba"

Aneesah ta mike tsaye tace "toh momy" tana karasa maganar tanufi dakinta,

Duk saida tayiwa dakin kaca kaca amma bataga wayarba,
Haka ta hakura tabi lafiyar gado ta kwanta domin tagaji, bacci yadauketa zuciyarta cike da tunanin dan uwanta afham

Na:-?Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles??
[7:58PM, 5/10/2016]
????Amanar aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??77 and 78??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Umma da hajna suna gefen hilal, sukaji ya motsa, a hankali yake bude idonsa, har idon yayashe,

Umma ta janyo kujera tadawo kusa dashi tarike hannunsa tace " ya jikin "

hilal yayi nishi yace "yawwa naji sauki"

Hajna takaraso gurin duk ta marairaice jikinta duk yayi sanyi tace " ya hilal ya jiki "
Hilal ya girgiza mata kai,

Umma taci gaba da cewa "nakira iyayen ameelah a waya yanxu haka suna cikin asibitin nan suna dakin da ameelah take"

Hilal yamike tsaye yana tangadi kamar zai fadi, umma tayi saurin rikashi, "ina kuma zakaje kajira kakara samun sauki mana"

Hilal yajanye hannunsa daga rikon da umma tamasa yana nishi yace "ummana kibarni natafi, wani irin zafi nakeji a zuciyata, matukar bnsamu amsar abinda nake zargiba"

Umma takara kallonsa da mamaki tace "dakin ameelah zakaje"

Hilal ya girgixawa umma kai,

Umma tace " to shikenan bari na rika kah muje "

Kama hilal tayi suka fita, hajna tana biye dasu a baya, tausayin hilal takeji matuka a zuciyarta, wace macci ce zata sami irin wannan mijin mai tausayi da nutsuwa amma tabari ya kubuce mata, gaskiya ameelah tacika maciyiya amana, duk a zuci hajna take wannan zancen, jita keyi kamar tatonawa ameelah asiri,
Bbhilal yayan tane taya zata rika bari ana cutar sa, cen kuma wata zuciyar tace itamafa halira sai an tambayeta akan taki fadan gaskiya,

Duk jikin hajna yayi sanyi a lokaci data tuna da wannan zancen lahirar,

Umma ce ta katse mata tunani dacewa "budemun kofar nan" a lokacin da suka kawo bakin kofar shiga dakin da ameelah take ciki,

Hajna tasa hannu ta bude kofar dakin,

Umma na rike da hilal suka karasa cikin dakin,

Yana shiga dakin momyn ameelah datake zaune a gefe tana kuka ta mike tsaye cike da hargowa tace "meya faru da 'ya ta, wa yake wunkurin kashemun ita, hilal kafadamun" takarasa magnar tana kuka,

Hilal yasaukar da murya yace "wlh nima momy bansaniba,"

Momy ta kallesa da mamaki tace "wannan kalmar taka ta bansani ta isheni hakan, a karo na farko, lokacin data fadi cikin dare, haka muka tambayeka meya faru da ita, amma saika furta mana wannan mummunar kalmar taka ta bansaniba, yanzuma haka zaka ce mana", kuka yahana momy karasa maganar,

abban ameelah yana gefe duk ya dau zafi jiyakeyi kamar yakai wa momy duka,

Momy tana shanshekar kuka tadago kai ta kalli hilal tace " wlh zuciyata tafara zarginka akan kaine kake yunkurin kashemun 'ya, meta maka mekake nema gareta" takarsa magan da kuka,

Abba yayi sauri karasawa wurinta yace "wannan wace irin magana ce, da wanne zaiji ciwon matarsa ko masifarki"

Cike da hargowa momy tace "nafada kuma nakara fada ina zarginsa, ta nunawa abba dan yatsa kafin taci gaba dacewa " daman nalura dacewa kaima bakason yarinyar nan, tin kafin tayi aure, meyasa" kuka yakara kubuce mata tasa hannun da toshe bakinta,

Abba yaja nunfashi yace "lallai yau kin tabbatar da cewa ke butuluce, kuma wlh yau kin tabbatar da cewa haukarki maras girma mamawace "

Hilal yafita daga jikin ummansa da tangadi yakaraso gurin momy ya sunkuyar da kansa yace " momy wlh banada abinda nake nema a gurin ameelah, kuma ni meye ribata idan nakashe ameelah"

Hajna tana gefe tana kuka ganin yadda hilal ke kuka tayi saurin karbe maganar dacewa " yaya hilal bakaine kake yunkurin kashe ameelah ba
Ameelah ce take yunkurin kasheka"......

Waiii !!! ?? kuyi hkr hannuna zafi,
Muje zuwa??

Na:-?Rabi 'atu sk mash Da Mr, Smiles??
[10:43PM, 5/13/2016] Mr, Smiles??: ????Amanar aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??79 and 80??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Ameelah ce take yunkurin kasheka,

Duban kowa a dakin yadawo kan hajna,

Momy tayi saurin dago kanta tace " karki shigo cikin maganar mu keme kika sani"

Hajna tashare hawayen tayi taku takaraso kusa da momy tace " ai kuwa ninasan komai, domin kuwa ni yarki take gayawa komai kuma a yanzu zantona mata asiri, nagaji da ganin yadda take cutar dan uwana, zumuncin dake tsakanina da hilal yafi wadda yake, tsakanina da ameelah..,

Hilal yada mata hannu yace "kar inji kinfadi komai anan "

jinkalaman hilal yasa hajna tasaka kuka tana cewa " yaya hilal saidai kayi hkr amma wlh saina fada domin nagaji da daganin yadda ameelah takecin AMANAR AUREN ka, ameelah tana chart da samari a wayarta, tun kafin tayi aure, kuma datayi aure saita kasa dainawa, hatta ranar da aka kai ameelah dakinta har A ranar saida ameelah tayi chart har kusan karfe biyun dare, ta charting Suka hadu da wannan mutumen, wadda tayi save din Number shi da hmm, soyayya sukeyi, kuma ta nunan masa cewa ita ba matar aure bace, shikuwa saurayin yayi matukar kamuwa da sonta,
Wata rana naje gidan ameelah a ranar tasanar dani cewa

Mutum da take tare dashi a chart yanada hadari sosai.

Hajna Tajuya gefen da hilal yake wadda tun alokacin data fara magana ya gazgata ta,

Suka hadu edo ita da hilal taci gaba da cewa "ya hilal idan bazaka mantaba kwana ukku da suka wuce naje gidanka, to aranar ne ameelah tasanar dani komai akan saurayin, domin kuwa shi saurayin yasanar da ita cewa shifa baa yaudararsa kuma duk maccen data yaudaresa to hukuncin kisane akanta,

Aranar nabawa ameelah shawar wari dadama akan tadaina chart da maza, amma taki ji daga karshema cemun tayi, tayi wani sabon saurayi hadande wai ko sunansa AFHAM kuma dan abuja ne..

Hilal ya zare ido?? yana kallon hajna, bakinsa na rawa yace Afham"

Momyn ameelah kuka take sosai tace "wallahi karya take, ameelah bazata iya yin wannan abunba, kazafine take mata"

Zuciyar hilal tadau zafi da karfi yadakawa momy tsawa "ya isah haka,"

Saida momy ta zabura, ganin yanayin edanunsa sunyi ja yasa takame bakinta, jikinta yadau rawa ta tazana sosai, har mamaki tarika yi a zuci "ayya kuwa wannan hilal ne, ba aljannu suka shiga jikin saba

Hawaye tab a edon hilal umma ma haka, hajna tana tsaye, tana kallon hilal habar bakinsan har wani rawa take,

Da karfi hilal yaja jikinsa, yafita waje, umma na kiran sunan sa amma yaji tsayawa,
Dataga baidawo ba, tabi bayansa ita da hajna da abban ameelah,

Dakin da Afham yake ciki ya nufa harya karasa bakin kofa, wasu likitoce da suke tsaye a bakin kofar suka hanashi shiga,

Tsawa ya daka musu saida dayan yafadi, bashiri suka bashi wuri kofar yabude ya shiga dakin...

Na:- ?Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles??
[12:23PM, 5/17/2016] Mr, Smiles??: [12:00PM, 5/16/2016]
????Amanar aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??81 and 82??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Afham yana kwance an kammala masa aiki, edonsa a bude yana kallon kafarsa, kamar zaiyi kuka,

Hilal yashigo dakin, ya isa gurinsa ya shaki wuyansa,

A daidai lokacin su umma da hajna da abban ameelah suka karaso cikin dakin, .

Afham sai kaki yake, hilal kuwa ko a jikinsa, matse wuyan yayi sosai, umma tana kuka takarasa gurinsa tana kokarin firgar hannunsa daga yuwan afham amma tagagara fitarwa,

Abban ameelah yayi saurin karasa gurin ya firge hannun hilal da sauri yasaki wuyan afham, edon afham sun fito sosai, abban ameelah yadaka hilal tsawa "meke damun kane hilal, yazakazo kasami marar lafiya kashakar masa wuya"

Hilal yana kuka yadafe kai wani irin bakin ciki yakeji da baa barshi yayi abinda yasoba,
Cikin kuka yadago kansa yace "abba shine fa "
Cike da mamaki abba yace " shine wah?"

"Shine afham wadda yake soyayyah da ameelah" hilal yafada yana kuka

Afham yana kwance yana matsar wuyansa dake masa ciwo yaji ankira ameelah, da karfi yasaki wuyan yana cewa "eh nine dan Allah ina ameelah nah, wlh danta kawai nazo garin nan, dan Allah kutaimakamun kununamin inda take" yakarasa maganar yana hawayen, zafin son Ameelah yakeji har cikin zuciyarsa,

Gaban abban Ameelah yafadi, sai yanzu ya gazgata maganar hajna " tabbas ameelah tana soyayya da wasu mazan a chart, wannan wace irin masiface take kokarin kunnu kai acikin wannan zamanin namu" duk a zuci abba yake wannan zance,

Hilal yana gefe sai kuka yake, tambayar zuciyarsa yake wane irin hukunci yakama yayanke akan ameelah,

Umma na hawaye takarasa gurin hilal tarikashi, duk zukatansu sundau zafi,
Afham yacika da mamaki, ganin kowa yana hawaye, duk ya firgita, muryarsa na rawa yace " dan Allah ina Ameelah, kodai ta mutu ne,

Hajna tayi karfin hali tana kuka tace " da ace mutuwa tayi da zai fi mata sauke fiye da wannan rayuwar datake ciki"
.
A daidai lokacin hawaye suka gangaro a kan fuskar afham yace "meya faru da ita..."

Cike da hargowa hajna taci gaba da masa magana " ameelah matar aurece, ameelah akwai hijabin aure akanta, ameelah taci AMANAR AURE, kayi gaggawar zuwa kayi istigifari tun kafin Allah ya sauko da masifarsa akanku"

Tunda hajna tafara magana afham yagaga tsayar da kukansa, kuka yajeyi sosai..

Na:-?Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[12:09PM, 5/16/2016]
????Amanar aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??82 and 83??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Afham yana kuka yace "yanzu ameelah matar aurece amma tabarni na fara sonta"

Umma tana kuka tayi saurin katsesa dacewa " tabbas matar aurece, kaga wannan shine mijinta, ta nuna hilal"

Afham yakara fashewa da kuka, nadama ta bayyana a fuskarsa karara yana cewa " kaicona, dana kasa fahimtar iyayena, mesukamun amma nakasa bin umarninsu", jikinsa yafara ja yayi yana yunkurin tashi,

A daidai lokacin likitansa yashigo dakin, yayi sauri zuwa gurin afham ya zaunar dashi yana cewa " ina kuma zakaje, ai kafar taka bata isah takawaba"

Afham ya janye hannunsa daga rikon likitan yace " kabarni naje gurinsa yakarasa kasheni, wlh banga amfanin rayuwata ba" yana nuna hilal da dan yatsa yana kuka,

likitan ya kalli hilal cike da mamaki yana cewa "to ai wannan shine ya kadeka, kuma shiya kawoka asibitin nan a lokacin daya kawoka bakamasan inda kakeba, kakoga da ace yaso kasheka da tuni ya kasheka"

Wani irin kuka mai kara ya kubucewa afham, tabbas yasan wannan ba komai bane face iftila i, ko ince kaddara, yayi nadama sosai akan abinda ya aikatawa iyayensa,

Abban ameelah yagagara yin kuka edonsa suncika da kwallah, da sauri yafita yakoma dakin da ameelah take,

Afham yayi nadama sosai, yaso abarshi yaje gida amma likitan sa yahanashi, tare dacemasa sai yayi kwana ukku kafin yatafi,

Umma taja hilal sukabar dakin da afham yake suka dawo dakin da ameelah take,

ran umma yabace sosai dashigowar su dakin da ameelah take tafara masifa " wlh ameelah kin wahalar da hilal, kin hanashi samun natsuwa a gidan sa, takara daga murya tana cewa "Daman Allah baya hukunta Azzalumi da laifi mai sauki sai wadda yasan baxai iya dauka bah, ta juya gefen hilal, a lokacin yadaina kuka amma zuciyarsa cike da kuna, umma tace " karka kuskura kakara barin ameelah takoma Gidan ka tun kafin ta farfado ka saketah"

Hilal yadago kansa da sauri yace " a a ummana ai baa yanke hukunci cikin bacin rai kibarta tafarka, inason nasan meyasa taci amanata"

umma tayi saurin cewa " wani irin kanaso kasani ai kasani kawai bata sonka ne"

Hilal yamike tsaye yanaji ajikinsa bazai iya sakin ameelah ba, har yanzu yana sonta, "ummana kiyi hkr tafarfado duk wani hukunci daya dace a yanke sai a aiwatar"

Jin kalamansa yasa ran umma yakabace tsaki kawai taja, sannan tajuya takamo hannun hajna sukar dakin, hilal yanata kiran sunanta amma taki saurarensa,

Suna fita daga asibin suka tare napep suka koma gida..

Na:-?Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[7:16PM, 5/23/2016] Mr, Smiles??: [6:43PM, 5/18/2016] Mr, Smiles??: [9:07AM, 5/18/2016]
????Amanar aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??84 and 85??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Koda hilal yafito daga asibitin su umma sunbar gurin, motarsa yashiga jinine kaca kaca, amma ahakan yashigeta yanufi gidan umma,

Koda yakarasa gidan yashiga umma da hajna suna zaune a falo, rankowa a bace yashigo falon yayi sallama, umma ta kyalesa hajna ta amsa,
Kujera mai dubin tasu yazauna yana fuskarta su ya saukar da murya yace " ummana kiyi hkr, nikaina bazan iya zama da ameelah ba amma inasone idan natashi hukuntata akan abinda tamun namata horo mai tsanani, yadanyi jim kafin yacigaba dacewa " sannan kuma cin fuskar zaiyi yawa ace agaban iyayenta zan saketa, dan Allah umma kiyi hkr"
Yana gama maganar yayi shiru,

Umna tayi shiru nakusan minti biyu kafin tajuyo gurin sa tace "shikenan naji zanbarka kazauna da ameelah amma da sharadi,
Umma tayi shiru tana kallon hilal,

Hilal yace "ummana wanne sharadi"

Umma tacigaba dacewa "sharadi na shine, inaso kakara aure, kuma bakowa nakeson ka auraba face kanwarka HAJNA, daman tun farko ita naso ka aura amma kabijiremun kaje ka aure ameeelah"

hajna datake gefen umma kunya tacikata dasauri tatashi da gudu ta wuce daki,

Hilal yace "umma hajna fa kikace, kifa tuna asanadiyarta na hadu da ameelah, kawarfa ameelah ce"

Umma tace "toh kuma aurenta haramun ne eh, ko shikenam dan tana kawarta babu aure a tsakaninku kenan, to bari kaji wannan umarni nake baka ba shawara ba dan haka tashi katafi kuma auren nan banaso ya wuce nan da sati daya,

Hilal yayi matukar girgiza shifa baitaba jin son hajna zuciyarsa ba, taya zai zauna da ita, amma bai musawa umma ba yatashi yatafi,

Hajna tana komawa dakin tadaka tsalle,
Tadanyi ihu kadan yadda umma bazata jiba, cike da jin dadi take magana tana dariya "Allah na godema daka cikamun burina, ashe mafar kina zai zamo gaske" takara daka tsalle, ta fada kan gado, wakar Adamu hassan nagudu tashiga rai raiwa inda yake cewa "Farin ciki yasameni tunda kace kayarda dani, shaukin bege yakamani acikin mata kanai dani, nazama tauraruwa acikin mata nice adon gari" ta kara tallatsa ihu, akan murna harda su hawaye, tana cikin murna kuma saita tuna da ameelah, ta murtuke fuska sai kuma tayi murmushi tace "kawata ameelah, kishiyata ameelah, hmm yanzu za a fara wasar"...

Na:-?Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles??
[9:16AM, 5/18/2016]
????Amanar aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??86 and 87??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

BAYAN KWANA BIYU

Ameelah ta farka, momynta tasanar da ita komai akan hukuncin da hilal yayanke, nacewa yanason yasan dalilin dayasa take cutarsa, ba wani kuka tayiba domin ita gani take bazata taba rasa hilal ba,
**** *****
Acen kuwa gidan su afham, kusan kullum sai aneesah ta nemi wayarta amma ta gagara ganinta,

Yauma tashigo dakinta tana kara dundubawa guraren dabata duba ba, cen sai tatuna da kasan gado, wadda tun ranar data fara neman wayar bata taba tunanin taduba kasan gadoba,

Bakin gadon taje tadauke katifar datake kan gadon, tana daukewa kuwa saiga wayar, cike da jin dadi tasa hannu tadauko,
Har a lokacin wayar tanada chaji, sakon da hilal yaturo taci karo dashi, tafara karantawa, tashin hankali karara ya bayyana a fuskarta,

Dasauri tafita taje tanuna momy, momy tana gani tanufi dakin abba, bayan takai masa ya karanta, cike da bacin rai yace "ba inda zamuje"

Momy tafashe da kuka tana cewa "haba alhaji ni wlh narasa gane wace irin zuciyace dakai, gabaki daya bakada tausayi, yanzu a aiko sakon yaronka yasamu hatsari amma saikace baza ajeba, toni zanje, kabani izini natafi," hawaye tap a idonta takarasa maganar,

"Ni ban baki izinin fitaba koda daga nan xuwa bakin zauren gidan nanne idan kuwa kika fita bada izinina, shikenan kuma kinsan zunubin fitar macce batare da izinin mijintaba" abba yafada yana karasa maganar yafita yabar dakin,

A hankali momy ta sulale tafadi kasan cafet tana kuka, zuciyarta cike da tunanin yaron ta afham,

Tajima tana kuka kafin tatashi tashare hawayenta, takoma dakin aneesah,.itama kuka tasameta tanayi,

Momy takarasa gurinta tace "kishirya gobe muje gombe, wurin afham" takara tambayar aneesah cewa" an rubutu sunan asibitin dayake a cikin text din,

Aneesah tace "eh anturo"
Momy tamike tsaye tace " toshikenan gobe kishirya mutafi" tohm kawai aneesah tace, momy tafita tabar dakin, ...

Na:-?Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles??
[5/18, 1:32 PM] ????Amanar aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??88 and 89??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Acen kuwa bangaren Afham har kwana biyun nan suka cika kullum a matse yake yanaso yakoma gida domin yanemi gafarar iyayensa,

Tun cikin dare yakarbo takardarsa ta sallama, duk da likitansa baiso hakan bah, amma ganin ya matsu yasa yabashi, a cikin daren likitin yatai maka masa yakaisa har hotel dinda yasauka suka kwaso kayansa, sannan ya hadashi da wani driver, motar afham yajayo suka hau hanyar abuja, cikin daren,

Koda gari yawaye su afham sun isah abuja, sai cikin harabar gidan su driver yaja parking,

Yafito yazo yataimakawa afhan yafito, suka nufi cikin gidan,

A bakin kofar shiga yaci karo da abbansa zai fitowa wani irin wawan kallon yamasa, ya murtuke fuska, ya tare gaban afham "ina zakaje"

Hilal ya sunkuye kansa kasa kai tsaye hawaye suka gaggaro kan kuma tunsa"
Yabude bakin zaiyi magana sai kuma, yafasa,
Abban yaci gaba dacewa "karka shigarmun gida kajecen, kazabi wasu iyayen domin ni baka daukeni da daraja ba" nan fa abba yaci gaba da masifa yana hargowa,

Momy da aneesah suna cikin dakin momy suna hada kayan tafiya sukaji hargowar abba a waje, shi suke jira yafita saisu wuce gombe,

Momy tafito da sauri aneesah tabiyo bayan ta,
A daidai lokacin da suka karaso gurin a lokacin abba ya ture afham,

Afham ya tangada yafadi kasa, ai kuwa nan yasaka kara,
Momy tayi saurin karasawa gurinsa, a lokacin yadafe kafarsa yana kuka, momy hawaye take tana taba jikin afham taji duk ya rame ya chanza,

jini sukaga yafara fita a kafar afham, momy ta firgita sosai, dasauri ta koma cikin gida tadauko mayafinta, gurin fitowa saida ta bangeji abba,
Amma bata kulashiba,

diver daya kawo afham tace yatai maka mata, susakashi a mota akwai asibitin guragu anan kusa dasu suje sukaisa a duba kafar,

Nan suka saka afham a mota sukafitar sukabar gidan,

Abba yayi tsaye, duk yaji yanayinsa ba dadi, aneesah tana kusa dashi sai rusa masa ihu take tana kuka,
Sai kuma yafara jin tausayin afham, meye ribar zafin zuciya, babu abinda yake haifarwa face nadama da danasani,

Bashiru yafara jin saukar hawaye a kan fuskarsa, a lokacin ya juyo ya kalli aneesah yace "tashi kishiga ciki kidauko mayafinki mutafi musamesu"
Da gudu aneesah tashiga gida tadauko mayafinta koda tazo harya tada motar nan suka wuce asibinn...

Na:-?Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles??
[8:54PM, 5/20/2016] Mr, Smiles??: ????Amanar aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
?? 90 ??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Koda su abba suka karaso asibitin har likitoci sun karbesa sunshiga bashi taimakon gaggawa,

Momy tana zaune su abba suka shigo, tana ganinsa ta mike tsaye cike da masifa tafara magana " meya kawoka, katafi kabarni dashi nizan iya kula da yarona, bazan bar ruywarsa ta lalace ba" abba ya karaso gurinta jikinsa a sanyaye, ya Bude baki zaiyi kenan likita yafito, momy tabar gurin abba tayi saurin karasawa gurin likita,

Likitan yace "hajiya saidai kuyi hkr, gaskiya daurin da aka masa a kafa yakara kwancewa, saboda haka sai aikin yadawo sabo, dan haka ba aikin gaggawa bane, a kalla zakuyi koda kwana biyarne a nan kafin mubarku kutafi dashi"

Momy tashare hawaye ta tace "likita ba matsala koda wata dayane zanyi idai har dana zai samu lafiya"

Likita yace "insha Allah zai samu lafiya, yanzu bara naje nadauko kayan aiki saimu fara" yana gama fada yawuce,

Abba yana gefe yakaraso gurin momy, momy ta dalla masa harara, abba ya soke kansa yanzu harwani kunyar momy yake, a hankali yadago kansa yace "komai yafaru kaddarace sannan kuma ..."

Momy ta daga masa hannu " banason naji komai daga bakinka yanxu, kajira sai yarona yasamu lafiya" abba yayi shiru,

Nan suka same guri suka zauna,
A ranar asibiti suka kwana, abba yayita tarairayarsu duk abinda sukeso shiyakeyi, yayi nadama sosai, ita kuwa momy tadaure masa fuska, gani take duk abinda yafaru da afham laifin abba ne,

Haka dai suka zauna asibiti suna jinyar afham,

**** ******

Ameelah

Please Login or Register in order to submit comment