Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai kama jikinta ba. Tun
daga nesa suke sakarma da junansu murmushi
mai sanyi. Ta zauna a kujerar dake fuskantarsa,
centre table ne mai bak'in glass a tsakiya wanda
aka d'aura kayan marmari cikin tray kala kala a
cikinsa, irinsu Apple, grapes, banana, orange,
pear da sauransu. Zamewa yayi ya zauna k'asa
gami da rausayar da kai yace.
"Barka da hutu!".
Dariya ya bata sosai saboda yadda yayi
maganar, tace
"Alhamdulillah, muna ta sha kam."
Yayi shiru zuwa wani lokaci sannan yace.
"Zuwa yaushe kike ganin za'a aurar da ke?"
Ita dariya ma ya bata tace
"Aure ay lokaci ne... sai lokaci yayi sannan."
Ya langa6ar da kai yace
"Haka ne, amma ni ko yanzu aka bani ke zan
kar6a hannu bibbiyu, zan nuna maki k'auna ta
ban mamaki, sai dai bansani ba ko ke zaki so ni
kamar yadda nake son ki... sannan ina so idan
Allah ya kaimu zan sanar da iyayenki cewar
aurenki zanyi..."
Ta lumshe idanu cikin wata sabuwar k'auna
dake k'ara mamayarta, ta kuma k'ara lallu6e
mata zuciyarta, tace
"Kar kayi tantama a kaina ya Faruk, soyayyarmu
had'in Allah ce, i respect you and your values..
Faruk d'in da nake so bana ganin kowa sai shi,
bana jin k'aunar kowa sai shi... haka ma banida
buri a yanzu sama da mallakarka a matsayin
mijin aurena na har abada..."
Sai bayan ta furta hakan kuma kunya ta kamata
had'e da mamaki, yadda ta zauna tayi ta zuba
kamar pampo, amma daga baya sai take ganin
kamar su6utar baki tayi. Sai tayi saurin cewa
"Nidai fatana ka rik'e soyayya ta, kada kaci
amanata, ka yarda dani, idan kayi min wannan
to ni kuma nayi maka alk'awarin baka dukkan
kulawa."
Sai ya rasa abin cewa kuma, murmushi tayi ta
sauko k'asa ta shiga yanka masa kayan
marmarin yana sha.
***
Bilki ta soma tsarguwa da yawan zuwan Faruk
cikin gidansu, da yawan ke6ewa da sukeyi shida
Meenah akan Zarah suna fira. Ga wata sabuwar
al'ada da Meenah ta 6ullo da ita na yawan
kwalliya wadda ta gama lura don Faruk take
yinta. Ta gigice ta shiga damuwa sosai, neman
k'arin bayani takeyi tasan Zarah bazata ta6a
fad'a mata ba saboda an ta6o 'yar uwarta haka
bata ganin aibunta, su koda wani abin ne ba'ajin
ta cikinsu kashewa sukeyi su rufe babu mai ji.
Ko fad'a sukayi baya wuce yini d'aya idan kuwa
sun dad'e to kwana d'aya ne sun shirya sun
kuma manta komai. Don haka taga babu mafita
illa ta tunkari Meenah tayi mata bayanin abinda
take zargi.
K'arfe tara na dare ta raka Faruk ya tafi, tana
dawowa ta taradda Mami tsaye gefen gadonta
ta hard'e hanyayyenta wuri d'aya tana huci.
"Mami....?"
Ta dube ta sosai daga sama har k'asa tace
"Amina....!"
Bata amsa ba illa ta dube ta a yadda take
kiranta cikin wata irin murya. Sai kawai ta jeho
mata tambaya
"Meke tsakaninki da Faruk?"
Ta sunkuyar da kanta k'asa, batayi magana ba,
sai da Bilkin ta daka mata uwar tsawa mai gigita
k'wala.
"Bada ke nake magana ba?!"
Cikin sark'ewar murya tace
"Da...ma yace yana...so...na tun muna Katsina,
kuma daman gobe ne Faruk d'in yake niyyar
sanar daku muna son junanmu... mun yanke
shawarar yin au..."
Ji kake tassa!!! Mami ta d'auke ta da wani irin
wawan marin da har sai data ga giftawar wuta,
ta nemi ji da ganinta ta rasa!
AUREN FANSA 22
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
Dedicated to Mrs Fawwaz, Sadnaf, Momyn
Sultan, my sakwara, Maman Khady, Jannatuwa,
Faridat Musa, Rufaida Yusuf. One luv guys❤️😍
🌹22 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bilki ta soma magana cikin fushi.
"Kin bani mamaki Meenah, yanzu har yaushe
idonki ya bud'e da kike neman k'wace ma 'yar
uwarki saurayi? Ke ko kunya bakiji ace 'yar
uwarki tana son wani kema kina sonsa? Fatima
fa k'anwarki ce Amina, ay na d'auka ke mai
d'auka ce ki sadaukar mata da wani idan ta
kama, amma wai ke! Kece mai k'wacewa
Meenah."!
Ta share hawayenta cikin tsantsan mamakin
Mamin tasu, muryarta na rawa ta soma magana.
"Mami Faruk bai ta6a cewa yana son Zarah ba,
ni yake so tun asali, ko ita Fatiman ba sonsa
take ba, ni bansan ina kika ji cewar saurayin
Fatima ne ba, idan ma kina tunanin cewar
saurayin Fatima ne to ki daina tun wuri." Sai
kuma ta juya mata baya gami da had'e
hannayenta wuri d'aya tace
"A baya kinsha k'wace min kyauta a makaranta,
amma gaskiya yanzu bazan yarda a k'wace min
Faruk ba, hak'uri zakiyi ki sa mana albarka!"
Sai kawai Bilki tasa salati, yau tana fad'a
Meenah na fad'a.
"Lallai wuyanki yayi k'wari ya isa yanka, akan
nace kin k'wace wa 'yar uwarki saurayi kike
neman ki fad'a min magana Meenah."
Ta fad'a tana nuna kanta.
"Bafa saurayi na bane Mami."
Duk suka d'aga ido tana tsaye bakin k'ofa
idanunta sun kad'a daga fari zuwa ja! A hankali
ta k'araso cikin d'akin tana share hawaye tace
"Akan me zaki mare ta akan maganar da bakida
tabbas a kanta? Mami! Ki sani Meenah 'yar
uwata ce ta jini, ta yaya kike tunanin zata
k'wace min saurayi? To bari kiji abinda baki sani
ba, Faruk saurayin Meenah ne bani ba, ko don
kinga ina zuwa muna fira dashi kikayi tunanin
saurayina ne?" Tayi murmushi tace
"To ba haka bane, ni kawai mun saba ne
sheyasa kikaga ina fita amma lokuta da dama
ay tare da Meenah muke zuwa, duk randa kika
ga naje ni kad'ai to Meenah ta tura ni akan in je
kafin tazo." Ta kalli Meenah dake hawaye wani
na bin wani, tasa hannu ta share mata tace
"Daina kuka 'yar uwata, kiyi hak'uri da abinda
Mami tayi miki, sannan kisa a ranki Faruk naki
ne ke kad'ai kinji?"
Suka rungume juna suna kuka.
Haushi ya kashe Bilku kafin kuma sum sum ta
fice daga d'akin cike da kunya!
A wannan daren Bilki batayi bacci ba, yadda
taga rana haka taga dare.
Washe gari Meenah taga fushin Bilki fiye da
yadda ta saba gani, da Zarah take sabgoginta,
itama sai ta kama kanta a d'aki tak'i fitowa
tana karance-karancenta. Sai dai zuciyarta cike
take da tsoron Mamin, data tuna marin da tasha
jiya sai gabanta ya fad'i.
*
K'arfe goma na safe Faruk yazo, Bilki na zaune
parlor tana chanza channel, tun daga jin
sallamarsa tabi ta d'aure fuska yadda bata ta6a
yi masa ba. Yana zuwa ya zube k'asa yana
gaishe ta, sai kawai ta kafa masa ido bata amsa
ba, k'arshe ma sai ta mik'e ta haye bene zuwa
d'akinta ba tare da tace komai ba. Meenah na
daga bak'in k'ofar kitchen tana ganin komai, ita
kunya ma ta kamata ta kuma kasa k'arasowa
ciki. Sai da ta d'auki akalla minti biyu sannan
tayi ta maza ta shigo parlon kanta a k'asa.
Dukkansu sunyi shiru aka rasa mai fara yin
magana a cikinsu.
Da k'yar Faruk ya daure yayi murmushi cikin
basarwa yace
"Munyi ma Mami laifi ko?"
Ta d'an d'ago suka had'a ido, ta lumshe idanu
tace.
"Tun jiya take haka, mun rasa gane mata."
Yayi shiru cikin tunani, can kuma yace
"K'ila bata amince dani ba..."
Tayi saurin cewa
"Bakomai zata huce ne."
Baba ne ya ke saukowa daga mattakalar bene
Bilkin na biye da shi tana rik'e da briefcase
d'insa, ya hango shi a parlor zaune, da sauri ya
mik'e cikin girmamawa yabi bayansa don yaga
kamar parlonsa ya nufa daga can 6angarensa.
Baba nakan kujera Faruk na gefensa daga k'asa.
Bayan sun gaisa kamar kullum cikin mutunci da
girmama juna, can Baba yace
"Umar Faruk."
Ya d'ago da fararen idanunsa ya dube shi yace
"Na'am Baba."
"Meke tsakaninka da Amina?"
Faruk ya rud'e ya shiga inda inda saboda yadda
yaga Baban ya masa kwarjini, take kuma ya
sadda kansa k'asa.
AUREN FANSA 23
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹23 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Baba yayi murmushi yana dubansa yace.
"Faruk ka saki jikinka dani mana, ka d'auke ni a
matsayin mahaifinka, ka bani amsar tambayar
da nayi maka."
Ya daure yace
"Da...dama Baba, dama... dama... ina so mu
lokaci ne, sannan na gabatar maka da kaina a
cikin manaiman auren Meenah, duk da dai tace
min batada wanda ta tsada, to amma... amma
mun daidaita kanmu."
Baba yayi murmushi gami da lumshe idanu na
'yan mintina, sannan ya bud'e su a hankali kan
Faruk.
"Haka ne, Meenah batada wanda ta tsaida,
hasali ma kai ne mutum na farko da ta ta6a yin
soyayya da shi, sai dai wani hanzari ba gudu ba,
kafin na amince maka da auren Meenah, ina so
kayi min alk'awarin rik'e ta bisa amana da
gaskiya, kar ka ci amanarta kar ka yaudare ta,
shine kawai abinda nake buk'ata daga gare ka.
Duk da nasan dai mahaifinka mutumin kirki ne
kuma ina da tabbacin tarbiyarsa gareku, kuma
ina masa addu'a Allah ya jik'ansu da gafara."
Yace
"Amin Baba, indai wannan ne kar kayi haufi a
kaina insha Allah babu matsala."
Baba yayi murmushin jin dad'i yace
"Alhamdulillah, amma kuma ina so ka bari in
tuntu6i yarinyar tukunna inji ta bakinta, nafiso
na tabbatar sai a sanar da kai don ka turo
magabatan naka." Faruk yayi murmushi.
Yace
"To Baba babu damuwa insha Allah."
Baba yayi murmushi gami da mik'ewa tsaye.
Yace
"Kana iya tafiya Allah yayi muku albarka. Ya
amsa da "Amin."
Baba ya yi gaba, Faruk yabi bayansa yana
jinjina al'amarin.
***
Abu k'arami na neman zama babba, tun tana
ganin abin kamar wasa ta fara ganinshi babba.
Cikin k'ank'anin lokaci Jidda ta fahimci Faruk
soyayya yake, kuma wacce yake so d'in ta kame
masa zuciya farat d'aya, duk wani observation
nata akan Faruk ta gama gane komai, tausayin
kanta ya kama ta. Anisah ce ta shigo d'akin
tana tsaye a bakin k'ofa ta k'ura ma Jidda
idanu, hannunta d'aya d'auke da cup d'in tea
d'ayan kuma yana rik'e da wayarta k'irar
Samsung galaxy S6, a hankali ta k'araso ciki
tana murmushi. Zama tayi kan gadon da Jiddar
ke zaune a kai ta dafa ta.
"Yaya Jidda..."
Firgit! Ta dawo daga duniyar tunani tana kallon
Anisah, sai kawai ta k'ak'alo murmushin dole.
Anisah tayi murmushi.
Meyake damunki?"
Tayi tsai kamar mai tunani kafin tace
"Babu komai."
Anisah ta girgiza kanta.
"Sam ban yarda ba yaya Jidda, na dad'e da
ganin chanzawarki, gaba d'aya kin bi kin sussuce
kin zama wata iri? Har Mama ta soma
tambayarmu abinda akayi miki,a gaskiya yaya
Jidda koma meyake damunki ki fito fili ki fad'a
mana, k'ila da akwai taimakon da zamuyi
miki..."
Har yanzu bata d'ago ba kanta na k'asa dai tana
kallon wayarta. Yusra ce ta lek'o tace
"Anisah ya Najeeb na kira, kuma yace kiyi sauri
kiran nada mahimmanci."
Sai a sannan Jidda ta d'ago tana dariya tace.
"Kice dai za'a je a soye, wai yanzu Anisah har ta
girma ta iya soyayya ko?"
Anisah ta sunkuyar da kanta k'asa tana
murmushi kafin kuma ta fice da gudu ganin zasu
sakata gaba da zolaya.
Yana zaune a garden bisa kujera yana sanye da
jar riga da ash wando (jeans). Kayan sun haska
fatarsa da take kalar fatarsa chocolate mai
haske, ta k'araso tana murmushi, tun daga nesa
yake kallonta har ta iso inda yake. Yayi nisa a
kallonta har bai san lokacin data zauna ba, sai
data kira sunansa yayi firgit ya dawo duniyar
tunani.
"Ya Najeeb."
Yayi sassanyar murmushi yace.
"Anisah kina lafiya?"
Tace
"Lafiya lau, ya naganka nan kai kad'ai?"
Yace
"Ke nake jira ki taya ni fira, ko baza'a ta ya ni
ba?"
Tace
"Uhm, daman Yusra tace kana nema na, sheyasa
na fito."
Yayi murmushi yace
"Hakane, ni nace ta kira ki, daman inji batun
karatunku ina kukayi applying?"
Tace
"Nayi applying first choice d'ina a Base nida
Yusra, sai second choice mukasa Turkish Nile.
Sai last mukasa BUK."
Yace
"Ok yayi Allah ya taimaka."
Tace
"Amin."
Yace
"To ya batun maganarmu ina aka tsaya? Har
yanzu fa baki bani amsa na ba, kullum dana miki
maganar baki bani gamsashiyar amsa, amma
yau ba inda zaki sai kin fad'a min."
Cike da kunya tace
"Wace magana ya Najeeb?"
Yace
"Kin fini sani."
Ta sunkuyar da kanta tana kallon k'asa, yace
"Ke nake saurare fa."
Tace
"Ya Najeeb, wai yanzu kake nufi za'ayi auren?"
Yayi dariya
"Eh mana idan har kin amince me ake jira? Bakiji
me Baba yace ba? Yace mu dukkanmu zai had'a
ya aura damu, yace mazan su fad'i matan da
suke so, matan kuma su gabatar masa da
wanda suke so, yace so yake yayi gaba d'aya ya
huta. Kinga ni da ke sai ayi 'yar gida tuwo na
maina. Ko ba haka ba?"
Tayi shiru bugun zuciyarta ya k'aru, tabbas tana
son Najeeb kuma shima d'in yana sonta sosai.
Tace
"To ya Najeeb Allah ya tabbatar mana da
alkhairi."
Yaji dad'in kalamantanta sosai yace
"To Amin ya Rabbi, daman haka nake so naji
daga bakinki."
Tayi murmushi.
Sai da suka kammala firar tasu ne kafin kuma
su tashi su shige ciki.
MSB💖
AUREN FANSA 24
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹24 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Baba na zaune a parlonshi ya kira Bilki yace ta
turo masa Meenah.
Tana d'akin Zarah a bakin gado tayi tagumi,
Zarah kuma na jera kayanta cikin wardrobe da
aka kawo daga wurin wanki da guga da safe.
Bilki ta shigo d'akin, da sauri Meenah ta d'ago
fararen idanunta ta kalle ta, kallo d'aya zakayi
mata ka tabbatar da tana cikin damuwa mai
tsanani, take Bilki ta 6alla mata harara tace
"Taso muje."
Ta mik'e a sanyaye tabi bayan Bilkin har parlon
Baba, jikinta yayi matuk'ar yin sanyi.
Baba na duba newspaper da idanunsa mak'ale
cikin farin gilashi a lokacin da suka shigo.
Ya ajiye takardun gefe ya kuma cire gilashin yabi
Meenah da kallo a lokacin da take zama kan
carpet, sai ya saki murmushi yace
"Aminatu jiya wannan yaron Faruk yake sanar
dani cewar yana sonki, kuma yana so in bashi
izini don ya turo da magabatansa, k'warai na
yaba da hankalin yaron da kuma nutsuwarsa,
amma kinsan bazanyi saurin yanke hukunci kai
tsaye ba, ina so inji ta bakinki tukunna. Shin
Amina kin amince Faruk ya turo da iyayensa ayi
magana, ko kuma baki amince ba?"
Farin ciki marar misaltuwa taji ya lullu6e ta har
ta gaza 6oye hakan, take kuma ta sadda kanta
k'asa fuskarta d'auke da k'ayataccen murmushi.
Ta kai dubanta ga Bilki taga yadda ta had'e rai
tayi murtuk.
"Amina." Ta d'ago ta kalli Baban tace
"Na'am Baba."
Yace
"Ke nake sauraro, shin kin amince Faruk ya turo
magabatansa ko baki amince ba?"
Da k'yar ta bud'e baki saboda matsananciyar
kunyar da takeji tace
"Haka ne Baba, kuma na amince."
Yayi murmushin jin dad'i yace.
"Alhamdulillah, idan yazo kice ya turo
magabatansa, Allah yayi muku albarka."
Kanta na k'asa tace
"Amin Baba."
Yace
"Tashi ki tafi."
Tashi tayi ta fita. Tana fita Bilki tace
"Alhaji!"
Ya dube ta yaga tayi kicin kicin da fuska yace
"Lafiya dai Bilkisu?"
Dama kamar jira take tace
"Haba Alhaji don me zaka biye wa yarinya daga
tace tana son mutum sai ka d'auke ta ka bashi,
sannan baka ganin yarinyar nan k'aramar
yarinya ce duka duka nawa take da zakayi mata
aure yanzu? Ko university fa bata shiga ba,
gaskiya ni ban amince ba sam." Sai ya kalle ta
yayi murmushi yace
"A lokuta da dama ku mata kuna bani mamaki,
kina k'in auren Meenah ne saboda k'aramar
yarinya ce? To ni banga k'ank'anta a tattare da
ita ba, shekaru goma sha bakwai gareta idan
baki manta ba wata mai zuwa shekararta goma
sha takwas, a hakan ne kike ganin yarinya ce?"
Tayi shiru tana ciccin magani. Ya cigaba
"Babu wani abu da iyaye zasuyi alfahari dashi
face suga sun aurar da 'ya'yansu, shine kad'ai
kwanciyar hankalinsu saboda idan zaki auna
karatu baifi aure ba, haka zalika zata iya cigaba
da karatunta d'akin mijinta. Saboda haka nake
gargad'inki da kiyi gaggawar kawar da wannan
gur6ataccen tunaninki ki koma hanya
madaidaiciya." Jiki a sanyaye tace
"Kayi hak'uri Alhaji, a had'o shayin ne ko sai
anjima?"
Yace
"Bari sai anjima."
A ranar duk wanda ya kalli Meenah yasan tana
cikin matanancin farin ciki.
Cike da farin ciki ta lalubo wayarta ta kira Faruk,
bugu biyu ya d'auka.
"My baby." Ya fad'a yana murmushi. Tayi
murmushin jin dad'i. Tace
"My soul." Sunan ta dake kiransa kenan.
"Albishirinka!"
Yace
"Goro."
"Fari ko ja?"
Yayi dariya
"In banda abinki ya ina ganin farin goro zan
d'auki ja? Ay farin zan d'auka."
Tayi murmushi
"Haka ne, to Baba ya baka izini ka turo iyayenka
my soul."
Yace
"Wow alhamdulillah! Gaskya nayi farin ciki insha
Allah zan sanar da Dada, i love you so much my
baby Allah ya nuna mana ranar auren mu lafiya."
Tayi murmushin jin dad'i tace
"Amin my soul love you too, bari naje Mami tana
kirana sai anjima."
Yace
"Awwn kamar kar ki tafi, amma zan kiraki
anjima, take care."
Sukayi sallama ta kashe wayan, yana cire wayan
a kunnensa ya hango Najeeb tsaye a bakin k'ofa
yana kallonsa. Ya hau susan kai yace
"Najeeb me kakeyi a nan? Ka k'araso ciki
mana."
Najeeb yayi ajiyar zuciya ya k'araso ciki ya
zauna gefen Faruk kan gado tare da dafa sa.
Yace
"Faruk a gaskiya banga dalilin da zaisa ka
yaudari yarinya ba alhalin ba itace tayi maka laifi
ba."
Faruk yayi murmushi yana kallon Najeeb yace
"Don na yaudare ta shine me? Wannan shine
first step da zan d'auka shine auren d'iyarsu!"
Najeeb yace
"Faruk da zaka ji shawarata da ka k'yale
yarinyar nan akwai hanyoyi da dama da zaka
d'auki Fansa ba dole sai ta wannan hanyar ba,
she's too innocent wallahi dana ganta ta bani
tausayi."
Nan take Faruk ya fara huci, bak'in ciki had'e da
6acin rai suka taru suka masa dirar mak'iya! Ya
mik'e a lokacin ne kuma idanunsa suka sauya
kala daga fari zuwa ja tsabar 6acin rai, shi
kanshi Najeeb ya tsorata da ganin yanayinsa.
Faruk ya soma magana cikin 6acin rai.
"Najeeb! Kar ka manta alk'awarin da na d'auka
a baya, na k'watar mana 'yancinmu, auren
Meenah shine abu na farko da zanyi, don
gudanar da duk wani bincike na da zanyi. Idan
har ban auri d'iyarsu ba ta yaya zan cimma
burina na gano musabbabin yadda aka kashe
mana iyaye? Dole sai na kusance su, sun yarda
dani sun kuma amince dani, ta haka kad'ai zan
sa ido sosai akansu. Bayan haka! Sai nasa sun
raina kansu, sai sunyi dana sanin abinda suka
aikata, ita kanta Meenah lokacin kad'an nake jira
dana aure ta zan kuma wulak'anta ta, dole idan
nayi haka abin zaiyi wa iyayenta zafi, to wannan
kad'an ne daga cikin abubuwan dana tanada!"
Najeeb ya mik'e tsaye da sauri zuwa inda Faruk
ke tsaye.
"Dan girman Allah ka sauke k'udurinka na
wulak'anta d'iyarsu, bata ji ba bata gani ba,
haba ya laifin iyayenta zai shafe ta?"
"Ya shafe ta! Kai harta karensu ko magensu
laifin ya shafe su, na tsane su, na tsane su! Na
tsane su! Wallahi duk sadda na kalli Meenah ko
wani nata sai na ji kamar yanzu nake kallon
gawar iyayena kwance cikin jini."
Ya runtse idanunsa gam gami da dunk'ule
hannu, take jijjiyoyin kansa suka mik'e tar!
"Ka barni na cigaba da abinda na sa gaba,
abinda kawai nake buk'ata daga gareka shine
fatan alkhairi, amma idan ba wannan ba to bana
buk'atar shawararka." Ya fad'a cike da 6acin rai
"Haba Faruk! Meyayi zafi haka? Kayi hak'uri don
Allah ka kwantar da hankalinka, mubi komai a
sannu, insha Allah zaka cimma burinka."
Take yayi murmushi. Rungume Najeeb yayi yana
fad'in.
"Yawwa ko kaifa, haka ya kamata ka fad'a."
Najeeb ya k'ak'alo murmushi kurum.
*
Da daddare bayan Dada yaci abinci sai ya aika a
kira masa Faruk, bayan ya shigo parlon Dada
yana kallon tashar BBC, rage volume yayi yana
kallon Faruk sadda yake zama kan carpet, bayan
ya gaishe shi kamar kullum Dada ya soma
magana.
"Faruk dalilin da yasa na kiraka shine, naji
labarin daga wurin Hajiya cewar ka samu matar
da kake so haka ne?"
Yace
"Haka ne Dada."
Dada yace
"To alhamdulillahi, daman abinda nake jira
kenan Allah yasa albarka 'yar gidan waye?"
Faruk yace
"Sunan mahaifinta Alhaji Hamza, 'yan garin
Katsina ne amma nan garin yake aiki baban
nata."
Dada yace
"To yayi kyau, da fatan kayi k'wak'waran bincike
kafin ka fara soyayya da ita?"
Yace
"Eh Dada, mahaifinta ma'aikacin banki ne, shine
manager na First bank yanzu haka, kuma
mutumin kirki ne, to yama ce na fad'a maka na
tura magabatana a yi magana."
Dada yace
"To alhamdulillah, indai wannan ne babu matsala
kar ka damu zamu je insha Allah, ni na d'auki
nauyin komai kai da k'anwarka, zan shirya nida
Alhaji Musa da Alhaji Sufyan (k'aninsa da
yayansa) sai muje insha Allah. Jeka kira min
Nabeel da Najeeb."
Yace
"To Dada."
Ya mik'e ya fita, ba'a juma ba suka shigo tare
gaba d'aya, bayan sun zauna Dada ya fara
magana.
"Kamar yadda nayi muku alk'awarin gina muku
gidaje, to an kammala, ga ma makullen nan, kai
Nabeel bazan baka ba sai ka samo wacce zaka
aura, amma da Faruk da Najeeb su tunda suna
da wad'anda suke so, sheyasa zan damk'a masu
takardun gidajen da kuma mukallen. Sai kuma
anyi maku order d'in motoci guda uku, zasu iso
nan da sati d'aya insha Allah. Sai abu na k'arshe
maganar lefenku Hajara (k'anwarsa) na damk'a
mata ragamar yin lefe na kowanenku, abinda
zakuyi list sai ku rubuta duk abinda kuke
buk'ata, Allah yasa alkhairi yasa ayi damu."
Suka amsa da "Amin." Sannan kuma suka shiga
jero masa godiya marar adadi tare da fatan
alkhairi.
Sai yanzu Faruk ke tunanin anya zai iya cin
amanar Meenah kuwa? Ko don albarkacin Dada
wannan kaya da ya masa haka? Sai dai ya
k'udiri a ransa ya zama dole ya d'auki Fansa
kota wani hali ne! Jikinsa yayi matuk'ar sanyi a
yayinda dayake fita daga parlon.
AUREN FANSA 25
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
Dedicated to Miss Hafsy and Aisha Ali Garkuwa❤️
🌹25 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Da gudu ta fad'a jikin Mama tana kuka sosai,
Mama dake had'a kayan wankinta a cikin
kwando ta dakata tana kallonta cike da mamaki,
sannan kuma tace
"Jidda lafiyarki haka zaki shigo kina kuka? Wani
abin ne ya faru?"
Ta k'ara fashewa da wani kukan har tana
shasheka. Hankalin Mama ya tashi matuk'a har
ta fara tunanin ko batada lafiya ne ma.
"Wai bazakiyi magana ba, ni sa'ar ki ce ina miki
magana kin min shiru?"
Cikin kuka tace
"Mama ki taimake ni! Mama idan na rasa shi
kamar na rasa raina ne, bazan iya rayuwa bashi
ba Mama ki taimake ni Mama!"
Taci gaba da kukanta. Da mamaki Mama tace
"Waye kuma idan kika rasa shi zaki rasa ranki?
Ke bakida hankali ne? Akan namiji ki zauna kina
wannan kukan, ni kin ma bani haushi. Wai waye
ana miki magana kin ma mutane shiru?"
"Ya Faruk ne Ma..."
Ture ta Mama tayi daga jikinta tana kallonta
galala sannan tace
"Wa kika ce? Wane Faruk d'in?"
Cikin kuka tace
"Na nan gidan, naji ance aure zaiyi, ni na yarda
ya had'a mu ya auremu tare da wadda yake
so..."
Buge mata baki Mama tayi hakan yayi sanadiyar
katsewar maganar tata, ta dafa wurin tana
cigaba da kuka.
"Lallai yarinyar nan ashe bakida mutunci? Kawai
sai a shiga hak'kin yaro babu dalili? Shi baice
yana sonki ba haka kawai sai a takura masa, to
wallahi ahir d'inki! Kar na kuma jin magana
makamanciyar wannan a nan gidan, tun wuri ki
fitar da Faruk daga ranki kinji na gaya miki, ashe
bakida wayau bansani ba? Tashi ni ki bani wuri."
Da gudu ta fice tana kuka, tsakanin d'a da
mahaifi kuma sai Allah, take tausayin Jidda ya
kamata don haka sai tabi bayanta.
Rarrashinta ta shiga yi da nasiha, har ta samu
tayi shiru, nan dai tayi ta kwantar mata da
hankali cikin hikima da dabara.
***
Ranar Juma'a magabatan Faruk suka gabatar
da komai na auren d'annasu. Duk wata dukiya
da ake buk'ata ta aure da kuma al'ada sun
gabatar tare da sadakinsu. Bayan kammala
komai aka saka bikin wata d'aya saboda Baba
ya buk'aci hakan, don yace yafi so ta fara karatu
a d'akin mijinta.
Bayan Sati biyu da hakan kuma suka kawo lefe
saitin akwati/jaka takwas da kit. Akwatinan
sunyi kyau kalar purple.
Yanzu bikin ya rage saura sati biyu kenan.
To daga nan kuma aka cigaba da shirye shiryen
biki, tun daga kan su dilka, gyaran gashi Baba
ne yasa aka d'auko ta daga maiduguri mai suna
Salima. Matar ta k'ware a gyaren jiki da gyaran
amarya. Kwanan ta d'aya amma Meenah ta fara
murjewa, ko wucewa tayi sai k'amshin jikinta ya
bugo mutum.
Kayan d'aki kuwa Baba daga dubai yasa akayi
mata order, gado set biyu masu matuk'ar tsada
da kyau, sai set d'in kujeru suma biyu, kayan
dining da kitchen ma duka a can akayi order
komai da komai. Don Baba a shirye yake don
nuna ma Meenah gata.
Hartta katin d'aurin aure daga dubai d'in aka
bugo su, sheyasa ya fita daban ko kallon shi
kayi kasan ya had'u!
Tun ana saura sati d'aya bikin Baba ya tafi
Katsina ya d'auko Goggo. Nan itama aka fara
hidimar biki da ita.
A 6angaren ango shima shiri sukeyi sosai, don
su mutum hud'u ake ma biki, da Faruk da
Najeeb da Yusra, sai Anisah, Nabeel da Jidda
suka rage kasancewar basu fiddo wad'anda suke
so ba. Don haka gidan ya kacame da hidima ba
kad'an ba.
Events d'in da Meenah zatayi kamu ne kawai
tasa sai yinin biki, sai d'aurin aure sai walima
sai kai amarya sai ango zasuyi dinner shikenan.
Tun ana saura sati d'aya aka fara jere a
unguwar Aso Villa, manyan gidaje ne jere guda
uku amma kowa da katangarsa haka ma kowa
da gate d'insa, babban gida ne ba laifi don yana
da wadatar fili, gidan dai yaji shuka banda
carpet grass dake shimfid'e a k'asa, ginin
zamani mai d'auke da parlor biyu, d'akuna uku,
kitchen da dinning. Gidan yayi sai dai fatan Allah
basu zaman lafiya!
Ranar laraba ta kama ranar da ake ma Meenah
k'unshi, nan fa aka zauna daga can garden aka
shiga yaryara mata k'unshi. Sai wata kuma
daban tana ma 'yan matan amarya da sauransu.
Ranar alhamis ranar da ake kamu k'arfe hud'u
za'a fara a gama k'arfe shidda.
Amarya tayi shiri cikin ja da silver bridal gown
wanda ya amshe ta ya kuma yi mata kyau! A
yayinda da Zarah suke sanye cikin ashobi pink
da black.
Bayan an gama shiri aka rufe mata fuska suka
tafi wurin kamu.
Nan kuma aka shiga gabatar da kamun yadda ya
kamata, tun a wurin kuma Nabeel yake ma
Zarah wani irin kallon da har sai da ta tsargu,
shikam tunda ya ganta yaji ta masa. Anyi taro
lafiya, ansha hotuna. K'arfe shidda daidai aka
kammala aka watse.
Bilki anata fama da jama'a, 'yan uwa, mak'ota,
abokan arzik'i, 'yan cin arzik'i, da kuma
k'awayenta don haka ko tana cikin 6acin rai ma
bazaka gane ba. Hidima tasha kanta, gidanta a
cike yake taf ba matsaka tsinke. Hartta dai
Hajiya Laila da d'iyarta sunzo tun ana saura
kwana biyu bikin.
Nabeel dai ya kasa hak'uri ya sanar da Najeeb
yana son k'anwar Meenah, aiko yaji dad'in haka.
Don haka ya sanar da Faruk, Faruk ya sanar da
Meenah ita kuma Meenah ta tuntu6i 'yar uwarta
taji ta bakinta. Batayi saurin amincewa ba sai
daga baya, take kuwa suka kar6i number juna
yanzu har sun fara gaisawa ta waya!
Ranar juma'a cikin garin Abuja dubban mutane
suka shaida auren FARUK ADAM DA AMINATU
HAMZA, NAJEEB DA ANISAH, YUSRA DA SADIQ.
Daga nan angwaye suka zarce walima a guest
house d'in Dada dake can Asokoro.
Washe gari akayi wunin biki, tun safe jikin
Meenah ya fara yin sanyi kuma, ko abinci tak'i
ci, jinta take kamar wata marar lafiya. Gashi
Bilki bata damu ba bare kuma ta tilasta mata
taci. Zarah keta lalla6a ta har dai ta samu tasha
ruwan tea.
Haka aka cigaba da gudanar da wunin biki cike
da kwanciyar hankali.
K'arfe takwas na dare motocin d'aukar amarya
suka iso.
Tun a sannan Meenah ta fara kuka, tun tana
ganin zata rabu da 'yar uwarta sai kuma
hankalinta ya tashi sosai. Take suka rungume
juna suna

Please Login or Register in order to submit comment