Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

raka shi bakin motarshi yace mata yau
da wuri zai dawo yaci abincin rana ta masa
amala da miyan ku6ewa d'anya, ta bishi da
"To." Da fatan dawowa lafiya.
Yana tafiya ta tashi tayi wanka ta kimtsa gidan
sannan ta hau mota tare da kud'in da ya bata ta
nufi kasuwa, ta siyo garin amala da k'ashin rago
da ku6ewa, tana dawowa ta fad'a kitchen ta fara
kacaniyar dafa abinci, k'arfe d'aya da rabi daidai
ta gama 1:30 pm, tana gamawa ta fad'a wanka
ta fito ta shirya cikin wata atamfa dark blue
d'inkin riga da skirt d'inkin ya zauna dabas a
jikinta.
Amma shiru ba alamunshi har wajen uku, ta
d'auko wayarta ta shiga neman layinsa nan ma
bai d'auka ba. "Oh God!" Ta fad'a tare da jefar
da wayar ta mik'e bisa doguwar kujera, sama
sama bacci ya ringa fisgarta tana k'in yi don
bata son baccin yazo.
Can wayarta ta fara ruri ta mik'e zumbur ta
d'auka yace
"Baby zan aiko a d'aukar min abincin nan don
meeting zamu shiga yanzun nan, idan nace sai
na dawo kafin na koma zan makara."
Tace
"Sai ka turo bakomai."
Ta mik'e ta had'a shi cikin basket, ta kira d'an
almajirinta Yusha'u tace
"Koda bacci zai d'auke ni idan wani yazo ka
d'auko basket bisa dinning ka mik'a masa."
Yace
"To Anty."
Ta koma tayi kwanciyarta. Itace bata tashi ba
sai k'arfe hud'u har da 'yan mintina, tashinta
yayi daidai da k'wank'wasa k'ofa, ta mik'e
zaune daga kwanciyar tana gyara d'aurin
d'ankwalinta, sannan ta mik'e tayi tattaki izuwa
bakin k'ofa gami da bud'ewa.
Wata budurwa ce sai dai ko ba'a fad'a mata ba
tasan yarinyar tana cikin matsala babba.
Ta bata izinin shigowa, ta koma kitchen ta had'o
mata kayan lashe lashe da tand'e tand'e, ta
koma ta zauna suka soma gaisawa a mutunce,
Meenah tace
"Baiwar Allah sai dai ban gane ki ba, sannan
meya faru da ke haka naga jikinki duk ciwo
haka?"
Maimakon budurwar tayi magana sai kawai ta
durk'usa har k'asa tare da fashewa da wani irin
kuka mai tsanani.
Meenah ta razana tana tambayar lafiya? Da
k'yar budurwar ta tsagaita daga kukan da takeyi
sannan ta fara magana cikin sanyin jiki.
"Mu talakawa ne tu6us, wanda har cin yau
yakan gagare mu, Allah yayi ma mahafina
rasuwa da jimawa, sai mahaifiyata, mahaifiyata
ita take fafutukar nema mana abinci da kuma
kud'in makaranta, ba irin aikin da batayi ba,
haka muka cigaba da rayuwa mahaifiyata itace
komai na, sai dai a kwana a tashi na had'u da
hatsabiban k'awaye wanda suke hure min kunne
har na biye musu na kai kaina a halaka!"
Ta share hawayenta ta cigaba.
"Nazo na fara fita lokacin dana ga dama na
dawo lokacin dana ga gama, tun mahaifiyata na
fad'an tana duka na har ta gaji ta bini da
addu'a, gashi bana jin maganarta, nabi na raina
ta ban d'auke ta a bakin komai ba, tasha yi min
kuka akan abubuwan da nake mata amma ni ko
a jikina, na had'u da samari 'yan k'arya suna
min wayau suna kaini hotel su bani kud'i, daga
nan idanuna suka ida bud'ewa gaba d'aya, bana
ji bana gani, sutura kuwa sai wadda na cire duk
akan idon mahaifiyata, har ta kai ta kowa
mahaifiyata bata iya fita unguwa, data fita za'a
fara nuna ta ana gulmarta.
Kwatsam wata rana sai na had'u da Jidda..."
Thursday, 14 September 2017
Maryam Saidu at 23:38
AUREN FANSA 46
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-
FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan
neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon
zuwa Ameen_
🌹46🌹
Da mamaki Meenah tace
"Jidda kuma? Meye mahad'inki da ita?"
Budurwar tace
"Nasan zakiyi mamakin idan na sanar da ke ni
ba kowa bace face Lubabatu wacce aka fi sanin
da Luby..."
Meenah ta mik'e tsaye a razane tace
"Luby? Kece haka?"
Luby da kanta ke k'asa tace
"Eh nice! Nice Luby aminiyar Jidda, ki zauna Zan
k'arasa bayani na."
Ta k'i zama still tana kallonta da mamaki, Luby
ta sake d'agowa tace
"Ki zauna don Allah ba don ni ba."
A hankali ta koma ta zauna tace
"Ina jinki." Luby ta cigaba
"Kamar yadda na fad'a miki a baya cewar na
had'u da Jidda a wurin bikin wata 'yar
makarantar mu da akayi, duk da ba ajinmu d'aya
da Jidda ba amma a ranar muka k'ulle muka
zama best friends. Nice sanadin lalalacewar
Jidda, ni na d'ora ta bisa gur6attaciyar hanyar
ita kuma ta bi, a tare muka cigaba da harkar mu
ta bin maza da sauransu. Nidai yanzu ba komai
ya kawo ni ba illa nazo neman gafararki, ba don
ni ba don Allah ki yafe min, nayi kuskure amma
yanzu na gane kuskure na, ki gafarce ni..."
Meenah tace
"No kar ki damu ni banida rik'o, kuma na yafe
maku, Allah ya tsare gaba, sai dai garin yaya
kika ji wannan ciwon haka a hannu?"
Ta kai dubanta ga hannun dake nad'e da
bandage gaba d'aya tace
"Wannan a ranar muka samu sa'insa da
mahafiyata akan ina so na fita da misalin k'arfe
takwas na dare, a lokacin mahaifiyata ta tashi
tace ita sam bazan fita ba, niko na dage akan
sai na fita sai dai ayi wacce za'ayi, na fad'a
mata maganganun sannan nayo hanyar waje, sai
dai daidai bakin k'ofa mahaifiyata ta tako da
sassarfa tana fad'in, Lubabatu idan kika sa k'afa
kika fita ban yafe maki ba, daga haka kawai ta
juya ta koma gida, ni kuma kawai naja tsuka na
fice abina ba tare da na damu ba. A ranar hotel
muka kwana bayan mun gama abinda mukeyi
muka zarce club, muna can har asuba, sai da
gari ya fara haske sannan muka fito don
komawa gida. Sai dai me? Muna kan hanya nida
saurayin nan nawa muna jin kid'a muna rawa a
mota ba tare da mun ankare ba muka yi had'ari,
shi saurayin nawa take ya cika ni kuwa asibiti
aka wuce dani rai a hannun Allah, sai dana
kwana bakwai ban farfad'o ba, bayan na farfad'o
naji likita na cewa sai an yanke min hannu, nayi
kuka nayi kuka, nayi bak'in ciki, nayi nadama ba
kad'an ba. A ranar nayi Allah wadarai da son
abin duniya gami da bijire wa iyaye, nidai cewa
nayi ban yarda ba, daga nan akayi wa hannuwa
na hotuna (Scan) kusan kala uku, gashi banida
kowa dole ni likitan yake tunkara da maganar.
Yace min k'ashin hannun ya lalace da yawa, ya
ratattake k'ashin, wato sai an yanke su, ido waje
na zaro nace
"Duka hannuwa na?"
Yace
"Eh to, zai iya yiwuwa dukansu amma gaskiya
hannu d'aya yafi samun dameji wanda idan aka
d'auki lokaci zai iya ru6ewa, zamuyi iya
k'ok'arinmu muyi miki 'yan dabaru a shi d'ayan
hannun, idan Allah ya taimaka sai ya zauna.
Sannan abu na biyu wurin yin 'yan bincikenmu
mun gano kina d'auke da wannan cutar wato
cutar H.I.V AIDS."
Luby ta d'an dakata saboda kukan da yaci
k'arfinta, haka itama Meenah sai da tayi
hawayen, Luby ta cigaba.
"Wani abu naji ya sokeni a k'irji kamar an sara
mani mashi, kuka nakeyi tamkar raina zai fita,
gaba d'aya duniyar da abinda ke cikinta sun fitan
min a rai, likita ya zayyano min kud'in aiki wato
gaba d'aya miliyan biyu harda rabi, kaina ya
d'auki chaji sosai, nace su sallameni na tafi na
samo kud'in aikin sai na dawo. Suka sallame ni
nayi gidanmu, na tarar da mahaifiyata tana
ganina ta razana tana tambayar meyasame ni,
na koro mata bayani, tayi ta min fad'a tace ita
ba ruwanta dani don haka na tafi na nemo kud'in
da kaina daman na saba neman kud'i, ta koro ni
na fito ina kuka. Babu wadda ta fad'o min rai
kamar Jidda, nasan ko bata bani kud'i ba zata
taimakeni da shawara, sheyasa na taho nan."
Meenah ta kalli Luby kallo na k'urilla sannan
itama ta koro mata nata bayanin.
"A gaskiya Luby idan har kud'in aiki kike nema
sai dai kije ki nemi taimako kamar su gidan
radio, wurin manyan k'asa, sannan Jidda da kika
zo nema bazaki same ta ba, saboda Jidda dai ta
haukace."
A razane tace
"Ta haukace kuma?"
Meenah tace
"Eh ta haukace, a ranar da kuka je wurin boka
amso maganin da zaku sa min ta saka min ya
koma mata, tun daga wannan ranar ta fara
hauka tana tona muku asiri, yanzun ma zancen
da nake miki ana can ana hadaniyar fidda ta can
k'asar waje neman magani. Luby wato ita
daman duniya haka take, duk yadda ka d'auke ta
haka zata zo maka, tabbas kin tafka babban
kuskure a rayuwarki, waya ce miki iyaye abin
wasa ne? Musamman uwa, kin wulak'anta
uwarki ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Kin bi
boka ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Kinyi
zina ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Shekara
da shekaru kina shayar da mahaifiyarki gubar
6acin rai, ke ba yarinya ba ak'alla zaki kai
shekaru ashirin da shidda yanzu a yadda nake
kallonki, yaci ace yanzu kina gidan mijinki kina
bautar Allah amma kin tsaya shashanci,
shekarunki sun kai ace kinyi hankali ki gane halin
da duniya ke ciki, abinda yafi miki kije ki rungumi
mahaifiyarki ki nemi gafara, ki mata biyyaya
sannan ki gyara rayuwarki tun kafin ki koma ga
mahaliccinmu. Ina so ki maida komai kamar
tafiyar ruwa ki kuma tari gaba, ki yarda da
kaddara mai kyau ko marar kyau, wallahi Allah
gafurur Raheem ne, kuma insha Allah nima zan
taimaka miki da wani abin, cikin gadon
mahaifina zan baki wani abu sai ki k'ara cikin
kud'in aikin da za'ayi miki."
Ta bud'e baki cike da mamaki sai kuma hawaye
suka fara wanke mata fuska.
"Meenah, nagode! Nagode Allah ya saka da
alkhairi, Allah ya k'ara bud'i, Allah ya jik'an
iyaye yayi mana gafara, bani da bakin da zan
gode maki, na bibiyeki da sharri ke kuma kin
saka min da alkhairi, haka rayuwa take daman
ko wannan ya ishemu ishara."
Meenah tayi murmushi
"Kar ki damu, bakomai wallahi ai yiwa kai ne,
wannan ba wani abu bane."
Tana kallo Meenah ta mik'e ta shiga d'aki, ba'a
jima ba ta dawo hannunta d'auke da paper, ta
zauna tana mik'a mata.
"Gashi."
Tasa hannunta mai d'an lafiyar ta kar6a tana
kuka, Meenah tace
"Yanzu shiga ta na kira Faruk, na masa bayani
shine yace na k'ara miki shima ya bayar." Luby
ta duba tace
"Har dubu d'ari uku? Kai nagode Allah ya k'ara
bud'i."
Meenah tace
"Wannan ba abu bane ba babu damuwa, Allah ya
k'ara tsare mana imaninmu, ya tsare mu daga
fad'awa halaka, Allah ka shirye mu ya ganar da
mu."
Luby tace "Amin ya Rabbi."
Luby bata tafi ba sai da Meenah ta bata abincin
rana tana mai k'ara mata fad'an ta nemi yafiyar
mahaifiyarta, a haka ta bar gidan tana mai
jinjina al'amarin.
BAYAN SATI BIYU
****
Ranar wata talata, tana zaune taji horn d'in
motarsa, ta mik'e cike da mamakin ganin ya
dawo da wuri, ta lalla6o ta fito don tun jiya bata
jin dad'i. Ta k'arasa wajensa sai fara'a yakeyi
yana mata murmushi itama tana tayasa duk da
batasan dalilin farin cikin nasa ba. Ta kar6o
jakarsa suka jero har parlor ta dire jakar ta
d'auko masa ruwan sanyi a fridge ta tsiyaya
masa ta bashi.
Bayan ta zauna tace
"Lafiya ka dawo da wuri yau?"
Ya kuma dubanta yace
"Lafiya lau, tafiyar nan ce ta taso wai jibi jibin
nan zamu tafi, kin tuna maganar da mukayi a
baya ko?"
Tace
"Eh na tuna."
Yace
"To itace yau abin ya ida tabbata."
Tace
"Masha Allah, yanzu jibi zaka tafi?"
Yace
"Insha Allah."
Tace
"Zaku dad'e kenan?"
Yace
"Da shekara biyu zamuyi amma yanzu insha
Allah bazai wuce shekara d'aya ba mun juyo,
kuma in mun dawo zamu iya samun chanjin aiki
da kuma k'arin girma. Yanzu ma so nake naje
na shaida masu Dada maganar kuma ke nakeso
ki raka ni."
Ta d'an yamutsa fuska tace
"To amma fa ni bana ma jin dad'i."
Ya zaro idanu yana k'are mata kallo, yace
"Kodai abin arzik'in ne ya samu?"
Tace
"Me kenan?"
Yaja hancinta yace
"Kinfini sani, amma banga ta zama ba tashi
zakiyi mu tafi asibiti a auna ki don a tabbatar."
Kafin ma tayi magana ya zura mata hijabinta
pink color tare da jawo hannunta suka nufi
mota.
Ba k'aramar murna Faruk yayi ba da yaji daga
bakin likita cewar ciki ne da ita har na kusan
wata biyu, tun da suka shiga mota yake washe
hak'ora kamar gonar auduga.
‹ › Home
View web version
Thursday, 14 September 2017
Maryam Saidu at 23:39
AUREN FANSA 47/END
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-
FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan
neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon
zuwa Ameen_
🌹47 🌹🔚
A ranar sukaje wajen Dada, ya dad'e yana sa
masa albarka tare da fatan dacewa, sannan ya
ce lallai lallai sai ya bashi takardar Jidda don
data warke ya mik'a mata, yasan dole zata koyi
hankali. Haka Faruk ya rubuta ya mik'a ma
Dada, haka ma Mama tayi masa fatan dacewa
da sanya albarka. Daga nan suka wuce gidansu
Meenah ya shaida ma Baba, Baba ya bishi da
doguwar addu'a ya sanya masa albarka.
Sai dai tun ana gobe zai tafi hankalinsa ya tashi
bai ta6a tunanin daidai da kwana d'aya zaiyi
nesa da Meenah ba gashi har za'a shafe watanni
bai ganta ba, yana shigowa d'aki a lokacin tana
kwance kan gado ya zauna gefenta yace
"A gaskiya Meenah bazan iya tafiya na barki ba,
kawai kiyi hak'uri ki shirya mu tafi tare." Ta juyo
tana dubansa tace
"Nidai jeka ka barni, ina nan gida Nigeria bazan
iya binka ba a yadda nake jina d'innan."
Ya tur6une fuska ya shiga zayyano mata
matsalar da zai shiga idan bata bishi ba, har da
cewa tayi differing semester d'in mana idan suka
dawo sai ta gyara. Da k'yar ta lalla6a sa yayi
hak'uri ya barta, amma idanunshi sun kad'a
sunyi ja, haka itama ta wuni tana kuka har bacci
yayi awon gaba da ita. A daren ranar Meenah
taga tarairaiya kamar wata k'wai, ya dad'e yana
shayar da ita zuma kafin kuma suyi bacci mai
dad'i.
Washe gari ya fara shirin tafiya, kafin ya tafi sai
da ya nemo mata wata mata dattijuwa da zata
zauna da ita har ya dawo, haka suna ji suna
gani sukayi bankwana har airport ta kaishi, sai
data ga tashin jirginsu sannan ta dawo zuciyarta
na k'una ta rasa meke mata dad'i.
Haka ta kwana tunaninsa har ciwon kai ya
sauko mata wanda kafin safe zazza6i mai zafi
ya rufe ta, sai da tayi ta shan magaunguna
sannan ta samu taji sauk'i.
Shi kuwa gogan naka yana sauka masaukinsa
dama ya siya sabon sim, yana sawa ya kirata,
bugu biyu ta d'auka.
"Hello."
"Baby ya nake jin muryarki can k'asa ko jikin
ne?"
Ta lumshe idanu tace
"Eh to zazza6i ne yake d'an damuna amma da
sauk'i."
Ya rude ya shiga mata tambayoyi.
"Kinsha magani? Yanzu meke miki ciwo? Ya kike
ji yanzu?"
Tayi murmushi
"Wallahi yanzu kam bana jin komai sai kasala,
so ya hanya? Ya kuma gajiya?"
Yace
"Alhamdulillah, gani nan na sauka masaukina
yanzu zanyi wanka sai na kwanta na huta."
Tace
"Ai gara kayi bacci kam, sannu."
Yace
"Yauwa baby, kema sannu."
Sun dad'e suna fira kafin suyi sallama, kowane
yana jin kewar d'an uwansa.
Meenah ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar
hankali, kullum cikin missing Faruk takeyi sai dai
kullum suna mak'ale a waya suna fira basa
gajiya da junansu.
Sun cigaba da zumuncinsu itada Zarah kusan
kullum suna ziyartar juna, haka ma Anisah wacce
ke fama da tsohon ciki itama tana k'ok'ari wajen
ganin tana zumunci dasu Meenah.
****
BAYAN WATA BAKWAI
Meenah na zaune a parlor tana cin guava kamar
a mafarki taji horn, ta yunk'ura da k'yar ta lek'a
ta window ganin motar haya ya sanya ta fara
mamakin ko waye?
Bata gama mamaki ba sai data ga ana fiffido da
akwatina daga boot, gabanta ya fad'i batayi
tsammanin ganinsa yanzu ba, yayi wani kyau
yayi k'iba sai k'yallin hutu yakeyi. Ga k'asumbar
nan tasha gyara sai walk'iya takeyi.
Ta lalla6a ta fito bakin k'ofa daidai nan ya
k'araso yana murmushi, take ya ware
hannuwansa duka biyun alamun ta iso gareshi.
Ta dafe cikinta daya turo gaba tare da sunkuyar
da kanta k'asa, yayi murmushi tare da takowa
daf da ita sannan ya rungume abarsa tsam tsam
kamar za'a k'wace masa ita don ma tulelen
cikinta ya hana shi ya rik'e ta sosai.
Ya sumbace ta a goshi yana dubanta yace
"Wow! Baby cikinnan fa yayi miki kyau sosai."
Ya k'arasa yana kashe mata ido d'aya, tayi
murmushi, ta zum6uro baki cikin shagwa6a tace
"Shine zaka taho ban sani ba?"
Yayi dariya
"I'm sorry baby, just wanted to surprise you
daman."
Hannunta ya rik'o suka k'arasa ciki, ta taimaka
masa ya rage kayan jikinsa yana ta zolayarta
wai yanzu ta zama k'atuwa ko tafiya da k'yar
takeyi, ita dai sai dariya takeyi. Bayan ya huta
kuma ya shiga bubbud'e akwatina yana fiddo
mata tsarabarta, kaya ne mak'il akwati guda na
kayan baby wanda babu abinda babu a ciki, kaya
masu kyau da tsada, sai akwati guda nata
wanda ya k'unshi leshi, atamfa da su kayan
bacci da kayan kwalliya da sauransu, tayi murna
tayi ta masa godiya ba adadi.
A ranar dukkansu sunyi kwanan farin ciki da
kuma kewar juna.
Washe gari sai ga Jidda itama ta warke ras,
tazo neman gafara kuma duk sun yafe mata,
tace ta samu mijin aure, sun taya ta murna da
fatan alkhairi inda har Faruk yayi mata
alk'awarin bata tasa gudumuwar.
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah yau Allah
ya sauki Meenah da misalin k'arfe biyu na dare,
Faruk yana tare da ita har ta haifi santalelen
d'anta k'ato mai k'oshin lafiya, bayan an gyare
shi tas aka mik'a ma Faruk shi sai kallonsa
yakeyi cike da sha'awa, ya sumbati kumatun
Meenah yace
"Wane suna zamu sa masa?"
Tayi murmushi tace
"Duk sunan da kaga ya dace dashi ka sa masa."
Yayi masa hud'uba da sunan mahaifinsa wato
Adam amma za'a ringa kiransa da Khalifa.
Ranar suna anyi taron suna lafiya kuma ya
k'ayatar mai jego tayi fes da ita tana sanye cikin
wani golden lace sai k'yalli takeyi kamar wata
amarya.
Mai jego da d'anta sun cigaba da samu kulawa
sosai a wurin Faruk, ga yalwatar arzik'i
musamman da akayi masa k'arin girma kud'i
sun zauna masa sosai, hakan yasa Meenah ta
bashi shawarar ya gina masallaci ya kuma ringa
bada tallafi a gidan marayu, ba k'aramin dad'i
shawarar nan tayi masa ba, yayi tasa mata
albarka yana jin dad'i.
A haka har sukayi arba'in inda ta cigaba da
karatunta a lokacin ne kuma ita Zarah ta haifi
d'iyarta mace sun sha suna babyn taci sunan
mahaifiyar Nabeel wato Sadiya, za'a ringa ce
mata Nasreen.
A yanzu su Meenah har sun kammala karatunsu
suna jiran result.
****
Zaune take tana shayar da Khalifah Faruk ya fito
daga d'aki da alama bacci ya tashi, yana zuwa
ya rank'wafo yana sumbatar kanta, yace
"Zo muje na baki wani abu."
Ta mak'ale kafad'a alamun a'a tace
"Nak'i wayon, nasan dalilin da yasa ka kirani."
Yayi murmushi yace
"A'a fa result d'inki zan nuna miki."
Da sauri ta aje Khalifah ta mik'e tsaye tana
murmushi tace
"Da gaske? Mu je nagani."
Ya wuce tabi bayansa suna shiga yasa ma k'ofar
key yana dariya k'asa k'asa, tace
"La daman wayau zakayi min ko? Ni gaskiya ka
bud'e min na fita."
Yace
"Nak'i, ga key d'in zoki k'wata."
Ta nufo sa ta fara k'ok'arin k'wace key d'in
aikuwa ya damk'e ta yace
"Wana kama?"
Ta fara kukan shagwa6a tana fad'in.
"Wayyo my soul, mun bar Khalifah shi kada'ai a
parlor fa kar yayi kuka."
Yace
"To tsaya mu nema masa k'anwa sai ki tafi."
Tace
"Nidai a'a."
Yace
"Aiko baki isa ba."
Ya fara k'ok'arin zage mata zip da k'yar tayi
nasarar k'wace kanta tana ta faman dariya sosai
sannan ta d'auki pillow ta jefe shi da shi har
yanzu bata bar dariya ba. Nufo ta yayi ya chafke
ta yace
"Zan baki punishment, kina jifan mijinki."
Kafin tayi magana ya had'a bakinsa na nata....
ALHAMDULILLAH!!!
Alhamdulillah da Allah ya nuna min farkon book
d'innan da k'arshensa lafiya! Darasin dake ciki
Allah ya bamu ikon d'auka, kuskuren da ke ciki
Allah ya ka yafe mana.
Godiya ta musamman ga dukkanin masoya na
da wanda na sani da wanda bansani ba kusani a
duk inda kuke ina k'aunarku.
Fatan alkhairi ga duk wani mai karanta novel
d'ina, Allah ya bar zumunci Amin.
Daga k'arshe ina mai bak'in 😭😭cikin sanar da
masoya na cewar zan dakatar da rubuta 😭😭😭novel
zuwa wani lokaci bisa wasu dalilai wanda basai
na fad'e su ba da fatan masoya na zasuyi min
uzuri zasu kuma fahimce ni, nagode da k'aunar
da kuke nuna mun nima kusani ina k'aunar ku a
duk inda kuke.😘
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment