Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu
mijinta zai kaita, nan kuma kowa ya fara shirin
tafiya.
A mota babu wanda yayi magana ko wane da
tunanin da yakeyi, ta kai dubanta ga Faruk da
alama ya zurfafa cikin tunanin, ta ta6o sa tace
"My soul wai meke faruwa haka ne? Sannan duk
ina zamuje da su Anisah?"
Ya karkato kad'an ya kalle ta sannan ya maida
kansa ga titi yace
"Ki gafarce ni my baby."
Tace
"Akan me fa?"
Yace
"Kawai ki yafe min akan abinda zai faru yau."
Cikin rashin fahimta tace
"Me zai faru yau?"
Bai kai ga bata amsa ba wayarsa tayi ringing, ya
d'auka yace
"Hello Usman."
Usman yace
"Muna hanya ka turo mana address d'in."
Yace
"Muma muna hanya, zan turo maka sai mun
had'u d'in."
Ya kashe kiran ya tura masa address d'in.
Meenah da zuciyarta fal damuwa tace
"Kaji my soul, wai meke faruwa?"
Yace
"Kiyi hak'uri zaki ga koma menene."
Ganin ya d'auki hanyar unguwarsu ya sanya
tace
"Daman gida zamu shine kak'i sanar dani?"
Ya d'anyi murmushin k'arfin hali a zuciyarsa
yace
"Nasan yau zanyi breaking heart d'inki my baby,
amma abinda zanyi ya zama dole in ba haka ba
hankali na bazai ta6a kwanciya ba."
Ya kalle ta yaga ta zurfafa cikin tuanani, yayi
ajiyar zuciya a lokacin da ya karya kwanar
layinsu Meenah.
Ganin motoci a k'ofar gidansu ya sanya ta d'an
razana kad'an gami da zaro idanu waje, ya
kalleta ya kawar da fuskarsa gefe, yasan kota
masa tambaya baisan abinda zai ce mata ba.
Yayi parking ya fito daga mota, yana d'an kalle
kalle, ganin ba motar Usman ya sanya yasan bai
iso ba, amma motoci hud'u sun iso na abokanan
aikinsa, su Zarah duk sun iso inda take ta
tambayar abinda ke faruwa. Amsa d'aya take
samu wato,
"Nima bansani ba."
Su Najeeb ne kad'ai suka san abinda ke faruwa
saboda ya sanar musu daman.
Ya d'auki waya ya kira Hajir ya sanar mata yana
k'ofar gida. Tace she's ready tun d'azu. Nan
suka cigaba da tsara plan d'in nasu.
Ita dai Meenah bata k'ara magana ba illa dai
gabanta da ya tsananta bugu.
A 6angaren Bilki kuwa tunda ta tashi da safe
k'awarta ta iso akan yau zasu walimar bikin
d'iyar wani sanata da za'ayi a cikin garin Abuja,
Baba kuwa yana d'akinsa yana wanka zai fita,
shiryawa tayi cikin wani dank'areren leshi mai
matuk'ar tsada sai k'yalli takeyi, wayoyin da ke
hannunta sun kai kala uku kuma manyan wayoyi
masu tsadar gaske, ta fito parlor sai zuba
k'amshi take kamar shagon saida turare, kaci6us
tayi da Hajir sanye cikin bak'ar after dress tayi
tsaye a bakin k'ofa idanunta manne cikin bak'in
glass wato no respect.
Suka ja suka tsaya Bilki ta kalle ta daga sama
har k'asa tace
"Ke Atika meye haka? Ina aikin dana saki zaki
zo kiyi wa mutane tsaye a ka haka! Matsalar
d'an k'auye kenan ka wayar da shi sai daga
baya ya nuna yafika wayewa. Mts."
Laila tace
"Gaskiya kam da alama don wannan yarinyar
'yar rainin hankali ce, ke Malama ki bamu wuri
zamu wuce."
Hajir ta kalle su da chewing-gum a bakinta sai
hannunta dake hard'e tace
"Wacece Atika don Allah?"
Bilki tace
"Ahh! Kiji min neman magana fa, yo wacece
Atika 'yar aiki in ba ke ba? Kaji min yarinya zata
nemi ta maida ni k'aramar yarinya."
Laila tace
"Gaskiya wannan ta samu wuri da yawa. Da nice
ke da tuni na sallame ta don bazan iya ba, zan
iya farfasa mata jiki."
Bilki tace
"Eh gaskiya ne, ke Atika! Ki wuce kije ki d'ora
girkin rana kafin mu dawo."
Hajir ta kallesu a wulak'ance tace
"I'm sorry to say Hajiya, amma bazanyi ba, sai
dai idan kece zaki je ki d'ora."
Suka fara salallami suna tafa hannu, Laila tace
"Wai bazaki gaura mata mari ba, ni wallahi
sheyasa kikaga bani d'aukar 'yan aiki saboda
bansan wadda zan kwaso ba, ya za'ayi ki zauna
kina fad'a tana fad'a? Ki d'auki mummunan
mataki akanta mana."
Bilki tace
"Lallai kin k'oshi da sadda aka kawo ki kamar
zakiyi min sujjuda amma yanzu kin k'oshi kin
mik'e k'afa ko? Lallai sannu Atika, to wallahi
kizo ki kwashi kayanta ki bar min gida munafuka
kawai."
Hajir tayi murmushin mugunta tace
"Daman yau zan bar miki gida Hajiya kar ki
damu."
Bilki tayi tsaye ta rasa ma me zatace sai tafa
hannu kawai takeyi.
Minti goma tsakani Faruk ya doka sallama, Bilki
ta washe baki tace
"Ah kinga surukinmu ne yazo, sannu da zuwa
Faruk."
Ya shigo yana k'are ma gidan kallo, yana d'aga
kwalar rigarsa yace
"Ki gyara kalamanki Hajiya ba Faruk zakice ba,
Inspector Faruk Adam Ishaq zaki ce."
Suka kalli juna itada Laila, Laila ta rad'a ma
Bilki a kunne
"Adam Ishaq fa yace, me hakan ke nufi kenan?"
Hajir tayi murmushi ta cire after dress d'inta
ta dawo kusa da Faruk tace
"Sunana Inspector Hajir ba Atika ba."
Bilki tace
"Ke kamar ya keba Atika bace, to wacece ke?"
Meenah da Zarah da Anisah suka shigo ganin
Ikon Allah a daidai nan Baba ya sauko yana
gyara hular kansa ganin mutane da hayaniya ya
sanya yaja tsaya yana tambayar lafiya?
MSB💖
BELLO
‹ › Home
View web version
Friday, 8 September 2017
Maryam Saidu at 14:37
AUREN FANSA 42
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
Ina yi ma d'aukacin musulmai barka da sallah,
da fatan munyi sallah lafiya? Allah ubangiji ya
maimaita mana Amin thumma Amin! ❤️
Wannan page d'in nakune Faty Ladan, Hauwee
Bash, Asma'u Ammani, Hafsat Kabeer, Farida
Bature, Feedn, Machika, and Aisha Basheer dama
sauran wad'anda ban ambata ba, nagode da
k'aunar book d'innan da kukeyi.😘
Fatan alkhairi ga Auren Fansa Fans😍Allah ya bar
zumunci.❤️
🌹42 🌹
Cikin girmamawa Faruk ya isa inda Baba ke
tsaye ya gaishe shi ya amsa masa yace
"Meyake faruwa ne haka a nan?"
Faruk yayi murmushi yace
"Yanzu zaka fahimci komai Baba."
Faruk ya koma inda Hajir ke tsaye yace
"Hajir ina so ki bani wayar nan dana baki zan
duba wani abu."
Hand bag d'inta ta bud'e ta fiddo ta mik'a
masa, ya maida dubansa ga Bilki yace
"Ina so ki nutsu ki kalla."
Tace
"Bangane abinda ke faruwa a nan ba, don Allah
ayi mana bayani mana."
Faruk yace
"Abinda nake k'ok'arin yi kenan ay."
Wayarsa ya zaro daga aljihu ya kira bugu d'aya
aka d'auka yace
"Usman bud'e motata ka d'auko min system
d'ina tana nan daga bayan seat, sai wasu
wayoyi amma ba'a jiki suke ba suna nan a gefe
sai ka d'auko mun su duka."
Bansan me Usman yace ba naji dai Faruk yace
"A'a motar a bud'e na barta kawai ka bud'e,
yanzu yanzu muna jira don Allah."
Baba yace
"Wai lafiya haka Faruk? Har yanzu ban fahimci
inda ka sa gaba ba."
Faruk yace yana k'ok'arin maida wayarsa aljihu
"Yanzu zaka fahimta Baba."
Bilki kuwa kamar ruwa ya cita haka kurum
gabanta ya tsananta bugu, don har wata kyarma
take duk da batsan abinda ke faruwa ba.
Usman ne yayi sallama hannunsa d'auke da
laptop da wayoyi, Faruk ya kar6a inda ya aje ta
a saman center table d'in dake ajiye a parlor
d'in, yayi ta had'e had'ensa ya jona nan ya
had'a can, cikin minti kad'an wani video ya
bayyana a saman screen d'in laptop nasa. Ya
juya ta setin da kowa ke tsaye ya danna play.
Hoton farko video Bilki inda take waya da Laila a
gameda makircin da suka had'a, maganar yadda
take kwasar dukiya da shawarwarin da Laila ke
bata akan yadda zata dage wajen cigaba da juya
dukiyar.
Next scene kuwa hoton Laila ne da Bilki suna
zaune cikin d'aki suna maganar yadda suka
kashe Hajiya Reema da Alhaji Adam, take Bilki ta
fara zufa itada Laila, wannan abu ya basu
mamaki ya akayi aka d'aukesu hoto haka?
"Waye ya d'auki wannan videon?" Ta fad'a
jikinta na kyarma, Baba kuwa kallonta kawai
yana salati, inda Zarah da Meenah ke tsaye suna
kuka suna mamaki.
Scene na gaba kuwa yana d'auke da video d'in
Laila da Bilki inda Laila ke narrating yadda akayi
kisan da kuma shawarar su cigaba da 6oye
sirrinnan, har Bilki ke nuna mata tsoronta kar
wata rana asirinsu ya tonu. Laila tana nuna
mata asirinsu a rufe yake babu mai ji.
"Wallahi bani na kashe su ba, wallahi Laila ce ta
kawo wannan shawarar."
Bilki ta fad'a tana kyarma, Laila tace
"Dana baki shawarar wa yace ki d'auka don
haka kina da laifi kema."
Bilki tace
"Nidai wallahi kin cuce ni Allah ya isa wallahi."
Laila ta buga tsoki tace
"Aikin banza, yo Allah ya isarki me zatayi min?"
Faruk ya cigaba da displaying duk wani abu da
aka d'auka na Bilki da Laila, tare da voice notes,
Baba da zufa ta jik'e shi jagab, ya kalli Meenah
da Zarah yaga yadda suke kuka, sannan ya juya
ga Bilki da take borin kunya suna chachar baki
itada Laila suna ta k'ara bankad'e asirinsu da
kansu.
"Tun farko ina zaman zamana kika kawo
wannan shawarar kika ce mu kashe su..."
"Dana kawo shawarar nace dole kibi ne? Kema a
lokacin kina jin haushin Alhaji Adam, akan ya
samu kujarar da kikeso mijinki ya mallaka ko
nayi k'arya?"
Bilki tace
"K'arya kike munafuka algunguma, abin naki
harda sharri kuma? To wallahi..."
Maganarta ta katse ne sakamakon wani zafafan
mari da Baba ya d'auke ta dashi, har sai data ga
gilmawan wuta sannan ta nemi ji da ganinta ta
rasa na wuchin gadin.
Dafe kuncinka tayi cike da azaba kafin kuma ta
ankara ya k'ara d'auke ta da wani wanda yafi
na farko zafi, kyarma ta fara yi inda hawaye ke
ambaliya a saman fuskarta, ya d'aga hannu zai
k'ara wanke ta da wani marin cikin azama
Meenah ta rik'e masa hannu gam gam tana
kuka, tace
"Kar ka k'ara mata wani Baba, ka rabu da ita
don Allah."
Baba ya fara k'ok'arin k'wace hannunsa yana
nuna Bilki yace
"Ashe ke mutuniyar banza ce bansani ba?
Shashasha marar mutunci! Ashe ke muguwa ce?
Makira! Anya kinada imani kuwa? Kin bani
mamaki ban ta6a zaton haka daga gareki ba..."
Sai ta fara borin kunya tana fad'in
"Yo har abin kunya ya wuce daga gareka? Kai fa
kana zaune da mutum ka kasa gaya mata
iyayenta na asali tsabar rufa rufa!"
Baba yace
"Ki min shiru a nan, anya kina da hankali kuwa?"
Tace
"Ras nake, yo tunda aka tona min asiri na wa
zan iya rufewa kuma? Ai wallahi sai na fasa
k'wan! Ke Amina! Kalleni nan Alhaji bashi ya
haife ki ba! Haka nima ba nice na haife ki ba!
Kije ki tambaye shi inda iyayenki suke."
Gaban Meenah yayi mummunar fad'uwa, dafe
k'irjinta tayi a yayinda hawaye suke kwarara a
fuskarta, Baba take kallo tace
"Ni 'yar tsintuwa ce ko?"
Faruk kuwa tsaye yayi cike da mamaki a yayinda
k'walwarsa ta tsaya cak da aiki....
AUREN FANSA 43
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
Dedicated to First Lady 😍
PML You are the best Allah ya bar mu tare👌🏼😉😌
🌹43🌹
Cikin wani irin yanayi yace "What?"
Bilki kuwa k'ara d'aga murya takeyi tana fad'in
"Ke Amina ba mu muka haife ki ba."
Laila tana ta d'an zunguranta akan ta bari ina
bata ma saurareta ba. Baba ya sunkuyar da
kansa yana mai tsananin jin haushin Bilki, ko
kusa bai so Meenah tasan matsayin ta ba, a
ganinsa hakan zai iya haifar mata da damuwa
sosai, da yawan tunani, duk da yasan sanin
matsayintan ba wani abin bane don kuwa
cikakiyyar 'yar sunnah ce, hakan yasa ya tattaro
nutsuwarsa yana kallon Meenah data tsareshi da
ido kamar yau ta fara ganinshi, yace
"Kar ki damu zan sanar da ke komai, Faruk
kammala aikinka sai mu tattauna."
Da k'yar Faruk ya tattara nutsuwarsa amma
gaba d'aya hankalinsa naga Meenah da kuma
son jin in da gaske ne zancen Bilki.
Police guda biyu ke tsaye a waje Faruk ya kirasu
suka shigo, da hannu kawai ya basu order
wanda su kad'ai suka san me yake nufi, sara
masa sukayi sukace
"Yes sir..."
Fita sukayi ba'a jima ba sai gasu sun dawo da
matasan maza majiya k'arfi su kusan biyar
masu k'iran 'yan daba, ko su Zarah sai da suka
tsorata da ganinsu, sai wani huran hanci sukeyi
suna zare idanun kamar kura taga nama. Take
jikin Laila ya fara 6ari don kaf d'insu ta ganesu,
haka zalika ita kanta Bilki sai ta fara salati tana
bada hak'uri da neman gafara.
Faruk yace
"Wad'annan sune wad'anda kukayi assigning
suka aikata kisan da hannunsu, suka kashe min
iyayena..."
Take tsikar jikinsa ta tashi idanunsa suka kawo
ruwa, ya kai dubansa ga Anisah yaga tana kuka
itama, duk sai ta basa tausayi a ransa yace
"Ke kenan da bakida wayau a lokacin bare kuma
ni."
Bilki tace
"Ni dai bansansu ba. Billahi bansan ko su waye
ba."
Baba ya daka mata tsawa
"Yi mana shiru a nan! Ko so kike sai na sa an
harbe ki ne da bindiga? Ga laifi an kamaki dumu
dumu amma kina k'aryatawa?"
D'aya daga cikin 'yan daban suka ce
"Tabbas nine wanda Hajiya Laila ta kira take
sanar dani irin aikin da za'ayi musu, sannan
sukayi min alk'awarin mak'udan kud'i idan na
aikata abinda suka sani, ita kuma Hajiya Bilki ita
bani umarnin kisan tace idan ban aikata ba to
tabbas ni zatasa a kasheni, haka sukayi min ko
wanensu zai bani dubu d'ari biyar biyar idan
aikin ya kammala. Don haka na samu abokanan
aikina na sanar musu yadda zamuyi aikin. Ko
bayan faruwan haka sai da suka mallaka min
gida da mota wai a cewarsu farin cikin abinda
nayi musu ne."
'Yan sandan suka matso kusa da su Hajiya Laila
sukace
"You're under arrest for the murder of Hajiya
Reemah and Alhaji Adam, you have the right to
remain silent, because anything you said will be
used against you in a court of law."
"Don Allah ka gafarce ni, ku yafe min abinda
nayi."
Ta matso kusa da Meenah tace
"Ki yafe min irin cin zalin da nayi miki a baya,
nasan kin sha wahala a wurina ki yafe min."
Baba yace
"Kamar yaya?"
Zarah ta matso tana share hawaye tace
"Baba, tunda na taso nake ganin yadda Meenah
ke fuskantar wulak'anci, mugunta da kuma
zalunci a wurin Mami, bugun yau daban na gobe
daban, ga sata aiki kamar jaka, abinci kuwa data
gama wannan sai a sata wani, wanke wanke,
wanki, wankin toilets, shara, goge goge, duk
Meenah ce keyi. Sannan bata cin abinci sai ka
kusa dawowa, haka zata wuni da yunwa ga
uban aiki, da ka kusa dawowa zata korata tayi
wanka taci abinci yadda bazaka gane ba. Ko
nayi yunk'ura fad'a maka sai Mami ta hana, ko
tace zata zane ni muddin na sanar da kai..."
Baba yace
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Bilki ashe
yadda na d'auke ki ke ba haka kika d'auke ni
ba? Tun farko dana san haka kike da ban d'auki
amanar maraininiyar Allah na baki ba, amma
kisani akwai ranar hisabi kuma Allah sai ya
mata sakayya..."
"Na tuba Alhaji, ka yafe min..."
"Bilki kije na sake ki saki d'aya..."
Kowa sai da ya zabura jin sakin da Baba ya
yiwa Bilki, sannan ya bita da nasiha da fatan
zata gane kuskurenta, haka aka saka musu
ankwa itada Laila aka jasu suna tirjewa da
maganganu suka fice.
Faruk gaba d'aya jikinsa yayi sanyin abinda yaji,
wai Meenah marainiya ce?
"Me nayi? Na d'auki alhakin baiwar Allah." Ya
fad'i a cikin ransa.
Duk da daurewarsa sai da k'walla suka zubo
masa, ya share sannan ya bi bayansu Bilki inda
Anisah ma tabi bayansa, suka bar gidan. Suna
fita Meenah ta kifa kanta a hannun kujera tayi ta
kuka kamar ranta zai fita, Zarah na ta aikin
rarrashinta inda itama kukan takeyi, Baba yaja
su suka shiga cikin d'aki yana ta faman
rarrashinsu.
*****
Daddare kowa ya nutsu a parlor amma daka kalli
kowa kasan ba a cikin nutsuwa suke ba.
Baba ya maida dubansa ga Meenah yace
"Dalilin da yasa ban ta6a fad'a miki ba shine, na
farko baniso kiyi kukan maraici, na biyu baniso
ki shiga damuwar rashin iyaye, don kinsan
yawan damuwa ga yaro ba abu bane mai kyau,
amma ina mai baki hak'urin 6oye miki da nayi
duk da nasan you have the right kisani."
Nan ya kwashe labarin komai ya fad'a mata, su
waye iyayenta da kuma yadda akayi ta dawo
hannunsu da zama. Sannan ya d'ora da cewa
"Duk da nasan banyi niyyar fad'a miki ba amma
wallahi ji nake kamar an sauke min wani nauyi
da ke bisa kaina, Meenah bana fad'a miki
maganar nan ba don ki shiga damuwa ba, a'a na
fad'a miki ne bisa tirsasawa da akayi min, sai
dai ina rok'onki da kada ki d'ora damuwa a ranki
don Allah, sannan ki cigaba da yiwa iyayenka
addu'ar samu rahama daga Allah, inda suka tafi
muma zamu iske su wata rana."
Ya fad'a da guntun k'walla a idanunsa. Meenah
ta share hawayenta tace
"Wallahi Baba ban ta6a sanin cewar bakai ka
haifeni ba saboda babu alama, duk wani gata ka
min shi, sai dai nace Allah ya saka da alkhairi,
amma kasani har yanzu bazan daina ganinka a
matsayin mahaifina ba saboda kaima mahaifina
ne saboda yaya kake ga mahaifiyata don haka
duk d'aya ne, kuma insha Allah na maka
alk'awarin cire damuwa a raina."
Yace
"Alhamdulillah, ke kuma Fatima kema kar ki
shiga damuwar ganin mahafiyarki da aka kama,
ki cigaba da yi mata addu'a."
Tace
"Insha Allah Baba."
Faruk da ke zaune jikinsa sanyi k'alau yace
"Baba inada magana idan an bani dama."
Baba yace
"Bismillah mana."
Faruk ya sunkuyar da kansa saboda nauyin
maganar amma kuma dole ne ya fad'i, don ya
samu su yafe masa.
Yace
"Baba, ka gafarce ni, nayi kuskure babba."
Sai kuma yayi shiru, Baba yace
"Kuskure kuma Faruku? Na me?"
Ya kalli Meenah yaga shi d'in take kallo, sannan
ya maida kansa k'asa yana wasa da zoben
azurfar da ke hannunsa yace
"Wallahi Baba da zan auri Meenah ba sonta
nakeyi ba... daman don na d'auki fansar abinda
akayi wa iyayena ne sheyasa na aureta..."
Ras! Ras! Gaban Meenah ya yanke ya fad'i, ya
d'ago ya kalleta yaga idanunta sun kad'a sunyi
jawur! Tana masa kallon mamaki had'e da
tsana...
"Meenah nasan nayi kuskure a nan amma
wallahi..."
Da gudu tayi ciki tana kuka mai sauti...!
Zarah ta bi bayanta da gudun itama tana k'wala
mata kira...

AUREN FANSA 44
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
http://MaryamSBello.blogspot.com
🌹44🌹
A bakin gado Zarah tayi arba da ita ta kifa kanta
tana kuka kamar wacce aka aiko ma da labarin
mutuwa, a hankali ta k'arasa gami da zama
gefenta ta d'an dafata sannan ta kira sunanta
cikin sigar rarrashi.
"Meenah..."
A hankali ta d'ago da jajayen idanunta tana
kallon Zarah a yayinda hawayenta suka cigaba
da zuba ba k'akk'autawa, Zarah ta sa hannunta
ta share mata hawayen tace
"Haba Meenah, meye haka? Meye abin kuka a
nan? So kike sai wani ciwon yaje ya kama ki a
banza? Don Allah kiyi shiru ku fahimci juna keda
mijinki."
Meenah tayi murmushin da ya fi kuka ciwo tace
"Zarah, a halin yanzu ba zaki gane halin da nake
ciki ba saboda bake bace aka yaudara ni ce aka
yaudara, ke kina can zaune lafiya da mijinki kina
sonsa yana sonki, ni kuwa fa? Ashe wanda nake
matuk'ar so kamar raina ashe yaudara ta
yakeyi? Mutumin da zan iya sadaukar wa
rayuwata domin farin cikinsa, mutumin da nake
da burin samun zuri'ah ta gari da shi, mutumin
da nake kallo a matsayin masoyina na hak'k'ika
ashe shi ba haka yake kallona ba, ya cuce ni! Ya
cuci rayuwata, yayi min wasa da feelings ba
kad'an ba, wallahi Zarah namiji mugu ne, namiji
bashida tabbas! Allah wadaran namiji!"
Zarah tace
"Haba Meenah! Ki saurari kanki ki daidaita
tunaninki, yes na yarda Faruk bai kyauta miki ba,
kuma baiyi amfani da hanyar da ya dace ya
d'auki fansa ba, amma tunda yayi admitting a
gabana dake da Baba kinsan yayi namijin
k'ok'ari, ina so ki sani ba ko wane mutum bane
zai iya haka ba, ya kamata ko nan kiyi
respecting decision d'insa, kuma ko rantsuwa
nayi bazanyi kaffara ba ya na matuk'ar sonki a
yanzu, kuma ya gane kuskurensa."
Ta mik'e tsaye tana huci
"Sonsa na banza, bana so ya rik'e kayansa,
kuma nidai na gama zama da mayaudarin
mutum kamar Faruk, bazan koma gidansa ba!"
Zarah ta mik'e tana kallonta galala kafin tace
"Are you kidding me? In ma wasa kike ki daina
tun wuri, Meenah kamar yadda na fad'a miki da
farko zan kuma maimaitawa, Faruk yana sonki
ko ki yarda ko kar ki yarda, koda can baya sonki
to yanzu Allah ya d'ora masa. Don haka kiyi
tunani."
Baba ne ya aiko kiransu, suka mik'e jiki a
sanyaye suka fice, a parlor suka iske Faruk kallo
d'aya zakayi masa ka tabbar da hankalinsa a
tashe yake, tunda suka shigo ya kafa mata ido
ita kuwa ko kallon inda yake batayi ba, suka
samu wuri suka zauna k'asa, Baba ya fara
magana.
"Da farko dai ina so nayi muku nasiha akan
zaman duniya, gaba d'ayanku nan musulmai ne,
kuma shi musulmi a duk inda yake ana so ya
zamto mai hak'uri da kuma juriya da kuma
imani, tabbas Faruk baka kyauta ba a wani
6angaren, amma kuma ina so ke Aminatu kiyi
hak'uri na tabbata yanzu Faruku yana sonki
bada wasa ba, kuma tunda ya fito fili ya fad'a
miki bai kamata kuma ki juya masa baya ba.
Don haka ina so kiyi hak'uri ki d'auki k'addara,
kuma komai na duniya mai wucewa ne, ki rik'e
mijinki kiyi masa biyayya don shine gatanki
duniya da lahira."
Meenah tace
"Nagode Baba, amma ni gaskiya bazan koma
gidansa ba, ya sauwak'e mini kawai."
Ba Faruk kad'ai ba hartta Baba sai da ya razana
da jin kalaman Meenah, Faruk sunkuyar da
kansa kawai yayi yana jin tashin hankalin da bai
ta6a ji ba.
Baba yana kallon Meenah yace
"Aminatu, kalamanki basuyi min dad'i ba, don
banyi zaton kamar ki mai ilimi da aiki da shi zai
furtawa mijinki haka ba, amma ina so ki sani
saboda gaba duk wani 6acin rai in zaizo miki to
kisan irin kalaman da zaki furta. Mijinki dai
mijinki ne. Sannan zancen ya sake ki ma bai
taso ba, idan ma ya taso sai kiyi tunani wa
kuma zaki aura? Maza majoritin mu halinmu a
rufe yake, kafin kuma ki gane halin sai kin zauna
da mutum.
Aminatu duk rintsi kiyi hak'uri ki zaunawa
aurenki, kedai ki cigaba da add'ua, duk wani
hargirsi idan ya taso a tsakaninku kok'ari zakiyi
wajen ganin kun zauna kun warware
matsalarku."
Ya gyara zamansa ya d'an yo gaba daga
jinginar da yayi, yayi ajiyar zuciya ya cigaba
"Kin bani kunya Meenah, ban ta6a tsammanin
haka daga gareki ba, ni kome Faruk yayi na yafe
masa, don haka kiyi k'ok'ari ki yafe masa kema.
Ki tashi ki fara shirin komawa d'akinki, Allah yayi
maku albarka ya kwa6e muku duk wata fitina."
Ya kai dubansa ga Faruk yace
"Allah ya jik'an iyayenka ya gafarta masu, ga
matarka nan sai a kiyaye gaba, ka kula da ita da
kuma kanka, kasan dai matsayinta yanzu, don
haka ka rik'e ta amana Allah yayi maku
albarka."
Yace
"Amin Baba, na gane kuskure na kuma insha
Allah hakan bazata sake faruwa ba, nagode
sosai insha Allah zan kula da Meenah, zan kuma
rik'e ta bisa amana da gaskiya."
Cike da farin ciki Baba yace
"Amin, zan shiga daga ciki na d'an kwanta."
Sukayi sallama ya fice.
Zarah ita da mijinta su sukayi mata rakiya har
gidanta da misalin k'arfe biyar da rabi na
yamma, suna nan har akayi sallar isha'i bayan
sunci abinci suka fara shirin tafiya, Zarah ta
k'ara yi mata fad'a sannan ta bita da nasiha,
sukayi sallama dasu suka shige gida suma.
Bayan ta shigo ta maida k'ofar ta rufe, yana nan
tsaye bakin k'ofa yana faman murmushi, ta
kauda fuskarta tace
"Ya dai?"
Yace
"Bacci nakeji my baby, amma inaso na fara yin
wanka kuma ke nakeso kiyi min da kanki, kinsan
na gaji da yawa rabona da bacci mai dad'i har
na manta."
Ta so ce masa bazatayi ba amma tuno da
nasihar Baba ya sanya bata musa ba ta bishi da
"To."
Ta kunna masa ruwan zafi da taimakonta ya
watsa, ta taimaka masa ya shafa cream mai
k'amshi shi kuwa duk wani motsinta akan
idonsa yake. Ta kammala ta tafi tayi wanka ta
fito sanye da kayan baccinta masu kyau da
kuma firgita tunani, sai zuba k'amshi take ya cije
lips d'insa na k'asa yace
"My baby, kullum k'ara chanza min kikeyi,
yanzun ma sai naga kinfi ko yaushe yin kyau."
Duk da taji dad'in kalaman nasa haka bai hanata
turbune fuska ba tana cigaba da linke kayansa
da ya cire yanzu.
Yayi murmushi ya mik'e ya jawo ta ta fad'o bisa
k'irjinsa yana kallonta cike da so da k'auna
marar misaltuwa, ita kuwa k'ok'arin k'wace
kanta ta shiga yi wanda ta kasa saboda irin
rik'on da yayi mata....
AUREN FANSA 45
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_
P.M.L
# *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-
FANS-459256761123035
# *http://maryamsbello.blogspot.com
_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan
neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon
zuwa Ameen_❣️
🌹45 🌹
Ya d'an yi tsai yana dubanta, ta kawar da
fuskarta gefe, yace
"My baby, ki tausaya min ki kula ni, idan har
kika za6i ki guje ni to wallahi rayuwata tana
cikin matsala, nayi laifi tabbas kuma na gane
kuskure na har ma na bada hak'uri, to meyasa
bazaki yafe min ba? Allah ma muna masa laifi
ya yafe mana bare mu mutane? Wallahi ina
k'aunar ki, da zaki bani dama da na nuna maki
hakan Meenah..."
Shirun dai ta kuma yi, yace
"To in bazaki yi magana ba, kiyi hak'uri ki saki
ranki, kin hak'ura?"
Ya shafi fuskarta yana mai juyo da ita, take tayi
k'asa da k'wayar idonta.
"Kinji ni baby? Ki tuna matsayina a gareki, na
baki hak'uri kiji tausayina don Allah Meenah. Da
me zanji? Kina fushi dani kink'i hak'ura, ke
kad'ai fa guda nakeda a halin yanzu, ina zansa
kaina Meenah? Please please! Tuba nake, na
tuba bazan k'ara ba, kar6i wannan takardar ki
gani abin farin cikin da ya same mu."
Ya zura mata takardun cikin hannunta, ta kalla
shek'ek'e ba tare da ta karanta ba ta mik'a
masa yace
"Yanzu har kin duba baby?"
Ta gyad'a masa kai, yace
"To me kika gani?"
Tace
"Oho!" Kalmar data ambata a ciki kenan ashe ta
fito fili, yayi murmushi yace
"Daman wannan takardar k'arin ilimi ne aka tura
ni na tsawon shekara biyu wanda zanyi shi a
k'asar ingila, shine nake neman shawararki
saboda karatunki."
Har ranta taji dad'in alherin da ya same shi
wanda ta tabbata yaga hakan a fuskarta
Sai kawai ta ce masa
"Na taya ka murna, sai dai duk yadda ka tsara
yayi min."
Yayi murmushi yace
"Alhamdulillah naji dad'i, sai dai inaga kamar
zamanki a nan don ki k'arasa karatun naki yafi,
amma zan rink'a waiwayanki, bawai natafi har
sai na kammal ba ne, a'a zan rink'a ziyartarki,
donma in banda ina son kiyi karatun da k'afata
k'afarki, yanzun ma idan kinfson mu tafi taren
sai mu ajiye shi gaba kya yi shi."
Ba tare da ta kalleshi ba tace
"Babu damuwa, kaje zan zauna."
Yayi murmushi yace
Ay da yake yanzu level 3 zaki shiga kinga dana
dawo kin kammala insha Allah, kinga dana dawo
sai mu baje soyayyarmu yadda ya kamata."
Tace
"Allah ya taimaka."
Haka yayi ta lalla6a ta kamar k'wai, sai wani
riritata yakeyi yana yi mata kalamai masu
tausasa zuciya har ya samu ta d'an sauko daga
dokin data hau har ma tana d'an kula sa.
Washe gari ne yayi shirin aikinsa, bayan ya
kimtsa ta

Please Login or Register in order to submit comment