Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da batada
hasken ana ganin kyawunta. Idan ta bud'e ido ta
kalli mutum zaka gansu manya ne farare tas!
Baya 'yan kwanaki a lokacin Amina ta kwana 20
cif a duniya Goggo ta kira Hamza da Bilki
gidanta akan cewa tana son magana dasu.
Bayan sun iso suka gaisa Goggo ta d'auko
Amina dake kwance kan gado tana bacci, ta
mik'a ma Hamza ita tana murmushi tace
"Hamza kamar yadda kasani marigayiya ta baka
amanar rik'on Amina kuma ka d'auki alk'awarin
haka, don haka yau na damk'a maka Amina a
matsayin d'iyarka halak malak, da fatan zaka
rik'e ta bisa amana."
Sai kuma ta juyo ta kalli Bilki tace
"Bilkisu ga amanar Amina nan ki rik'e ta amana
saboda kar ki manta marainiya ce gaba da baya
idan har kika ci zalinta Allah zai mata sakayya."
Hamza yace
"Insha Allah Goggo kar ki damu ina k'auanar
Amina kamar 'yar dana haifa haka nake jinta a
raina. Insha Allah zamu rik'e ta amana, Allah ya
taya mu rik'o."
Goggo tace
"Amin, daga cikin dukiyar da mahaifinta ya bar
mata a ciki ake siya mata su pampers da su
madara, sai kayan sawa da sauran abinda ba'a
rasa ba, amma ba kasafai nake amfanin da
kud'in ba sai idan ba kud'i hannuna, amma
tunda yanzu zata dawo hannunku da zama
sheyasa zan damk'a maka kud'inta a hannunka
ka adana mata ko ka juya mata su duk yadda
kaga ya dace."
Jiki a sanyaye Hamza yace
"Insha Allah Goggo."
Daga haka Goggo ta tashi ta had'o kayan Amina
tas sannan ta kira mai gadinta ya saka cikin
mota.
Sai da suka ci abincin rana sannan suka koma
gida, inda ko a mota Bilki ce ta rik'e Amina
sannan ga mamakin Hamza bata nuna komai ba
har rungume ta tayi tana fad'a ma Hamza d'iyar
ta shiga ranta sosai. Ba k'aramin sanyaya mishi
zuciya hakan yayi ba, duk wata fargaba dake
ransa ta kau yadda yaga Bilki na tarairayar
Amina kamar 'yar cikinta.
Bayan sun koma gida da daddare Bilki ta had'a
ruwan zafi tayi ma Amina wanka tas sannan ta
shirya ta cikin kayan baccinta wato overall pink
wadda tayi mata kyau, gashin babyn ya wani yi
irin pam d'innan sannan duk da haka a nannad'e
yake gwanin kyau.
Bayan ta gama ta had'a mata madararta ta bata
tasha ta k'oshi, sannan ta rirrigata ta tayi bacci,
duk akan idon Hamza wanda yake mata kallon
mamaki, abinda baiyi zato ba yau gashi Bilki
nayi.
Bayan ta rirriga Amina tayi bacci zuwa tayi kusa
da Hamza tana rok'on gafarar abubuwan da ta
masa, bai gasgata ba sai da ya ga Bilki na kuka
sosai tana rok'onsa, take ya yarda ta yi nadama
don haka sai ya yafe mata suka shirya.
Haka cikin dare da Amina tayi kuka Bilki zata
tashi ta bata madara har ta koma bacci, gashi
sam bata kukan dare yunwa kad'ai ke tashinta
da kuma an bata madara zata koma shikenan
kuma sai asuba.
Da safe ma haka tayi mata wanka tas ta bata
madararta, koda wasa Hamza bai yi tunanin
za'a samu wata matsala ba daga wurin Bilkin
ba.
Don haka sai ya saki jikinsa ya manta da
maganar k'arin aure.
Duk sadda Hamza ke gida to Amina na
hannunsa yana mata wasa, yana ce mata
"Meenah!" Ya bata madara, ya chanza mata
pampers, ya mata tsarki, sannan ya rirriga ta
har sai tayi bacci.
A haka har sunan ya bita don Hamza Meenah
yake ce mata idan yana mata wasa.
Watan Meenah biyar amma ta zama wata irin
k'atuwa tayi nauyi sosai, da k'yar ake d'aga ta,
ga bata wasa da abinci komai ci takeyi, sai
dad'a kyau takeyi kullum.
Hamza na matuk'ar nuna mata kulawa kullum
yana manne da ita especially weekends ranar da
ba aiki, baya zuwa ko ina zai zauna gida yana
kula da Meenah. Sannan komai yana siya mata
daidai gwargwado bai ta6a nuna gazawarsa ba,
tsaye yake kai da fata wajen ganin Meenah ta
taso cikin ingatacciyar rayuwa.
Watan Meenah bakwai daidai Bilki ta samu ciki,
Allah cikin ikonshi cikin baya bata wahala, murna
had'e da godiya ga Allah suka yi ba adadi.
Zo kuga zakwad'i da rawar kai wurin Bilki. Tun
cikin bai tasa ba ta fara siyayyar kaya kamar
hauka a 6oye, tasan Hamza zai bata kud'i idan
lokacin yayi amma tsabar son abin duniya yasa
bata iya hak'uri. Ko kuma ta d'auka idan ya aje
da yake bai ta6a tunanin tana masa sata ba
sheyasa bai farga ba, sai dai idan yaga kamar
kud'in ba daidai suke ba yayi ta tunanin yadda
akayi ya kashe su.
***
Faruk ne kwance bisa gadonsa na alfarma yayi
ruf da ciki yana game cikin system d'insa. Sai
yanzu na k'are ma d'akin nasa kallo, color d'in
d'akin dark da light blue ne, hartta gadonsa blue
ne da bed-sheet d'in da ke shimfid'e a sama.
Carpet d'in da ke shimfid'e a d'akin blue ne.
Gefe guda kuma study table ne shima blue, sai
cikin wata k'atuwar box kayan wasansa ne
wanda mafi yawa nafi hango jirgin wasa kala
kala, hartta kan gadonsa jirgin wasa ne yakai
biyar gefensa, d'aya kuma a hannunsa, a raina
nace to shi kuma son jirgi yake?
Mummy ce tsaye bakin k'ofa tana kallonsa kafin
kuma ta k'araso tare da zama a kusa dashi ta
dafa shi.
Juyowa yayi yana kallonta kafin yace.
"Mummy na."
Murmushi tayi tana shafa gashin kansa sannan
tace
"Faruk ya naga kana game? Ba nace kazo ka
koyi hardarka ba, ba gobe zaka bayar ba a
islamiyya?"
Murmushi yayi yace
"Nayi Mummy."
Tace
"Anya Faruk?"
Yace
"Allah yanzu na gama."
Tace
"Ok zo muje muyi dinner Daddy da Anisah (auta
'yar shekara uku) suna jiranmu."
"Ok." Yace a yayinda ya d'auki jirginsa ya bi
bayan Mummy....
MSB💖
AUREN FANSA 06
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹06 🌹
Kan dinning suka nufa inda Daddy da Anisah ke
zaune suna labari harda dariya, zama sukayi
itada Faruk
da Daddy ke musu fira a yayinda Mummy ta
zuba ma kowa abincinsa. Wurin kuma yayi tsit
sai k'arar spoon ake ji. Anisah ce ta katse shirun
ta hanyar jefo ma Daddy tambaya.
"Daddy idan na girma me zan zama?"
Daddy dake shirin kai loma a bakinsa ya dakata
yana kallon Anisah kafin kuma yace
"Anisah kenan, duk abinda kike so shi zaki zama
ay."
Anisah tayi dariya
"Ni banason na zama komai nafiso na shiga
aljanna."
Kowa a wurin sai da ya maida hankalinsa gareta
kafin kuma Mummy tace
"Insha Allah zamu shiga aljanna kinji ko?"
Mummy tace
"Abban Faruk ya batun baka manager d'in ko
sun fasa?"
Daddy yayi murmushi
"Ba fasawa sukayi ba Reemah, sai sun duba
cancanta kafin su bada, idan na dace a bani
manager zasu bani, idan kuma wani ya dace a
ba za'a bashi."
Tayi murmushi
"Haka ne kuma, nidai fatana Allah ya baka sa'a
a dukkan lamuranka"
Yaji dad'in addu'ar matarsa ba kad'an ba,
abinda ke k'ara masa sonta kenan kullum cikin
yi masa addu'a takeyi yana murmushi yace
"Amin ya Allah Reemah."
"Ka fidda ranar da zamu tafi Disney world d'in
kuwa?"
Reemah tace bayan ta had'iye abincin dake
bakinta. Daddy ya sha cup d'in Apple juice kafin
yace
"Eh zuwa upper week dai insha Allah lokacin su
Faruk sun gama exams a islamiyya."
"Yeeyy! Mummy Disney world zamuje da gaske?"
Mummy tayi murmushi tace
"Eh Mamana ko bazaki ba?"
Anisah ta zum6ura baki
"O'o ni zanje."
Faruk yace
"Kalle ta to baza'a dake ba."
Anisha ta sa kuka
"Daddy wai baza'a je dani ba?"
Daddy yayi murmushi
"Ya isa yace bazaki ba, ay kece head d'in tafiyar
gaba d'aya zamu iya barinsa amma ke bazamu
iya barinki ba."
Gwalo ta ma Faruk tana share hawayenta. Faruk
yasa dariya. Anisah tasa kuka.
"Mummy kinga Ya Faruk na min dariya ko?"
Mummy ta harari Faruk
"Zaka fara ko Baba na? Meyasa kakeson ganin
kukan k'anwarka ne?"
Yayi dariya
"Aww dariya ma kakeyi Faruk? Bazaka bata
hak'uri ba?''
Ya buga k'afa.
"Wannan 'yar yarinyar zan ba hak'uri? Tab
bazan bada ba."
Daddy yace
"Just say sorry Faruk, you know she won't stop
crying unless you apologize."
Mummy tace
"Oya Faruk now!"
"Ok sorry!"
Take ta bar kukan inda kuma ta cigaba da cin
abincinta kafin kuma ta kalli Daddy
"Daddy zansha ice cream."
Mummy tace
"Me nace miki akan zak'i?"
Anisah ta turo baki
"O'o ni zansha."
Mummy zata k'ara magana Daddy ya d'aga
mata hannu
"Ba ruwanki Reemah, zan siya mata ice cream."
Anisah tashi tayi da gudu ta wuce parlor tana
tsallen dad'i.
Daddy yayi dariya Mummy na taya shi tace
"Anisah kenan, badai rigima ba."
Daddy yayi dariya
"Lokacinta ne, kema kinyi naki ay."
Mummy tace
"Daddy Faruk fa na wurin."
Yayi dariya
"To sai me? Sai na fad'i abubuwan da kikayi ay"
Da sauri ta tashi tana fad'in
"Haba Daddy!"
Yayi dariya
"Kina tantama ne? Bari kiga..."
Kafin ya k'arasa tayi sama da sauri tana dariya.
Daddy ya tashi ya bi bayanta
"Guduwa kikayi Reemah!"
Faruk tsayawa kallonsu yayi yana dariya cikin
ransa yace
"Allah ka k'ara had'a kanmu what a lovely
family!"
***
Meenah na zaune kan carpet tana wasa da abin
wasanta haka kawai kuma sai tasa kuka, Bilki
dake zaune saman kujera tana shan rake tana
kallon wani movie da take so kukan Meenah ya
cika mata kunne. Tsawa ta daka mata
"Ke da Allah kiyi mana shiru yarinya sai shegen
kuka haba!"
Abinka ga yaro wannan tsawa da aka daka mata
ita ta firgita ta yasa ta k'ara fashewa da wani
irin kuka. Haushi ya cika Bilki yasa ta tashi tayi
shigewarta d'aki ta bar Meenah nan na ta faman
kuka kamar zata shid'e. Meenah tayi kuka
baiwar Allah har ta gaji. Nan ta kwanta k'asa
tayi ta ajiyar zuciya har baccin wahala ya
kwashe ta a nan.
Bilki na kwance a d'aki ta jiyo k'arar shigowar
motar Alhaji. Da sauri ta fito tazo ta d'auki
Meenah dake a k'asa ta rungume ta tare da
zama kan kujera tana rirriga ta.
Haka Hamza ya shigo ya same ta, da murmushi
a saman fuskarsa ya k'araso. Yana zama Bilki
ta kalle shi
"Sannu da zuwa Alhaji."
Yana murmushi yace
"Yauwa sannu da aiki Bilki, Meenah bacci akeyi?"
Tayi murmushi
"Eh wallahi yanzu ta gama rigima sai na rirrriga
ta tayi bacci."
Yayi murmushi
"Meenah kenan, ay batada rigima ma k'ila dai
baccin takeji daman."
Tayi yak'e
"Sosai ma ay Meenah baiwar Allah ce batada
rigima."
Yace
"Hakane Allah ya raya mana ita."
Tace
"Amin."
Yace
"Bari naje na watsa ruwa na gaji."
Tace
"Ok sai ka fito."
Tana ganin shigewarsa ta kalli Meenah taja
dogon tsaki, sannan taje ta kwantar da ita a
d'akin Meenah d'in kan gado.
Bayan Alhaji ya gama wanka suna zaune kan
dinning suna cin abinci ya kalli Bilki yace
"Bilki a gaskiya ba abinda zance miki sai dai
nace Allah ya saka da alkhairi akan aikin ladar
da kikeyi. Allah ya baki lada."
Ta kalli Alhaji tace
"Haba Alhaji meye na godiya ay yi wa kaine,
kuma ma Meenah kamar d'iyar dana haifa haka
na d'auke ta. Idan har kana min godiya sai naji
kamar baka d'auke ta a matsayin 'yar cikina
ba."
Yayi murmushin jin dad'i
"Wallahi ko kusa ba haka bane, kawai dai na
yaba da k'ok'arinki."
Tayi dariya
"Allah sarki. Uhm uhm Alhaji dama madararta da
pampers sun k'are shine nace ya kamata a bad
a siyo mata wasu."
Yace
"Wannan ba damuwa zan baki isashen kud'i ki
siyo mata wanda zai dad'e, naga kamar tafison
madarar ma akan abinci."
Tace
"Hakane."
Bayan sun gama ya d'auko kud'i har dubu goma
ya bata. Amsa tayi tace
"Shikenan zanje na siyo mata.
Yace
"Toh ko ki bari idan na fita na siyo mata mana."
Da sauri tace
"Kai haba kai ina kake da lokaci? Ni da nake
gida kullum ka bari zan siyo mata."
Yayi murmushi
"Toh shikenan."
***
Watan haihuwar Bilki ya kama. Kullum sai ta
tambaye shi kud'in siyayya bai ta6a hana ta ba
saboda har ga Allah ya d'auka Bilki ta shiryu.
Wata rana nak'uda ta kama Bilki gadan gadan,
Hamza ya kaita asibiti, suna zuwa ba'a jima ba
ta haifi 'ya mace. Kyakkyawa fara tas mai
k'oshin lafiya.
Haka aka cigaba da zaman barka inda komai
Hamza yayi mata daidai gwargwado komai yana
tafiya daidai.
Ranar suna yarinya taci sunan kakarta ta wurin
Hamza wato Fatima. Haka aka gama taron suna
aka watse lafiya kowa ya koma gidansa....

AUREN FANSA 08
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
Another page for my Ummi Aisha thanks for all
the support and care one love dear💖Allah ya k'ara
basira Amin🌹
🌹08 🌹
Laila ce ta cigaba da magana.
"Ko dai har yanzu baki fahimta ba ne?"
Ajiyar zuciya Bilki tayi, sannan tace
"A gaskiya Laila ban iyawa, kisa fa kika ce? Don
ina son dukiya sai akace na kashe su, gaskiya
mu chanza shawara dai."
Laila tayi kwafa.
"To sai akace mu zamu bisu mu aikata
k'udirinmu? Ko kusa ba haka nake nufi ba,
abinda nake nufi a nan shine..."
Nan naga ta rad'a mata wata magana daga
k'arshe dukkansu suka kwashe da dariya.
Bilki tana dariya tace
"Shegiyar gari, lallai Laila sai dai a barki amma
ke shu'uma ce wallahi."
Hajiya Laila ta k'yalk'yale da dariya sosai
sannan tace
"Kema haka."
Bilki ta tashi tana gyara zaman d'ankwalinta
tana kallon Laila tace
"Kamar naji kuman Zarah bari na dubo ta."
Laila tace
"Yi sauri kuwa nima naji."
Jim kad'an sai ga Bilki ta shigo da Zarah a
hannunta da alama yanzu Zaran ta tashi daga
bacci, tana zuwa Laila ta mik'a hannu ta fara
mata wasa, can sai ga Meenah ta fito da alama
bacci ta tashi don kuwa kanta buzu buzu yake,
saboda yanayin gashinta mai cika kuma ga
tsawo sheyasa ko ya ta kwanta sai yayi buzu
buzu. Zuwa tayi kusa da Bilki tana murza idanu.
Su kuwa sai faman ta6e baki sukeyi. Meenah
tace
"Maama wunwa."
Laila ta ta6e baki tace
"Uban me tace?"
Bilki tace
"Ohon mata, ke tafi can ki bamu wuri."
Abinka ga yaro da ba ganewa tayi ba, sai ma ta
matso kusa da Bilki ta jingina da ita. Da sauri
Bilkin ta hankad'e ta gefe ta fad'i k'asa tim!
"Wannan yarinya anyi mayya! Mts." Cewar Laila
had'e da jan tsaki.
Bilki ta jawo hannunta da k'arfi, Meenah ta
fashe da kuka.
Kitchen suka nufa ta had'a mata tea a cup tana
tsaki sannan ta dire mata k'asa.
"Oya zauna kisha yarinya bata aje komai ba sai
ci? Haba!" Nan ta zauna ta shanye tas sannan
ta fito daga kitchen d'in.
Tana gama fad'an haka ta fice taje ta had'o ma
Zarah cereal ta koma parlor, Laila ke bata har ta
kammala sannan aka bata ruwa.
A tare suka girka abincin rana inda Laila tayi ma
Zarah wanka, sannan suka dafa fried rice da
papered chicken sai had'ad'en salad. Wuraren
uku da kwata Laila tayi sallama da Bilki ta tafi
gida.
Sai wurin biyar saura sannan Bilki tayi ma
Meenah wanka ta bata abincin rana.
Kamar kullum bayan Alhaji ya dawo gida yayi
wanka yaci abinci, suka zauna palor suna 'yar
fira kafin a kira sallar magrib. Kasancewar
Meenah batasan dawowar Baban nata ba, tana
can d'aki tana wasa. Sai data fito, aiko tana
ganin shi ta rugo da d'an gudunta ta zo kusa da
shi tana fad'in
"Dada!"
Cike da jin dad'i Alhaji yace
"D'iyar Dada ashe ana ciki, zo nan."
Tana zuwa ya d'auke ta ya zaunar kan cinyarsa
yana mata surutu tana dariya. Can kuma sai
tace
"Dada kaga Maama ta bije ni d'azu."
Ya ware idanu
"Me kikayi wa Maama ta bige ki?"
Tayi shiru tana kallonsa can tace
"Bakomai."
Bilki ta taso tana dariya tace
"Kai yaro ma dai daban ne, d'azu ne fa na shiga
wanka nazo na iske ta tana zubar da madara,
shine fa nace mata kar ta k'ara. Alhaji yayi
dariya
"Ah ah Meenah a daina 6arna ba kyau kinji ko?
Idan Maama tace a daina a daina kinji?"
Ta gyad'a kai. Sai kuma yace
"Bilki ya naga Meenah ta rame ne ko bata son
cin abinci?"
Tayi dariya tace
"Ay Alhaji inda kasan yadda nake da fama da
yarinyar nan akan taci abinci ko? Sai kayi
mamaki sam batason ci na rasa dalili."
Yace
"To kuma ya baki sanar dani ba? Muka sani ko
wani abin ke damunta? Kinsan yaro tunda ba
fad'a zatayi ba."
Tace
"To k'ila dai."
Ya juyo da dubansa ga Meenah
"Haba Meenan Dada, meyasa baki cin abinci?"
Nan ma shiru. Yayi murmushi
"Zaki sha ice cream?"
Nan take da washe baki tana murna. Shima yaji
dad'i yace
"Yauwa to bari idan na fita yanzu kafin na dawo
gida zan siyo maki harda biscuit ma."
Saukar da ita yayi daga cinyarsa yace
"Bilki bari na wuce masallaci lokacin sallah yayi
sai na dawo."
Tace
"A dawo lafiya."
Sai da ya fita ta bishi da harara dashi da
Meenah dake tsaye a tsorace gaban Bilki.
Tana huci tace
"Gaskiya abinnan ya fara isa ta, sai wani nan
nan yake da yarinyar nan amma naga ba
ruwanshi ma da Zarah, lallai Alhaji ka haifi d'iya
a cikinka amma ka nuna son d'iyar wata? To da
sake mts."
Daga nan ta shige d'aki, Meenah na tsaye tana
zare idanu.
Haka kuwa akayi Alhaji da zai dawo sai da ya
tsaya ya siya ma Meenah ice cream da biscuit
sai ya k'aro mata kayan lashe lashe na yara.
Zarah kuwa wani d'an abin wasa ne na yara ya
siya mata tunda yasan bata isa shan wad'annan
kayan ba.
Yana dawowa Meenah ta tare shi tana murna,
ya bata ice cream d'inta nan ta zauna ta shanye
tas sannan ya bata biscuit d'inta ta tafi d'aki.
Abin wasan yara ya bama Zarah dake hannunsa
yana mata wasa. Ita kuwa sai dariya takeyi.
Bilki na zaune kusa dasu tana wasa da Zarah.
Can Alhaji yace
"Ina Meenah tayi ne?"
Tayi tsaki a ranta tace
"Yanzu ta tafi d'aki ay ta ga k'wad'ayi kuma
tunda bazata ci abinci ba."
Tashi yayi yana fad'in
"Ina zuwa."
Ta6e baki tayi tana mai jin haushin Meenah.
Yana shiga d'aki ya ishe Meenah kwance k'asa
da biscuit a hannunta bacci ya kwashe ta.
Murmushi yayi ya d'auko ta ya d'ora ta kan
gado, ya gyara mata kwanciya sannan ya kashe
fitilar ya fito.
Koda ya fito Bilki bata nuna komai ba, Zarah ta
k'ar6a tayi d'aki da ita don yi mata wanka.
BAYAN KWANA BIYU
Bilki ta fito wanka da safe kiran Laila ya shigo,
tana d'auka Laila tafara magana
"Kash Hajiya Bilki yanzu naji labarin iyalen Alhaji
Adam sun koma Abuja gaba d'aya."
Da sauri Bilki tace
"Haba dai? To yanzu ya kenan?"
"Bansani ba nima, plan d'inmu ya rushe don
gidansa na Abuja akwai tsaro sosai, ko ina sojoji
ne a gidan."
Bilki tace
"Gaskiya akwai had'ari mu ce zamuyi wani motsi
yanzu. Amma ki bari tukunna a sake shawara."
"To shikenan." Laila tace tare da katse kiran.
Nan tayi ta sak'a da warwara ta rasa mafita.
***
Haka rayuwar ta cigaba da gudana har akayi
shekara d'aya amma har yau sun rasa wata
mafita.
A lokacin kuma Meenah ta shekara biyu harda
rabi Alhaji ya fara shirye shiryen saka ta
makaranta da kuma islamiyya. Don ya fuskanci
zata iya da wuri don a yadda ya fahimce ta, ta
iya saurin d'aukar abu da kuma maganarta ta
fito ga surutu ba abinda bata fad'i.
Sheyasa ma yanzu Bilki ta rage takura mata don
muddin Alhaji ya dawo zata kwashe komai ta
fad'a masa. Tana gudun kar tun baya tunanin
komai har ya fara zarginta...



AUREN FANSA 09
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹09 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Haka kuwa akayi washe gari da safe Hamza da
Bilki suka fita don saka Meenah a makaranta.
Gobarau Academy itace makarantar da suka
nufa, da zuwansu da komai basu wuce minti
talatin ba aka kammala komai aka saka ta Pre
nursery, duba da shekarunta kuma a k'a'idar
makarantar idan yaro bai kai shekara 3 ba to
baza'a saka shi nursery ba daman. Daman 'yan
pre nursery ba'a saka musu uniform.
A ranar aka barta makaranta kuma ko kuka
batayi ba da su Hamza zasu tafi don ta samu
abin wasa sai dad'i takeji.
K'arfe 12 suke tashi don haka dole Bilki ke
d'auko ta don Hamza na wurin aiki lokacin, ba
yadda ta iya haka nan take hak'ura tana d'auko
ta d'in.
Haka rayuwar ta cigaba da gudana cikin hukunci
da hikimar ubangiji, Meenah har ta shiga
nursery. Meenah Allah ya bata k'walwa komai
aka koya mata ta iya sai dai idan ba'a koya
mata ba, kuma idan ta dawo gida ta dinga yi
kenan ko gajiya batayi.
Ba'a saka Zarah makaranta ba sai da Meenah ta
shiga nursery 2 a lokacin ita kuma Zarah tana da
shekara 3 a duniya yayinda Meenah keda hud'u.
Ranar wata juma'a akayi ma su Meenah hutu
suna zuwa gida Meenah ta fara neman babanta
don nuna mai report card nata, sai
dai rashin sa'a yayi tafiya zuwa Lagos a safiyar
ranar, tayi ta kuka tana kiran ita Baba.
Bilki tana tsaki ta ansa report card nata dana
Zarah tana dubawa, abin takaici a wurinta wai
Meenah na d'aya tayi ita kuwa Zarah na ashirin
tayi cikin su ashirin da shidda. Bilki kamar tayi
kuka don takaici. Wato Meenah dai tafi d'iyarta
k'ok'ari kenan?
"Gaskiya da sake!" Ta kalli Meenah tace mata
"Ke! Zo nan!" Meenah tayi tsaye idanunta k'wal
hawaye a duniya tana tsoron Bilki, fizgo ta tayi
da k'arfi.
"Ke dan ubanki sai da kika yi na d'aya wannan
karon ma? Kin manta bugun da nayi maki last
term kenan? Salon kija babanta ya dawo ya
zane Zarah ko? Ke ga mai k'ok'ari ko? Shegiya
mai kama da mage! Wuce ki bani wuri!" Da gudu
Meenah tayi d'aki tana kuka sosai, jawo Zarah
tayi ta rungume tace.
"Don Allah d'iyar Baba ki dage kifi waccan
yarinyar k'ok'ari kinji?" Zarah ta gyad'a kai.
Da rana ta zuba ma Zarah abinci ta shiga
wanka, Meenah na zuwa Zarah tace.
"Zo muci." Ba musu ta zauna suka fara cin
abincin tare.
Ba'a jima ba Bilki ta fito wanka tana lek'owa
taga Meenah nacin abin da d'iyarta abinda ta
tsana! Da tsawa tace
"Ke!" A firgice Meenah ta tashi tana kyarma,
Bilki ta k'ara daka mata tsawa.
"Bana hana ki cin abinci tare da Zarah ba?
Shegiya wuce ki tafi d'aki." Tayi d'aki da gudu a
tsorace. Zarah ta aje cokalin hannunta tace
"Bazan ci ba nima sai da Meenah." Daman Bilki
tasan abinda zatace kenan, tsaki taja tace
"To sai dai kar kici wallahi amma bazakici tare
da Meenah ba, kinji na fad'a miki!"
Aikuwa aje cokalin tayi tana fushi sosai ta bar
parlon. Tsaki Bilki ta k'ara yi tana k'ara jin
haushin Meenah...
***
Sauri yakeyi ya dawo gida don nuna ma iyayensa
result nasa na shedar kammala jss3 nasa. Driver
na yin parking ya fito da gudu yana murna
shigarsa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga
masa hankali, ya kuma gigita shi a lokaci guda,
take zuciyarsa ta fara bugawa da sauri a
yayinda k'walwarsa ta tsaya cak! ta bar aiki
lokaci d'aya!!!
Iyayensa ne kwance jina jina, a yayinda wasu
mutane kusan su bakwai ke tsaye cikin
bak'ak'en kaya hartta fuskokinsu an rufe da
black mask!
Tsaye yayi ya kasa tantance a wace duniyar
yake, take kuma ya fashe da kuka yana fad'in.
"Su waye ku? Mey...asa ku...ka kashe min
iyaye?"
Direwa yayi k'asa yana kuka yana jijjiga iyayen
nasa a yayinda yake kiran Anisah! Mutumin yayi
dariya yace.
"Ka bar kuka yaro, sun tafi inda ba'a dawowa
kaima kuma yanzu zaka bisu!" Yakece da dariya
sannan ya saita bindigar daodai saitin k'irjinsa
ya harba.
A gigice ya farka duk da Ac d'in da ke aiki amma
hakan bai hana sa yin sharkaf da zufa ba. Ta6a
jikinsa ya soma yi amma baiga jini ba, ajiyar
zuciya ya sauke ya shiga yin addu'a don ba
k'aramin tsoro yaji ba.
"Wane wane irin mafarki ne haka..... ?"
Ya fad'a yana mai k'ara tunawa da mafarkin da
yayi. Zumbur! Kuma ya mik'e ya fice da gudu
don duba lafiyar iyayensa don gani yake kamar
da gaske ne....!

AUREN FANSA 10
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹10 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
"Mummy...! Mu.." A firgice suka farka daga
bacci, da mamaki suka ce
"Waye?" Kasancewar d'akin gauraye yake da
duhu fitila a kashe take, Daddy ya kai hannunsa
ya kunna bedside lamp yana kallon Faruk dake
tsaye, da sauri Faruk ya rungume mahaifiyar
tasa yace.
"Alhamdulillah! Ashe duk lafiyarku lau, wallahi
naji tsoro."
Mummy tayi murmushi don tasan ya k'ara yin
mafarki. Tace
"Faruk nasha fad'a maka mafarki ba gaskiya
bane ka daina d'aga hankalinka akan mafarki,
nasha fad'a maka bakaji."
Faruk yace
"Nasani Mummy amma meyasa a duk lokacin da
nayi mummunan mafarki sai naji gabana ya
fad'i, sannan na kasa samun nutsuwa, gani nake
kamar wani abu na shirin faruwa da mu!"
Daddy yace
"Haba Faruk! Ka zamo mai tawwakali mana, an
fad'a maka mafarki ba gaskiya bane haba! Tashi
kaje ka kwanta."
Sum sum ya tashi ya fice, Daddy ya kalli
Reemah yace.
"Wai shin kuwa yaron nan na addu'a a duk
lokacin da zai kwanta bacci?"
Reemah tace
"Yana yi, kullum sai na je na tabbatar da sai
sunyi addu'a kafin su kwanta su duka."
Daddy ya numfasa yace
"To Allah ya kyauta amma sai ya k'ara dagewa
da addu'a sosai."
Reemah tace
"Insha Allah."
***
BAYAN WATA D'AYA
Zaune yake yana karatu wayarsa ta fara k'ara,
ganin sunan Daddynsa yasa yayi saurin
d'agawa.
"Hello kaine Faruk?"
Yace
"Eh nine lafiya ina mai wayar nan?"
"Sai dai kayi hak'uri mai wayar nan ya rasu
dashi da matarsa!"
"What? Innalillahi wa'inna ilahir raj'un!"
"Ya Faruk!"
A firgice ya farka ganin Anisha tsaye gabansa
tana kakkarwa, yasa yace
"Ke lafiya menene?"
Ta fashe da kuka.
"Mummy! Ya Faruk Daddy da Mummy babu."
Yace
"Kamar ya? Ina suke?"
Tace
"Wasu mutane na nan sun zagaye Mummy da
Daddy..."
Kafin ta k'arasa ya mik'e da gudu ya fita."
Zuwansa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga
masa hankali lokaci guda kuma ya gigice ya
shiga rud'ani! Murza idanunsa ya fara yi don
yayi tunanin wannna karon ma mafarki yakeyi,
la6ewa ya shiga yi a bakin k'ofa yana sauraren
mutanen da ke tsaye. Kusan su hud'u majiya
k'arfi.
"Hello Hajiya Laila Sunusi! Aikin da kika samu fa
an kammala abu biyu ya rage. Na farko bamuga
yaransu guda biyu da kika lissafa mana ba! Na
biyu takardun gidannan da sauran mahimman
takardun da kika ce a baki."
"Yes Ma! Ok Ma! Insha Allah na miki alk'awarin
cika miki dukkan aikin da kika
samu da ke da aminiyarki ya sunan ta ma?
Haha yes Bilkisu Ringim! Ok..."
Kamo hannun Anisah yayi yana kuka d'akinsa ya
fad'a ya kwashi wasu takardu nasa dashi dana
Anisah na makarantarsa da abubuwan da yake
buk'ata ya jefa jikka suka fito da sauri sukayi
hanyar fita. Anisah na kuka shima yana kuka
suka fito gate, gaba d'aya masu gadinsu basu
nan, security sunfi goma amma yanzu bai ga
kowa ba. Adaidaita ya samu suka wuce wata
police station, yana zuwa ya fad'a masa dukkan
abinda ya gani ya kuma ji sannan yace suzo su
ceci iyayensa kafin su mutu.
Ba 6ata lokaci suka nufo gidan sai dai da
zuwansu abin mamaki ba komai gidan asali ma
gidan a rufe yake da kwad'o sai dai gawar
iyayensa, nan akayi examining d'insu aka
tabbatar da basuda rai, take Faruk ya rasa a
wace duniyar yake, kansa yayi dip, hawaye kuwa
kamar an bud'e pampo. Sambatu kawai yakeyi
yana fad'in.
"Daman nasha yin mafarki an kashe mana iyaye!
Nace abin kamar zai faru amma ba wanda ya
kula ni..."
Duk police d'in da yayi yunk'urin tab'asa da
niyyar rarrashi turesu yakeyi suna fad'uwa k'asa,
gaba d'aya kamar ya zauce. Yama k'i nutsuwa
asan ina danginsa suke a sanar masu de abinda
ya faru. Gaba d'aya gidan ba mota ko d'aya,
motocin mahaifinsa sunfi kala takwas amma
yanzu ko d'aya babu.
Nan kuma kan Faruk ya fara juyawa kafin ya
ankara ya fad'i k'asa tim!
AUREN FANSA 11
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹11 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
A hankali ya bud'e idanunsa bakinsa d'auke da
salati, sai kuma ya fara kiran
"Mummy! Daddy! Wai da gaske ne an kashe su?
Ina Anisah? Wallahi duk wanda ya kashe

Please Login or Register in order to submit comment