Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Farida ta saki, tana toshe bakinta, nuna inda Amal take, Amal d'in ta wani tashi kanta a karkace hannuwanta sun lauye hatta k'afafuwanta sun bandare, wani kalar jini bak'ik'k'rin dashi yana dalalar mata a baki, wani irin shegen gunji take tana wage bakinta dake d'auke da wasu tsiraran hak'ora irin na horror masu shan jini, bakin nata kanshi ya koma baki gaba d'aya kalarta ta gaba sauyawa daga D'an Adam zuwa dodo.

Gaba d'ayansu zabura sukai suna duban Amal data zame masu abun tsoro.
An rasa wadda zai fara fita daga motar, gashi Zombies kamar k'ara Koro su ake inda motarsu take a tsaye, daga can gaba kuma Faruk ganin haka ya tayar da Motar yana zan wani uban birki yaba Motar wuta, suna jin yadda Zombies ke wani irin ihu yadda Faruk d'in kebi ta kansu yana latsewa.
Suda ke baya kuma fad'uwa sukai a sadda yaja birkin da k'arfi, da wani mahaukacin sauri su duka suka zabura suka mik'e ganin yadda Amal ke neman kawo masu farmaki.

Allah ya bata sa'a ta kamo k'afar Doctor d'in Mace dake jikin namijin d'an uwanta, wadda suka shigo motarsu suna gaf barin Asibitin da aka kwantar da Faisal.

Wani razanannan ihu had'e da wata irin murya mai k'arfi ta kama cewa.

"Na shiga uku na, ku taimaka min karta shafa min cuta wayyo Allah zata kashe min rayuwa, Ina ji ina gani wayyo wayyo wayyo Allah na".
Da harshen turanci take fad'ar Hakan.

Abunda take iya fad'i kenan Doctor d'in, iya k'arfinta take furta Hakan.

Gaba d'aya an rasa wadda zai nufi inda suke, shi kansa Al'ameen mai tada jijjiyoyin wuya akan Amal d'in ya kasa koda motsawa daga inda yake, ido a waje yake duban Amal dake son kaima Doctor cizo da bala'i.
Ai d'ayan Doctor d'in da suke a tare bai san lokacin daya fara waige-waige ba, yana son gano wani makami domin cetan y'ar uwarshi ba.

Ai ko yana cikin dube-dube ya hangi wani k'arfi mai kauri a cikin Motar, yasa k'arfinsa ya fisgo shi bai tsaya wata-wata ba, ya d'aga shi sama yana ihu iya k'arfinsa saboda k'arfin yana da wani irin shegen nauyi, dan da kyar ya daga shi, ya kuwa sauke ma Amal shi a tsakiyar kanta, nan take kamar kyaftawa da Bismillah kanta ya rabe gida biyu, jininta yayi wata irin tsartuwa yana feshe na kusa da ita akan fuskarsu, ko shurawa Amal batai ba nan take ta zube babu rai a tare da ita.

Gaba d'aya zan iya cewa wa'inda ke wajan sumen tsaye sukai gaba d'aya sun runtse idonsu zuciyoyinsu na harbawa da k'arfin gaske, zufa na tsiyayo masu ta kota ina a jikinsu.

Farida zan iya cewa nan take ta sulale ta zube ta sake wani sumen.
Al'ameen ko kamar wadda aka zarewa rai a tare dashi, domin yana tsaye ne amma baya motsi.

Sai zuwa can suka ji ya fasa wata gigitacciyar k'ara ya zube a wajan shima a sume.

Duk wadda keda sauran motsi a cikin Motar sunyi jingum-jigum kamar basa numfashi suma, ido kawai ke motsi a tare dasu.

Hanan ce ta fara fasa wani irin azababben kuka mai tab'a zuciya, tana sa tafukan hannunta ta rufe fuskarta dasu, wani irin kuka take na tsananin tausayin Amal da rasata lokaci guda da sukai. Mi zasu gaya ma Abbie?, ya ma za'ai su fara tunkararshi da maganar babu Amal a fad'in duniyar nan a yanzu?, to suma suna da tabbacin zasu bar Goa a raye ne?, mi yasa basuyi dogon tunani ba kamin suyi tafiyar nan?.
Muryarta na rawa da kuma kuka take fad'in.

"Wayyo Allah na, ashe Aunty Anam abunda kike hango mana kenan na wannan tafiyar ba alkhairi ba ce?, kika so hana tafiyar nan dani, mi yasa Aunty Anam baki kulle ni d'aki kika bige ni ba, ko k'ila na fahimci abunda kike hango mana?, shikenan nasan nima mutuwa zanyi wallahi tunda naga gawar Amal nasan nima tafiya zanyi inda taje".

Ta k'are maganar bakinta na rawa wajan furta kalmar.

Kusan gaba d'ayansu maganar da Hanan d'in keyi ta saka su kuka, domin daka kalli gaba d'aya fuskokinsu hawaye ne ke kwaranya akansu.

Doctor d'in nan data mik'e tana rungume d'an uwanta likitar nan, sai kuka suke suma, duk da sunji da Yaran da Hanan d'in tayi magana da Hausa tayi, basu ji miye take cewa ba, to amma yanayin yadda take kuka tana jijjiga take maganar, zaka san mai tab'a rai ce.

Faruk dake baya ya sami wani waje inda ba Zombies sosai ya faka, jin shuru a bayan Motar ya b'alle marfin Motar ya fito, yana bige wani Zombie dake son kamo hannunsa, shi kad'ai ya gani a kusa, sai wasu tsiraru dake nisa da inda yayi parking d'in motar, da sauri ya b'alle marfin ya shige gidan bayan.

Juyowar da zaiyi bayan ya mai da marfin ya rufe, kawai ya hangi tashin hankalin dake yashe a k'asa, ga gawar Amal data yi raga-raga Kwakwalwar kanta ta fashe jini mai yawa kalarsa bak'i na zuba a tsakiyar motar.
Sai Al'ameen dake zube a sume.

Zan iya cewa Faruk Kwakwalwarsa ta kusa zarewa domin girgiza kai ya rink'a yi yana wani murmushin daya fi kuka ciwo, yana nuna Amal yana magana marar kan gado yana cewa.


"Kai amma dai Amal wasa kike ko?, ki tashi ki maida kwanyar kanki mana, mi zai sa ki cirota daga kanki, kina son mutuwa ne?, tashi mana. Kai kuma Al'ameen daga shigowarka bayan Mota sai kaje kayi zamanka?, au bacci ma kike kenan?, to Maza ka tashi kaima ko mun bar wajan nan".

Wani irin kuka mai sauti Jasmin ta fashe dashi itama, Hanan da Anjali na taya ta ganin Faruk na son haukace masu.

Anjali ce ta kamo shi tasa shi a jikinta tana tallafe kansa take magana.

"Dan Allah Faruk karka birkice Amal ta mutu bazata dawo ba, shi kuma Al'ameen suma yayi, ba sai na tsaya ina maka baya ni ba, Kasan an riga da an Ciji Amal tun kan mu baro Asibiti, dan Allah ka dawo hayyacinka".

D'ago kansa yayi daga jikinta, yana girgiza kansa wasu zafafan hawaye suka shiga zuba masa.

D'ukewa yayi k'asa yana sakin kuka mai sauti, d'aga kansa yayi sama yana kurma wani uban ihu.
Kamin ya dawo da dubansa inda gawar Amal take.

Nunata yake yana cewa.

"Ya zaki mana haka Amal?, mi kike so muje mu gaya Abbie?, mi yasa da kika kamu da cutar baki zo gare ni ki cinye naman jikina ba?, bazan iya hanaki ba ai, mi yasa baki cije ni ba?, muka koma iri d'aya, why why why why Amal?".

Yadda yake kuka jikinsa na jijjiga had'e da wata irin kyarma da jikinsa keyi yasa Anjali jawoshi jikinta ta rungume suna kukan a tare.

Jasmin ce mai k'arfin halin d'aukar wani sauran ruwan da Anjali ta tab'a watsama Farida a sadda tayi suman farko, ta d'akkosa ta watsama Al'ameen shi, amma shuru bai tashi ba, ta kusan k'are ruwan a jikinsa, da kyar yaja wani lumfashi, yana bud'e idonsa akansu.

Matsawa tayi tana watsama Farida itama akan fuskarta, sauran ta d'aure gudun sake suman wani a cikinsu.

Kallonsu kawai yake yana binsu dana mujiya, kamar ya fice daga hankalinsa kwata-kwata shima, domin wani murmushi ya rink'a jifansu dashi yana duban gawar Amal shima yana magana yana nuna Faruk dake jikin Anjali da ya d'an zame yana kallon d'an uwansa daya farka, zuciyarsa cike da tsananin tsoron kar D'an uwansa ya haukace gaba d'aya, gara shi ya d'an dawo tunaninsa amma ba sosai ba.

"Faruk kana gani wai Amal wasa take mana da hankali, ka ce mata ta tashi dan Allah, miye hakan take yi?, ji wani abu data shafa akan fuskarta tana mana wasa, ka ce mata bamu saba irin haka da ita bafa".

Wani irin rauni ne ya rufe Faruk yana kallon Al'ameen dole tasa ya danne duk wani tashin hankali da yake ciki yabar jikin Anjali ya matsa inda d'an uwansa yake ya rungumesa yana basa baki, amma kamar sake hautsina Kwakwalwarsa ma yake, hauka fa tuburan Al'ameen ke neman yi gaba d'aya.

A gefe guda kuma Farida na farkawa batai wani ihu ba, sai binsu da take da kallo, jin abunda su Al'ameen ke cewa da ganin yadda Al'ameen Kwakwalwar kansa kwancewa yasa Farida sakin kuka mai sanyi tana curewa waje d'aya, gaba d'aya tausayin kansu da kansu ne ya rufe mata jiki da ruhi, wannan wacce irin masifa ce haka?, wacce irin jarabawa ce Allah ya jarrabe su da ita?.


Faffasss fafffassss fasss kake ji had'e da wani gunji marar dad'in sauti ke k'ara kusanto inda suke.

Kamin ma suyi wani yink'uri kamar an harbo wasu dondozen Zombies masu yawan gaske suka yayyab'e Motar, kamar had'in baki tako ina tururuwar haye motar suke.
Da k'arfin da Allah ya zuba masu suke shirin kifar da motar gaba d'aya.

Wani irin sabon tashin hankali ya rufe na cikin motar, duk da haka har yanzu Al'ameen hauka yake yana fad'ar wasu kalami marassa kan gado.
Hanan da Jasmin kuka suka sake fashewa dashi suna k'ank'ame samarinsu, har suna had'a baki wajan cewa.

"Dan Allah ku taimaka mana mubar wajan nan, kunga fa sun gama yayyab'e mu, gashi babu kowa a gaban motar, shikenan mun mutu wallahi".

Farida ma k'ara curewa waje d'aya tayi jikinta na rawa, sai wani irin kyarma jikinta keyi tana girgiza kai, dan itama ji take kamar Kwakwalwar kanta nasan haukacewa.
Faruk ne yayi jaruntar tashi yana mik'ama Anjali Al'ameen ta rik'eshi, domin ko iya tsayuwa baiyi.
Kamin yayi wani uba, kawai suka ga an jirkitar da motar su, ta kife a k'asa.
Gaba d'ayansu suka fad'i a tsakiyar motar suna k'undun bala, har suna bigewa da junansu da kuma jikin Motar.

Gummmmm wata k'ara Farida ta saki jin yadda ta bige a goshi a sadda motar ta jirkice da su, tafe take da wajan, tana sa d'ayan hannunta tana dafe inda take kwance.

Faruk ne yayi k'arfin halin sake mik'ewa a jirkicen da suke, bakin window d'in motar ya rarrafa ya nufa, rik'e da k'arfin da Doctor d'in nan ya kwad'ama Amal shi. Ya bud'e ya fito, kamar jira Zombies suke suka yayyab'e shi.

Jikinsa rabi na cikin motar sai rabi na a waje.
Iya k'arfinsa ya yakice wasu, ya dage yana d'aga k'arfen da k'arfi ya rink'a kwad'ama duk wani Zombies dake yayyab'e da jikin Motar.
Ya d'auki lokaci suna yak'i da Zombies d'in, kamin Allah ya basa sa'a ya d'anci galaba akansu.

Da sauri ya koma cikin motar yana basu umarnin kowa ya fito daga motar ta window d'in daya fara fita, sunyi sauri da hanzairin barin cikin Motar domin gaf take da kamawa da wuta.

Shine ya fara ficewa da Al'ameen, sai su Jasmin dasu Farida.

Gefe d'aya suka tsaya suna gani Motar ta kama da wuta gawar Amal na ciki.

Sai lokacin Al'ameen ya saki wani kuka mai sauti yana d'ukewa k'asa.

Babu wadda ya ce masa danmi yake kukan?, saima suka rabu dashi yayi mai isarshi.

Sun dad'e a tsaye a wajan, kamin da sauri kamar an tsikari Faruk ya kamo hannun d'an uwansa, suka fara tafiya, taka k'afarsu kawai suke duk inda suka sa gaba, basu san inda suke nufa ba, tafiyar kawai suke cike da tsananin tsoro, danma a haka wai asuba ta kusa yi masu.

Sai zuwa yanzu ne ma Farida taji y'an cikinta sun kad'a jin wata irin azababben k'ishirruwa da mak'oshinta ya bushe k'amas ko miyau babu sosai a bakin nata, sai kuma yinwar data ke ji a yanzu, duk da bata ji yinwar ba, sai yanzu da k'ishirruwa ta addabe ta, yo dama idan kana cikin tashin hankali wata yinwa ai ba ta ita kake bama.
Dafe cikin nata tayi jin yadda ya d'aure mata waje d'aya, a d'uke take tafiya, tsabar wata azaba da cikin nata ke mata a yanzu, ga sallolin dake kansu bata jin tunda suka shiga wannan iftila'in sun tuna da sallah, sai ita da abun ke damunta a ranta.

Kamar ance ta waiga ta hango wani gida d'an k'arami, da aka gama canza masa kamanni, duk an fasa gilassanshi na jikin widows dake gidan, duk an faffasa su, hatta jikin bangon gidan jini ne ke zuba, suna tafiya suna taka gawawwakin jama'a wa'inda Zombies suka gama dasu.

Da sauri batai nauyin baki ba wajan cewa.

"Please y'an uwa ga wani gida can a can, muje dan Allah ko sallah muyi, mu rok'i Ubangiji daya kawo mana d'auki, mu rama sallolin dake akanmu".

Yamutse fuska Jasmin tayi tana d'an dafe cikinta itama jin wani k'ungin yinwa daya yi mata itama.

Ba wadda ya ce k'ala suka nufi gidan, zuciyarsu na fargabar shiga cikinsa.

Farida ce tayi namijin k'ok'arin bud'e k'ofar gidan, da aka gama k'aryawa tana dafa k'ofar ta fad'i a wajan, har sai da suka d'an matsa daga jikin k'ofar gidan.

Shiga sukai suna faman dube-dube, zuciyarsu ta d'an buga lokacin da suka yi tozali da Gawar mutum biyu a cikin gidan, wani Yaro ne shida Mahaifiyarsa daga gani, gawar tasu yashe a k'asa sai gawar wani mutum da suka hanga a yanzu zaune akan kujera, gawawwakin nasu bama kyan gani kwata-kwata, domin wani an cire masa ido d'aya an yayyaga fatar fuskarsa ba kyan gani, gaba d'aya jini yayi dame-dame akan fuskarsu, kai gaba d'aya ma halittar da Allah ya zuba masu an sauyata zuwa abun tsoro.


Da kyar suka samu suna neman inda zasu zauna, Farida ko batai Sanya ba, ta nemi ban d'aki tana shiga ta saki wani ihun daya jawo hankalinsu, Anjali ce tayi saurin nufar toilet d'in. Ganinta a tsaye ta rufe bakinta tana ihun, ta kai dubanta ganin Gawar wata mace ta gani a toilet d'in babu kyan gani, domin gawar tata tafi ta sauran Muni wacce suka gani a parlon gidan.
Hawaye kawai Farida keyi tana kuka dafe da bakinta.
Sauke ajiyar zuciya Anjali tayi tana dafe da k'irjinta, bata ce mata komai ba, ta dawo zuwa parlon, ganin yadda duk suka shiga halin tsoro, yasa ta d'an masu jawabin babu komai su kwantar da hankalinsu.

Zata iya cewa kusan duk taji irin ajiyar zuciyar da duk suka sauke kusan a tare.

Tana gani Jasmin ta nufi kitchen d'in gidan, ta d'an samu biskit tana ci su duka ma abun tab'a baki suka samo suka d'an tusa a cikin nasu, ba dan suna jin dad'insa ba, sai dan kawai su kori yinwar dake sasak'ar y'an hanjin cikinsu.

Farida da kyar ta fito daga toilet d'in, tana zuwa tasa d'ankwalin kanta ta saisaiti alk'ibila ta kabbara sallah, ta dad'e tana sallah, tana idarwa ta d'aga hannunta sama tana hawaye tana kai kukanta wajan Mahaliccinta.

Suma sallar suka gabatar bayan sun d'auro alwala.
Anjali ce ta matso inda Farida take ta mik'a mata wani biskit da ruwa, amsa tayi tana ci kawai har yanzu hawaye take, tana ji yadda idonta ke mata wani rad'ad'i na tsananin kukan data sha, da kuma hawayen da suka k'i daina zubar mata har yanzu.............

*GAWA TAFE*
(Zombies story)
On2025


*©Zahra Royal Star*


*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*



*EPISODE 7TO8*


Tunda sanyin asubahi su Farida suka bar gidan da suka yada zango a cikinsa, domin idan ma basu barshi ba yana gaf da gazawa, domin har sai da Faruk ya kwad'e wani Zombies, kwana saukai babu bacci, shi yasa duk sun fita yaccinsu, ido yayi zuru-zuru.

Suna cikin tafiya Farida cikinta ya sake d'aurewa gefe d'aya ta d'uke k'asa tana kiran sunan Allah.
D'an dakatawa sukai gaba d'aya suna dubanta, Hanan ranta a d'an b'ace da Faridar ta ce.

"Ke wai Farida miye haka kike k'ok'arin yi ne?, zaki tashi mu cigaba da tafiya ko kuwa mu barki a nan, kinga ko sunanki GAWA".

D'an mik'ewa tsaye tayi a hankali ta fara takawa tana runtse idonta had'e da cije leb'enta.
Jasmin ma tsaki taja suna yin gaba suka barta ita ce k'arshe.

Da d'an gudu-gudu suka k'araso kusa da wata k'aramar Mota, suna kallon yanayin unguwar da suka shigo jiya cikin dare gabanin asubahi, babu yawan jama'a a unguwar, amma yanayinta tayi kaca-kaca Malam, babu kyan gani, duk an hargitsa unguwar duk kyan ganinta amma ta koma kamar Mak'abarta, motoci ne birjit a tsakiyar titin unguwar wasu sunyi had'ari sun kama da wuta, wasu ko mutane ne a ciki zombies sunyi masu mummunan kisa.

Faruk ne ya fara shiga motar Al'ameen ya shige gaba shima, Motar fa na neman masu kad'an kowa kuma burinsa ya shiga kar a tafi babu shi a ciki.

Wani gunji suka fara jiyowa suna cikin kokowar shiga motar, gaba d'aya zuciyoyinsu ne suka buga da k'arfe har suna rige-rigen waigawa bayansu.

Abunda suka gani ne yasa suka saki baki da hanci suna kallo, zuciyoyinsu na wani irin tsalle na tashin hankali.

Wasu Zombies ne su kusan guda biyar a jere a bayansu, suna dubansu, duk jini ya b'ata masu jiki, fuskarsu ba kyan gani, wani tsabar muninsa ma babu ido d'aya, wani an cinye rabin fuskar, wani babu hannu guda d'aya, sai gundinmin hannun kawai, amma a haka suke jan k'afa suna sun cin masu.

Doctor d'in nan ne yake son bangaje su ya shige Motar, yana baya amma yana k'ok'arin bangaje kowa ya shiga Motar, ai ko daga bayansa yaji y'ar uwar nan tashi ta fasa wata gigitacciyar k'ara had'e da kiran sunansa da k'arfi.
Ai bai san lokacin daya dakata da niyar shigewa motar da yake niyar yi ba.
Juyowa yayi gaba d'ayansa yana zaro ido waje k'irjinsa na d'agawa na tsananin kid'ima da razana.
Wani uban ihu ya saki yana nufar inda y'ar uwar tashi take, Anjali ce ta rik'e masa riga, ganin yana son kai kanshi inda zai halaka.

Fad'i yake "wayyo Allah ku taimaka ma y'ar uwa ta zasu kasheta, wayyo Allah bazan iya rayuwa babu ita ba, wayyo Allah. Ki sake ni na ce naje inda take"

Suna gani Zombies d'in nan suka rufa akanta, sunyi mata kaca-kaca, kamin su rabu da gangar jikinta data daina motsi.

Suna jin k'amshin Bil Adam suka barta suna niyar kamo wani su turmushe.
Faruk ne ya fito daga Motar yana komawa daga bayansu cikin hikima, k'arfe ya samu ya daddage iya k'arfinsa ya rink'a sauke masu shi a bayansu wani a tsakiyar kai, nan take suka zube a sume, domin su kansu su Faruk d'in sun lura idan ba b'are masu kai kayi ba ya rabe gida biyu, to kuwa ba mutuwa suke ba, suma ne suke kawai da an d'auki lokaci zasu tashi.

Sauke k'arfen yayi yana sauke ajiyar zuciya yana dafe da bayansa, sai jan iska yake a bakinsa, suna kallonsa cike da tausayi.

Shiga motar sukai gaba d'aya, sai Doctor d'in nan dake tsaye bai da alamar ma zai shiga motar sai hawaye yake, ga Zombies dake sun rufe unguwar a yanzu, domin duk inda wani mutum yake kamar k'amshinsa suke jiyowa duk nisansu dashi kuwa k'amshin zai kai har inda suke.

Suna kallonsa Al'ameen ya kwala masa kira, zaro ido sukayi ganin Doctor d'in nan wacce Zombies suka gama bidirrinsu da ita, ta mik'e ta koma Zombie itama.

Jikinsu ne ya kama rawa ganin duk yadda Zombies d'in nan suka ji mata ciwoka a jikinta duk d'aukarsu mutuwa zatayi amma ji yadda ta mik'e itama ta zama irinsu.

Suna gani Doctor d'in nan ya nufi inda yake yana hawaye yana tsaye inda take, harta k'araso ta cin masa kawai ya wani rungumeta, ita ko dai-dai wuyansa ta kafa masa wani uban cizo tana wani irin gunji had'e da gurnani.

Juyowa tayi dashi saitin da suke, suna jin ihunsa had'e da mik'a hannunsa yana alamar a ceceshi, sai ihu yake ita kam har lokacin bakinta yana wuyansa sai tsotsar jininsa take had'e da yago fatar wajan tana ci.

Yo ko kallonsa sun sake yi, Faruk ya tayar da Motar jin su Jasmin suna cewa.

"da'aAllah Faruk ja mota muje, kaji d'an rainin wayo Malam, a sadda muke kiransa ya dawo mu tafi ba k'i yayi ba, sai da yaji azaba zai wani nuna a taimakesa yake, ai ga k'auna nan ya gani, nikam banga wadda zai zama Zombies ba na kashe kaina akansa ba wallahi".

Gaba d'aya samarinsu ne suka dubesu, ba wadda ya sake magana, dan suma kusan zan iya cewa abunda ke zuciyarsu kenan, kowa tashi ta fishsheshi ake kawai.

Wani irin matsiyacin gudu Faruk keyi dasu, dan duk inda suka bi suka wuce Zombies ne keta shawagi a cikin garin Goa, sai mutanan da baza'a rasa ba a mab'oya, amma duk wadda idonka zai gane maka shi a tsakiyar garin to ya riga da ya zama Zombies.


Wani munafikin burki Faruk yaja har saida su Farida
Dake baya suka bige da jikin Motar. Hanan dake dafe da goshi inda ta bige ta d'ago tana niyar magana kawai idonta ya hasko mata wasu dondonzon Zombies da suka tare masu gaba, yawansu ya zarce masali ma, dan tsananin yawansu basa jin zasu iya bi ta kansu.
Ko wanne ka kalla daga cikinsu ido a waje ga wata irin zufa data rufe masu jiki gaba d'aya, yadda kasan an watsa masu ruwa a jikinsu.
Kowa ya kasa magana sai bakunansu dake bud'e a hangame tsabar tashin hankali.

Anjali ce tayi k'arfin halin fisgo magana daga bakinta tana cewa.

"Faruk kabi ta kansu kawai, Allah zai bamu ikon wuce su da yardar shi".

Tayar da motar yayi yana bata wuta, sosai yaja da baya kad'an kamin ya jata da k'arfi yabi ta kan Zombies, amma duk da haka wasu sun watse wasu ko sai da suka manne a jikin Motar.

Sai da ya rink'a jijjiga motar had'e da samin wata bishiya ya rink'a goga motar a jiki ne wasu wadda suka mak'ale suka zube suna wani irin ihu.

D'aga kai Farida tayi jin yadda wani Zombies ke buga tsakiyar motar da suke ciki yana daga can samanta ya mak'ale sai gunji yake da gurnani kamar wani Zaki.

Faruk yaja birki bai tsaya ba, cike da kwarewa ya rink'a juyo da Motar wai dan dai Zombie d'in nan daya mak'ale ya fad'o k'asa, duk sun jigatu sun wahala, saboda uban gudun da ake dasu, gashi sai wurwura su ake cikin Mota, da kyar Allah yasa ya fad'o ta gaba Faruk bai tsaya ba yabi ta kansa ya latse suna iya jiyo ihunsa.

Gaba d'ayansu sauke ajiyar zuciya sukai, duk da sun san zasu iya gamuwa da wani iftila'in zombies d'in a gaba, domin sun san duk inda zasu shiga a yanzu Zombies sun gama karad'e gaba d'aya K'asar Goa.

Motar ce kawai suka ga ta tsaya tak'i baya bare gaba, Faruk sai sun tayar da ita yake amma ina.

Wani tsaki Faruk ya saki had'e da kai ma sitiyarin Motar wani naushi yana cewa.

"Ohhh My God, mai d'in Motar ne ya k'are, ya kamata muyi hanzarin sauka daga cikinta, kar wata masifar ta rufe mu muna ciki".

Ai kamin ma ya dire maganar gaba d'aya sun b'alle marfin Motar suna ficewa daga cikinta.

Sai da suka gama sakkowa suna dube-duben inda ya kamata su fara nufa a yanzu kuma.

Wani company nin yin shinkafa suka ci karo dashi Al'ameen ya nufi wajan yana fad'in.

"Kuzo muje ko mun d'an huta a cikin wancan Company d'in da nake gani a gabanmu".


"Kai kam Al'ameen ai bamu ga hutu ba, ni wajan ne ma bai wani kwanta min ba, dan Allah mubar wajan nan".

Fad'in budurwarsa dake mak'ale dashi, sai wani waige-waige take, idonta a waje na tsananin tsoro.

Ko magana bai mata ba suka biyo bayansa domin suma a mugun gajiye suke.

Shiga sukai cikin Company nin suna kallon irin illar da Zombies sukai a cikinsa, kusan GAWA tafi a k'irga suka rink'a cin garo da ita ta mutane gasu nan cikin jini, gashi wajan yayi wani irin shuru sai wata iska dake busuwa a wajan, wacce saita sa mutum tsorata dan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment