Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

talaka Babyn, ya maganar tafiyarmu Gowa?".


"Ohh abunda na zo mu tattaunawa kenan, mu y'an gidanmu su Faruk mun gama tsara yadda za'ai tafiyar, kaga ni da kai sai Jasmi na kira wayarta itama zata zo nan zamu had'u yau zamu gama tsara yadda za'ai".

"Yawwa Baby ki shirya zuwanmu Gowa zaki bani kyautar.....

"Na sani ba sai ka fad'a ba ai"

Murmushi ya saki na shak'iyaancin yana kanne mata ido d'aya.


"Wow My friend ashe har kin rigani isowa?".

Zama Jasmin tayi tana fad'ar Hakan.

Tafawa sukai Amal ta ce.

"Shegiya K'awata wannan muguwar shiga haka, kina lokaci fa".

Dariya Jasmin tayi tana kallon wani D'an iskan wando data saka da wata y'ar riga ko cibiyarta bata rife ba.

Ta ce "kema kinsan bana son kaya masu nauyi just bana son takura. Yawwa wai yaushe ne zamu bar K'asar nan ne na K'usa fa Guys?".


"Maganar da muketa yi kenan, inaga bamu wuce cikin Satin nan gaskiya".

Fad'in Amal.


Jasmin ta d'aga kai ta ce "wai ina shegiyar nan ne Hanan?".


"Hhhh ai ko yanzu kin ganta wajan nan itama ai duk da ita za'ai tafiyar". Cewar Faisal

"Ki ce zamu rak'ashe da yawa a Gowa, Gowa zatai d'ibar Y'ay'an Manyan K'asar Nigeria".

Fad'in Jasmin tana murmushi da d'okin tafiyar.


*HANAN POV*


"Ke Farida kiyi saurin had'omin Copi, ina sauri ne zan fita pls".

Hanan ta k'are maganar tana zama d'aya daga cikin kujerun babban parlon gidan nasu, tana latsa waya, bata kalli inda Farida ke goge a parlon ba.

Farida da rawar jiki ta amsa tana shigewa k'aton kitchen d'in parlon. Duk da yawan ma'aikata dake kitchen d'in amma ita ce kad'ai suka yadda da girkinta, shi yasa tana aikatuwa a cikin gidan ba d'an kad'an ba.

Da rawar jiki ta k'araso inda Hanan take a zaune, rik'e da cofi na copin data had'u mata.

"Gashi Ranki ya dad'e an gama".

Hannunta ta mik'a again tana latsa wayarta ta amshi k'ofin dake hannun Faridar.

Kaiwa bakinta tayi tana latsa waya, kurb'a d'aya tayi da mugun sauri a zabure ta furzar dashi sai akan fuskar Farida.
A zabure Farida ta saki k'ara tana mik'ewa tsaye, domin taji zafin copin ta furzar mata akan fuskarta.

Hanan rai a b'ace tana nuna Farida da yatsa tana cewa.

"Kan uba, so kike ki kashe ni Farida?, kinji zafin abunda kika had'u min kuwa?, waike mi yasa komai zaki yi sai kinja an zagi ki?, wannan wane irin jakanta ce haka, ace mutum kullum sai ance baiyi dai-dai ba, sai ka ce wacce ke da Kwakwalwar kifi".

Zubewa Farida tayi a k'asa tana had'e hannunwanta waje d'aya alamar neman afuwa tana cewa.

"Kiyi haku......

"Dalla can rik'e hakurinki Malama".

Ta k'are maganar tana sakin kofin a hannunta ya fad'i k'asa ya tarwatse, ta nunata da yatsa ta ce.


"Ki kiyaye a nan gaba, idan ba haka ba kin san sauran, kuma ki fara shiri domin dake zanyi tafiya Gowa, domin ki rink'a min hidima a can, saura idan munje can d'in ma ki rink'a min Jakanta kamar yadda kike min nan".


Rasssssss Farida taji gabanta ya yanke ya fad'i lokaci d'aya, haka kawai taji gabanta ya ci gaba da bugawa, jin abunda Hanan d'in ke fad'i, bata san mi yasa taji ta tsani ayi tafiyar nan da ita, tasan zasuyi tafiya tabbas zasu bar K'asar zuwa shak'atawa amma b'ata tab'a tunanin cewa wai da ita za'a tafi ba, b'ata tab'a ganin irin haka ba ita kam, zaka je shak'atawa tsabar sangarta har sai ka tafi da mai maka hidima?


"Tsayuwar uban mi kike kuma a nan?".

Fad'in Hanan tana ma Farida wani duba.

Da sauri Farida ta katse tunanin data fad'a jiki na rawa ta ce.

"Yi hakuri Ranki ya dad'e".

Ta fad'i hakan tana barin wajan.

Anam ce ke sakkowa tare da Mom har Anam na kyarmar fad'in.

"Mom kinji miye waccar yarinyar ke fad'i ko?".


"Naji mana, to miye a ciki?, idan ta tafi da Farida, ai zata rink'a mata wasu abubuwan ne a can".


"Nooo Mom bai kamata ma ki bari taje wani yawan shak'atawa ba wallahi why Mom d......

D'aga mata hannu Mom tayi dai-dai sun idasa sakkowa k'asan ta ce.


"Kinga Anam bana ce miki ki daina shiga harkar da babu ruwanki a ciki ba?, so please ki kyale yarinya tayi yadda take so mana, kuma nake ganin ai ba ita kad'ai zatayi tafiyar nan ba, ita fa dasu Amal da kuma su Al'ameen Yayyunta, zasu tafi, kinga kuwa banga abun tada hankali ba ai".

"Mom ki ce kawai shashancinsu zasu tafi wallahi, ai duk inda aka sami su Amal dole akwai shashanci a ciki, Mom dan Allah kima Dad magana ya soke masu
Tafiyar nan, ni haka nan tunda suka fad'i tafiyar na ji kwata-kwata bata kwanta min ba, suyi hakuri da ita mana zuwa wani lokacin".

Hanan dake kallon Anam ji tayi kamar ta shik'e mata wuya, tsabar jin haushinta. Ji mata da'aAllah nason masu bak'in ciki k'iri-k'iri.

"Kinga ko Aunty Anam babu abunda ya sha miki kai da tafiyarmu, ai bamu ce dake zamu je ba dai ko?".

"Ki rufe min baki Hanan, ni yama za'ai nayi tafiya irin wannan daku Allah ya tsare ni wallahi, kuma zaki ci ubanki ne idan ina magana kina sak'o min wannan shegen bakin naki".

Kwab'e fuska Hanan tayi tana murgud'a mata baki.

Mom data zauna akan kujera tana d'aukar romot d'in Tv ta canza tasha tana cewa.

"Kwantar da hankalinki Autata babu wadda ya isa hanaku tafi Gowar nan, tama yi ta gama"


Sakin baki kawai Anam tayi tana duban Mom, can ta sauke wani lumfashi tana gyara tsayuwarta ta ce.

"To tunda dole ne ance tafiyar ta su, Mom karta sake ta ce zata d'auki Farida su tafi tare, domin banga dalilin da zaisa dole sai an d'auki Farida ba".

Wani kallo da Mom ta jefa mata ne yasa ta d'an had'e wani miyau daya tsaya mata a mak'oshinta, tana sake kallon Mom d'in.

"Anam kifa fita ido na rufe tom, da ita d'in zata tafi, ko ke ce kika d'auke ta aiki ne ban sani ba?"

"Ni Mom bani na d'auke ta aiki ba, am...

"Kinga zo ki wuce wajan aikinki ya fiye miki, domin b'ata ma kanki lokaci kawai kike a yanzu".

Ranta babu dad'i ta juya ta fice daga parlon.

Mom na kallon ta fita taja wani lumfashi duk da itama tafiyar bata wani kwanta mata ba, amma kamar an d'aure mata jijiyoyin jikinta da bakinta ta kasa furta ainafin abunda ke cikin ranta.

A hankali ta ce.

"Ace ayi mutum yayita shiga abunda babu ruwansa".


Hanan dake murmushin cin nasara ta rungume Mom tana cewa.

"Mom wallahi shi yasa nake k'ara sonki, bari naje su Amal na can suna jira na, zamu tattaunawa akan tafiyar da zamuyi Gowa".

"To sai kin dawo, am....

"Haba Mom karki ce komai, kawai sai na dawo d'in dai".

Ta k'are maganar tana kai mata kiss a goshi tayi saurin ficewa daga parlon, domin ta lura kamar Mom d'in na son yarda da maganar Anam d'in.

_______________________
*HARUN POV*

a hankali yake juya y'ar kujerar da yake zaune akanta.
Sanye yake da kakensa na Soja, wadda suka k'ara haska fatarsa Chocolate color, dara-daran idanuwansa ya lumshe yana sake bud'e so. Dokar daji ce suke, yak'i ne akai Babban gaske, daka kalli yanayin wajan da suke zaka shaida hakan, saboda gawawwakin dake yashe a wajan, da wasu tsirarun Sojoji dake wajan, sai wasu Gawawwakin Sojoji suma dake kwance a wajan cikin jini.

"Harun Yaya dai?".

Kallonsa ya kai inda yaji kiran nashi a hankali ya sake ware idanuwansa sosai akan abokinsa shima dake sanye da kaken Soja.

Cike da tsananin gajiya ya ce.

"Noo ba wani abu Captain Joha"

"Dole Harun jikinka yayi ciwo, ban tab'a ganin mai k'ok'arinka ta fanin yak'i ba, dubi fa irin mutanan da kashe wajan aikin nan, yama kamata muzo mubar cikin jejin nan gaskiya"

A hankali ya d'an mik'e akan kujerar da yake kai duk jikinsa jini ne sai wasu y'an ciwuka da baza'a rasa ba.

Kujerar daya tashi Joha ya kalla domin irin kujerar Mota ce data rugugguje ta fita daban, a dai-dai lokacin daya kashe wani d'an daba wadda ya addabi mutane da dama, sunsha artabu da Harun kamin Allah ya basa damar kashe sa, yana kashesa kuma ya fad'a kan kujerar yana sauke wani lumfashi mai cike da gajiya.

Ganin Harun d'in yayi nisa ya barshi ga jirginsu dake shirin tashi domin barin Jejin, da sauri da d'an gudu-gudu ya k'arasa inda yake, kusa a tare suka shige jirgin ya d'aga dasu suka bar cikin Jejin dake ci da wuta ga gawawwakin jama'a nan, sun bar wasu Sojojin na aikin jidar wa'inda suka rasa ransu a wajan.............

*GAWA TAFE*
(Zombies story)
On2025


*©Zahra Royal Star*


*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*



*EPISODE 3*


"Why Amal zaki je tsakiyar titi ki fito kina ma mutane tsawa?. Ki duba video yadda y'an adawa ke yad'ashi suna magana marar dad'i akai na da iyali why mi yasa?".

Fad'in Abbie dake tsaye yana nuna ma Amal wayar dake hannunsa ransa a b'ace yake maganar.

Amal kuwa dake tsaye shagwab'e fuska tayi tsabar ta saba masa sangarta ta ce.

"Sorry Abbie wallahi banyi hakan dan b'ata siyasarka ba, kasan talakawa ba abunda suka iya sai shige ma masu kud'i, kawai fa Abbie muna tafiya tsakiyar titi wata banzar Mata ta shigo mana gaba, ni kuma shine......

"Shine ke kuma kika tsaya tsakiyar titin kina d'iyar Gwamnan Jahar nan kina cece kuce da jama'a, kuma dama kin san magauta kiris suke jira su yad'a abunda bashi kenan ba. Yaushe ne tafiyarku Gowa?".

Wani murmushi ta saki na tsallar murna ta ce.

"Yesssss Abbie cikin weekend zamu tafi".


"Noo na dawo da tafiyar taku zuwa gobe, gara ki bar K'asar keda wa'innan Yayyun naki kuje can ku d'an huta, saboda maganar mutane akanku yanzu tayi yawa, gara ku tafi can, dan in kina ganin mutane irin na K'asar nan dole hakan zata rink'a faruwa, canfa duk masu kud'i ne ke zuwa K'asar shak'atawa, so kamar nawa kuke son tafiya dashi?"


"Wayyo dad'i Abbie Allah ya saka, Abbie kamar Million's......

Faruk ne ya yayi saurin katseta da shigowarsu kenan parlon suka ji maganar Abbie ta k'arshe inda yake tabbayar kamar nawa zasu ishe su tafiyar.

"Abbie kamar Million's biyar-biyar ko wannan mu ta ishesa nake gani ko guys?".

Ya fad'i yana duban su Amal da Al'ameen.


"Yesss Abbie saboda muda friend d'in da zamuyi tafiyar dasu"

Cewar Amal tana kallon Abbie dake kallonsu.

Abbie ya juya wajan P'A d'insa yana basa umarnin ya turowa kowannan su naira million shidda-shidda ta account d'in kowa daga cikinsu.

Wani tsalle Amal ta daka tana rungume Abbie jin harda k'ari yayi masu akan wadda suka tabbaya d'in.

Murmushi ya d'an saki yana cewa.

"But sai kun rink'a lura idan zaku fita cikin gari, kusan inda ya dace ku rink'a abubuwa, saboda yanzu sai kuga abu k'arami magauta na son mayar dashi babba, yanzu miye dan kawai kin fito kin tsawatarwa wannan Tsohuwar?, why mutane yanzu kamar jira suke su fara zaginka, dama nasan shirrin mak'iya ne kawai, sai ku kiyaye gaba d'ayanku, baima kamata kuna bi Local waje irin wadda zaku rink'a had'uwa da wa'inda basu san miye duniyar take ciki, just ku rink'a ma K'anwarku fad'a Faruk".

Da to suka amsa ya haye sama P'A d'insa yana take masa baya. Yana bin Y'ay'an gata da kallo, lallai giyar Mulki na d'ibar wasu mutanan, dubi dan Allah yadda yayi kyauta Millions shidda ga kowannan su, kamar yayi kyauta naira biyar.

Fad'in P'A d'insa a zuci yana bin bayansa yana maganar zuci.

_____________________
*1100pm Umaru Musa Yar'Adua Airport Katsina State Nigeria*


Gaba d'ayansu ne tsaye a filin jirgin.
Wasu matsiyatan kaya suka saka kusan zan iya cewa duk iri d'aya ne, saboda k'ananun kaya ne wadda sukai masu mahaukacin kyau.

Daga gefen Amal harda Anjali za'a tafi saboda ta rink'a tare mata wasu abubuwan, tana kula da ita, sai Jasmin.
Hanan ma tare suke da Farida wacce aka bata kwancan kaya, shigarta itama ta k'ananun kayan ne, dan dai ita ko ina a jikinta a rufe yake. Daka kalli yanayin fuskarta zaka shaida cewa ba dan tana so za'ai tafiyar nan da ita ba.
Domin sai da sukai uwar watsi da Inna Zubaida a sadda ta koma gida take shaida mata zasuyi wata tafiya da ita k'asar waje, ita gaskiya zata ce masu ta daina masu aikin, bazata wani bisu zuwa K'asar da bata sani ba, tafiyar ce kwata-kwata bata kwanta mata ba. Ai ko tasha zagi da kwashe albarka sai cewa mata take
"Sannu y'ar bak'in ciki irin tsiya dangin tsiya sannu kinji na ce. Ai ko ko kina mutuwa kina farfad'owa billahir azim Farida sai kin bisu ko da bangon duniya ne kuwa, shi uban naki da bai da aikinyi sai Faci ba gashi can a bakin titi ba, kullum ba abunda ya iya sai maula, ni ce dai rufin asirinku gaba d'ayanku, to wallahir azim baki isa ba, garama tun wuri ki fara shirin tafia, ke baccin ma baki da tunani da hankali za'aje dake k'asar waje kina wani k'i, tsabar dama ke ta daji ce, ba abunda kika sani sai k'auyenci, yo ina laifin wadda ya ce zai kaika inda baka tab'a zuwa ba ko a mafarki, baki tab'a tsammanin zaki fita wata k'asar waje ba, ke ko Niger wannan dai ta kusa damu, ubanki baida arzik'in kai ki, bare ance k'asar turawa zakuje".

Inna Zubaida ta dad'e tana zagin Farida kamar zata rufeta da duka.
K'arshe dole Farida ta yarda da tafiyar, tana kuka ta koma gidan aikin nata, tana tunanin da Mahaifiyarta na raye wallahi tasan ko za'ayi mi, bazata tab'a bari taje ma aikatau d'in ba, bare harta had'u da wa'inda basu san darajar mutum ba, bare kuma ace za'ayi wata tafiya da ita.

"Keee wai wacce irin sakarai ce ne, komai sai ance kiyi ne? Ko kuwa komai sai an nuna miki yadda zakiyi? Tsabar k'auyenci irin naki?".

Fad'in Hanan tana banka mata harara.

"Kayi hakuri Ranki ya dad'e banji miye kike cewa ba?".

"Ya za'ai kiji mi nake cewa, tunda kin lula duniyar k'auyenci, sai wani bin mutanan wajan nan kike da ido".

K'asa tayi da kanta, ita harga Allah tana dai kallon jama'a ne amma wani abu can take tunani a ranta, ba wai kallon mutanan wajan ba.

"Sai ki mai da hankalinki sosai za'a fara kiran sunaye, idan kinji naki Zaki iya biyo bayanmu, bana son yawan magana na gaya miki".

"Insha Allah Ranki ya dad'e za'a kiyaye".

Tsaki kawai Hanan taja tana k'ara gyara y'ar jakar dake hannunta irin ta gayu, sai wayar da take shirin sakata a ciki.

Amal ta kalli Hanan ta ce.

"Ashe kema haka kike fama da irin gidadawan mutanan?".

Ta k'are maganar tana kallon Farida da kanta ke a k'asa tana jinta.

" Wallahi fa kin dai gani, ai ni uban mutum nake ci wallahi a zauna lafiya, domin ni bana d'aukar shashanci".

"Hhhhh haba k'awata, nima sai ka ce baki san wace ni ba, ni ai inaga na fiki rashin d'aurkar raini wallahi".

Dariya zaku saki a tare suna kai dubansu wajan su Faruk da wanne cikinsu yake nanik'e da budurwarsa, sai ka rantse ka ce wasu ma'aurata ne.

Suna cikin haka aka fara kiran sunayen fasinjojin jirgin, wadda zai d'aga k'arfe sha biyu dai-dai.

Gaba d'aya kusan sune suka fara shiga jirgin kwansu da kwarkwatarsu Y'ay'an manyan k'asar ne, abun kamar had'in baki ma, babu wani d'an tagajan-tagajan a cikin jirgin.

_____________________
*ANAM POV*


A hankali Doctor Halisa ta dafa kafad'ar Anam cike da mamakin yadda ta dad'e tana mata magana amma shuru ba amsa, shine yasa ta d'an dafa kafad'arta.

D'an firgita tayi tana dawowa yaccinta.

"Lafiya kike kuwa Anam?"

"Uhuhmm da sauk'i dai Halisa"

Zama Halisa tayi tana duban Anam d'in cike da mamaki tana aje wasu takardu dake rik'e a hannunta ta ce.

"Mi yake faruwa ne?".

Sauke ajiyar zuciya Anam tayi tana zare wani abun Doctor's dake rataye a wuyanta kamin ta ce.

"Akan Family namu ne kawai, wai wata tafiya suka shirya kawai don suje yawan shak'atawa, wai yau da safe har Dad yake ma Hanan kyautar Million biyar, why Fisbilillahi kamar Hanan y'ar haka da ita za'a rink'a mata kyauta Million biyar?".

Zaro ido waje Halisa tayi tana had'e wani miyau a zuci take cewa "wayyo Allah dama nice a matsayin ku".

A fili kuma ta d'an maze tana cewa.

"Tabd'i jam gaskiya anaji da Hanan d'in nan taku, to ai ni Doctor Anam banga abunda shiga damuwa ba a nan".

Wani kallo Anam tama Halisa tana cewa.

"Amma wallahi ban tab'a tunanin jin haka daga gare ki ba, da nasan abunda zaki ce kenan da bazanyi gaggancin sanar dake damuwa ta ba, haba baki da K'anwa ne a gidanku Halisa?, kamar Hanan ana bata irin wannan mak'udan kud'ad'en, ya za'ai bazata lalace ba, gata tana mace, dama ace namiji ne wannan komi yayi ido ne, ita fa?".

Bata san hawaye take ba sai da taji saukar hannun Doctor Halisa akan fuskarta tana d'auke mata su.

Jiki a sanyaye Halisa ta rik'e mata hannu ta ce.

"Ko kad'an ba abunda kike zargi bane, ni a nawa tunani kawai ki bita da addu'a shine ya kamata, dama a gida ana samun zakka a ciki, ki rink'a sata a cikin addu'o'inki insha Allah komai zai wuce, zaki ga kamar batayi ba insha Allah".

Sauk'e lumfashi Anam ta rink'a yi saboda hawayen dake mata zuba sai ma wani k'ara gudu da suka rink'a yi.

Rungumeta kawai Doctor Halisa tayi tana d'an bubbuga bayanta.

_______________________
*HARUN POV*


Gaba d'aya d'akin taron ne aka d'auki tafi, jin an kira sunan Harun.

A hankali cike da natsuwarsa ya tashi yana nufar inda shugabansu na Sojoji ke tsaye cike da izzarshi yake tafiya mai jan hankali da class.
Kai tsaye inda shuban nasu yake ya tsaya yana Sara mashi.

Wata number yabo shugaban ya d'akko ya ratayama Captain Harun, yana saka masa aka sake d'aukar wani tafin mai k'arfi sauran Sojoji dake tsaye kuma suka Sara masu.

Number yabo aka basa mai girma tare da k'arin matsayi mai girma a cikin Sojojin.

"Mtswww"

Kallon na kusa dashi Captain Joha yayi wadda sarai yaji tsakin da ya saki a lokacin da shugaban Sojojin ke k'ara gode ma Harun tare da jinjina akan namijin k'ok'arin da yake yi ta fannin yak'i.

Joha ya kasa hakuri ya kalli Abbakar ya ce.

"Abbakar ya da tsaki kuma?".

"Mtswww nifa na tsani bawan Allahn can wallahi, ace komai sai shine zai zo na d'aya, komai za'asa dashi shine akan gaba, sai kace ba tare Muka zo dashi Hukumar Soja ba, matsayinmu d'aya dashi ada amma yanzu ya k'are mu".

Wani murmushin gefen baki Joha ya saki yana kai dubansa inda su Captain Harun suke tsaye, a yanzu ya amshi abun magana yana d'an jawabi cike da muryar nan tashi mai kauri had'e da natsuwa.

"Banga abunda Captain Harun ya tsare maka ba Abbakar, sai nake ganin kamar hassada kike masa kana bak'in ciki da ci gaban da Allah yake basa ne, ya kamata zuwa yanzu ka daina duk wannan indai akan Harun ne zaka mutu da ciwo a ranka kuwa".

Wani dogon tsaki Captain Abbakar ya saki cike da jin zafin Captain Harun ya mik'e ya bar masu wajan, yana ji a ransa ko wuk'a ya samu ya sami dama kuma zai iya kashe Harun wallahi.

Captain Joha ya bisa da kallo yana masa Add'aur shiriya, duk da ya kasance shi ba addini d'aya suka had'a ba, baya bak'in ciki da d'aukakar da Allah yayi ma abokinsa, ko da da rana d'aya ne kuwa, duk da cewa kusan matsayi d'aya suka fara aiki a tare a Hukumar Sojan, amma gashi yanzu Captain Harun d'in ya kare su nesa bama kusa ba, bai tab'a jin wani abu saboda da haka ba, ace sai d'an uwansa wadda suke addini d'aya ne yake jin haushinsa haka.
Kusan abokai ne harda Abbakar d'in Kuma duk tare suka zama Sojojin.

______________________
*Airport Rd, Dabolim Goa*


A hankali Fasinjojin jirgin daya sauka a filin jirgi dake K'asar Gowa ya sauka a dai-dai k'arfe takwas na dare.
Gaba d'aya suka fara fitowa d'aya bayan d'aya.

Kusan zan iya cewa Farida ce k'arshen fitowa ita da Anjali suna rik'e da akwatunansu gaba d'aya.

Farida ba abunda take sai tasbihi ga Ubangiji wadda shine mamallakin komai dake cikin duniyar nan tamu da kowa a cikinta, gaba d'aya garin Gowa ya tafi da imanin Farida, tsabar yadda ya had'u iya had'uwa, zata iya rantsewa da Allah b'ata tab'a ganin garin da yake dad'in ace zaka shak'ata kamar Gowa ba, lallai bata ga laifinsu Amal da suka dage sai wannan K'asar zasu zo yawan shak'atawa ba, K'asar tayi kyau kam iya kyau, an tsarata ta tsaru.

Garin kalle-kalle Farida harda su tuntub'e saura kad'an ta kife a k'asa, tsawar da Hanan ta buga mata ce ta kusan sata idasa zubewa a k'asa bata shirya ba.


"K'auyencin zaki fara nuna mana ko?, ki natsu ki shiga hankalinki wallahi Farida".

Da rawar jiki Farida ta d'aga kanta maganar ma ta kasa, da gudu ta k'araso inda wasu motoci suke parking a wajan.

Motoci ne sunkai biyar ko wanne ya hau wacce yake da ra'ayi dama kuma tarbarsu aka zo yi.

Farida kanta ai bai k'ara kwancewa ba sai da taga sun iso wani matsiyacin Hotel wadda tunda take a duniya b'ata tab'a ganin irinsa ba.
Hotel ne amma yadda kasan kana cikin gidan ubanka.

Kai zata iya cewa babu ce kawai babu a hotel d'in, iya had'uwa D'akunan da suka kama sunyi kyau na k'in k'ari.

Kowanne cikinsu tare da wa'inda suka taho suka kama d'akuna.
Su Faruk da Baby's nasu d'aki d'ai-d'aiya suka kama kowanne, sai kuma Amal da Faisal d'aki d'aya, abun ya so ba Farida mamaki tunda dai ai take ganin ba ma'aurata bane, amma su ko a jikinsu, ita da Anjali aka kama ma d'aki d'aya, ita kanta Hanan sai yanzu ne ma Faridar ta lura da wani saurayi da Hanan ta taho dashi, ita wallahi da duk bata lura dashi ba, sai yanzu da ake shirin had'a d'aki d'aya dashi d'in.

Ita kam yau tana ganin ikon Allah, sufa a haka gani suke wayewa ce ba wani abu bane kwana d'aya da namiji wadda ba maharramunka ba ko?.

Irin wannan tunanin take a zuciyarta.


A cikin daren sai da suka d'an huta, kamin suka fara shiga wanka aka fito aka d'auki wani shegen wankan, ana shirin fita yawo tun a ranar.

Duk d'aukar su Anjali sai zuwa safiya zasu fara fita yawon, sai kawai suna zaune aka buga masu k'ofar d'aki suna fita Amal ta basu umarnin su fito zasu d'an fita daga gari ne a kamin gobe da safe ayi mai gaba d'aya.

Da mamakinsu taje ta sanar da Farida.

Farida harta fara wani wahalallan bacci taji an tayar da ita.
Ba dan ta so ba ta fito suka iske su suna jiransu.
Hanan sai fad'a take tana masifar sun barsu a tsaye sai ka ce wasu sa'anninsu.
Basu da ikon cewa komai suka shige mota suka nufi cikin garin Gowa.

Sunsha yawo cikin daren, kamar bazasu dawo makwancinsu ba.

Iya gajiya Farida ta gaji ai nun, amma ba damar nunawa, tana kallon Anjali ita ko a jikinta, tunda zan iya cewa ta saba dama da irin hakan ita.

Kiiiiii
Gaba d'aya motocin suka ja birki.

Fitowa suka rink'ayi gaba d'aya suna kallon motar su Amal dake gaba ita da Faisal wadda sune suka ja birkin suka tsaya.

"A'a ya naga kunja birki mi ya faru ne?".

Fad'in Jasmin.

D'an kallon ta Amal tayi tana zare hannunta daga na Faisal dake kallon abunda ke gabansu wani Kare ne tsaye a wajan saura kad'an su take sa ma.

Tsaye yake sai kunji yake bakinsa yayi daje-daje da wani bak'in jini, idonsa kuwa jawur kamar garwashin wuta, kamar Kuma wuta naci a cikinsa.

Farida tana kallon yanayin Karen gabanta ya yanke ya fad'i har sai da ta d'an ja baya tana addu'a a zuci, haka kawai taji mugun tsoro Karen.

"Wallahi wai Kinga wani Kare ne ya shige mana gaba, shine yasa muka ja birki saura kad'an mu take sa ma Allah ya tak'aita"

Fad'in Amal itama tana mai do dubanta wajan da Karen yake ganin Faisal ya nufi inda yake yasa ta d'an ja da baya tana sake cewa.


"Kaii kaii Honey please karka matsa inda yake, kasa dutse ka jefesa ya bamu waje kawai mu wuce dan Allah, ni haka nan ban yarda da Karen ba".

Haba

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment