Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai baima jita ba nufar Karen kawai yake yana wani murmushi irin ya saba da Karnukan nan yana cewa.


"Haba Baby ba abunda fa zai faru, baki ga Karen turawa bane babu ruwansu da fad'a ma bare suji ma mutum ciwo".

Ya k'are maganar zai kai hannunsa jikin Karen.

Kamin ya kai hannunsa jikinsa kawai kamar an harbo Karen yayi wani kukan kura ya fad'a jikin Faisal yana kafa masa hakura a dai-dai k'afarsa.

Wani bala'in ihu mai k'arar gaske Faisal ya saki, jin wata azaba da tayi ma Kwakwalwar kansa sallama mai shirya ba.

Gaba d'aya zaro ido waje sukai wasu na komawa baya, Farida ko wani zawo ne taji yana shirin zubo mata.

Da kyar wasu Y'an Sadda suka k'araso wajan, suka kori Karen daga wajan yayi cikin daji yana lashe jinin daya tsotsa a jikin Faisal.

Faisal da kyar ya mik'e idonsa jawur na tsabar azaba tunda yake bai tab'a jin cizo mai zafi da rad'ad'in azaba irin na wannan d'an iskan Karen da ya cije sa ba.

Da kyar Amal ta rik'e masa hannu yana d'angyasawa, suna ta masa sannu, sai dai kawai ya girgiza kai yana d'aga masu hannu alamar yaji.

Kai tsaye Wani Babban Asibiti suka nufa dashi domin gyara masa cizon da Karen yayi masa, domin harya fasa masa fata sosai sawon hak'oran Karen b'aro-b'aro a cikin k'afar Faisal inda ya kai masa cizo.


Doctor's sunyi mamakin yadda wajan da Karen ya cije sa yake komawa wata color daban, wani irin bak'in jini wajan ke zuba.

An masa allurar bacci tare data kashe rad'ad'i domin Faisal wani ihu ya rink'a masu na cewa wajan na masa wani irin azababben rad'ad'i, dole tasa Doctors yi masa allurar kashe zafi.

Amal sai kuka take kamar wacce aka ce ma mutuwa zaiyi...........

*GAWA TAFE*
(Zombies story)
On2025


*©Zahra Royal Star*


*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*


*EPISODE 4*


*V.M Salgaocar Super Speciality Hospital Goa*


Zaune suke a d'akin jinyar da aka kwantar da Faisal, sunyi jingum jigum kowa da abunda yake tunani a ransa.

Hanan ce ta d'an matsa kusa da Amal dake zaune bakin gadon da aka kwantar da Faisal wadda yake wani dogon bacci har zuwa biyu na dare Shuru kake ji bai farka ba.


"Ya kamata wasu daga cikinmu suje Hotel d'in da muka sauka su d'akko mana kayan anfani, ba zai yuwu mu kwana gaba d'aya a asibitin nan ba".

Fad'in Al'ameen yana duban su gaba d'aya.

Hanan data k'arasa inda Amal take ta ce.

"Ni gaskiya ina nan nida K'anwata sai dai kai ka tafi kaida Garl d'inka"

Shuru ya d'anyi, haka kawai yaji baya son tafiya ya barsu, cikin k'arfin hali Al'ameen ya dafa kafad'ar Faruk yana cewa.

"D'an uwa da kai zamu wuce ne ko kana nan?"


"Why not mu zauna gaba d'ayanmu zuwa safiya, sai mu wuce mu dawo?"


*Farida & Anjali POV*


Su Farida dai na daga waje k'ofar d'akin da aka kwantar da Faisal suna kallon yanayin asibitin.

Wata y'ar hayani ce ta fara kusanto inda suke, hakan yasa da mugun sauri Farida ta zabura ta mike da kyar Anjali ta rik'e mata hannu ganin tana neman banka masu cikin d'akin jiyar.

Zaro ido waje tayi tana kallon Anjali tana cewa.

"Wallahi Anjali kwata-kwata hankali na ya kasa kwanciya da inda muke, ke gaba d'aya ma K'asar ce bata kwanta min ba, ki duba ki gani daga isowarmu har wasu abubuwa marassa dad'i sun fara faruwa damu fa, yanzu ki dafa k'irji na kiji yadda yake bugawa da k'arfi har ya wuce misali, zuciyata da ruhi na dank'are suke da tsoro na rasa mi yasa Hakan".

Sauke wani gajeran lumfashi Anjali tayi tana jin wani iri a ranta kamin ta ce.

"Kusan nima zan iya cewa ina jin kaso mafi girma da fargaba a raina, duk da ba yanzu ne karo na farko dana bar K'asar Nigeria ba, no a ko da yaushe muna tafiya irin wannan da su, amma wannan sai nake ji ta banbanta da sauran, kwata-kwata, bana jin tafiyar a raina, ki natsu insha Allah babu abunda zai faru kinji".


Suna cikin magana wasu Doctors guda biyu suka nufo inda suke tsaye, zasu wuce hankalinsu a mugun tashe da harshen turanci Anjali ta ji kamar suna cewa.


"Akwai babbar matsala a cikin gari ya kamata ayi gaggawar kulle hospital d'in nan, kamin matsalar ta shigo ciki".

Hankali a mugun tashe d'ayar keba d'aya amsa daga cikinsu tana cewa.


"Akwai fa marar lafiyar da aka kawo yanzun nan D'an Sanda ne wai wani mahaukacin Kare ya cijesa a hannunsa, kuma da alama kamar Karen shine ke son yad'a wata cuta, dan yanzu haka ance cikin garin Goa ba lafiya cutar da Karen ke yad'awa ce, yaje ya sake cizon wata mata ita kuma matar ta tafi gida ciwo nata cinta, k'arshe kawai mijina ta kama tana cizo had'e da yagar naman jikinsa tana ci, a labarin dana na gani ma ta cinye rabin gagar jikin mijin nata fa, hatta Yaronta k'arami ta cije sa, amma ance shi ya gudu dashi da ita ne suka rink'a cizon mutane har cutar ta fara yawa a cikin gari, shine ina cikin kallon abunda ke faruwa kika shigo min da maganar ana son kulle hospital d'in nan gudun kar cutar ta iso cikinsa, to amma fa......

Tsaye suka tsaya inda su Farida suke, Farida sai zare ido take tana binsu da kallo ganin yadda suke magana hankali a tashe suna rik'e da hannun juna, tana dai jinsu ne amma kwata-kwata bata fahimtar yaranda suke yi, sai Anjali dake jin komai tana fahimtar su, itama k'irjinta sai bugawa yake, idonta da hankalinta kacokam yana gare su, ta tsaya sake da baki tana jin abunda suke cewa ji take abun kamar a cikin film ko labarin wani littafi.

Farida ce ta kamo hannun Anjali tana d'an girgiza ta tana cewa.


"Dan Allah kina jin miye suke cewa?, naji a jikina kamar abun suke fad'a ba alkhairi bane, kamar zai shafe mu ne, dan Allah ki sanar dani miye suka tattauna a Kai".

Zatai magana taga d'ayar Doctor d'in ta ce.

"Ohhh my God kina nufin wadda aka kawo yanzun nan shima cizon Karen ne?, to ai wannan d'akin ma wadda aka kawo shima cizon Kare ne an masa allurar bacci ne shine ma zanje na dubasa yanzu, Doctor Darniyal ne ya bani umarnin zuwa na gani ko ya farka".

Ta k'are maganar tana nuna d'akin da aka kwantar da Faisal.

Kai gaba d'aya fa Farida ta rud'e, tun kamin taji abunda suke tattaunawa akai, y'an cikinta sai kuka suke, mararta tana ji ta cika da wani fitsari na tashin hankali.

Har suka shige d'akin da aka kwantar da Faisal Anjali na binsu da kallo, har sai da Farida ta d'an mata magana a tsawace sana ta dawo hayyacinta.

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Anjali ta fara saukewa tana kallon hanyar da wa'innan Doctors d'in suka biyo, ji take kamar hayaniya na nufo inda suke again, ji take kamar wani tashin hankali na kusanto su.

A hankali ta furta.

"Akwai matsala babba Farida, dake faruwa a wajan Hospital d'in nan da garin Goa baki d'aya"

"Innallihi wa'inna alaihir raju'on, dama na ce wallahi tunda jikina bai aminta da wannan tafiyar ba nasan akwai wani abu marar dad'i da zai faru, dan Allah mike shirin faruwa ne?".

Farida ta k'are maganar hawayen tsananin tsoro na kwace mata a fuska.

"Ki natsu dan Allah Farida, naji suna cewa Karen da ya ciji Faisal ne wai yake cizon jama'ar gari, kuma wata cuta mai ban tsoro ce take kama gangar jikin mutum ta cin naman mutane".

Wani irin jaaaa da baya Farida tayi ido a waje kamar zasu fad'u, daga kalli k'irjinta yadda yake d'agawa zuciyarta ce ta sake shiga rud'ani mai tsananin gaske had'e da wani masifaffen tsoro ya sake rufeta, bakinta na rawa take fad'in.


"Miye hakan kike cewa Anajali?, ko dai baki ji da kyau bane?, taya za'ai mutum ya kamu da cutar da zai rink'a cin naman D'an uwansa?, haka kawai zai turmushe d'an uwansa ya kama yagar naman jikinsa yana ci ko mi kike nufin cewa ne?".

Kamo ta Anjali ke k'ok'arin yi tana son k'ara mata bayani, amma Farida na sake ja da baya, gani take kamar Anjali d'in ma cinye ta zatai a yanzu.

"Abunda naji suna cewa kenan nima Farida, komai na iya faruwa Farida, saboda dama ko wacce asalin cuta ana iya samunta daga Dabbobi dama, kuma Kinga Karen daya ciji Faisal fa kamar wani abu ne yaje ya ci ko yasha shima kamar naman mutane yake bi yana ci ko yasha jinin mutum".

Muryar Farida har tana tashi tsabar kid'ima da tsananin razanar gaske, wata irin zufa gaba d'aya ta gama wanke mata jiki, take fad'in.

"Kaii inahhh ya za'ai hakan ta faru?, ban tab'a ji ko gani ba, ya za'ai da hankalinka ka kama D'an uwanka ka ci namansa?, ni dai kawai nasan akwai Mayu akwai kuma Y'an k'ungiyar asiri, amma su ai ba ta haka suke halaka D'an Adam ba".

"Bazaki tab'a fahimta ta ba Farida, nima fa abunda naji ne nake sanar dake, nima yadda kike cikin tsananin rud'ani haka na shiga a sadda suke bayanin abunda ke shirin faruwa da K'asar Goa".

Kamar jira ake Anjali ta rufe bakinta Doctors suka fito a guje daga d'akin da aka Kwantar da Faisal suna cewa.

"Wallahi kowa yayi ta kansa shima wannan ya gama kamuwa da cutar nan, ayi Maza a kira Sojoji ko Y'an Sadda duk wadda ya kamu da cutar a harbeshi kawai, Maza-maza muje a sanar da Doctor Darniyal ya sanar da jami'an tsoro cutar ta gama shigowa hospital d'in nan".

Wata irin zabura su Anjali da Farida sukai suna k'ank'ame juna zuciyoyinsu na harbawa.

Sunma kasa motsawa daga cikin d'akin suna iya jiyo ihun su Amal bare muryar Amal dake fituwa had'e da ihun azo a taimake mata zai kashe ta, kamin su gama tantance mike faruwa suka ji k'arar an bugama mutum k'arfe a saman kai sai kuma sukaga suna fitowa da mugun gudu daga cikin d'akin.


Faruk ne rik'e da hannun Amal da Faisal ya danna mata cizo a tsintsiyar hannun nata jini sai tsiyaya yake a hannun nata.
Farida kallonta kawai take wani masifaffen tsoro gaske na sake rufeta ganin Al'ameen ya jawo d'akin ya gark'ame had'e da sauk'e nannauyar ajiyar zuciya yana dafe k'irjinsa.

Sake waro ido Farida tayi tana ganin inda Faisal ya ciji Amal har jinin dake zuba ya d'auke, sai wata irin color ta jinin daya sauya, daga ja zuwa blue, da wajan ke canzawa yana komawa Blue jijiyoyin wajan sunyi mugun tashi rad'au a wajan, fatar wajan kanta ta koma blue itama, gashi sai yamutse fuska take tana fad'in akwai zafi sosai wajan ke mata, wani shegen zafin wajan da Faisal d'in ya cije ta take ji, gashi sai wani irin kuka take mai tab'a zuciya tana kallon d'akin da masoyinta yake.

"Tunda nake a duniya ban tab'a ganin tashin hankali irin wannan ba, ya kama muyi gaggawar barin Asibitin nan gaskiya, domin naji Doctors d'in can da suka fita daga d'akin nan suna cewa cutar ta gama shigowa hospital d'in nan gaba d'aya".

Cewar Faruk yana rik'e da budurwarsa dake mak'ale a bayansa. Matan sai kuka suke Hanan ma tana rik'e da hannun nata saurayin mai suna Ahmad, ai tana jin wani sabon tashin hankali na rufeta, sai yanzu ta gama fahimtar cutar da Faisal ya gamu da ita, cutar dake yad'uwa kamar wutar daji dandanan take kashe gari komai yawan jama'ar dake garesa kuwa.

Al'ameen da hankalinsa shima baya jikinsa ya k'ank'ame hannun budurwasa yana yin gaba domin fita harabar Asibitin yana cewa.

"Ya kamata muje, zama waje d'aya ba namu bane ana cikin wannan hali, domin shi kansa Faisal zai tashi a kowanne lokaci ban tab'a ganin k'arfi irin wadda Faisal ya nuna yanzu ba, kamar wani Zaki, na rantse da kyar na shammace sa fa na buka masa k'arfin gado a kai, shine fa ya suma ba wai mutuwa yayi ba".

Bin bayansa sukai suna tafiya a hankali kamar wadda za'ace masu gasu nan su harta na kare.

Amal sai kuka take tana turjewa wai ita bazata tafi tabar Faisal a haka ba, sai da Faruk ya wanke ta da wani gigitaccan mari sana ta nutsu tana kuka mai sauti, ya rik'e hannunta suna nufar harabar Asibitin.

Kamar jira ake su fito harabar Asibitin idonsu yayi masu tozali da wani gaggarumin tashin hankalin daya kusa sa zuciyarsu bugawa.

Domin k'atotan Get d'in Hospital d'in Doctor Darniyal ke shirin bada umarnin rufesa, kamin akai ga rufesa ma Dondozen Zombies wadda suka gama kamuwa da Cutar sun danno kai cikin Asibitin, gaba d'aya masu tsaron Get d'in suka watse suna gudu had'e da ihun neman taimako da tsira da ransu, suna ganin yadda idan Zombies suka kama mutum suke yagar naman jikinsa suna ci kamar sun samu abinci, da sun saka farcensu suke yago fatar naman jikin mutum sai dai kaga ta taho kamar ansa al'makashi an yanko ta haka take yi.
Sabon tashin hankali sai da suka ga wata mace ta zama Zombie itama ta nufi inda Doctor Darniyal yake k'ok'arin harta na kare ta cafke masa hannu ta kafa masa hakura sai jini suke gani yayi wata irin tsartuwa, ihu yake yana sun kwace jikinsa sai ma wani k'arfi data sa ta kaisa k'asa ta turmushe, dai-dai cikinsa ta kafa hak'uranta sai dai kawai sukaga ta farke cikinsa tana d'ebo y'an cikin nasa tana cusawa a bakinta, tana wani irin gurnani da gunji babu dad'in ji, tun yana shure-shuren zafin fitar rai had'e da wani ihu wadda baya fita harya daina kwata-kwata, suna gani ta cire hannunsa da k'afarsa gudu d'aya yadda kasan ba naman mutum suke ci ba, kamar sun samu naman Dabba wacce aka gyara domin ci kawai.

Farida dake jikin Anaji ta fasa wata gigitacciyar k'ara had'e da sumewa a jikinta.
Da kyar Anjali ta iya tarbeta sosai a cikinta dake rawa na tashin hankali itama.
Zan iya cewa ba Farida kad'ai ce ta suma ba, harda Hanan, Ahmad ne ya kinkimeta ya sab'a a kafad'arsa, da gudu Anjali ta d'auki Farida dake sume a hannunta tana nufar wata Motar Asibitin tana cewa.

"K'uyo sauri zasu iya dawowa inda muke, kuma bana jin zamu iya k'are kanmu, tunda bamu d'auke da wasu makami a hannunmu".

Ai tun kamin ta dire maganar, Zombies wasu da suka gama cinye wasu, wasu ma nan take suke mik'ewa suma sun zama irinsu suke take masu baya.
Da gudun gaske suka fad'a cikin motar, Faruk ne ya shiga mazaunin Driver sai Al'ameen mai zaman banza, sauran kuma suka shige bayan motar, domin Motar tana da zurfi.

Zasu rufe murfin baya na Motar kawai wata Doctor tare da wani namiji suka shigo bayan a guje, har suna fad'uwa.

Ganin sun shigo suka jawo murfin a tare suna sauke lumfashi.

Ba wadda yayi magana, sai kallon harabar Asibitin suke yadda lokaci d'aya ya koma ya hargitse kamar wata mak'abarta, ga Zombies dake son yayyab'e Motar suna buga gilashin Motar suna son ba'lleshi, da mugun k'arfi suke buga gilashin, ba abunda suke buri sai cimma wa'inda ke cikin Motar, sai wani shin-shine suke suna jiyo k'amshin Bil Adam a ciki, sai hauka suke suna wani gunji marar dad'in ji.

Da kyar Faruk yaja wani uban birki had'e da zubar da Zombies d'in da suka yayyab'e Motar da suke ciki, wasu nan take ya bi ta kansu ya latse, yaba Motar wuta, wajan Get d'in fita ba sai da yabi ta kan wasu, suka fice daga Asibitin, Asibitin da zasu iya cewa duk mutunan da yayi saura a yanzu kam sunansa GAWA,
Domin har motocin dake parking lot na Hospital d'in sun fara ci da wuta, suna kallon yadda wasu Zombies dan naci suka biyo motar a guje, wasu kuwa tafiya suke a slowly suna mik'a hannunsu gaba suna tafiya suna shin-shine, jini yana dalala a bakunansu.

Su Faruk dake gidan gaba, suna bin K'asar Goa da kallo na tsallar mamakin yadda a y'an awanni cutar ta gama yad'uwa a wasu sassa na cikin garin Goa d'in.


"Kai Malam na rantse munga bala'in yau, wannan Cutar bala'i ce wallahi, duka fa k'arfe uku na dare ne yanzu duka yaushe muka kawo Faisal bamuyi fa awa uku cikakka ba, amma dubi yadda garin ya koma kamar Mak'abarta, dan Allah duba ka gani".

Fad'ar Al'ameen yana nuna garin gaba d'aya.

A bayan Motar Anjali dake rungume da Farida tasa hannunta a bayan rigarta Allah ya so tana d'auke da wata roba ta ruwa, ta kwance ta tana watsa ma Farida ruwan akan fuskarta.

Saida ta watsa mata ruwan ya kai sau uku sana taji taja wani irin lumfashi.
A zabure kuma a kid'ime ta farka.
Tana wata irin jijjiga na tsallar tashin hankali.
Sai da d'aya daga cikin Doctor d'in da suka shigo motar daga baya Macen ta matsa inda suke, tana d'an dubata, a hankali ta rink'a murza tafin hannunta, har ta samu ta d'an dawo dai-dai.
Wani murmushi Anjali ta saki tana kallon Matar ta ce.

"Thanks"

Murmushin yak'e kawai Matar ta saki a hankali ta matsa daga inda suke tana komawa inda namijin yake, jikinta a sanyaye tana kallon gilashin Motar yadda Zombies ke shawagi a cikin garin, wasu ma suna gaf motarsu suna tab'a ta da son cin masu, dan ma a hakan wani irin matsiyacin gudu Faruk d'in keyi dasu, shi yasa ko sun shige masa gaba ta kansu kawai yake bi.

Farida dake wani irin nishi kamar mai shirin kamuwa da wata cuta, da kyar ta iya bud'e baki ta ce.

"Wai ba mutuwa nayi ba dama?"

Ta k'are maganar hawaye masu zafi na sake yanke mata a fuska.

Wata uwar harara Hanan ta banka ma Farida ta ce.

"Sai tsoron masifa cike da ciki, harda su sumewa mutane, wallahi baccin Anjali da sai dai mu barki a can su cinye ki kowa ma ya huta"

Wani kallo Anjali tayi ma Hanan ta kasa hakuri ganin shi Saurayin nata Ahmad ya kasa fad'a mata itama fa suman tayi, kawai ta farka ne da kanta, ta kuma riga Farida farkawar.

"Kema fa Ranki ya dad'e suman nan kikayi, ko ni nan kad'an ya rage zuciyata bata buga ba, wannan tashin hankalin ai dole yasa Kwakwalwar kanka tab'uwa, ban tab'a ji ko labarin irin wannan abun da nake gani a yanzu ba, ace mutum nacin naman D'an uwansa"

Wani kallo Hanan ta watsama Anjali tana d'auke idonta daga kansu tana wani basarwa, ganin Anjalin na son tuna mata asiri a gaban y'ar aikinta.

Kamar saukar aradu suka ga Amal ta mik'e tsaye ta fad'i k'asa tana wata jijjiga had'e da wani irin ihu had'e da gunji, ga wani sauti dake fito daga jikinta kamar ana k'arya k'asusuwan jikinta, domin ji kake k'assss k'assss k'ak'k'asssss.

Gaba d'aya zabura sukai suna mik'ewa tsaye, mutuwar tsaye kawai sukai suna duban yadda Allah yayi da Amal, zuciyoyinsu na harba da k'arfin gaske, ga wata zufa data wanke masu jiki.
Kai Jasmin tafa kasa hakuri ta ce.

"Gaskiya a tsayar da Motar nan a fitar mana da Amal, idan ba haka ba kuma zata halaka mune muna ji muna gani, ni kuma tsakani da Allah ban shirya mutuwa ba wallahi".

Ta k'are maganar cike da tsananin tsoro tana sake ja da baya sosai.

Zan iya cewa Amal ta ji duk abunda k'awar tata ke fad'i, domin wasu zafafan hawaye ne suka yanke mata, tana jin wani mugun rad'ad'i a zuciyarta, ga jikinta dake sauyawa dan har ta fara jin k'amshin naman mutane itama, tana son ci, ji tayi ba abunda take mugun son ci kamar naman Bil Adam, harta fara y'an shin-shine, kamin ta gama fita daga yaccinta gaba d'aya ta tuno da maganar da Tsohuwar nan tayi mata a sadda suka bigeta, inda take cewa, "ta kuka da duniya, wata rana zata had'u da wata matsalar zata nemi taimakon na kusa da ita, Kuma tana ji tana gani zasu kasa taimaka mata, gudunta ma zasu rink'a yi, kuma babu yadda ta iya da su", jikinta yayi wani irin mugun sanyi na zallar nadamar da bata anfani a yanzu. Gaba d'aya jikinta ya koma fari tass kamar wacce aka shafama ruwan toka. Suma tayi suka jita shuru, sake zabura sukai har bakin Hanan itama na kyarma wajan kiran su Faruk, da mugun sauri suka ja wani matsiyacin birki kiiiiiiiiiiiiiiiiiii, jin uban kiran data kwala masu, ga dondonzon Zombies dake son cin masu a wajan da suka ja birkin.............

*GAWA TAFE*
(Zombies story)
On2025


*©Zahra Royal Star*


*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*


*EPISODE 5TO6*


dafa Faruk Al'ameen yayi yana cewa.

"Karka sake ka fita, bari ni naje bayan Motar naga miye ke faruwa".

D'aga kansa kawai Faruk yayi, Al'ameen da zuciyarsa ke bugawa ya d'auki wani k'arfi dake a gaban Motar k'ark'ashin Motar ya zaro shi yana b'alle marfin Motar ya fito zuwa waje.
Zuciyarsa ce ta halba da k'arfi ganin wani Zombies ya rik'e masa riga da fitowarsa, sauran Zombies da hankalinsu baya Kai, sukayo kanshi kamar suna jira.

Yana zufa ya daddage iya k'arfinsa yana buga masu k'arfen dake rik'e a hannunsa.

Wasu su watse wasu kuwa su k'ara tashi suna kawo masa hari.
Da kyar da sub'in goshi ya isa bayan Motar da mugun sauri har yana shirin kifewa k'asa ya bud'e marfin Motar na baya, yayi wani tsalle ya fad'a cikin motar. Yayyab'e bayan motar sukai, da kyar suka taru harda Ahmad suka rink'a dukan hannayen Zombies da suke shirin shigowa bayan Motar kamin da kyar da dabara suka rufo bayan Motar.

Idon Al'ameen ne ya sauka akan Amal dake yashe a k'asa har yanzu cutar bata gama kama jikinta gaba d'aya ba, amma color d'in jikinta gaba d'aya ta sauya, ta koma kamar horror ga wasu zak'o-zak'on farce da suka fara fito mata a y'an yatsunta.

Zuciyarsa na bugawa da tsananin k'arfi zai nufi inda take Hanan tayi saurin rik'e hannunsa tana cewa.

"Dan girman Allah Al'ameen kayi hakuri ku fitar da Amal daga motar nan, idan ba haka ba muna cikin had'ari in.......

Tasssss ya wanke fuskar Hanan da wani gigitaccan mari idonsa a waje na tsabar tashin hankali da b'acin rai mai tsananin gaske, bakinsa na rawa na tsallar masifa yake nuna Hanan da yatsa yana cewa.

"Ni kike gaya ma na fitar da y'ar uwata cikin annoba, su cinye naman jikinta, nin.......ni.....ni zan iya kai y'ar uwata a inda za'a gama da ita?, kar wadda ya sake ce min na fitar da ita daga cikinmu, sai dai duk mai buk'atar raba hanya damu k'ofa a bud'e take zai iya barin cikin Motar nan ga hanya nan".

Ya k'are maganar yana nuna bayan Motar, kamin ma ya sake wata maganar, Ahmad ya ci kwalar rigarsa yana cewa.
"Karka sake sa k'azamin hannunka ka ce zaka tab'a Hanan. Kuma ai gaskiya take fad'a, ya za'ai mubar ajalinmu a cikinmu, muna ji muna gani, bazai tab'a yuwu ba wallahi baka isa ba, sai dai kune zaku fice mana daga Motar nan amma ba dai mu ba".

Zan iya cewa yadda naga jikin Al'ameen na d'aukar rawa had'e da wani irin huce da yake na tsananin b'acin rai komai na iya faruwa a tsakaninsa da Ahmad.
Gafe gudu Farida har yanzu ta kasa motsi dan ita hankalinta gaba d'aya ma baya tare da ita, hankalinta kacokam yana ga bala'in dake tunkaro su, amma su jiba kwata-kwata sunma manta da irin halin bala'in da suke ciki, suna shirin had'a kwanji.

Kamar ance Farida ta waiga inda Amal take kwace, zan iya cewa dama kusan rabi hankalinta naga Amal d'in, sai kuma rigimar da su Ahmad keyi, kamar zasu cinye junansu d'anye.
A mugun-mugun zabure had'e da wata irin gigitacciyar k'ara

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment