Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakin ta iske Gaishina ba yadda take Ma'azzara ta fashe da kuka ta fada samanta.
Husaina ta shigo dakin hankalinta a tashe.
Ta ce"Ma'azzara kibar kuka tashi kamata muje hospital" Husaina ba tare da kyankyami ba ta kama gaishana tana fitar da numfashi daket Ma'azzara ta kamata tana kuka Husaina ta ce"Ma'azzara saketa zan rik'eta dauki kayan da zaki canza gobe da safe ki saka hijabi ki cire mayafin." Ma'azzara jikinta na rawa ta nufi gurin gari yayi zafinta ta ciro riga da zani na bakin yadisu na bugaje mai.kyau duk yasha ruwa a wanke fes sai kamshi yake ta daukarma gaishana ma ta cire mayafin, ta saka hijabi ta linke mayafin ta nasa cikin ledar kayansu ta iso gurin Husaina.
Husaina ta ce"yauwa to kamata mu tafi." Ma'azzara ta kama sharan kafadar gaishana Husaina share suka fito.

Adamsy yana hangosu ya kashe wayar da suke da Faruk Babban aminsa ya fito ya bude musu motar suka shigar Gaishina, wacce take a halin jigatuwa dan Adamsy yayi mugun tsorata da ganin tsohuwar sai sannu ya ke mata.
Ma'azzara ta shiga kusanta ta zauna Adamsy ya rufo mota ya kama hannun Husaina ya shigar da ita gaba ya rufo ya zagaya ya shiga ya tashi motar ya dauki hanyar hospital din da suka fito.

Husaina ta kwantar da kanta kirjin Adamsy yana driving da hannu daya dayan yana shafa kanta da fuskarta, Husaina ta ce" Adamsyna" Ya shafi fuskarta ya ce"Na'am Husaianta yi hakuri zan temaka musu hakika suna neman temako." Shiru Husaina tayi ta lafe jikinsa.

Ma'azzara ma tana rungume da Gaishina sai wani irin nishi take da huci.
Suna zuwa hospital likitoci suka amshi gaishana aka fara bata teamakon gagawa domin ceto ranta dan tana mawuyacin hali.
Husaina ta rungume Ma'azzara tana kuka tana lallashinta. Adamsy sai hararan Ma'azzara yake dan gani yake ta amshe masa matarsa.
Kusan 2 hours sukayi kafin likintan ya fito.
Lokacin Ma'azzara tayi bacci jikin Husaina.
Adamsy ya tari likitan ya ce"Dr yaya mai jikin?" Dr ya ce Alhmdllh da sauki amma gaskiya ciwon ya cita sosai dan kodarta d'ayar har ta fara zagwanyewa, dan wlh dole gobe sai an mata operation amma dole Agadez zaku kaita ayi k'ok'ari goben ." Adamsy ya ce"Allah ya kaimu insha Allah babu damuwa a bata duk kulawar da ya dace goben da zaran anyi sallah Asubah zan zo na tafi da ita." Dr ya amsa da "babu damuwa ku shiga ku ganta"Adamsy bai yi magana ba ya daga kansa ya dawo gurin Husaina ya ce"Bebeta ya za'ayi tayi bacci tashi muje gida na dan huta". Husaina ta tashi Ma'azzara firgigita ta farka.
Husiana ta kama hannunta suka nufi room din da gaishina take Adamsy na biye dasu.

Suna shiga suka ga an mata Karin ruwa harda abun Karin numfashi a jikinta.
Ma'azzara ta isa kusanta ta dora kanta saman kirjinta ta rufe idanunta.
Tausayinta ya cika Husaina tazo ta kama Ma'azzara ta temaka mata ta hau saman gadon, ta ce"kanwata ki kwanta ki huta zamu je gida da safe zamu zo insha Allah kinji". Ma'azzara ta gyada kanta bata bude idanuba.

Husaina ta gyara mata kwanciyarta ta juyo gurin Adamsy ta kama hannunsa ta ce"Yayana Muje na maka tausa kayi bacci". Murmushi Adamsy ya saki ya kara damke hannunta suka fito ta janyo masu kofar.
Tun a cikin motar Husaina take dannawa Adamsy jikinsa tana masa sannu murmushi kawai yake sakar mata har suka iso kofar gidan.
Rumfa ce katuwa a kofar gidan saboda yan amsar gaisuwa.

Gidan dan madedeci ne ya hadu ta ko ina tamkar ba a kauye ba, Lokacin da suka shiga duk jama'ar gidan sunyi bacci sai Ummee kadai a parlor tana jiransu.
Suna shigowa wata kyakyawar dattijuwa yar kimanin 45 year farar buzuwa mai kyan gaske wacce kallo daya zaka mata kasan akwai masu gidan rana.

Ummee ta tarbesu ta rungume Husaina Adamsy ya rungume Ummee ya shagwab'e ya ce"Ummee ni baki tawa sai ta yarki" Ummee ta kai masa dukan wasa ta ce"To yanzu abar gaishe-gaishe sai da safe kuje kuyi wanka ku huta na shirya maku komai". Ta fad'a tana sakinsu ta shige bedroom.
Adamsy ganin Ummee ta shige ya dauki Husaina cak suka nufi part din da suke sauka idan sunzo.
Suna zuwa wanka sukayi saka saka kayan bacci suka kwanta manne da junsu Husaina ta dan ma Adamsy tausa har tayi bacci kafin itama baccin ya dauketa tana manne jikin mijinta Asuba ta gari.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Washe gari bayan sunyi sallah Asubah Adamsy ya lallaba Husaina ta koma bacci, dan bayaso tasha wuya ta ce zata bishi Agadez dan so yake ya isa da wuri da zaran an gama operation ya dawo Audarass bayan ya nemi mai kula da tsohuwar.
Adamsy ya fad'ama Ummee komi ta bashi goyan baya barin ma da taji gaishana ce dan tasan tsohuwar sosai, duk zauwar da zatayi kauyan sukan gaisa kayan breakfast Ummee ta hada masa ya taho dasu.

Adamsy lokacin da yaje hospital Ma'azzara tayi wanka ta canza kaya tayi tsaf da ita bayan tayi sallah ra saka kakarta gaba tana mata hira, dan kasa kunna panpon tayi sai da ta kirawo.likita ya kunna mata.
Adamsy ya bawa Ma'azzara kayan breakfast ta ko amsa ta shige karkashin gado taci iya cinta, dan ya ce gaishana bazata ci komai ba bai wani saki fuskar saba ya dai ce mata ya mai jiki ya zauna kusan gaisha yana mata Sannu amma ina bata san inda take ba tana dai numfashin.
Ma'azzara kuwa bayan ta ci abun da taci ta fito taje ta wanko hannunta ta tsare Adamsy kur da idanu baima san tana yiba a shagwab'e ta ce" Uncle ni ce yar lelanka har goyani kake yi kana mun waka mai dadi da hira mai dadi , har wannan abun da naga kama Anty jiya nima kana mun wai bakajin tsamin bakin mutum wlh ni sai naji kamar zanyi amai...."Manyan idanunsa ya zaro ya mike ransa a bace ya ce"Ke wai uban waye...." maganar sa ce ta tsaya saboda kofar da aka turo Dr tane Adamsy ya juyo ya kallesa Dr ya ce"Yallabai an gama shirya tafiyar" Adamsy ya ce"Ok muje ko" wasu nurse suka shigo da gadon marasa lafiya suka ajiye suka dauki gaishana sai lokacin ta bude idanu tana tari ta kalli Adamsy, shima da sauri ya iso yana mata sannu.
Hannunta ta bashi da sauri Adamsy ya kama ya rike.
Gaishina ta jimke hannunsa, bakinta ta bude tana magana ba'a ji Ma'azzara ta matso ta ce"Gaishnata an sallame mu gida zamu kinji sauki gobe sai ki fadamun maganin zafi na tafi tallah...." Adamsy ya ce"Ke bamuson shirme" gaishina ta ce" Dan Allah ga Amana zan baka ka rik'eta amana bata da kowa bata da gata sai ni sai Allah ina yarinyar jiya ku taru ku rike Amana...." Cak bakinta ya tsaya tana shakuwa tana fadin wani abu amma ba'a jinta, Adamsy cikin tsawa ya cema Dr "Dallah malam ku duba lafiyarta kafin mu wuce Agadez". Adamsy bakinsa ya tsaya cak ganin gaishina bata motsi idanunta a bude tar.
Wata irin zufa yaji ta keto masa.
Nurse suka maidata kan gadon Dr ya fara dubata Ma'azzara ta matso kusan Adamsy ta kamo hannunsa ta ce" Uncle kaga yadda take ko jiyama haka tayi, dan Allah a mata magani itace gatana bani da gata sai ita." Adamsy ya kasa magana jikinsa sai rawa yake gabansa na faduwa.
Muryar Dr ya tsinto yana cewa" Allahu akbar kabiran kullun nafsin za'ikatul maut" Adamsy ya ce"Dr pls karaka cemun ta mutu, dan Allah ni ina zankai Amana, taya daga ganina baki sani ba ki bani amanar mutum, ya zanyi Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun" Ma'azzara ta saki hannuna Adamsy tana ja baya ta kece da kuka ta ce"Karya kuke bata mutuba wlh idan kuka kashe mun gaishana wlh sai kunyi nadama a rayuwarku" ta fada tana kuka ta nufi gun gawar Adamsy ya karaso gurin gawar Ma'azzara ta taba jikin gaishana ba inda yake motsi Adamsy ya beka hannunsa ya shafema gaishana idanu.
Ma'azzara ganin da gaske gaishana ta mutu ta kurma wani gigitaccan ihu tayi luuuuuu zata fadi Adamsy ya tareta ta fado jikinsa sumammiya, Idanu Adamsy ya zaro ya ce"Ya Allah wannan lamari ya kenan"...................✍🏻
*Real Ladingo ce*😅

*Karku manta ya koma na kudi kan fara shi me sauƙi sbd masoya nera 200 kacal +22792589446/+22796515805*


Ummu Fareesa💋

*💖BANI DA GATA💖*






*MALLAKAR*
👇🏻

Yar mutan Niger🤙🏻



*Bismillahir Rahamanir Rahim*



*Chapter 3*

....Adamsy hankalinsa a tashe ya nufo kofar fita, yana rungume da Ma'azzara ganin bata motsi, duk ma ya rikice saboda bai saba shiga irin wannan tashin hankalin ba.
Har ya kai kofar zai fita likitan ya ce"yallabai maidota na temakon gagawa" Adamsy bai juyoba ya tsaya ya ce" Dr muje wani room din saboda inaso a bata kulawa mai kyau ta samu hutu kayi mata alluran bacci wqnsa akalla zata kai lokacin da za'a binne kakarta bata farfado ba, idan san samune ta wuni Rana bacci bayan ba nutsu zan dawo ga amanar Allah". Ya karasa maganar yana ficewa yana mai cike da tarin damuwa fuskarsa ta nuna hakan karara dan baisa ya zaiyi da amanar yarinyar ba.
Adamsy yana fita likitan yabi bayansa tare da nurse guda.
Wani room da ba kowa likitan ya nunama Adamsy ya shiga ya kwantar da ita saman karamin gadon ya gyara mata kwanciyarta ya juya ya fice.
Likinta ya dukufa ceton ran Ma'azzara cikin 30 minutes Ma'azzara ta dawo haiyacinta ta kurma wani uban ihu tana kiran uncle da gaishana, tana fizge-fizge daket likitan ya riketa dama nurse ta hada alluran ta ba Dr ya tsura mata ko minti biyar ba taiba bacci ya dauketa tana kiran uncle da gaishana.

Adamsy yana fita ya nufi motarsa inda ya faka ya shiga ya kira Ummee yana fad'a mata, hankali a tashe ta ce zata turo masa mutum biyu su raho da gawar zata tura a kira Salamatu kanwar gaishina ta fad'ama sauran dangisu su zo a hadu a zauna ayi zaman makokin ana gidan su ummeen tunda Bature da Hassana nason temakonsu itama tana so.
Adamsy ya hana ta fad'ama Husaina dan ka hankalinta ya tashi baya kusa bare ya lallabata.
Haka kuwa akayi Ummee ta turo masa agali da gumar akayi komai aka gama aka basu gawar suka nufi gida, lokacin Ummee har tasa an kirawo yan tsarekun yan uwan su Ma'azzara wanda basu damu da rayuwarsu ba amma harda kukan munafurci kafin ma a iso da gawar, Hussaina kuwa tana can tana barcinta cikin nutsuwa dan ummee bata so ta tajima har sai na binne gaishina.

Ba'adau wani dogon lokaci ba adamcy suka k'araso da gawar gaishina aka shirya gawar aka tafi da ita gidanta na gaskiya.
Usaina ba ita ta tashi ba sai bayan da aka kai gashina yenuwan nasu ma sun soma tafiya , dama su mutuwar bawani damunsu tayi ba dan koh muazzara basu tambaya ba sunsha koke kokensu na karya da nuna tsantsar damuwar .

Daki Adamcy ya wuce dan dubo usaina ya tadda ba kowa a dakin karan ruwan dake fito a setin toilet ya tabbatar mai da usaina na ciki,Zama yayi bakin gado yana jiran fitowarta yashiga kololuwar tunanin Muazzara shi Yanzu ya zeyi da amarta da akabashi Yanzu matarnan tamishi adalci data hadashi da amarna mutum tayaya ze rike amarta bayan ko kadan bason yarinyar yake ba jininshi kwata kwata be hadu da yarinyar ba abunda yakuma samai tsanar yarinyar haukar datake mai tana kiranshi da uncle shi sam besan yazeyi ba ,
Yayi nisa cikin tunaninshi Hussaina ta fito daga wankan datake zaune saman gado ta ganshi yayi jugum kallo daya za'amai asan hankalinshi baya kusa dashi ita sam batasan ma da shigowarshi ba
Murmushi tayi ta k'arasa kusa dashi ta dafo kafadan tace" Mon trèsor meya faru yaushe ka shigo ne, k'okarin seta kanshi yayi da boye damuwarsa ya janyota jikinshi ta zauna kan cinyarshi yace "Ma babe shigowa kenan ,tashi muje na shirya ki Chak yadauke ya dire gaban mirrow yashiga shafa mata mai tare da shiryata cikin salon so da kaunar junaa...


Ta cikin mirror din ta kalleshi tace" Mon trèsor ya jikin Gashinan yaushe za'a mata aikin ne matar nan ba karamin tausayinta nakeji ba kaga irin halin datake ciki da jiya bamu taimaka ba bansan halin da zata shigaba zuwa yau kilama ta iya rasa ranta,
Hankalinshi ne yakuma tashi yasan Husaina batasan da mutuwar gashina ba taya ze Sanar mata da gashina ta mutu yasan halin Husaina da rikicewa akan abunda bekai yakawo ba bare kuma wannan da suka shiga ranta daga haduwar farko.
Maganar Husaina takoma da Adamcy daga duniyar Nazarin daya shiga ,

*💖BANI DA GATA💖*



*MALLAKAR*
👇🏻
```Real Ladingo Sweet Baby```




*Bismillahir Rahamanir Rahim*



*Chapter 4*

.... Suna shiga gun Ummee Hussaina ta zare hannunta ana Adamcy, ta nufi gun Ummee ta zauna kusanta cike da jin kunya tace "Ummeena ina kwana ya hakurin mu Nini ta tafi ta barmu Allah ya jiqanta da rahamarsa, Allah ya kai haske da ni'ima kabarinta.." janyota jikinta Ummee tayi tana shafa kanta tace "Amin ya Allah Husainata, ya kuma muka ji da ƙarin hakurin wannan baiwar Allah itama?" Da sauri ta dago kai tana kallon Ummee kafin ta juya a hankali ta kalli Adamcy dake tsaye, a bakin ƙofa hannayen sa zube a cikin aljihunsa ya zubo musu idanunsa zuciyarsa cike da fargaban damuwar da zata shiga idan aka fada mata mutuwar Gaishina.

Tana kallon Ummee fuskarta cike da alamar tambaya tace "Wace ce kuma ta rasu Ummee?" Juyawa Adamcy yayi ya dauke kansa gefe, domin baya son ya kalleta yaga irin damuwar da zata shiga saboda ba zai iya jurewa ba, kara kamota jikinta Ummee tayi a tausashe tace "Wannan baiwar Allahn mara lafiya itama Allah ya karbi abarsa..” a razane ta juya tana kallon Adamcy daya dauke kansa da sauri yayi kamar bai ji abinda Ummeen ta fada mata ba, tana girgiza kanta ta fada jikin Ummee ta kankameta hade da fashewa da wani irin kuka mai karfi da taba zuciyar duk wani mai sauraro, yayinda a gefe guda kuma ga tsantsar tausayin Ma'azzara da damuwar irin halin da zata iya shiga idan taji labarin mutuwar kakarta mafi soyuwa agareta ya risketa, saboda ta lura akwai tsantsar kauna da soyayya mai ƙarfin gaske a tsakaninsu ita da kakar tata.

Zuciyar Adamcy na tsananin suya da mugun radadin kukan da take yi, ya taka da sauri ya isa gabanta ya zauna a gefenta ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam a kirjinsa yana lallashinta, Ummee na shafa kanta da bayanta itama tana lallabata da bata baki, sai da ƙyar da sudin goshi sannan suka samu tayi shiru bayan taci kukanta sosai ta gode Allah, a hankali ta share hawayenta tana sauke ajiyar zuciya tana jan numfashi ta kara lafewa a jikinsa, dan sosai taji mutuwar Gaishina ta taba zuciyarta ga wani tsantsar tausayin Ma'azzara dake manne a zuciyarta. Ganin tayi shiru yasa ya dan janyeta a jikinsa ta koma jikin Ummee ta kara lafewa ta rumtse idonta tana jin wani iri a jikinta, ya mike a hankali ya fice daga ɗakin ya nufi kofar gida wajen zaman makoki ya zauna gurinsu Harun da Gumar da Hashim suka kara yiwa juna ta'aziyya sannan suka ci gaba da karbar gaisuwa gurin jama'a da suke zuwan musu, daurewa kawai Adamcy yake yi, amma gaba ki daya hankalinsa da tunaninsa duk sun tafi, tunanin yanda zai iya rike amanar da akabar masa kawai yake yi, wanda yake ji a ransa da zuciyarsa kamar an daura masa nauyin duniya ne da abinda ke cikinta duka a kansa.

Haka yana nan zaune a daddafe har aka kira sallar Azuhur a masallaci, suka tashi sukayi, sannan ya shiga cikin gida yayi wanka ya canza kaya ya fesa turarukansa masu tsananin ƙamshi da daɗi, nan Husaina ta kafa masa rigimar ba zai fita ba ta hanasa sakat sai da ya kamota ya lallasheta yayi mata romance ya lallabata har tayi bacci sannan ya kwantar da ita ya sakar mata kiss a kumatu da goshinta ya juya ya fice daga ɗ'akin ya koma kofar gida rumfar zaman makoki.

Sai bayan La'asar sannan ya sake komawa cikin gidan ya yiwa Husaina wanka yasa ta daura alwala suka fito tayi sallah, ya shiryata tsab tayi kyau sosai shima ya sake kayan jikinsa suka nufi asibiti gurin Ma'azzara.

Suna isa direct ɗakin da aka kwantar da ita suka nufa, lokacin da suka shiga ta farka likita na tsaye a kanta tanata fizge-fizge tana zuba ihu tana kiran sunan Uncle da Gaishina, da gudu Husaina ta nufeta ta kamota jikinta tana ƙoƙarin lallashinta ta sake fizgewa taƙi tsayawa ta ci gaba da fizge-fizgen da takeyi tana kiran sunan Gaishina da Uncle tana kuka, cike da damuwa Husaina ta kara kamota jikinta tana lallashinta ta sake zamewa taƙi saurarawa, a marairaice Husaina ta ɗago tana kallon likita cikin tsantsar damuwa tace "Dr dan Allah kayi wani abu akai mana..?" Likita yana kallonta da damuwa a fuskarsa yace "Tun ɗazu faman da muke tayi da ita kenan tun da ta tashi amma taki tsayawa... sai kiran Uncle take." Ya faɗ'a yana juyawa ya kalli Adamcy yace "Kazo dan Allah kayi mata magana zata tsaya.."

Wani irin haushi da tsantsar takaici Adamcy yaji a zuciyarsa, shifa baya son sakakkun yara shagwaɓaɓɓu dan yaga alamar yarinyar kuma ta fiye sangarta da shagwaɓa da yawa ya buɗe baki zai mata tsawa kenan ya tuna da amanar da Gaishina ta kamo hannunsa ta damƙa masa, take sai jikinsa yay sanyi ya matsa a hankali kusa dasu ya zauna a bakin gadon, ya karb'eta a hannun Husaina ya riƙe hannunta a hankali ya ɗan dora kanta a kafad'arsa cikin lallashi da kwantar da murya yana bubbuga bayanta yace "To yi shiru ga Uncle d'in naki yazo... Mene ne.?" Jin muryar Adamcy da tayi yasa ta tsaida kukan nata cak tana sauke ajiyar zuciya ta kara nitsa kanta a ƙirjinsa tana shasshekar kuka haɗe da sauke numfashi, cike da ƙyanƙyani yasa hannu ya tattare mata gashin kanta mai tarin yawa da santsi ga tsayi ya daure mata, sannan ya gyara mata zaman hijabin jikinta, Husaina sai daɗi take ji tana sakin murmushi tace "Mon trèsor ko kai fa. Wallahi naji daɗin hakan da kayi, ka lallabata." Ta faɗa tana jin daɗi sosai a ranta.

Ma'azzara kuwa tunda dai taji muryar Adamcy a kusa da ita hankalinta ya kwanta tai luf ta kara lafewa sosai a jikinsa, shi kuma a hankali cikin ƙyanƙyami yake shafa kanta mai laushi a zuciyarsa yana jin tsananin ƙyamar taɓa jikinta da yake yi sosai yake jin ba daɗi a ransa, amma ya zama dole ne ya kula da ita dan babu yanda zaiyi saboda ta zama amanarsa.

Ganin ta natsu tayi shiru yasa Dr ya sake dubata yaga bata da wata matsala, Adamcy ya ɗago yana kallon Dr yace "Ko zaka iya sallamar mu idan babu wata matsala?" Jinjina kansa Dr yayi yace "Eh dama kaman abin ya firgita ta ne tayi doguwar suma, amma bata da wata matsala zan iya sallamarku." A hankali Adamcy ya janyeta a jikinsa ya matsa gefe Hussaina ta matso ta rungumeta, shiru tayi tana bin Adamcy da wani irin kallo kamar zata lashesa, dan ita babban burinta kawai ta kasance tare dashi, har wani farin ciki take ji yana ratsa zuciyarta wata natsuwa na saukar mata a gangar jikinta, sai a lokacin ta tuna da mutuwar Gaishina abin ya dawo mata, tana jin mugun ciwo da zafi mai haɗe da raɗaɗin baƙin ciki a zuciyarta ta sake rushewa da kuka ta fizge jikinta daga jikin Hussaina tana kuka haɗe da ihu tana fadin "Gaishinata...Wayyo Allah Gaishinata.... Wayyoooooo Gaishina ta.." ta sakko da mugun gudu ta rirrike Adamcy a kiɗime tana "Uncle ka gaya min da gaske ne ta rasu..?" Wani iri yaji a zuciyarsa a hankali ya kamota ya riketa yana kallon fuskarta cikin sanyin muryarsa da lallashi yace "Kiyi hakuri, dan rasuwa ta rasu, amma insha Allahu zan riƙe ki amana kamar yanda Gaishina ta bamu amanarki nida Hussaina..." Ya fad'a yana kamo Hussaina jikinsa suka haɗu su uku suka rungume juna, Ma'azzara tana kuka Husaina ma na kuka, da ƙyar Adamcy ya samu ya lallaɓasu, likita ya sallamesu, yana riƙe da hannun Husaina, Husaina na riƙe da hannun Ma'azzara suka fita, suka shiga mota suka nufi gida.

Ma'azzara na zaune a baya Adamcy da Hussaina na gaba yana riƙe da hannunta ɗaya yana tuƙi da hannu ɗaya, yayinda itama Husaina har lokacin take riƙe da hannun Ma'azzara dake ta rasgar kuka tana kiran sunan Gaishina, a haka har suka ƙaraso gida, Husaina ta kaita part d'insu ta had'a mata ruwan wanka ta kaita toilet tayi wanka ta wanke mata gashinta ta gyara mata jiki, ta dauko mata kaya a cikin nata ta bata ta saka, suka ki shigarta sai da ƙyar saboda sun mata kaɗan sosai, domin ita Husaina bata da jiki Ma'azzara ta fita ƙiba, duk surarta ta fito 'yan ƙananun matasan nonuwanta duk suka fito, ta gyarata sosai ta shiryata tsaf ta bata abinci taci sosai ta ƙoshi sannan ta kama hannunta suka nufi part d'in Ummee.

Suna zuwa Ummee ta riƙota ta rungumeta a jikinta tana jin tsananin tausayin Ma'azzara a zuciyarta, ta fara lallashinta cike da nuna tsantsar kulawa tana fada mata daɗaɗan kalamai, kan tayi haƙuri ta yiwa Gaishina addu'a itace kaɗai abinda take bukata daga gareta, tana gyaɗa kanta wasu hawaye na sake zirarowa kan fuskarta.

Da misalin karfe tara na dare su Hussaina na zaune a parlo da yan tsirarun mutane Adamcy ne ya shigo waya manne a kunnansa yana sakin murmushi, ya magana cikin siririyar murya sa tamkar baya son maganar ya zauna kusan Ummee, ya dora kansa a kafadarta cikin harshen fransanci ya ce "ma tant ga Ummee kuyi magana". Murmushi ummee tayi ta gano Rukaiyya ce mahaifiyar Hussaina.

Amsa tayi ta kara a kunnanta tana sakin murmushi. Ma'azzara kuwa tana jikin Hussaina tana bata labari mai dadi, amma Ma'azzara tayi nisa aduniya kallon Adamcy ko kiftawa bata yi Adamcy ya kai kallonsa gefen su Hussaini karaf suka hada idanu da Ma'azzara ta kafesa da idanu.
Kansa ya dauke gefe k'asan makoshi ya furta "Wannan inaga mayya ce tirr ina dalili". Ya fad'a yana kai kallonsa kan Hussaina wace ta dukufa tana ma Ma'azzara hira.

Haushi ya ciki Adamcy kenan bata ta tashi ma mik'ewa yayi tsaye, ya zura hannunsa aljihu ya ce"mon Bebe zo na ganki". Hussiana sai lokacin ta d'ago ta kalli Adamcy taga fuskarsa murtik ba walwala da sauri ta janye Ma'azzara ta mik'e tsaye ta nufi gunsa tana langwab'ar da kanta. Adamcy ya nufi kofar fita tabi bayansa da gudu Adamcy yana dab da fita Salamatu ta shigo da sallama, Adamcy ya amsa yana kallonta ganin suna yar kama da Ma'azzara tsaye tayi daga inda take, ta kalli Adamcy tace"Nazo na tafi da Ma'azzara ne ni kanwar Babanta ce uban mu daya dashi bazamu barta cikin daula ba taje ta manta da butar ubangaji, dan haka ke taso mu tafi ta nufi gurin Ma'azzara tana zaro mata idanu.

Ma'azzara a mugun tsorace ta mik'e jikinta na b'ari da gudu tayi kan Adamcy tana kiransa "Uncle ka ceceni karka bari su tafi dani" Adamcy ya warema Ma'azzara hannunsa ta kara so ta fada jikinsa tana kuka, jikinta sai kyarrrrma yake dan tana mugun tsoron Salamatu.

Adamcy ya maida hannunsa ya zagaye bayanta ya watsama Salamatu mugun kallo wanda yan hanjinta saida suka kada, amma saboda tsabar dauriya da mugunta da take cinta, dan yau ta tsara naunin azabar da zata mata ta ce" Haliru ku shigo a yita ta kare wlh sai sun bamu yarmu haka kawai salon a sata ta manta da Ubangijinta wlh sai kun bamu yarmu saboda.... tsawar da Adamcy ya mata ne, yasa sauran maganar ta mak'ale mata..................✍🏻
Real Ladingo ce😅

*Na kudi ne Kan fara shi Nera 200 kacal +22792589446/ +22796515805.*

Daga...✍🏻ummu Fareesa💋💋💋

*💖BANI DA GATA💖*




*MALLAKAR*
👇🏻
```Real Ladingo Sweet Baby```

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


*Chapter 5*


.....Cike da tsoro ta matsa baya tana zare idanu. Haliru ya shigo yana Washe baki ya ce"Yauwa ke taho mu tafi gida, wannan ai rashin tarbiya ne ki shiga jikin samgameman kato haka subahanallahi, dole zan aura miki Mati mai wanki kya karasa girma a gidansa". Haliru ya fad'a yana nufo gun Adamcy. Ummee ta mik'e ta bisu da kallo cike da mamaki, haka sauran jama'ar ma kallon ikon Allah suke. Cikin kakausar murya Adamcy ya ce

Please Login or Register in order to submit comment