Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan uncle.
Ganin taƙi daina kukanne kana taƙi yin bayani, ya sanya Adamsy daka mata tsawa cikin faɗa yace.
"Ba tambayarki nakeyi bane? Meyasa bakya jin magana ne ke? Zakimin shirune ko sai na makeki yanzu anan!."
Jin tsawa da faɗansa yasa Ma'azzara shiga yanayin tsoro, amma hakan da yayi sai ya ƙara jefata acikin shauƙin yin kuka, hakan yasa ta ɗan ja baya da tashi tayi akan kujeran, da gudu ta juya inda take sake sakin sabon kuka ta nufi stairs don komawa ɗaki, gaba ɗaya sautin kukanta ya cika falon, sam ko lura da Hussaina dake tsaye tun ɗazu akan stairs ɗin tana kallo da jinsu batayi ba, gaba ɗaya idanunta sun cika da hawaye ko kallon gabanta sosai bata yi.
Jikin Hussaina ne yayi sanyi, da sauri takai hannu dan kamo Ma'zzara amma ina tuni Ma'azzara tayi mata nisa, don har takai ɗakinta.
Har ta gama haurawa steps din bai ɗauƙe idanunsa daga kanta ba, har saida ya daina ganinta, hannuwansa ya sanya inda ya rufe fuskarsa, sam bayason kukan Ma'azzara ko kaɗan, yana jin kukan nata har acikin zuciyarsa.
Abinci yake da niyar ci, amma hakanan yaji gaba ɗaya abincin yafita daga ran shi, ko yunwar ma yaji ya daina jinta, daman baici na rana ba, miƙewa yayi daga zaunen da yake, da sauri ya ɗauki ummu Saudat ya rungumeta ya nufi bedroom ɗinsa yana shiga ya rufo ƙofar,  da kallon mamaki Hussaina ta bisa, ta fahimci cewa sam baima ganta ba, ahankali ta gama sauƙowa daga kan step ɗin, kaitsaye ɗakinta dake ƙasa ta nufa.

Adamsy na shiga cikin ɗakin ya faɗa kan gado, ya dora ummu kirjinsa, a hankali ya lumshe idanunsa, yana mejin wasu irin abubuwa na yawo ajikinsa, karon farko kenan da yaji wani abu ajikinsa, sakamon rungumarsa da Ma'azzara tayi, sannan hakanan yaji zuciyarsa tayi masa zafi sosai da ganin hawayenta, wani irin haushin kansa ne duk yabi ya lulluɓesa sakamakon tunawa da irin yanda ya ɗaga mata murya,  har yanzun sautin kukanta ne ke yawo acikin kunnensa, rumtse idanunsa yayi da ƙarfi, sakamakon tunawa da yayi cewar itaɗin Amana ce agaresa, sam kome tayi bata cancanci tsawa irin wanda yayi mata ba, wani irin yarrr haka yaji ajikinsa sakamakon tunawa da yanda ta shige cikin jikinsa da yayi, wani irin ɗumi na musamman yaji ajikinsa,  da sauri ya kawar da wannan tunanin daga mine ɗinsa, tashi zaune yayi, ahankali yaji zuciyarsa na tsananta bugawa, yayin da yake jin ƙirjinsa yayi masa nauyi kamar zai faɗo,  lumshe idanunsa yayi tare da sanya hannu ya dafe daidai saitin zuciyarsa,  ko kaɗan baya fatan abun da zai tarwatsa rayuwa da jin daɗinsa, baya son gaskata tunaninsa,  sosai yake jin tsoron sabuwar ƙaddaran dake shirin zuwar masa batare daya shiryawa hakan ba, tabbas idan abunda yakeji azuciyarsa ya zamanto gaskiya baisan ya zaiyi da rayuwarsa ba, menene matsayinsa kenan?   Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da sanya tafukan hannuwansa ya dafe kansa, tabbas yasan SO yakuma san alamominsa, saidai kuma yana jin tsoron Soyayyar Ma'azzara da ta jima tanacin ƙasan zuciyarsa batare daya sani ba, saidai kuma wani lokaci yakan ji cewa ba soyayya bace, kawai tausayinta yake ji domin itaɗin ta kasance Amana ne agareshi.
Duban agogo yayi yaga ƙarfe 6 hadda rabi, hakan yasa shi kwantar da ummu wacce take ta halba ƙafafunta tana zullo harshe waje, ya shiga toilet ya ɗauro alwala,  yana fitowa daga cikin toilet ɗin Hussaina na shigowa, sosai tayi kyau cikin shigar doguwar rigan dake jikinta, dubanta yayi tare da ɗan sakar mata murmushi, itama murmushin tayi masa, ahankali tashiga takowa zuwa garesa, saida ta kawo daf dashi kafun ta tsaya, shagwaɓe fuska tayi tare dayi masa kallon tsantsar so, akasalance tace "Mon trésor masallaci zakajene?."

Kansa ya gyaɗa mata alamar "Eh." murmushi tayi tare da jinjina kanta, so take tayi masa magana akan abun da yayiwa Ma'azzara sam baidace ba, amma kuma wani abu da zuciyarta ke faɗa mata yasanya ta yin shiru, so take tagaskata tunaninta akansa, saboda haka zata ƙyaleshi kawai,  matsowa kusa da ita yayi inda ya manna mata kiss akan goshinta, Ummu ta ɗauko, tana kissing ɗinta Adamcy ya kama hannunta suka fice daga cikin ɗakin,  suna zuwa falo ya saketa, inda ya fice daga gidan gaba ɗaya, itama ɗakinta ta koma danyin nata sallah'n.

Ma'azzara kuwa koda ta koma ɗakinta, kuka ta cigaba dayi mai tsananin taɓa zuciya, tayi kuka sosai har saida taji kanta nayi mata ciwo, lokaci ɗaya idanunta sukayi luhu luhu dasu,  sosai takejin wani irin azababben kewa na game gaba ɗaya ilahirin jikinta, shiga jikinsa da tayi yasa ta shaƙo daddaɗan ƙamshinsa, wanda ako da yaushe ke ƙara hura mata wutar so da sha'awarsa,  sosai tsawan da yayi mata ya taɓa zuciyarta, hakan yasa taƙara narkewa  tare da jin cewa tarasa madafa,  taso ace ya fahimceta amma me yasa yakasa fahimtar ta, tayi alkawali daga yau zata kama kanta, ko mafarkin ma da tanada damar hanashi zuwara mata da tayi, tayi alkawalin ko zata rasa ranta bazata ci Amanar Aunty Hussy ba, ko maza sun ƙara wlh bazata taɓa yarda Hussy taga son mijinta a idanunta ba, ko shi kansa daga yau bazai sake gani ba, sosai yunwa ke ƙwaƙulan cikinta amma hakanan taji abincin ma yafita aranta, jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne ya sanyata tashi ta ɗauro alwala, koda tayi sallan magriba bata tashi akan sallayan ba nan tazauna tanajiran aƙira sallan isha tayi....

************** ******** **************
Bayan sati ɗaya

Garin Audarass

Acan garin na Audarass kuwa yau Ummee ta kawo masu ziyara, bayan ta kwashi hutun kwana goma A garin na Agade, ta isa lafiya, inda ta shirya da kanta tanufi gidan Salamatu don isar da saƙon da Farouq ya bata.
Tun daga zauren gidan taketa kwaɗa sallama amman babu wanda ya amsata saima hayaniya da masifan da takeji na tashi acikin gidan, tun daga cikin zauren taji wani irin ƙara irin na tusa marar daɗin ji, tuni ma kafun taƙarasa shigowa gidan masifaffen warin na tusa ya ziyartota, da sauri ta sanya mayafinta ta toshe hancinta, kana ta ƙarasa kutsawa cikin gidan, Salamatu ta hango atsakiyar gidan ita da wata mata sai dakuwa suke, yayinda Halliru da kuma Malam Musa ke ta ƙoƙarin rabasu amma sun kasa, tuni zanin Salamatu ya faɗi ƙasa, babu abun da kake hangowa sai wani macaccen buje wanda yaci uban datti,😹 saboda tsabar dattin dayake dashi har baka iya tantance wani kala gareshi, uwa uba jikinsa kota ina jurwaye ne, ba abun dake tashi ajikin bujen sai tsamin tsiya.🙊
Cikin ƙarfin hali irin na Salamatu ta kamo kan Kaltume me adashe,wanda da itane suke faɗan, duk dan wai akan tazo kan maganar adashe, don ankwana biyu Salamatun batayi zubi ba, shine tabiyo jin dalili daganan kuma faɗa ta kaure tsakaninsu, kasancewar dukansu masifaffun mata ne kuma sam basuda haƙuri. Cikin ƙarfin hali irin na Salamatu ta kada Kaltume mai adashe, nanfa ta ɗale kan Kaltumen inda ta kamo kan Kaltumen ta nannaɗe cikin bujenta,  wani irin ihu haɗi da kururuwan neman taimako Kaltume ta shiga yi, inda take cewa.
"Wayyo Allah Na jama'a kutaimakeni, zata kasheni da wannan fitinannen warin bujen nata, nashiga uku wani irin buje ne wannan?." Tuni maganan Kaltume ya maƙale sakamakon wata ƙatuwar tusa da Salamatu ta sake, wayyo Allah tuni ɗaci yacika maƙoshin Kaltume mai adashe, yayin da warin tusan yakusa zautar da ita, cikin gajiya haɗi da tsananin neman taimako,  tace. "Don girman Allah Malam Musa ka ceceni, zata kasheni wayyo Allah na wannan wani irin masifaffen warine mai kama da guba, wallahi wannan warin na buje da tusan yamafi guba illa." Tarine ya sarƙeta don kuwa tuni cikinta harya fara wuntsulawa, sakamakon wari da tsami.

Ummee dake tsaye ne tasaki murmushi, sosai itakam take mamakin ƙarfin hali, da shegen yawan tusosi irin na Salamatu, ba abunma dake bata dariya kaman yanda Kaltume mai adashe ke ihu tana neman agaji,  Malam Musa kuwa babu yanda baiyi ba akan Salamatu ta sauka akan Kaltume, amma sam taƙi saima ƙara zauneta take, Halliru kuwa komawa gefe yayi yanata buga dariyarsa, don ya tabbata Kaltume yau saitayi jinyar kusan sati guda, donshi kansa da sukayi faɗa da Salamatu, duk da baiji ɗoyin bujenta ba, amma saida yayi kwana uku cur yana jinyan jikinsa da kuma numfashinsa wanda ya sanja, yazama idan ma ya shaƙi numfashi warin tusosin Salamatu kawai yake shaƙa, saboda yanda tayita buga masa su, hakanan sanadin faɗansa da ita ya daina jin wari da kuma ƙamshi.
Ganin dagaske Salamatu na shirin  nakasa Kaltume yasanya Ummee ƙarasowa da sauri, cikin tausasa murya tace "Hajiya Salamatu ayi haƙuri hakanan, nasan zuwa yanzu ta tuba."
Jin baƙuwar murya yasa Salamatu ɗagowa don ganin wake magana, ganin Hajiya Ummee ya sanyata washe baki, lokaci guda ta miƙe tsaye, cikin farincikin ganin Ummin tace.
"Ranki ya daɗe sannunki da zuwa, ae inanan ina koyawa wannan Kaltumen hankali, bansan da zuwanki ba." Taƙare maganar tana me laluban zaninta ta ɗaura.
Kaltume kuwa jin Salamatu ta ɗagata hakan yasa awahalce ta yunƙura zata tashi, wani irin amaine yazo mata take tashiga kwarara aman awajen, tayi matuƙar galabaita.
Tsalle Salamatu tayi ta dire, cikin sabon fitinan daya ciyota tace.
"Kutumar Ubancan! Kaltume ni kike zubawa ƙazanta acikin gida? kan babban bala'i, to wallahi saikin kwashesa tsaf, kokuwa kisa harshenki ki lashesa, idan bahaka ba kuwa mu ɗaura daga inda muka tsaya, dan Uban mutum ae yanzun kam zai san cewa ba tsoronsa nakeji ba!."
Tuni cikin Kaltume ya ɗuri ruwa, cikin matsanancin tsoro, tayi ƙoƙarin maida aman daya kuma taso mata, tayi imani cewa yanzu kam Salamatu na ƙara maida ita cikin bujenta, to wallahi mutuwa zatayi, yanzun ma kaɗan ya hana ta suma, ko yanzun ma bawai ta tsira bane, dole nema sai taje asibitin cikin gari anyi mata wankin ciki, don warin tusan Salamatu kaɗai ya isa ruɓar da hanji.

Ummee ne taja Salamatu suka koma gefe dan sauri take zata koma, ita kuwa Kaltume tuni ta rarrafa ta arce da gudu batare data kwashe aman da tayin ba, kwafa Salamatu tayi tare da cewa.
"Wallahi zankwashe nakuma samiki aleda abiyoki dashi har gida."

Murmushi kawai Ummee tayi tare da gyara zama, nan suka sake sabon gaisuwa da Salamatun harma dasu Malam Musa, da kuma Halliru,   babban ledan dake gabanta ta miƙowa Salamatun cikin halinta na nagarta tace.
"Wannan saƙone daga wajen Farouq , wato wanda yake neman auren Ma'azzara, shida kansa yace akawo muku!."
Baki Salamatu ta washe take ta jawo ledan tare da buɗewa, ganin abun dake ciki yasa ta dafe ƙirji, cikin mamaki tace.
"Ƙalu innalillahi duka wannan nawane? kayafa nake gani niƙi niƙi Hajiya, halan ko mai shegen arzikine shiɗin?."

Jin abun da Salamatun ta faɗa yasa Halliru matsowa da sauri, ya ƙaraso wajen yana kiran Ladi matar sa , so yake ya leƙa cikin ledan amma tuni Salamatu ta kulle bakin ledan ta ɗaga ƙasan bujenta ta tura ledan, fuskarta cike da tsananin farin ciki marar misaltuwa tace.
"Wayyo daɗi barni daraina karka kasheni, ashe Ma'azzara zata zamo alkhairi agaremu, kai nagode sosai Hajiya, Allah yaƙara muku arziki dukanku, a'a wannan abu ae yayi daɗi  hahahhhhh, lallai wasu zasu mutu da baƙinciki." Taƙare maganar cikin matsanancin shauƙi, har wani karkaɗa ƙafanta take, tana girgiza kai alaman duniya tafara samuwa agareta.
Murmushi Ummee tayi, tare da miƙewa tayi musu sallama, nan fa Salamatu ta rakota Itada da Halliru da Ladi matarsa, suna tambayar lafiyar Ma'azzara da uwayan hidanta, sun duk a gaishe su, har bakin ƙofar gida suka rakata, Salamatu ta dawo sai washe haƙora take, kai kace bushara akai mata da aljanna.
Tana dawowa gida ta baje akan ɗan rumfan dake bakin ƙofar ɗakinta, nanta buɗe ledan tare da zazzage duk wani abu dayake ciki, atamfofine masu kyau sosai guda uku, sai kuma yadin shadda na maza masu kyau suma guda uku, sai kuma takalman maza ƙafa uku, haka na mata ma irin flat shoe ɗinnan suma masu kyau,  sai kum kuɗi naira Jaka ashirin ta cefa, guɗa Salamatu tayi saikuma ga tusa mai ƙarfi ta biyo baya, cikin tsananin jin daɗi tace.
"Ayyiririii!! Saini Salamatu, tabbas dama naji ajikina cewa duniya takusa fara damawa dani, ahayye nanaye!." Taƙare maganar tana sake sakin guɗa.
Ganin uban kayan dake gaban Salamatun yasa Halliru sakin murmushi, cikin jin daɗi yace.
"Kai amma kuwa Salamatu mun more suruki, lalle zamu fantama ji wasu yadukan shadda masu uban kyau." Yaƙare maganar yana kai hannunsa daniyar ɗaukan shadda ɗaya ya duba.
Hannu Salamatu ta sanya ta buge nasa hannun, wata uwar tusa ta sake mai shegen masifar wari tare da galla masa harara, aharzuƙe tace "To mazari, sarkin azarbabi, harwani bakin yaba kaya kake dashi, inace nannan kwanakin baya, kadinga zugani kan cewar kada na yarda na bar musu Ma'azzara, yanzu kuma shine da alkhairi ya isoni, kake neman shigewa jikina muci tare ko, to ƙwalelenka."

Hannu Halliru ya sanya ind a ya toshe hancinsa, sosai warin tusan kesawa yana jin ɗaci amaƙoshinsa, kwantar da murya yayi cikin son lallaɓata yace.
"Haba Salamatu mufa ƴan uwan junane, kuma kin manta tun kwanaki muka shirya muka kuma daina faɗa, inkin bani ae ba raguwa zakiyi ba Salamatu, kuma kin manta da cewar ma ita matan ɗazu da sunan Hajiya ta ƙiraki? Hajiya Salamatu fa tace, kika sani ma ko shirye shiryen kaiki Makka suke!." Halliru yafaɗi haka cikin son Koɗa Salamatun.
Aikuwa ta famfu don lokaci guda taji kanta yaƙara girma, take ta washe baki, nan fa taciro shadda kala biyu da takalmi kala ɗaya ta basa,  take ya cika da matsanancin murna, haka ma taɗauki shadda kala ɗaya da takalma kala biyu tabawa Malam Musa dake tsaye yana jinsu tun ɗazun, dubu bibbiyu tabawa kowannensu,ita kuma tasa sauran aƙasan bujenta, nan sukayi mata godiya.

*Naimey*
Yau tsawon sati ɗaya da kwna 2 da faruwar al'amarin, Ma'azzara ta kame kanta bata yarda ta nuna wata damuwarta tana ƙoƙarin cire uncle Adamcy a ranta, sau biyu rak suka hadu, amman bata yarda ta nuna masa wani abubu gaishe sa kawai take, ta saki ranta suna hira da Hussy tana ma ummu wasa. Hakan yasa Hussy watsar da duk wani kokwanto, Hassana kusan kullum se tazo amman bata samun ganin Adamcy ko Ma'azzara dan ta maida hankalinta karatu, bata dawowo sai kusan 5 pm.

Yau ta kama Weekend ne Adamcy yana gida amman yana ɓangaransa can suka wuni suna sheƙe ayarsu da Hussy unmu Saudat kuwa na gun Ma'azzara, wacce yau se kuka take ta rasa dalilinsa.
Tunda Adamcy ya fita bayan sun gama more rayuwar su da Husst, yafita gidan bashi yadawo ba sai bayan sallan isha.

Hussaina ce zaune tayi jigum inda take karanta text message ɗin da ƴar uwarta Hassana taturo mata, wanda gama wayarsu da ita kenan,  ahankali take karanta text message ɗin, inda aka rubuta saƙo kamar haka.
_Ni ƴar uwarki ce Hussaina, bazan faɗa miki maganar da take bahaka ba, babban kuskuren dakikayi arayuwa shine bawa tsintacciyar mage dama, nafaɗa miki amma kinƙi amincewa, kan cewar lallai yarinyar nan da Adamsy son juna suke, shikenan to amma inaso kibani haɗin kai don mujarraba, idan muka gwadasu kikaga saɓanin abun dana faɗa miki, nayarda kada ki gaskata tunani na._
Shiru Hussaina tayi, har acikin ranta gani take cewa shirme kawai Hassanan nata ke faɗi, waima bayan tace Ma'azzara ne keson Adamsy, yanzu ta dawo tamace wai Admsyn nata ma nason Ma'azzara, murmushi kawai Hussaina tayi, tabbas tasan idan tabiyewa bahagon tunani irin na Hassana, to fa tabbas zata kwan aciki, amma kodan ta ƙaryata tunanin Hassanan zata amince su jarraba, tasan dai babu wani abu tsakanin Ma'azzara da Adamsy, sam baima yiwuwa ace wai Adamsy da  Ma'azzara son juna suke, tasa aranta cewa shirmene kawai irin na Hassana.
Tayi nisa acikin tunaninta,saiji tayi ya kwanta abayanta, murmushi tayi tare da juyowa ta fuskancesa.
Idanunsa ɗaya ya kashe mata, ahankali yace. "Kin manta dani ko?."  
Lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa ta shafa, tare da shigewa cikin jikinsa, fuskarta ya ɗago inda ya haɗe bakinsu waje ɗaya,  ahankali yake bata professional kissing.

Ma'azzara kuwa tana idar da sallan isha, miƙewa tsaye tayi, ɗan madaidaicin fridge ɗin dake cikin ɗakin ta buɗe, goran yoghurt ta ciro, inda tasha kaɗan ta maida sauran,   komawa kan gado tayi ta kwanta tare da duƙunƙunewa waje ɗaya, ahankali hawaye ke tsiyaya daga cikin idanunta, kasancewar tayi kuka sosai, hakan yasa tana kwanciya bacci ya ɗauketa, wanda ke cike da mafarkin Uncle ɗinta, mafarki masu daɗi tayi dangane dashi, wanda sune suka gusar da damuwar zuciyarta.

Washegari, Saturday.
Tun 7 yabar gidan domin suna da meeting da wani babban kamfani da zasuyi.
Kasancewar yau weekend yasan ya koda tatashi bata fito ba, sai wajen 8 sannan ta sauƙo,  Nan ta iske Aunty Hussaina zaune a falo, tana bawa Ummu Saudat nono,  cikin girmamawa tagaishe da Auntyn nata, tare da zama akusa da ita, nan ta karɓi Ummu Saudat ɗin, tanayi mata wasa, duban tsab Hussaina tayiwa Ma'azzaran, take taji wani abu ya ɗarsu aranta,  saurin kawar da tunanin da ke ranta tayi, ahankali taƙira sunan Ma'azzaran.
Ɗago kai Ma'azzara tayi ta dubeta, murmushi tayi tare da cewa "Na'am Aunty."
Cikin kulawa Hussaina tace "Meyasame ki naga idanunki sun kunbura, kuka kikayi ne?."
Da sauri Ma'azzara tayi ƙasa da kanta, cikin sanyin murya tace.
"A'a Aunty kawai dai ƙwaro ne ya shiga idona."
Murmushi Hussaina tayi tare da cewa, "Allah ya sauwaƙe."
Tashi tsaye tayi tare da duban Ma'azzaran tace. "Gacan kayan break ɗinki nan a dinning, ki kulamin da Ummu Saudat, ni zanje gida bazan jimaba zan dawo."
"To" Kawai Ma'azzara tace, tare da ƙarasawa gaban dinning ɗin, still tanayiwa Ummu Saudat wasa.

Sama sama Hussaina tayi kwalliya inda tayafa mayafi ajikinta, sallama tayiwa Ma'azzara sannan tafice daga gidan.
Tana fita tasamu Hassana acikin mota, tana shiga cikin motar tace.
"Gaskiya ni gabana faɗuwa yake Hassana, akan menen zaki tursasani zargin mijina da kuma yarinyar da take matsayin amana awajenmu?."
Murmushi Hassana tayi tare da cewa.
"Zaki gaskata maganata nanda wasu mintuna." Key tayiwa motar inda suka gangara can gefen hanya,  duban Hussainan tayi tare da cewa "Ƙirasa."
Cikin faɗuwar gaba Hussaina ta danmawa Adamsy ƙira, bugu uku ya ɗauka.
Cikin fargaba ta kwantar da murya tare da cewa.
"Mon trésor ya meeting ɗin dae?"
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Lafiya lau mun ma gama ae, kuntafi ne?."
Ɗan jim tayi tare da cewa "Eh, amma na ɗanyi mantuwa please ko zaka koma gida ka ɗaukomin, ina gida saika kawomin please mon trésor!."

Shiru Adamsy yayi tare da cewa.
"Mantuwa kuma? hope ba Ummu Saudat kika manta ba."
Ɗan murmushi tayi tare da cewa "No ba ita bace ita nabarta wajen Ma'azzara, kasan yau saturday ba school."

"Su biyu kaɗai kika bari agidan?."
Mamakin tambayan da yayi matane yasanya ta cewa. "Eh amma ai akwai Hadiza me aiki a ɓangaranta, hakan baiyi bane?."

"A'a" ya faɗa ataƙaice tare da cewa "Sai nazo." ƙitt ya kashe wayan,  ajiyar zuciya ya sauƙe tare da dafe kansa, dama yana buƙatar komawa gida, domin zuciyarsa cike take da son bawa ƴar amanarsa haƙuri akan abun dayayi mata tsawon kwana 8 dole zai lallaɓata ta yanda zata goge tunaninsa daga mine ɗinta.
Hussaina na aje wayar ta dubi Hassana cikin damuwa tace.
"Nafaɗa masa, amma Hassana...."
Da sauri Hassana ta katseta tahanyar cewa. "Shiiii! Kedai ki zuba ido kisha mamaki."

After 25 minute.

Ma'azzara ce zaune akan kujera, gefe kuwa Ummu Saudat ne keta wasa, shiru Ma'azzara tayi tare da lumshe idanunta, sosai take jin matsanancin kewar Uncle ɗinnata, amma kuma idan tatuna da abun da yayi mata kwanaki, sai taji ranta duk ba daɗi.
Cikin takusan mai ɗauke da nutsuwa ya ƙaraso cikin falon,  tsayawa yayi tare da cusa duka hannuwansa acikin aljihun wandonsa, inda ya zubawa Ma'azzaran kyawawan idanunsa, wani irin matsanancin tausayin su ne ya rufesa,  aƙalla ya ɗauki sama da mintuna 6 yana kallon kyakkyawar fuskarta, ahankali yaƙara so har inda take, zama yayi akusa da ita,  batare data saniba dan sosai tayi nisa cikin duniyar tunani.

Ahankali cikin silent voice ɗinsa yaƙira sunanta.
"Ma'azzara!."
Jin sautin muryarsa acikin kunnuwanta, ya sanya ta buɗe idanunta ahankali, tarwal ta sauƙe ganinta akansa, azabure ta tashi tsaye tana me mamakin ganinsa, tuni kuma tsawan daya yi mata kwanaki 8 da suka wuce ya sanya ta ƙarasa miƙewa da sauri, taku ɗaya zuwa biyu tayi ya riƙo lallausan hannunta tare da jawota jikinsa, tuni tataho luuu tafaɗa cikin faffaɗan ƙirjinsa, hannuwansa ya sanya duka biyu ya rungumeta ajikinsa, ae kuwa take tasaki kukan shagwaɓa, idanunsa ya lumshe tare da ɗaura kansa adaidai gefen wuyanta, bakinsa yakai saitin kunnenta ahankali yace.
"Am so sorry Ma'azzara! am really sorry, kwanaki nayi miki faɗa sosai ko, kiyi haƙuri kinji, bazan ƙara ba!!." Cikin matsanancin sanyi ya ƙare maganar.
Jin abun daya faɗa yasa Ma'azzara tasake shigewa cikin jikinsa, still kuka take mai tsuma zuciya, sake tausasa murya yayi inda yace.
"Kiyi haƙuri Ma'azzara, nasan kinajin ciwo sosai, amma girman ciwonki ko kwatankwacin nawa bai kai ba, bansan tayayane zan fahimatar da keba, bansan mezance ba amma kiyi haƙuri, haka tamu ƙaddaran take, natabbatar Faruk zai zamo garkuwa agareki, haka kuma zai baki farin ciki, shi yaka mata kiso, zuciyata tana barazanar tarwatsewa bisa wani dalili na daban, mu ɗau ƙaddaranmu aduk yanda tazo mana shine abu mafi kyau, ki daina kukan nan kinji!!." ya faɗi maganar yana me ɗan bubbuga bayanta.
Ahankali sautin kukan nata ke raguwa, cikin matsanancin bugun zuciyarta daya tsananta tace.
"Uncle yazanyi? nafaɗa ma kaine acikin mafarkina, haka kuma kaine azahirina, Ina Ina Ina......" Muryarta ne ya sarƙe sakamakon kukan daya zo mata.
lumshe idanunsa yayi tare da ɗago fuskarta ya haɗe goshinsu waje ɗaya, har takai ga numfashinsu na gauraya dana juna.
Rab rab rab haka sukaji tafi natashi acikin falon, da sauri ya sauƙe Ma'azzara dake jikinsa, a matuƙar razane su dukansu suka juya, idanu Ma'azzara tazaro cike da matsanancin tsoro, don kuwa Hassana ce ke tafin, yayinda Hussaina kuwa ke tsaye jikin ƙofa, lokaci guda ta fashe da wani irin razanannen kuka mai ɗauke da tsananin tashin hankali, tace"Na rantse da girman Allah se ka zaɓa ayau ko ni ko Wannan tsintacciyar magen a yanzu ɗinan, ashe Namiji ba ɗan goyo bane ba?" Ma'azzara cikin wani mugun tashin gankali da bazai musaltuba tace"Aunty Wlh ba..." Bata ƙarasa ba! Hussy ta ƙaraso wanketa da gigitattun maruka guda uku wandan suka ɗaukema Ma'azzara jinta da kuma ganinta. Cikin ƙaraji tace"Adamu dakai!! Nake zaɓi ɗaya ni da ita a yanzu nan...?" ta faɗa jikinta na ɓari, dede lokacin Ummu ta fashe da kuka tana harba ƙafafunta. Ma'azzara da ko ganin kirki batayi ta miƙe tana tangadi ta nufin gun Ummu zata ɗauketa, Hussy ta fizgota ta hankaɗata ta faɗi ƙasa, saman carpet ta saki wani irin kuka tana cewa"Kai cona ni Ma'azzara banyiwa kaina adalciba na butulcema Aunty ga inda rayuwa ta kaini yau inaji ina gani dole zan rabu da ita ga ummu, ya Allah ka ɗauki raina a yanzu." ta faɗa tana wani irin kuka.

Wani irin faɗuwar gaba ne ya ziyarci Adamcy cikin matsanancin mamaki yake kallonsu, sosai zuciyarsa ke tsalle tana bugawa Ko a famarki bai taɓa zaton irin wannan kaddara zata hau kan saba.

```(Tofa readers, mekuke ganin zaifaru a next page? wanda se Lallai kun biya zaku sani, don yanzu aka fara wasan, shin wai ko kunsan ma cewa Hussaina nada matsanancin zafin kishi? hmmmm kubiya naira 200 kacal kusha karatu, don kuwa wanda bai karanta ba ansha dashi, yanzun aka soma wasan, sannan yanzu wasan ya ɗauko zafi, kada kubari wannan badaƙalar ta wuce ku, don kuwa akwai rigima, zazzafan ƙauna, haɗi da zallan makirci, kudai kubiyoni, ni Ladingo ƴar mutan Niger Uwa ga Fareesatu, don ni kaɗaice zai iya warware muku komai, babban abun tambayan ma shine wazai auri Ma'azzara Adamcy ne ko Fariuq? hahhhhh akwai chakwakiya fa, da wata irin mahaukaciyar soyayya wacce, abin ba'a cewa kome, amma dai sai kun biya zakusha karatu Real Masoya ina jiranku se kunzo gobe zamu fara kafta wasan fa🤣⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️.)```

*Real Ladingo ce*
  *Sweet Baby💋*








Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels

Please Login or Register in order to submit comment