Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in fada maki........Idan har kinaso ki cigaba da cin abinci a cikin gidan nan topah dole kiyi girki,matata ta iya girki musamman take dakamun yajin citta yajin gauta yajin daddawa duk wa'innan traditional abubuwan dole ki koya yin mun su... otherwise duk businesses din mu da companoninmu Are nollified!!!!! Dake da uwarki zakuyi Bara a kwalta" yana fadin haka ya mike a hankali ya dauki glass cup din tataccen ƴaƴan itacensa ya kurba

Harraqo masa tayi da fitina da sauri ya dakatar da ita ta hanyar cewa "kamar na manta ban fadi wani abu ba...oh yawwa Dabi'unki na banza dole zan sauya maki su i will draw You into my feet" yana fadin hakan ya juya a hankali yana tafiya cike da gadara yana doro yana tokare baya da kafada.

Wani gigitaccen qara ta kwantsama "Adeel Na tsane ka!!!" Hankade mata kafadarsa yayi irin ko a jikinsa din nan ya dage kai ya bar wajen.









Oum Aphnan
09065990265
[6/27, 1:09 PM] Chuchu👻: Zaune Yusrah take a falo ta rafka tagumi tana kallon joy prime da suke nuna latest waqoqin turanci wanda sukayi trending ,amma rabin hankalinta ne ke wajen sauran kuwa tana tunanin yanda rayuwa yake mata atishawan Quda ne.gabdaa ta koma rayuwar abaya en abayoyinta kadai take sawa don bazata iya sa kayan matacciya ba ,gabadaya ta sukurkuce gayunta ya ragu.
Cikin gadara ya shigo falon ya kakare a gabanta ta yanda bazata iya kallon tv din ba kuma .siririn tsaki taja ciki²
"Ina fatan kasan dai kai You Are not a transparent da zaka tsaya mun a gaba kuma in iya kallon abinda nike kallo"
Bai kula ta ba yasa hannu ya dauki remote din tvn ya sauya zuwa tashan qwallon qafa,ya maida remote din ya aje a inda ya dauka .
A fusace ta dauka remote din ta sake sauya channel din .
"Ke idan kallon shashashn tashan nan kike son kallo tashi kije upstairs akwai Tv sai ki kalla a can"
"Anan nike son kalla ,kai kaje saman mana"
"Ki tashi ki bar wajen nan this is my living room muna da set din Tv guda goma sha biyu ne a gidan nan don haka kije ki kallonki a ko'ina Amma ki fita a nan...ina fatan kinsan gidan nan da abinda suke ciki mallaki na ne "
Wani irin dariyar qasa qasa tayi masa kawai ta harde qafa daya kan daya .
"Excuse you🤨😎😏Wai magana kake yi? Wannan wani yare kenan ? Naji Sam bai mun kama da yaren mutane ba"

"Humm magana ake ta arziki i mean dukiya ba na matalauta ba irinku"

Sosai maganarsa ya soya mata rai take anan idanuwarta suka sauya sukayi jaaa.
Gyara zama tayi ta dago tana kallonsa

"Kasan menene? Nagartaccen namiji ,I mean isasshen mijin aure ba ya taba cin zarafin matarsa bare har ya ringa zaginta yana mata gorin arziki ,amma fa ga wanda ya gaji arzikin ba wanda yayi hayen sa ba...amma kai dai kam hmmm☹️"

Dariya ya soma qyaqyata mata har yana duqewa wannan yasa ta dago gamida tattare giran sama da qasa tana binsa da kallon mamaki.

Cikin dariya yake bata amsa "wai dama ke kallon mace kike ma kanki? Oh above all matata? Hummm ai wannan matsayin na matata ce kuma kin kashe ta" zumbur ta mike tana gyara zaman rigarta.

"Kasan menene bazan tsaya ina musayar miyau da kai ba ,you're just a rediculous coward wanda ya dauki cin zarafin mace ado 🙌gorin Arziki abin tinkaho...saidai bari kaji ,ba'a haifeni don a taka Ni ba kuma wallahi ina maka kyakkyawar albishir da cewa har abada nafi qarfin kayi over shadowing dina" ta qare magana tana banbanka masa harara.

"Dallah yimun shiru da kucakin turancin ki sam ke bagidajiya ce turancin ma baki iya ba "

Dariya ta fashe dashi tana tafa masa hannu "Nagode Allah kaji ko ,a hakan kake gane Yaren bagidajiyar kuma daqiqiyar har kana musu da ita ,kai ina wayewan naka yake wallahi kai matsolo ne na raina maka aji....."


Knock knock knock
Aka fara dukan kofar dakin daga waje.

Da sauri yaje ya bude kofar wata hamshaqiyar macece ta shigo mai manyan mazaunni fara sol tana janye da trolley na matafiya .

Yusrah kallon er cakulin jikinta tayi kana ta juya ta kalli almighty body din wannan bakuwar ,kawai sai ta harde hannu a qirji tana kallon ta.

"Assalamu alaikum ina kwana ranka ya dade"

"Barka da zuwa" cike da fara'a ta masa godiya kana ta daga hannu tace "Hiii Yusrah🤩 "

Tattare giran sama da qasa tayi kana ta amsa da "waye ke"

"Oh😃sunana Zuby(ina fatan dai kun tuna zuby kwartuwan Major a guess inn) Sabuwar malaman ki Yes your new teacher!"

Wani miyau ne taji ya sarke mata maqoshi qiris ya rage ta qware .

"Oh ban gane ba kikace kece wane dina?😂😡?"

Yar ma yusra tayi da trolley din kayanta a tsakiyar falon "Kinaji maza biyoni da akwatina saman bene bari in dan kintsa ,shower up sai muyi magana " ta wuce cakas cakas tana juya mata mazaunai,shikuma yabi bayanta kamar wani shashasha suka wuce suna kwasan dariya

"Oh kin dawo daga Dubai din kenan ,ban tsammanin zaki dawo da wirwuri hakan ba ,muje ki fada mun how was your trip"












Oum Aphnan
09065990265
[6/28, 3:27 PM] Chuchu👻: Washegari yusra ta ɗan sha gayunta tana kwance akan resting chair din falonta na sama ,kunnenta maqale da bluetooth tana miming waqan nicki minaj a hankali .a saman kanta ta jiyo zuby na kwarara mata kira
"Yusrah! Ke Yusrah"

A nutse ta zare earpod din kunnenta guda daya tana kallonta
Ba tare da tace mata kanzil ba .

Zuby watsa takardun hannun ta da biro tayi akan table din gabansu ta samu kujeran kusa da ita ta zauna tana gyara zaman matsatsen rigar jikinta da ya fallasa asiri manyan boobs dinta ta v-neck din rigarta.

"Excuse me yanzu lokacin karatunki yayi "

Galala tayi mata da baki kamar goluwa tana mamakin abinda wannan zata koya mata a haka dinta wanda ko bata qwanqwasata ba zata iya assesing ilimin dake cikin kwanyarta.

A sama taji tana mata introduction "wannan aikin koyar da gyaran hali ne,zan koya maki yanda ake magana ,yanda ake tafiyan ɗaa ,yanda ake gaisuwa da maida ma na gaba dake magana ,ke harma da yanda ake gyaran gida da girki.....yanzu dai da farko zan fara da tambayar ki.....Menene kika fahimta da kalmar *LADABI*?"


Cikin gatsali da rashin daukan abu da muhimmanci Yusrah ta fara mata magana
"Kin tabbatar kin ko cancanci wannan position din? Nifa kallon jahila na gasken gaske nike maki? Kin kalli suturan jikinki kuwa? Irin na kilakin nan en good evening masu neman maza su dauke su su cisu over night a siya masu indomie da qwai ko gasasshen kifi in sunci mugun sa'a a basu gasashen kaza da rufaida yoghourt safe in yayi a basu dubu biyu su gaida gida.....fada mun anya ke din ba irinsu ba ne"

Gabadaya zuby ji tayi an gama muzantata.
"Ban fahimce ki ba ! Ki natsu kina jina ko? Bazan dauki duk wani nau'in rashin da'a daga wajenki ba...ki saka nutsuwarki duka anan wannan shine job dina "

Caɓe mata baki tayi gamida dage mata giran sama😏🤨
"Ok fadamun bisa qiyasi bisa dari ,matakin nawa zaki ba kanki na wannan fitsaran taki...?"

Ba tare da yusra taji komai ba ta ɗan dafe kai kamar mai tunani "uhmmm Daidai dana Uwarki!!!😳 Hahahaha😂"

Dafe qirji zuby tayi ta maza ta gyara zamanta tana duddulo mata ido cike da ɓacin rai ita kuwa yusra sai dariya take tana wasa da ƴan yatsun hannunta tamkar batayi komai ba

"Kina da hankali kuwa? Ni kike zagi?😡"

"Laaa wai kinji haushi ne? Tambayan raayina fa kikayi kuma na baki amsa...oh make nah calm downn o"

"Excuse me?"

Kwatseta Yusrah tayi cikin bala'i nan da nan ta saka ma fuskarta salon tijara "Dallah yi mun shiru shashasha ,sakarya er kwalta ,what is even your Educational qualification again? Are You Nonsense? Ni zaki koya ma karatu ? Waye ubanki a Nigeria For goodness sake? Ni girman Turai rainon cokali me yatsu ,You Are very mad!!!"

Zuby ganin yanda yarinya ficiciya ke mata madarar tijara yasa ta kame mutuncin kanta ta komar da kanta qasa tayi sanyi da muryarta "to tunda kin bukaci sani nayi degree na a qasan turkey inda na karanci ilimin kasuwanci a halin yanzu ina mastering degree na a qasar swithzerland..."

Dariya yusra ta fashe dashi ta mike tsaye tana tafe hannu "oh really? Ke yanzu kina nufin kinzo ne ki koyar da senior ɗinki karatu? Abunda kike nema Ni tuni na same shi a University din da kike magana and again i've 2 degrees in different caurses business da psychology kafin in daura masters dina ....kuma duk nayi karatun ne ba don komai ba sai jahilai ƴaƴan ƴan tasha irinku masu dagawan sunje Turai karatu ,ƴaƴan mitsiyata masu ɓata sunan yaran hausawa irinmu da iyayen mu ke daukan dawainiyar mu kuje ku bude ma turawa qafa suyi ta tumurmusheku ku dawo Nigeria kuna feleqe .move jhorrrr..."

Qamewa zuby tayi a kujera ta kasa mata magana ta fara tafiya cakas cakas har zata wuce ta dawo ta tsaya mata qerere a kai

"Kar in barki cikin duhu...have You heard about best student of this year from your department ? Wanda ta tafi tabar turawa da mamaki? Pepper Yusrah inkiya filosofi? To nice nan ,kije kiyi searching dina a goggle zaki samu cikakken qarin bayani,soooo in karatun kike so a shirye nake ki sa littafi in koyar dake indai za kiyi mun biyayya"








Oum Aphnan
09065990265
[6/28, 3:50 PM] Chuchu👻: Washegari

A fusace Yusrah ta fito daga kitchen tana kwarara ma Zuby kira ,zuby na zaune daga ita sai guntun skirt rabin cinya da wata damammen riga da ya fallasa asirin qirjinta.
Sai latsa waya take tana chatting da Major wanda ya jima da cika cikinsa da abincin zuby .

"Ke zubaida kike ko wa? Kece kika dauke mun fresh fruits Salad din da na aje a fridge?" Banza tayi da ita ,wanann ko ya sake tunzura yusra

"Am i not talking to a human being,kardai ace me halin ɓera aka kawo mana gida "

"Dramarki ya kusa zuwa qarshe mu zuba Ni dake Yusrah da qarfin tuwo sai na saki kinyi la'asar ,taushi zakiyi lumus kamar sakwara dakan inji"

"You're stupid,wai Ni kam ma zaman me kike mun a cikin gida ne ,abinda na kasa fahimta kenan?Dole ki bar mun gida na ,bazan iya zama da karuwa mai halin ɓera ba ,bari mijina ya dawo"

Fashewa da dariya zuby tayi "dan maimaita wa kikace ?"

"Nace Bari mijina ya dawo ya koran mun ke aidai nan gida na ne ko dole ki fice daga rayuwa ta da mijina"

"😂😂😂anya kuwa matar ne? To in kin kasa gane me ye dalilin zamana a gidan ki ,ina zaune ne ina cike gaf din da kika bari na gurbin mata da miji ,sannan ina so ki sani nan Afrika ne ba qasar waje ba ,munada lasisin cin duriiiihhhh ahhhh"
Ta qare magana tana lashe leɓenta na qasa kamar kwartuwa

"Ya Allah ,zuby Ni kike ma haka? Ni kike ma gadara and You think kina da capacity? Idan bacin bana son Major ke me kike dashi da zakiyi tunanin iya sarrafa mun miji a gado and beside kina iqirarin kedin kwartuwansa ce ? Ya Salam,kodayake nasan makircin diya mace so bazan biye maki ba wlh mijina kintsatse ne ya dauko ki dai don ki koya mun darasin da na girme maki ,so watch me in action"

"Allah srki kinajin har a jikinki kina da wani abu da zaki burge nagartaccen mutum kamar Adeel ? Shahararren mai kudi mai baiwa gomnati bashi ,Nigeria na Alfahari dashi ,jibeki fa me kike dashi"

"Ke ke na gaji ,na gaji da sauraron rubbish ɗinki ,kinsan menene minti biyar tak na baki ki tattara komatsanki ki bar mun cikin gidana"

"Dallah yi mun shiru"

"Zubaida ki tattara kayanki ki fita ko kuma zan nuna maki asalin kalan hauka na"

"Oh shut up she-goat 😏"

Nunata da yatsa tayi
"Ok kar kice ban gargadeki ba,plz kar kice ban maki warning ba" tana fadin hakan ta juya fuuu ta fice a dakin.

Girgiza kai tayi gamida jan tsaki "hmmm Yusrah kenan yaro man kaza😊"







Oum Aphnan
09965990265
[6/28, 4:50 PM] Chuchu👻: After Isha
Major Adeel yana zaune a falonsa na qasa yana shan chocolate coffee din da zuby ta hado masa ,kadan kadan yake sipping yana kallon news

Zuby saman kansa ta tsaya ta fara marmatsa masa kafada a hankula ,cike da gwanancewa na karuwai da suka goge wajen tunkado sha'awar da namiji ,ya dauki cup din coffee din yakai baki yaji tana masa tafiyar tsutsa a bayan wuyarsa ,dayan hannunta tana masa wasa da gashin kansa .
Wani yarrrr dummmm yaji kunnensa ya dauka ya dode na wuccin gadi da sauri ya hadiye wanda ya guntsara ya dire cup din akan table din gabansa Saida ya gyara muryarsa kana ya kira sunanta " Zuby"

Maimakon ta amsa sai kama lilin kunnuwarsa tayi tana shafawa ,muryarta can qasan maqoshi tace "humm"

Da qyar yake qoqarin saita kansa saboda yanda take masa susan kunne da er qaramar yatsan hannunta
"Amma kinsan dai Ni me aure ne ko,kuma a gidan aure na nike kuma Matana ta na nan ko?kina nan ne saboda manufa ta"

"Amma ai dai kasan qwalama da muradin zuciya plz karka haramta mun abinda nike qawa kaima fa na gani sarai a qwarar idonka abun nan kake so...and beside me yusran take dashi wanda banda gomansa kalleni fa"

"Kawai dai kina nan ne saboda manufa ta so concentrate on that"

"But why😢me yasa?"

"Ki yi kawai abunda na baki umurni banason musu"

"Haba now ya zakayi mun haka Major bayan kasa na dandani romon ka ,ka bari muyi ko sau daya ne ,kana sane waccan yarinyar mai kama da kifin Hausa bata da komai da zata iya gansar dakai Ni naji bance dole sai ka aure Ni ba amma let us be friend"

"Bazai yiwu ba na dauke ki ne ina biyanki don ki sauya mata rayuwa kiyi abunda nace and go ... plz "

Bude baki tayi zata sake magana ,hannunta nakan haɓarsa tana dan shafa masa gemu ,saidai suka ga yusra a kansu .ko kallon sashen zuby batayi ba tai masa qerere akai cikin wata ɓingilar riga ga kan nonuwarta sun caccarko ta cikin rigar ,kallo daya ya mata yayi saurin sunkuyar da qawarar idonsa amma cikin idonsa sai gizo shape din nonuwanta suke masa so yace ya sake dagowa ya kalla amma where is his steeze?

"Adeel Ahmed?"!
Ta kira sunanshi a gaba daya ,wani dararas yaji qirjinsa ya buga ,when last aka kirashi da wannan sunan?

"Adeel ina magana?"

"Ehen?"

"Inaso ka koran mun watan nan abar yanzu yanzun nan"

Kafin ya mata wani magana zuby ta kwatseta "Dallah tattare mana plates din nan da ya ɓata da cups din nan zuwa kitchen bansan yaushe zaki natsu ki dawo hayyacinki ba"

"Ke qaramar karuwa jira sai na dawo ta kanki yanzu da mijina nike yi tukun jahila kilaki!"

Tassss! Taji ta yanke ta da gigitaccen mari ,da sauri Yusrah ta dafe kunci ta fasa ihu ,Adeel kam da sauri ya rimtse ido ya toshe kunne yana dan murmushi .

"Sai yaushe zaki koya dabian iya magana? Ehyeh?"

Dago jajayen idonta tayi suka kalli juna "kika mareni?"

Banza tayi mata tana girgiza hannunta rike da qugu

"Adeel ,zama za kayi kana kallon wannan karuwar tana humuliating dina a gabanka?" Maimakon ya bata amsa sai ya sake daukan cup din coffee ya kurba a hankali fuskarsa fal murmushi da annuri

"Ƴan mata ,ina da urgent meeting a office a daren nan so bye" ya tashi tsam ya fara tafiya yana zuwa gaban yusra ya tsaya gamida yin qasa da murya "Nasan ke jarumace bari in bar maku gidan ku dambatu kinji ! Ki mata dukan mamaki" yana fadin hakan yayi saɗaf saɗaf ya fice yana guntse dariya kamar tsohon munafuki😂

Hangame baki Yusrah tayi hannunta still dafe da kuncinta.
Tana kallo har ya fice,dangas dangas zuby tazo ta gabanta tasa qirjinta ta wani kai mata bangaji ,tayi taga taga zata kifa.

"Zo kiyi dambe dani qaramar mara kunya"

Ta wuce fuuu tana taku da qarfin izzah ta bar ta yashe cikin rashin madafa a falon





Oum Aphnan
09065990265
[6/29, 7:28 AM] Chuchu👻: Washegari
Yusrah kwance take tana barci akan gadon ta sai juyi take tana jin dadin barcin ta tun bayan sallah asuba ,bata da niyyar tashi ma .
Zuby ne ta shiga dakin a hankali hannunta rike da cup din ruwa ,tana zuwa tsakiyar kanta ta fara tsiyaya mata ruwan sanyin nan a fuska.a gigice yusra ta bude ido cikin haki da tashin hankali take tambayar waye ... Waye...

"Dallah tashi ki bamu waje malalaciya ,kina matar aure har qarfe takwas da rabi baki tashi barci ba"

"Shine zaki tsiyaya mun ruwan qanqara a fuska ? Kinyi hauka ne? "

"Zaki tashi ki taho muje kichen ko sai nayi qasa qasa dake ?" Kafeta da ido tayi tana mamakin ta amma ita ko dage ido ta kalleta ma batayi ba.

Na baki minti biyar ki fito kar ki bari in dawo in tardake a gadon nan malalaciya,ta sheko mata sauran ruwan cup din hannunta wani gigif Yusrah tayi gamida jan ajiyar rai itakuwa zuby ,ta wuce fakam fakam ta fice ta banko mata kofa gararam!

Sukuti Yusrah tayi wasu irin silent hawaye suka fara silalo mata a fuska
Girrrrr ! Wayarta ya soma vibrating ,a sanyaye ta mika hannu don ganin mai kiranta da wannnan duku dukun safen. A sarari ta furta momy sai dai ko ki bazaka iya yi ba saboda yanda Muryar tata ya dushe.

"Hello auta ta yakk"

Shiru auta ta kasa magana sai hawaye wani na tunkude wani "auta Are You alryt?"

Da qyar ta hadiye kukan ta muryarta nadan rawa tace "Yes i am fine momy"

"Kinajin dadin zaman kuwa"

"Yes" ta bata amsa a takaice saboda kar ta fahimci halin da take ciki

"Tom ya Adeel din hope dai yana kula dake sosai"

"Sosai da sosai mom ,yana da kirki kuma yana sona "

"Uhm that's gud yanzu ina ne zakuje honey moon"

Dararas ! Gabanta ya fadi "momy muna dai ta tunani bamu riga mun yanke shawara ba"

"Kai har yanzu? You guys arent try at all!...ina Adeel din nasan yana kusa dake sa maganata a speaker"

Duddulo ido waje tayi
"No momy yana qasa yana haɗa mun abin karyawa ,yana da sona sosai"

"Break fast kuma? Ina masu aikinku kuma?"

"Momy yace sabon aure baya son mutane suna damunsa maybe sai mun dawo honey moon din sannan"

"Oh ohk i missed u my angel"

"Nima nayi kewarku sosai momma na " ta qare maganar tana sharce ruwan hawaye

"We cant wait to see You back to the office"

"Yes mom...I love U" ta fadi a hankali tayi ending call din ta tsaya tayi shiru hannunta rike da wayar "Nine wannan banzar zata watsa ma ruwa?

***
Adeel kam yau tunda ya tashi yake neman wasu documents amma ya rasa inda ya watsa in zai iya tunawa tun late wife dinsa nada rai ,kuma in baiyi kuskure ba ita yaba ta ajiye masa lokacin .
Wannan yasa ya tafi dakin mamaciyar ya fara fiddo takardunta yana bincika wa ,cike da farinciki yaga doc din da sauri ya fiddo shi a jikin jacket file din ,wani farar takarda ne yaga ya fado ,haka siddan yaji gabansa ya fadi especially ganin rubutun tsohuwar matarsa ,da sauri ya duqa ya dauka ya fara karantawa


"Dear my loving husband,Mijina abun alfaharina ina sonka a koda yaushe ,Ina matukar godiya da inganta mun rayuwata da kayi ,Nagode ma Allah da samun nagartaccen miji kamar kai ,thank You For making me mother to be,Allah ya qara haɓɓaka hanyoyin arzikinka ya barrantaka da haram ,ya baka zuriya dayyiba saliha idan akwai rabon aure a tare da kai a gaba Allah ya baka mata saliha wacce ma ta fini komai ,Allah ya jikan iyayenmu Allah ya barmu tare har Aljannah.....Nagode mijina Happy our weeding anniversary 😍"

Tun da ya fara karanta wasikar idonsa ya fara tsiyaya da hawaye ya kasa dauke damuwarsa ,tunda ta rasu bai taba mata kuka ba sai yau ,kamar tasan zata rasu take roka mun mace ta gari sai dai kuma kash na samu fankashaliya oh god 😭😭😭 Yusrah kin cuce mu kin cuci Innocent soul baiwar Allah mai riko da addini wacce bata dauki duniya ko arziki a bakin komai ba....








Oum Aphnan
09065990265
[6/29, 12:40 PM] Chuchu👻: Da yanganta da kauɗinta ta shigo dakin kamar an wirgota ,cak ta ja ta tsaya tana kallonsa cikin mamakin ganinsa yana hawaye
Cikin rashin kula ,amma dai da dan nuna yanayin zaman tare tace "meke faruwa kuma?"

Ɗagowa yayi ya kalleta da jajayen idonsa da sukayi kace kace da hawaye .
"Kece zan ma wannan tambayar Yusrah kece..."
Sakatoto tayi masa da fuska tana kallonsa ,cikin raunin murya and tremble irin na mai kuka ya sake maimaita "Yusrah duk kece "

"Na shiga uku daga tambaya sai cibi ya zama qari Alhaji sha kukan ka ka qoshi ka ga nayi nan"

"Dama iyakan abunda zakice kenan tunda kin Koreta kuma kin maye gurbin ta,dama abinda zakice kenan tunda kin kashe ta ....Yusrah me wannan baiwar Allah tayi maki ,mace macen kirki mace ta gari ,naga dai Ni nayi maki laifi tun farkon fari na zubar Maki da magani ,me yasa Ni baza kiyi mun ba sai ki huce akan Innocent wife dina???

Ɗaga murya yayi cikin kuka "shikenan kin kashe ta kinji dadi yusra kin kashe ta!!!"

Ji tayi kamar saukan aradu da sauri ta dafe kai ta burkice ta fice a hayyacinta tunda take dashi bata taɓa ganin ya mata tsawa irin hakan ba ,bude baki tayi zatayi magana da sauri ya nunata da takardan hannunsa

"Idan kikace tak wallahi sai kinga mummunar matankin da zan dauka a kanki" yana fadin hakan yayi cilli da takardan ya fice a gigice.shiru tayi tana kallon takardan dake yashe a qasa kafin a kasalance ta duka ta dauka ta soma karantawa a hankali cikin zuciyarta.

A take taji zuciyarta ta karye tsautsayi da qaddarar zuciya ya Kaita ya barota da duk bata kirata a waya ba da ynz duk hakan bata faru ba da yanzu yana tare da matarshi ta gari da cikin en biyunsu.

Yanda ya fita cikin damuwa itama haka ta yini cikin damuwa ,Adeel bai dawo gidan ba sai sha biyu saura kwata na dare .

Zuby na daukin ta zuru tasha ado tasha makeup duk batasan halin da mutan gidan suke ciki ba ,ita dai ta qudure a zuciyarta yau sai ta kusanci adeel ko yanaso ko baya so sai ya biya mata bukatarta. Don haka tana jin shigowar motarsu ta maza taje ta hado masa hadadden shayi yasha na'a na'a da sauran kayan shayin larabawa ,coz ta lura shi yafiso ta dauko maganin da suka taɓa bashi ita da surayya a wancan karon ta zuba a shayin ta jujjuya .

Da wannan seducive dress dinta kamar wacce zataje night clubbing ta nufa dakinsa ,tana zuwa ta iskesa a falo yayi tagumi yana ta raba ido gefensa wayarsa ne ke fitar da sautin karatun qurani a hankula.

"Oyoyo gwarzon namiji" kallo daya ya mata yaji ya tsaneta ,waima me ya shigo masa da wannan dattin cikin rayuwarsa?

"Nasan ka debo gajiya and definitily You will need this. your favorite"
Amsa yayi gamida yamutse fuska ba tare da ya tanka mata ba ya fara kwankwada.
Taune leɓe tayi gamida murmushi qasa qasa kai tijaranka in kaji magani za kayi mun bayani.ta fadi a zuciyarta amma a sarari sai cewa tayi

"Bari inje in kawo maka abinci ko?" Tana fita yawatse akan kujeran cikin drowzy response.

Yusrah a sanyaye ta fito falon saidai yanda taga ya watse kan kujera ko takalmi bai cireba ya bata mamaki

"Sannu da zuwa"

"Karkizo kusa dani ,me kyawon dan maciji ku dubeta ita ta kashe mun matata ahhhhhh...ke wata irin makira ne with just a phone call You killed her"

"Adeel plz calm downn ok? Me yasa kayi shaye shaye uhm 😢laifi na ne wallahi ni naja amma it was a mistake da hayakin kaina...plz tsaya in cire maka takalmin nan dont mess up "

"Karki taba ni kina taba Ni sai na shaqeki,kashhh waima me yasa bana dukan mata? Wallahi da sai na kashe ki kowa ya huta jibeki ,muguwa kawai in kasheki a rage mugun iri ba dai kina taqama ke mai kudi mamanki billionier ba sai na talautaku ,kodon talakawa su huta da bakin zuciya Irin taki Allah kadai yasan rayukar da suka gurɓata sanadiyyar..."

Dafe kai Yusrah tayi "ya Allah bari in kawo maka ruwa oh na hada chapman ma bari in kawo maka ko yaya clearing abinda kasha "

"Bana so karki dawo nan"

Bata saurare shi ba ta fice dakin da sauri don kawo masa abinda tace.

Cikin minti biyu sai gata ta dawo da chapman mai sanyi tayi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment