Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auri junanku da wirwuri haka Adeel matanka ko arba'in bata yi ba..."
Kafin ya bata amsa Yusrah tai karaf tace "Personal purpose ne mama ,wani dalilin mune kawai mama"

Yarinyar fa kanta na hayaqi,matsalar yaran Abuja din nan kenan ɗiyoyin masu kuɗi akwai gadara ! Amma Instead taji yarinyar batayi mata ba sai ji tayi kamar tana qara burgeta.

"Amma ɗiyata ...."

Kafin maman tayi magana tayi gaggawar dafe kai
"Kash mama wlh wlh Ni mutum ne marasan yawan tambaya ,duk na zama exhusted ki yi hakuri in na shigo family din naku kya yimun duk tambayoyin da kuke so ...(ta juya ta kalli Adeel) bakace mun gidan ku in ana so a aure ku Ku maza ana dinga titsiye mutum da tambayoyi ba kamar gidan mahukunta ko Alkalai ....anyways plz ina mota in ka gama kazo ka maidani gida"

Ta mike batajira cewan kowa ba tayi wucewarta.









Oum Aphnan
[6/15, 7:15 PM] Chuchu👻: A month later
Duk yanda momy Juwairiyya taso ta hana auren amma Yusrah she insisted,don haka ta sanar ma dangin mahaifin Yusrah ,maganar auren ƴarsu ,sunji dadi sosai saboda a zamanin nan da ya lalace in yaro ya samu inda zai zauna yayi zaman aure to ba abunda ya fishi dadi ,bare kuma ita marainiya da mahaifinta ya rasu suna can suna nan basu san ya yanayin tarbiyyar ta yake ba a wajen mace ,duk da dai sun san Hajiya Juwairiyya mace ce mai addini kuma tsayayya amma kuma duk da haka suna sane sarai Yusrah taɓararriyar yarinyace Shiyasa sunsha mamaki ma da ta yarda ayi mata aure da wuri........Ni kuwa nace rashin sani.

Tuni dangin Adeel suka hallara a babbar gidan su Yusrah kuma a yanda sukaje tambayar neman izini da saka rana ,bayan sun gabatar da komai Adeel ya roki a daura masu aure nan take tunda dai amaryar ta yarda da haka kuma sun fahimci juna kuma dai akwai dama na iya yin duk wani hidima da ya dace to babu bukatar sai an jata da tsayi tunda duk waliyyan Ango da amarya sun hallara.

Aure da mutuwa isuwar ubangijine Allah ke sa ayi shi a sanda yaso don haka ,babu ɓata lokaci aka daura aure dangi na nesa suka biyo jirgi saidai Hajiya Juwairiyya Sadiq ta ji hayaniyar dangi daganan aka shiga shagalin biki aka saka Yusrah a lalle washekari akayi kamu .
Tun kafin a watse wajen kamu dangin ango suke shelan duk wanda zaije ganin gidan amarya to ga motoci nan don babu wanda zai kwana ,amarya kuma ango da kansa zai zo ya dauki abarsa🫤love nwantiti.

Tunda dangin amarya sukaji haka sukayi ta ɓururuwar zuwa ganin gidan amarya ,gidan sane dai inda matarsa ta rasu a ciki amma an sauya masa fasali dingurgum kudi kenan masu gidan rana .

Sai qarfe tara da rabi na dare Adeel ya taho cikin farar ferrari daukan amarya .Yusrah kam ido qemandagas don ita duk bidirin da ake bata dauke shi aure ba tasan dai auren manufa ne ,to meye nata na tayar da hankali ? Kwana nawa ne zata dawo gidansu ta nema zuqeqen miji ta aura?

En uwa da dangi suka shiryo Yusra cikin gown me mugun tsada suka lullube mata kai suna sakata a mota . Sai a sannan ne Major Adeel ya dinga hotuna da danginta don tunda aka daura auren ba wanda ya sake ganin qeyar ango ,itama kuma dama amaryan ba qawaye ne da ita ba don haka a sauka lafiya hutaroro .

Sai sha daya saura kwata suka fice daga gidan ana ta masu addu'ar zaman aure me cike da zaman lafiya mai daurewa suka rankaya zuwa gidansu .

Ita dai Yusrah ba uhm ba uhm uhm kanta na sunkuye tana chatting da wayarta abunta har suka iso gidan .sai da sojoji suka bude masu gate guda uku kafin suka isa asalin harabar gidan.

Lallai komai ya sauya ji gida? Ni sanda nazo ba haka yake ba wannan gida mai suffar jirgi fa ,ga wasu gangama gangaman gate kamar na masarautun indiya ,ga wasu sojoji sai kace su zasu hana dan adam ya mutu go tulin motoci sunkai ashirin wanda itadai in ba qarya tayi ba wanda ta taba ganin irinsu basu wuce biyar ba ,ga mashin nan irin na tseren gudu sunkai biyar kakkafe a rumfunarsu.
Tacan gefen gidan wajene akayi fensing dinsa aka malale wajen da adon grass carpet da er madaidaiciyar jirginsa helicopter a kafe.

Dafe baki tayi ,wai shin Ni kuwa wani irin kudi mutumin nan yake dashi??
Duk wannan abubuwan a abinda bai fi second goma ba ta qare na komai kallo .Sarai tana jin yanda danginta suka gigice da kudin Major Adeel da yanda suke zuzuta motocin daukan amarya duk sababbine daldal a leda kuma daidai da tint din motar ruwan toka ne wanda sam babu mai irin tint din sai gidan Major . Kuma yanda aka shiga da motocin aka ajiye su haka duk suka fito kowacce aka danqa mata key din motar Ba wasu dai zafafan motoci bane masu tsada Corolla S ce amma fa ya tada hankalin danginta .kowa sai fatan Alheri yake da fatan kar ta bawa mata dansu kunya.








Oum Aphnan
[6/15, 7:15 PM] Chuchu👻: Da kansa ya bude mata kofar shiga tangamemen living room din gidan,Yusrah kam cike da yauqi da daga kai take tafiya har ta shiga dakin da yafi dacewa da a kirashi Aljannah duniya.

"Barka da zuwa gidan Adeel"
Kallonsa tayi irin kallon Nan mai cike da harara.
"A cikin wannan mansion din akwai dakunan barci guda sha biyu,Manyan dakuna guda bakwai,wajen hutawa guda uku garden biyu,awimming pool baban daya kananu biyu ,dinning room uku ,sashen baqi da boys qtrs......"

Tunda yake magana ta qame qam nade da hannu a qirji tana jin duk wasu bayanan shi har saida yakai qarshe kana ta daura da tambaye cike da gatsali da izgilanci

"...and so..?"

"Yes so,akwai wasu dokoki da zan shimfida wanda binsu diqin diqin farilla ne...idan kuma aka qi bi za'a fuskanci tara mai girma"

"May I?"
Ta tambaye shi sannunsu in single words

"Kamar yanda dai kika ga gidan nan bai kama da gidan Tsoho da tsohuwa ba ,to la shakka duk abunda kika ɓata sai kin biya"

"Ban fahimta ba🤨saboda ka kawo Ni wannan kejin da kake kiransa gidane zaka ishemu da gadara? Can U listen to ur self ? This is silly jokes"

"To shikenan zaki fahimci ba'a iya ganin ki....Umurni na farko shine zaki ringa wanke gidan nan ciki da bai duk sati ,i mean har bangon gidan nan sai kin wanke ai dai kina ganin fentin leda leda ne ba laifi bane in an wanke....Na biyu wanke wanke farilla ne safe da yamma da duk sanda akayi mun kalar abincin da na bushi iskan ci......oh biyoni muje in nuna maki wajen wanki" cikin taqama ya fara takawa tas tas

Wani dariya ta bushe dashi gami da jan tsaki.


"Mtsewwww kana shirme ,Ni in bazaka iya nuna min dakina ba Bara in je in nemeshi da kaina " ta wuce fuuuuuu ta barshi anan wajen .








Their first night a haka ya gantale.don tuni tai ma kanta mazauni a dakin qasa kuma ta mirza makulli tayi wanka ta miqe a gado.







Oum Aphnan
[6/15, 7:41 PM] Chuchu👻: Washegari
Ya kama monday ,qarfe takwas Yusrah ta fito ta fesa wanka cikin wasu suit riga da wando baqaqe sai rigar ciki royal pink ,ta saka takalmi da jaka masu musulman tsada ,ta maqale agogon ta na diamond da dan kunnen diamond ta fito fuskarta fayau sai sheqin man baki yake ta tufke tulin gashin kanta ta baya ta ɗan yano siririn mayafinta mai kama da maka wuya saboda ba abinda ya rufe rabin gaban gashinta a bude kazalika iska na ɗan ɗagawa za'a hango tulin gashinta ,wannan mayafi bacin tsawo da baida banbanci da handkerchf.

Cikin cat walking tazo ta wuce shi a falon yana zaune yana kallon CNN taje ta murde qofa ta fice ta isa asalin main door din da zai sadaka da farfajiyar gidan shima ta murda zata bude saidai kuma garam ta jishi a garqame ,ta murza handle din ta mirza amma fa kan kam ba ya ko motsi .

A yatsine ta dawo gabansa ta tsaya ,shikam ya dage kansa kan kujeran ya lumshe ido tamkar baisan da ruwan tsuruwanta ba dukda lafiyayyen qamshin turaren ta da ya masa maraba

"Zan tafi office a bani makullin kofa"

Ba tare da ya dago ko ya bude ido ba yace "....Doka ta ta biyu kuma...,Matata dole ta zama sit at home house wife ,cikakkiyar matan gida nike nufi"

"Ni?😳Ni yusra carrer lady kake dangantawa da matan gida? Ka manta daga family din da ka dauko nine ? Kaga nayi maka kama da matan gida ?"

"Halastaccen aure nayi bisa sadaki don haka a aure babu sharadin fita aiki ,tabbas kamfanonin da duk wasu kadarori yanzu naku ne amma ke?! Ke?! Bake zaki dandani dadinsu ba...ki fara qirga kanki a matsayin house wife not a carier wife"

"Humm Adeel You Are not normal ? Me kake so inyi hannn my friend ban key in fita jhorrrr " ta qare maganar cikin tsawa tsawa da hassala

"Ki wuce sama ko sauya kayan jikinki na tanazan maki riga da zani da dan kwali ki sauya kayan jikinki dasuka fi suffan taki da bayahudiya .ki saka kayan da na tanajar maki irin namu na Hausa Fulani .in kin gama tassss ina jiranki da tuwon dawa miyar farar kuɓewa ɗanya da stew din kayan ciki da ganda. "

Riqe haɓa tayi tana kallonsa🤔mamaki zatayi ko mene ma oho


"Yauwa a matsayina na bafullatani ki tabbatar ki soya mun isasshen man shanu yaji albasa ki taho mun dashi"

"Kai wai ban gane ba ,dani kake yi?"

Sai sannan ya dago yana kallonta ya dan kai hannu ya dauki cup din drink ya kurba
"Uhm uhm ba dake nakeyi ba da inuwar ki nakeyi" yana kaiwa nan ya yunkura a hankali ya mike yana gyara zaman guntun wandon sa na sojoji .hannunsa rike da glass cup din drink dinsa.

Itadai tana tsaye qiqam kamar drawing har yazo dab inda take kana yayi magana a hankali daidai kusa da kunnenta

"Ina jiranki a sama da abinci na and karki manta da soyo mun wadataccen man shanu...."

Mamaki ne yasa ta hangame baki har ya wuce yau ya kasa bashi amsa .

Sai da tayi kamar second biyar kana tace "Ni Yusrah? Hummm wannan mutumin bai Sanni ba"







Oum Aphnan
[6/15, 7:59 PM] Chuchu👻: Bayan awanni uku
Bankado kofar dakin taji anyi wanda ya sata mikewa akan gado a firgice gamida dafe qirji "wash Allah na"

"Meye haka? Ke Ni fa bana jurar jira bazai yiwu ba kuma a matsayina na soja bana wasa da cikina,me kike yi anan ? Ina abinci na?"

"Wai waye zai ma girkin?"

"Ke ! Ke nake nufi ai siyanki nayi da sunanan kudi masu yawa ,don haka dole ki mun bauta a gidana aikinki shine ki kula da Ni ,aikin ki shine ki mun girki ,aikinki a gidan nan shine ki mun wanki,sannan ki bani lafiyayyen sex a duk sanda na buqace ki a gado na"

Wani ragagab taji maganarsa na qarshe kamar saukar aradu .
Duddulo masa duk idandunanta tayi waje.
Saidai kafin tayi magana ya daura da cewa .
"Karki manta zamanki a gidan nan da bin duk wani dokata shi zaiba uwanki daman zama a wancan gidan har ta juya kamfanin can da yi ke so-call yours , rather!!! Zan koraku kan titi a qasqance in qwace duk wasu dukiyata mallaki na! So abi umurnina a zauna lafiya"


"Haka kace? To kuwa ka taro bala'i zakaga yanda ake fitina zakaga masifa ta wanda baka taba ganin irinsa ba ,bazan taba suarara maka ba Adeel"

Kallon sama da qasa ya biya dashi yana kallon tiny body dinta

"Banga jikin fadan ba en mata ,a yanda kike kamar lawashi so i maza kije ki dafo mun abinda na saki,kuma kar ki sakaci in sake zuwa in tuna maki"

Ya bude qofa ya fice ya barta anan wajen.

Dafe kai tayi kawai saiga wani qwallan takaici yana gangaro mata .da gudu ta mike tana goge hawayen fuskarta .Not me? Kuka kuma ? Tun ina nursery kenan sanda ake rabani da momyna in zanje makaranta amma ba da girma na ba....kuma yanda kasa hawayena ya ɗiga kaima sai kayi baka kukan ko a zuci ko a sarari mu zuba!!!







Oum Aphnan
[6/15, 8:16 PM] Chuchu👻: Washegari.

Qarfe 7.10am na safe Major Adeel ya fito cikin shirin sa na manyan sojoji ,waya kawai yake daga office ba qaqqautawa ga dukkan alamu yana cikin ujula kuma ana tsananin bukatar sa a daidai wannan lokacin
Tun daga bakin qofa yake qwalla ma driver dinsa kira
"Idris a fito da mota na makara"

Cikin ladabi ya gaishesa kana ya daura da cewa
"Tayan motar tayi faci oga"

"To a fitar mun da lamburgini"
"Itama tayi faci "

Shaye da mamaki ya dago yana kallonsa "to pah! To fiddo ko wannan ne kai ko wancan highlander din ne fiddo mun ita mu tafi "

"Sir rankatakaf tayoyin motocin gidan nan a sacce suke"

"To garin yaya haka"

"Wallahi muma shine bamu sai ba sir"

A nutse ta fito sanye da strght gown wanda aya fallasa shape din cocacola dinta cikin yauki da tafiyar taqama ta ja ta tsaya dab da su .

Shikuwa Adeel cike da bala'i ya hayayyake ma idris
"Kaje ka nemo mun ko mota mai datti ne a gidan nan nidai ka kaini office i need to go to the office now!!!!"

Dariyarta suka jiyo gamida tafa hannu,wani rausayar dakai tayi gamida yin masa fari kamar wanda suke zaune lafiya
"Awwwn sweet😍 meye ya firgita ka haka ne nene?takan motoci sunyi faci? Kayi hayan taxi mana ko keke nappep kaga ai kaima sai ka dandani ya talauci yake ko "

Wow kawai sai gaka a keke nappep ,tab! Topic of the day ai ka bawa en jarida dama"

Duddulo mata ido yayi cikin tashin hankali kamar ya yanke ta da mari

"Ke?!!! Ke kika sattar muna da tayoyin?"

Gintse fuska tayi kamar bata taɓa dariya ba ,a take ta kaurara murya kamar yanda yayi mata a baya
"Aah bani bamayi inuwa ce ta huda su....in bazaka damu ba ina son ganin mijina yanzu yanzu nan a daki" ta wuce fuuuu ta barshi a nan

"Sir ya zamuyi?"

Wani harara ya bankada masa wanda yasa idris sunkuyar da kai da sauri

"Mashinan koyon gudu na suna na ?" Jinjina masa kai yayi ma'ana eh su ba'a huda ba

Da gudu ya kwasa ya dare bayan mashin din ya nufi hanyar gate








Oum Aphnan
[6/26, 5 PM] Chuchu👻: Yanda Major Adeel ya fice a harzuke haka ya dawo a fusace ,saidai yana shiga gidan ya tadda main entry din a garqame dam dam ko motsi bayayi yasa thumb print din yatsunsa don kofan da thumb print yake aiki amma yaqi budewa he was shocked don haka ya fara dukan qofar ,saidai tsit kake ji ba alamun dame nunfashi a cikin dakin .a Hassale ya juya wajen sojojin da ke gadin gidan.
"Idris??!" He shouted his name

Da sauri ya qame ya Sara masa "Yes sir "

"Idris ina Madam?"
"Madam tana nan a ciki sir"
"Haiii amma kamar ba kowa a gidan" ya furta a Hassale ya sake juyawa yana dukan kofar
"Yusrah ? Yusrah ?? Come and open the door..."
Cikin gadara ya juyo muryarta daga can saman benen gidan tana leƙoshi a kasa so restless yana pareti kamar me atisaye.
"Hello young man ,bazan bude ba saidai ko ka koma inda ka fito ko kaje hotel amma bazan taɓa bude maka ba"

Duddulo ido yayi cikin masifa da tashin hankali "hey Are You kidding? Wasa dake nakeyi ? Gwara ki bude mun kofar cikin gidana and face your punishment idan kuma ba haka ba the worse thing will follow ,don dake da uwarki saina qasqantar daku na jaku zuwa titi.."

Murguda masa baki tayi ta na farfar da ido ta rike kwankwaso "Plz do it if You can and dont be a looser kaji?"

"Kizo ki bude kofar nan kafin in cin maki a nan wajen "

"Hauro mana,nace ka hauro in zaka iya,Yau daya da baka cikin gidan nan kar ka tone nishadin zuciyata ,so ka tafi can hotel ka huta zan kiraka if i am done with my beauty sleep but as For now barci nake ji ,and bazan bari kayi distirbing sleeping circle dina ba"

Wani takaicine ya taho ma Major Adeel wuya ya shakesa ,kamar taɓaɓɓe haka ya bude murya yana kwarara ma yaran sa kira
"Oya ku bani tsani ,quick quick give me a ladder"

"Tsani???" Ta nanata masa cikin alaman tambaya.

"Let me climb up and meet You sai nayi qasa² dake"

"Oho da gaske?🫤😳to ka jira zamu gani" itama ta zura hanyar dakunanta da gudu.

Su kuwa da sauri sukayi backyard din gidan da gudu suka dauko dogayen tsani Irin na qarfen nan masu qwari mai kama da na nepa suka hade masa .cak idris ya tsaya yana kallon ogansa da yake neman zama taɓaɓɓe saboda mace ,muryarsa qasa qasa yace "sir wai me zakayi dashi?"

"Me idonka yake gane maka? Haurawa sama zanyi in shiga gidana inje in maganin watancan qaramar halittan"

A sittin sai ga yusra ta dawo hannunta damqe da wani abu ,cak ya tsaya yana qare ma hannun ta kallo daga qasan da yake kana ya daura da tambayarta

"Meye wannan a hannunki?"

"Ina ruwanka da abinda yake hannuna ? Tsorona ka soma ji....?" Banza yayi mata kana ya kama tsanin zai hauro.

Kwarma ihu ta yi gamida bude iya Muryar da Ubangiji ya bata "Mutanen gari kuzo ku gane ma idonku abunda nike gani ,Major Adeel gawurtaccen soja kuma qasaitaccen dan kasuwa mai kamfanoni mai mahaukatan kudade motoci da gidaje da jiragen sama gashi yau yana ɗanewa a tsani kamar mai yankan wutan nepaaaaaaa....duk wai don yazo yayi fada da matarshi ewoooh abun kunya"

Dakatawa da hawa yayi saboda kar a hango shi daga waje
"Ke wai kin san ko Ni wanene kuwa?"

"Nima kasan ko Ni wacece ? Jeka tambayi qawayena dalilin da yasa ake kirana da suna small pepper🌶️"

"Yusrah Yusra ina tausaya maki ,Yusrah "

"Ni kar ka sake tausayina mu fafata i can fight the hell out of U ,ayi balain wanda yaji wuya yayi surrender "

Cikin mamaki da qanqance ido yace "ke wai kin manta nan gidana ne?"

"Ehen Ni kuma kace bamu da gida halan a bila ka tsinto Ni?"

Cigaba da haurowa yayi cikin fusata ,ba abinda ya Qosa irin yaji ya damqi wuyarta

Ai tana ganin hakan ta kinkimi botikin ruwa daya daga cikin wanda ta jere a wajen,kafin ya ankara ta sheko masa tun daga saman maɗigan kansa .

Gantsarewa yayi ya bude murya yana kwarmato ya sakko qasan da sauri saboda kar tsantsin ruwan ya kadashi daga interlocks din da suke shimfida a wajen masu tsananin tsantsi kamar tiles.

"Ni kike watso ma ruwa? Ni kike jiqawa?"

"Badai You want to disturb my sleep ba? Badai nace ka koma sai na tashi ka dawo ba ,to wallahi in ka sake attempting haurowa i will sprinkle pepper 🌶️ a cikin ruwan inna hautsina ruwan da garin borkono na sheko maka zaka san dalilin da ake kirana small pepper 🌶️"

"Yusrah kin shiga uku,Ni dai ko?"

"Weeeeeh kaji tsoro wwweeeeh amasa a tule hauro mana ko tsoro na kake ji?"

"Humm wallahi yusra You must pay For this wannan abun shine qarshen ki mu zuba " ya wuce da sauri yayi hanyar parking lots don barin gidan.

Tale qafa tayi tana masa tafiyan en iska tana karkada masa medium nyash dinta ,girgiza kai yayi cikin malolon baqin ciki ya shige motan yana doka ma duk yaransa tsawa da gudu driver din yazo ya shiga don driving dinsa to the hotel.








Oum Aphnan
09065990265
[6/26, 7:59 PM] Chuchu👻: Sai dare ta bude qofar wajen 11 ya dawo gidan bai cema kowa komai ba ya wuce part dinsa ya rufe kansa.

***
Washekari
Da yangarta ta fito daga bathroom tasha wanka tana tsane gashin kanta da qaramin towel ta tsaya a gaban mirror ta bude roban chewing gum mai qamshin vanilla ta saka a baki tana taunawa a hankali ta isa gaban closet dinta ta bude da nufin ta dauki kayan da zata saka

Ya Salam! Wayam ta gani kamar an share.
A tsorace ta isa gaban dayan ta bude shima wayam haka ta biya duk ukun babu tsinke me sunan kayanta sai wani madaidaicin akwati a qasan closet din ,cikin mutuwar jiki ta tsuguna ta bude akwatin abayoyine danke sunfi kala ashirin .Ai bata san sanda ta daura hannu aka ta kwarma ihu ba tayi waje karce ta fice da gudu tana kwarara masa kira "Adeel ?...Adeel??where is that devil in a man...ADEEL??"

Tun daga saman bene take kwarara masa kira da qyar ta laluboshi a can garden din gidan yana zaune kan kujera yana karanta jarida kan table din gabansa tataccen fruits ne yana sipping a hankali ,kayan da yake sanye dashi na exercise ne wannan zai tabbatar maka da motsa jiki ya gama .
Duk ihun kiransa da takeyi baisa ya motsa ba Sa da tazo gabansa ta rike kwankwaso
"Adeel ban ga kayan sakawa na ba ,suna ina kenan?"

Cikin yamutsa fuska na wanda baisan maganar da akeyi ba yace "to me yasa kike tambaya na"

"Saboda daga Ni sai kaine a cikin gidan"

"Ok jeki gym house ki duba "
Dago kai tayi tana kallonsa
"Rainin wayo ko me? Me zai kai suturuna wajen gym ?"

"Ina ganin Zaifi maki dadi kije ki duba fiye da ki tsare Ni da tambayoyinki maras answer "

Batabi ta kansa ba ta ruga da gudu hanyar wajen motsa jikin gidan saidai tun kafin ta qarasa ta soma perceiving qaurin kaya da suke cin wuta dararo idanuwarta tayi duk waje ta fasa ihu .

A gigice ta dawo wajen sa tana aiko masa da zagi

"Mugu Azzalumi kana ina ....maqetaci ina ruwanka dani wai me nayi maka ne akan me zaka tsane Ni ,ina ruwanka da kaya na ha'ahhh? Kawai gwara ka kashe Ni ka kashe Ni ka huta Adeel "
Tana magana ne jikinsa na rawa hawaye na tsiyaya mata a fuska.

Cikin rashin damuwa ya dago tamkar baiji duk abunda take cewa ba

"Aah wai kuka kikeyi?Gani fa nayi wannan kayan da kike sakawa sun cika yin tsirara tsirara,wannan ya baki daman juya mun jikinki anyhow a gaban yaran aiki na ,soooo naga ya kamata in qonasu ,tun da dai Matana tana da decent clothes sai ki cigaba da sa kayanta,kinga in na ganki a cikin kayanta zai ringa tuna mun da ita...ko an fada maki zaki shigo mata gidane kina mata shigan fitsara kamar wata model bayan kin kashe ta?"

"Oh🤨🤨🤔Kana nufin ka qona mun rankatakaf designers din kayana masu arnan kudi da tsada ? Kana nufin ka kona mun unique kayana da ba'a samun irinsu ko a qasashen waje sai mugun sa'a? DUK SABODA IN SA KAYAN MATACCIYAR MATARKA???"

cikin murmushin qeta ya amsa ta da "Eh kuwan"


Dafe kai tayi cikin rashin madafa
"Oh my goodness wai ma taya na hadu da wannan mutumin ne mai ciwon Qwaqwalwa ma tukunna ,ya Salam!!! Ni zansa kayan gawa?....humm kasan menene? Wallahi wallahi na tsane ka!!!" Ta juya bakan bakan zata wuce ciki .

Dariya ya kece dashi,wanda ya sata dakatawa ta waigo tana kallonsa "hhh wannan qumbunan roban da kike sakawa da wannan parking din gashin kanki da kikeyi kamar er bebin roba dama ina so in maki warning tabbas ki daina dole ki zama er gargajiya irin matata ,shigar riga da zani ki daure kanki tamau da kallabi gashi daya bana son ya leko waje ,ko atamfa ko riga da zani sune kadai kayanki a gidan nan kuma kar in sake ganin kanki ba dan kwali "

Dariya ta fashe dashi "oh really ? Baka da lafiya bai kamata ina biye maka ba kaje ka nemi consultant na mahaukata"

"Oh yes! And na manta ban fada maki ba duk wa'innan takalmar naki na rashin da'a duk na qonasu ..." Waro ido tayi ta nuna shi da yatsa hawaye na shararo mata a kunci

"Ka qona mun takalma ,Adeel kasan yaya na same su kuwa?"

Oh yes ! And in addition,Duk account ɗinki na bankuna na rufe su ,na lura duk su suke saki zama almubazzara ki ta facaka da kudi so na rufe" ita ko jin surutansa ma bata yi kawai tunanin tsadaddun takalmarta takeyi ,idanta nakan bakinsa har saida yayi shiru tace
"Adeel ka qona mun takalma? Worth more than 33m dollars?😭

Jinjina mata kai yayi yana murmushi .

"Adeel ka qona mun takalmana qirar malaysian,Arabian,Indian ,europian duk ka qone su? Duk na rasa su kake nufi🙆‍♀️😭😭😭?

Dafe kai yayi da sauri alamun ya tuno wani abu
Da sauri ya daga mata hannu "kinga sorry kar ki mantar dani wannan,dan saurara

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment