Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan mu,sannan mu sakata tayi wani fuck up ko sau ɗayane mu bada hujjar da zaisaka ta zuwa gidan yari,shikenan,

We need her out of our home and our lives.

Sannan Maganar Jamaimah dole muyi confronting Hamma ,wannan ba abu bane na boyewa cos idan Ya bar abun nan a boye nan gaba Outcome ɗinsa babu kyau,

Kaɗa kai yayi cikin gamsuwa da shawararta ,bayan sun gama cin abinci kowa Ya koma kan aikinsa Akan idan suka koma gida zasuyi magana da Nameer.


**************

CAMEROON DILAH PALACE  .

     Jamaimah bazan gaji da faɗa miki ba kinyi girman da masarauta ke buƙatar kiyi Aure ,sannan kinfi kowa sanin Al'adar mu babu wani namiji da zaki Aura bayan wanda muka zab'a miki shima ɗan AHALINMU,Saboda shi kaɗai ne wanda zamu ɗora kan kujerarmu saboda kinsan dai mazan Mata ke sarauta ba gado ba,shi yasa muke zaban na jikinmu,masarautar nan baki ɗaya kece mace wanda mijinki zai gajeni.

Tun Kina yarinya muke miki abunda kike so kika zaba ,kama da abunda zakici zuwa sutura ,zuwa zabin karatu,wanda ke Kina kallo yarda akayi tataburza zuwanki China,

Yanzu kuma Lokacine da magabata suka zab'a maki mijin Aure HARITH bana san azo an'a wayace Jamaimah,

Mahaifinta Sarki Rais Ya faɗa ciki harshensu na Fulanin cameroon fuskarsa fal dumuwa.

    Gyara zamanta tayi tana mai kallan girman faɗar mahaifinata wanda Ya gada guri mahaifin Mamanta ,kamar yarda baban nata Ya faɗa dukkansu idan kabi zagayen masarautar da tarihin mulkinta maza da matansu AHALI ɗaya ne,shi yasa Aurensu mace ɗaya wanda a haka aladarsu ta tafi muddin zakayi mulki macen nan guda ɗaya,

Kallan mahaifinta tayi cike da fitsara cikin yaren nasu da kuma salo na amfani da soyayyar da mahaifin nata yake nata tace "Lamiɗo ,kafi gane nayi Aure cikin wannan masarautar nazama baiwar wani wanda saboda ni yake mulki badan Ya kai yayi ba,,

Kamar 'fa kaine Lamiɗo, yarda Dada na ta ɗoraka kan kujerar nan amma kana kallo abinci nan bata ci sai ka gama tukunna taci sauranka indai Kana gurin wai da sunan al'ada,alada a mey?

Ni gaskiya Lamiɗo ka yafe ni ,dan babu wani da Zan Aura wanda kuka zab'a 'dan kawai na maidashi Lamiɗo,sai dai sarautar nan tabar ɗakinmu ta koma wani ɗakin tunda Ai masarautar nan akwai yaƴan mata da kakannin akwai yarda zakuyi ku ɗora harith d'in idan shi kuke so,ga yan mata a gidan,amma banda Jamaimah 'dan yarda nake zab'an duk wani abu da nake so a bisa yarda kuka lalatani da zab'ar abinda nake So haka nan yanzu ma zaku barni da wannan lalatar na zab'i wanda nake san Aura dan har nama zab'a .

    Da fuskar lallashi lamido Ya Kalleta yace "idan kin sakko zamu sake magana yar Albarka ,naga alamun yanzu bazaki fahimci Mai nake nufi ba,"

Tashi tayi tana Mai sake basa girmansa kana Ya fita a fadar wadda dama daga ita sai shi ,

Tana ƙokarin fitowa wani bafaɗe yana koƙarin shiga inda bai Aune ba sukayi gware,

Ɗago kai da yayi yaga itace ba ƙaramun rawar jiki Ya fara ba 'dan yasan rashin mutuncin Gimbiya Jamaimah yau zai hau kansa,

Ille kuwa bai Aune ba ta ɗauke fuskarsa da wani irin tafi wanda yayi bala'in gigitasa,

Alƙabarta da Ya goga ta cire ta cilla masa kana ta miƙa hannunta wanda ƙuyangunta sarai sun fahimci Mai take nufi,

Da gudu ɗaya ta ƙaraso da ƙwarya a hannu ɗaya kuma da ruwa a wani tulu ta fara zuba Mata tana ɗauraye hannun data mari bafaden dashi,

Alamu tayi da hannu zuwa ga bafaɗen wanda sarai Kungarta ta hannun dama ta fahimta ,kai tsaye gurin Bafaden tayi da ƙokan da ta wanke hannu ta kama kanta ta kafa masa ruwan sai da Ya shanye tasa kana tace "a ɗauke mun shi akaisa gidan gyaran hali ,ruwan nan da yasha shi kaɗai nake san Ya riƙesa har gobe ."

Take kamar jira suke kar suyi wani laifin suka kama dakarin wanda yake ta ihun bata haƙuri amma taƙi koda sauraransa,

Kai tsaye sashen mahaifiyarta ta nufa wanda yaji kayan Alatu na sarauta,a kishingiɗe ta tarar da ita,

Kuyangun na ganinta suka fita dan basu guri 'dan yanzu Gimbiya Jamaimah zata maka wulaƙancin da zakaji baki ɗaya ka tsani kanka,

Zama tayi kusa da ita tana Mai ɗora kanta Akan cinyarta kana ta shagwabe fuska tace "Dada wai shi kam lamido bai gajiya da magana ɗaya?"

Ki samu lokaci fa ki faɗa masa nikam ina da miji a Nijeriya sannan ban Aura ba sai da na dirje,sannan nayi hakuri dada da har Yanzu banbi mijina ba abisa umarninki na 'in sake hakuri ,yakusa karewa fa Dada kifaɗa musu.

"Shafa yalwataccen gashinta mai santsin gaske Da Ya fito ta baya dadan nata ta fara tana Mai cewa"Jamaimah na faɗa miki Aurenki da yaran chan na Nigeria ba Aure bane ba,kaddararki itace ki maida Harith Lamiɗo wanda dole zakiyi,'dan haka gudun karmu sab'awa mahalicci muyi Aure kan Aure Ya kamata aje Nigeria a kamo yaran nan ko kuyi magana tunda akwai hanyoyi na zamani a kashe auren kizo ki bawa Harith Lamiɗo kiyi addua ke ki haifi diya kamar ki ta bawa wani Lamiɗo cikin Ahalimu bana san rigima surbajona,."

    Tashi Jamaimah tayi a cinyar Dadan nata ba tare da tace komai ba dan idan tayi magana rashin ɗa'ane zai fito sannan a rayuwarta duk da fitsara da izza irinta mulki jininta take bata so koda yayane tab'atawa mahaifiyarta ,amma 'fa itama bazata bari a b'ata mata ba ,

Tana mutuwar san Nameer wanda shine babban dalili da yasa ta Auresa sannan tayi imani da Allah koshi bai isa Ya raba kansa da ita ba sai dai Allah Ya rabasu ,saboda a yarda take jinta babu wani namiji da zai kalleta yace wai yau baya santa zai rabu da ita ,tabbas 'dan kuwa duk inda kake jin kyau Jamaimah takai,

Takanas ta miƙe tana Mai faɗin ma Dadan nata "na barki lafiya sarauniya babba",

Sanin maganar ce bata so a ja yasaka mahaifiyar tata rabuwa da ita tunda duk guje gujenta tasan sai ta Auri harith,

    Tunda ta fito 'dan nufa sashen ta take neman mai rabon shan wulaƙanci bata samu ba har ta shiga sashenta,

Zaune ta tarar da Harith a dining ɗinta yana Mai shafawa wata kuyangata ɗuwawu,

Ƙaramar dariya tayi lokacin da idanunta suka sauka Akan wanga al'amari,

Da sauri yarinyar ta matsa daga gefensa jikinta na ƙarma inda shikuma Ya lashe leb'ensa na ƙasa yana Mai kallan JAMAIMA da maita.


Ya kukaji character ɗin Jamaimah?

Shine mene ra'ayoyinku bisa rayuwarta?

Shin Mai kuke tunanin kan Fadil?

CHUCHUJAY

Tbc
[3/6, 5:11 PM] Chuchujay✍️: AHALINA

(Siblings of different father's)

Book two 'in Aure Uku series

        By

chuchujay

Episode 1⃣7⃣➡1⃣8⃣

  Tasowa Harith yayi yana Takowa ga Jamaima kamar babu abunda ta kamasa ya nayi,

Yana ɗaya daga cikin abunda Ya saka ta tsanesa ,a kullum idan zai ganta sai Ya nuna a fili jikinta yake so.

Kallan kuyangar dake ƙarma tayi tace "idan ma nace zan miki wani abu maine zan miki,kije kanki kike cuta saboda shi Yarima Harith ɗin da kike biyewa babu inda zai kaiki sai dai Ya baroki,sannan wani abu Mai daɗi da nake so ki sani,kinyi babbar sa'a da Ya zamana ba nawa bane kuma bazai zama nawa ba,'dan haka ki bace mun a guri sannan idan kika kuskura na sake ganinki sashe na sai na yagaki ,Alƙwarin gimbiya jamaima kenan,kinsan zanyi fiye da haka,"

Bace mun a guri stinky whore .

    Da gudu yarinyar ta fita har tana tuntube 'dan tagama sawa aranta ta mutu kawai a sanin halayyar jamaima ,amma ga mamakin ta sai taga akasin haka,

Daf da ita harith Ya matso ,bata matsa ba sannan batayi gizau ba ,jira kawai take taga ƙarshen iskancinsa ƙugunta Ya kamo ya jawota jikinsa yana Mai mata wani irin shafa a ƙugu,

Wani karamin dariya tayi tana mamakin ƙarfin guts ɗin Harith,tayi imani da Allah idan baiyyi wasa ba akan jikinta shi zata fara kashewa,

Kansa Ya sako dai dai saitin kunnenta yace "Ki daina wancan furucin na ni ba naki bane ba kuma Zan zamo naki ba,ƙaddarar mu a haɗe take gimbiyata,Nan da ƙwana uku ki shirya mayar dani lamiɗon ki domin hakan zai faru ko Kina so ko baki so,a yayin da nikuma nake kan murnar da bana tunanin da wani Lamiɗo da zai Kaini,saboda na farko Zan samu masarautar nan sannan na biyu Zan samu sarauniya Mai kyau da diri na jiki nayi yarda nake so da ita Akan gadon milkina,ina mutukar kwadayin jikin ki Gimbiya jamaima ,sannan kar ki damu 6 inch ne D*ck ɗina kinsan babban goro sai magogar ƙarfe., "

    Kafun yayi Aune tayi wani irin Hankaɗe sa ta ban mamaki da Kafarta inda Ya faɗi kasa wanwar,binsa tayi ta ɗora Kafarta kan kirjinsa ta taka da karfi kana tace "Abu na farko da nake so ka sani saboda yan iska irin ka koda naje china ba karatu kawai na tsaya ba sai da na samu Black belt a taekwondo ,idan na maka wani dukan sai  anyi tunanin hatsarin mota ne kayi,

Kana daukar kanka jarumi ba?

To kai da b'awan gyada a gurina baka da banbanci ,b'awan gyaɗa wanda zanyiwa b'ara ɗaya ya fashe ,gwanda da kasan cewa babban goro sai magogin ƙarfe domin jikina yafi karfin wannan abun dake gabanka da kake bin low life kuyangu dashi ,be guided Next time idan ka kuma tab'a mun jiki Zan saka takobi nasare dukkan hannun ka da Ya taba ni,

Stupid scumbag ,

Yawu ta tofa masa a fuskasa ta bar gurin,

Mikawa yayi yana binta da kallo yana tunanin hanyoyi da dama da zaibi Ya wulakantata ,tabbas da ace baya san zama sarkin garin da babu abunda Zai hanasa yi mata fyaɗe tuntuni 'dan shi jikinta yake so ba ita ba,

Amma yazama dole Ya ƙwantar da wuya muddin yana san cimma burinsa guda biyu,na samun jikinta da kuma zaman sarkin DILAH,."

Tashi yayi daga ƙasan da yake yabar sashen da Tunanin kala kala.

    Jamaima kuwa bayan ta shiga ɗakinta Gadonta ta hau ta ƙwanta ta jawo system ɗinta,

Maiyi mata tausace ta shigo,alamu tayi mata da ta tafi ,babu musu ta koma cikin girmamawa,

Page d'in Nameer na Instagram ta shiga,sababbin hotunan sa ta gani da Fadil,

Murmushi tayi tana Mai jin wani irin masifaffan sansa a cikin zuciyarta ,tayaya ma zata iya zama a raba ta da Nameer wanda take jinsa shine rayuwarta?

Tayaya?

Zumbur tayi ta miƙe da ta tuna maganar Harith na cewa nan da kwana uku zata zama tashi,

Dole tasan abunyi domin ta fahimci idan ta tsaya a gwiwowinta za'ayi mata shirme ne a masarautar,dan haka idea ɗin guduwa taje gurin Nameer shine kawai Ya faɗo mata,

Passport ɗinta ta nemo tare da ID cards ɗinta,

Take tayi Booking flight d'in da zai tashi Nigeria da yamma,

Aƙwatinta ƙarami ta haɗa da dukkan wani jewelry nata da kuɗaɗe masu yawa aje gefe tana tunanin ta yarda zata gudu,

Driver ɗinta ta kirawo,

Babu daɗewa yazo ,ƙaramun akwatinta ta bashi yayin da ta dauko kit din tabi bayan sa,

Kai tsaye Airport Ya kaita,suna zuwa ta wani haɗe rai ta kallesa tace "Zan kiraka anjima kazo ka ɗauke ni amma for now zaka iya tafiya,"Babu musu yace to cike da girmamawa,wani daɗi taji lokacin da Ya bar Airport d'in tana Mai jin wata iskar freedom na shigar ta ,atleast har ta bar kasar babu wanda zai san guduwa tayi,

Zama tayi dan jiran akirasu idan lokaci yayi,

A hankali ta rufe idanunta tana Mai fadin "Nameer gani  nan zuwa gareka."


*************************

    Tunda Hafsatu ta iso garin Adamawa taji hankalinta yayi wani irin ƙwanciya da bata iya misaltawa,bata tab'a zuwa garin ba amma a karo na farko ɗin nan taji baki daya komai nata Ya aminta da garin,

    Samun gidan innan mahaifinta bai mata wahala ba saboda tunda ta taso suke communicating da juna,

Ƙauna babu irin wadda Inna talle bata nunawa Hafsa ba ,ba sai ta faɗa ba Babanta yana ɗaya daga cikin abubuwa mafi soyuwa a gareta,abu ɗayane wanda ta kula Innar tata tana cikin shine hali irin na talauci sosai ,bata da kowa sai yaranta Muhammad shi ɗaya wanda yake sayar da rake a ƙofar gidan ,dukanin shekarun sa bazasu wuce Goma sha ɗaya ba,kamata yayi ace yana makaranta a wannan shekarun ba wai zama saida rake ba wanda ƙwataƙwata ribar tasa nawa Take,

Sawa tayi a ranta bazata bari ta zamar masu wani karin nauyi ba ,ko aiki ne zata nema tayi dan basu nata tallafin duk da kuwa itama tana da burin nata karatun ,bari tayi sai ta ɗan kwana biyu zata wa Innar tata maganar Aikin nata ,

Ille kuwa bayan ƙwanakinta Huɗu a gidan wata safiya bayan ta gama karyawa da ɗan kunu da alala ɗin da Muhammad ya fita Ya siyo mata,

Kallan ta tayi tace "Inna wai ni kam babu wani aiki da Zan iyayi a garin nan koda wanke wanke ne da shara,kinga muhammad ma ya kamata ace yana zuwa makaranta Kema kuma gaki Ana ɗan fama da jiki idan na fara aikin wani abun Ya ragu.

    Dan shiru Inna tayi tana nazari kafun tace "a yi haka kuwa Hafsatu,yau duka ƙwananki nawa a garin nan da har kika fara maganar aikatau,haba dan Allah,kar ki wani sakawa kanki damuwa ,muhammadu nan kawuna dake kano yayi Alƙwarin daukar nauyin karatunsa wanda dai nasan abunda yasaka baiyyi magana ba ƙilan wani abu ne yayi masa yawa,"

Karki damu Allah zai rufa asiri ,ke dai ki zauna ki huta babu abunda zai gagara.

    Dan shiru Hafsa tayi kafun ta kuma cewa"Inna na dai dage ,sannan ba wai dan an Gaza ɗin bane,ni kaina zaman guri ɗayan zai dameni da yawa,"

Shiru Inna tayi a karo na biyu tana Mai juya maganar Hafsa,tabbas suna buƙatar taimako tunda dai ita a yanzu karfinta Ya ƙare,ga tsufa ga kuma yan ciwace ciwace da baza'a rasa ba,

    Ajiyar zuciya tayi tace"shikenan hafsatu Zan kira Balarabe idan yaso ko Mai yace hakan za'ayi,bazan so ace daga zuwan ki kuma kin fara aikatau ba ba tare da yasani ba,"

    Kamar yarda inna tayi suggesting su kira Baban hafsa haka kuwa akayi inda shima yayi na'am da maganar aikin Sannan yana Mai yin alfahari da ɗiyarsa,

Bayan ƙwana biyu da maganar Inna tayima wata ƙawarta magana wadda dama sana'arta kenan raba yan aiki,cikin murna da jin daɗi matar ta cewa Inna dama kuwa akwai matar da tayi mata magana tana san yar Aiki budurwa Mai nutsuwa ,ina ganin Hafsatu zata dace da aikin kuma matar bata da matsala ,kawai dai abu ɗayane,ki jamata kunne babu idanunta kan mijinta,

    Godia sosai Inna tayi mata sannan ta tabbatar mata insha Allahu bazata samu wata matsala daga Hafsa ba ,

a haka suka tsaya inda aka yanke washe gari zasuje gurin hajiyar,

Washe gari da Inna da Hafsa da ƙawar inna hajiya mai yara suka nufi gidan da zatayi aikin,Bayan isarsu gidan Akayi masu iso zuwa falo,

Kallan gidan Hafsa take a hankali tana Mai yaba irin arzikin da Allah yayi musu dan tunda Take bata tab'a shiga Gida Mai kyau irin haka ba,

Suna zaune suna zaman jiran Hajjiyar ta sauko daga benenta wanda matattakalar kawai abun kallo ne,

Zama tayi tana Mai amsa gaisuwarsu wadda suke mata kamar suna jira,da fara'ata fal fuska ta amsa su ,

Hajiya Mai yarace tace "Hajiya Shatuh ga dai Mai aiki nan an kawo ,idan batayi maki ba to ,gata nan dai zaune,"

    Kallanta Aunty shatuh tayi tace"Yaya suna ki yan mata ,"

Ƙasa Hafsa tayi da kai tace hafsa,

"Kice tsohuwa ce ,to ina fatan dai kunyi magana da maman yara ,sannan gaskiya Mai kwana nake So ba wadda zatana jeka ka dawo ba,"

Shiru sukayi baki ɗayansu dan maman yara bata faɗa musu ƙwana zata nayi ba,

Kafun Inna tayi magana Hafsa ta rigata ta hanyar faɗin "Babu komai Hajiya amma ina san amun alfarma ranar asabar ina zuwa gida ,"

Murmushi Aunty shatuh tayi tace"baki da damuwa sannan duk wata zan na baki dubu talatin".

    Jin kuɗin yasakasu fara mata godia yayin da daga bisani Inna da Hajiya mai Yara suka wuce Akan washe gari za'a kawo mata kayanta tunda sun tafi ne bada niyyar aikin kwana ba.


*********************

   Kai tsaye Nadiya na isa gida ɗakin Nameer ta nufa da Fawha ta tabbatar mata yana ɗaki,

Knocking tayi har sau uku kafun yabata izini ta shigo,

Zaune ta tarar dashi kan abun sallah,

Zama tayi kan couch ɗin dake ɗakin tana mai yi masa ƙaramun murmushi,ninke abun sallan yayi yana Mai kallanta yace "yau Baby Sis kin tuna da hamman ki kenan ,hope im safe ,"

Wasa ta farayi da Kafarta kafin tace"i dont think you are actually,"

Wayarta kunna ta shiga kan Information ɗin Aneesa ta miƙa masa 'dan Ya karanta ,

Da mamaki Ya gama karantawa a yayin da wani chilled tsoro Ya shigesa musamman da ya san cewa Anisa ɗin  na tsamo tsamo cikin AHALINSA,

Kallan Nadiya yayi yace "Nadiya mai yasa kike ajiyan wannan Info ɗin a hannunki ba tare da an kaima police ba sunyi arresting ɗinta,kinsan she's dangerous amma kika yi shiru?

Tashi yayi yace "dole mu san abunyi,"Bari na kira commissioner Hadi.

    Ƙarb'ar wayar tayi ta haɗa da tashin da yake ƙokarin yin wayan tace "kana tunanin zai solving komai?"

Mai yasa Bakayi tunanin abunda Ya saka take yawo freely ba har Allah Ya kawota gidan mu,

Bro tana da masu mata cover ,sannan tana da haɗarin gaske ,and na zo na faɗa makane badan ka tada wani tarzoma ba ko kayi wani abu da zata gane cewa mun san ita wacece,

A hankali zamu saka mata trap d'in da zata kama saboda dukkan wani wayau da kake tunanin Anisa na dashi,After all akan wayan aka basu horo,

I told you dan ka zama alerted .

  Zama yayi yana Mai dafa kansa yace "Ya rabbi,

Sis Mai yasa nazama nine silar wannan dilemma d'in da muke ciki,bana tuna b'atawa wani da har zai kai ga tura mun assassin har cikin gida sannan da ƙazafi mafi muni,what's going on ?

    Kama hannunsa Nadiya tayi tace "ƙwantar da hankalinka Hamma zamu zo dai dai nan gurin cos a yanzu maganar da nake maka ana bincike Akan motive ɗinta na zuwa wanda nasan za'a gano ,"

Juyowa tayi ta Kama hannunsa tana Mai kallan cikin idanunsa tace"Hamma ,im your sister sannan duk wani abu da zanyi bazan tab'a yin wanda zai cutar da kai ba,hasalima farin cikin ka a kullum shine abu na gaba a gurina ,babu wani abu da kake boye mun?"

    Dan shiru yayi yana kallanta cikin nazari kafin yace "abu kamar me ?,bana tunanin akwai wani abu da nake boye miki Nadiya trust me.

Kafarta ta ɗora kan ɗaya tana Mai saka fuskar damuwa tace "Hamma akwai,sannan Ya kamata ace kayi magana musan abunda zamuyi saboda muddin mami taji maganar nan kaima kasan gidan nan zai haɗe sama da ƙasa ,so talk to me".

    Shiru yayi still 'dan shi har a lokacin baiyyi tunanin tasan maganar Jamaimah ba ,sannan ƙwataƙwata bai kawo ma maganar bace domin yasan babu yarda za'ayi ta sani,sannan haɗuwarta da Fadil ma ba sani ba ,kallanta yayi yace "just tell me Sis bani da wani tunani na abunda nake boyewa.

Ganin Ya kasa ganewa ne Ya sakata cewa"maganar Auren ka da Jamaimah ,"

Kamar saukar aradu haka yaji maganar dan 'in his wildest dream bai tab'a tunanin Nadiya zata san maganar nan ba,cike a mamaki yace "ina kikaji maganar nan".

    Dauke kai tayi bata san haɗa ido dashi tace "ina kan binciken Anisa ne da san gane gaskiyar abunda tazo dashi  na fara bincike akanka rayuwarka a china,im Sorry ban faɗa maka ba,so 'in the process na gano Auren ka ,Hamma wannan ba abu bane na boyewa ,yes kayi ba dai dai ba sannan kun yi wasa da girman Aure amma bashine yake nufin za'ayi shiru da abunda,we All know that babu wanda Ya wuce mistake and you made one,duk kaifin tunanin mu iyayenmu sun fimu tunani da hagen nesa,so mu faɗa musu koda zasuyi fada suji ba daiɗi amma su zasu zo da solution."

    Kamo hannunta yayi cike da tsoro fal ransa yace "Nadiya ke da wa kuka san maganar nan,?"

"Abdallah,"ta bashi amsa.

Wani yawu Ya haɗiya wanda Ya saka Adam Apple ɗinsa motsawa yace "Nadiya please lets not tell mami about this,kinsan yarda take ba,musamman da case ɗin Anisa a ƙasa ,inajin ƙarshe disowning ɗina zata yi. "

    Cike da tausayinsa tace"Hamma amma Ai bazamuyi ta boyan maganar nan ba har abada ,idan ita kuma yarinyar tazo fa?"

Da sauri yace "nasan Jamaimah bazata taba zuwa mana ba cos kilan ma ta manta da wani Aure tunda bet ta ɗaukesa,'dan Allah Nadiya kafin mu gama maganar Anisa kiyi shiru tukuna sannan shima Abdallah kisa yayi shiru 'in yaso After that na maki Alƙawari da kaina Zan faɗawa mami da Papa. "

Ganin yarda ya marairaice mata yasa Nadiya kaɗa kai tace "i Trust you Hamma and namaka Alƙwari duk wani yanayi da ka tsinci kanka ina tare da kai."

Suna cikin wannan moment ɗin aka ban kaɗo kofar ɗakin aka shigo,

"Anisa?"

Nameer Ya faɗa da ɗan duburburce sanin maganar da yake da Nadiya.


CHUCHUJAY ✍🏽

TBC
[3/6, 5:12 PM] Chuchujay✍️: AHALINA

(Siblings Of different Father's)

Book two 'in Aure uku series

    By

   CHUCHUJAY

Episode 1⃣9⃣➡2⃣0⃣

    Tana karasa shigowa ciki ta saka hannunta a bakin ta tayi gasping tace "OMG"

Zama tayi gefen gadon sa tace "har na tina wani littafi da nagama karantawa jiya,"F*CK me Brother,"

Cije kasan lebenta tayi tana maiyin wani 'dan iskan sound tace "It was aiishh,so hot and steamy,best Erotic novel dana taba karantawa kenan cos a karatunka kawai kafun ka gama kayi wet da zaka nemi ɗauki,

It started with a fingering cos sister ɗin bata cika san rufe jikinta ba gashi komai nata is heavy duk da dai ita tafara seducing yayan but she succeeded da kullum akwai diff sex da style,

Kamar dai ke yanzu Nadiya Ai komai yaji babu wuya zaki shawo kan Namiji gashi  dama kin saba cin forbidden fruit,trust me da ace ina bin mata da tini na biki,i wont mind eating your pinky.


Cikin fushin Nameer ya mike jin kazamin ƙazafin da Anisa ke jifansu dashi,

Yana ƙokarin kai mata duka Nadiya ta riƙesa ,

Tashi tayi tace "Hamma don't stain your hand With dirt,kasan idan mutum kazami ne mazinaci gani yake kowa ma haka yake ,da mindset irin na Anisa duniya bazata tab'a ci gaba ba,"

Tasowa tayi ta tako gaban Anisa wadda ke zaune gefen gadon Nameer,

Kallan kazamar rigar dake jikin ta ƙarfe baƙwai na dare Ya sakata ƙaramar dariya tace "im sorry da zan using Vulgar tone dake,kallan riganki kawai yasa na tabbatar you're trying hard amma ga dukkan Alamu Hammana har yanzu bai samu nutsuwa dake ba,'Allah sarki,

Bari na faɗa miki,muddin kina zaune cikin rayuwarsa haka ne zaita faruwa,saboda you stink wanda bana tunanin kina ji,

Yakamata ace idan mutum na wari shi zai fara ji ,amma ke kam irin jakan nanne da basu gane ma suna warin,ko da yake bama ki da kwakwalwar da zaki gane.

Kince muna abunda bai dace ba da Hamma ki?

Kinga na kasa maimaitawa saboda mu da kika gani mun samu mahaifiya ta gari da ta bamu tarbiyya,kinsan mafarinta daga uwane idan uwa ma bata dashi ina yaranta zasuyi,and bama karanta nasty novels keep your suggestion,sannan im that spec da nima da ina mata Allah Ya kiyaye bazan yiki ba,Allah Ya tsareni.

    Tasowa Anisa tayi da zafin rai tayi kan Nadiya tace"idan kika sake kiran Mahaifiyata da bakinki ɗin nan kazami sai na kasheki,"Ke bama ke ba babu wani isashen da yake da tsarkin bakin kiran Mahaifiyata a gidan nan .

Ganin tana ƙokarin kai Nadiya bango ya saka Nameer jawota Ya ɗauke mata fuska da mari yace"ina fatan,na faɗa miki kar ki sake shigo min ɗaki?Get out kafun nayi maki abinda zakiyi dana sani na shigowa gidan nan,banza ƙazama mara hankali,tunkiya kawai ".

    Shafa inda Ya mareta ɗin tayi tana mai yin ƙaramar dariya cikin hawayen dake zuba kan kuncinta tace "na rasa dalilin da zaisa kuna kirana kazama bayan ina wanka a kalla sau  biyu a rana,amma babu komai,na maka Alƙwari kaga wannan kazamar ,i will have you and i will get you craving for more,

Tana kai karshen maganarta ta kalli Nadiya kamar zata kashe ta kana tabar ɗakin,

    Gyara tsayuwa Nadiya tayi tace "ouhh hamma yarinyar nan 'fa is insane for real bata da hankali,"

Amma wait yarda take maganar mamanta she's furious 'fa anya zuwanta gidan nan bashi da Alaƙa da mamanta?.

    Kamar Mai tunanin Nameer Yace "tazo nan gidan ne

Please Login or Register in order to submit comment