Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'yasaka Malam Balarabe yin nan da nan ganin 'ya nemawa yarinyarsa mutunci dan bayan bikinta har gyaran gida yayi,abinci 'ya bada akayi masa a waje sanin wacece laure matar da bata sake hali,habaici kuwa da zage zage Babu wanda bata saki ba amma yayi mata banza tunda yasan a wannan gejin sai dai tayi zagin domin kuwa yafi karfinta sannan duk wani abu da take masa kuwa ya karye domin ɗiyarsa yake san dama 'ya nutsar gidan miji yayi Aure kuma burinsa 'ya cika Alhamdulillah Auren kawai 'ya rage masa 'dan har mata 'ya samu.

Tarba ta mutunci yayi musu kamar shine macen gidan ,kafun kace mene labarin Zuwan Hafsat 'ya karaɗe gari wanda 'ya jawo yan tsurku zuwa ganin ta,Hasiya dake zaman zawarci gida kuwa babu abuunda take ma Abdallah sai shisshigi tanan addua Allah yasa cikin shishshiginta tayi wuff da wani abokinsa,

Motel Abdallah 'ya samawa kansa da kyar duk yarda kuwa Malam Balarabe yayi ya kwana gidan 'dan suna da masauki amma yarda Hasiya ke shige masa hankalinsa bai kwanta da yarinyar ba 'dan haka 'ya tafi akan da safe zai dawo inda a ranar dama zasu wuce,Ƙawayen Hafsa da dama sunzo ciki kuwa harda hauwa da Lawisa da tayi aure a doro,tsokananta hauwa ta ringayi akan ta kwace mata crush dama shi tabi Adamawa.

Washe gari da rana suka wuce bayan sha tara ta arziki da Abdallah yayi ma yan gidan da yan gari,bayan komawarsu Adamawa kuma da kwana biyu suka wuce Mecca inda suka bude sabuwar rayuwarsu cikin Aminci da ƙauna.

****************************

FOUR YEARS LATER.

NEWYORK CITY.

Green Sea palace .

Organized gurine wanda Sai ka tara zaka kamashi saboda tsadarsa,ammaa a guri na zuri'ar Tasu its just a piece of cake ,baki daya AHALINSU na gurin wannan ƙaramun taro da Grandpa Bulama 'ya haɗawa yan uku dan murnar gama karatunsu a cewarsa "a kasar 'da suka kare karatu anan 'ya kamata a tayasu murna ba wani guri ba dan haka suna gama taronsu na makaranta wanda kwansu da kwarkwatarsu suka je suka nufi Green Sea ,Nameer yazo da Twins ɗinsa"Afra da Afreen,Abdallah yazo da yaransa Muhammad,Nadiya tazo da yarinyar ta Fatima,yayin da Abbu,Ummu ,Affan da Afnan ƙannen Imam paki baki daya suka halarta,ciki kuwa harda gayyar gidan Grandpa Bulama da masu so da wanda babu yarda zasuyi amma a fuska bazaka ce ba,dama ko wanne AHALI ya ƙunshi hakan addu'ar mu kawai shine Allah ya sake haɗe mana kan zuri'a baki ɗaya, "

Washe gari suka wuce Nigeria baki ɗayansu .

Zazzaune suke lokacin dinner baki ɗayasu da ƙarin jikoki domin yin break fast,Afra yarinya yar kimanin shekara huɗuce ta kalli Muhammad Wanda ke tsaye cike da iyayi tace "Ya Muhammad ijlis mana "

Baki ɗayansu suka saka mata dariya banda ita da ta haɗe rai,cike da pouting lips ɗinta irina mahaifiyarta Jamaimah cos ita take kama da ita tace"mene kuma kuke mun dariya ai kunsan ba wani hausa yake ji ba, "

Zama yayi yana mai kallanta cikin hausarsa da bata fita da kyau yace "Ummi na bani hausa"

Dariya sosai sauran jikokin suka saka suna tsokanarsa har sai da Mami tasa musu baki suka bari kana suka nutsu suka fara cin abincinsu gwanin ban sha'awa.

Rayuwar cikin Ahalinsu rayuwace gwanin ban sha'awa da zaman lafiya duk da kuwa ko wacce zuri'a ta kunshi up and downs nata amma Alhamdulillah bangaren haɗe kansu abun gwanin burgewa,a gidan Nameer Yana zaunne lafiya da matarshi da yaransa wanda bayan haihuwansu ta fara aiki a company dinsa yayin da Nadiya da mijinta Ahmad da yarinyarsu suma suke aiki cikin haɗaka,bangaren Su Abdallah kuwa bayan haihuwarta 'ya maida ta makaranta nan cikin garin Mecca inda ta cigaba da karatunta wanda ta dauko farko,

A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu in which they live happily ever After.

ALHAMDULILLAH anan na sauke biro na daga kan takardar littafin AHALINA ,

Ina mai mutukar nuna godiyata gareku masoya da irin dumbin kaunar da kuke nuna mun,ina sanku fisabillilah sannan na sadaukar da wannna littafi daga AURE UKU zuwa AHALINA gareku masoya domin idan baku Babu ni,

My wattpad family mafari na ,ina mutuƙar maku godiya inda kuka kaimun AURE UKU 12.5k,AHALINA 2.2K ah cikin kwanaki kaɗan fa my series book 'ya samu view haka ,i cant thank you less,nagode.

Kuskuren dake cikin Allah ya yafe mun idan kuma rubutuna 'ya bata maka ta Wata sigar ina neman afuwa cikin rashin sanine,

Ida kuma ya amfaneka ko ya nishaɗantar da kai komai kankantarsa to kamun addua .

Yauwa kafun na manta zan amfani da wannan damar wajen sanar daku zuwan sabon littafina amma na kuɗine, amma fa a wannan karan a complete zaizo ma'ana zaka iya siyan complete idan baka san page by page ,book 1 free book 2 na kuɗi,

Sannan a wannan page din inasan jinjinawa masu tsayawa suyi comment inajin daɗi sosai Allahu ya barmu tare,wadda kuma ya cinye comment section baki ɗaya itace UMMU SUBAI'A sharhinta yana mun daɗi kuma yana karamun zeal na sake dagewa wajen rubuta abunda nake rubutawa ,daki daki sharhinta yake fita yake sani gyara abubuwa da dama,nagode sannan tukuicinki shine littafin gaba da zaki karanantashi baki ɗaya a kyauta idan Allah ya aramana rayuwa bayan sallah insha Allah.

Asha ruwa lafiya and barka da Sallah 'in advance

Nice taku a kullum

Amina Jamil Adam

Mrs Buhari

Ommu Mahnoor

CHUCHUJAY ✍️

Duk ni ɗaya🥰😁.

Follow me on my media platforms

Wattpad page:CHUCHUJAY

X:Ameenatourh_jay

IG:Chapter_green_

Fb:Ameeatourh jameel

Ku huta lafiya❤
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment