Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zo amsar Auren Hafsa Mama laure ta sare,kai ba ma ita ba, Babu wanda a garin baiyyin yamaɗiɗi da maganar ba mussamman da yakasance Mahaifin Hafsa 'ya nemi da Hafsa ta cigaba da zamanta gidan Innarta shi da kansa zaizo ayi duk wani Abu da za'ayi dan da fari ma a Adamawa yaso a ɗaura Auren Amma Daddy Bulamaa yace kar ya damu Zuwa Adamawa bazai taba zuma musu abu mai wahala ba after All hakkinta ne aje har gidan mahaifinta a amsa Auren ta,

Bayan ɗaurin Aure wanda ya tara jama'ar yankin garin da sukazo shaida wannan ɗaurin Aure ,Malam Balarabe mahaifin Hafsa 'ya shiga gida gurin yan uwansa da suka hallarci bikin da ba amarya domin sake gaisawa dasu,wata Innar Mama laure ce da tazo daga cikin garin katsina ta saka akayi mata magana dashi,

Cike da girmamawa yazo ya duka yace "inna usai gani,"

Ciike da kunmfar baki tace "ai Balarabe ba sai kayi mun mur mur da ido na munafukai ba naji komai,idan ba lalacewa ba ta yaya za'ace Hafsatu na Aure babu ita garin da ubanta yake,bana tunanin ko binciken kirki kayi akan ɗan nan saboda ƙwalama da ka saka a gaba tunda ance Malamine ɗiya masu kuɗi,To bari kaji ko gwamna Hafsatu Ta Aura Laure ce domin kuwa da bata raineta ba lokacin da uwarta ta mutu ta barta da ba'a Kai nan ba dan kilan ma da tabi uwarta,To ina san kasan Abu ɗaya da bazar Laure Hafsatu ke taka rawa. "

Da mamaki Malam balarabe 'ya kalli Inna kana yace "amma hala inna kin manta da dukkan ukubar da Laure tayiwa hafsa hala,duk wani cin kashi da azabtar da ita da tayi duk baki gani ba kin manta,To bari kiji na faɗa miki wani abu,duk abunda hafsa ta zama a rayuwa ƙaddarar tace ba tsarin Laure ba domin kuwa da ace Ta Laure ce da yarda taso da tuni Hafsa ta zama ƙaramar bazawara domin kowa yasan wanda tayi niyar Aurawa matsiyacine wanda baisan darajar mutum ba,zaman Ta a chan Adamawa kuwa Nine na saka domin Babu wanda yake da iko mun da ɗiya,idan kuma kuna san ganinta ne sai ku bari idan sunzo bankwana ita da mijinta sai kuyi domin da Allah ya tashi ɗagata bayan wata biyu a Nigeria zasu wuce ƙasa mai tsarki danyin rayuwarsu,idan kuma da mai saƙon da zai faɗa mata cikinku to 'ya bayar danni uban ɗiya zani Adamawa.

Tashi yayi dan barin gurin muryar Laure ta katse sa ta hanyar faɗin"kazata bamu san ubansa Dan fashi Bane,uwarsa kuma mai biye biye ce Dan da ta fara irga Aure sai da tayi goma,idan da ƙwadayi ai da wahala."

Murmushi Yayi yace"nine da godiya Laure sannan waɗannan da kike lissafi haka akansu su 'na zaba 'na bawa ɗiyata kiyi abunda zakiyi ita yarki da kike san Aurawa Dan mai gari gashi ai 'ya mata ciki 'ya gudu ya barta "

Bai jira cewarta ba ya bar gurin Dan Tafiya Adamawa,banbami da sumbatu Mama Laure ta ɗingayi tana zagin malam Balarabe wanda ko ta kanta baibi b inda 'yan uwanta suka dinga tayata suna tsinewa Balarabe da yarsa .

Jirgi Papa yayi ma Mahaifin Hafsa zuwa Adamawa wanda babu wani bata lokaci ya sauka a Adamawa wanda driver yana nan yana jiransa,inda 'ya nemi su kaisa nan suka ajesa wato gida Inna,koda aka ajesa Yayi mamakin ganin yan uwa na kusa da nesaa da suka masa kara ,tabbas ya yarda Laure ce Babbar mutum wadda ta ja katangar karfe tsakaanisa da yan uwansa ,chan ya haɗu da amaryar ɗiyarsa wadda dukkan wani nauyin gyarata Aunty shatuh ta dauka 'dan sai ana gobe daurin Auren ma ta koma gidan Innarta,karamci iya karamci Aunty shatuh ta nuna masu domin komai na hafsa ita ta daukesa ,

Dukkan wani kuɗi da ta samu tsakanin Innarta da mahaifinta ta raba su wanda da kyar suka karba, musamman ma inna da aka dauke mata karatun Muhammadu har ya gama,

Da rana dangin Abdallah sukazo 'dan tafiya da ita family house ɗinsu wanda nan zata fara zama kafun su wuce ita da mijinta,nasiha sosai mahaifinta yayi mata mai ratsa jiki,kuka sosai take yi haka zalika shima mahaifin nata wanda ya kasa riƙe hawayen da ke neman kwace masa,tabbas Aure yana kai mace ko ina amma baiyyi tunanin zai ɗauke hafsa da ƙasarta ta haihuwa ba.

***

Ya maganar gidansu Amaryaa Nadiya kumafa?

Tun a wajen gidan Dr Imam da Dr Umaimah zaka san ana bikin kuɗi a gida ,shige da fice shine abu n'a farko da zai faɗa maka Hakan ,yan uwa na kusa da nesa duk sunzo ciki kuwa harda su Fawza,Fawzan,Fawha wadanda suka baro karatunsu domin zuwa taya yan uwansu murna domin abun murna ne a yi masu yasan mutum biyu a gida ,

Bikine akayi gangariya n'a gani na faɗa wanda ya yaɗa kasa da ketarenta baki ɗaya,mahaifin Nadiya yazo amma cikin bakin daurin Aure wanda babu wanda ya nuna masa wani abu face karamci wanda babu daɗewa ya bar gurin domin zaren ba kalar yadin Bane domin kuwa yasani ya rasa Nadiya da mahmud har abada,

Gagarumun liyafar da aka haɗa wa amaren da angwayen an haɗa tane cikin gidan Dr Imam wanda aka haɗe da baby shower Na Jamaimah wadda bata samu wani liyafa ba na Aure 'dan haka itama aka tsantsarata cikin shiya irin ta amaren hakazalika Nameer wanda shima ya haɗe cikin shiga irinta Angwayen ,bada labari na yarda wannan taron Ya haɗu bata lokacin domin kuwa iya haduwa Ya hadu,abune akefa na sanannu a ƙasa ,media babu abunda take sai ihunsu dan kuwa abu ya ƙayattar musamman ta hanyar da baƙi suke samun ƙyaut ta ban mamaki wadda basu tsammanin samu 'dan kuwa kowa a AHALIN Ya saki bakin Aljihu .

Bayan taro Ya watse Nadiya suka fara tafiya da mijinta da Aunty shatuh da Affan ƙanin Dr Imam domin kaita gidan mijinta dake cikin garin Kaduna wanda ita dashi suka zabi gari for a Good change,cikin unguwar marafa,a yayinda Aka kai Hafsa sashe mijinta dake cikin Gidan iyayensa wanda aka gyara sosai duk da kuwa ba zama ne na daɗewa ba

Haka zalika ango da amaryarsa mai cikin wata ɗaya suka nufi gidansu domin sake rubuta soyayyarsu dake shirin zama tsakanin mutum uku.



Bari na kama hannayenku domin kaima sabbabin Auren nan ziyara.

Mu haɗu a page na gaba 'dan jin Ya zata kaya sannan ina farin cikin sanar daku sauranmu bai wuce kaɗan ba.

Kusha ruwa Lafiya.

Nice taku a kullum.

CHUCHUJAY ✍️

ummumahnoor...
AHALINA

(Siblings of different father's)

Book two in Aure uku series

By

CHUCHUJAY

Episode 6⃣1⃣◼6⃣2⃣

KADUNA NIGERIA.

Kebancewa tsakanin amarya da ango yanayine da ko wanne ma'uraci ke san kasancewa ,haka wannan rana da Dare keda matuƙar muhimmanci gurin Nadiya da Ahmed,

Bayan kasancewarsu su Kaɗai wani irin yanayi Nadiya ta tsinci kanta wanda bazata iya fasaltashi da menene ba amma tafi dangantashi da Alhini irin Na ko wacce amarya,

Zaune take kan katafaren gadonta jikinta sanye da less wanda yaci mayan ɗinki,dashi tazo jikinta wanda duk ya dameta amma tana tunanin wanka ta zama amarya mai zaƙewa domin kuwa ko angon bai shigo ba,

Tana wannan zaman ya shigo bakinsa dauke da sallama,saurin aje ledar hannunsa yayi yana mai faɗin"My Queen wannan lullubi bai maki zafi ba,"

Tsintar kanta tayi da duƙawa bisa jin kunyarsa a karo Na farko,fahimtar hakan ya sakashi murmusawa ya ƙarasa Inda take ya zauna ,hannunta ya kama kana ya saka hannu a hankali ya janye lullubin dake kanta wanda ya haɗa tare da ɗwankwalinta, madaidaicin gashinta wanda ya sha kitsone ya bayyana,hannunsa ya saka Ya ɗago fuskarta yana mai faɗin"tsarki ya tabbata ba ubangijin da ya yiki ya yini sannan ya malaka mun ke a matsayin matata,kissing hannunta yayi yace "bazan iya rayuwa babu ke ba Nadiya ke Alheri nace , Na maki Alƙwari idan Allah ya yarda bazan taba guje miki ba da lafiya ko akasin Haka,duk da ɗan Adam ajizine amma ina so kafun nayi maki laifi a nan gaba na nemi yafiyar yin haka,sannan na maki Alkwarin sanki a koda yaushe domin kuwa ina sanki ,zan yi duk iyakacin ƙokarina wajen ganin na zama namiji masanin addininsa domin anfanar da ke matata da kuma zuriar da zamu tara,ina so a daren yau ki bai hadin kai mu zama abu guda ɗaya akan tafarkin gaskiya,

Matsowa yayi daf da ita yana mai fadin"I've been dreaming To touch you,duk wani corner 'na jikinki ina san nayi marking ɗinsa ta hanyar baki hickeys wanda zai bada shaidar ke tawace,i want To make love To you a manner ɗin da ni dake bazamu taba mantawa dashi ba,give me that chance".

Wani irin soyayyarsa taji tana faman fusgarta,licking lips ɗinta tayi tace"ni matarkace ba sai ka tambaya ba Just have your ways"

Murmushi yayi yana mai saka hannu a waist ɗinta yace "na sani ina san ya zamana bani kaɗai na ji daɗin ba ,so nake duk da nasan This is going to be your first sex ya zamana kina mai faɗin"Baby more and trust Me ina da inch mai girma and im also a virgin"

Saurin saka hannu tayi a fuskarta saboda tsabar kunyar maganar da yayi,sau da dama akan mata kallan yar duniya saboda shes ambitious amma hakan bashine yake nufin itama ba little princess ɗin da mijinta zai ririta bace ayayin ita kuma take narke masa tana bukatar Ya shagwabata.

Kai tsaye yayi bathroom da ita wanda ta nema privacy Ya bata cos yasan she needs time,bayan fitowanta shima ya faɗa wanda tayi sauri waje kimtsa kanta cikin kayan bacci riga da wando silk farare,sake bawa jikinta ƙamshi tayi kana ta koma kan gadon ta zauna tana jiransa ,jim kaɗan kuwa sai gashi nan Ya fito da farin towel wanda yake deadly about To fall daga ƙugunsa,kallan shi ta fara daga kan faɗaɗan kirjinsa wanda gashi madaidaici Ya ƙwantawa luf zuwa ga lafaffen cikinsa wanda ke ɗauke da packs,ta sani ko a riga ka kallesa Ya ginu amma bata taba tunanin a zahiri idan Babu riga jikinsa ba haka yake,he looks yummy.

Gyaran murya yayi yana mai shafa wani serum a hannunsa ,saurin ɗauke idanunta tayi cike da kunya,ɗan tabe bakinsa yayi Ya murmusa yace"Gulma ,nasan kina san abunda kika gani ,Ya burgeki for real,well kar ki damu a daren yau zan mallaka miki kaina,sake kudundunewa tayi cikin bargo tana mai ƙaramun murmushi tare da jin kunyar kamata da yayi tana masa irin wannan kalan.

Bayan Ya gama shirinsa Ya ɗauko jallabiya Ash cikin kayansa Ya saka kana ta nufi gareta Ya janye Blanket din yace"yafi ki tashi muyi sallah mu godewa Mahaliccinmu then sai Na baki abinci kema ki bani".

A yarda ya gabatar da abunda addini Ya kunsarwa Ma'aurata Ya birgeta domin bata taba tunanin Ya samu ilimi haka ba,bayan idarwarsu Ya ciyar da ita duk da nuƙunuƙu ɗin da take masa kana shima yaci ,kafun tayi Aune ya suretta Ya kai gadon su,a hankali ya Fara undressing ɗinta inda within a moment naked jikinta ya bayyanar masa,neckborn ɗinta yayi licking da tip din harshensa inda lokaci ɗaya ta bada wani irin sound,hannunsa yasa Ya kashe dim light ɗin dake ɗakin a yayin da Ya saka bakinsa dai dai kunnenta yace cikin raɗa"i never had sex When i was a christian,be my first baby,kafun tace wani abu yayi capturing lips ɗinta inda ya ɗauketa zuwa duniyar da shine mutum na farko da ya fara kaita kuma tana fata ya zama mutum na karshe.

ADAMAWA STATE NIGERIA.

Bangaren Ango Abdallah da amaryarsa kuwa a ranar da aka kaita bai samu shiga sashensa ba duk kuwa zumuɗin da yake kan hafsa saboda yan uwanta da sukazo ya basu damar zama tare da ita tunda masu nisa ne wasu ma baya tunanin zasu ƙara dawowa daga wannan zuwan ,washe gari kuwa bayan kowa ya watse ya ƙira Fawza sashen Nameer inda nan ya kwana,kallo ɗaya tayi masa tace "brother ka gaji da haɗuwa,kallan kansa ya sake yi a mudubi,sanye yake cikin Brown Kaftan na yadi mai kyau da tsada,murmushi yayi yana mai gyara hular kansa yace "kin tabbata ko cos ina san matana idan ta kalleni ya zamana tana tuna irin kyau ɗin da nayi mata,"

Alamu Fauza tayi da hannu tace "Hamma Abdallah da gaske nake you look Good kasan 'fa gidannan daga ni a kyau sai kai,nima ɗin da Kaɗan 'na fika kyau,."

Dariya ya saka yana mai nuna ta da yatsa yace "wannan yarinyar Allah ya shirya mun ke"

Ledar da ta shigo da ita ta miƙa masa wadda take ɗauke da kazar amarya da fresh milk,ƙarba yayi yana Faɗaɗa murmushinsa yace"ƙanwa ta zama abokin yaya,kinsan ni bana abokai Bane and bana ganin amfanin kawo wani aboki ya rakani ɗakin matana"

Murmushi tayi tace"kaima dai Hamma kasan 'dan Hamma Umar baya nan dama dai shine right hand man ɗinka and da mukayi waya jiya yace 'na wakilcesa wanda gashi nan inayi without complaining,"Dan tabe baki yayi yace"zanje Mecca ɗin 'nan Ai sannan zai amsa query ɗin dalilin soyayya da ƙanwata,kar yaga tun yarinta muka tashi idan Abu ya haɗa da AHALINA bana wasa. "

Kunya ce ta kamata tayi saurin Juyawa da gudu Dan bata taba tunanin Abdallah yasan tana soyayya da Abokinsa Umar ba.

Dariya yasa ganin abunda tayi kana ya nufi gurin sanyi idaniyarsa,koda ya isa ƙofar Falonsa a buɗe yake dan haka yana shiga 'ya kulle sannan ya rage haske 'ya nufi ɗakinsa,a kashe haske yake dan haka ya kunna mara haske sosai yana mai faɗin"Noor kina in haka?"

Kan gado 'ya hangota a kudundune , da sauri 'ya haura yana mai sake kiran sunanta,tana jinsa amma ta kasa amsa masa saboda Azabar dake cinta wanda ita ɗaya tasan mai take ji,ɗagota yayi cikin ruɗewa yace "mene 'ya faru ,"

Hannunsa still naka mararta,wata irin shagwabe masa tayi tace "ni marane ke ciwo,im having cramp"

Cike da kulawa yace "Subhanallah shine baki kirani kin faɗa mun ba kika dawo kika kwanta da ciwo,?"cikin muryar dake ɗauke da sigar irinta Mai ciwo tace "to ni ai wayana 'ya mutu kuma ban iya sawa a charge ba,and dama inayi na saba"

Cike da kiɗimewa 'na ganin yarda take jin ciwan ya ƙwantar da ita yana mai faɗin bari na kira mami,da saurinsa 'ya nufi sashenta yazo da ita,

Injection Mami ta bata tana mai faɗin "mestral cramp ne amma tunda na bata allurar nan zata samu relief ,"

Sauke wani gwauran numfashi yayi yana mai faɗin Alhamdulillah,saurin takawa gareta yayi yana mai faɗin sannu Noor,

Cike da kunyar kasancewar Mami a gurin ya sakata duƙar da kai,murmushi mami Tayi tace "kai ne dai maganin matsalar cos mostly yana tafiya ne da sexual intercourse ,wanda sadly a yanzu period 'ya bata maka"

Wata irin kunya ce ta kamasu baki ɗaya kamar su nutse kar ma ace hafsa ,tasowa Abdallah yayi ganin zata sake magana yace ,Mami pleasse.

Murmushi tayi tace"im here a matsayin doctor ɗinku ba maman ku ba ,"

Ganin yarda hafsa ta shiga awkwrd position ya Sakata basu guri still tana mai sake tsoknarsu,tana fita hafsa ta jawo bargon dake gefenta ta lullube baki ɗaya har kanta,

Dariya Abdallah yasa 'ya tako inda take 'ya zauna kusa da ita yana mai fadin "love kinji abunda Mami tace ba,we need to became one idan muna so ciwan nan naki 'ya warke ."Sake dunƙule kanta tayi tace"Ni ni kabari Babe bana so"

Dariya yasa yace"ya kikeso na daina magana bayan ina faɗa maki waraka ga cutarki,kinsan ni idan abu akankine babu extent ɗin da bazani ba cos kece ni Nine ke,"

"Tashi 'yayi ya rage kayan jikinsa ba tare da wani disappointment ba domin dama ya saka aransa koda yazowa Hafsa ta nuna tsoran mu'amala dashi ta hanyar saduwa zai lalabata kamar kwai 'ya tarairayeta cikin so da ƙauna.

Kan gadon ya faɗa ya kwanta gefenta bargon yayi lifting 'ya jawota jikinsa,Babu musu wannan karan ta lafe kanta a kirjinsa,cikin wani irin yanayi tace "kayi hakuri Dee ,first night ɗinmu had to come with My period,a hankali ya shafa kanta yace "insha Allahu muna da rayuwa mai tsayi a tare ,nasan kuma yau ba ranar da zan sameki Bane amma ki sani,nazama ke kin zama ni and im ready to wait for you,"

Wani irin sansa da kaunarsa taji yana ratsa ko wanne sashe na jikinta ,a hankali yace "i love you to the Moon And back"

Kissing goshinta yayi yace "i extremely love you too wifey and i cant wait to show you that".

Cikinta ne yayi kugi wanda yake nuna bataci abinci ba,chak 'ya ɗauketa domin bata abinci ,batayi masa gardama ba cos She's stabbing like hell dama,sai da ya tabbata taci ta ƙoshi kafun ya sureta kamar yarda ya ɗaukota 'ya mayar kan gado,zaunar da ita yayi Dan cikinta 'ya sauka,'ya juya dan sauka ta kamo hannunsa,juyowa yayi ya saka idanunsa cikin nata kafun yace wani abu ta jawosa tayi capturing lips ɗinsa cikin rashin tsammani,murmushi yayi 'yana mai mata responding cike da passion wanda ke sake tunatar masu adadin san da sukema juna,

Da haka yayi cuddling ɗinta har bacci mai daɗin gaske yayi awan gaba dasu wandaa Babu ɗayansu da 'ya taba samun irinsa ba.



Iftar MUBARAK

CHUCHUJAY ✍️
AHALINA

(Siblings of different fathers)

Book two in Aure uku series

By

CHUCHUJAY ✍️

FINALE

Baki ɗaya kwanciyar Hankalin da suke nema sun samu domin kuwa kowa a gidansa idan ka kalla suna zaune ne cikin zaman lafiya mai daɗi,

Idan kana kallan rayuwarsu bazakace akwai wani abu behind it ba karma ace yarda Haɗin kai na AHALIN yake, idan ba wai an faɗa maka ba bazaka taba cewa wai yaran Umaimah Shida kowa da ubansa ba,AURE UKU da tayi ta yarda babu daɗi amma ta gamsu da cewa duk wani abu da ubangiji 'ya tsara maka shine gaskiya,babu wani abu bayansa sannan baya taba ɗora maka abu wanda yafi ƙarfin kanka,sannan every failure' is a blessing domin kuwa mutanen da suke jiran ganin failure' na Aurenta sunfi masu fatan ya ɗore.

Taro ne suka tsantsara na Family bayan Wata guda da Auren Su Nadiya duba da yanayi na kowa zai tafi,Yan uku zasu koma makaranta Abdallah kuma da matarsa Adamawa domin Gaida iyayen Hafsa daga nan kuma zasu wuce mecca domin Aikinsa yayin da Nameer Baba Bulama ya yanke masu ranar zuwa Cameron wanda tafiyace yake san suyi baki ɗaya domin kwantarwa da iyayen Jamaimah hankali akan tana cikin hannu mai kyau,ille kuwa ranar saturday da 'ya zamana weekend suka dugunzum wajen tafiya masarautar.

Tun da jirginsu 'ya tashi kirjin Jamaimah ke dukan tara tara wanda Nameer 'ya kula da yanayinta,cike da kulawa 'ya kama hannunta yana mai shafa hannunta a hankali cikin sigar lallashi,ajiyar zuciya tayi tace "babe im scared bansan 'ta inda xan fara da iyayena ba,sake rubbing hannunta yayi yace komai zai daidaita ,insha Allahu babu wata babbar matsala,kar ki manta da Gradnpa Bulama a wannan tafiyar da Abuh da Papa da Mami da ummuh ga nan su Abdallah, su kansu zasu san guduwanki mai amfani ne after all ga ɗan Abbah a ciki ,

Tsintar kanta tayi da murmusawa tana mai faɗin"stop joking a moment ɗin nan abunda nayi musu ba dai dai bane ba".

Kaɗa kai yayi yace"na gamsu ba dai dai bane ba amma Abun daɗine da 'ya zamana kin dakatar dasu daga aikata ba dai dai ba domin kuwa da kin zauna zasuyi miki Aure ne wanda haramun ne saboda kina da Aurena wanda koda babu iyayen mu halsataccene duk da wata mazhabar kance babu aynayin waliyyai bai hallarta ba amma a musulunce munsan ya hallarta tunda an shaida kin karbi sadaki an daura wanda dama Aure shaidu yake buƙata ,dan haka ki kwantar da hankalinki komai zaizo da sauki da ikon Allah."

A haka Nameer 'ya ringa assuring Jamaimah har suka isa kasar,already dama kafun isar su Granpa Bulama ya saka an sanar da sarki RAIS maganar zuwansa ta hanyar connection,duk da babu abunda 'ya taba haɗasu amma mahaifin Jamaimah ya saka aka shirya tarbasu tunda shi din sanannan mutum ne wanda zuwansa gurin mutum bazai taba zama sharri ba ,

Koda suka iso sarkin da kansa 'ya Aika a daukosa a airport',kallan Jamaimah kawai Drivern da aka aika 'ya ɗaukosun yake dan bazai taba manta fuskarta ba duk da kuwa baƙone shi,fuskarta tayi mutuƙar yawo domin mahaifinta lokacin batanta 'ya saka Milliyan biyu a kuɗin Nigeria ga duk wanda 'ya kawota,kasar ta dauki kara akan wannan offer da sarki rais 'ya bada hakazalika matasa sukayi chaa wajen neman Jamaimah , tashin hankali kuwa babu irin wanda harith bai shiga ba domin wannan gangancin shi Jamaimah tayiwa dan haka har a ranar bai daina nemanta ba a duk inda tunaninsa 'ya kai masa zataje,karshe kuwa da yayi yinkurin kashe Sarki Aka ɗauresa.

Koda suka isa masarautar babban sashen dake daukar baki akayi dasu,gurin 'ya gaji da haɗuwa da girma ,kafun isowarsu kuwa makil aka cika ɗakin da kayan cima na alfarma domin tarbar su,basu dade da zuwa ba sarkin 'ya bayyana domin girmama bakin nasa,fadawa suka fara shigowa kana Sarki Rais a baya,

Koda ya shigo idanunsa basu sauka akan kowa ba sai batacciyar ɗiyarsa,wani irin abune 'ya daki zuciyarsa wanda bazai iya fasalta menene ba domin kuwa yanayin rabon sa dashi tun lokacin da aka sanar masa da sarauniyarsa ta haifi Jamaimah,

Take ruwa 'ya kawo a idanunsa,a hankali Jamaimah ta tashi ta nufi garesa tana mai fashewa da kuka,ganin haka yasa fadawan darewa domin basu guri,kan gwiwowinta ta zube tasaka kuka sosai,saurin goge ƙwallar dake kokarin kunyatasa yayi ya duƙa 'ya Kamota 'ya rungumeta,kafun kace mene Mahaifiyarta tazo gurin wadda tun tafiyar Jamaimah bata kuma lafiya ba amma da labarin Zuwan Jamaimah ta risketa Babu shiri ta taso tazo,tana kuwa shigowa bata ma kula da mutanen dake gurin ba tace"yarinyata,jin muryar ta yasa Jamaimah raba jikinta dana mahaifinta ta nufeta tana mai faɗin "Uwata"

Wani irin kuka mahaifiyar tata ta saka kana ta rungumeta,

Kafun kace mene maganar dawowar Jamaimah ya zagaye gari kamar bonfire.

Zama sukayi domin tattaunawa da sakewa iyalan Bulama godiya domin kuwa dawo musu da Jamaimah da sukayi yafi masu masarautarsu da abunda ke cikinta.

Cike da nutsuwa Grandpa Bulama 'yayi musu bayanin duk wani abu da 'ya faru kama daga Auresu a china har izuwa zuwanta NIGERIA,hakuri 'ya sake basu da cewa,munyi maku ba dai dai ba damu sanar daku kai tsaye ba lokacin da tazo garemu duk da kuwa tazo da halayya mafi munin da Babu wanda zaiso ɗiyarsa mace ta kassance dashi dan haka muka hukunta su ta hanyar watsar dasu su gyara tunda Auren da sukayi Babu manyansu shine babban Laifi,to Alhamdulillah a yanzu ɗiyarku watace daban domin kuwa an samu chanji sosai a yarda tazo yanzu abu guda 'ya rage wanda shine kuyi hakuri ku karbi Aurenta domin kuwa a tare da ita akwai rabon shi Nameer din,gashi nan bayan wautar da suka aikata bashi da wani aibu sannan ba wai dan yana jikana Bane kuje kuyi bincike idan kukaga halayyarsa ta banza to ni da kaina zan saka 'ya sauwakewa ita Jamaimah ɗin,a yanzu kuwa gata nan yarda kukace haka za'ayi domin hakkin ku ne.

A yarda sukayi tunani iyayen Jamaimah zasu dauki abun ba haka Bane domin kuwa sosai suka nuna farin cikinsu da 'ya zamana Jamaimah ta faɗa hannunsu sannan suka

Nuna mutuƙar dana sani wajen hanyar da suka ɗauka na nuna mata soyayyar banza da izzar mulki wanda 'ya so kaita ga hallaka.

Bayan sadda zumunci wanda 'ya wakana tsakanin AHALIN biyu iyayen, da samun daidaituwa iyaye Nameer suka wuce suka barshi nan da matarsa akan su kwana biyu inyaso idan zasu koma NIGERIA iyayenta su bisu suga inda ɗiyarsu take.

Bayan komawarsu gida tafiyar Abdallah da matarsa Hafsa ta kama zuwa saudiyya inda 'ya saka ranar zuwa Katsina domin gaida iyayenta duk da kuwa mahaifinta yace kar 'ya damu amma ganin chanchantar hakan yaga 'ya kamata ace sunje ɗin,

Yan uku suka fara wucewa Newyork kana Abdallah da hafsa da Aunty shatuh suka tafi garinsu Hafsa,

Sanin zuwansu

Please Login or Register in order to submit comment