Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya rayuwa ba sai da ke, da wane amon murya kike so na faɗa miki ina son ki ki yarda? Da wane martani kike so in fahimtar da ke irin son ki da kaunarki da nake yi ki yarda? SALIMAH ni kaina ban taɓa ji ko a labari akwai irin son da nake miki ba Allah ne shaidata bayan mahaifana ba na kaunar wata halitta sai ke. Da a ce ɗan adam yana iya tsaga kirjinsa ya nuna so a yarda da shi da na buɗe miki kirjina da kin duba cikin zuciyata ki ga yadda son ki ya cika zuciyata ko da ba za ki so ni ba idan kin gani za ki yarda da ɗimbin makahon son da nake miki wallahi ba na ji, ba na gani, bana gane rashin ki masifa ne a wajena sai kin yi nesa da ni, na yarda na amince ki koma gidana ki mini duk azabar da za ki gasa mini na yarda ki mini fiye da abubuwan da kike mini, zan ɗauki komai zan jure komai in har zan rayu da ke a inuwa ɗaya, wallahi, wallahi, wallahi ba zan taɓa butulcewa ba, ba zan taɓa haɗa ki da wata mace ba idan kika dawo gare ni ba zan taɓa miki kishiya ba ke kaɗai za ki rayu ki yi yadda kike so da ni, ni naki ne zuciyata taki ce SALIMAH" Ya kai karshen maganar rauninsa yana bayyana a cikin nuryarsa.


Wani uban tsaki ta doka, wanda ya sa hawayen da suke makale a kwarmin idansa gangarowa, wannan tsakin ya tabbatar da maganganunsa tamar busar sarewa ya yi wato sun shiga ta kunnenta na hagu sun bi ta kunnen dama ko alamar tasiri kalamansa basu yi ba. FAROUQ wani tausayin abokin nasa ya kara kama shi, ko shi da yake namiji maganganun ABBAS sun shige shi amma ita SALIMAH da ake yi wa kalaman sannan ita ce mace kuma an san mata da tausayi kuma zuciyarsu tana da rauni a kalla ko da bata amince za ta koma ba ta masa wata kalma mai taushi.


"SALIMAH" Ya furta a daidai lokacin da ya durkusa gwiwoyinsa a kasa yana durkushe a gabanta, bai yi la'akari da farin yadin jikinsa ba shi damuwarsa ma duk so da yake mata bata gaskata shi ba ya ma gabanta kwata-kwata.


"Ya kike so a yi, mai kike so in yi ko kina so in ɗayo miki fatar jikina ki yarda, ko akwai wani ɓangare na jikina ko koda ta kike so zan iya bari a cire guda ɗaya ko da kare kika ce a dasawa zan yarda ko da hakan zai zama siyar mutuwata ai a dalilin so ne son ma naki SALIMAH...


"Kai ya isa haka ABBAS mai ya sa kake kalami a inda ba za a tausaya maka ba? Wannan da kake gani ko ranka za ka cira ka bata ba za ta yarda ba kai alamunta sun nuna ko mutuwa za ka yi ba za ta tausaya maka ba, na lura mugun tsanar da ta yi maka ba iya kai take wa ba talaucin da kake ciki ne bata so da a ce kana da ɗimbin dukiya ba sai ka ka roke ta ba, dukiya ce kawai a ranta duniya ce kawai a gabanta ka daina ɓata gishirinka a dahuwar kaho, ka zo mu tafi ka roki Allah ya cire maka son ta ka samu mai kaunarka ka yi sabuwar rayuwa ka manta da ita...

."Ita nake kauna FAROUQ"

. Wani haushin su ne da ya turnuke SALIMAH ya sa ta kasa magana sun mayar da abu tamkar a wasan kwaikwayo ko littafin hausa, sai wani kalaman soyayya yake tamkar wani romeo, ita fa ko kalmar so bata damu sosai a furta mata ba ta fi damuwa ta ji dumus wato masu gidan rana, kuɗi da ake kira kare kukan ka, kuɗi aljannar duniya mai kuɗi ya huta sai yake shagalinsa.

. FAROUQ kuwa jin furucin da abokin nasa ya yi sai ya juya musu baya, don ya gaji da ganin abubuwan takaicin da ABBAS yake a kan so ana wulakanta shi. SALIMAH kuwa ganinsa durkushe a gabanta sai wata tsanarsa take tsarga mata zuciya musamman in ta tuno da maganar Umma cewa zuwansa wajenta barazana ne ga zuwan manyan Alhazan zawarawan ta, zuwansa zai zama shamaki ga cikar burinta hakan ya sa ta ji gwara ta masa hukunci.


"Dan Allah SALIMAH... Maganar ABBAS ta makale ne a daidai lokacin da SALIMAH ta ɗaga bokitin ruwan tsarin nan ta sheka masa tun daga saman hular kansa, har bayansa jigilif ya jike, FAROUQ da sauri ga juyo jin zubar ruwa sannan jin wurin ya ɗumame da wari, ya san kafin SALIMAH ta fito kamshi wurin yake amma tun da ta zo yake jin wani wari tunaninsa ko kwata ake kwashewa a wani wajen amma yanzu kuma sai ya ji warina dab da su hakan ya sa ya gane cewa ruwan wannan ne dama yake warin wanda ko kaɗan bai kawo a ransa cewa ruwa ne ma a bokintin hannunta ba.


"Wannan kaɗan kenan daga abubuwan da za ka fuskanta matukar ka ci gaba da zuwa kofar gidanmu, ba za ka hana ni rawar gaban hantsi ba, nan gaba zan iya watsa maka tafashashshan ruwan zafi ka ga idan fatar jikinka ta silsilge ka hakura da zuwa in kuma baka daddara ba akwai wasu abubuwan da na tanadar maka har sai ka janye kafarka ta fukara'u a kofar gidan nan" Lokacin da ta wasa masa ruwan sai ya ji wani sanyi ne da ruwan tamkar ruwan randa ko na firji, ga wani wari da ruwan yake har fuskarsa ruwan ya wanke, jikinsa jigilif babu inda ruwan bai taɓa ba a take wani kaikayi ya fara masa sallama a fatarsa. Duk wannan batutuwan da take masa ba ya ma fahimta, tsaye ya mike yana kallon kwayar idanunta bai ga salama ko tausayi ko rangwame daga idanunta ba. Laɓensa na kasa ya cije da hakoransa an kai gaɓar da bakinsa ya kasa furta komai da a ce wani ne ya masa haka ba SALIMAH ba da sai ya gwammace kiɗa da karatu.


"Ke wace irin wawiya ce, mai ya sa kika ɗauki ɗan adam ba a bakin komai ba, kike wulakanta ɗan adam, bayan ubangijinmu ma ya faɗa a littafinsa mai tsarki cewa ( Wakakadi karramana bani adama,,, hakika mun karrama ɗan adam)" FAROUQ ya faɗa a kufule yana jin tamkar ya hau ta da duka.


"Yanzu zan nuna maka wawiya ce ni" Ta ce tana juyawa wajen kwatar gidansu inda aka yi wa makwararan wanke-wanke hanya ruwan yake taruwa a kwatar simintin da aka yi bokitin ta saka ta kwalfo ruwan ta nufo su a wanna lokacin su duka za ta watsawa don shi ma abokin hakan ya zama izna gare shi nan gaba ba zai sake yarda ya rako shi ba. Tana ɗagawa za ta fara shekawa ABBAS FAROUQ ya yi saurin ɗaga hannu zai wanka mata mari, cikin sauri ABBAS ya saka hannu ya rike masa hannun nasa, ba wai don abin da ta yi bata cancanci mari ba sai dai ba ya so a taɓa lafiyarta gani yake da a mare ta gwara shi a mare shi zai fi jin saukin abin a ransa.

."Da ka bar shi ya mararwa kansa bala'i wallahi sai na saka an kulleka har igiya ta yi saura, ba kai kaɗai abin zai shafa ba har danginka, kuma in kara gani wani ya zo wajen na" Ta ce tana nuna FAROUQ da yatsa tare da shekar da ruwan kwatar a waje ta yi jifa da bokitin ta juya abin ta tana dab da shigewa gidan ABBAS ya ce


"SALIMAH" Tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba.


"Idan har hakan zai sa ki farinciki na yarda na amince ba zan sake zuwa ba na zaɓi na rayu da kuncin rashinki ke ki yi farin ciki"

."Hahahaha wa ya faɗa maka barno gabas take, ai in ka ji mutum yana cewa ba zai iya ba bai kama shi bane ka ji uwar bari" Ta ce a zuciyarta wani daɗi yana baibayeta ganin ta yi galaba a kansa ashe akwai barazanar da za ta masa ya kyale ta.


A fili kuma sai ta ce


"Naka ya rage ABBAS za ka iya cigaba da zuwa ni kuma ba zan gaji da maka hukunci ba, kuma gobe za mu zo mu kwashe kayanmu daga wannan gidan kaima ka huta da biyan kuɗin haya" Tana gama faɗa ta juya.

"Za ki yi da na sani wata rana, za ki dawo ga ABBAS a lokacin da ya miki nisan da sai dai ki hango keyarsa daga nesa, yadda kika wulakanta shi na tabbatar Allah ba zai barki haka ba, yadda kika raina matsayi da samunsa na tabbatar akwai lokaci yana zuwa ki rubuta ki ajiye za ki ce dama FAROUQ ya faɗa mini indai auren mai kuɗi ne, auren jari, auren da ba don Allah ba ga wurin nan wasu masu kuɗin suna da kirki da duk kyawawan abubuwa tun da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba amma ke saboda abin da kika yi wa ABBAS sai Allah ya jarabce ki! " FAROUQ ya ce cikin ɗaga murya dama da ta juya ba tafiya ta yi ba sai da ta gama ji tsaf. Dogon tsaki ta ja ta ce.


."Bakin ka ya sari kashi, kuma mugun fatanka ya koma maka, babu abin da zan gani, sai dai ya kare a kan ka" Bata jira cewarsu ba ta shige gida.

Har ta ɓace wa ganin ABBAS amma bai ɗauke idanunsa daga wurin ba tamkar dai zai ganta haka ya kurawa wajen ido. A hankali FAROUQ ya yi taku ɗaya biyu ya dafa kafaɗarsa ya ce

."Abokina" Ya ce cikin tausayawa ABBAS ɗin. Ya san ba laifinsa bane so abu ne da yake cikin zuciya idanu ba ya ganinsa bare hannu ya taɓa shi.


ABBAS kawai juyowa ya yi ya rungume FAROUQ duk da jikinsa a jike kuma yana warin ruwan tsarin da ta watsa masa amma bai ji tsantsani ba, yana jin irin yadda kirjinsa yake bugu da sauri da sauri.

."Ka yi hakuri ka ji, idan so cuta ne hakuri magani ne" Kai kawai ABBAS ya gyaɗa masa saboda ya ma rasa bakin magana ba ya gane komai kuma ba ya fahimtar komai. Da lallashi FAROUQ ya saka suka hau machine ɗin suka tafi. Da sallama suka shiga gidan Mama inda ta shiga kallon yadda ABBAS ɗin yake a jike.

"SALIMAH ce ko?" Mama ta jefa musu tambayar don ta san ita ce kaɗai za ta aikata wannan aikin. Shi dai ABBAS bai ce komai ba, FAROUQ ne ya bata amsa amma bai faɗa mata yadda suka yi ba ya dai ce mata ta ce ba a ta koma ba gobe za su zo su ɗauki kaya.

"Allah kawo su lafiya, ya sa haka ne ya fi alkairi' Mama ta ce tana jin ciwon wulakanta mata ɗa da SALIMAH take.

ABBAS ɗakinsa ya shiga ya kwanta rubda ciki, jinsa yake tamkar ba shi da lafiya, ga jikinsa ma ya ɗau zafi jin sa yake tamkar a wata duniya ta da ban.

"ABBAS baka jin yadda kake warin ruwan nan?"

"Ba na jin warin abu ɗaya na sani ina jin kamshi"

"Kamshi fa ka ce?" FAROUQ ya tambaya da mamaki.

"Ai tun da SALIMAH ce ta watsa mini ba zan ji warinsa ba, kuma zuciyata bata ganin laifinta sannan kuma har abada ba zan daina sonta ba" Ya ce har lokacin yana nan kwance rubda ciki.

"To majnun na Laila ai sai ka tashi ka je ka yi wanka ka cire jikakken kayan nan, ni na tafi sai da safe" Bai jira cewarsa ba ya fita daga ɗakin ya wa Mama sallama ya tafi. Mamar ce ta shiga ɗakin take masa nasiha dakyar ta shawo kansa ya yi wankan ga zazzaɓi mai zafi ya rufe shi magani ta bashi ta rufe shi sai numfarfashi yake.


Washe gari da yamma Mama tana waje makwarara ta rike ABBAS ɗin da yake ta kelaya amai, da yake da zazzaɓin ya kwana ga ciwon kai mai tsanani hakan ya sa da safe ta kira FAROUQ suka je asibiti magunguna allurori da drip aka rubuto masa, wani abokin su FAROUQ ya kira ya zo gida ya saka masa drip ɗin bayan ya masa allurorin. Bayan an cire ne kuma ya ce zai yi amai Mama ta fito da shi da yake yanzu su kaɗai ne a gidan FAROUQ ya tafi.

Bayan ya gama aman ne ya zauna a kan wani ɗan dakali da yake tsakar gidan, Mama sai kallonsa take da tausayawa, suna cikin wannan halin ne suka tsinkayi muryar ana sallama.

"SALIMAH ce Mama" ABBAS ya ce yana tashi tsaye yana faɗa jin muryar SALIMAH tana ɗaya daga cikin masu sallamar duk da bai ganta ba amma ba zai kasa gane muryarta ba amon muryarta yana ɗaya daga cikin sautuka masu muhimmanci a rayuwarsa. Mama hannu ya kai ta rike shi ganin yana karkarwa kuma duk ya ruɗe ga jikinsa ba karfi, sallamar ta amsa tana jin wani ɗaci a ranta jin ya ce SALIMAH ce.

Cikin gidan suka shigo, su biyu ne, ita da wata kawarta ƴar unguwarsu wacce kusan shekara uku da mutuwar aurenta, ita ma bata yi auren ba har yanzu. Suna wani gani-gani suka shigo gidan su duka suna taunar cingam tana kas-kas cike da rashin kamun kai mayafin nan sakale a kafaɗunsu ko arzikin yafawa bai samu ba.


"Mamar ABBAS ya kike?" SALIMAH ta ce cike da shekiyanci. Shi kuwa garau ya mata da idanu yana kallonta har ba ya son ya kiftawa ya zama tamkar wani zararre, gani yake tamkar yau ne rana ta karshe da zai sake ganinta a rayuwarsa tun da ya yarda ba zai sake zuwa gidansu ba ita kuma ba za ta dawo ba.

"Ina lafiya" Mama ta bata amsa cike da gatsali kamar yadda ta yi don Mama ji take ta tsani yarinyar nan yanzu ma bata so ta shigo mata gida ba za ta fama wa ABBAS mikin ciwon sonta da ta tabbatar ko jinyar nan da ya kwanta ita ce sila.

"Mukullin akurkin kajin can za a bamu za mu kwashe kayanmu" Kawar tata mai suna RUKY ta faɗa tana yi wa Mama kallon up and down.

Ko kala Mama bata ce ba ta ja ABBAS yana togewa amma a haka ta nufi ɗakinsa da shi, sai waiwayenta yake, Mama tana zaunar da shi ya yunkura zai tashi wata harara ta zabga masa da ta sa ya koma ya kwanta a katifar dama ba karfin jikinsa yake ji ba. Mukullin ta ɗauka ya fita daga kofar ɗakin ta tsaya ta jefa musu ta koma ɗakin ABBAS yana jin lokacin da suka fice idanunsa a rufe yana jin yadda bugun zuciyarsa yake bugawa sosai.


Da motar ɗaukan kaya suka je da maza uku suka kwashe kayan tas don sauran kayan ABBAS ma a nan aka watsar masa su suna bi ta kai suna wucewa, hatta ledar tsakar ɗakin sai da suka naɗe kayan nasa a dandamalin kasa suka ajiye, da suka gama suka rufe musu gidan. Motar kayan tana biye da napep ɗin da su SALIMAH suke ciki, a kofar gidan Mama suka tsaya, ita da RUKY dai suka shiga da sallama suna wani yatsina. Mama da ta fito daga ɗakin ABBAS jin sallamarsu bayan ta amsa sallamar kafin ta yi magana SALIMAH ta cillo mukullin suka juya suka fice daga gidan. Sosai Mama ta jinjina rashin tarbiya da rashin girmama na gaba tabbas in ba kaddara ba ma babu abin da zai sa ABBAS ya auri SALIMAH don ko hanya basu haɗa ba ya bata rata a komai na daga nagartar tarbiya.


ABBAS da yake cikin bargon da Mama ta rufe shi yana jin karan dirin tsayuwar motar da shigowar su cikin gidan da kuma fitarsu, sannan ya ji lokacin da motar da napep ɗin suka tashi idanunsa kawai ya runtse yana jin wani zafi a ruhinsa.


SALIMAH basu yi masauki ba sai a ƴan kafintoci, in da ABBAS yake aiki saboda rashin mutunci wai a can za ta siyar da kayan haka suka je aka sauke kaya aka yi ciniki aka biya su, gida suka karasa ta sauke tarkace da sauran kayan kicin ɗinta ta sallami masu motar da napep ɗin bayan an shigar mata da kayan gida.


Dubu biyar ta ba RUKY a cikin kuɗin sauran kuma ta ba Umma ta ajiye bayan ta ɗauki dubu ashirin don har kujerun ta siyar.


"Yo ajiyar mai za a yi ke da idan kika fara samun kuɗin sai mun rasa yadda za mu yi da su, ai kawai mu yi cefanen kayan daɗi mi fara wankin ciki tun yanzu, ki ɗauki wani abun ki yi ɗinkunan kafin na kece raini ya zo wato na zawarawa" Cewar Umma.


09013181851



KU MATSO DOMIN JIN DADDAƊAN LABARI
💃💃💃💃💃💃💃💃
. ZAN CIKAWA KOWANE MUTUM ƊAYA DUBU GOMA 1OK

Shin kin taɓa jin labarin 52U? Yadda mutane suke register da cin moriyarsa, da dala 21 ake yi $21 kimanin 35k. Duk wacce za ta yi register a team ɗina zan cika mata dubu goma 1OK ta kawo 25k sannan duk wata zan ke bata 15k tsawon wata 3 idan acc ɗinta ya cika wata shida zai buɗe sai ta cigaba da kwashe kuɗaɗenta.

Mutum 2O nake nema kar ku bari damar nan ta wuce ku ki mini magana a PC 09013181851

[1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA*



NA


MAMAN AFRAH


*GARGAGAƊI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.


SADAUKARWA

Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.



PAGE 6



*ZARIYA*

*Unguwar Gwalagwaji*


Kwance take a kan tsohuwar tabarmar wacce ta shimfiɗa musu zannuwa guda biyu, SABEER wanda ya ɗora kansa a jikinta duk ya takura saboda fitsarin da ya yi ɗan yalolon zanin da ta rufe su ta cire daga jikinta ta rufa masa, a haka bacci ya yi awon gaba da ita kasancewar ayyukan da ta yi ta gaji. Hajiya Rayyanatu wacce ta nufo ɗakin nasu da sanyin safiya ɗauke da ruwa a jug ta shigo ɗakin tana jan wani tsaki tare da toshe hanci, ruwan ta ɗaga ta sheke musu a jikinsu a gigice suka falka SABEER yana sakin kuka da sauri ta ja shi jikinta ta rungume shi tare da jijjiga shi alamar rarrashi duk da yake in da sabo ya ci a ce sun saba don kullum ruwan shi ne abin da ake tashin su da shi daga bacci sai dai hakan ya ki zama sabo kasancewar mai bacci ba ya son a zuba masa ruwa hakan yana zuwar wa mutum a bazata kuma duk wanda yake da ikon tsawatarwa kan cewa kar a zuba masa ruwa ko da ba a bacci bane zai tsawatar amma a inda yake da iko ba kamar su ba da basu da kataɓus maraici ne silar komai mutuwa mai yankan kauna da yanke jin daɗin duniya a lokacin da ba a zata ba, kuma ba a tsammata ba mai raba ɗa da mahaifi ta musu shigar sauri ta yanke musu rayuwa da mahaifansu a lokacin da suka fi bukatarsu a lokacin da suka sakankance suna rayuwar da basu kawo rabuwa da juna ba.

Sai dai shi tsari na ɗan adam da ban yake tsarin ubangiji na da ban yake, a lokacin da kake lissafin sherakara goma za ka yi kaza kai baka san cewa saura minti goma ka bar duniyar ba Allah ya bar wa kansa sanin wannan ya ɓoye shi ga ɗan adam sai dai zama koyaushe cikin shirin da sakawa a rai cewa ko da yaushe mutuwa na iya riskarka shi zai sa ka yi duk wani abu wanda zai kusanta ka ga aljanna, ka nesanci wanda zai kai ka ya zuwa wuta!.


"Ki tashi ki tafi ki haɗu da ƴan aiki kin zo kin kwanta gari har ya waye ko har yanzu dakikiyar kwakwalwarki tana miki tunanin rayuwarki ta baya ne? To nan ba da gidan ubanku bane gidan kanen ubanku ne, uban naku yana can cikin kasa a rufe" Hajiya Rayyanatu ta ce tana aika musu kallon mugun tsana.

Kallon ta Hauwa'u( Hawwa) Ta yi tana jin zafin kalamanta bata san irin zafin da take ji ba idan aka sosa mata mikin mutuwar mahaifanta wanda mutuwa ta ɗauke musu su a rana ɗaya a lokaci guda ba tare da ciwon komai ba sai kaddara da karar kwana.

"Ai Aunty Hawwa ta ce Ummie da Abbie za su buɗe kasar su dawo mu koma gidanmu ko Aunty Hawwa" SABEER ya ce yana karkarwar sanyi. Kai kawai Hawwa ta gyaɗa masa tausayinsu yana kara shiga zuciyarta har gwara ita yanzu shekarunta sha takwas, iyayanta sun rasu tana da shekara sha shida, shi kuma SABEER shekara bakwai lokacin yana ɗan shekara biyar suka rasu amma kasancewarsa yaro mai wayo da rashin mantuwa har yanzu bai manta komai ba.

"Kai dalla rufewa mutane baki uban waye ya ce maka idan an mutu ana dawowa duk wanda ya mutu ba zai taɓa dawowa ba, su ma suna can sun tafi kenan" Da kuka ya fashe yana kifa kansa a kirjin Hawwa ita ma Hawwa hawayen take tana jin kukansa har kasan ranta tana kuma jin haushin maganganun Hajiya Rayyanatu wacce ta kasance matar kanin mahaifinsu.


"Za su dawo mu koma gidanmu" Ya ce cikin kuka, Hajiyar ce ta karasa gabansu ta saka jug ɗin hannunta ta kai masa bugu ai kuwa Hawwa ta saka hannu ta kare dukan da ta kawo ita aka same ta a hannu, ganin haka sai Hajiyar ta juya akalar dukan zuwa gareta ta rangaɗa masa jug ɗin a ka da karfi. Bata ce komai ba kuma bata yi yunkurin komai illa iyaka ta sunkuyar da kanta kasa hawaye suna malala daga idanunta tana tunanin ranar da za su bar gidan nan su fita daga ukubar da ake musu da gallazawa.

"Idan kika kara minti biyar baki fito ba wallahi sai kin gwammace kiɗa da karatu shegiya mai farin fatar zabiya, wannan farin naki na maita ne gadon tsiya gayyar na ayya gayyar tsiya" Ta ce tana juyawa ta fita daga ɗakin. Hannu SABEER ya saka yana share mata hawaye n.

"Aunty Hawwa ki yi hakuri daga Ummie da Abie idan sun dawo za mu bar musu gidansu mu koma gidanmu ko? Inda muke kwana a saman bed, har Ummie take ce miki Hawwa in kara gani kin ce a ɗakin SABEER za ki kwana shi ɗakin naki dafawa za ki yi ki ci? Muke cin abinci mai daɗi direba ya kai mu makaranta ya dawo da mu Abie ya ka kaimu wurin wasa da gidan zoo" Ya ce har yana murmushi tunowa da ya yi da rayuwarsu lokacin iyayansu suna raye. Rungume shi ta yi tana tuno abin da ya ce Ummie tana cewa ɗin har jiyo sautin maganar ta yi yadda take mata faɗan cikin wasa saboda tsokana irin ta Hawwa sai ta je ta kwanta a ɗakin SABEER yana tashi ya ganta a kan gadonsa tana bacci sai ya ringa

Please Login or Register in order to submit comment