Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu ba, dan su kansu suna bukatar hakan."

Alokacinda affan yasamu labarin abunda marshall yayiwa intisar har cikin ransa bayai yaji dad'ii ba."
Ransa yabaci sosai kuma yasan umma(kilishine) tajawo mata, bai sake tsinkewaba da tausayinta ba saida yaga yadda intisar tarema lokacii d'aya tausayinta yakamashi, aikuwa dabad'an dan uwansa vane yayi mata wannan wulakancii da'anga yadda zasu kwashe, wasu kuma daga cikinr y'ay'an kilshi cewa sukai aidama namiji ba'ayimasa auran dole, Allah yasa hakanne yafii mata saukii agareta,


Kilishine gaban bokanta tana zaune dirshan daka ganta kasan magan ganun dayake fad'a mata ranta baiyi mata dad'i dasuba."



To be continued



Ur's
zaynab bawa
*BIBIYATA AKEYI*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*


_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_


_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_



_Your fifth page, is here my *HAJJA CE* Allah yabarminke har abada, ke abun alfaharice ga al'umma."_
_Allah yaraya mana ihsan musha biki."_


====================

Tabbas ke k'awar arziki ce *ASMY B ALIYU* godiya da mai yawa ga dumbin soyyayarki gareni Allah yabar zumunci."



*
page 99

Bayan sunbar shashin mai martaba, kusan gabaki d'aya shashin ummii aka nufa, alokacin harsu yaya hindu duk sunzo, murna dai ranar acikin wannnan dangii ba'acewa komai, hanna ne zaune da su anty afeeya, dakuma sauran yayaunta, kallon anty afeeya tayi sannan tace nifa bqnga labba ba, dafqrko nadauka tana gidaki kuma naga haryanzu bata iso ba, murmushi anty tayi sannan tace labba kam tana nan tana tayqki kishi tama tattare kayanta gabaki daya takaoma wajen dangin ummii, tun jiya nake kiranta taki dauka tunani takeyi dan fad'a mata zancen and'aura aurenne ne, anty *hanna* labba tashiga tashin hankali, kowa yashiga tashin hankalin rashinki, yaya hindu ce ta kar6e maganar da cewa *hanna* ki gode Allah kina tare da masu k'aunarki dayawa, hakan yakasance abun dubawa dukda bazai kasance kowa yasoka ba arayuwa, idan kaga mai k'iinka saika tuna da dumbin masoyanka, mungode Allah daya dawo mana dake cikin koshin lpy, wannan kad'ai ya ishemu farinciki, kuka *hanna* tafara tana cewa kuyafeni en uwana, bason raina bane na 6ace nabarku cikin tashin hankali, nima nayi missing dinku sosai fiyeda yadda baki zai iyq furtwa, nayi missing dinku fiyeda yadda hankali zai d'auka, fiyeda tunanin yadda tunani zai dauka, inasonku sosai, inasonku tafad'a had'eda share hawayen fuskarta." kar6an wayar hameeda tayi sannan Tad'auki number din labba awayqr afeeya, dialing tayi, harta kusan katsewa ba'a daukaba,"
Labba dake kwance kan gado hankalinta duk yana gida amma batason komawa ne dan bataso takoma tajii and'aura quran yaya yareema ta intisar, intisar er uwartace bawai batason auran bane dan batason intisar ba, a'a saidan ganin rashin dacewar hakan, hakan yakasance butulci da'ace *hanna* tana nan yaya yareema zaiyi aure abun bazaiyi mata ciwo ba, kamar yadda ace batanan ta 6ace, yanzu wayanasan ma, kodan yaya yareeman akayi mata wannan abun ta6ace, yanzu rana d'aya ace *hanna* tadawo tasamu wannan labari wani irin hali zata shiga?"
D'an tsaki taja yayinda wayarta ta dameta da ringing kamar bazata d'aukaba harya kusan tsinkewa tak'arajan tsaki akaro nabiyu sannan tayi picking, shiru tayi batace komaiba, daga d'aya bangaren kuma *hanna* dataji and'auka, dasaurii ta ambacii *habibtiii* aikuwa labba ko bacci tatashi dashi bazata mance wannan murya ba, Batason lokacin da tafad'o daga kan gado ba, ita tayi gefe wayar tayi gefe, k'arar fad'uwar wayanne yacikawa *hanna* kunne yasa tayi saurin d'agawa daga kunnenta tana kallon wayar, sauri labba tayi ta nemo wayar, hango waya tayi agefe, daukan wayar tayi sa'arta d'aya wayar bata mutu ba, saurin karawa tayi akunnenta tana cewa, habibty habibty, dai-dai lokacin *hanna* tamayar da wayar akunnenta, na'am *hanna* ta amsa had'eda farfara ido kamar tana kallonta, jiki na 6ari labba tace sis ta gaske kece, gashi kuwa kinjin hanna tabata amsa atakaice, sannan tad'aura dacewa saura 4days suna yqronki, kiyi kizo idan ba haka ba baby yayi fushi dake, zqtayi magana *hanna* tayi saurin katse wayar ta kasheta gabaki d'aya, dariya afeeya tasaka sannnan tace aikuwa kin iya maganainta, yanzu zata fara shiri sannnan tatashi hankakli anem mata visa, aikuwa baku kyauta mataba, cewar yaya hindu yanzu haka zakusa hankalinta yatashi, dariya kawai *hanna* sukayi."

Palour suka koma waJen mama momy dakuma ummiii da inne da kakarsu, ita kuma hussentu tana taredasu *hanna* da yarinyar isshaq, sukuma Sadiq da isshaq suna masaukinsu, basu dad'e da zama afaon fa marshall yashigo d'aukeda sallama, mafii yawanci d'akinne suka amsa, sannan yakarasa shigowa kayan sodier's ne ajikinsa yayi masifar kyau, fuskarsa d'aukeda murmushi, da annurii, tsugunnawa yayi yagaida manyan dake wajen sannan yadubi mama yace," mama akwai wayanda zasuzo daga bauchii ne? Eh akwai tabashi amsa atakaice, sannan tadaura da cewa inaga kaman Aisha da rabi'atuh da ammansu zasuzo nikuma zankoma saboda su karima akwai hassana da husaaaina d'azu karima takirani sunata kuka, babuk'atqr komwarki marsall yafad'a sannan yad'aura da cewa inaso na aika soldier's yau za'a taho dasu, sannan masu zuwan su jira soldoer's su isa sannan su taho tare sabilida hatsarin dake cikin tafiyarsu su kad'aii," jirgi zasu tafii dan haka ba wani jimawa zasuyiba." d'aga kaii kawai mama tayi jikinta duk yabi yayi sanyi tasan lokacin rabata da yaran dasuka riga sukabi jinin jikinta yazo, ahanakali ta furta Allah yayi taimako yabaku sa'a abdallah kakula sosai kasan hatsari irin na way'annan mutanen." squran dake d'akinma addu'ar suka yi masa, juyawa yayi zai fita *Hanna* Wanda tun shigowarsa idanuwanta yake kansa sakamakon wani irin kyau da yayi, har zuwa lokacinda yayi gaisuwa idanuwanta yana kansa, alokacin da yafara magana kansu karima ne tunaninta yafara canjawa abubuwa dayawa sukayita dawo mata way'anda suka faru abaya." kukanda *hanna* tasakane yasashi juyowa tsayawa yayi kawai yana kallonta, maamakine yakamashi menene kuma nakukan?" ohow, yabawq kansa amsa, *hanna* akan gwuiwowinta, ta tsugunna agaban ummii tana kukaa tana cewa ummii dan Allah kihanashi zuwa wallhy akwai abunda zai faruu, marshall ne yace shhhhhhhhhhhh *hanna* bbu abunda zai faru, akwai tafad'a kayi shiru kawai kai baka sani ba, kabarsu da Allansu kawai plz karkje wani abuu yafaru dakai way'ananna mutane hatsabiban mutane ne."
Tsayawa kallonta yayi kawai dan baisan mai takeson cewa ba, sqka bayan hannunta tayi ta share hawayen fuskarta, taja majinar dake hancinta sannan tace ummiii sune way'anta suka sa aka harbeshi adubai gaban ummii ne yafadi daran tace hanna me kike shirin cewa ne??, hard'e hannayensa a k'irji marshall yayi, a iya saninsa yasan bai ta6a furtawa *hanna* cewa anharbeshi ba, sannan yasan bawai tasanda hakan bane, a hankali yafurta tayaaya akayi kikasan hakan *hanna*, nan da nan tashiga basu labarin abunra yafaru a highcourt lokacin zuwansu da amira wajan babanta, takara da cewa alokacin naso nasanar dakai toh idan zanyi hakan bansanka ba bqnkuma san a'ina zan sameka ba, amira ce ta hanani sanrada wani sabilida akwai hannun manyan mutane aciki bakasan wa zaka fad'awa ba dakuma mai hakan zai janyo Ba, labari taci gaba da basu, har izuwa lokacinda taji sanarwa a tv akan cewa an harbeshi bbu tabbacin yanada raii kokuma yamutu, dakuma mafarki da takeyi dashi, hanakalin ummiii yatashi sosai jin irin wannan labari, mama girgiza kai tayi sannan tace assha asssha *hanna* meyasq kika kasance mai zurfin ciki haka?" ni mahqifiyarki ace munkwana daki daya muntashi d'aki daya kikasa fad'amun wannan?" kuka kawai *hanna* takeyi takaea cewa komai, marshall wanda kukan *hanna* yafii d'aga masa hankali fiyeda maganganun da tafad'a masa yace shhhh *hanna* taso kizo nan, bbu musu tatashi tanufeshi, kama hannunta yayi suka fice waje sukabar mutanen ciiin wajen da zullumi, ummii idan tace bata shiga mummunan tashin hankali bama toh wannan ta yaudari kanta ne , tunowa da tayi irin tashin hankalin da tashiga lokacinda akasabarda ita cewa an harbeshi ahalin yanzu da sukasan cewa rayuwarsu tana cikin hadari dole zasu nemi yadda zasuyi kuga bayansa,"
Ayanzu kam bataga na zama ba dole dukansu sutashi da addu'a."
Lokacii d'aya suka miqe da mama kamar wanda ko wacce tasan abunda d'an uwanta yake sakwa acikin zuciya, alola sukayi sukai nafiloli sannan suka runga roqan Allah yarabasu da matsalolinsu sannan yarabu daga sharrin duk wani mai sharri."

Marsahall har shashinsu ya zarce da hannunsa riqeda na *hanna*," zaunarda ita yayi bakin gado sannan ya canja kayansa daga na sojiji zuwa, ainihin shadda geznah, jamfanne amma batayi girma sosai ba, links yad'auko yana k'okarin sakawa *hanna* tataso takar6a sannan taaaka masa, bud'e wadrop d'in tayi tad'auko hula tasaka masa, juyawa yayi yakoma kan gado yakwanta, kallonsa tayi tace ba futa zakayi ba, girgiza kai yayi sannan yace," nikam bbu yanda zanje, ina zaune dake agida, karasowa tayi sannan ta kwanta agefensa tace," duk wannan kwalliyar tawace kenan?" ke kad'anki ma kuwa yataba amsa." murmushi tayi, ba'a dad'eba kiran labba yashigo wayan marshall yana d'auka ko sallama batayiba tace ya yareema plz kafad'am sis tadawo, dariya tabashi yace labba ko gaisuwa bbu rabonki raki nemeni tun yaushe, fushi kikeyi dani kenan?" toh bazan fad'a ba, tunda yaune kikasan amfanina, dariya tayi sannan tace aii bama saika fad'aba yanayin yadda kake magana yanunamin, tana fad'in haka takashe wayarta tafita neman visa."
Karima ne zaune awani garden, tun d'azu take jiransa, bai isoba gashi yanzu bataso sutafii batareda tatafi tasanar dashi yadda zaai sameta, ba gashi ta tabbata yanzukam anata jiranta, ranta bbu dad'i tatashi zata tafii," hango motarsa tayi yayi parking nufota yayi tayi, bata tsaya ya k'araso wajanta ba tayi saurin ajiye masa wata farar takarda, tashige adai-daita dinda yake jiranta." bai bitaba dan yasan ba tsayawa zatayi ba, k'arasawa yayi yad'auki takardan data ajiye, d'in sannan yajuya tana zuwa kuwa tasamuu ita kad'ai ake jira dasaurii tashiga, taduko abunda zata buk'ata tafito abida kam ta dad'e da shiga mota itada twins, da kabir, karima itama tashiga motar suka, nufiii airport, duk saita kejin bbu dad'i, batajin zata iya rabuwa da mama, jitakeyi yanzu basuda mahaifanda suka fisu ita kanta tasan cewa bbu wanda, zairiqesu kwatankwacin yadda mama ea sauran mutanen gidan suka riqesu, ashe ba ita kad'ai take wannan zullumin ba, su kansu y'an uwanta Abunda ke cinsu arai kenan," haka suka isa airport, ran karima cike fall da tunanin mutumin da batasan koshi wayeba, bata ta6a bashi damarda ko sau d'aya zaiyi magana da itaba,"
Amma wannan sak'onda tabar masa ta tabbata, har indai dagaske yadda yake fad'in yansonta akullum saidai bata fitaba yana bibiyar rayuwarta, to tabbas idon son gaskiyane zai nemeta."
Daganan jirginsu yad'aga zuwa kano."




Kilishi ta firgici tadawo gida, ad'aki tasamu intisar ta kulle k'ofa, bugawa tahauyi kamar zata 6alla kofar, dasaurii intisar tataso ta bud'e kofar, ganin kilishi ahaka yasata tsorata tun daga kofa tafara tambayarta kan cewa lpy kuwa taganta haka, kilishi tace ina kuwa lpy er nan zama tayi bakin gado ta lalu6o number din hajiya hadiza takira, tana d'auko ko sallama bbu tace hajiya komai ya6aci, kinaji sharad'in daya bani cewa idan yayi aiiki har indai aikin bai tafii dai-dai ba to tabbas zanmutu, idan kuma ba'ayi aikin ba to tabbas zan haukace, nikuma bazan iya daukab risking haukacewa ba," ya tabbata har indai banaso nayi hauka sainaje nafad'a musu duk wani abunda na aikata kafinnan da gobe," ta cikin wayar hajiya hadiza tace toh nikuma meye nawa aciki kafin ayi aikin ainafad'a miki cewa akwai sharad'i kikace kinji kin dauka dan haka zaiki za6a acikin uku diff takashe wayanta."
Cire kwalin kanta tayi, intisar dake gefenta tace na shiga uku umma yaya zamuyi nimaa bansaniba, tabata amsa atakaice,"



Wajen k'arfe uku su ammah dasu karima suka iso, kai tsaye shashin ummii aka wuce dasu, zuba idanuwa sukeyi kawai koda cewa zasuga *hanna* amma shiru sai jaririn dake hannun afeeya, amma ne bakinta yakayin shiru tace, nikam ina d'iyata, idanuwana suna bidar ganinta, bakina yakasayin shiru karimace tace wallhy nima tun d'azu nake zuba idon ganinta, murmushi ummii tayi sannan tace, barina kirata d'aga wayanata tayi takira layin marshall," karar wayane tatashesu daga bacci mqi.nauyi daya daukesu, daukan wayan yayi ganin ummi yasashi saurin miqewa ya amsa," katuro *hanna* yanzu ammanta tazota." dama wayar a speaker take hanna tanaji da gudu tamiqe tayi waje, girgizakai marshall kawai yayi yana murmushi,"
*Hanna* tana isa da gudu tafad'a jikin ammma murna kamar tayi yaya, haka tayi farin cikin ganinsu karima sosai."
Nan aka shiga jajanta maiyafaru, kowa sai alhini yakeyi, kowannen cikinsu yakwana da zullumin abunda zai faruu gobe mafii yawancinsu basuyi bacci ba, sun kwana sunakai kukansu wajan ubangijinsu,"


Washe gari da sassafe *hanna* dasu karima suka wuce court tareda marshalll" anan sukarima suka kalli yayarsu rauda wacce take kasar waje tana aure," marshall ne yasanarda itaa cewa k'annenta suna raye."
Sosai tayi murnar ganin k'annenta hadda kukan murna."
Bawata shari'a mai tsayi akayiba kasancewar marshall yad'ade da gabatarda shaida, basuda wani abunda zasu kare kansu," Mafii ywancinsu an yanke musu hukuncin kisa yayinda wasu daga ciki aka d'auresu rai da raii, ayau su karima sunyi farin ciki duk da kasancewar bawai angabatarda sharia akan mahaifansu da aka kashe bane tunda bawai sunada wat kwararriyar shaida bane, amma hakan yayi mata dad'ii tunda sunga, wanda sukeson gani awulakance."
Haka suka tattaro suka dawo gida kowannensu cikeda farinciki."



Kilishi ce zaune ad'aki tarasa wacce shawara zatabi, tarasa mekeyi mata dad'ii." shin tatashi taje tasanar dasune komai zai biyo baya ya biyo kokuma tajira tagani koda gaske boka yakeyi mata."




To be continued




Ur's
Z33iiyyb3rw3r
*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

الحمدالله

*Alhamdulillah en uwa barkanmu da sallah, Allah ya mai-maita mana* عيد مبارك

*Page 100*

Jikin kilishi dai abun ba'acewa komai dan sai k'ara gaba abuu. yakeyi."
Yaranta gabaki d'aya hankalinsu atashe yake kana kallOKnsu gabaki d'aya sunfita hayyacinsu, away'anna ranaku suna kallon tashin hankali, kokadan basuyi zaton haka daga wajan mahaifiyarsu ba." ahalin yanzuma kilishi tbii shawarar kawqce, tabbas acikin kawaye baduka aka taru aka zama d'ayaba, akwai 6ata garii Acikin su, kamar yadda akwai nagarii cikinsu, akwai masu bada mummunan shawara akwai kuma masu bada kyakkaywan shawara, sannan bakowace irin shawara bace yakamata ana baka kadauketa, bakuma kowacce shawara bace zaka yada ita, aduk lokacinda akace anbaka shawara toh ana bukatar ka nutsu, kayi amfani da kwakwalwarka wajan taceta, haiqaqq akwai bata garin kawaye wanda, afuska zasu numa suna sonka amma azuciya kuma, suna kinka da'ace wani abun farinciki zai sameka cikin zuciyarsu suna bakin ciki." tabbbas kilishi tahad'u da irin wannan kawaye, wanda ayanzu waye garii yawaya, tana cikin wani mumuunan hali duk ta dalilin munannniyar abota."
Kasancewarta abaya mace mai tsoron Allah, saukinsu daya shine duk cikin masarautar bbu wanda yasan cewa kilishi batada lpy, hatta da kuyangu da jakadai an dakatar dasu dag shiga shashinta, wanda yaranta ne kwai sukayi hakan, babban tashin hankalinsu shine shirun da mai martaba yayi."
Tun ranarda yashigo yaganta sannnan yajii irin magan ganunda take fad'i bai kara komawa ba, kuma har yanzu baice komai akan wannan al'amarin ba, yaran kilishi harsunyi zarya sun gajii,"
Zai zauna dasu suyi mgana amma daga zaran sun d'auko masa zancen mahaifiyarsu zai 6ata rai sannan kuma bazai kara cewa komai ba, harsu tashi subar wajan, abun yana matuk'ar damunsu ga abuu sai gaba yakeyi." awannan lokacii su affan suka fara tunanin naimo mai maganii tunda sunjura harsun gaji."
Ranarda kilishi tacika satii d'aya da fara rashin lpy, aranar duka yaranta suna zaune afalo yayinda ita kuma kilishi ke kulle ad'aki, shashekan kukan intisar ne yacika falon, yayinda mafii yawqncii haushinta sukeji, dan dasaka hannunta mahaifiyar su tashiga wannan hali, tsaki affan yaja sannan yace, nifa gaskiya nasamo mafita wadda hakanne kawai zaiyi mana kyau sannnan yayiwa umman ma kyau, zama shirun mufa bazai haifar da komai ba, sai abunda yake gaba ma."
Yaya khadija ce ta amshe maganar ea cewa eh nima fa haka naganii, dan yanzu haka basa anyi mun magana damai maganii, affan ne yayi saurin cewa a'a yaya, nazauna nayi tunani kan hakan fa, baidaceba ace mun shigoda wani mai magani cikin wannan masaurauta bada sanin abba ba, ikilima tayi saurin katseshi da kai dallah rufe mana baki ni ahalin yanzu bansan wani dacewa ba, lapiyar mahaifiyarmu kawai nasanii, shii abban yayi shiru yak'i cewa komai, karfa ka manta duk mugun halinta ita ta haifemu, kuma duk cikinmu bbu wanda yau zaice tata6a daurashi wata mumminar hanya, nasan da wannan arfan yace sannan yakara da cewa" yaya koda aynzu ace umma tasamu lpy, wallhy aikin banza mukayi idan har bamu nema mata lahirarta ba."
Kamar yaya suka tambaya, gyara zamansa yayi sannnan yace abunda bake nufii, yanzu duk cikinmu bbu wanda abunda tayi yadawo kanta ba, dabakinta tafad'i dan haka ita wacce akayiwa abun zamuje munema mata gafara agunta, sannan ayi zancen neman magani,"
Kana ganin hakane nafita, kuma ita hanna zata yarda ta yafee mata?" hava yaya wallhy nasan *hanna* sosai tanada tausayi sqnnan ga hakurii, duk hakurin yaya yariima da kike kallo Allah tafishi."
Gabaki d'aya batada riqo arayuwarta, jijjiga kai sukayi sannnan sukai na'am da cewar sa."
K'arfe takwas na dare 8:00pm su affan suka nufii shashin ummmiii."
Tunda aka gama suna *hanna* takeson tafiya gida, ean tafiso saitayi arba'inn sannan tadawo, da tasamu marshall da maganan yakii fiirr ganin haka yasakata, samun ummii tasanar da ita, ummii bataki mata ba, amma har cikin ranta bawai tanason tafiyanta bane." halin yanzu irin shaquwarda tayi da *hanna* ta dabance, balle yaronda kullum yana gunta, idan kaganshi wajan mahqifiyarsa to tabbas yunwa yakeji, gashi yanada hakurii saiya ini currr ma baiyi kuka ba."
Ummii tasamu mai martaba da zancen tafiyan *hanna* gida, amma shii bai k'ii ba baikuma ce tatafii ba."
Zaune suke ummii da *hanna* a falo, sai labba dake d'aki dauke da jariri, suna cikin zaune marshall yashigo, dan tunda yafita dasafe dawwarsa kenan, ummii ne tayi masa sannu dadawowa sannan tashige ciki, *hanna* ganin ummii tatashi dasaurii tanufii fridge tadauko mai ruwa mai sanyii 6arewa tayi sannnan tabashi ruwan yaja." ajiyar zuciya yasauke sannan yace aikuwa kamar kinsan da ishin ruwa nadawo, nasanii mana tafad'a takaice, ina tare dakaiifa, murmushi kawai yayi bai kara furta komai ba su affan suka shigo da sallama, cikin sakewar fuska suka amsa musu,"
Zama sukayi sannnan suka ta6a hira kad'an, sannan yayya khadija tashiga zayyane musu abunda ke faruwa kafin sugama bayani hanna hawaye ya wanke mata fuska," nan suka had'a da nemanan gafara, kokadan *hanna* bata riqeta ba, alokacin tashaida musu tayafe mata, godiya suka runga yi tareda matsanancin kunyarta data kamasu."
Shikuwa marshall baice komaiba tunda har wanda akayiwa tace tayafe, baiga dalilin dayasa shii zai dauki zafii ba."
Cikin nuna al'ajqbi marshall yace yanzu wayake yimata nagani, bbuu suka bashi amsa atakaice, dan haryanzu abba baice komaiba," aikuwa yakamata yace, marshall yafad'a dan zama hakan ba mafita bane yana gana fad'in haka yajuya ya kallii *hanna* sannnan yace jeki sqnarwa ummii sannnan tafito mutafii baki d'aya muje duba cikin ummma dasauri ta miqe tajeta tasanarda ita abun yacika ummii da al'ajabii, amma haka tafito suka fice, koda suka isa *hanna* kuka tarinka yii ganin jikin kilishi har ummii sanda ta zubda hawaye." dagudu *hanna* tafice bata tsayya ko inaba sai shashin mai martaba, tsugunnawa tayi kan guiwowinta tana kuka tana cewa, abbba mun tuba kamana raii wallhy abba umma najin jiki, kayi hakurii kanema mata wanda zai mata magani, nikam abba nayafe mata, har indai dannii kaki cewa komai."
Tsayawa kawai yayi yana
Kalllon *hanna* , wannan yarinya wace irin zuciya gareta haka, duk wanda zaiyi mata sharrii ita da alkhairii zata bita, ajiyar zuciya yasauke sannan yace" *hannatu* diyata share hawayenki, kinjii kidaina kuka, wannan abuu baiyi dadii bakam nikaina ina neman gafararki, ni abbab bakayimun komaiba itama har cikin zuciyata na yafe mata."
In sha Allahu daga yau za'a fara yimata magqnii zan sanarda madibboo, amin ta amsa sannnan tatashi tafice."
Aikuwa kwanan kilishi biyu dafara magani, tasamu lpy aikuwa tana kuka tanemi gafarar *hanna* kamar yadda hanna tashaida wa kowa tayafe, haka itama ta shaida mata."
Zama sosai akayi agidan yadda mai martaba zafff yayiWa kilishi Sannan yashaida mata dalilin dayasa bazai saketa ba dalilin yaranta ne, anan kuma yasaka intisar ta fiddo da miji."
Aikuwa bata dad'e ba tafito dashi, cikin kwana biyu akayi auran, mijinnata yanada mata d'aya da yara hudu, yanada dukiyarsa, bai nuna bambamcii tsakanin ta da matarsa, zaman lpy sukeyi sosai."
*Hanna* kuwa tatafi gida saita tayi kwanaki arba'in 40 curr acan dan saida akayi auran najeeb da karima kafin tadawo." har tagama kwana arba'in dinta bata ta6a tad'awa wani Kan abunda kilishi tayi ba."
Aranarda zata dawo marshall da kansa yazo d'aukanta,"


*BAYAN SHEKARA BIYU*


*Hanna* tagama karatunta, alokacin kuwa amiira ra yaya jalal shekaransu d'aya da yin aure sannnan tanada tsohon ciki, lokacin labba itama tayi aure dan dangin mahaifiyarsu ta aura, dan haka vatama kasaar."
Hemeeda tahaihu yarinyarta kykkyawa, yayinda hafsat ma tahaihu tahaifii yaro,"
Itakuwa rabi'a haryanzu shiru da zaran saurayi yazo anacewa yafito zai gudu, tun abun yana damun amma har tadaina damuwa dan ta tabbata abunda tashukane ke bibibyarta."

Saukan *hanna* kenan daga k'asar india daga wajan d'aurin auren abiid da fariisa wanda ya aurii matar shahid, matarsane da kanta tasaka ya aurii matar abokinnasa bayan rasuwarsa, dan tana tunanin wanda zai riqeta tsakni da Allah, da mijinta kawai ta yarda shiyasa ta roqeshi, ita kuwa fariisa dafarko ansamu matsala daga wajanta, dan tana kallo kamar tacii amanar mijinta da kuma kawarta ne, sai dakyar kafin ta amince."

Agajiye sosai *hanna* take dan dakyar ta iya k'arasawa falonta nakasa tayi shame-shame, dakinta ma sai marshall ne yak'arasarda ita, aikuwa nan tashiga zazza6i mai zafin gaske gwajin farko yanuna tana d'auke da cikin wata uku, murna wajan dangin marshall baya misaltuwa, bayan wata tara ta haifo yarinyarta mai kamada ita sakk, gar rashin hasken fatarsu ma d'ayane."
Ansha suna sosai yayinda tacii sunan mahaifiyar *hanna* suna kiranta da ainihin sunanta har su inne sunzo sunan tareda isshaq da matarsa wacce ya aura, itakuwa hussentu vata samu damar zuwa ba, sakamakon ciki da takedashi tsoho haka akayi suna aka gama cikin kwanciyar hankali."

*BAYAN SHEKARA BIYAR*

*Hanna* na hango tazama mtashiyar mata wacce bazata wuce shekara ashirin da bakwai ba."
Sai Abdulaziz yaronta nafari dakuma amina mai sunan mama, sai kuma hindu itace ta ukun sannann najeeb d'an karamun yaronda yake d'auke ahannunta."
Dasaurii tashige gidansu bayan tafaka motarta, yaran suka bita abaya, gida naganii acike damm da alamu biki akeyi, Cikin saurii *hanna* tashige d'akin amma tana cewa," hava yaya rabi'a kuyi saurii fa ku fito, ke kince bazakiyi komai ba sai walima, walimar ma yanzu lokacii yanata k'urewa, owwhh *hanna* idan kikayi hakurii yanzu zamu tafii cewar hafsat dake shirin fitowa, aigaradai dabata amsa, ita kuwa *hanna* dakin mama takora yaranta, tawuce wajan walima, washe garii kuwa da sassafe aka d'aura auran isshaq da rabiat bayan kwana biyu kuwa aka wuce da ita cameroon, *hanna* kuwa bataje ba dan marshall bai barta ba, washe garii bayan en biki sun watse kuwa, *hanna* nazaune dakin mama tana shirya kayansu dan gobe zasu wuce, amma tashigo, dafara'a *hanna* ta amsa sallamar sannan tace ammah bakiyi baccii ba?
Banyiba *hanna* ammah tabata amsa atakaice, zama kusada ita tayi sannan takamo hanunnunta tace, *hanna* nagode nagode,
Kwace hannunta tayi sannan tace haba ammah wannan abun fa duka yiwa kaine, eh dai *hanna* nasan rabiah er uwarkice ammafa sharrii na nemeki dashi

Please Login or Register in order to submit comment