Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki."
Sosai baba yaji bbu dad'i aranar yakamo hanya yazo garin, yana isa ya wuce fada, dake shikad'ai yazo Ko driver bai d'auko ba."
Sosai mai martaba yaji dad'in ganinsa, bayan sun gaisa ne mai martaba yasa aka kira masa ummii, takai 15minute kafin ta iso, duk tarame gabaki d'aya ta lalalce, bayan sun gaisa ne, baba yad'an nisa kafin yace, shawara ce nakawo, wanda ina tunanin shine mafita dashi damu kuma baki d'aya, mai martaba ne yace, muna jinka, dan yanzu dolen mafita muka zauna nema, baba yacigaba da cewa, ni aganina abunda zai zama maslaha damu dakuma yaronnan shine kawai, ak'ara masa aure, gaban ummii ne yayi wani mummunan fad'uwa, tace haba da Allah, wai ce muku akayi *hanna* baxata dawo bane Ko kuma?" girgiza kai kawai baba yayi yace Ko d'aya ba'ace *hanna* bazata dawoba, kuma shi ai mijin mace hud'u ne, koda tadawo saidai tayi hak'uri, amma Ganin wata kusada shi zai rage masa damuwa,zai rage yazauna yana tunani, mai martaba baice komai ba juya maganar kawai yakeyi, sai dayaji kowa yayi shiru sannan yace, amma kana ganin hakan shine mafita bbu wata hanya? Girgiza kai baba yayi sannan yace gaskiya idanma da'akwai wata hanyar nidai bansanta ba."
Mai martaba yace, toh Allah yaza6ar mana mafii alkairi, da ameen baba ya amsa, sannna yacigaba da cewa, baka ganin er k'aninka, naga kusan kamarsu d'aya da ita *hanna* d'in ai sai ka tambaya masa ita, dasaurii ummii tacafe, tace wah wai hameeda kuke nufii, amma wannan babban cin amana ne, er uwartata xaku aurawa mijinta dan bbu idonta, wallhy Allah bada yawuna za'ayi wannan auranba, tatashi tafice tana sharar kwalla."
Binta da kallo sukayi su dukansu, sannan mai martaba yace, kasan halin mata da wani irin abuu, abunda Allah ya halasta su zasu nemi haramta maka shii."
Nan sukayi sallama suka tashi akan baba zai wuce su zauna suji yadda za'ayi shida, abba."

Umma nashiga d'aki tafashe da kuka, kawai tana jajanta abunda ake shirin aikatawa baiwar Allah."

Labba ne tamatso kusada ita tace, ummii menene yafaru?"
Wani abunne yasamu yayan?"
Girgiza mata kai ummii tayi, sauke ajiyar zuciya Labba tayi, ummii ne tace kayya er nan daina wata ajiyar zuciya ina maraban wani abu yasameshi, da abunda ake shirin aikata masa yanzu."
Riqo hannun ummii Labba tayi tana zazzaro ido sannan tace, me za'ayi masa?"
Aure zasu masa, ummii tabata amsa atakaice, aure kuma ummii?"
Eh aure kuma wai er uwarta hameeda, subhanallahi hameeda ummii?" wannan wani irin cin amana ne, nan danan idanuwanta suka fara zubda kwalla."
Tatashi dasaurii tafice dagudu, bata tsaya ba sai sashinsa, tana zuwa tafara bugawa kamar wata mahaukaciya, jin bugun yayi yawa yasa yatashi, dakyar yabud'e, kofan."
Dagudu Labba tashige jikinsa tana kuka, bubbuga bayanta yafarayi, amma bai iya magana ba, sanda tagaji dan kanta tad'ago tadubeshi tace, yaya Allah aure zasu maka, suwa? ya tambaya, su abba, mana, d'agota yayi yace kai Labba kodai bakiji dakyau bane?" ni nace musu inason aure?" Allah kuwa yaya wai kuma da hameeda, zaro ido yayi yace hameeda kuma labba, eh Allah yaya, ajiyar zuciya yasauk'e yace to ai yazo gidan sauki, zuwa gobe, zanshawo kan matsalar har indai hameeda ce, dawatace sai in damu."
D'agowa tayi tadubeshi tace Allah yaya, d'aga mata kai yayi yace, Allah kuwa acikin week d'innan zan shawo komai."
Sai alokacin hankalin Labba yad'an kwanta, tadubeshi tace yaya kaci abincii ne, girgiza kai yayi yace banjin yunwa ne, yakamata kaci ai tabashi amsa takaice."
Tashiga kitchen tahad'a masa abincii, dakyar yaci, sanda yaci kuwa tabar shashin, taje tafad'awa ummii Yanda sukayi, Allah yasa adace kawai ummii tace."

Baba ya isa gidan abba suka zauna, sukayi magana, abba fur yak'ii yarda, sanda baba ya nuna masa bacin rai, ya ce, idan kanaso kanunamin bani nahaifeta ba shikenan, amma ni nadauka yarana da naka duk d'aya ne, nan danan abba yarikice, har idanuwansa suka ciko yace haba yaya, wannan wani irin magana ce, baba ne yace idan bahaka kake nufii ba, mai yasa zanyi magana kace bahaka ba."
Kayi hak'uri yaya wallhy hameeda erka ce duk Yanda kakeso kayida ita."
Tom nagode idan kashiga kayiwa matarka magana kajii, nima idannaje zanmata magana."
Ahaka sukayi sallama."
Abba ya tashi yashiga gida jikinsa bbu kwarii."

To be continued

Ur's
Z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

```Alhmdllh am so much bless, addu'anku sunyi aiki, godiya Mai yawa```

================

PAGE 92

*
Yau ma kamar wancan karon sassafe sadiq yatashi yatafi ruga d'an d'auko malam,
Dake malam baisanda zuwansa ba, kuma baishirya ba, sanda yajirashi ya shirya, sai 1:00.suka iso, yana zuwa yabaukaci ganin *hanna*, kawota akayi sai zazzare idanuwanta takeyi kamar wanda tayi k'arya, dasaurinta tak'arasa gefen inne tazauna."
Cikin damuwa inne tafara yimasa magana, tace, malam duk randa nabata ruwan addu'oii nan, saitayi k'ok'arin halaka kanta kokuma abunda yake cikinta, kuma tanashan wuya sosai."
Malam ayad'anyi shiru kafin yace, maganar gaskiya yarinyarnna turan aljanu aka mata, kuma ahalin yanzu idan aka matsa sai anciresu, kafin su fita zasu cutarda ita kokuma abunda yake cikin ta, zasu iyayin sqnadiyar cikin, idon inne ya cikciko tace yanzu wannan yarinya wani abu zatayi dahar za'a tura mata aljanu, mutane kokad'an bbu imani."
Malam ne yadanyi jim kafin yace, Aibasai tayi musu wani abunba, yanzu d'an adam ake kiwo, ba dabba ba."
Yanzu nakaoma zanyita yi mata addu'a da sauk'an qur'ani, yanzu zaikai kaman yaushe haihuwanta?"
Diddi ne tace, ba lallai ya k'arasa nanda wata biyu ba."
Toh in sha Allah nan da wata biyu zata samu sauki, dan yanzu Allah kad'ai yasan halinda danginta suke ciki."
Jijjiga kai inne tayi tace, hakane dole zuri'arta zasu kasance cikin tashin hankali da zullumii."
Allah yabata lpy, dukansu suka amsa da amin, sai bayan la'asar, sadiq yamayar da malam."

Marshall ne zaune da kayan soldier's, ajikinsa rabonsa da saka kayan yakai 7month, yarame kam sosai, amma Sun masa kyau sosai, wayansa yad'auko yayi dialing numb d'in, captain Ahmad wanda ayanzu yadawo genaral Ahmad, yana shiga kuma aka d'auka, baijira wani sabon zance ba, yace kasameni a shahi na."
Kusan 30minute kafin yak'araso sanda yakirashi yanemi izinin, shiga kafin yashigo, ganin agonnasa ayanayin daya dad'e bai ganshi ba yasa yak'araso dasaurii, yana fara'a, wajan zama yabashi, sannan yace magana nakeson muyida kai sannan kuma, ina neman alfarma, dasaurii, G Ahmad yace hava, yallabai yanzu har zaka nemi abuu awajena, sai ka kirashi da, taimako, kafadeshi kawai kai tsaye amtsayin umarni, Murmushi Marshall yayi sannan yace, yanzu zaka goyi bayan nayi aure?"
Aure kuma yallabai kokadan bazan goyi baya ba."
B'atan madam ba hakan yana nufin bazata dawo bane, wallhy yallabai Ko 10yrs zatayi kajirata, dannasan idan itane awajanta, itama jiranka zatayi."
Yak'e Marshall yayi akaro na biyu sannan yace, kuma er uwarta sukeso na aura, girgiza kai G Ahmad yayi yace, gaskiya hakan baidace ba,
Jijjiga kai Marshall yayi yace shiyasa nakeson kataimaka mun yau daddare kaje gidansu amatsayin, kana sonta, banso kab'oye mata komai, inason kaida ita, ku nunawa iyayenmu kun dad'e kuna soyyaya, dannasan nata wajanma bayarda zatayi ba, idan kaje mata da wannan maganar zatayi saurin amince wa."
G Ahmad ne yace indai hakan zaitaimaka, to nayarda zan aureta, zanje yau nasameta, nagode Marshall yace, Ahmad ya girgiza kai yace bbu godiya atsakanina dakai."
Ya tashi yafita."
Dad'i ne yakama Marshall nafarko yarabu da aurenda akeso ayi masa, nabiyu kuma, na cikawa *hanna* burinta, dan bai manta lokacinda tace masa, inason kacikamun burina kasa, C. Ahmad ya auri hameeda."
Tashi yayi fuskarsa ad'an sake yanufii sashin mahaifinsa."
Su kansu sojojin sa sunyi mamaki, yanda yau suka ganshi, yana cikin kuzarinsa, da sallama yashiga, falon mahaifinnasa, amsawa mai martaba yayi dan ya dad'e baiji shi da irin wannan muryar ba."
Koda zaiyi sallama saidai yayi ciki-ciki, kallonsa mai martaba yakeyi, har yak'arasa shigowa,
Yazauna yana gaidashi, shi kansa yaga fara'a kwance fuskar mahaifinsa, alamun yaji dad'in ganinsa ahaka."
Mai martaba ne yacigaba da cewa, dama gashi inason muyi magana, sosa kai Marshall yayi yace to ai gani abba."
Gyaran murya mai martaba yayi yace, dama inason na fad'a maka munyanke shawrar yimaka aurene, zaro ido yayi, sannan yayi kamar baisaniba yace, aure kuma abba, eh aure tunda kakasa daukan qaddara, kuma er uwar matarka zan aura maka, wacce kenan abba?, er gidan k'aninsa, kamar da gaske Marshall ya nuna firgici yace, abba budurwar Ahmad nefa, wani Ahmad? Dan gidan kanwan ummii mana, abba shine saurayinta, yaya za'ayi haka, k'anina nefa kamar yanda nakejin affan haka nake jinsa, kuma ku kad'ai yasani matsayin iyayensa, zai d'aukeku masu sonkai idan kukayi haka."

Shiru mai martaba yayi duk jikinsa, yayi sanyii, yadubi Marshall yace tashi kaje, zankira Ahmad d'in zanji tabakinsa zansame ka."

Tashi yayi yamiqe yafice murna aransa fall, yayi nasara danya fahimci jikin abba yayi sanyii."

Abba ne yashigo afalo yasamu umma, badai yadda take walwala ada ba, zama yayi kusada ita yace khadija, juyowa tayi takalleshi, yace inaso muyi magana, amma kuma yakamata ki fahimceni, yakamata ki fahimci mezan fad'a miki, dan kada kiyi mana gurguwar fahimta, kisani komai mukaddarine daga Allah, nan yafara zayyano mata bayani, kallonsa kawai umma takeyi, ji takeyi, kamar tashaqe shi kokuma tarufeshi da duka, juyarda kai tayi gefe, har yagama bayanansa ya wuce, tabishi da kallon banza kawai dan wani haushi yabata."

Tashi tayi tanufii d'akin hameeda, tana zuwa taganta kwance akan gado, duka ta d'aka mata, wanda yasa hameeda zabura tatashi, tana shirin kurma ihu."
Umma tace da Allah rufamin baki, nasan abbanku zuwa jmawa zaizo miki da maganar wai zasu aura miki mijin er uwarki, idan kika kuskura kika amince nidake, zaro ido hameeda tayi, sannan tace umma er uwata kuma wacce?" mijin *hanna* zasu aure miki, wallhy idan kika amince saina kasheki, kuka hameeda tafashe dashi, tace haba umma yaya za'ayi na'amince, kamar uwa d'aya uba d'aya fa muke, kima amince dan wallhy zan iya kasheki, kokuma in tsine miki, kuka takeyi tana cewa wallhy bazan amince ba umma."
Rufo mata k'ofar tayi da karfii, itakuma takoma takwanta tacigaba da kuka." jitakeyi kamar amafarki wai mijin *hanna*,


K'arfe takwas dai-dai mai gadi yashigo afalo yasamu umma yagaidata, sannan yace, hajiya wani yana sallama da hajiya hameeda, ak'ofar gida, umma ne tace jeka kace tana zuwa, leqa d'akin hameeda tayi taganta tanata kuka kamar ranta zai fice, bak'in cikinta d'aya wai arasa wanda za'ace ta aura sai mijin er uwarta."

Kitashi kije ana sallama dake awaje, mamakine yakama hameeda ganin, Ko ance ana sallama da ita umma sai tace ace batanan."
Yau itada kanta take cemata tajeta ana kiran ta, harta juya zata fita sai tace, yauwa sannan ki gyara fuskarki, ki tareshi da tad'i, har babanku yazo yasameki."
D'aga kanta kawai hameeda tayi, sannan tatashi tashafa powder, da turare tasaka hijabinta tafito fargabanta d'aya Ko waye yazo wajanta, itadai data aurii mijin *hanna* gwamma koma waye ta aura, afalo tahad'u ta umma, har tawuceta tajii umma nacewa, kuma kada kiga nace kifita kije kiyi rawar kai, ki kulada mtumcinki, kisan cewa Allah yana ganin ki, d'aga kanta kawai tayi tafice."

Ajikin mota tasameshi yana jingineda mota, tun kafin tak'arasa tagane wanene."
Tana isa tagaida shi, ya amsa, bai boye mata komai ba yafad'a mata yanda sukayi da Marshall, Jijjiga kai tayi tace wallhy hakan yafii, bansan wani irin abuu sukeson aikatawa ba."
Kallon fuskarta yayi yace, kin amince dani kenan, kai kawai tad'aga masa, nan ya bata labarin sa, har tad'an saki jiki dashi suna hira."
Motan abbane tadanno kai, tun daga nesa yahangeta tana hira, bai kulata ba yayi saurin parking Motan ya fito ya shigewa gida."
Anan falon yasamu ummii, zama yayi cikin sanyin jiki yace wai baki fad'awa hameeda wannan maganar bane naganta atsaye tana hira, umma ne tace, banfad'a mata ba, tunda naga tanada wanda takeso, kulllum yana zuwa hira nayau d'aya ace anmata miji, dawuya ace na fad'a mata wannan zance lokaci d'aya sai dai idan kai zaka fad'a mata idanta shigo."

Ganin lokaci yaja g Ahmad yace, barin tafii time yanaja sai gobe zanzo, kai tad'aga masa, sannan yace kuma kada kisake yin kuka anshawo kan matsalar dan fuskarki tanuna kinyi kuka, bazan sake ba tace sukayi exchange na number, sannan sukayi sallama."

Afalo tasamu abba gabanta yayi mugun fad'uwa naganin sa, amma tadake tace sannu da dawowa abba, yawwa sannu yace, tana k'okarin wucewa, yace dawo nan zamuyi magana dake, dawowa tayi tazauna yadubeta yace, waye wannan wanda naganshi tareda ke yanzu, sunna kai tayi kamar maijin kunya tace, abba k'anin mijin *hanna* ne, shima sojane yanzu yakai matakin general, gaban abbane yafad'i, ya k'ara maimaita k'anin mijinta kuma, tace eh, yace Yau yafara zuwa kenan, girgiza kai tayi tace, A'a abba tun bikin *hanna* muka had'u baku ta6a had'uwa bane."
Yadad'e ma yana cewa zai turo banbashi dama bane."
Abba bai iya cewa komai ba yace tashi kitafii, tashi tayi tamiqe, dad'ii yacikata ganin yanda jikin abba yayi sanyii."

To be continued

Ur's
Z33iiyyb3rw3r
*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

```Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi yace, (man mata) Manzon Allah yace duk wanda yamutu, (wahuwa yad'uu ma'allahi iddan) alhali yana kirawa Allah kishiya, wato yanayin shirka, yana had'a Allah dawani, (dakalan nara) Manzon Allah yace zai shiga wuta."
Allah karabamu da yin shirka, domin na d'aya daga cikin munanan ayyuka."```


Wannan shafin nakine *ZAYNAB UBA AHMAD (momyn yasmeen)* inasonki irin sosai d'innan Allah yaraya mana *yasmeen* musha biki, har shoki saina kwaso."
Mummynta zeeyy na gaidata, yasmeen d'ina agaishemunda *baabaa(ameerah)*😜 ace mummy na gaidata, itada *iyah(ummii)*🙊🙊

```Raheenat mahmoudouu, tunatarwane agareki, inasonki, irin bohut bohut d'innan, Allah yabarmu tare, ranar aurenki sai naje nijar fa."😜
Niamey zatayi bak'i."```

.

==============

Page 94

*
Bakin labour room suke azazzaune, yayinda i'shaq ke zagaye, wajan yakasa zama, gabaki d'aya hankalinsa atashe yake, gani yakeyi kamar *hanna* zata mutu kamar yadda, maman ihsan tarasu wajan haihuwar ihsan d'in,
Mata uku ana kawowa, kusada d'akinda take suna haihuwa." amma itakam shiru, ihunma takasayi, dan ita ba hankaline da itaba, kuma ba bakine da itaba balle tayi ihuu."
Nan hankalinsu yak'ara tashi, barin i'shaq da jikinsa har 6ari yakeyi, idanuwansa sun kad'a sunyi jajjir."
*Hanna* cikin labour room, abu yak'icii, gabaki d'aya, dan duk yadda sukeso *hanna* batayi, da azaba ta isheta tafara kai musu duka, nan suka fahimci hankalin ta ba k'alau ba, fitowa wata nurse tayi, dasaurii i'shaq ya nufeta, tambaya d'aya da yayi mata shine, ya take?"
Girgizakai nurse din tayi, sannna tace, bata sauk'a ba, amma tanada ta6in hankali ko?"
Wani irin bak'in ciki ne yatokare i'shaq yace, jin takirata da mai ta6in hankali nan danan ransa ya6aci, cikin zafin rai yace, ke wace irin wawiyace da bazaki duba file ba kafin kifara aiki, kisan awani yanayi zakiyi treating patient, wannan sakarci ne, ashe bakisan aikinki ba kenan, ko anfad'a miki bai rubuce cikin file d'inne, wallhy idan kika sake Wani abu yasameta, ki kuka da kanki."
Ganin yana masifa kamar wanda ke shirin dukan nurse d'in, diddii ta fahimci halinda yake ciki, tasan abunda zaijii, awannan lokaci, mutuwar matarsa sabo fill zaidawo masa, gabaki d'aya ya rikice, kamoshi diddii tayi tace, zo kayi hak'urii, in sha Allah, zata sauk'a lpy."
Sannnan tajuya takalli nurse d'in tace, kije kici gaba da aikinki." juyawa nurse d'in tayi cikin k'unar rai."
D'aure *hanna* sukayi yadda bazata 6ata musu aiki ba."
Dan su kansu sun gaji, tun safe ake abu d'aya."
Dan har ancanja wasu nurses d'in."
Sosai haihuwar tazo gadan gadan."
Wani irin ihuu *hanna* tasake, yace, ```yareeemahhhh``` da k'arfin gaske, wanda saida har wajen d'akin, ya amsa, dasaurii i'shaq ya miqe atsorace zai shige d'akin, kukan jaririn dayaji ne, yasashi tsayawa bbu k'akk'autawa, kuwa yaro yacigaba da tsala ihuu."
Juyowa i'shaq yayi ya kalli diddii yace, diddii ta haihu fa, d'aga masa kai kawai tayi, dawowa yayi yatsaya, yana jiran fitowarsu."
Wani k'atoton yaro *hanna* ta haiho, bbu yanda yabar mahaifinsa, sakk, gashi cikin k'oshin lpy, dansai kuka kawai yakeyi, itakuwa *hanna* tunda yaron yafito tajii kanta yafara juyawa, har aka mata stiching (dinki) batasan anyiba."
Jini tafara zubdawa Sosai."
Jinin yafita ajikinta wanda su kansu, doctor da nurses d'in abun yabasu tsoro."
Nan suka rufu akanta Dan suga sun tsaida jinin amma abun ya faskara."
Sunfii 30minute kafin yatsaya, nurse ce tashirya yaron, ta fiddashi su diddii suka ganshi, kar6an yaron inne tayi, tace masha Allah wannan d'a ai inaga ubansa balarabe ne, dan bbu yanda yabar larabawa, k'arasowa kusada ita sukayi suna kallon yaron, kyakkawan gaske."
Sai mutsul-mutsul yakeyi, cikin k'aramin tissue towel." nan dumfull d'insa ya bayyana, afili, subhanallh😍 mahaifinsa sakk, dasaurii hussentu takai hannunta wajan tana cewa, diddii kalli."
Nurse d'indake bayansu ne wanda takawo yaron, tamiqo hannu tace ku bani shii."
Yanzu za'a kaishi nursery, kar6an sa tayi sannan tajuya zata wuce, i'shaq yayi saurin tsareta, wanda shi duk rubibin kallon yaronda sukeyi hankalinsa yana wajan *hanna*, tsaida ita yayi yace, yajikin mahaifiyar yaron."
Kallon sa nurse d'in tayi tace, tana buk'atar jinine, yanzu muje nakai yaron sai agwada naka dana wannan, tanuna sadik, ko akwai wanda zaizo dai-dai."
Binta sukayi bayan ta ajiye yaron, taje gwada jinin, duk cikinsu bbu wanda jijinsa yazo d'aya da nata, dan jininta O+ ne, yana wahalan samu."
Nan suka shiga neman jinin, har dare yatsala ba'a samu ba."
Ahaka *hanna* takwana agalabaice, bbu yanda take, danko numfashima dakyar takeyi."
Marshall shida yaransa, camroon suka wuce, dan anyii rikici, sosai." Awani jiha, dake cikin camroon, yaje dubasune, amma daaa baiyii niya ba, zancan aurennnan ne yasa shi barin k'asar, yafake da zuwa nan, Awani hotel suka sauk'a."
Yana zama tunaninsa d'aya wani hali *hanna* zata shiga, idan tajii wannan zancan auran, haka kawai yakejin yana, closed to *hanna* dan duk wani lokaci da zai had'u da ita tunkafin ya aureta, har indai zasu had'u saiya jishi awannan yanayi."
Yana zaune afalon d'akin hotel d'in yaji ana knocking, idonsa arufe yace coming, shigowa soldier's d'in sukayi, dake dama tundaga floor din k'asa da sama, sunkmashi da sojojinsa, saraa masa yayi yace, sir time yana wucewa,
Shiru yayi nay'an minute kafin yamiqe yayi hanyar waje, shima yabishi abaya, kai tsaye asibitin suka wuce, suna shiga gabansa ya tsananta fad'uwa, dafe zuciyarsa yayi sannan ya lumshe idanuwa, bayan sunshiga, doctor's d'in dama sunsanda zuwansa, suka taryeshi, suna zagaya kowani sashi dashi, yagama duba patient d'in, wata nurse ce tashigo, takalli babban nurse dake bin marshall abaya tace, 6ta patient dinkinnan fa tanajin jiki, yanzu haka numfashinta yana sama-sama, d'ayan nurse dinne tace nikam narasa yadda zanyii, bayadda ban nemi jini kamar nata ba amma narasa,"
Marshall wanda yatsincii kansa da sauraren maganarsu, yajuyo yakallesu yace, kizo ki gwada nawa, idan yayi asaka mata."
Duk doctor's nawajan mamaki yakamasu, bai sake maganaba yanemi waje yazauna, babban doctor na hospital d'inda kansa yagwada, aikuwa yazo dai-dai, eban jinin suka farayi, laida biyu suka eba, ya tashi ya ja, hannun rigarsa, yasa bottle ya wuce zai fita, soldier's dinsa suka rufa masa baya."
Sanda yazo fita a hospital d'in gabansa ya tsananata faduwa fiyeda shigowarsa."
Tsayawa yayi yajuya yakalli asibitin, yafii 3minute yana k'are masa kallo sannan aka bud'e masa k'ofa yashiga motar, sukaja, sukatafii."

Batare da 6ata lokaci ba aka sakawa *hanna* jinin, laida d'aya kawai ta shanye, and'qura na biyun ta farfad'o."

*Kuyi hak'uri wallhy ciwon, k'in typing yakamani, irin sosai d'innan fa, kuyimun addu'a nayi nagama nahuta."*



To be continued

Ur' s Z33iiyyb3rw3r
*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

```I wish the hand of the clock would works faster than normal, Wallhy am morethan eager kawai naga nayi completing novel d'in nan, but soon in sha Allah, i know you too are eager, sweetys, Har nafara missing naku, before, Nima nagama nasami peacefully rest."```

```The most important person shike Samun the most, expensive gift, idan kaga anbawa mutum kyauta tabbas yayi deserving dinta ne."
Nidai nace u deserve more my *HAJJA*, kyautar wanna page for u and upcoming 4 pages." Allah ya raya mana ihsan."
Kece silar k'arfafamun gwuiwa, kinyi encouraging dina, tanks for everythings."``` *_ILYSM_*

.
================

Page 95
*
Wajen amare yau akayi walima dake gobenne yakasance d'aurin auren, hafsat da hameeda duk a bauchi akeyin komai, yayinda itakuwa intisar tana kano event kuwa anyi sunfii kala shidda, bbu wanda ango ya halarta aciki, duk da tajii zafii bbu yanda ta iya, dan tasan burinta yana gabb da cikawa, gashi gobe d'aurin aure bbu ango bbu alamunsa, ita ba waya sukeyi ba, balle tatambayeshi yanda yashiga, tunda wannan abun yazoma, kotakirashi baya d'auka."
Ta lula cikin tunani, kilishi dake k'are mata kallo, ta ta 6ata, dasauri tajuyo tana kallon ta, 6ata rai kilishi tayi sannan tace, mekike tunanine haka?" ko kinaso kiramene gobe d'aurin auren ki?" girgiza kai intisar tayi tace, Wallhy umma yaya yareema nake tunani, gobe ne d'aurin auren amma bbu shi bbu dalilinsa." ta6e baki kilishi tayi tace, ai gwanda daya tafii d'in idan yananan zai iya jaaa mana matsalla, kar mahaifinsa yaga yashiga wani hali yafasa, kuma kinsan irin sonda fulani ke masa, zai iya zuwa yagaya mata, karki ga kina matsayin jikarta, Wallhy saitace afasa." ajiyar zuciya intisar tasauke, kilishi tayi murmushi tace yawwa d'iyata, idan yaga dama kada yadawo sai aurenda wata d'aya mudai burinmu yacika ana d'aurawa zamusan yanda zamuyi dashi ya mance, wancan shashashar."
Sai alokacin intisar hankakinta yakwanta, tashi tayi tanufii wajanda k'awayenta suke."

Tunda aka fara zancen bikinnan afeeya ko leqo qafarta gidan batayi ba, su halima ma dan gudun 6acin ran kilishi ne, balle labba ta tabar k'asar gabaki d'aya."
Ummii batada bakin magana, ido ne kawai nata."


*Hanna* ta farfad'o, lokacin su diddi suna zazzaune ad'akin itada inne, da i'shaq, hussentu sadik yamayarda ita gida, dan zataje dabo abinci, dakuma kawo sauran kayanda ake buk'ata."
Da kallo *hanna* tabisu alamun rashin sanii, atattare dasu, dasauri diddi tamiqe tana sannu bodd'i kada kiyi garaje mana, kinsan jikinki bbu k'arfii, bayanta *hanna* take leqawa ko zata gano marshall, saidai akasinsa, wanda i'shaq ne, dawowa da kallonta wajan diddi tayi tace, ina yareema?"
Diddi tarasa wanne zatayi dan da'almu *hanna* tadwo hankakinta, murnar dawowa hankakinta zatayi?" kokuma bak'in cikin mantasu da tayi?"
Tasowa inne tayi tace, ki kwantarda hankalinki, kinga bakida lpy yareema kuma bayanan, girgiza kai tafarayi tana cewa, Wallhy yana nan, ga jininsa ana k'aramun nan."
Kallon juna sukayi, sannan i'shaq yace, ya'akayi kikasan jininsane? Bayan kina sume aka k'ara miki jinin."
Harara ta wulla masa, sannan tace jinin abunda nakeso d'inne bazan iya ganewa ba." bacin nasan duk duniya bbu wanda zai bani jininsa saishi."
Maganar ta doki i'shaq sosai, shiyasa yayi Shiru baik'ara cewa komaiba, don shi ya tabbataa sonta yakeyi."


Kuka *hanna* tafarayi tana cewa, dan Allah kuyiwa girman Allah kufad'amun yanda yake, rarrashinta sukeyi, sannan diddi tace wallhy bbu wani yareema Anan, dasauri *hanna* tad'ago tadubeta tace,

Please Login or Register in order to submit comment