Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayaya zakice bayanan to a'iina aka samo jininsa?."
Ku suwaye? Ni wallhy bansanku ba."

Basukai ga bata amsa ba, nurse tashigo d'aukeda jaririn aciki bed nasu tana turashi, zagayanta uku kenan, tana samu *hanna* bata tashi ba." k'arasawa tayi gaban gadon tace, kin farka, tafad'a tana ciro yaron, kar6eshi ki shayar dashi, kwanansa d'aya bai cii komaiba."
Dakallo tabi mutanen d'akin, ita dai bata ta6a sanin tanada ciki ba balle kuma har yaro, d'aga mata kai inne tayi tace k'ar6eshi, yaronki ne, saka hannu *hanna* tayi tak'ar6i yaron Sanda gabanta ya buga, kamannin yaron d'aya sakk da ubansa." kallon su tayi tace nashiga uku, dama inada ciki ne, yaushe?" k'arasawa kusada ita inne tayi, tace ki kar6i yaron ki shayardashi zanmiki bayani." riqe yaron tayi dakyau,"
Futa i'shaq yayi yabarsu ad'akin."
Tace wallhy bazan shayardashi ba harsai nasan ku su waye." wannan yaronkam ko ba'a fad'aba nasan yaro nane, kama bazata nuna k'arya ba."
Idankuma mafarki yakeyi plz kutasheni."
Ba mafarki kikeyiba injii inne, watanki takwas awajanmu, zaro ido *hanna* tayi tace wata takwas, kwarai kuwa injii, diddi, tun lokacinda muka tsinceki, bamu sameki cikin hankalinki ba, munsameki baki da bakima balle kiyimana bayani."
Kuka tasaka kawai tarungume yaron tsammm ajikinta, tana Kuka tace nagode muku, nagode sosai da kulawarku, samun mutane irinku sai an tona."
Amma dan Allah kada kubarii yatafii agarinnan wallhy yananan, dan inada tabbacin wannan jininsane," a lokacin i'shaq ya shigo da sallama yace." hasashenki bai zama gaskiya ba."
Wannan wani soldier ne yaji ana neman jini yabaki."

Murmushin takaicii *hanna* tayi cikin babbar murya tace, field marshall Abdullahi abdulaziz lamid'o, zaro ido daga nurse d'in har i'shaq dayanzu yaje yatambaya yayi, dan sunanda aka gyamasa kenan."
Takawarda kai gefe dan jikinta ciwo yake mata, k'arfin hali kawai takeyi."
Zama i'shaq yayi baida bakin magana."
Sai a lokacin hussentu ta dawo itada sadik, daukeda kayan tea ahannunta, had'a mata tea d'in akayi sannan aka miqa mata, wata iriyar yunwarda takeji tasakata shanyewa tass."
Sannan tad'an koma ta kwanta."
Diddi ne tace yaronnan yanajin yunwa, kibashi abinci."
Shiru tayi kamar bataji ba, Sanda tad'auko yaron tasaka mata shii agabanta."
Tashi *hanna* tayi tak'ar6i yaron, diddi tagwada mata yanda zatayi, kunya yasa ta sakashi cikin hijab, tafara bashi." runtse idanuwanta tayi tanajin son yaron akowani ga6a na jikinta, yafiii 30 minute Sanda tajii alamun yayi bacci sannan tacireshi."
I'shaq ne yashigo, yadubi *hanna* yace," ganinsa zai mun wahala sosai, yanzu tunda an sallame muje gida kiyi wanka, sannan mutafii wajansa."
Tattarawa sukayi suka koma gida, nan diddi ta wanketa itada yaron tass, cikin kayayyaki masu tsadar gaske, wanda i'shaq yasaya aka sakawa yaron."
Sai yamma liqis suka nufii hotel d'inda yake, amma tundaga compund d'inda yake furr akaqi barii su shiga."
Har magrib suna wajan, receptionist kuma sunki kiransa awaya, tundaga nan *hanna* tafara kuka."
Dakyar suka lallasheta takoma gida."

Washe gari kuwa, can nigeria sai shirye shiryen d'aurin aure sukeyi, kasancewar yanda abun zaifii sauk'ii yasaka, aka d'aura dukkanin auren akano."
Ababban masallaci da farko aka fara d'aura auren *hameeda da Ahmad sannan bilal da hafsat."
Ak'arshe aka d'aura auren marshall da intisar, bayan angama akayi reception." kowa sai tambayar marshall yakeyi amma kuma bbu shii."
Hakanne yasa mai martaba yad'aga waya, yakira shi, cikin zafii yace masa yanaso ayau d'innan yakwana agida, duk abunda yake yi, yabari yazoshi, and'aura aure, kashe wayar marshall yayi tsabar ba k'in ciki Sanda yayi kuka."
Nan danan idanuwansa suka kad'a sukayi jawurr."

Ba'adade dafad'a masa wannan maganarba, kawai saiga wani soldier yashigo sara masa yayi sannan yace, yalla6ai, tun Jiya wasu mutane sukazo wai sunason ganinka." yauma gashi sundawo."
Cikin zafii marshall yace, bazan samu damar ganin kowaba, yanzu haka and'aura aurena, kasanar nanda 30 minute zantashi zuwa nigeria."
Da toh ya amsa yafita yana tausyin agonnasa duk dacewa bawai yadad'e dashi bane, amma anfad'a masa bacewar matarsa dayake bala'in so."
Samun su *hanna* yayi yace, ku tafi oga, bazai saurareku ba, yana cikin wani yanayi, yanzu aka d'aura aurensa."

*Hanna* dake zaune Sanda tazube k'asa, dan firgicii, zata sake magana yayi saurin katseta ya wuce abunsa."

To be continued

Ur's

Z33iiyyb3rw3r
*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

_Your secound page, is here my *HAJJA CE* Allah yabarminke har abada, ke abun alfaharice ga al'umma."_

*Idan kuka kalli, late reponds Kuyi hak'uri massage suna yawa wallhy har taraddadin bud'e data nakeyi dan nasan abunda zan tarar, Allah nafiku k'aguwa na gama na huta." dan Allah idan kinyi magana banyi reponds ba amin uzurii." kunsan d'an adam ajizi ne, nima inasonku danna tabbatar masoyinka shike nemanka." ina sonku sosai."*

*Y'an group dina kad'an yarage ayankani yau." nadaiyi nahuta😒abarni nasha iska*

.

================

Page 96
*
Wani soldier ne yazo wajanda suke, fuskarsa ko annuri bbu, yace kufice awannan block d'in dan yallabai zaifuto yanzu, yana fad'i yana hucii, kukan *hanna* yatsananta, mitumin da tafii kowa kusancii dashi, shine wanda ake mata iyaka dashi."
Juyawa tayi kawai tana tafiya bawai dan tasan yanda take zuwa ba."
Suma Juyawa sukayi suka bita abaya."
Sanda tafice a hotel d'in tazube agate a k'asa tana rusa kuka, kamar wanda mahaifiyarta tarasu."
Duk rarrashinda yakamata sumata sunyii amma takiyin Shiru."
Inne tariqeta tana cewa habba bodd'i dan har yanzu *hanna* bawai ta fad'a musu sunanta bane, kitashi azaune ak'asa, kwananki biyu da haihuwa, hakan zai iya zama miki illah."
Kuka takara kecewa dashi tace, barni kawai nayi kuka, rayuwata gabaki d'aya bbu haske cikinta, da irin wannan rayuwar gwara na mutu ma."
Hussentu ne tamatso kusada ita tace, haba bodd'i wannan wace irin maganace?"
Kisan cewa kowani d'an adam da nasa jarabawar, kidubeni ki gani, aranarda aka d'aura aurena aranar mijina yarasu, sannan matar yaya i'shaq wajan haihuwa tarasu, mahaifinmu yau shekara, ishirin da biyu da b'acewarsa amma haryanzu bamu ta6a jin labarinsa ba." ki godewa Allah daya kasance kindawo cikin hankalinki, zaki iya fad'a mana k'asarku, kokuma garinku mu kaiki, idan kuma bazaki je ba, Wallhy zamu riqeki har iya k'arshen rayuwarmu."
Girgiza kai *hanna* tayi tace, mahaifana suna raye bansan wani hali suke ciki ba." shikansa wannan da nazo wajansa mij,,,,,,, ai bata k'arasawa ba motocin marshall suka fara futowa, kallo tabi motocin idanuwanta nazubda kwallah, kallon motarda marshall yake kawai takeyi."
Bak'in glass ne kawai, yarufe ko'ina, sanda motar ta6a cewa ganinta kafin ta kawarda ido, tak'ara fashewa da kuka, ba tafiyarsa bace tasakata, kuka A'a sai tunowa datayi dole yanzu su biyu ne awajansa."
Koda takoma ikonta yadawo kad'an awajansa, share hawaayenta tayi, tatashi tamiqe, tana tafiya wanda ita kanta batasan ina zataje ba."

Marshall wanda gabansa yayi wata mummunar fad'uwa a lokacin da akazo dabb gate d'in hotel d'in kuma haryanzu bawai gabansa yabar bugawa dasauri bane."
Wani tunanine yasa yace kai tsayarda motannan, afili kuma yace, nasan a mutum d'aya kacal nakeda wannan feellings d'in, buga goshinsa yayi yace kuma idanna ji, aiyakamata natsaya naduba. Shikad'ai yaci gabada magana kamar zaccauce," kallon d'an driver d'in yayi yace, kajuya zuwaga hotel d'in da muka baro." waya yayi yasanarda sauran motocin."
Juyawa sukayi, itakuwa *hanna* tana ta tafiya akan titin, hussentu nabinta abaya itada i'shaq, yayinda jaririn yake cikin mota shida diddi, dakuma inne, sadik najan motan ahankali yana binsu abaya."
Sunzo dabb da ita, *hanna* kuwa hankakinta baya jikinta balle taga dawowarsu, fad'uwar gabanda yajine yasashi cewa tsaida motan, hange yafaryi ta cikin glass ya hango wata yarinya tana tafiya tad'an wuce motocin da d'ayan tsallaken titin, jikinta tafiyarta sakk na *hanna* tsayawa tayi tariqe cikinta dake ciwo, dasauri hussentu da i'shaq suka k'araso wajanta, su inne dake mota ma suka fito suka nufeta, inne ce tafara magana, bodd'i kiyiwa giraman Allah kizo mutafii amota, jikinki bbu k'arfii."
Tsallaka titin marshall yayi yanufii wajan dan tabbatarwa idanuwansa cewa itace." tsayawa yayi akanta kawai hawaye yanabin idanuwansa, jikin *hanna* yabata ana tsaye akanta ana kallonta, gashi kamshin datafii so duk duniya ya mamaye wajan."
Hawaye tajii a idanuwanta wanda ita kanta batasan na mainene ba."
Bata d'agoba cikin muryar kuka tace, maiyasa kadawo?" kallonta sukayi duka suna tunanin kwakwalwarta, tak'ara samun matsala," Marshall bai iya Bata amsaba sai cewa kawai yayi, ya Allah idan mafarki nakeyi ka dawwamar mun da wannan mafarki har iya k'arshen rayuwata, sai alokacin suka d'aga ido suka dubeshi, kallon tsoro suka masa, wanda su atunaninsu balarabe ne, amma kuma ga hausa rad'al abakin sa."
*Hanna* na kuka tace nikam zanfii buk'atar mafarkinne amma kuma nafarka yanzu."
Honey please kafad'amun abunda kunnena yajii k'aryane, please kafad'amun bakayi aureba." Marshall yarasa mai zaice, ganin yayi Shiru yatabbatar mata da gaskene, wani kuka mai cin raii *hanna* keyi, tace mai yasa bazaka iya jiranaba?" alokacin su inne sun fahimci cewa mijinta ne, juyawa marshall yayi yadubii, soldier dinda wayarsa ke riqe ahannun sa yace, ban phone d'ina jiki yana 6ari yaciro yabashi."
Number d'in intisar yayi dialing tana d'auka yasaka a handsfree, itakuwa intisar farincikine yasaka tadauka dawuri, tattaro kawayenta tana cewa, bebs habibiy yakirani, ku matso kusa, itama tasaka a handsfree, duka k'awayenta suka matso danjin mai zaice, itakuma tayi hakanne, dan d'aga ajii, k'arya tayiwa k'awayenta akan aikine yahanshi halartan bikin, koda suka nuna cewa aibaya kiranta saita nuna musu, yana jejii ne Wajen aikii."
Shiyasa yanzu ta gayyataosu."
Da wata irin murya tayi sallama wanda yasa marshall murmushi, tace sannu da aikii, mijina, yawwa ya amsa, yagajiyar biki, sanda tayi wani farr tace, ai gajiya tanan, saika dawo zamu sauketa tare, maganar Sanda tayiwa marshall banbarakwai, yana godiya ga Allah dayabashi *hanna* mace mai kunya."

Jikin *hanna* duk yagama yin sanyii wato namiji ba d'an goyo bane, agabanta ma yake gwada mata yanda suke soyewa."
Kawarda kanta tayi hawaye yana zuba, a idanuwanta shikuma duk maganarda yakeyi idanuwansa yanakan *hanna*
yaushe aka d'aura auren?" yatambayi intisar, hmm d'azu ko 2hour's ba'ayiba, dan Allah kadawo yau wallhy ina bukatarka, murmushi yayi yace, dole ndawo yau, tunda burinki ycika, wata dariya tayi tace tabbas burina yacika, ok tom dama sak'o ne nakeson fad'a miki kanna iso, dan nasan idan na iso ba lallai nasamu damaba, hayaniya da kuma abubuwa, cikin kissina tace hakane kam my love inajii."
Intisar nasakeki saki d'aya, dasauri *hanna* tad'ago tana kallonsa, 😳intisar nasakeki saki biyu, intisar nasakeki saki ukuu, Wallhy banta6a sonki ba, bakuma na tunanin zansoki, koda nan gaba, Wallhy bazan ta6a son wata mace ba, bayan *hanna* murmushi ne yahad'e da hawaye fuskar *hanna* idanuwanta nacikin nasa kamar yanda shima nasa idanuwan ke cikin nata tunda yafara magana."
Idan kinsamu miji ayanzu and'aura miki aure, baki da idda, Wallhy sau dubu za'a d'auramun aure, aranar saina saki matar."
*Hannan* nandai ita kad'ai nakeso, kuma bazan daina sontaba har k'arshen rayuwata."
Yafad'a had'eda kashe wayar itakuwa intisar tun kafin yagama magana tasume, sai kqwayenta dasuka gamajin komai."
Suka ruga kiran umma (kilishi)."

Sukam su i'shaq anbarsu da kallon abun al'ajabi."
Ware mata *hannu* yayi dasauri tana tatashi tana guduu ta fad'a jikinsa tana, kuka kamar ranta zaifita, shima rufeta yayi ruff, yanajin, wani irin farincki."
Sunfii 20minute ahaka bbu wanda yagajii, dan kanta yana dai-dai zuciyar sa, tanajin bugawar zuciyarsa, ta lumshe idanuwanta."
D'ago kanta tayi tafara dukan k'rjinsa hannu bibbiyu, dariya kawai yakeyi dan bazai iya hanata ba."
Ta turo baki tace, da tafiya zakayi kabarni ko?" girgiza kai yayi yace duk yanda kike jikina yana bani."
Bazan iya barinki ba." yanzu harna kama hanyar airport najuyo jikina yabani kina nan."
Murmushi tayi tace, tun jiya nake zuwa wajanka, tanuna wani soldier wancan mummunan ya hanani ganinka, nida mijina."
Kama kunne yayi yace, amai afuwa cutie baisonki bane, nasake sabon soldier 's."
Sai a lokacin ta tunoda da su inne kunya takamata, tafara kokarin kwacewa yak'i sakinta, ahankali tace ana kallonmu fa honey, d'aga gira d'aya yayi yace ina ruwana."
Dakyar takwace tajuya garesu tace, diddi ga mijina nan, da fara'a diddi tace ainagani, yanzu muje gida amiki wanka sai kutafii naga yana hanya."
Tajuya ta kalleshi tace sune way'anda suka rik'eni tsawanon 8month, dinnan."
Marshall yabawa i'shaq da sadik hannu suka gaisa, yagaidasu diddi yace, yanzu please muje gida, sai muyi magana acan, sunfara, mota suka nufa."
Amota yake ce mata, cutie cikin yazube ko?" girgiza kai tayi tace, A'a jiya nahaihu, matarda kabawa jini a hospital niceh, murmushi yayi yace jikina yabani kina asibitin." yanzu ina gudan jinina."
Harara ta wulla masa tace ni kad'ai fa nayi nak'udar, marairaicewa yayi yace cutie kinsan da ina nan, da tare zamuyi, yanzu ina yake ya fad'a cikin zumud'i."
Yana wajan diddi bari mu isa."
Suna isa marshall bbu kunya yazage yatambayi d'ansa kawo masashi akayi." kallon yaron yakeyi kamar ya had'iyeshi dan soyayya, kamninsu d'aya, sai peck yake bawa yaron, inne tatsaya tana kallon yaran zamani."
Aka shigada *hanna* wanka." Sanda diddi tamata wanka tace, takawo mata abincii, tazauna takii, dan tunda sha tea takicin komai tun jiya."
Ai kuwa cin abincinta tayi sosai."
Tana gamawa marshall yaroqi akan dan Allah su tafii nigeria tare, yanzu yasan ana jiransa agida."

Dake bawani abuu sukeyi ba, yasa suke amince aka dugunzuma duka akayi nigeria."
Nan jirginsu yad'aga."

To be continued
*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

_Here is your third Page my *HAJJA CE* ILYSM_

*NOTE*_ _naga sakonninku dayawa nacewa wai baikamata marshall yasaki intisar ba, kusani cewa Allah yace ka aurii mace d'aya idan zakayi mata adalci, sannan yace idan kaza iya adalci zaka iya auren mata biyu, idan zaka iya yiwa uku adalci, ka auresu har izuwa hudu, amma kowanne sai ankira adalcii atsakani, d'ayanma idan baza ka mata adalci ba and'auke maka baizama wajibi ba, kusani cewa bawai sonkai bane yasa marshall yasaki intisar ba A'a saidan yana nemawa kansa adalci, baiso yatashi gobe kiyama b'arinsa d'aya ashanye, yasan bazai iya adalci bane yasa Bai cutar da itaba."_

.
================

Page 97

*
Hafsat da hameeda, duk gidan mai martaba za'a fara kaisu, dake ita hafsat mijinta d'an libya ne, shikuma G. Ahmad gidan yatashi." daga bauchi duka aka d'aukosu, sukayi kano."


Kilishi atsorace tajuyo jin irin kiranda, k'awar intisar take mata."
Tashi tayi dake tana cikin k'awayenta tana tambaya, manene yafqru haka aikin tsoratani."
Agigice tace intisar tasume." Saka hannu akayi, Kilishi tayi tace, wana irin tasume manene yasameta, ke kinada hankali kuwa."
Yarinyar tafara wallhy umma ba k'arya nakeyi ba."
Angonne yanzu yakirata waiya saketa saki uku shine......?" aibata k'ara saba, Kilishi ta danno wani ashar dan babban,,,,,,, ta mako shi, dan uwarsa k'arya yakeyi, ba'ahaifi kakar uwarsa bama."
Tana danna ashar tawuce zuwa shashin mai martaba, danko takan intisar batabii ba."
Yana tareda bak'ii amma taso shiga aka hanata."
Zuciyarta tana zafii tawuce shashin ummii, wanda ke zaune batasan abunda ke faruwa bama."
Tana shiga ko sallama batayiba, kuma gamutane ashashin y'an uwan ummii tasukazo, bikin ahmad, dake dan k'anwartane mamanshi da babanshi sunrasu tun yana yaro duka iyayensa larabawane, kasancewar and'auke marshall lokacin yatafii makarantar army, yasa tanemi abatashi, bawanda yamata gardama, aka batashi tagoyashi."


Tana bankad'owa tasamu ummii acikin en uwanta, tatsaya tak'ara musu kallo, sannan tace matsiyata(😳😳kajimun mata, wai su ummii ne matsiyata 😂😂😂kishiii) shegu munafukai, tajuyo ga ummii tace, munafukar uwa kin zuga d'anki yasaketa ko?" To wallhy kijira kiga abunda zaibiyo baya." idan wannan shrgiyar matar tasace, yarabu da ita har abada, yacire raii da ganin tama."
Tabisu da kallo wanda suka tsaya suna kallon ta, batareda sunsan abunda take cewa ba, idan kacire ummii, itakuwa bata tanka mata ba, har tagama tafice."
Har cikin ran ummii bawai tajii dad'iin sakinda marshall yayi bane, duk da cewa bason auren takeyi ba, amma kuma aitunda anrigada and'aura yakamata yayi hak'uri." ba tasan lokacin da taja tsaki ba, en uwanta suka tsaya kallonta suna tambayarta menene yafaru?" nan tashaida musu abunda marshall yayi, masu yawan cikinsu sunyi murna wasu kuma suka jajanta abun."

Bayan mai martaba ya sallami bak'insane zance yakai kunnensa, ransa ya bala'in baci, bai ta6a neman abu yarasa wajan yareema ba saiyau."
Tunfarko dayace bazai iya aurenta ba, bai maida masa yarinya bazawara ba."
Duk da cewa amatsayin budurwa take, bahakanne zai hana mutane ce mata bazawara ba."
Yakira layin marshall yafii sau 80 amma baishiga ba."

Intisar bata farfad'o ba sai da tayi 2hour's, da kuka tatashi, takasa magana, babu abunda yake cimata raii kamar yadda ko 2hour's ba'ayiba da d'aura auren yasaketa, dake ita kad'aine daga ita sai Kilishi yasa tace, Wallhy ummma gobe gobennen kije kiyi abunda za'akashe wannan yar banzan, Wallhy tamutu kawai, natsaneta, ta dalilinta yamun wannan cin mutumcin." wallhy umma shima kada ki kyaleshi, duk sonda nake masa yanzu najii natsaneshi."
Kawai kimin maganinsa, yadda bazai k'ara wulakanta wata mace ba."
Kilishi tace haba y'ata aikema kinsan wannan zaunannan zance ne."
Dole zan hukuntashi dai-dai da laifinsa, yanzu ki kwanta ki huta." futa Kilishi tayi tabarta tana, jin zafii da yanzu tana shirin zuwa wajan diner."

Ummii takira afeeya ta fad'a mana, afeeya harda ihu da tsallan murna." tana cewa wallhy yaya yareema yabiyani arayuwa, tsaki ummii taja tace kyajida shirmanki, sannan takashe wayan."
Da yamma aka kawo su hameeda da hafsat, nan shashin ummii aka saukesu, dan Kilishi bazata sauraresu bama."

Harda mama akawo amare tadubii, ummii tace, amayar yarona tana inane, danni tawajnta zanii."
Murmuahin k'arfin hali ummii tayi tace, kayya wana yaronki mai jawowa mutane abun fad'ah, kamar yaya mama ta tambaya."
Ummii tace ana d'aura auren yakirata ya mata saki uku."
Salatii mama tad'auka tama kasa magana, sukuwa y'an uwan *hanna* dake wajan dad'ii ne yakamasu."
Mama takasa cewa komai kawai tayi Shiru, fahimtarda ummii tayi Jikin mama yayi sanyii yasa tace, kinsan Allah bazan masa fad'a ba."
Lokacinda da suka yi shawarin auren bbu wanda ya shawarceni." ballantana natausheshi, gabaki d'aya nunawa sukayi banda iko." Sannan yanzuma daya gwada musu halinsa nima bazan tsawatar masa ba."
Allah yakyauta mama tace, sannan tace amma yarima baikyautba gaskiya."

Suna zaunane mai martaba ya aiko akirawo ummii, ummii tatashi tajeta."
Tana zuwa tasamesu zaune shida Kilishi da intisar wanda take ta shar6an kuka."
Da sallama tashiga, mai martaba ne kawai ya amsa bayan ta zauna yad'anyi y'an wasu, addu'oii kafin yafara magana, kinjii abunda yaronki ya aikata ko?" ya nuna mana mu bamu isada shiba, mu mahaifansa bazamu sakashi abuu yamana ba."
Kilishi tace wallhy yaron baida tarbiya kokad'an, bai d'auki iyayensa da daraja ba."
Murmuahin ummii tayi tace wallhy d'ana yanada tarbiya, bai ta6a gujewa umarnin d'aya daga cikinku ba."
Tajuyo ga mai martaba tace, kai kanka kasani tunda kake baka ta6a haifan yaronda yake maka biyayya fiyeda shiba, cikin kissa Kilishi tace ki gyara harshenki sannan Kisan agaban waye kike da sarkii kike magana."
K'arya kikeyi ummii tabata amsa tamijina nake magana, a waje yake sarki, tunda yarigada yshigo d'aki, nice sarauniyar, abunda bakisaniba shine, inada Lokacinda zanmasa magana amatsayin sa namijina ba sarkii ba."
Sannan kada kace yaro yak'ii bin umarnin ka, ko sau d'aya baka zaunardashi kace na umarceka daka aurii intisar ba, A'a jin magana yayi awaje wanda hakan yanuna kunbi ra'ayin yarinyar kenan, shi kuma ba'a nemi tasa amincewar ba."
Nina d'auki cikinsa wata tara nahaifeshi, kuma naraineshi, amma nima ba'anemi shawarata ba, duk wani d'a na halal yana kishin mahqifiyarsa, kuma d'ana maibin umarni nane, ko sau d'aya da annemi na zaunardshi na nusardashi da zai hakura, kai amatsayinka na mahaifinsa baka bashi umarni ba, nikuma matsayin mahaifiyarsa ba'a bani damata ba."
Ai inaga bai kamata anemeni danya 6ata muku ba, kenan yanzu ansan amfanina kenan?"
Tajuya takalli Kilishi tace inaso kisani ba'a ta6a canjawa tuwo suna, ni mahifiyace, wanda y'ay'anta ke alfahari da ita."
Sannan kijira agama bikinnan wallhy talllhy tunda kika furta cewa *hanna* bazata dawo ba har abada saikin fitoda ita, dan hakan yana nufiin da hannunki a6atanta." zan lamunci komai, amma wannan kam bazan lamunta ba, dansai kin fitomin da d'iyata tana fad'in haka tatashi tafice."
Mai martaba Shiru yayi yau yasan ankaita k'arshen makura, tunda ita bamai magana bace, jikinsa duk yabi yayi sanyii yasaka yashige d'aki, itakuwa Kilishi mutuwar tsaye tayi, tunda aka kawo ummii yau shekara 37 talatin da bakwai amma bata ta6ajin wata kalma mai k'arfi abakinta ba, sai su shari watanni bataji koda tarinta ba, amma yau wai itane ke irin wannan magan ganun?"
Kama hannun intisar tayi sukabar falon."


7:30 suka tafiii diner, zuwa 9:30 kuwa sundawo dan ummii tace kada su dad'e, aikuwa hakan akayi amare sunyi kyau sosai, Saidai tunda aka fara bikin kullun sai sunyii kukan rashin *hanna* sunsan tabbas datana nan bakin saiyafii haka armashi."

Afeeya wanda tahalarci diner duka sun tattaro sunyi gida."
Amaren na daki asashin ummii, yayinda su kuma ummii da y'an uwanta had'eda mama wanda a gidan zata kwana suna falo suna hira."

Tun 9:20.pm jirginsu su marshall yasauk'a, wani irin sanyin dad'i da ni'ima ne ke ziyartar *hanna* bayan wata takwas yau ita ce a k'asarta, gobenna saiya kaita wajan mamanta, ta fad'a cikin zuciyarta, dukansu sun lurada farin cikinda take ciki."
kai tsaye, gida suka nufa, sunakai 20minute kafin su isa, mamakine yakama su diddi ganin sunnufii gidan sarauta, abun sai al'ajabi yanzu da mummunan riqo suka mata fa."
suna zuwa marshall yadubii *hanna* yace cutie ki wuce shashin ummii, nasan yanzu mai martaba yana jirana, zanje najii yadda zata kaya."
D'aga masa kai kawai tayi."
Tanufii shashin ummii da zamud'in ta, suma suka rufa mata baya."
Gani takeyi kamar bazata isaba."
Tana zuwa da gudu tashige ko sallama bbu, su ummii mama da Anty Afeeya tagani wanda sauran bata tsaya dubawaba, dagudu ta fad'a kansu arzane suka d'ago suna dubanta, wani irin ihuu Afeeya tasaka ta rungumeta kamar zata tsagata, itama hannan ihuu tasaka, nan suka fasheda kuka, mama da ummii basuga fuskan ba, saida Afeeya tasaketa, da karfii ummii tace *hanna* d'iyata, aikaman akunnen mutanen gidan kowa yafito hadda amaren, ummii da mama lokacii d'aya suka rungumeta, suna kuka, su diddi suna gefe suna kallon abun al'ajabi, da wata irin soyayya wanda suka rasa afamily dinsu, wanda sai zuwan *hanna* tabasu shi."

Ummii nasaketa da gudu tayi wajan hameeda ta rungumeta suka fasheda kuka."
Tajuyo ga mama tashige jikinta, mama Shiru tayi tanajin d'umin y'arta ajikinta."
Sunfii 15mimute ahaka ummii tace, dukanku ku tashi muje muyi alwala, mu nunawa Allah godiyar mu."
Zuwa sukayi kowa yayi alwala suna nan aka gabatar da sallah raka'a biyu."
Ummii tace *hanna* ke meyasa bazakiyi sallah dinva?"
Muryar inne dasuke can bakin k'ofarne takatsesu datace, kwananta biyu da haihuwa aii."

Hamdala sukayi, sannan Afeeya tace ina d'annwa naganshi?" tana tare d'anta tana cewa narabu da d'an aro tunda nawa nakaina yazo, *hanna* nawasa da yatsunta tace, yana wajan yareema yayi shashin abba."
Ummii ne Tajuyo gasu inne cikin fara'a tace dan Allah Kuyi hak'uri mun barku awajan bbu komai sukace, nan suka shigo aka basu wajan zama had'eda kayan motsa baki."

Mama tace *hanna* ina kika shiga tsawon lokacii haka? Baki nemi gidaba, sunkuyarda kanta tayi tace mama bana hankalina, kwanana biy da dawowata hankalina, atare mutanen wajan sukace Allah yayaye."
Ta nuna su diddi tace su suka riqeni tamkar y'arsu ko ince fiyeda y'arsu, ba abunda nanema narasa."
Godiya aka shiga yi musu."
Inne tace bbu komai aid'a nakowa ne, nan aka shiga labarai da surutai, wanda kowa kana kallonsa zaka ga farinciki kwance fuskarsa, mamane tafara bawa *hanna* labarin irin halinda marshall yashiga, *hanna* kuka takeyi kamar ranta zaifita, jitakeyi wani irin soyayyar marshall nabin duk wata ga6a na jikinta, ummii ne ke aikii rarrashi tace, haba

Please Login or Register in order to submit comment