Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sameeha da wata mum suka rikeni muka fito, tunda aka fito dani waje ya kaure da busa da kide kide maroka ma sunayi aka Sani a wata makekiyar mota sanan jamaa aka fara shiga mota,duk yawan Mutanen da suke wajen saida aka debesu hada sauran motc.
Gidan me martaba sarki aka wuce dani aka kaimu wani part a gdn bayan anci ansha yan kawo amarya suka watse aka barni da friends dina dana Yaya Sumy muka kwana. Washe gari Maman Prince kuma fulanin sarki ta hada mana Royal eve akayi taro na gani na fada wata shegiya alkyabba aka bani nasa wajen da aka tsara mana a zama ma kadai abin kallo ne Prince ma acikin shigar alfarma irinta yayan sarakunan da suka amsa sunansu yazo ya zauna a kusa dani anyu budar kai mutane sun zubar da kudi kamar balkcn bahariyya ba matan sarakuna da yawa sunzo irisu matar sarkin zazzau, Kano, Gombe, katagun, bauchi, yobe da sauransu.
Bayan taro ya watse naje nayi wanka nasa wata atamfa Hilton dinkin yayi kyau sosai aka bani wata alkyabbar nasa bayan na gama shiryawa kanwar Prince Hanifa tazo ta kama hanuna mukaje part din sarki a zaune na samesu da Prince da me martaba da kuma mamansu ta zaunar dani a kusa da Prince kaina a sukuye na gaishe su me Martaba yayi gyaran murya ya fara mana nasiha me shiga jiki, bayan ya gama Maman shi ma tayi mana sanan sarki yace mu zabi kasashe guda uku da zamuyi honey moon idan ka zaba saika sanar dani ya bani kyautar set din sarkar gold ta wajen miliyan biyu nayi masa godiya sosai sanan ya cewa Prince ka dauki matarka Ku tafi Allah yayi muku albarka ya bada zaman lpy Prince ne ya fara mikewa ni kuwa da kyar na tashi nabi bayansa har bakin mota Hanifa ta rakomu ya bude min kofa na shiga motar mukayi sallama da Hanifa muka nufi dankareren gdn da Prince ya gina a unguwar AREA 7 a nan dutse, shi ya zana gidan da kansa a USA ya gano design din gdn, kuma nima iyayena sunyi rawar gani wajen hade gdn da lafiyayyun furniture's.
Toh Prince da suhailat nikam saidai nace Allah ya bada zaman lpy

ALAHAMDULILLA sai mun hadu a littafina me suna πŸ“πŸ“πŸ“Fatima BintuπŸ“πŸ“πŸ“πŸ“

For more info call 08067063932
Maman AyshaπŸ’–πŸ’›πŸ’œ



Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment