Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dam... shi Fahad ɗin ? Eh mana.!






*ANTY MMN TEDDY*
Tun da Umaima tayi shiru bata kuma cewa komai ba sai Fa'iza ce dake ta faɗin " Hello kina jina Umaima...Shurun da taji ne yasa ta katse kirar yayin da ita Kuma Umaima ta Juya tana jefar da Wayar Ɓarayi guda . Dafe kan ta tayi gami da kuncin ta tana maganganun sa dana Sauran Abokanan sa na dawo mata " Wannan da kuke gani Budurwar Fahad ce a wannan makarantan kar wanda yayi kuskuren... Umaima..! Muryar Hajiya Turai ne ya katse ta , wanda bata san ma ta shigo ba , gigif tayi tana buɗe idanun ta tare da amsa ta da" Na'am . Kallon ta tayi tana ƙare mata kallo baki ɗaya kana tace " Kina lafiya kuwa?. Murmushin yaƙe Umaima tayi mata don ta nuna mata babu komai nan tace " Momy komai lafiya , Waya muka gama yi yanzu da Fa'iza ,tayi mun maganan school shine hankali na ya karkata gare ta . Shiru Hajiya Turai tayi kamin ta dafa Umaima tana cewa " Kin san dai me Umair yace dake ko??. Maganan makarantar nan a barta , saboda Umair juyayye ne . Kallon Hajiya Turai Umaima tayi cikin ɗan damuwa Umaima tace " To Momy kuɗin da Kuka kashe mun fa ? Duka a barshi ?? . Eh ki barshi ... To shikenan Momy . Amma ina Son Na je gida na gaida su Umma na. Ai wannan me sauƙi ne . Ki kirya ina so Anjima kaɗan ki raka Ni ,zanje mall Nayi siyayya na dawo . To Umaima tace da ita kamin Hajiya Turai ta fice ita kuma tana komawa tare da bin lafiyar gadon tana ƙwantawa a hankali tare da tunanin abubuwa , ita dai har ga ALLAH bata jin Zata iya rabuwa da karatun ta akan zancen Umair. Wannan ma fa ɗan rainin hankali ne , ban da rainin wayo da tunani har ya manta abubuwan da yayi mun a baya tun yanzu ya fara sharaɗɗa mun wasu zancen wofi ?. Taɓ to yanzu ina ga yaganni a cikin gidan sa abin ai sai inda ya kai kuma.
***


Kaman yanda Umaima tace zata taho gida , hakan ya faru , a tunanin Hajiya Turai gidan ne kawai a zuciyar ta , bata san zuciyar ta tunanin makaranta bane. Don tana komawa A washe gari ta shirya tsaf tayi na makaranta . Rayuwarta kawai take yi , don ita sam ta fara mantawa da Umair a ƙwana biyu ,sai dai wani abu ɗaya da yake sakata tunawa dashi shine ,duk idan Fahad yazo gareta ko ya jata zuwa wani wuri babu wanda take tunawa face Umair , a haka ta cigaba da rayuwar ta . Wanda duk shige da ficen ta har dawowan ta Umair ya sani . Bai tada hankalin sa ba ,sai da yaji labarin Fahad. Wannan yasa shi kirar Ammie Hankali tashe yana tambayar ta da izinin waye Umaima ta koma Makaranta??. Ammie da taji abun nashi yayi ƙamari ne yasa ta cewa " Au Har Makarantar ka kashe mata ne Tun yanzu yanzu ??. Sai a sannnan ya tuna da basu yi maganan da ita ba , wannan yasa shi datse kirar cikin sauri yana kirar Hajiya Turai .




Salallami Hajiya Turai ta ɗauyi tana faɗin Umaima ce ta koma makarantar?? Bari zan kirata yanzu . Gida fa tace zata koma ,tana Son ganin Umman ta. No Mom Kar ki kirata Bari zan dawo.! Zaaakk kamin Hajiya Turai tayi maganan ne taji ya katse kirar . Cikin sauri ta fara lalaubar lambar Umaima amma baya shiga . Kaiwa da komowa take tana faɗin " Umaima wai me take nema da zafi ne akan wannan karatun nata?? (Kuji mun Rainin hankali ma🙄) .Haka Ta cigaba da kirayen wayann ta amma amsan daya ne Wato Is not reachable at the moment .


***


Fa'iza ce ta taɓo Umaima tana ce mata a hankali " Fahad ya shigo . Saurin ɗagowa daga rubutun da take yi tayi , tana kallon Fahad da yake kurɗaawa ya iso har zuwa inda take , ba tare da yayi duba ga lecturer ɗin tasu ba.




A gaban su ya tsaya yana kallon Umaima wacce itama shi take kallo . Yau me ake maku? . Kallon Fa'iza tayi kamin tayi masa magana yana juya yana kallon Whiteboard din da lecturer Ke gyefe . Ohk taso mu tafi sai na koya maki . Miƙewa Umaima tayi tana kallon ɗaliban da lecturer a ido ido ,amma da mamakin ta sai ji tayi lecturer tace " Dr Fahad Hala dai wannan itace Surikar shiyasa kake cika zaƙewa da yawa?. Dariya Ɗaliban suka yi har da shima Fahad ɗin kana ya rike da jakar Umaima suka fuche daga hall ɗin . Mayafin Abayar ta ta gyara tana kallon gyefen ta , wani irin yanayi ne taji ya kamata , tsoro ne ko meye taji yana kai kawo a zuciyar ta . Bin filin wurin tayi da kallo , ganin motoci ne wanda dama suka zama ana aje su a wurin don gaban hall ɗin tasu fili ne sosai da ake aje kowani irin abun hawa .ji tayi gaban ta na faɗi. Wanda ya sata ja ta tsaya . Saurin kallon ta Fahad yayi tare da cewa " Menene?? Meke faruwa??. Cikin rawar murya ta kalle shi tana cewa" Ina ji a jiki na kamar Ya Umair yana wurin nan??. Kallon ta yayi kamin yace " Waye shi??...Kamin ta bashi amsa ne taji Ƙamshin sa ya durar ma ko ina na wurin . Can ɗan nesa ta kalla , ganin sa tayi ya fito daga cikin moton sa , wani guard ɗin sa ne ya biyo bayan sa , ammma sai kuma taga ya ja ya tsaya , shi Kadai Umair ɗin na takowa zuwa inda suke . Jikin ta ne ya hau rawa karrr³ , hannun ta tasa tana ƙoƙarin Amsan jakarta , amma sai Fahad ya riƙe jakar yana mata wani irin kallo na rashin fahimta .


Ƙari kowa zuwa inda suke Umair yayi ba tare da ya sauke bakar gilashin sa ba , fuskar sa a murtike take haka girar sa da yake a haɗe , sam baya tsammanin zai iya duba da inda Fahad yake tsaye , wanda ko ba'a ce masa ba ,yasan shine wanda Umaima take kokarin hada soyayyar shi da nata . Taho mu tafi.! Shine Abun da Umair yace da ita yana miƙa mata hannun sa . Idon ta na ya raina fata ganin Yanda Fahad duk da ya san waye Umair a kallon Farko ,yasan matsayin sa a yau Nigeria ,amma kun san So me sanya ido ya makance ka faɗa ko wani halaka , cikin wani irin murya yace " Me yasa zata bika ? Kaine wane??.




Wani irin murmushi Umair yayi yana kallon Fahad kana ya juya yana kallon Umaima dake ce masa" Yaya na ne??. Taho mu wuce.! Kallon Fahad yayi kamin yace " To duk wannan ɓarin jikin na mene? Kawai saboda ya kasance Yayan ki??. Kiiiiii...! Umair ya daka masu uban tsawa . Wanda yasa Umaima saurin rabuwa da Fahad tana barin masa jakar ta nufo inda Umair yake , Hannun sa ta rike Muryar ta na rawa tace " Yi haƙuri muje don ALLAH. Wani irin kallo yabi Fahad dashi kana ya riƙe hannun Umaima da ta riƙe gammm don tsoron abin da zai iya biyo baya . Saurin nufar motocin sa tayi . Yayin da securities din sa suka yi saurin buɗe masa moton Umaima ne ta fara shigewa kana ya shigo .




Hankalin Umaima gaba ɗaya ya gama tashi , hawaye ne suka fara zubo mata , kawai sai ta fara kuka a hankali tana kauda kan ta izuwa kallon ɓarayin window side . Duk da ransa a ɓace yake amma kukan ta ji yake na fi komai taba masa zuciya . Laptop ɗin da yake operating don har yasa a binciko masa waye Fahad ? Waye uban sa? baya Son sanin meye tsakanin sa da Umaima?? Don shi ba ma kawo kmane ya Gani da idanun sa . Rufe Laptop din Yayi yana sa hannun sa tare da rungumo ta jikin sa . Sam bata ki ba , don gaba ɗaya hankalin ta da natsuwar ta ta rasa shi a lokaci guda . Shafa bayan ta yake a hankali alamun rarrashi duk da shima baiƙi ya samu mai rarrashin zuciyar tasa ba a halin yanzu . Sorry I'm verry Sorry dear , Na taɓa maki bugun zuciyar ki , na raba ku a lokacin da baki So ba ko??. Saurin ɗagowa tayi tana kallon sa , sai kuma ta kauda kan ta zuwa ƙasa tana kallon dogayen yatsun sa . Hannun ta tasa tana ɗaurawa saman nasa tare da kamasu tana haɗewa da nata , Wasu marayun hawaye ne suka fara sauko ma kuncin ta wanda suka fi na baya , a hankali ta buɗe baki zata masa magana ,Amma sai zame hannun sa ɗaya yayi yana daurawa a saman laɓɓan sa . alamun baya Son jin wani Magana daga gare ta. Tsayawa tayi tana kallon sa na yan daƙiƙu yayin da shi kuma ya juya kan sa gyefe yana kauda kallon sa daga gareta .




Sakin kuka tayi a hankali , gani tayi ya juye mata ,ya koma mata tamkar ranan da ta fara ganin sa a rayuwar ta .


Ƙara rushewa tayi da wani irin kuka tare da juya kan ta itama gyefe tana fara tunanin rayuwar ta da Umair a yanzu?? Tabbas tasan zaman gidan sa dole? Amma kuma bata san da wani irin salo a yanzu zasuyi rayuwar tasu ba . Momy don ALLAH ki fahimce Ni a rabani da Ya Umair wallahi mugu ne.! Juyowa yayi yana kallon ta , wanda ya sata saurin rufe bakin ta don maganan Zuci ne ya fito sarari ba tare da ta sani ba ... Hawaye ne ya cigaba da ƙwaranya mata . Tana kallon sa yayin da shima ita yake kallo , kallo ɗaya yayi mata ya fahimci duk wani abu dake cikin zuciyar ta . Tsoron ƙwana dani kike?? Ko kuwa tsoron Sex dani kike? This time around , Komai nawa kisani ya sha banban da ta da . Ki shirya amsan ko wani irin hukunci daga gare Ni . Kin san meye?? Kamin na taho nan , Wurin Baba na fara zuwa , Kar ki tunanin guduwa ta ko wani Faraga ba zaki samu dama ba, Kin san meya sa?? Hajiya Turai.! Wani irin kallo Umaima take masa , me take So dake dani?? Bana ce ba , don bazance ban san komai ba , na sani...!!!! Saurin girgiza kan ta Umaima tayi wasu irin hawaye na mata ambaliya , A'a Ya Umair babu ....ba babu Komai .! Motsa bakin sa yana alamu zayyi magana kawai sai yaji tasa hannun ta duka cikin ruɗewa da tashin hankali ta faɗa jikin sa tana rufe bakin nasa , kuka take sosai har idon ta na kumbura saboda zuban ƙwallah ...!








*Littafin the sexy boss na kudi ne , don ALLAH kar ki karanta idan baki biya Ni ba.. Regular group₦300 vip group₦300 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan Numbobi 08081202932*
*Littafin THE SEXXY BOSS na kudi ne , Regular group ₦300 VIP group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko MTN card ta wannan number 08081202932*




Yanda yake take kukan ne yayi matuƙar karya masa zuciya ,duk da dama Soyayyar nata ta samu gurmi ta musamman a zuciyar ta ,hannun sa yasa yana ƙara haɗawa da nata a hankali ya furta " Ba haka bane Umaima? Ai haka yake , Ni nasani ko baki faɗa mun ba, nasan Momy Tana Son Aure na dake ne saboda ta cimma wani buri nata , sannan matsalar ma abun dake daɗa sa ma zuciya ta damuwa shine ke.! Yayi maganan yana lumshe lulun idanun sa tare da cijan laɓɓan sa na ƙasa . Cike da wauta Umaima ta riƙe hannun sa , Ya Umair kayi haƙuri , Momy zata sauya , amma wallahi a karon farkon nan dana taho gidan ka ba ita ta turo Ni ba , Kawai Ni ne nazo kaji Yah Umair...ware manyan idanun sa yayi yana zuba su akan fuskar ta kana yace " Kinji matsalar, Umaima kece.., Baki taɓa ce mun kina Sona ba , ko alama kin san ya zuciya ta take ji kuwa?? Sauƙin ta ɗaya idan na kalli cikin idanun ki anan kaɗai nake ganin Soyayayya ta , ga shi nan , anan ne kaɗai Bakya iya ɓoyemun . Sada kan ta ƙasa tayi tana yin shiru , jin Muryar sa tayi yana cewa " Faɗi mun duk abun dake kike so ,Zana baki Umaima , Kuɗi??? Kallon shi tayi saurin yi , a zuciyar ta tana cewa" oho a inda ya aje Ni kenan,so kuɗi tun da sanadin kudi komai ya faru tsakani na dashi . I love You ,ina Son naga na kasance dake har abadan abada . Faɗa mun ko nawa ne zan baki tun daga kan dala biliyan zuwa sama . Ƙurrr yaga tayi masa da ido , tana kallon shi ƙwallah na taruwa a saman ƙwarmin idon ta .




Girar sa ya gyara mata ,alamun ita yake sauraro . Shi dai Umair baiyi aune ba yaji Taji Dunkule hannun ta ne tana haɗa yatsun ta tare da bugun cikin sa . Ashhh. Ya saki ƙara don yaji zafin bugun nata . Dari ya ta sheƙe dashi tana yin baya , har da kama ƙwallah na mugun ta . I luv you.! Ya furta yana kallon ta , kallon idanun sa tayi kana ta saki murmushi tana cewa " Dama ashe Soja yana jin zafi idan an bige sa??. kamin yayi magana ne ta kuma cewa " Ina Son zama dakai Ya Umair, Ka san menene?? Shiru yayi mata bai ce mata komai ba sai dai idanun sa dake akan ta ,alamun yana sauraren ta . Ƙwallah ne ya fara gangaro mata , hannun ta tasa tana gogewa kamin ta motsa laɓɓan ta tana mai cewa "Aduk lokacin dana zauna Ni kaɗai bana tunawa da kai a zuciyata . Amma a duk lokacin da wani ɗa namiji yayi rabe Ni ,sai naji wutar Soyayyar ka a zuciyata. A da baya na ɗauka Wauta ce , kuma nayi kokarin hana zuciya ta faɗawa soyayyar ka ,amma ta gagara . Ina Son ka ya Umair...Ta ƙare maganan tana riƙo hannun sa . Hannun sa ya ware mata alamun taje garesa . Da sauri ta faɗa jikin sa tana jan shashsheƙa . Ina ji kaman Soyayya ta tafi taka?. Hannun sa yasa yana rufe bakin ta , kamin yace " Kar ki ƙara faɗin haka ba daidai bane , Ni dana zabi na bar komai na sa boda ke , na daina Kula kowacce mace ,amma ke Baga shi ba.




Shiru yayi da faɗin maganan don ji yayi zuciyar tasa na masa wani irin harbawa tuno da Fahad. Ɗago da kan ta tayi ba tare da ta tashi da jikin sa ba tace " Amma fa har yanzu Ban haƙura da kyeta mun mutunci na da kayi ba ,babu imani bare tausaya wa . I'm verry Sorry dear . Maƙale kafaɗa Tayi tana mai da kanta tare da lafewa jikin sa . A haka sam ta mance da wai a mota take , don mota ne suke cikin ta wanda ta amshi sunan ta , baka ko jin hayaniyar sauran abun hawa ,yanda kasan tana inner room din ta . Tafiya ce mai tsawo suke yi , wanda ganin ba zai iya komawa Abuja a mota ba yasa shi sawa a taho masa da jirgin yawo Helikwafta .




Ji tayi yana taɓa fuskar ta a hankali yana maida ita tare da ƙwantar da ita . Saurin buɗe ido tayi tana kallon gyefen da gyefen ta , wanda taga pilot Yana ƙoƙarin tada jirgin . Har ya dauke ta daga moton bata sani ba don barci ya ɗauke ta a jikin sa. Saurin kallon sa tayi cike da mamaki tace " Yah Umair Ina Zamu je?? . Ta ƙare maganan tana kuma juyawa tare da ganin Jirgin na sama dasu . Juyowan da zata yi da fuskar ta ne ya haɗe da nashi , haɗe bakin shi yayi da nata yana tsotsan harshen ta a sukune yana sa hannun sa tare da shafa gadon bayan ta , kasa motsi tayi don ji tayi gaba daya ya sakar mata da duk wani laka nata . Kusan mintuna biyar suka debe a haka kana ya zare bakin sa daga nata tana jan dogon ajiyar zuciya tare da sauke numfashi a hankali . Murmushi ya sakar mata wanda har hushiryar sa na bayyana kana cikin Muryar sa ta ingarman namji soja tsayayye , ya furta " Abuja nan da 1 hour Zamu sauka . Cox naga kinyi gaji da yawa. Bin sa tayi da kallo , cike da mmki kana ta komawa ta kwanta tana yin shiru , first a Rayuwar ta na duniya wai yau itace a jirgi . Ohh Umaimatuwa kenan😂 .


Kusan 50mins taji jirgin na ƙasa a hankali har ya ida sauka ,wannan ya alamta mata cewan sun fa iso . Hannun ta ya kama yana kallon ta cikin murya mai kama da rarrashi yace " Zaki iya sauka? Ko na...a'a zan iya ,ta katse shi cikin sauri tana miƙewa tashi daga jikin shi . A hankali ta sauko shima yana bin bayan ta . Hannun sa yasa yana rungumo ƙugunta tare da manna ta da jikin shi , kallon sa tayi tana Son raba jikin ta da nashi ,ganin ta a wani gida na daban ,ga kuma securities da sauran masu tsaron gidan da bata san ina ne ba . Ji tayi duk a takure rungume tan da yayi da jikin sa . Shi kam bai ganin yayi wani abu . Nufar wani apartment suka yi , wanda sai a sannan a hankali cikin sanyin Muryar ta tace " Ya Umair ina ne nan? Ai ba gidan Daddy bane nan . Hannun sa yasa yana kama subu subun kumatun ta ,yana murmushi tare da cewa " Calm down my Swt Ccbr . Wani kallo ta watsa masa na ita yake zolaya . Dariya yayi yana cewa" Our Swt House . Nan zamuyu rayuwa Ni dake , with ur kids , nasan they will come verry soon inshallah . Murmushi Tayi cike da jin kunya tayi kasa da kan ta ,don taga yana mata kallon kasa kasa. Wanda duk sai taji yarrrr. Nufan Wani falo Sukayi da babu komai sai glsses da suka kewaye ko ina . Gani tayi kamin su karasa basu danna ko ina ba wurin ya bude kaman hanyar kofa , suna shiga ya koma ya rufe , Ohhh wato da Ƙamshin jikin mutane yake aiki kenan.? Kallon ta Umair yayi kamin yace " Me kika ce??. Saurin dawara tayi don bata san maganan ciki ya fito sarari ba ,tace " A'a ban ce komai ba. Ohk taho mu shiga daga ciki yayi maganan yana kai hannun sa gareta . Saurin ja baya tayi tare da cewa " A'a Su Ammie fa basu san zaka kawo Ni ba. Huuuuu Sauke numfashi yayi tare da furxarwa yana kai hannun sa tare da shafa sumar kan sa.. tun da sun hana Ni mata na ,basai na kawo ki nan muyi amarcin kwana ɗaya ba ,idan kin koma sun gan ki da juna biyu sai Kice nawa ne sai su dawo mun dake dole ,daganan mu tafi honey moon da suka.....Ya Umair.!!! Ta kira sunan sa cikin tsoro da ɗaga murya na mamakin furucin sa gare ta ........










*MMN TEDDY*
*Littafin THE SEXXY BOSS na kuɗi ne , Regular group₦300 VIP group ₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,ko katin MTN ta wannan number 08081202932...idan kuma ki ka karanta baki biyani ba keda ALLAH*




Tare da ja baya kaman taga Abun tsoro , A hankali ta furta " Don Allah Ya Umair ka maidani gidan Daddy , Don Allah na roƙeka Pls ya Umair. Yanda tayi maganan ya kusa saka sa dariya amma sai ya mai da dariyar sa ciki yana mata kallon da ta rasa gane manufar sa . Kinji fa Wai Yaya...Ni kike kira Da Yaya a matsayi na na mijin ki , Kina ji Pls Mah wife ki bani dama just na kwana ɗaya , zan miki wani Abu mai daɗi da aƙwana ɗaya zaki sauya mun wannan sunan da kike kirana irin yanda su Fareesat ke kirana dashi kema a matsayin na Matana ace kina kira na dashi?? Kai kaiii ina ina ina??? Ya maimaita maganan kusan sau uku . Cikin sauri cike da tsoron sa kar yayi mata abun da take tsoro tayi saurin matsawa kusa dashi tana cewa " Zan sauya To , Wallahi zan sauya faɗa mun wani Sunan kake So ,Amma Ni dai don Allah ka maidani gida Ya Umair ". Shikenan ta maimaita ". Yayi maganan tare da kallon Gyefen Window Glass ɗin dake Kusa dashi. Kwana Biyu zamuyi ina koyar dake daga bisani sai na dauke ki na maida ki wurin Su Momy ya ƙare maganan tare da juyawa yana shirin tafiya , da gudu ta bi bayan sa tana sa hannun ta tare da maƙalewa a bayan sa tana sa hannayen ta duka biyun tana rungume sa ƙaammm , Cak ya ja ya tsaya ji yayi wani abu mai kamar shocking na kama tun daga ƙafafun sa yana circulating blood nashi har zuwa kan sa . Lumshe ido yayi yana jin tamkar suyi ta tsayuwa a haka kar ta cika shi , har sukai Wani yammacin a haka a tare . Cikin dadɗan Muryar ta wanda Fareesa ke cewa " Shine kaɗai mai daɗi a tare da Umaima bayan shi ita bata ga Abun da Yah Umair ya nace ya kuma maƙale mata ba . A Hankali yaji Muryar ta tana furta " I'm sorry My champ . Ba zan sake ba ,wannan yayi maka ko a sauya?. Lumshe lulun idanun sa yayi yana ware su . Wow'. Shine kalmar da ya furta , kamin yayi magana ne tayi saurin cika shi tana juyowa tare da fuskantar sa .




Hakan yayi ko? To mu tafi gida. Habawa my Bul bul , ki bari mana ki ci abinci ki shirya a gidan mijin ki ... Juyawa tayi tana bin kanta da kallo a tsakankanin glsses ɗin dake gaban su da bayan su . Haɗe girar sama da ƙasa tayi tana cuno baki , a sarari ta furta ,tabbas kuwa naci sunana Bul-bul gani nan can ƙasan ka , ga kuma kiba mai muni . Buɗe baki yayi dariyar da yayi ta danne ta ya kuɓce masa , haushi ne ya kamata , saurin juyawa tayi tana kallon sa kamin ta kai hannun ta tana riko nasa , meye na kauda kai kuma Yallaɓai.? Fuskance Ni kayi dariyar ka ,nima zan rama ai . Ayya Sorry My Swt Ccbr . Au ka ƙara ko?? Kace swt Tomato Mana kawai . Tayi maganan tana juya masa baya tare da sa hannayen ta tana naɗewa a ƙirjin ta . Ji tayi ya ɗaga ta cak yana sama da ita .wayyo Umma na sauke ni , Please Yah Umair Ka sauke ni ,juyi da ita yake yi bai tsaya ya saurare ta ba , sai dariya da yake mata ,wannan yasata saurin ƙanƙanesa itama tana Dariya . Yana ɗauke da ita suka nufi Ciki ,inda anan ne taga komai complete falo , kujerun ba royals bane ba , Amma sunyi masifar ƙyau tafi ganin su a season Film na ƙasashen Turai . Sauke ta yayi a hankali tana bin falon da kallo cikin burgewa take furta " Kai Falon nan yayi ƙyau sosai ,Wow my champ yayi ƙyau , Tamkar ba'a gida Nigeria muke ba . Waya faɗa maka Best colour ɗina dana ke So .! Tayi maganan tana kallon Yanda akayi Adon Falon da Pich and Ash colour

Please Login or Register in order to submit comment