Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


D'AN DAKO

NA UMMI AYSHA

MARUBUCIYAR.
AL'MAJIRIN GIDANA
AURAN YARINTA
WAYA CAN'CANTA
AURAN USTAZ
ZAMAN TASHA
TAYA ZAN GANESHI.
AN NOW
D'AN DAKO.

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM.

YA ALLAH KAMAR YANDA KA BANI IKON FARAWA LAFIYA KASA IN GAMASHI LAFIYA.

NA KUDINE AKAN FARASHI MAI SAUKI.

DARI UKKU KACAL.

KATSINA STATE.


""Katsina garine daya hada jinsin mutane daban daban yan kasuwa da yan boko wayayyi mutane ne ga karatun Addini garine mai yalwar mutane dakuma karrama bako mafarin takenta da KATSINAWA DIKKO DAKIN KARA KUNYA GAREMU BADAI TSOROBA.

Tana da yalwar unguwanni masu dumbin yawa na talakawa dana masu kudi.

G.R.A
Kyakyawar unguwace data tara hamshakan masu kudi yawancin su duk yan bokone sai yan kasuwa unguwace da baka ganin gilmawar mutane barkatai sai dai kowa yazo da abun hawanshi ya wuce sahoda shimfidaddan titine daya wadatu da kwalta da tatafi dodar gefe da gefen titin kuma wasu irin shukokine masu tsawon gaske da sukayima gidajen dake jere reras cikin unguwar kawanya hakan yasa titin yakasance mai masifar kyau da daukar hankali bakajinkomi sai na isakan dake kada shuke shuken .

Tsaye nayi ina karema tafka tatkan gidajen dake unguwar kallo ka na gilgiza tare da cigaba da tagiya ina tinanin kamar bazaa mutuba da mutane ke gina irin wannan katafaran gidajen.

Wani wawan burki naja gajin wani tamfatsetsen gida dayafi kowane gida akan titin kyau da tsaruwa tindaga get dinsi da kalar penti dake garai da irin furanni da aka zagayeshi da su.

Jin ana kakaniyar bude babban get din ne yasa nayi tsaye danba idona abinci.

Wani dattijone mai kimanin shekaru hamsin zuwa da biyar ya wangale get din da kyal .

Inda wata jar mota kirara FERARI ta sheko da gudu takusanyin kan yatsun dattijon nan da gudu ya kauce tare da tsayawa gefe yana maida numfashi.

Ganin motar ta wuce batare da tatsayawaba yasashi gilgiza kanshi tare da bude bakinshi yace Allah ya shiryaki AMNAH yasa kifara ganin daraja manyanki som halinki ba dayaba da mahaifiyarki babu abunda kika rage na mahaifinki.

Dakyal yasamu ya maida get din ya rufe tare da zama akan dan bencin dake gefe yafara saita Radio dake hannushi.

Wata matashiyar budurwa da bazatafi shekaru 17 bace ta fito da sauri daga cikin faskeken gidan ta nufoshi tanafadin .

"Baba Madu wai Amnah fita tayi ne?

Da sauri ya ajiye radio ya mike tsaye yace.

" eh hajiya Amal tafita badanjimawaba ina kwana."

Kanta ta gilgiza tana Aro fararan idanuwanta tace baba da allah kadaina gaidheni nifa jikarkace wallahi mantawa nayi bangaishekaba ina a rudeme tare fa Mamy tace zata aikemu yo sayayya kasuwa wai ita bazatab taita karo da talakawa tafison super market kuma taya za'ayi asaida kayan da Mamy ke rabawa cikin Watan Ramadan super market?

Murmushi Baba Madu yayi yace
"To kuje inda takeso mana Hajiya Amal.

Kanta ta dago ta kalleshi tace baba kayan fa da yawane irinsu masara gero dawa acca Alkama baba kasan sai kasuwa.

Shuru yai sai murmushi dayaketa zuvawa batarr dayace komi ba Dan yana ganin matsalar suce ta guda bai kaqta ta shafeshi ba.

Juyawa tayi cikin gida ranta amatukar bace .

Kallonta yayi ya gilgiza kai tare da cewa allah kenan yayoku ciki daya amma ya bambanta halinku kekuma sai kika rakko na mamanki ita kumabta dauki na babanku.

Kai tsaye babvar kofar dake zagaye da glass din palon ta bude tashiga babban falone sosai yasha blue da gold na kujeru da labulaye da carpet bakajin kominaciki sa karar Ac da wani irin sihirtaccen kamshin tiraran Wuta mai masufar dadi.

Zama tayi tare da dafe kanta tana jin bacin rai na halin da yar uwarta take nunama talakka.

Jin kara tafiya daga saman benen yasata saurin dago kanta inda ta saukesu fess akan kyajyawar fuskar magaifiyarta dake sakkowa fuskarta cike da alamaun mamaki.

Kyakyawar macace fara sol da ita daga ganinta buzuwace ko balarabiya sanye take dawani dakeken lace maroom da kyanshi ya usa fallasa asirin tsadarsa yan kunne gold je akunnanta hannayenta sanye da manya manya zobuna gold maeu masifar kyau da tsada.

Cikin daddadan magaja ta sakko kasa tare da zama kusa ea Amal tasanya hannunta ta juyo da habar Amal din tare da tambayar.
"Lafiya bakuje ba tare bayan naji karar fitar motar Amnah"?

Ido cike da kwallah tace Mamy ta tafi ta barni nason ta tafi yin gaban kanta ne ai dama batayi niyyar zuwa kasuwar nan ba som taya za'ayi tace sai super market abinda in kasuwane da munje layin yan Awo zamu shiga gasunan masu kyau sabbi bana super mariet ba da wasu zakiga sun kwashi shekaru saboda ba acen ne mahallinsu yake ba.

Shuru mamy tayi ranta abace .
Sai da ta nisa kana ta dakko wayar ta ta lallatda ta kara akunne tana huci tare da gilgiza kafarta daya da tasha jan lalle.
Jin an daukane yasata fara magana cikin tsanainin fushi.

"Kin kyauta kinyi abunda Ranki da Zuciyarki suka Raya miki, Amma wallahi kisani kika siyomun tsaffin kayan da Zanyi sadaka dasu sai ranki ya masifar b'aci, Saboda nafiso in'bada abunda zan iya ci, Sakarai kina Mace amma kinkasance mai kyamar talakawa bayan bakison inda Aure zai kaikiba, Shashasha kawai ta tsinke wayar.

Suna zaune kimanin 30mnt sukaji an buÉ—e get din gidan.

TSuke fuska Mamy ta karayi tare da maida hankalinta ga waya tana latsawa

Bayan kamar ten mnt sukaji an'buÉ—e kofar tare da sakin siririyar Sallama.

Sanin muhimmancin sallama yasa Mamy batare da ta dago kai ta kalletaba ta amsa.

Masha Allah itace kalmar dana furta lokacin da idanuwana sukayi tozali da kakyawa budurwa da bazata wuce shekaru Ashirin da biyu ba aduniya, Farace sol irin farin Mamy ,Gawasu mayun idanuwa dake gareta wayanda suketa lumshewa kamar zatai bacci, Daga cikin kwayar idon nata kuwa wata zaiba -zaiba ce ke shinning aciki ,ga wani dogon hanci har baka ,sai É—an bakinta mai Dauke da pink lips,Atakaice Dai kyakwace ajin farko, gata doguwar mai faffadan jiki dai- dai misali ,Tana da wani irin shape mai masifar É—aukar Hankali, Ga wasu cikakkun Brea's da hips É—inta masu tsananin fadi da girma, sanye take cikin wata Abaya brown mai duwatsu tabi jikinta tayi luf sai kafarta dake sanye da coffe din Tom's da yar jakarta data kasance coffe.

Ahankali ta karaso cikin palon Idon'ta naga kan mahaifiyar Tata ,Gudan Hannunta kuma na rike da madaidaiciyar kula.

Waje ta samu gefe da ita sosai ta zauna tare da fadin
"Mamy nah fushi kike dani?
Nifa ba kasuwa naje ba,
Naje gidan Nene ne tayimun Danbun kaji gashi fita zatayi shiyasa kamin Amal ta shirya naje na dawo, Amma sai faÄa kike Mamy babu ko Saurarawa, Halan wannan yarinya ta hadamu takarasa tana sakarma Amal harara.

Baki Amal ta turo tana sake lafewa jikin Mamy'n.

Kai Mamy ta dago jin Abinda tace tare da sassauta fuskarta tace.

Ai'nasa gaban kanki kikayi Amnah,Nasanki sarai wallahi zakiyi fiye da haka!.

Kanta ta shafa tare da yatsina fuska tace
"kema Mamy kibari Abba ya wadata gidan da ma'aikata wayanda zasuna miki komi Amma kinki, Amma kamarmu Ace wai mune zamuje kasuwa muyo wannan sayayya, Inama laifi Ace shinkafane ko drinks Amma kawai sai Aganmu munje yin awo, Som kamanni mu bai dace da hakaba !Takarasa cikin natsuwa kamar ba ita ke maganaba.

Ido Mamy ta tsiramata sosai tana kallonta, acikin zuciyarta kuwa Abubuwa da dama take sakawa game da gudan jinin nata, Kanta ta gilgiza tare da faÉ—in.

"Ki ajiye wanna Kular Naman kitashi kuje, in kuma bazakiba bani kudina ,Ma'aikata kuma banaso so kuke in lalataku sai an'kaiku gidan aure a koroman ku akan baku iya komi ba ko?

Baki Ammah ta turo tace nida gidana nike fatan a wadatashi da kayan more Rayuwa, aƙalla inaso inga mutum sama da goma aƙal kashina suna mun bauta ina biyan su,Ta yanda ko hakki zan ɗauka akwai wanda zayyi saurin mikoman, Saboda abun ya kasance aikin shi ne.

Cike da bacin rai mamy tayi kwafa tare da cije bakinta.

Cukin natsuwa Amnah ta mike tsaye tare da gyara rolling É—in dake kanta ta sargafa jikkarta key din motar ta ÆŠakko ta rike tana gilgizawa Tare da kallon Amal batare da tace komi ba ta sanya kai ta wuce.

Amal tason bazata tankamataba hakan yasa da sauri ta mike tsaye tare da yafa gyalanta tace .
"Mamy nah sai mundawo."

Fatan Alkhairi tayi musu tare da kishin giÉ—awa akan lallasan kujerun palon tana lallatsa waya ta kanga a kunne.

Jim tayi kafin a É—auka.

Ana É—aukar wayar kuma ta sauke ajiyar zuciya Tare da faÉ—in.

""Akwai matsala Haj Lubna, Akwai ga garumar matsala wallahi, Halin Amnah yana masifar bani tsoro da mamaki, ita som batason haɗa jini da talaka ba ina bauta zai mata ba, batason ƙulla mu'amullah da talakka batason shiga inda talakka zaije, Ita kawai ta ɗauki talakka An halitto shine dan Yayi bauta a'sallameshi, Kana ta ɗauki talaka mutum ne mai kasada Akan Rayuwar shi in Dai zaka bashi kuɗi ƙalilan, Tana ganin Talaka mutum ne wanda zai iya bada ranshi da rayuwarshi dan kudi, Hajiya Lubna ina ganin lokaci yayi da zan zaunar da ita ina warware mata zare da Abawa..

Ajiyar zuciya ta sake saukewa akaro na biyu kana tace shikenan sai na ganki ta kashe wayar..

Amnah
Suna fita ta faÉ—a motar ta tare da kifa kanta akai ta sauke ajiyar zuciya, Haka nan take jin wani yanayi marar daÉ—i dakuma bakin cikin da baida musultuwa , Ko kaÉ—an tanajin kamar zatajene inda za'ayan'yanka naman jikinta ,Karshentama tason yanda talakawa basu da hankali suna iya takamata kafarta.

Da sauri ta rintse idonta tare da dago jajayen idonta da suka canza launi ta zubasu ga Amal data buÉ—e motar ta shigo.

Cikin rawar murya mai hade da tashin hankali tace.
"Hankalin ki ya kwanta zaki kaini inda zuciyata bata aminta da zuwa ba ko? Wallahi Amal inajine kamar numfashina zai ɗauke saboda masifar baƙin cikin da nike ciki, Waiku wace irin zuciyace daku keda Mamy Nason shishigema Talakka? Muna da kuɗin da in mutum dubu mukeso mu aje awannan gidan zamu ajeshi kuma zamu kyautata sallamasu, Amal jibi gidan ubanmu jibi irin motar da muke hawa amma ace da ita zanshiga kasuwa takarasa tana dunkule hannunta tare da dukan dayan.

Tsoro furgici ruɗu suka ziyarci Amal lokaci guda,bata taɓa tinanin abun yar uwar nata ya girmama haka ba ,tana ganin da duk abunda take kamar wulakancine sai yanzu ta tabbatar da duk abunda take akan gaskiyarta take yinshi.

Motar ta tada Tare da janta afusace.

Cikin sauri Amal ta kalleta tare da kallon get din.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin tini Baba Madu ya bude get din tare da lafewa bayanshi.


Karcet ta fita da motar tare da cillata kan titi.

Cike da kwarewa take murza sitiyarin har suka fara shigowa cikin gari inda Amal ke mata nuni da Hannu inda zata shiga dan ita batama taba zuwa wajen dake da cinkoso ba irin wannan.

Duk inda suka gifta ido ke dawowa kanta, kasancewar motar samanta bude yake.

Siririn tsaki taja tare da furta.
"Jakai kawai motar ma sai ankalla kai talakka baiba."
Ido Amal ta rintse tare da kauda kanta gefe.

Ahankai suka shigo cikin faskeken get din da aka rubuta CENTRAL MARKET,
inda suka dinga wuce wurare har suka bullo ta get DIN yan Awo.


Tsaki ta ƙaraja akaro na ba Adadi Tare da Ɗakko wani brown din glass ta toshe idonta da shi, Tare da kara tsuke ɗan karamin bakinta dake zagaye da pink lips.

Amal tace ga inda zamuyi parking cen kana mufito ba.

Kallonta tayi a kufule kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta tsaya dai dai wajen wasu mutane dake tsaye suna rike da buhun huna gero.

Wani dattijone cikin kamala yace yam Mata gero kike sone.?

Kamar zata kyakeshi kuma ta daure tace
"Eh".

Tare da buɗe jikkarta ta yago wata paper tayi rubutu kadan tare da mikamai dan gani take tsayawa magana da shima ɓata lokacine.

Jujjuya takarda yashigayi dan yakasa fahimtar mita rubuta dan da turanci tayi rubutun.

Kafeshi tayi da ido tana kallo dan ta fahimci abunda yake nufi, tsaki ta saki sosai wanda yasashi juyowa ya kalleta saikuma yafara kokarin magana.

"Babaaaa"

Itace kalmar data ratsa dodon kunnasu ta katsema dattijon magana da yake kokarin yi.

Ahankaki ya juya ga saurayin da yayi shigar buzaye inda ya rufe fuskarshi baki ɗaya da baƙin rawani, Ƙafar shi sanye da slipas masu saukin kuɗi, Baƙin wandone jikinshi sai farar riga ta wani yadi da yasanya ,Baka ganin komi sai kwayar idonshi .

Dattijon yace Yawwa Habu kaimun wannan takarda shagon Mai Shadda kace nace ya fad'amaka Abunda akasanya saika kawoman.

Dan jim yayi kana ya dago ya kalli mutumin baice komi ba kuma yafara tafiya cikin sassarfa.

Anan na karemai kallo dogone sosai gashi da wata irin kira ta karfafan maza ,Cike da sassarfa yake tafiyar har ya shawo wata kwana inda ba yawan mutane sosai Kana yasamu wuri ya zauna ya duba takarda baki dayanta yana gama dubawa ya tashi ya maidata aljihu yayi gaba ya dawo inda dattijon yake.

"Akausashe yace bayanan amma na haɗu da wani na bashi ya dubaman tana bukatar gero dawa masara acca alkama buhu hamsin- hamsin sai kamata lissafin kudin kana Asamata mota,Ya ƙarasa yana kokarin wucewa.

Yalwataccen murmushi ya faÉ—aÉ—a ga fuskar Dattijon yace.

" Kai amma Alhamdulillah dama yau mukayo sabon sari duk zata samu, Kai Habu kaje store ka kwasomata kayayayyakin kana sawa a'mota ko kunzo da motane Hajiya?
Ya tambayi Amnah.

Bakinta ta tabe ta juya kai da sauri Amal tace aa baku da D'AN DAKO ne wanda zai kai a'mota?

Da sauti yace ga Habu nan zai kai maku duk inda kuke so.

Kallonshi Amal tayi sosai tace sai kasasu a'mota kabiyomu ko?

Kanshi ya gilguza batare da yace komi ba.

Cikin sauri yafara tafiya zuwa wani É—an shago dake tsaune da hatsi cike da jarumta yake sabo buhun nan y'ana sasu bayan motar.

Sosai Amna ke kallanshi tanaji inama ace kasanta yake dayasha bauta son rai , Da n daganinshi zai jure wahala .

Saida ya Tabbatar da ya cika bayan karamar mota kana ya koma wajen Dattijo'n cikin wata irin murya da som batai kama da ta buzaye ba yace .

"Baba nagama amma duka buhu hamsin nasanya zanje indawo sai inkwashi sauran.

Da sauri Baban ya daga kai tare da cewa yawwa kaga kana da naira dubu biyar kenan a wayanda ka É—ora, kuma suna son buhu kusan dari biyu kaga yakama zaka samu dubu ashirin yau kenan.

Bai ce komi ba haka kuma babu wani alamun farin ciki a abunda aka faÉ—amai ya juya ya shiga yar gwatsar motar ya tada inda duk ya wuce zakaga hayaki mutane kuma na kiranshi da Bukar Buzu .

Duk uban kiran da akemai sai dai ya juya ya É—aga musu hannu amma babu wanda ya taba cewa ga kalar fuskarshi ko kalar magana shi sai Dattijo.


Tafiye suke har suka shigo cikin gari sosai inda keda cunkoson ababe hawa.


Cikin fushi ta tsaida motar .

Ganin haka yasashi shima tsaida tashi dake bayan tasu.

Afusace Amnah ta fito ta isa wajenshi rai aɓace. "Tace kai wane irin shashashane kidahumi ? taya zaka cikamun kunne da ihun wannan gwatsar motar taka ?Miyasa bazaka bari inyi nisaba kamin ka biyoni? Matsala mu_amullah da jahilai kenan talakawa masu aiki irin na dabbobi,Dan kaja al'umma su raina ajina kaja aga tare muke ,ina mu'amullah da kazami irinka wawa kawai mtssss.

Tinda ta fara magana bai tankamata ba haka kuma babu niyyar tankamata a'tattare dashi.

Afusace Tace kai D'AN DAKO Bakajinane.

Shuru yamata yana kallon titi.

Dogon tsaki taja tare da watsamai yawu ta wuce.

Ahankali yasanya gefen rawaninshi ya share baice komi ba sai Yatsun hannunshi da ya dinga É—aÉ—É—agawa ahankali saman sitiyarin motar.

Motarta ta koma ta tada tare da cillata bisa titi aguje.

Tada tashi yayi yabi bayanta har suka ido kofar gidan nasu.

Hon tayi da sauri Baba madu ya bude ta danna hancin motar ciki .

Ganin haka shima yasanya tashi aciki dai- dai tsakiyar gidan yayi parking bai yarda ya karasa wajen da ta ajiye tataba ya fara sakko dasu cikin Sauri, Cikin ƙanƙanan lokaci yagama yayi tsaye yana jiran abashi cikon da zai kaima Baba kana ya Ɗakko sauran.

Amal ce ta fito da sauri ta karaso wajenshi ta mikamai kudi tace dan Allah kayi hakuri dazu naga kamar Aunty Amnah namaka faÉ—a ko?

Kai ya gulgizamata cike da gundura shi kudin shi kawai yakeso tabashi ya wuce ta tsayamai tambaya.

Kudin ta mikamai tare da fadin munafa jiran sauran yanzu.

Bai cemata komi ba ya faɗa motar yafara ƙoƙarin tadata amma taki tashi.


Ahankali ya sakko Tare da kwanciya ƙasan wajen ya danyi taɓe -tabe 'nshi kana yakoma yatada amma still taki tashi.

Fitowa yayi tare da dafe kanshi yanajin kamar ya saki kuka ga wata mahaukaciyar yunwa da kishi da yakeji , Babu abunda yaci ya fita kasuwar yana zuwa kuma aka haÉ—a shi da wannan aikin.

Tausayi sosai Yaba Amal dake tsaye gashi ya nade fuska duk uban zafin da ake da alama ruwa za'ayi dan garin ya É—auki wani mahaukacin zafi, Cikin sauri ta koma palonsu tare da shiga kicin ta samu wani katon flat tazubo shinkafa da miya da taji naman kaji da coslow gefe ta dauki wani flat madaidaici ta cikashi da Pepe chicken tare da É—aukar kunun Aya mai sanyi ta tsiyaya a madadaicin juk ta É—auki robar ruwa guda daya ta shirya kayan akan babban tire tafito da sauri.

Akan hanyar fitane daga palon sukaci karo da Ammah ta bita da kallo.

Fuska Amal É—in ta É—aure sosai tare da buÉ—e kofa tayi saurin ficewa.

Kai tsaye inda yake ta nufa tare da.

" Cewa sannu kana ta shan rana motar yaki tashi ko?

"Um" yace agajarce.

Dago kanta tayi ta kalleshi ganin yanzu har girar shi ana gani sabanin É—azu da kwayar idon shi ke rufe.

Ganin hakan ne yasa da sauri ya jawo rawanin ya lullube ko in nashi yabar kwayar idon nashi abuÉ—e.

Murmusi ta saki tare da cewa ku buzaye bakwajin zafi bakwajin kuma nawi?

Shuru yamata yana jin ɓacin ran surutunta shidai yatsani atasashi gaba anamai magana .

Abincin ta ajiye gabanshi tace" ÆŠan Allah ka zauna kaci sai in'kiramaka mai mana gyaran mota kaji?

Kai ya gilgiza cikin kuma yanayinshi na sanyi ya bude baki .
Yace nakoshi Allah ya amfana .

Ido ta zaro tare da haÉ—a hannayenta tace dan Allah da manzonsa ka zauna kaci abincin nan, Na rokeka, in'ba hakaba Amnah zatamun dariya wallahi, ka taimaka takaras tana dora kanta akan wuya alamun roko.

Dan jim yayi sai kuma yace shikenan na gode amma kijuyemun aleda kar in ɓata muku kwanikka yakarasa cikin sanyi.

Tausayi yabata sosai wato yana ganin bai kai matsayin da zaici abinci cikin kwanan da zasu ciba kenan.

Cikin natsuwa tace aa mudakai duk yan Adam ne bawani abu kaci kawai.

Jin cikin shi namai wani mahaukacin yatsinawa ne yasashi mika hannu biyu ya É—auki kayan abinci tare da buÉ—e Bayan motar ya ajiye kana yashiga ciki shima yayi shuru yana jiran ta tafi.

Fahimtar hakan yasata juyawa ta koma ciki tana mamakin yanda yake da kamun kai haka da kunya kamar ba DAN DAKO ba dan tason su da fitsara.

Yana ganin wucewarta ya juya ya kalli ko ina ganin babu kowa sai mai gadi da shima ya juya baya yasashi kai hannushi bayan rawani ya kwance tare da fara zagaye fuskanshi dashi har ya kwance.

Ahankaki ya ÆŠago kanshi yana sauke numfashi.

Wani irin tsalle zuciyata tayi da tasani sakin wayar batare da na shirya ba......
5/18/22, 09:33 - MY MTN 2: 🌹D'AN DAKO

MALLAKI

UMMY AYSHA🌹
3ï¸âƒ£&2ï¸âƒ£

""Masha Allah itace kalmar da ta samu fitowa daga cikin baki na.

Wani irin haɗaɗɗan saurayine fari sol irin farin larabawa, ga wata tausassa sumar da tayima kanshi ƙawanya, ga sajenshi da yayi ma sumulmula fuskarshi kyau yayi shar sakamakon zufa da fuskarshi tayi, Wani irin dogon hanci gareshi da yatafi D'oɗar har baka, ga wasu jajayen lips da suka dace da kyakyawar fuskarshi, yana da idanuwa masu masifar kyau da ɗaukar hankali.

Ahankali yaja hannun rigarshi sama kutt na furta lokacin da idanuwana sukai tozali da kyawawan hannayenshi da suka kasance farare sol, Ga galgasa da tama hannu rumfa irin dogayen nan mai tsananin sheki da sulɓi.

Robar ruwan ya É—auka tare da fidda hannunshi waje ta window mota ya fara wanke hannun shi.

Yana gamawa yaja kwanikkan tare da buÉ—e su.

Idon shi ya lumshe dan yaushe rabon da yaga abinci mai kyau kamar wannan.

A'hankali yayi Bissmillah tare da fara tsakurar abincin kaÉ—an -kaÉ—an yana ci.

Baiwani ci da yawaba ya ture tare da turo hannun shi still ya wanke ya É—aga cup din Kunin Ayar yasha sosai saida yayi rabi kana ya ajiye.

A'hankali bakin shi ke motsawa alamun Addu'a yake ta bayan gamacin abinci(ALHAMDULILLAHI LAZI AÆŠÆŠA'AMANI HAZA, WARA ZAKNIHI MIN GAIRI HAULIN MINNI WALA KUWWA)

Idon shi ya lumshe tare da jingina kanshi da motar.

Dai -dai kuma lokacin ne aka fara iska mai tsananin karfin dake nuni da ana gaf da sakko da Ruwan sama.

Idon shi ya lumshe tare da shaƙar kanshin ƙasa dake tasowa.

Da kallon gefen da kayan daya ajiye musu yake wanda ya tabbatar da in ruwa ya safka akansu sun gama yawo.

Cikin natsuwa ya maida rawanin fuskar shi tare da fitowa yafara tsakula motar dan yasamu ta tashi yakara gaba kar ruwan ya safko amma motar taki tashi.

Tsananin fushi yatasomai wanda yasashi kaima motar wani wawan dukan dayasa marfin ɓallewa ya fita.

Aƙufule ya kwaso tiren kayan abinci tare da ajeshi cen gefe inda za'a iya gani kana ya dawo yana ɗaga kanshi sama ganin yanda garin ke rinewa sosai.

Tsaki yasaki tare da fara kokarin tafiya.

Dai -dai lokacin ne kuma Amal da mam6y da Amnah suna fito cikin sauri Amal tace .

"ÆŠan uwa dakata mana."

Shuru yayi batare da yatsayaba kuma bai fasa tafiya ba.

Yana gab da cimma get Amal tace katsaya Dan Allah.

Cak yatsaya batare da yajuyo ba.

Rai ɓace da ganin yanda yaketa izza Amnah da tasha wasu riga da wando da suka masifar yimata kyau rigar orange mai ratsin Black sai wandon kuma daya kasance Black mai ratsin orange kanta sanye da wata Black din hula data ɗan turata baya yalwataccen gashin goshinta duk yafito, daga Baya kuma foygon gashinta ya bazu akafaɗata sai sheki yake,Cikin isa tafara tako cike da izgili har zuwa inda yake.

Cikin tsananin ɓacin rai tace.
"Mene Acikin Tumbi banda kashi,Ina ɗan burburi ina niganci,Ina talakka ina girman kai,Ina D'AN DAKO ina iskanci da har za'adinga kiranka amma kayiwa mutane banza ka kyalesu kai ga shashasha ko? Wawa baƙauyen da yakasa gane gabas da yamma, Kayi maza kaje anason ganin ka koba sallamaka za'aiba da kake nunama mutane iko, Takarasa tana nunamai inda su Mamy suke tsaye akan Bagala..

Da zata lura baki dyayan jikinshi kyarma ya d'auka kyarma da rashin ganin fuskarshine yasa aka kasa ganewa...

Amal tace Mamy kije da kanki kartamai wani abu fa.

Cikin amincewa da maganata Mamy ta tattako cikin dattako har inda suke tsaye.

Sallama tayi tare da cewa bawan Allah munata magana amma shuru .

Baice komi ba sai juyo da kanshi da yayi ganin Babba maca ce cikin mutunci ya buÉ—e bakin shi ya gaishe ta .

Amsawa tayi cikin fara'a .
" Tace dan Allah ko zaka iya zuwa ka kwashemun kayan nan, Naga kamar za'afara ruwa kuma munan bamu da masu kwashewa wancen Tsohon bazai iyaba saboda halin girma ta nuna mai gadi.

Kai ya jinjina batare da yace komiba yayi gaba cikin sassarfa.

Yasa hannu zai É—auki kayan kuma yayi tsaye yana tinanin ta ina zai dosa dasu ga bakin shi yayi Nawin da bazai iya magana ba.

Mamy takatse mai tinani da faÉ—in ga inda zaka ajiyesu acen, Wancen store É—in dake kusa da dakin Baba Madu.

Baice komi ba sai kwasar kayan da ya fara cikin jarumta yana kaiwa kamar ya d'auki kwali.

Yana gab da gamawa akafara iska mai matsanancin ƙarfi.

A'hankali ya duƙa yakama kowanne buhu da hannu ɗaya yazamana buhu biyu ke ahannunshi yafaraja da sauri.

Suduka kallo suka bishi dashi inda Mamy jarumtar saurayin ta burgeta, Hakanan taji sha'awar samunshi amatsayin wanda zai dingamata hidimar gida koda kuwa aikin kula da get ne, Dan taga dakyal Baba Madu ke buÄeshi yana rufewa.

Zai kai buhun karshe cikin sauri jin ana yayyafi gefen buhun ya fashe wanda yasa Dawar dake ciki fara shatata.

Saurin ajeshi yayi cikin zafin

Please Login or Register in order to submit comment