Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka É—auke man ya É—aya tak aka kaita gidan wannan tsohon.
Tinda ta tare.
Duk kan dare na Allah zai kaima Saude ziyara, amma bata amince mai, da duka yakushi bugu take hanashi, daga bayama sai ta dunga rufe ƙofa.

Hakan ya fusata shi dama yana da mata hudu ganin Saude ne yasa ya saki É—aya, Ya maye gurbinta da Saude,ga babba matsala duk wani siddabaru yayi amma abanza baya kama .
Gidan shi dake da yawan yara kwatsa-kwatsa ya tara dukkan mutan gida, hadda saude data buÉ—e kofa ganin gari ya waye ta fito cikin taron...

Anan yake faÉ—in daga ranar ya hutar da kowa aiki a gidan Saude zata dinga mai, Dan bata da É—a'a da ladabi.

Sanin halin shi ne yasa suka amince mai tinda dai ba kwana ya hanasu ba.

Daga ranar take wahala tuka tuwan gidan ma kadai aikine, sai dai tayi tukunya ukku tinda ba iya da yawa zatai ba.

Cikin sati biyu ta fara fita hayyacinta, yarin yata mai garin jiki amma duk ta bushe , Gashi duk sadda nayi niyyar zuwa gidan sai in kasa.
haka Saude taita rayuwa har ta cika shekara ukku. ya kama shekarata sha biyar ,babu abinda ya shiga tsakanin ta da Mai malmala, saboda har lokacin rufe ƙofa take da mangari ba tayi.

Ranar da ta manta bata rufe kofar ba bacci ya kwasheta aranar Allah ya kaddara da rabon yarin yar nan, saboda ranar ya hakemata yamata illah mafi muni dan har yoyon fitsari ta kamu dashi kuma ya kore ta, saida nayi bara kana muka samu mukaita zarya Asibiti,kudi da yawa aka samana hakan yasa gidan da nike ciki na sai dashi dan in samu kuÉ—in magani ta , Da sauran muka kama haya inda ka ganni.
Cikin ikon Allah abun ya tsaya aka sallamo mu muka dawo gida.
Kwana ta ukku da dawowar saiga Mai Malmala a fusace ya shigo gidan nan, kamin in'magana yaja hannuta suka tafi tana turjewa,suna isa gida ya É—auketa ya watsa ga gado ya shaga biyan bukatar shi.
Daga ranar ya maidata jaka koda wane lokaci yana hake da ita, kasancewar shi harijine shiyasa mafi yawan mata basa zama dashi Saboda suna cutuwa..

Sosai Saudat ke shan azaba duk ta rame ta fita hayyacinta ,ga shigar ciki da laulayi amma baya ÆŠagamata kafa, ga matan shi sun fara matsamata ,suna ganin baya kwana wajen su kulkum yana like da ita .

Ahaka cikin rayuwa wahala cikin ta ya mika, yafito sosai su kuma daga lokacin suka dauki aniyar dukanta ,Duka km bana wasa ba, Dan sunga bata da kowa daya fita makaranta allon shi zasu hadu su mata shegen duka, Cikin fatan su cutar da cikin amma ina Allah bai nufa ba .

Gashi ya hanani zuwa ingañta, dana doshi gidan zanta ganin wasu abubuwa dole nike komawa, itama baya Barinta fita dan kar ta gudu..

Wata safiyar litinin ce ana ruwan sama kamar da bakin kwarya, Saude ta fara Nakuda .

Mijinta dake Makaranta ya tada Almajiran sa ya taso ya shigo gida abuƙace ya afka ɗakin ta.

Tana gani shi ta fashe da kuka .

Bai tsaya komi ba yayi kanta anan yayi yanda yakeso sama da awa biyu gashi dama cikin nakuda take , Dole nakuda ta sake tashi amma ba tausayi babu jin kai ya shareta tanata wahala shi kam yana bacci.

Addu'a ta farati tana kuka akan Allah ya kuɓutar da ita daga gidan dan ta gaji.

Cikin ikon Allah bacci mai nawie ya kwashe shi.
Hakan yasa ta fara rarrafowa tana ƙoƙarin fitowa ɗakin ta .

Saiga uwar gidanta da gudu wai ta tashi ta doramusu ruwan koko yaran su naji yunwa.

Saude tace bata iyawa .

Anan ta fara jibgarta kamar ta samu jaka, ga bugu ga nakuda ahaka taita rarrafawa tana kuka.
Uwar gidan na jawota tana fadin babu inda zata tana dukan ta.
Cikin ikon Allah Saude ta tureta ta fito daga gidan da sauri har ta kawo bakin Titi haihuwa ta tashi rigi- rigi ,ga karfin ruwa nata karuwa Suna sauka akan ta.

Anan saman kwalta ta duke tana kuka tana nishi har Allah ya bata sa'a taji Baby ta faÉ—o cikin zanan ta.
Kasa tashi tayi kuma ta kasa motsi ,saboda halin da take ciki garuwa na dukanta.

Wata motace ta yanko da gudu anan taja burki. A'rikice wata mata tafi to dan jinin da taga yanabin kasan Saude É—in ne ya sata tsayawa.
" tace'' ke lafiya?.

Saude ta kasa motsi matar ta iso kanta da lema hannuta ta É—an matsar da ita dan taga tushe abu.
Anan taga Baby nata billayi kasa ga cibi ba ayanke ba.

Salati ta saki ta watsar da lema ta dakko kayan aiki cikin mota ta yankemata cibiya, kana ta sa Baby a gyalan ta ta naɗe kana ta sata a'mota,A gulguje ta ɗan bama Saude taimako kana ta dakkosu ta buƙaci sanun inda suke.

Anan ta faÉ—amata har sukazo gidana suka shigo taman bayani ita Likita ce sunan ta Turai, anan ta ajiyemuna kudi tace zata dawo.

Daga lokacin ne muka fara sabuwar rayuwa ta kunci.
Watan ta daya Mai malmala ya turo da takarda sakinta da zagi kala- kala.

Aranar ne nikuma Allah ya budemun bakina na fara jin takaicin abubuwan da yama ta.

Da kaina naje na siyo barkono na daka shi haka nan na hura icce na dafa ruwan zafi na juye yajin ciki kana na fita na nufi makaran ta shi.
Yana kwance yana bacci na koma gefe na fara mai wanka tindaga saman fuskar shi ,kai ,har cikin wandon shi.,
Ihu yake yana kari amma baison waya mai ba na fita hankali kwance ba tare da kowa ya ganni ba.
. To bayan kwana ukku ne kaganmu Acikin wannan yanayin na rashin kudin haya.....

Hawaye na share naji tausayin Saude ya shiga raina, Gaskiya an'kashe rayuwarta ,shiya sa bata ko son magana.
Anan na nemi alfarma magana da ita Nene ta amince.

Bayan munkeɓe nike mata magana son zama miji a gareta.

Da fari taku amincewa saida naita lallashinta tare Da Bayyana da alƙawarin zamema ɗiyarta uba kana ta yarda.

Alokacin ne kuma kwasam Mai malmala yasamu labarin Auran ta har ya gano gidan. sai gashi shida yan uwansa wai abasu É—iyar su zai tashi daga katsina ya koma kauyen ÆŠAN ÆŠagoro, anan yake so ya fara sana'a saida hatsi.

Aiko anan Saude ta nuna mai ba Mai hakuri bai iya fushi ba, Ranar hadda mari ta rafkama tsoho nan, Da nuna mai itace uwa da uban yarta ,bata fatan har abada É—iyar ta tason shine ya haifeta.

Rigima sosai akayi inda yace "ya barmata amma ta sani duk ranar da aka tashi auran ta to bata da uba ,kuma in dai har yasani to Babu mai auranta.

Tace mai taji tana turashi waje ya fice gida.

Shekara na zagayowa muka angwance, muka tafi da Amnah ina mata duk kan wani gata.
Har saida ta cika shekara biyar kana Allah ya bamu cikin Amal.
Nayi murna nina zanga gudun jinina, amma na fiso da shakuwa da Amnah sama da wadda na haifa wannan shine tarihin mu.

Wani irin kuka Amnah keyi yanzu itace aka haifa cikin gararin rayuwa, Lallai ita bai dace data tsani jinin talakaba har saita fara zuwa taga mazaunin ta..

Mikewa tayi tsaye tana fadin "abata address din gidan mahaifinta.

Nene tace muma bamu sani ba sai dai muje unguwar da muka bari a tambaya ,amma ki bari aje Abuja adawo.

Shuru tayi badan taso hakan ba.

Sadeeq ya kama hannuta yace" muje ki huta kinga bakyajin daÉ—i.

Mikewa tayi dan tana buƙatar hakan suka tafi ɗaki shi ya rufe.

Hijjob inta ya cire tare da zame mata rigar ta ya cirar nashi kana ya jata jikinshi suka kwanta.
Take ta fara sauke ajiyar zuciya, cikin lokaci baccin yayi gaba da ita.

Saida ya tabbatar tayi nisa kana ya tashi ya maida kayan shi ya fito .
ya fita waje tare da tsaida machine ya doshi goruba roud.

Bayan yaje ya sauka wani faskeken gida,take wani soja yazo ya buÉ—emai yana mai saramai.

Shiga yayi yana tafiya cikin ƙasaita har zuwa wani kofar palon dake farko ya tura ya shiga.
Anan yaga Bily zaune tana kuka.

Dukawa yayi kusa da ita yana mai zaro sabuwar waya da sim card sabo ya bata yace" samun number ÆŠan Akuyan ubanki.

Kallon shi tayi tace "Uncle Dee.harda cin mutunci, ni dake buƙatar taimaka ma.

Mari ya kaimata yace" zakisa ko sai na sanya karnuka sun yaga naman jikin ki.

Da sauri ta sanya ta bashi.
Shikuma Ya danna mai kira.

Bayan an'É—auka ya saki Murmushi mai ciwo.
Daga cen bangaran Alhaji Musbahu yace" wanene akan layi...?

Sadeeq yace "DEE S.S"

Azabure ya mike yana faÉ—in kana nufin Sadeeq S Sadeeq ,ubanwa ya baka number nah, kuma dama da ranku,Aiko zakuci uban ku ..

Cikin natsuwa yace "ai'kagama cinshi tinda har ka karshi, yanzu kuma nine zanci naka agabanka, baka kuma da abinda zakai.
Da fari ga karyar yarinyaka nan hannu na,Kason ka tarbiyyan tar damu da son kuɗi, Dan haka fansar ranta million dari biyu ne,Ma'ana kudin da Abbana ya Sanya ajikkar da kuka kwasa sama wanda ƙasa ya samaku na bogi...

Cikin ihu yace" wallahi wallahi ka taɓa mun ya saina kasheka har lahira, bayan yaudara da kukamun kaida matsiyacin ubanka zakamun wata kai ga maye mai gadon Asara ko?.

Afusace Sadeeq ya zaro bindiga ya saki halbi saman kujera daya gigita Bily ta saki ihu sosai, Yayin da jikin Alhaji Musbahu ya dauki rawa ya fara faɗin" ba dai kasheman ya kaiba, kai kana da hankali ,yar tawa data ragemun, Ƙaseem mafa ya mutu , Dan Allah Dee kar kamun haka, dan Allah ita kadai garan..

Yace kayi maza ka bada kudin fansarta ciki 3hr,
Niku ma in sanya acire bullet din Kafar ta, in'kuma kaƙi to dan ubanka zaka zo katarar da gawarta ta kumbura ko inba karnuka su cita..

Salati ya É—auka yana faÉ—in" Dee zan hadaka fa da hukuma.

Yace karka manta nima hukuman kainane, sai na jika kill ya kashe wayar tare da mikewa ya fita..

Washe gari da sassafe suka dayuki hanya harda Bily, Bayan su kau zugar motocine sunfi a kilga sai jiniya suke...

Zuwa azahar suka shiga garin Abuja .

Kamin su isa Sadeeq yayi waya da mahaifinta inda ya tabbatar mai da ya biya kudin...

Murmushi yayi yana jawo wayar shi ya kira wani mutum yace" sako yazo.

Yace" eh Yallabai sunzo kuma mun kilga sun cika ..

Kashe wayar yayi yana doka Murmushi...

Suna isa kwanar yaga gidan mahaifin shi ne, Bazai taɓa mantawa ba, Wato shine aka gyara kenan suke ciki ,hooooo ɗan nmadam kenan Ya kashe mai abu ya mallaki gida.
Jiniyar suka kashe sadda suka isa.

Bayan sunje suka fara fitowa wasu suka zagaye gidan, wasu kuma suka nufi get din gidan gadan- gadan ,ciki kuwa harda Nene dasu Abba sai uban gayya da Ammi..

Kwan-kwasa wa sukai mai gadin ya fito yana faÉ—in" waye ?

Sadeeq yace" ka bude yar Alhaji muka kawo.

Da sauri ya buÉ—e suka turashi suka fara shiga gidan zuga guda .

Salati mai gadin yasa Amma ganin iyayen shi ne a iskanci yasa ya koma gefe yana kyarma dan yason soja ba mutunci...

Wani Bakin glass sadeeq ya dauka ya toshe idon shi daya fara jin hawaye na neman zubomai tinowa da rayuwar da sukayi da Uban su agidan da yar uwar shi.
Bindigar hannu shi ya gyara tare da sumba tar goshin Amnah yace". kikoma wajen su Nainah.
Tace to tana mai É—agamai Hannu.

Cikin kuzari ya isa gaba tare sa kutsa kai baban palon da yasha kayan Alatu..

Tsaye yayi yana kare ma palon kallo ,komi na more rayuwa akwai ciki na zamani.


Zama yayi akan kujera tare da É—ora daya kan É—aya yana gilgizawa, fuskar nan babu rahama som.

Ganin babu kowa yasa ya É—aga bindiga sama ya halba jikake "dammm..
"
Kamar saukar aradu Alhaji Musbahu da Matar shi suka ji abin nan suna tsaka da zaman jiran ganin yarsu.

Aguje su kayo palo inda suka ga Sadeeq hakimce duk da ya ƙara girma ya kara cika da kyau hakan bai boye musu fuskar shi ba dake kama data baban shi...

Wani mahaukacin tsoro ya Dirar ma Alhaji Musbahu musamman dayaga Sodoji dakin cike suka zare ido.
Take jikin shi ya dauki rawa ya fara ƙoƙarin koma daki ..

Kan ya ƙarasa yaji saukar bindiga a kafar shi..

Ihu ya Kwallah tare da murginowa daga kan step din da yake sai gashi tam gaban Dee..

Bindigar shi ya gyara yana mai taka ruwan cikin shi yace" yama karin maganar nan da gayusawa kece wa?

. shiru Musbahu yayi sai jikinshi dake kyarma yana fidda hawayen azaba...

Sadeeq yace'' nason bazaka amsamin ba, to rana daya ta ɓarawo daya tak ta mai kaya , Dan haka gani gaka, yau sai mugwada kwanji muga wazai nasara.


Kamar haka ne shekara goma data wuce kasa aka taramu palon nan, aka muna cin mutunci da illah babba, daga karshe aka kashemun Abba nah da sst na mafi siyuwa agare ni, to yau kaima agaban ka zankashe kowa naka kamin in dawo kanka....

Kuka sukaji irin na tsofafi daga gefe.

Sadeeq ya waiwaya yaga Umma ce tanata jan kugu tana sauri, Duk tayi mugun tsufa ta lalace...

Tana ƙarasowa wajen su ta kallesu tana kuka tana buƙatar tayi magana amma ta kasa.

Sadeeq ya toshe hanci yace "dama da ranki, to Alhamdulillah, yanzu in kinga mutuwar su ina fatan taki ta kawomaki ziyara, kamin nan Ammi, Nainah, My Wife, Amal, Abba kuje waje dan Allah zamuyi magana..

Suna ƙoƙarin fita Nene tace "wallahi saina ramama ɗana zalinci da kuka mai.
Ta dawo da gudu ta cire takalman Amal masu tsini har ta kusan ya data ta nufi wajen Alhaji musba dake kwance cikin jini.

Takalman ta rike duka hannayen ta ta fara kwalama Alhaji Musbahu a fuska tana kaimai mari dasu.

Ihu yasa sosai Yayin da Sadeeq ke tafi yana faÉ—in kaga kakar soja, Allah yaja da ranki Nainah.

Kamar ya ƙaramata kuzari taci gaba da marin shi, sai da taga ko in ta tashi fuska tayi sumfut kamin ta gaji ta mike ta kaimai naushi tace" Matsiyaci nice nan uwar Sadeeq,m dan ubanka ta ƙarasa tana nishi tare da nufar wajen Umma.

Tan ida da karfi ta shureta tare da kai mata mari ta fizge hular kanta ta kwalamata takalman tana fadin kafura la'ananna mai zuciyar azzalumai, ashe ki kaita cutar yarona, kina zalintar sa , Dan bake kika haifeshi ba, to dama ina ke ina haihuwar yarona fari mai farar aniya , Amma ke kam kafurar daga ganin ki baki da mutunci munafuka sai kukan kyankyasai kike mana ..

Kuka Umma tasa tana gilgiza kai kamar zata shiÉ—e.
Nene ta fita tana tsogwami da faÉ—in zata kara mata wani.

Suna fita Sadeeq yasa aka rufe ƙofar, tare da mikewa ya juya baya ya cema yaran shi ku kwantar da yar shi gatanan kuyi Abinda kuke so wanda kamin ya wullah lahira zai tafi da bakin ciki ,ni nace kuyi abinda kuke so..


Hifufuuuuuuuuu zakuna sunga nama ,har rige rige suke wajen doso inda Bily take.

Ihu mamanta tasa da Babanta yana faÉ—in noooo Sadeeq, kwara ka kasheni daka sa aketa mutuncin yarinyata gabana.....
5/30/22, 10:15 - Ummi Tandama😇: *Littafin🌹DAN DAKO🌹 na kudi ne biya ki karanta cikin Aminci. Biya 300kacal to 0006454115 Amina Dahiru jaiz bank,or MTN card to this number 09165832002. then send the evidence of payment via 07038423451* ðŸ¤ðŸ™ðŸ¤²


Alhamdulillah! Alhamdulillah!!
Yan uwana mata ina kuke ku malmatso ga wanni sirri da nike son baku, ita ya mace sai da kamshi, ina macen da take ganin izgili da wulakanci da ake cewa maza nada shi, hmmm yar uwa to inkin kasance a haka da alama akwai ayar tambaya akanki. Tambaya ta ta farko gareki da wane irin turare kike amfani a jikin ki ?,da wane irin turare kike turara gidan ki,shin dawane irin turare kike Zukunni, hmmm to matso kusa kiji yar uwata.
Shi kamshi Annabi muma ya faÉ—a abin sone,kuma Abune mai sanya natsuwa da girmama ma'aboci shi , Da Yawon son kusantar sa.
Duk kan wulakanci da izgilanci na maza akwai turaran da zai miki maganin sa da izinin Allah,ba boka ba malam,wanda zai karkato da hankalin mijinki akan ki ku samu fahimtar juna.
Ko kin son kamshi na dakusar da fitinar É—a namiji yar uwa? kigarzayo ki kwashi rabonki ga shaharariyar yar mai Dugurin nan mai suna UMSAD INCENSE ,Mace mai kishin mata da son Fiddo martaba mu.
Nayi Amfani da turaranta naji masifar daÉ—in da yasa nakasa barwa raina. Nace bari in yaÉ—amuku dan kowa ya mallaki nashi cikin farashi mai sauki.
Da fari bari in zayyano muku su kamar haka.👇

Maleek Al'oud
Royal kush
Cous-cous
Kajiji
Original sandal
Sandal flex
Sandal bange
VIP mix
Hawi
Al'oud
Kindikay
Danal banat
Darot
Habil
Gaf-Gaf
Sirrun nisaa'i
Sandal chips
Kwalacca
Humra black and body milk
Attractive humra.

Yar uwa zanmiki Dallah- Dallah.
Akwai turaran da zaki sanyama kayanki .
Misali! kisa kabasa kiturare kayanki .
Akwai humra da bazaki sataba sai zaki turaka.
Akwai turaran kaya ,na jiki, Dakuma na ɗaki. Akwai kwallaca sirri, amma bama badata gaskiya sai ga wanda baida kishiya , Dan muddum kina amfani da ita tofa gabaki dayan hankalin mijinki akanki zai dawo,Dan yana juyo da hankalin namiji akanki baki ɗaya ,zaki zama shalele Baby, Akwai sirrin nisaa'i. hmmm Dagajin sunan kason na dabanne,na baki sati ɗaya ki gwada ki gani Hajiya ta, tsugunno ake akai ga mai buƙata ya tunɓe mu ta wannan layin 08028827241 karku manta UMSAD INCENSE mune na ɗaya.
Muna aika kayan mu duk inda kuke.
Kamshin jiki martaba mutum....

5ï¸âƒ£1ï¸âƒ£&5ï¸âƒ£2ï¸âƒ£

"""Banza Sadeeq yayi dashi sai window da yake kallo yana É—an jijjigawa, Tare da goge kwalla da suka zubo mai saboda tinowa da yanayin da suka tsinci kansu kamar haka sadda suke neman taimako daga garesu ,amma saida suka cimma buri .

Ihu Bily ke kurmawa yayin da wani basamuden kato ya kaimata ziyara, Tason tayi iskanci kala -kala amma bata taɓa haɗuwa da Jibgegen gardi ba kamar wannan kasurgumin ba.

Cikin kururuwar su ta Arna yake ihu har saida ya cimma buru kana ya koma gefe yana sauke numfashi.

Ahaka sukaita ratsa jikinta one bye one tin tana ihu har ta kasa, Saboda sumewar da tayi.
Yayin da jinin azaba ke gangarowa daga jikinta yana lailayowa har wajen fuskar Alhaji Musbahu dake kwance kamar ruwa yana kallon yanda ake casu da É—iyar shi.

Ita kam Umma sai karta kai take tana siririn kuka, Dan Nene duk ta kwankwashe mata ƙeya.

A ƙalllah awa biyu suka samu ana musayar Bily wa katti, Wannan ya ɗauka yaba wannan ,kana Sadeeq yace'' musu ya isa zasu iya maidota gaban iyayen ta, Dan shi bazai iya yarda yayi kisan kai ba kamar jahili...

Kamar tsohuwar mota haka suka jawota gaban uban ta dake kuka kamar ranshi zai fita.
Magana yake burin yi amma bakin shi ya kasa buÉ—uwa.
Itakam Mamanta tini ta sume.

Cikin natsuwa Sadeeq ya jiyo tare da zama akan kujera da yake yace" Wannan kadai na maka dan kaji zafi,Kaji kwatankwacin wanda naji.

Cikin awa biyu ina so ka tattara uwar ka da matar ka da yar iska yarka kubar mun gidana .
Inko kunƙiya zansa a rushe gidan gaba ɗaya, kuma wallahi zanbada umarnin a hada daku ɗan iska tsoho kawai.

Gidan da mahaifina ya gina kuka zauna kuka kwantar da hankali kuna saɓon Allah, to kaje Allah yamaka yanda kamun, bazan kashe kaba, bazan kuma kashe kowa naka ba, sai dai nabar wanda yayi ka yayi ni da yamun sakayya, ku tashi ku tafi kubar mun gida ya fada cikin in inaaa Sosai....


Cikin matsananci kuka Alhaji Musbahu yace" kayiman rai Sadeeq, taya zan iya tashi ka gurgunta ni,ina kake so inje bayan komi nawa ka kwace, wallahi kwanannan na rasa duk kan wasu shagunan dana bude,Wayan nan kuÉ—aÉ—an daka karba sune wayanda nike fatan fita dasu inyo sabuwar sayayya.
Ina kake so in'koma? bayan bani da komi, kamin rai, kamain halacci Dan Allah Dee ko dan rike ubanka da uwata tayi....

Tsawa sosai ya dakamai jikinshi narawa yace" Sadda kake bibiyar ubana kamar ÆŠan Akuya katina hakuri da yake baka, to ina da labarin komi,kasani wallahi baka ba sake kwana gida na,Kuma uwarka rikon da tamaka tama uban nawa,shegiya tana fama da banzan kanta kwal kamar Toch light.

Cikin ihu ya fara basu umarnin a fitar dasu.

Da gudu sodojin nan suka fara sungumar Alhaji Musbahu da umma, da bily da Mamanta suka sanya a wata mota, wadda ita kadai ta rage musu wadda yake hawa,haka suka sanya su ciki wani bisa wani kamar awakai.

Umarni ya bada da akwashen duk kayan su duka a fita dasu, A kaisu cen wajen gari a ajiyesu da kayan nasu.

Cikin lokaci suka fara kwale kayan Ɗakin, kan kace mi sunma gidan tumɓur.

Haka aka kwashesu da kayansu aka nufi cen wajen gari aka sauke su, aka bar musu motar da kayansu jibgi guda suka juya...
Alhaji Musbahu tashin hankali ya sashi sumewa, bai ƙara sanin inda kanshi yake ba.

Bayan komi ya lafa .
Sadeeq ya fito yana share hawaye, yayi wajen su Nene.
Da sauri Nene ta cimmashi tana mai rungumeshi ta fashe da kuka.

Ammi ma kukan take sosai tana tino rayuwar su.

Amnah kau zazzaɓi mai zafi takeji da ciwon kai wanda ko ido bata iya buɗewa sosai....

Sadeeq ya mike daga jikin Nene yayi inda take zaune.

Durkusawa yayi kusa da ita yana mai ɗago haɓar ta yace "my wife minene? kina lafiya ? ko karar bindiga ta tsoratamun ke,, kiyi hakuri kinji matata, kisa ba kinji, inkuma bakyaso kifaɗamun aikin da kikso in fara sai in nema.

Kai ta gilgizamai tana kuka tace" waye Baba na, shine nike so ingani, wane irin mahaifi ne Allah ya bani mai zalintar iyalin sa...

Sadeeq yace Kiyi hakuri yau zamu koma insha Allah, na riga nima dana gama da Abuja har abada yanzu haka takadda transfer nah zanje ƙarba, na fiso a mayar dani Break din katsina bata kaduna ba, kinga sai musiya gida acen ko bakyaso?

Kai ta É—agamai tana faÉ—awa jikin shi.

Cikin ƙasa da murya yace.
" Yadai wajen ya daina ciwo ko yanayi ,muje hotel in sake gasaki ko?

Cikin jin kunya da.maganshi tayi ƙasa da kanta.

Yace "ok tashi mutafi in_gani..

Mikewa tayi A'hankali tana matse baki...

Nene dake kallon su tayi tsaki tace "Saddi ashe kai ɗin nan ma jarabbabe ne, ina ganin Amnah zata kadaga amma dan rashin mutunci sai gashi ka ɗauketa ka lafta da ƙasa, wannan ai cutane ,muje ka kaita Asibiti nasan Ɗinke yal banza zasuyi kamar kwarya...

Kan shi ya sosa yace". Taya mace zata kada namiji .
Naina dan Allah ki rage sanya ido ,miye ruwanki da har ka mata da miji.

Su Mamy kam lokacin nema suka farga da abinda ya faru.

Cikin tsananin farin ciki da jin daÉ—i take kallon su, Duk damuwar ta taji ta sauka, Alhamdulillah kawai take faÉ—a da Allah ya hadamata kansu...

Waya akama Sadeeq akan takardar shi ta fito .

Da murna suka shiga mota zuga guda sukayi wani hadaddan gidan Abinci, Bayan sunci suka É—auki hanya har Kaduna inda da ya fara aiki, Bayan yashiga suka tayashi murna yayi cike- ciken shi na tabbacin dawowar shi aiki kana suka wuce.....

Karfe tara na dare suka sauka Katsina ajigace likis dan ma suna tsula gudu.

Anan Ammi tace ma Mamy" A wuce da Amnah gobe tinda safe sai suje cen kauyen su.

Cikin tsananin jin dadi Mamy tayi godiya.
Sadeeq daya anso mota ya taho cikin jin daÉ—i yace "my wife muje gida ki huta ko...

Kallon shi tayi ta kwabe fuska tace "Ba Ammi ta hana ba.

Ido ya zaro yace mita hana?

Tace "wai batare zamu kwana ba,a gidan Mamy zan kwana.
Yace" innalillahi wa inna ilaihi Raji'un ,Minai musu,miyasa bazasu faÉ—amun laifina ba in basu hakuri,miyasa zasu horani da rabani dake.?..

Shuru tayi tanayin ƙasa da kanta , Dan ita komi ma baya mata daɗi...

Motar ya rufe ya isa ga su Mamy.
Kan su an'kara ya duke ƙasa tare da yin ƙasa da kanshi yace" iyayena kuyi hakuri Dan Allah, in akwai abinda na muku to akan kuskurene,Amma Dan Allah karku hora zukatan mu ta hanyar raba ganga jikin mu,kubarni da matata mana zan bata kulawar da ta dace..

Nene'' Dake shan ƙaton mangwaro tace "na shiga ukku ni Aminatu,wai mike damun yaran zamanine,Anya shegiyar allura nan da kuke kaisu ta bbc (BCJ)ake cemata komi ba allura rashin kunya da fitsara bace?.

Cikin ta fasa zuciya ya juyo gareta yace'' Nainah Wallahi babu wata kunya da zanji, saboda dukkan su iyayena ne,Babu wani kunya da zanji tunda matata ce ,in'kin son ba sawa zakiyi abani ba to dan Allah Nainah kiyi shuru..

Nene tace'' Bazan ba Kwandon Sukari, dama tinda kaga yau an'baka muƙamin soja naga kanata hura hanci, kana ƙoƙarin duka na ,to babu inda zaka da ita sai ta warke, ko-ko so kake abaka ita kaje ka ƙara

Please Login or Register in order to submit comment