Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi tare da kwantar da kanta a jikinshi sai yanzun da suke cikin shekara uku da aure kafin rabo ya zo.
Cikin dare Hajiya Laraba ta kira wayarshi a rikice domin jikin Hisham ne ya tashi. Kasancewar wayar a silent yake bai ji kiran ba, ni ce da fitsari ya tashe ni naga wayar na haske ban san tsautsayin da ya kaini daga kiran ba ashe dai rabon na sha zagi ne “Hello...” “Ke jakar ina ce da zan kira mijina ki ɗauka? Dalla ba shi waya malama uwar sanabe an bi an manne wa mijina” Siririn tsaki na ja wanda ban san dalilin sa ba na kuma kashe wayar ma gabaɗaya. Kallon wayar Hajiya Laraba ta yi tare da sake kira nan ta ji wayar a kashe wani uwar ashar ta ƙunduma tare da fitowa ta kira mai gadi suka fita da Hisham zuwa mota wanda ya ɓata gaban rigan shi da aman jini, gabaɗaya ya fita cikin hayyacinsa haka suka nufi asibiti sai dai tun kafin su isa rai ya yi halinsa. Koda suka isa likita ya faɗa mata ai ya rasu zubewa ta yi ƙasa tare da ɗaura hannu a kai tana faɗin “Na shiga uku na lalace Ɗana ya mutu wayyo Allah! Wallahi duk wannan yarinyar ce sila shegiya baƙar ƙaddara ƙarshen ki ba zai yi kyau ba, in ban da boka ya ce min aiki ba zai tasiri a jikin ki ba wallahi da na daɗe da hallaka ki” Haka ta dinga faɗe-faɗe har a asibitin har wayewar gari.
***
Ni tun yaushe ma na manta da Hajiya Laraba ta kira wayarshi sai da muka tashi sallah ne ma na tuna nake sanar mishi da matar shi ta kira. Shi ma sai da ya yi sallah ya ɗauki wayar ya kunna kiran Hajiyarsa ne ta fara shigowa bayan kalma Innalillahi wainna ilaihir rajiun babu abin da yake nanata wa kallon shi na yi da sauri tare da faɗin “Lafiya? Mai ya faru?” Sauke wayar ya yi daga kunnen sa yana faɗin “Hisham ne ya rasu...” “Ya Allahu!” Kalman da na furta kenan ina jin ba daɗi a raina, haka muka shirya a gurguje zuwa gidan rasuwan ina saka kai na cikin falon na tsinkayo muryanta tana faɗin “Shegiya la'ananniyar mayya 'yar matsiyata kin lashe min kuruwan Ɗa fita min a gida!”
Hajiyar shi dake zaune ta ce “Subahanallahi Balaraba wacce irin magana kike haka? Kayya! Bai dace ba sam, wannan kalaman sam ba ta yi min daɗi ba, ke Nuriyya zo nan ki zauna.”
“Na rantse da Allah Hajiya wannan annobar yarinyar ba za ta zauna gidan nan ba ta wuce ta fita in ba haka ba, ita ma ta baƙunci lahira 'yar iskar yarinya ai da na kira wayarshi jiya kashewa ta yi bayan ta yi min tsaki..” Da sauri na fita ina share hawayena Suhaima ce ta miƙe tare da biyo Nuriyyan. A farfajiyar gidan na haɗu da Mamanmu ita da su Fiddoh hannun Mamanmu na kama hawaye na tsiyayomin “Sannu Nuriyya ya haƙuri kuma? Amrah ce take sanar da ni rasuwan duk ba mu ji ba.." Shigowan shi ya sa suka fara gaisawa hannun Amnoor ya kama ya shiga da ita cikin falon Suhaima na biye da shi haka ma Maman Nafisa da Zaliha Fiddoh kan ta zame jikinta ta fita ganin Alhajin da take mutuwar so shi ne mijin 'yar'uwarta. Wani irin zafafan hawaye ne ya shiga wanke mata fuska, ita kodan ba ta taɓa ganin shi tare da Amnoor ba shi ya sa ba ta gane shi ba? To ita ko waya ba ta riƙe wa balle ta gane shi ne mijin yar'uwarta ko lokacin da Nuriyya ta zo musu gaisuwar sallah tana jin yanda Zaliha ke zuzuta kyawun da suka yi a hoto ita da mijinta amma ba ta taɓa ɗaga kai ta kalli hoton ba bare ta gane shi. Shi kenan babu ta yanda za a yi ta mallake shi tun da dai yayarta gudan jininta ce ke auren shi. A can gidan rasuwa kuwa rigima aka yi sosai lokacin da Hajiya Laraba ta ga Maman Nafisa tsohuwar 'yar aikinta kuma wai ita ce Maman kishiyarta aikuwa nan ta dinga zage-zage har Hajiya Umma yau ta zagu duk da kasancewar ta yayar mahaifiyarta kuma uwar mijinta hakan bai sa ta raba musu ba, Alhaji Aminu kuwa ya zuciya sai da Hajiyar shi ta dakatar da shi, jikin Suhaima ya yi sanyi sosai lokacin da ta ga Maman Nafisa, nan ta dinga nadaman abubuwan da ta yi mata a baya.
Sai da Maman Nafisa suka fito ta lura da babu Fiddoh tare da su. Suna ƙara so wa gida ta sameta zaune ta rafka uban tagumi ga hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta. “Mamanmu ban shi ne mijin Noor ba, sai yanzu na fahimci komai, dan Allah Mamanmu kar Amnoor ta san wannan maganar kar ki bari ta san mijinta nake so dan Allah, ni na amince zan auri Emanuel kawai” Rumgumeta Maman Nafisa ta yi tare da faɗin “Ma Sha Allah! Na ji daɗin jin wannan furincin, kuma In Sha Allahu Nuriyya ba za ta ji wannan labarin ba, Allah Ubangiji ya yi muku albarka”
Tun daga wannan ranar bai sake barina na je gidan rasuwan ba, har aka gama zaman kwana bakwai kowa ya watse. Saƙon zagi kam ina sha daga wurin Hajiya Laraba tun abin na damu na har na watsar da ita ganin babu abin da mijina ya rage ni da shi musamman ma yanzun da cikina ya fara fitowa soyayya kuwa sai wanda ya ƙaru. Haka muke cin karen mu ba babbaka a gado ma haka muke kashe kanmu da daɗi, lokacin da cikina ya shiga wata biyar aka yi auren Suhaima bayan haka da sati biyu aka yi bikin Fiddoh wanda ba ƙaramin daɗi na ji ba. Bayan wata huɗu Allah ya sauke ni lafiya inda na samu 'yan biyu duka maza faɗar irin farinciki da murnan da Alhaji Aminu shi da Hajiyar shi suka ɓata lokaci ne, Hajiya Laraba kuwa ƙiri-ƙiri da ta zo barka ta faɗa min maganar da ya girgiza ni hatta jama'ar ɗakin sai da suka ce na yi hankali da matar nan dan ga dukkan alamu za ta aikata abin da ta faɗa na ganin bayana da yarana da ta ce za ta yi. Cike da tsoro na kira Mamanmu ina kuka na sanar mata dariya kawai Maman Nafisa ta yi tare da faɗin “Ai ki kwantar da hankalin ki, kamar yanda a baya ba ta yi nasara a kan ki ba, ta je ta jiggata haka ma yanzun babu abin da za ta miki, dan duk sheɗancinta ba ta isa ta taɓa yara ba balle kuma ke, ki kwantar da hankali ba abin da zai taɓa ku ln Sha Allah” Amnoor na kashe wayar Maman Nafisa ta ce “Ina ga Hajiya Laraba na nema wa kanta mutuwa ne wallahi, dan in ta kuskura taɓa min 'ya da jikokina ko Ashraf bai yi mata komai ba ni zan mata”
Ba'a sauya musu sunan su ba, haka ake kiran su da Hassan da Hussaini duk da na yi tunanin zai mayar da sunan Haisam sai na ga ba haka ba, ni ma kuwa na ji daɗi da bai mayar da sunan ba. Wankan gida kan ya ƙi amincewa na tafi, duk yanda Maman Nafisa ta so na dawo gida haka bawan Allahan nan ya murzawa idanunshi toka a kan babu inda za ni. Haka na yi jego na a ɗakina a ranar da na yi kwana arba'in Amnoor ya ce shi haƙurin shi ya ƙare a daren ranar ba mu runtsa ba saboda shagalin da muka kwana yi dan an ci uwar sabada.


Ƙarshe. END


ALHAMDULILLAH! A nan na kawo karshen littafin AMNOOR kuskuren dake ciki Allah ya yafe min, da ni daku masu karatu Allah. Ina muku fatan alkairi masoyana jama'ar Wattpad Arewabooks WhatsApp ina sonku domin Allah. Sai mun haɗu a sabo A'isha JB ke muku fatan alkairi sai mun haɗu a sabo.
08062715485 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment