Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mugun miyau. “Koma ki bi shi ku tafi!”
“Maman mu..”
“Rufe min baki munafuka ke har kin yi wayon da za ki dinga satar hanya kina bin miji? Karki kuskura ki shigo gidan nan...” Shuru ta yi ba tare da ta ƙarasa maganar ba tana kallon Alhaji Aminu da ya juyo zai yi mata magana “Alhaji Aminu kai ne mijinta?” Kallon shi Nuriyya ta yi tare da kallon Maman su tana mamakin daman ba ta san mijinta ba? Amma ta yaya ta kira sunan shi kai tsaye ? da alamun dai ta jima da sanin sa...


Paidbook ₦500
09079740079


_Washh Allah na gaji wallahi_🙁


#Amnoo!
#Romance
#Sexstory
#Sadstory
#Sisterslove
[5/9, 11:45 PM] FARHATULƘALB💔🤗: *♡AMNOOR...!*
_A romantic story_
Wattpad: ayshajb
Arewabooks:ayshajb
®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
★F. J. W. A★


Free page 31_32


Ku je YouTube ku yi Subscriber Channel ɗi na FARIN JINI HAUSA TV. Domin samun ƙayatattun littafanmu.


H-P Place Group.


“Dan Allah Mamanmu ki yi haƙuri..” A fusace ta ce “Ungo nan, shashasha mara lissafi ai ni kin gama ba ni mamaki tun da har kin san dabarar da za ki yi ki bi miji kuna yawon gantalewa a titi, na faɗa miki muddin kika yarda na ga ƙafarki cikin gidan nan zan saɓa miki. Ki bishi ku ƙarata can”
“Daddy ka gani ko? Ka ga irin abin da nake tsoro yanzu ta fusata wallahi ba za ta taɓa yarda ba tun da ta ce haka, ba ta canza magana...” Na yi furucin hawaye na zubo min shi kuwa ya ma rasa me zai ce mata, wani iri yake jin abin ya san idan Laraba ta san matar da yake aure 'yar mai aikinta ce akwai matsala. Fitowar Zaliha da jakar kayana shi ya sake tabbatar da Mamanmu ba za ta sauko daga dokin fushi ba, ina kallon shi ya ɗauki kayan ya saka a mota “Aunty Amnoor ku ta fi kawai, tun da ta ce haka kema kin san halinta bare yanzu ban san abin da yake saurin fusata Maman Nafisa ba, abu kaɗan za ka yi mata ta hau faɗa, ki yi haƙuri kawai” Juyawa ta yi ta koma cikin gidan tana ji ya kama hannunta tare da buɗe motar ya saka ta. “Sai ka ce mara gata? Wallahi Daddy duk kai ka ja min wannan abun, babu 'yan rakiya daga ni sai kai za mu ta fi...” Hannunta ɗaya ya kama yana jin yadda sautin kukanta ke taɓa zuciyarshi. “I'm sorry Amnoor, duk laifi na ne amma please ki daina kukan nan yana taɓa zuciyata” Kwantar da kanta ta yi a kafaɗarshi tana sheshsheƙan kuka yana daidaita parking motar ya buɗe mata tare da kamo hannunta dricet yai hanyar ɗakin shi da ita, zaunar da ita ya yi kan bed tare da riƙe hannunta cikin na shi “Ki yi haƙuri..” Gyaɗa mishi kai na yi ina danne kukan da ke shirin ƙwace min. Fita ya yi daga ɗakin can sai ga shi ya dawo da kular abinci freezer ɗakin ya buɗe tare da kwaso tarkacen driks, duk wannan abubuwan da ya jere su gabana ban kalli ko ɗaya da niyyar ci ko sha ba, illa wani haushin sa da ya cika zuciyata. Kayan jikinshi ya cire tare da ɗaura towel a ƙugunsa, juyowa ya yi yana Kallonta kana ya ce.
“Tun da ba za ki ci abincin ba zo mu yi wanka” Kallon shi na yi tare da ɗauke kai dan na lura bai ma damu da damuwata ba, sai ma wani kallon da yake binta da shi. “Please...” Ya faɗa tare da kamo hannunta yana cire himar ɗin da ke jikinta, tare suka nufi toilte ɗin tana kallon ikon Allah ganin yadda aka tsara komai tare da narkar da dukiya. Saukan numfashinsa ta ji a wuyanta yayin da hannayen shi ya kasa zama wurin ɗaya, ta lura Daddy yana daga cikin fitinannun mazan nan ne wadda ko da za su kwana yin abu ɗaya ba zai gajiya ba, kunna musu shower ya yi tare da jan zip ɗin rigarta nan take yai ƙasa tsakiyar bayanta ya ci gaba da shafowa tare da ɓalle pin ɗin brezian ta. Shafo gashinta yai tare da haɗe fuskokinsu yana goga hancinsa saman nata. Ajiyar zuciya ta sauke tare da buɗe tsumammun idanunta tana kallon yadda yake lumshe na shi tare da sauke ajiyan zuciya. Tallafoshi ta yi tare da manna bakinta saman na shi, nan suka shagala da abu ɗaya sun jima sosai a toilte ɗin domin sai da ya juya ta ya ji ya samu nutsuwar da yake buƙata sannan suka yi wanka, ai tana fitowa ta sauka kan abincin da ya ajiye wanda har ya huce, sosai ta ci abincin domin cikinta tamkar wacce aka yashe. Kallonta yai tare da sakin murmushi sannan ya fita ɗakin Laraba ya nufo “Yaushe ka dawo? Na ga har ka yi wanka ka sauya kaya” Yana riƙe da hannunta suka zauna gefen gado. “Ban jima da dawowa ba, sai dai na ɗauko Amnoor..”
“Wacece kuma Amnoor?” Ta faɗa tare da zare hannunta ta mike tsaye “Matata mana..”
"Ka ɗauko ta? Tun ba a yi bikin tariyar..” Dakatar da ita ya yi. “Na faɗa miki na ɗaukota ne don kar sai gari ya waye ki ganta...” Da ƙyar ta iya danne abin da ke ta so mata kana ta ce “Na fahimta” Daga haka ba ta sake cewa uffan ba har ya gama zaman shi ya fita a ɗakin. Wani dogon tsaki ta ja tare da ɗaukar wayarta ta kira ƙawarta. “Alhj Aminu dai ya ɗauko wannan shegiyar matar ta shi, ya zo yana faɗa min ya taho da ita, sai ka ce ba ta da dangin da za su kawo ta” Dariya ƙawarta ta yi sannan ta ce “Ba rashin dangi ba ne ki fahimta, a yau babu uwar da za ta ɗauki wannan iskancin a yi aure sama da wata takwas 'ya na zaune a cikin gida, ba na raba ɗayan-biyu ko dai yana lallaɓata suna shoshalewa ko kuma dai uwar ta fahimci wani abun shi ya sa suka ba shi ita ba tare da su sun kawota ba”
Laraba ta ce “An ya kuwa Aminu zai iya tarawa da ita a waje? Kai! Ba na jin zai yi haka..”
“Ban katse ki ba, amma ba a shaidar namiji musamman ma mijinki ke fa kike faɗa min yadda yake bin ki ba ya miki da wasa, a rana zai iya juye miki so biyar kar ki ji mamaki dan ya ɗauke ta sun fita holewa. Wancan karon ai tare suka yi tafiya ya dinga raina miki hankali ke ga ki shashasha kina zaune sake da baki mijinki na can yana shan madarar budurci...” Runtsa idonta ta yi tare da faɗin “Ya isa haka! Yanzu yaushe za ki koma wurin malam?” Wani mugun dariya Fumi ta yi sannan ta ce “Haba ƙawata barshi ya sha romon budurci kafin a datse masa jijiyar jin daɗi...”
“Ba fa zai yuwu ba! Tun yanzu nake so a shafe jijiyar a mayar da shi lagwali ya kasa taɓuka mata komai ba na so ya mu'amulance ta bare har ya sake ajiye wani ƙwan a duniya. Wallahi tun da ta aure min miji sai ta ɗanɗana kuɗarta wani jin daɗi, ko farincikin aure ba za ta taɓa jin shi ba, sai na datse duk wani farinciki..”
Ajiyan zuciya Fumi ta sauke sannan ta ce “Shi kenan za a miki yadda kike so sai kin turo da abin sadakar”
“Wannan ba matsala ba ce zan tura miki yanzu” Haka suka ajiye wayar.
Lokacin da ya koma ɗakin ya samu ta kwanta shima kwnaciyar ya yi tare da shigar da ita cikin jikinshi “Amnoor..” Ya kira ta murya can ciki, lamo ta yi a cikin jikinsa tana sauke ajiyan zuciya. Kanta ta manna saitin zuciyarshi tana sauraron bugun da zuciyarshi ke yi. “Amnoor zuciyarka na bugawa da sauri me ya sa?” Ta yi tambayar tare da shafo tsakiyar ƙirjinshi. “Duk sa’ilin da zuciyata take irin wannan bugun adadin soyayyarki da ƙaunarki sake ninkuwa take cikin zuciyata. Noor! Ina matuƙar son ki..” Wani ƙayataccen murmushi ta sakar mishi tare da kissing ƙirjinsa. “Hubby Amnoor, adadin soyayyar da nake maka baki ba zai iya faɗarsu ba, yadda ka ke ji na a ranka, yana da bambanci da yadda ni ma nake jinka a raina” Ta yi maganar tare yin fari da idanunta wadda ya sa shi kamo ta yana faɗin “Kamar ya ya?” Ya ce yana kwance igiyar rigan barcin da ke jikinta riƙe hannunshi ta yi tare da faɗin “Nawa ya fi naka..” Haɗiye sauran maganar ta yi jin yadda ya shafo ƙirjinta zuwa mararta. Bai samu damar zuwa babban fada ba, kasance kasala da wani ciwon kai da ya sauko mishi duk yadda ya so kasawa yai. Haka suka kwana yana matse da ita cikin jikinshi.
****
Cire mata hannun da ta yi tagumi Maman su ta yi cikin faɗa ta fara mata magana “So hauka ne? A kan wanda bai san ki na yi ba za ki kassara rayuwarki? Namiji kike yi wa kuka da ta yin kanki? 'Ya'yana suna da kyawun da za a so su, ko Nuriyya da babanku ya takura mata ba rasa samarin ta yi ba, kwarjininta ya sa maza ke ƙin zuwa inda take, dirin jiki da ƙiba kawai ta fi ki, kyau da fari kin fita don me za ki tsaya sai shi bayan ya ce miki yana da matar da take mutuwar son shi, shima kuma yana sonta. Ba ga samari nan suna bin ki ba..”
“Duk ba su yi min ba! Ni shi nake so Mamanmu ni shi kaɗai na ke so gabaɗaya kin kasa fahimta yanzu kin zama me zafi, kina magana cikin faɗa bayan da ba haka kike mana ba” Kwantar da kanta ta yi saman cinyarta tana shafawa “Firdausi rayuwa babu yadda ba ta juya mutum, ko ni ina mamakin yadda na koma mafaɗaciya, halayyar babanku na daga cikin abin da ya sa na koma haka, da kuma yadda 'yar'uwarki ta raina min hankali tana bin mijinta wani lokaci har kwana take wurinshi a tunaninta ban fahimta ba, ba ta san na yi mata shuru ba ne..”
“Shi ya sa kika ce lallai sai ya ta fi da ita? Kin san ba ki kyauta mata ba, dan ɗazun ma sai da muka yi maganar da Amrah a kan yadda mijinta ya ɗauke ta ba tare da 'yan rakiya ba gaskiya ban ji daɗin hukuncin ba”
Maman Nafisa ta ce “Alhj Aminu shi ne wadda na yi aiki a gidansa, kin fi kowa sanin irin wulaƙancin da matarsa da 'ya'yansa suka min ai na ba ki labarin komai, shi ya sa na ce ya ɗauke ta su ta fi” Zaune Fiddoh ta miƙe tana faɗin amma Mamanmu me ya sa mijin Amnoor yake rawar jiki a kanta? Ki tuna lokacin da baba ya ɗauke wayarta still ya sake sayo mata wani ba tare da ɓata lokaci ba, yana girmama al'amuranku ke da baba, ki kalli yadda ya saya mana wannan gidan da muke haya ya dawo mallakin mu, sannan ya keɓance mana na mu ɓangaren ya gyara ya zuba komai na more rayuwa, ko akwai wani abu ne?”
Ɗan murmushi kawai Maman Nafisa ta yi tana faɗin “Abin a jininmu yake, duk 'yan gidanmu haka maza ke rawar jiki a kansu, muddin suka ji yadda abin yake..”
“Kenan akwai wani sirri na daban?” Fiddoh ta yi mata tambayar tana son tabbatar da akwai ɗin, domin irin hakan ta ganshi a karan kanta, yadda maza ke binta da zaran sun yi sau ɗaya haka za su ci gaba da bibiyarta gashi duk wulaƙancin da take musu suna shanyewa musamman ma Emanuel har yanzu ya kasa rabuwa da ita duk inda ya je haka zai dawo yana ba ta labari ba kamar ya ita ba, domin ita ɗin tana da wani baiwa na daban.
“Akwai amma ban san mene ne ba, na san dai namiji ba zai taɓa wulaƙanta min 'ya ba” Miƙewa Fiddoh ta yi tana faɗin “To! Duk yadda zan yi sai na yi wurin ganin na mallake shi, kuma koma wacece matar shi ko matan shi sun shiga uku muddin mijinsu na shiga hannuna, ba zan bi boka ko malam ba, amma ƙissa da kisisina tare da duk wasu sheɗananci zan yi don mallake shi!”
“Allah ya kyauta Ubangiji kuma ya shirye ki, kullum girma kike amma har yanzu ba hankali, kina tsaye kina kallo na kike faɗar za ki yi duk abin da zai sa ki mallake shi? Kenan za ki kutsa kai inda ba a yi da ke?”
Fiddoh ta ce “Ko yana sona ko ba ya sona ni dai na ji na gani shi nake so..” Tana gama faɗar haka ta fita a gidan “Allah kai ka ba ni ita, Ubangiji ka shiryar da ita, Allah ka nutsar min da ita ta dawo gida ta zauna ta bar rayuwar da take” Addu'ar da kullum take yi wa Firdausi kenan, domin ba ta jin daɗin rayuwar da take yi musamman da mutane suke aibata ta, sai dai duk zagin da mutum zai yi mata bai isa ya kalli ƙwayar idonta ko ya tunkare ta da wannan maganar ba, domin tana iya illata mutum. Police kuwa sun santa dan abu kaɗan za ta sa a cilla mutum a cell. Mutane da yawa na shakkar ta dan ba ta ɗaukar iskanci yarinyar da uban da ya kawota duniya ma ba ta raga mishi ba wa za ta ƙyale?.
★•°•°•°•°★
Maƙontan su na cikin gida ne suka je mata jere duk da ya zuba mata komai amma haka Maman Nafisa ta shiga kasuwa ta yi mata sayayya domin yanzu kam Alhamdulillah suna samun kuɗi daga bangaren shi ma yana musu aike kama daga kayan abinci, atamfofi, da duk abin da za su buƙata, a hakan ma tana taka mishi burki domin hidimar ta yi yawa. Ta yi mata sayayya daidai gwargwado babansu kam ya ce sisi ba zai kashe ba, tun da ta zama mai kuɗin banza miji ya zuba mata komai amma tana nan tana kashe kuɗi sai ta yi ta yi. Dariya kawai ta mishi dan yanzu ba ta cika mishi dogon magana ba, amma in zai kawo mata wargi tana taka mishi burki wadda yanzu ya fara shakkar ta ganin ta zama masifaffiya. Kuɗi kam idan ya ƙyalla ido ya ga ta ajiye cinikin turare kwashewa yake yi, in ta yi faɗar ta gaji haka za ta yi shuru, amma duk abin da ya danganci 'yar gaban gishinsa ba ya ma taɓawa sai dai ya sake adana mishi dan ta fi shi rashin daraja har cikin mutane take bin shi ta tsutsiye shi lallai sai ya dawo mata da abin da ya ɗauka, an yi haka ba so ɗaya ba, ba so biyu ba. Da ya ga lallai ta fishi sheɗanci tuni ya daina taɓa kayanta.


*°*°*°*•°
Ba ta fuskantar matsala daga matar shi suna zaune lafiya. Dan tare suke shiga kichin su yi aikin abinci sa’i da lokaci Suhaima ta kan kawo musu ziyara domin dai ya ƙi yarda ta dawo gidan ganin yadda Amnoor take da fara'a kuma suna zaune lafiya da mahaifiyarta ya sa ita ma ta sake har suke gaisawa da 'yar hira tana girmamata a matsayinta na matar mahaifinta domin sai da Hajiya Umma ta ja mata kunne sosai tare da gindaya mata kashedi na ba ruwan ta da Nuriyya bare ta ce za ta taya uwarta kishi, da ke tana tsoron kakar tata shi ya sa ta nutsu take mata biyayya. Yanzu tana ɗan fita yawon daren ta ganin Hajiyar ba ta takura mata Lil ne dai ya ƙi saukowa tun faɗar da suka yi da Fiddoh duk inda ta samu labarin yana zuwa bin shi take yi. Amma ko kallo ba ta ishe shi ba.
“Amnoor ya dai na ga kin yi wani yanayi na daban a kwai wani abun ne?” Ya faɗa tare da kamo hannunta, ɗan murmushi kawai ta yi tare da juyawa tana ƙoƙarin shafa mai towel ɗin da ke jikinta ya kai hannu zai kwance mata, ba ta hanashi ba, domin ta san ba abin da zai iya yi mata wanda ya wuce ya jagwal-gwalata tana jin shi ya fara taɓe-taɓe ita dai ba ta ce komai ba bayan shurun da ta yi. “Ki yi haƙuri wallahi ni ma ban san abin da ke damuna ba”
“Uhm ka ji na ce wani abu dangane da rashin kafiyarka? Ko na ce maka na gaji da..” Rufe mata baki ya yi da sauri yana faɗin “Baki faɗa ba, amma alamu sun nuna kina kewata ko? Na sani ni ma ina kewarki” Danne damuwarta ta yi tare da haɗe fuskokinsu kissing lips ɗin shi ta yi. “Hubby karka damu In Sha Allah za ka ji sauƙi”
“Kin tabbata babu damuwa?” Juyowa ta yi tana kallon shi tare da faɗin “In sha Allah babu komai” Jan karan hancinta yai tare da faɗin to ki gama shiryawa sai mu je asibitin tare ko?” Gyaɗa mishi kai ta yi, yana tsare har ta gama shiryawa kallonta kawai yake yana haɗiyar miyau shi dai wannan ciwon ya katse mishi jin daɗi. Har za ta shafa man baki sai ta ajiye domin ta san ko ta shafa haka zai lashe, yana riƙe da hannunta har wurin mota Hajiya Laraba ta rako su tana musu a dawo lafiya, motarshi na fita a gida ta kwashe da wani mugun dariya tana faɗin “Haka za ka yi ta gantalin neman magani ba za ka taɓa samu ba” Suna zaune gaban likitan da ta duba shi hannunshi na cikin nata ya ji likitan na faɗin “Alhj ni kam wannan lamarin naka yana ba ni mamaki, duk da an yi aiki a wurin kuma kana shan magani amma dai har yanzu fa sai a hankali...”
“Kamar ya ya sai a hankali?” Likitan ta ce “Batun iyalinka nake nufi sai...”
“Dalla dakata malama ban fahimce ki ba?” Kallon shi likitar ta yi ganin yadda ya fusata.
“Duk kuɗin da na ba ku? Ke kisan abin da nake ji kuwa? Matana biyu fa? Ki kalleta da kyau kina nufin haka zan zauna ina kallon ta da kuruciyarta?”


“Sau nawa kake yi? Kallon Amnoor ya yi sannan ya sake kallon likitar “A sati ko a rana?” Sunkuyar da kai na yi domin na fahimci a kan me suke maganar duk sai na ji kunya ta baibaye ni amma shi ko a jikinshi likitar ta ce “A rana”


“Ke sau nawa kike yi?” Ya wurga mata tambayar dan ya lura tambayar renin hankali take mishi “A'ah Alhaji ba ka ba ni amsar tambaya ta ba”
Riƙe mishi hannu na yi tare da matsewa ina mishi alamar rarrashi domin na lura ya fusata da maganar likitar. “Idan na faɗa miki adadin da nake yi a rana tsorata za ki yi, domin tun ba ta saba ba haka har ta saba tana nema da kanta, shi ne yanzu za ki faɗa min wani zancen banza ina ga ba ku san aikin ku ba ba zan iya zuba ido ina kallo mace ba tare da na juye mata abin da...” Riƙo shi na yi tare da faɗin “Ki yi haƙuri Dr tun da aka ce mafitsarar shi ya samu matsala yake a fusace, musamman ma idan aka ce ba zai iya tarawa da iyali ba” Na faɗa ina kallon ƙwayar idonshi “Ni na ce miki ba na jin ƙarfin da zan..”
“Mu je gida lokacin shan maganinka ya yi” Dariya kawai Dr ɗin ta yi domin daga shi har matar tashi dariya suke ba ta ganin yadda ta ɓata rai tana cewa su je ya sha magani shi kuwa sai faɗin “Ni na ce miki ba ni da ƙarfin da zan yi wani abu? Wato kin raina ni yanzu saboda kin ga ba ni da lafiya ko? Ya yi kyau!”
“Dan Allah duk wannan rigimar ka ajiye shi har mu ƙarasa gida tukun na lokacin ne zan kulaka amma ban da nan domin idon jama'a na kanmu” Suna ƙarasawa gida ya fisgota da ƙarfi kamar zai ɓalla mata hannu “Saboda ba ni da lafiya shi ne kike min haka? Kin gaji da ni ko kina son rabuwa da ni dan ba na biya miki buƙatar ki...” Hannunshi ta riƙe har cikin falonta Zaliha ta iske zaune. “Aunty Noor kun dawo? Daddy ya jikin ka? Na zo Maman Suhaima take cewa kun je asibiti” Da sakin fuska ya amsa mata sannan ya fita zuwa nashi ɗakin. Zama Nuriyya ta yi tana faɗin “Ai na manta yau za ki zo ga shi ban girka mana komai ba ko za ki shiga ki mana girkin?” Miƙewa ta yi tana faɗin “To” Kayanta Amnoor ta adana mata sannan ta nufi ɗakinsa yana kwance ta ɗauko magani da ruwa tana miƙa mishi karɓa ya yi tare da ƙure ta da ido, ɗauke kanta ta yi sannan ta miƙe ta fita a ɗakin.
Da yamma suka haɗu dukkansu a falo suna cin abinci suna kammalawa Laraba ta yi ɗakinta domin tun da Amnoor ta tare ta sallama mata shi tun da ta san abin da ta ƙulla musu. Kwana biyu Zaliha ta yi ta tattara ta ce za ta koma gida dan masifar da suke yi kullum dare ya ishe ta ɗan kullum da dare sai sun yi faɗa yau da wuri ma suka fara rigimar ta su. “Daddy mai ya sa kake min irin haka? Kana ganin ƙanwata na nan amma kullum sai ka ta da rigima ka bari ta koma mana in ya so koma mene ne sai ka yi tun da ka zama mafaɗaci..”
“Ni kike faɗawa wannan maganar? Amnoor zan mare ki...” Da mamaki ta matso tana faɗin “Daddy ai ba sai ka faɗa ba, daman na daɗe da fahimtar kana son kai hannu jikina wallahi na gaji da wannan fitinar naka haba dan Allah sai ka ce wani ƙaramin yaro kullum sai an jiyo muryan mu...”
Kallon hannun shi ta yi tare da faɗin “Shi kenan ka mare ni ko wutar da ke cin zuciyarka zai ragu” Fitowa ta yi a ɗakin zuwa nata ɗakin dan kusan sati basu kwnaciya tare tun da ya tsiro da faɗar dare. Kallon Zaliha ta yi tare da faɗin “Ke lafiya na ganki da jaka?” Zaliha ta ce “Aunty Noor gaskiya ni gida zan ta fi wallahi ba zan iya da diraman ku ba” Ɗauke hawayen da ke zubo mata ta yi sannan ta ce “Shi kenan ki gaishe da Mamanmu ki ce mata ina kewarta” A haka suka yi sallama. Zama ta yi tare da fashewa da kuka dan ta rasa abin da ke jawo musu wannan fitinar kullum dare babu kwanciyar hankali sai sun yi faɗa sun koma tamkar karnuka tun ba ta kula shi har ya fara kaita maƙura.


#Paidbook 500
09079740079
[5/9, 11:45 PM] FARHATULƘALB💔🤗: *♡AMNOOR...!*
_A romantic story_
Wattpad: ayshajb
Arewabooks:ayshajb
®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
★F. J. W. A★


Free page 33_34


Ku je YouTube ku yi Subscriber Channel ɗi na FARIN JINI HAUSA TV. Domin samun ƙayatattun littafanmu.


H-P Place Group.


“Ya Nuriyya suke.?” Maman Nafisa ta yi mata tambayar bayan ta ajiye jakar Zaliha da ta karɓa. “Gaskiya babu lafiya Maman mu, dan kullum Aunty faɗa suke yi da mijinta...” Dakatar da ita Maman Nafisa ta yi da faɗin “Hajiya Laraba ke haɗa su faɗar ko? Dan na san za ta aikata fiye ma da hakan in dai a kan mijinta ne..” Cikin sauri Zalihar ta katse ta da faɗin “Ko ɗaya Mama mu, ai Maman Suhaima tana da kirki kuma suna zaune lafiya sai ma kinga yadda suke komai tare tamkar ma ba kishiyoyi ba tsakaninta da Daddy ne ban san me ke faruwa wanda kullum yake haddasa musu rigima ba” Shuru Maman Nafisa ta yi tana juya zancen a ranta ta san muddin Nuriyya ta ce ta yi kewarta tabbas tana cike da damuwa mai tarin yawa ne. Yinin ranar haka ta yi shi zuciyarta cike da tunanin ɗiyar tata, da a ce Fiddoh za ta amince da ta kaiwa Noor ɗin ziyara amma ta san da kamar wuya. Aikuwa Fiddoh na dawowa ta tare ta da maganar buɗar bakinta sai cewa ta yi “Ni in je gidanta? To in yi mata mene?” Da ga haka ba ta sake

Please Login or Register in order to submit comment