Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taba zatayi maganinsa itama.


Abdulhakim daya kame atsaye hannunsa arike da juna yahau gyada kansa yana fadin "lallai Abdallah wuyansa ya isa yanka agabana yake fadin haka wato inje ingayawa dady ma baya shakka? Tabbas ina tunanin akwai abokan da suke hure masa kunne aiko walh baxan taba barin yaringa wulakanta kiba khadija kada kisa wannan abin daya fada arai kinji wallahi ko yana so ko baya so sai yayi xaman Aure dake cikin kwanciyar hankali da lumana.


Ta wacce hanyar "!? Ta fada aranta amma afili saitace dashi "Aini walh Abokin birni bari kaji abinda baka saniba sbd kai nake zaune agidan nan da kuma dady domin inhar akace yau nanemi saki nakoma kauye to abin zaizame muku magana ace kun kasa rikeni ko ayi muku fassara dayawa duk lokacin da kukaje nunaku za.a ringayi amma da ace bakwa xuwa garinmu to walh da baxan yarda naxauna bama balle har akai ga hakan.


Yahau gyada kansa yana fadin "that is true khadija.!


takama baki tana cewa "ikon Allah me hakan kuma kenufi? Kasan niba jin wannan yaren nakeba bafa abokin birni dan Allah fassara min


Yayi dariya yace mata "wannan gaskiya ne shine abinda nafada khadija domin duk maganarki gaskiya ce kuma naji dadi da kk kasance me hangen nesa shiyasa kk burgeni dan haka inaso daga yau kiyimin alqawarin zaki zauna da dan,uwana da zuciya daya zaman Aure babu gaxawa.


Tayi jim kana tace "nima saikayimin Alqawarin wani abu kana zan maka.


Yace "fadi naki nayi alqawarin zan mk kowane irin abune kinji Dijah.


Ta lumshe idonta jin dadin sunanta daya fada


Ta bude idonta ahankali ta watsasu akanshi aiko dai take yaji wata kasala na neman rufeshi agun


Tace "inaso kaimin Alqawarin kullum zakazo gidana muyi hira.


Yayi jim kana yai murmushi yace "wannan bame wahala bane nayi mk alqawari saidai kinsan jiki da jini zan iya taashi daga aiki inji gajiya kinga dole inxauna agida inhuta ko?


Ta gyada kanta


Yaci gaba "to inkinmin Alqawarin dafatan zaki cika?


Ta daga kanta tana murmushi


Yace" to inaso akullum ki kasance kina me gaida mijinki kiringa masa kuma sannu da zuwa tunda gashi naga bakiyi masaba.


Ta make kafada tace "tabdijan nikam bazan shigar masa daki ba dan innakai kaina duk abinda yaimin ninajawo kana ganifa yanxun ma maganganu yagayamin masu zafi saidai in inringa tsayawa inya futo zai futa ingaidashi afalon


Abdulhakim ya murmusa kadan yace "kina da kafiya khadija amma hakan ma is fine




Ta kama baki tana dariya "niko dan Allah inason inkoyi wannan yaren naku me dadin ji.


Ya tintsire da dariya yace "turancine fa ba yaren muba nida kk ganina bahaushene usul kuma turanci baida wuyar koyo inmutum yasa kansa dagewa kawai zakiyi wajen koya din.


"To yaushe zamu fara da gaske nakefa Allah


Yace mata "daga gobe khadija, innazo gobe sai mufara tun daga A,B,C,D


Tahau murna tana dan buga tsallenta yabita da kallo yana girgixa kai tabbas akwai yarinta atattare da khadijan


Yace mata dakata daina murnar hakan nikuma inaso inkoyi fillanci yaushe zamu fara knn.
??


Tayi farat tace "aini ko yanxu inkanaso saimu fara.


Ya girgixa kai yace "mubari goben innaxo saimukoya tare kiyimin nayi miki.


Tace to "


Ya mike yana shirin tafiya


Tayi narai narai tace "kai abokin birni har tafiya?


Yace "ah!to inban tafiba kwana zanyi? Mijinkifa yadawo khadija yakamata kibashi kulawa ko domin samun lada.


Hawayene suka xubo mata domin taki jinin taji ance Abdallah mijinta gashi kuma yau kaunar datakewa Abdulhakim din tadawo sabuwa tadawo danya shakaf


Yaji kamar yasa hannu ya goge mata hawayen amma ba dama


Sai yahau girgixa mata kai yana mata alama da hannu cewar ta daina kukan harda yi mata dabara "kiyi saurin tsaida hawayenki khadija kiringa boye damuwarki domin inhar kika bari Abdallah yaga kina kuka dadi zaiji yaxaci shiyasaki a bakin ciki kuma kinga dadi zaiji dan haka ki kiyaye kinji.


Ta gyada kanta


Haka sukai sallama jikinta asanyaye takoma bedroom ko kallon dakin Abdallah batayiba don zuciyarta tashiga jaxaba ta soyayya


Shikansa Abdulhakim din da tunaninta ya kwanta ga wani tausayinta daya mamaye masa zuciya to waishin ta yaya zai taimaki khadija ne? Zaikuwa iya jurar ganinta adamuwa??


********


Washe gari kuwa Abdulhakim yacika mata alqawari yaxo mata da yammaci kusan biyar da rabi


Ranar mubina ta tafi da wuri ana la,asar ta tafi wai zasuje unguwa


Amma da intaxo mata sai magriba take tafiya tana koyarda Dije girki kal kala da abubuwan da bata saniba


Tatsalo wankanta cikin wata doguwar riga da aka kawo mata cikin kayan da akace angone yahado musu akwatina daddaya


Tayi kyau ainun


Dan Abdulhakim dayaxo sauran kiris ya yaba kwalliyar saikuma yatina bai daceba hakan saiyaja bakinsa ya tsuke


Ruwa me sanyi dije takawo masa a jug


Yasha kadan yadire yana fdin "ina Mijinki ko bai dawoba?


Fuskarta ba fara.a tace "banajin yadawo don baishigoba


Yace ""hhhmmm yayi kyau ai.


Tace "abokin birni intambayeka mana.


" Inajinki " yafada yana kallonta


Tace "wai dan Allah ya kuke da Abdallah anya momyce ta haifeshi kuwa?


Yayi dariya yace "itace ta haifeshi mana nine dai ba itace ta haifeniba don mahaifiyata ta rasu itada mahaifina hatsari sukai dady dan,uwa ne gun mahaifi shike rike dani tun ina yaro


Ta gyada kai asanyaye tace "Allah yajikansu.


Yace "Amin. Yanxu dai mufara karatu ko?.


Tace "Eh mana ashirye nake ai




Yace "baki shiryaba tunda banganki da littafi da fensir ko biroba


Ta yarfar da hannu "toni ina xangansuma aikai yakamata katahon dasu tunda ba fita zanyi innemoba ko


Yace "to aishikenan kinga yau karatuna za.ayi knn,ke naki ayi gobe innaxo da abin rubutu knn.


Ta gyara zama tace "To, dame za.a fara maka?


Yace "Da gaisuwa ko kirge nakeso mufara


Tace "to kaga dai *1-GO'O* *2-D'id'i* *3-Tati* *4- nayi* *5-Jowi* *6-joweego'o* *7-joweed'id'i* *8-jowee tati* *9-joweenayi* *10-Saffo*………yadaga mata hannu "Saurara haka *"yar fillo* atsaya iya nan gobe ma dora inyai yawa zan mance yanzunma saikin maimaito


Taringa masa dariya datake fada yana fada din harda zolayarsa "walh dai kunji dadinku da har baku dage kun koyi fulatancin ba garin fa mahaifan kune.


Yace mata "a.a kada kiyimin gori ni uwata kawai aka haifa a kauyenku.


Tace "naji yanxu dai muje wani abun inka shirya muci gaba


Ya gyara zama yana dariya yace"nashirya muje zuwa nakwashe wancen.


Tace " to koro tambaya mana ingaya maka da fulatancin.




"Yawwa idan zance kyakykyawa da fulatanci me zance ?


" *Bod'd'um* tafada atakaice


"To mummuna fa?


Tace " *Yiddud'um*


Yahau tafa mata yana cewa " najinjina mk fillo


Tace "bajinjinar da tafin ba dai karike shine.


Yace "zanrike inada babbar kwakwalwa yarinya.


Yaci gaba "to idan zance zantafi masallaci fa?


" *Mi dillay juulirde* _Zantafi masallaci_


"Ina rubutu fa?


Tace " *Mi d'on winnda.* _Ina rubutu_


"mun godewa Allah fa?


tace masa " *yettoore Allah* shine mun godewa Allah ka fahimta?


Ya gyada kansa


Yace "to abarshi haka kinga magriba tasawo kai zuwa gobe maci gaba


Ya mike zaitafi tahau fadin "Amma daka tsaya kaci abincin dare anan ko.


Yagirgixa kai yace "a.a nagode kawai gobe naci kinji Dijaa


Nan sukai sallama tabi bayanshi da kallo kawai tana girgixa kanta


*****
Abdallah yana kwance akan doguwar kujera a part din Ni,ima yana kallon Ajent Ragab.


Saiga Ni,imar takawo masa ruwa me sanyi


Tasha kananun kaya nasace xuciya don kusan ana ganin tsiraicinta da kwarkwasa ta dire masa agabansa tana masa sannu da hutawa ba laifi yasaki fuskar tasa harda ce mata "yawwa.


Ta zauna akujerar kusa dashi


Wayarsa tahau tsuwwa


Yana dubawa yaga babyn sace lowerst yadaga da fara,arsa cikin yanga da karairaya Ni,ima ta mike tadauko remote akan reciever tarage volume tadawo da tafiyar yauki ta zauna kusa dashi


Hankalinsa baya kanta sai soyayya suke zubawa shida masoyiyarsa awaya abinsu hankalinsa tashe yahau lallaba lowerst yana mata dabara na hanata ziwa Nigeria domin tasaka ranar da zatazo shikuma bayaso tazo taga yayi Aure ta tashi hankalinta ko kuma tayi masa hauka sbd tanada matuqar kishi yanxu saita yanki mace akansa


Ni,ima najinsa ranta na mata Quna ashe dama zancen da ake ceqa yanada budurwa aturai gaskene wacce ba musulmaba lallai ta yarda yana sonta tunda gashi taga har wani lallaba yake akan tace zatazo gunsa bayaso taxo ms yanzu


Ni,ima ta dura dayawa tacika tafashe jira kawai take yagama wayar ta tuhumeshi wacece suke waya kuma yau tana son taji matsayinta agunsa donta gaji da ajiye budurci ba.a lasa ms zuma......








_Tab muje zuwa_
🐄 *YAR FILLO* 🐄
_Dijen Kauye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕













*True life Story*






PG 45-50


Abdallah yana gama wayar da yakeyi da babynsa lowerst ya mike tsaye zaibar falon


Da sauri Na,ima ta tare gabansa ta kama kugu tace "babu inda zakaje saika gaya min wacece wannan kuke waya har kake mata alqawarin zaka Aureta agabana kokuma arniyar karuwar taka ce?


Ran Abdallah yai matuqar baci batai Auneba saijin saukar mari tayi akuncinta


Ta kama gun tana kuka "ni ka mara akan wata yar,iska.?


Bata kai ga rufe bakinba yasake kawo mata wani marin tayi sauri ta goce ya mari iska.


Ya nunata da hannu "ke kin isa ki aibata mini masoyiya kinsan kuwa irin matsayin da take dashi aguna? Toki kiyaye dan zan iya mk komai akanta domin ita kadaice zuciyata ke so kuma muddin ina raye saina cikawa zuciyata burinta na Auren muradinta.


Tahau kuka tana fadin "aiko walh baka isa ka kawo mana christan familyn nan namuba kuma inhar ka kara saka hannunka afuskata saina gayawa dady.




Yaharxuko mata "ki gayawa dadyn mana saime? Zai gutsirani ne ? Bari kiji ma ingaya mk daga yau in kika kara dosar inda nake saina matuqar bata mk domin saina mk abinda bazaki taba mancewa dashiba


Ya bangajeta ya wuce


Ta durqushe agun tana gunsheken kuka


Ta dade tana kukanta agun ta rasa mafita domin tana son Abdallah baxata iya nesa dashiba dan ko ganinsa tayi tanajin dadi


Sallamar Zannura taji da sauri ta goge hawayen tana ajiyar zuciya


Taso ta boyewa zannun to amma ta makaro domin zannura taji sautin kukan nata tunkafin ta shigo kuma ga idonta nan yayi jajir


Zannura tajata jikinta tace mata " kawata nafuskanci kina ckn damuwa kada ki boyemin domin damuwar ki tawace kuma nime iya samo mk mafitane sannan boyewar dazakiyi baxai amfaneki dakomai ba sai karin bakinciki


Ni,ima tayi tsit ajikin Zannuran tana jinta amma takasa magana


Zannura taci gaba tace "fada min meya saki kuka yaya ne ko?


Nan ma Ni,imar tayi shiru tana ajiyar zuciya


"Nasan shine domin naga futarsa azuciya yatada mota zai futa kamar ya tashi sama. Plz gayamin mana meya hadaku?


Ni,ima takama hannayen zannu tace "Zannura ke kawatace kuma ta wani bangaren ke kanwar mijina ce nasan zaki iya riken sirrina kuma keme taimakona nace dan Allah ki kawon mafita domin ina cikin wani hali,ina son yaya Abdallah so mai matuqar wahalar da zcy gashi ina sha,awarsa amma har yau baya kulani sbd shi nake duk wannan shigar dan intsokanoshi amma abanxa wata can arniya ta dauke masa hankali yanxuma akanta ya mareni yakuma ce kada inkara xuwa kusa dashi to nikuma baxan iyaba sbd Allah yayoni da sha,awa araina ina sha,awar inganni ajikinsa amma har yau nakasa samun wannan damar walh tsoro nake kada yajefani ahalaka




Zannura tahau girgixa kanta ta tausayawa Ni,ima hakkun don akwai mata dama masu sha,awa me yawa azahiri wanda basa iya dannewa


Tasan yayanta tasan halinsa Inya kafe a abu babu me tankwasashi to amma kuma ya xa.a yi mace har mace kamar Ni,ima ya kasa kyasata anya kuwa yayan nata baya bin mata ?




Ni,ima ta dafa Zannura tace "ki samo min mafita kawata walh inajin mugun sha,awar Abdallah aduk lokacin da sha,awarsa ta motsamin walh saidai insaka BF in kalla sannan nake jin dadin kaina natabbata kuma inba mafita nasamu to tabbas akwai matsala


Zannura tace "kinsan Yarinyar dayakeso ce ke daukar hankalinsa akan kowacce mace ya nace akanta Kowa afamilyn mu baya son ta bama akasar nan takeba Amma kinsan me zamuyi akai kuwa?


Ni,ima ta gyara zama tareda girgixa kanta da sauri


"Walh zuwa zamuyi gun wani malamin ayi musu farraqu kawai inyaso sai asaka sonki aransa ta qarfi da yaji


Ni,ima tayi murmushi tace "To yanzu yaushe zamuje ?


Zannura tace "ki shirya gobe sai muje, kigayawa yaya kice zakije gidanmu gaidasu Momy inyaso inkinzo saimu fito taren muje.




"To nagode hakan za.ayi zanzo muje.




*******
"kai Amaryar mu kinganki kuwa walh kinyi kyau meye sirrin ?




Dije tayi dariya ta harari Mubina tace "meye sirrin kuwa, bawani sirri to me kika gani ?


Mubina tace "naga kin kara wani kyau ne gashi kinyi kiba ga haske da fatarki ta karayi.


Dije tahau shafa fatarta tana cewa "kai mubina bandafa sharri dama can fatata fara ce.


"To amma dai kema kinsan kin canxa ko?


"Ina wani canji kullum ina faman tunani ai bawani canji saina rama danaga nayi.


Mubina ta kama baki tace "kai Amaryar mu tunani kuma?to tunanin me kkyi haka ?


Dije ta gyara zama tace "mubina ina tuna wani da zuciyata takesone walh ba son yayanki nakeba akwai wanda nake so Amma baisan ina sonshiba.


Mubina ta kyalkyale da dariya tace "shirmen banxa kenan kicema Son maSo wani kikeyi ?




Dije ta hade rai tace "Au,dariya ma zakiyimin muguwa bama zaki tausaya min ba inma shawara ce kibani ko addu,ar da zan ringayi inji sauki.


Mubina tace "aini shawarar da xan baki bata wuce ince kiso yayana ba.... "Allah ya kiyaye ke nifa walh inda wanda natsana kaf duniyar nan bai wuce shiba dan Allah mubar zancen nan mushiga wani.


Mubina ta hade rai itama tace "Amma dai Aunty khadija bakyamin kara walh amma agabana kiringa cewa kin tsani yayana kadafa ki mance uwa daya uba daya muke dashi yakamata ki sassauta kiringa rage tsanar don watarana nasan zaki soshi tunda tsana nakomawa Kauna


"Ta yaya? Cewar Dije


Mubina ta gyara zama tace "kinga abinda nakeso dake anan shine ki xama jajirtacciya wajen ganin mijinki yasoki domin ki zama ta gaban goshi tunda bake kadai bace a filin yakin, kadafa ki manta cewar Aunty Ni,ima tana sonsa ga wata can agefe dayake so kinga ke kadaice jinin bai haduba kinga acan gaba zaki iya zama bora.


Dije tace "wacece agefe take son nashi?


"Hhhmmm wata arniya ce bata sallah acan kasar waje take tare sukai karatu zamansa akasar shine sukai soyayya kuma yadage ita zai Aura amma su dady sun hanashi.


Dije ta ce "tab! shi yanzu nan arniya zai aura? lallai bai burgeba walh don ko ya Aureta insun haihu sai ansami arna ackn "yayan nasu.


Mubina tayi dariya tace "to ai shi musulintar da ita yakeso yayi sai suyi Auran in iyaye sun yarda.


Dije ta tabe baki tace "Allah yasa iyayan su yarda


Mubina ta dakar mata kafada "Amma dai kekam anyi sokuwa harma addu,a kk tayashi wato bama zakiyi kishi ba knn.


"Tab !kime?kishi akan wancen mara mutuncin tabdijan Allah ya yaye min ma in zanyin agaba. Ai ni dadima naji to meye acki ?idone nawafa kowa ya debo da zafi ai bakinsa


Mubina tahau tafa hannu tace "gud "yar fillo ashe kema kin iya karin magana


Dije tace "Au! kinzaci fanko ce ni to ai muna kwashewa inmunji hausawa nayi muna kuma fahimta.


Mubina tace "ni yanzu dai abu biyu ne yakawoni gidan nan, nafarko inaso kiringa koyamin filatanci domin Saurayina danake Saran zan Aura Bafulatani ne.


Dije tace "Angama bakida matsala tanan.meye abu na biyun.?




Mubina ta janyo wata lefa baka ta fito da kaya tace "kinga wadannan kayane nakawo mk kiringa sawa domin ki dauki hankalin yaya dasu don naga masha Allah kinada diri Aunty khadija komi yaji.


Dije tayi dariya tana d'add'aga kayan tana fadin "tabdijan ni zansaka wadannan fandarinka tsiraran? Aiko walh badaniba ko za.a bani miliyan baxan sanyasu ajikina aga tsiraicina abanxa ba.


Mubina me zatayi inba dariya harda kama ciki


"Yanzu dan kinsa kananan kaya mijinki yagani shine abanxa? To ai yabiya sadaki kinga ba zai zamo abanxaba saima lada zaki samu.


Dije ta maida kayan leda tana fadin "kenifa baxan sakaba kome zakice walh maxa kikoma dasu indai ladane mahadu a Sallah da Azumi.


Mubina taringa dariya tace "to ai shikenan Amma inaso dan Allah gobe kizo gidanmu kitayani yin Snacks da drins Saurayina zaizo


Dije takama baki tace " meye hakan kuma? Kayan Kwalliyane haka ?bantabaji ba


Mubina tace "a,a ba kayan kwalliya bane Snacks kayan motsa bakine da akeyi na Soye soye da wanda ake gasawa irinsu miet pie da cake,dasu cincin da donut da samosa da spr....koda yake nasan ma baki san wasu ba kokin taba cin Samosa?


Dije takama baki tace "ni dije a ina zan sameshi walh bantaba ci ba.


Mubina tace "to aiko gobe inkinzo zakici zakuma kiga yanda akeyinsa


"Dije " tace to saiki gayawa Abdulhakim yaxo yakaini gidan naku ko.


Mubina tace "kigayawa mijinki yakaiki dai inxai fito goben amma fitarki ba hurumin Abdulhakim bane dan haka indare yayi saiki gayawa yaya Abdallan inyadawo.


Dije tace "kenifa bana shiga safgarsa dan banaso aimin wulakanci


"To aiko dai baxaki fita babu ixinin saba kuma dole shine me bada umarnin futar ba.


Dije tace "to zangwada nagani saidai matsalarsa baya shigowa da wuri nikuma da wuri nake bacci gashi inaso nafito goben


Mubina tace "saiki kasa kitsare knn kihana idonki bacci kizauna falo zaman jira.




Hakan kuwa akai domin Dije bata koma dakin taba afalo ta zauna tun bayan tafiyar mubina tana kallo a TV har bacci yai awon gaba da ita


Abdallah bai dawo ba sai dayan dare kuma abinda ya dade baiyi bane yau yayi domin ya shawu yayi mankas dashi Allah ne ma yakawo shi gida lfy daga Cluv yake me gadi ne ma yafito dashi daga motar yashigarshi bangaren Dije ammafa aranar abangaren Ni,aima yakamata yakwana tunada kwana 2,2 yake musu


Har falo me gadi yakaishi ya kwantarshi akan doguwar kujera dije tana 2 siter tana ta baccinta

Saida me gadi yafuta da mintina kusan biyar ta farka saijin munsharin mutum taji akusa da iya


Atsorace ta farka


Aiko ta tsorata da ganinsa ahakan sai tsamin giya yakeyi


Ta ringa tashinsa tana cewa "Mallam tashi ni zanyi magana dakai


Abdallah ya bude idanu cikin maye ya nunata yace "ke dan ubanki ni sa'an kine?


Saida taji yanayin muryarsa sannan ta tabbatar da yasha giya domin tasan yanda "yan giya ke magana insun shata




Aiko ta girgixa matuqa takuma tsorata domin taji ana cewa in sunsha giya suna dukan matansu


Ya yunkura dakyar ya mike aiko dai taku d'aya yayi yafado kanta rikicaa!!


Ta tureshi yabugu da kujera take amai yabiyo baya yaringa kelaya amai agun,


"Nashiga uku ashe ni da dan giya nake zaune bansaniba "


Bakin cikinta ma daya bata mata falon da amai wari da tsami yagauraye koina afalon yanzu meya kamata tayi ina mafita .
………??








*Auntyn Sayyada da Shahida ce*👌🏼
🐄 *YAR FILLO*🐄
_Dijen Kauye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕








*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)








PG 100-105


Dan Allah ayi min uxirin posting din yau baxaku samuba sai gobe ko jibi ina fama da mura da ciwon kaine ………














*sorry fans*


_tommorow insha Allah zamu jone_
🐄 *YAR FILLO*🐄
_Dijen kauye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕








*Alhamdulillah Masoya "Yar fillo kunnuna min Soyayya gashi Allah yabani lfy nasami sauki ina godiya na nunamin kulawa masu sako da bugo waya najin Dijen kauye shiru nagode sosai Allah yabar kauna Amin*








*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)






-PG
50-55


Dije dan bakin ciki harda hawaye tarasa ya zatayi dashi yau


Itadai ba iya daukarsa zatayiba balle takaishi dakinsa kuma bata tabah shiga gun Ni,imaba balle ta shiga tagaya mata don tazo ta taimaka tunda ko banxa ai mijin sune tare


Tahau tunanin ko dai me gadin zata je tagaya masa halin da ake ciki


Ganin Abdallahn ya mike tsaye taga taga zai fadi yasa tayi saurin rikeshi da karfin tsiya ya jingina da jikinta


Batasan tanada wannan karfin ba sai yau domin jansa tayi jikinta ta sakalo hannuwansa kafadunta suka hau tafiya ahankali zuwa dakinsa


Takwantarshi akan gadonsa


Ta bude siff dinsa ta dauko wata jallabiyar ruwan toka ta cire ta jikin nasa datasha amai ta canxa masa da mai kyau




Sosai taringa juriya takauda kanta gefe don ganin tarin gashin kirjinsa lallai shi din dan baiwane


Jikinsa ya burgeta tana son namiji me fadin kirji da gargasa saidai kash! inama jikin Abdalla ne haka domin har kullum tana saka ran wataran zata auri Abdulhakim din


Saida tasaka masa rigar sannan takai me aman toilet tareda jiko tawul taxo ta goggoge masa fuskarsa da hannuwa da kafafunsa ganin amai ajiki taringa toshe hancinta tsami yacikata


Taduba mirro dinsa ta dauko Air freshner zata fesa dakin saikuma wata zuciyar ta hanata "kul kada ki fara salon inya farka ya yaba miki ko kuma ya zageki ya gwasale ki, sanin kankinefa ba.a yiwa wannan banxan gwaninta


Ta maida Air Freshner din amazauninsa tareda fucewa dg dakin jiki asanyaye


Saida tagyara falon tas ta feshe shi da turaren k'amsasa daki kana ta tafi takwanta ranta cunkushe da bakin ciki na gano halayyar Abdallah tashan giya tabbas agobe zata gayawa Abdulhakim komi,tasan bazai goyi bayan taxaunawa dan giya ba kuma tabbas zata gayawa iyaye don araba Auren domin baxata zauna da dangiya ba




Da bakin cikin Abdallah cunkus aranta takwanta


Shiko gogan baifarkaba sai safiya tangararan


Giyar ta sakeshi yamike yana mika tareda mamakin ganin inda yake da kuma ganin jallabiya Ash, ajikinsa shidai yasan fara qal yasaka daxai fita kuma mamaki yake shin waye yadawo dashi gida dg cluv?


Ya shige toilet yasallo wanka yayo Alwala sannan yafito yayi makararriyar Sallarsa


kicin din Dije Yanufa domin ya dora ruwan zafi shayi yake son yasha


Ransa yai matuqar baci naganin babu gas cikin cilinder din




Yaza.ai ckn sati biyu ace Gas yakare to uban me take dafawa akullum haka?


Idonsa rufe yanufi dakinta da ayaune karo na farko daya fara shigarsa

Yana shiga yabuga kofar tareda kwalla mata kira "ke "yar kauye kina ina?fito kigayamin gidan uban wa kk kai gas din kicin?


Afurgice Dije ta tashi tana mitstsika idanu don bacci takeyi yatayar ta


Ya tsaye mata aka ya nunata da yatsa "wato kinganshi bitalmanu shine kika saka aka zuk'e aka siyar mk kika aikawa tsoffin kauye kudin ko?


Dije bata gane nufin saba saitahau zare idanu


Yaci gaba da masifa "bari kiji ingaya mk nan ba gidan da akeyin almubaxaranci bane don da kudi muke siya ba.a ruga muke debowa ba


Harya juya zaifita yakuma dawowa yatsaya akanta yace "zanje yanzu nayi refelling sbd bukatar kaina ba takiba don hk kikula kada inkara ganin gas yagaxa wata inko ba hakaba zansiyo mk ice domin dashi dama kk saba,


Waima ya akai kika iya kunna gas ne ma? Yatambayeta da wulakanci yana harararta


Ta bude baki da tsiwa itama tace "tambaya kakeyi? Intambaya kakeyi kaje aji malam yabaka amsa aikin kawai.


Tana gama fadin haka ta sauko daga gadon ta wullar da bargon data rufe jikinta saigata daga ita sai gajeran wando da yar shimi data kamata bigil




Ita tama mance meye ajikinta to bata saba ba dama jiya da dare tafara saka irin shaidanun kayan nan Mubina ce ta dage saita fara koyar sawa


Saida ma taje bandakin data ganta a mirro tahau jinkunya tana cewa "wayyo nashiga uku yanxu ahaka yaganni? Aradu na mance a yanayin danake amma banso wancen banzan gardin yaganewa Abdulhakim jikin danake masa tanadi ba😭😭


Shi ko gogan ai baku saniba idan ba jikin Dijene ya furgitashi tab! Fatarta dake sheki kadai ta shagaltar dashi ga nashanunta daya fito waje sukai tozali 😱 lallai haka abin yake ashe ?


Koda tazo shiga toilet ma bin bayanta yai da kallo yaga maxaunai na motsawa gwanin sha.awa ckn 3 kwata me mannewa afatar jiki


Ya dade adaki yanata zarya yana dukan hannaye abango kyakykyawan jikin Dije yana masa gixo a idonsa


Shaff yamanta ma zaije yai refelling gas


Saiyaji yanaso yakara ganinta akaro nabiyu


Kai tsaye yashiga dakin dayake yasami tacewa


Yatararta gaban mirro da daurin kirji tana shafa


Yatsaya daga kofa ya harde hannaye ransa abace yace "ke waye yashigo ya ciren riga ya canzan wannan?.ya nuna ta jikinsa


Takalleshi awulakance tace masa "kafara zuwa katambayi me gadi kaji cewar ajiya da dare awane yanayi kadawo tukunna saikaxo inkarasa maka amsarka.


Yace "ainasan da me gadin amma naxo na tambayeki ko?


Ta rausayar da kanta tace "Eh nasan da haka amma shima

Please Login or Register in order to submit comment