Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dayake zaune a Gombe


Uncle Ahmad attajirine yanaji da Abdallah tun yana yaro dama yana xuwar masa hutu gidan akwai sa,anninsa da jininsu xahadu amma terrorine basaji suma yan rawar kaine yusuf da umar




Yanda ran dady yabaci da tafiyarsa haka ran Abdulhakim yabaci don yasan daya san xai tafi baxai barshiba bada motar gida yatafiba lallai abokinsa yayi fushi da gida tunda har ya iya hawa motar haya




Abin yatsayewa dady rai domin fafutuka yagama musu na bude musu wani babban kamfani yakuma yakuma basu mukamai aciki Abdallah yasami babban matsayi kowanne nada office ack da kuma babban matsayi na bangaren abinda xai tsare






Aranar da dady yasa zaije kauyen rogo aranar yashiryi tafiyar shida Abdulhakim




Dady nason Abdulhakim sbd yanda yake masa biyayya ko d'an cikinsa baya masa




Inhar yaxartas masa abu to ya zauna baxai musaba balle daga murya ballantana takai dayai fushi dashi




Koda suka sauka agidan gona


Dady yana canyana hutawa


Abdulhakim yaxame jiki yatafi gidansu kawarsa




Ta tsala kwalliyarta ckn kayan saki tayi ubansun kyau tamkar dan ita aka sak'a kayan






Ta dauko tallan furar tafito zaure kenan taga ansako kai ciki


Tsorata tayi ta daka tsalle gefe hannunta rike da kwaryar nonon


"Handi in boni ni dije wayyo Allah na... tana shirin juyawa takoma ckn gidan knn taji muryar abokin birni yana cewa "dawo kawata matsoraciya ninefa aboki




Asukwane tajuyo suka hada idanu tace " Ashe!?




"Ammafa kasa natsorata dayawa to yaushe agari haka?




Yakasa shigowa ckn zauren yace "yanzu yanzun kuwa tare muke da dadynmu yana gdn gona ma yanzu haka




Takama baki tace "laaa kace tare kukaxo a,a lallai bari nayi masa damu na musamman kakai masa.




Ta dire kwaryar da sauri tashiga gida tadauko kwanan sha mekyau sabone ma tahau damu da sauri harda suga tasa


Furar taji nono mekyau mara tsami




Ta rufe yana tsaye yana kallonta da sha,awa yanda tayi kwalliyarta gwanin burgewa




Ta mika masa tace "rike ka kai masa kace injini.


Yakarba yana dariya yace "saidai kizo muje kikai da kanki.
Takama baki tace "wuuuh rufamin asiri kada yaganni yar kauye yace min kaxama kamar dan,uwanka yaki sha.


Abdulhakim yace "ashe kina yarda da zancensa? To bari kiji khadija keba kaxama bace hassada kawai yake miki kinada kyau kinada tsafta kada ki damu muje kikai masa dady baida wulakanci bakuma zaiki shaba dan fura mutuniyar sace.


Tace "gaskiya baxanje dan,uwanka yaimin wulakanciba dan baxan raga masaba ko gaban waye.


Yayi dry yace "sha kuruminki badashi mukazoba.




Jin haka yasa tace "to zankai masa amma kaxo muje infara kai furata bakin kasuwa kada wasu su tsaremin guri ko.


Yace "a,a zansiye furar yau inyaso sai akaiwa momy dan tanason furarki nataba kai mata tayita santi.


Bayanda ta iya haka tashiga gaba suka tafi gidan gonar




Shike rike da kwananshan damammiyar furar dadyn




Dady na kishingide sai ganin bafulatana kyakykyawa yayi tashigo kanta dauke da kwaryar nono sun nufoshi itada Abdulhakim




Har kasa ta durkusa ta gaidashi


Ya amsa yana fara.a


Abdulhakim yadire masa fura yace "dady ga fura maikyau daga khadija gatanan surukar kace taxo gaidaka.




Wata kunyace tarufe dije donjin ance ita surukar dady ce


Ashe dama ba ita daya ke fama da ciwon son Abdulhakim ba shima yana sonta gashi har xai iya furta cewa ita suruka ce gaban mahaifinsa


Taji kamar tatsaga kasa tashige takasa daga idonma takalli dady don kunya


Dady ya kafa kai yad'and'ana take yahau santin fura


Yace mata "kai masha Allah amma naji dadi surukata y
asunanki?


Kanta akasa tace " *Dijen kauye*




Kamar yadara saikuma yadake




to ai dama dijen kauyece😅😅


"Sannu kinji nagode Allah yayi mk albarka.


Ta mike akunyace tace "Amin.


Dady yazaro kudi baisan yawansuba yabaiwa Abdul yace "gashi abaiwa khadija tukuici


Abdul yai godiya yace "to muje atahowa da momy tata furar.


Nan suka tafi suka bar Dady yana shan fura me dadi ko abirni yadade baiji kamar taba


Tas yashanyeta kuwa


Nan Abdul yadawo yatararsa yaxauna kusa dashi Dady yace "a ina kasamo wannan yarinya me nutsuwa da kirki haka.?




Abdul hakim yace "Ai dady tun xuwanmu kauyen nan Allah yahadamu take mana hidima ita da iyayanta duk adalilin tana son Abdallah Amma bakaga yanda Abdallan ke mata wulakanciba




Dady yaharxuka "Au dama Abdallah takeso? Ainazaci ko budurwar kace danaji kace surukata lallai Abdallah yacika mara kirki wato ga yarinya me hankali tana sonsa shine zaikawo mana arniya wacce ma bamusan asalintaba to tabbas zanyi maganinsa anan zan tsaya tsayin daka inga tazama matarsa kabarni dashi ayau zuwa gobe kafin mutafi zanje ga magabatanta atsaida magana kada ka kuskura kagaya masa ta waya dan sai andaura auren tukunna yasani




Ran Abdulhakim yai fari dama target yahada kuma yakama sbd yaci alwashin saiyayi maganin Abdallah na abinda yakeyiwa khadija kawa




Cikin kwantar da murya Abdulhakim yace "to Amma dady ba anyi zancen ni.ima ba?


"Kabarni da duka zancen nasu ba xanjanyeba tare zan daura auren dana yar fulanin nan dana ni,imar duk su xama matansa inga ta tsiyar Auran kristan kuma duk inda yaje ai dole yadawo.




Abdulhakim yahau gyada kai


Can kuma yahau tausayin Abokinsa amininsa daya tuna yanda yatsani matan nan guda biyu gashi kuma zasu zama matan sa wai yaya kenan ………???








_Muje zuwa_






[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:😅😅😂🙆🏼
🐄 *"YAR FILLO...*🐄
_Dijen K'auye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕










*True life Story*








*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)












PG 15-20






Kwana yakama dady a kauyen Rogo domin baa shirin kwana yazoba


Dole saida yaga mahaifin Dije wato marikinta knn mijin addaji




Baffa yawale mutumin kirki Yatarbi Dady cikin karamci da murnar ganinsa domin duk cikin kauyen ansan dady da irin taimakonsa ga wanda bayadashi gashi da son shiga ckn dattijan kauyen inyazo shiyasa kowa yasanshi






Baffa yawale yai masa shimfida azaure suka gaisa a mutumce tareda gabatar da juna




Dady yace "Nasan kasanni amma ni bansan kaba saigashi Neman Aure yakawoni gidanka yara sun hadamu.


Baffa yace "to!to madallah naji dadin hakan.




Dady yagyara xama yace "wato dama d'an wajena ne yake son "yarka nikuma Shine nabiyo baya domin atsaida maganar Aure kuma banason aja kwanaki dayawa.




Baffa yace "waye kenan yake sonta ? Yasunansa ? Ko wancan na wajen danaga kunzo tare? Yana nufin Abdulhakim da sukazo tare yatsaya awaje


Ddy yace "Yana birni bamuzo dashi ba yayi tafiya dafatan za.a bamu auran khadijan domin so nake nan da sati mudawo adaura auran kuma bana bukatar asiya mata komi zanyi mata kayan daki da duk abinda yakamata .




Baffa yaji dadi sosai har ransa take kuma yai amanna da wannan daddad'an batu yacewa dadyn '"Naji dadin wannan magana takaruwa da farin ck dakaxomin da ita nidai anawa bangaren na amince saidai kuma akwai wanda yake tamkar jigo gareta da zan gayawa kafin atsaida ranar daurin auren duk da nasan shima baxai ki ba kanin mahaifin tane don ni daka ganni kanwar mahaifinta nake aure yarinyar marainiyace rikonta nakeyi kawai.




Dady yagyada kansa yace "Allah sarki A ina kanin mahaifin nata yake domin inaso inje dakaina nasameshi muyi mgnr sbd agobe sassafe zankoma




Da baffa yaga Alh mustafhan amatse yake da zancen saikawai yatashi dakansa yarakashi har gidan kawu Amadu


To shima kawun nata mutumin ne me saukin kai kuma yaji dadin wannan magana taneman Auren dije da murnarsa yakalli baffa yace "to inbanda abinka baffa yawale kaida diyarka meye naka nasaikaxo guna neman yardata Alhalin duk dayane kuma "ya dai takace kyauta aka baka komi kayi daidaine tunda baxaka cutar da itaba




Baffa yace "wannan ai dole ne inga nabaka hakkinka kada kuma nayi abu nikadai




Kawu yace "to hakane amma saidai naji kuna batun ayi biki kwanannan aikyanta abamu lokaci sbd musamu damar yin kayan daki tunda birni zata xauna balle muyi mata "yan tagajan tagajan




Nan baffa yai ms bayanin da dadyn yai masa kan cewar su zasuyi mata komi basai sun wahalar da kansuba




Ai dajin haka kawu ya aminta da batun tunda Allah yahutarsu


Kafin dady yatafi saida yadire sadaki dubu dari komi da komi gaisuwar iyaye nagani inaso toshi, sannan yadire dari yace abaiwa amarya tayi siyayyar kayan da zatayi fitar biki da sauran hidima




Sosai sukaita mamakin wadannan dubban kudaden don basu taba ganin ankawo su haka a auren kauyenba




Kudin agun kawunta yk domin baffa yace shiyafi cancanta yarike bashiba dukda saida akai tirjiya kafin yakarba shima




Koda baffa yaxowa da Addaji batun tayi murna sosai tasawa abin Albarka


A al,adar kauyen kuma ba.a taba zanta Auren budurwa Agabanta balle agaya mata inhar antsaida mk da miji saidai kawai kiji anayi


Hakama in ita takawo mijin to idone nata kawai


To wannan ce tafaru ga dije domin kuwa kwata kwata batasan bidirin da akeyiba na Auren da za.ai mata


Itadai akullum tana tunanin Abokin birni tana jin zugin sonsa aranta tana tunanin ta yaya zata gaya masa tana sonsa tunda yaki ganewa




Shiko Abdulhakim ransa qal yai mugun qulli tsakanin dijen da Abdallah dama can yasha aiyana cewar inama yaga Allah yakaddara auren Abdallan da dijen yaga shin yaxaiyi yaga yanda zaiyi da rayuwarsa tunda yazama mijin wacce yafi tsana aduniya.




Murmushi kawai yakeyi inya hanga yahango irin xaman tabbas yasan akwai daru da tirka tirka


Saiyaringa jin kuma tausayin kawar tasa yasan tabbas zata shiga wani hali tunda itanma ba son Abdallah takeyiba tatsaneshi shine shaida to amma zaici damarar taimaka mata azaman da zatayi da Abdallah ganin bai cutar taba zai ringa kai kafa akoda yaushe domin debe mata kewa can wata xcyr tace dashi shin kodai akwai son khadija aranka? Dasauri yahau girgixa kansa yana fadin "ko kusa ko alama babu kaunace ta tsakani da Allah da haduwar jini kawai. Yabaiwa kansa amsa




Abangaren dady kuwa dayajewa da momy wannan labari ba karamin dadin hakan tajiba itanma domin tanada labarin dijen kauye tun tuni tunda Abdallah naxuwar mata da furarta da nonon




Saigashi xata xama surukarta koda yake dama ita momy ba sawa ba cirewa indai akan dadyne tana son duk abinda zai nuna yanaso baitaba nuna baki yace farine shi tace masa a.a ba fari bane ina aikomi yace e, hakane shine amsarta




Baikarajin dadi ba sai Aunty maryam tazo taji itanma ta amince da hakan domin taji ance ankai kudin komi kuma baxa.a fasa na Ni,imaba itanma tanason abinda duk iyayanta keso to balle yarinyar da suke yabo kuma aikin gama yagama tunda antsaida ranar aure ai dole itanma taso ko taki ko taso


Dady ya aika wakilansa suka kai kudin aure gidansu Ni,ima baban Safna mijin Aunty maryam ne yakarbi kudin shine waliyyinta amatsayinsa na babban yayanta




Nan ma dai antsaida magana akan cewa nan da sati biyu daurin Aure dai dai dana dijen kauye rana daya za.a daura knn 15/4/2019


Nan ma dadyn yacake makudan kudade


Gida gari guda yasaiwa ango wanda ke unguwar ladanai babban gidane flat house me part 2




Ango dan gata knn wasuma itasa suke nema basu samuba😅


Babu wanda yagaya masa koda ta wayane ammafa jikinsa nabashi akwai abinda ke shirin faruwa dashi yakikkira Abdulhakim yafi biyar aranar amma bai daga kiran saba kuma bai biyoba to ko daganan yasan ba qalau ba gashi aranar Uncle din nasa yake sanarsa cewa yashirya agobe zasuje kano gidansu Zasuyi muhimmin wani abu.


Nanma yasha jinin jikinsa saiyashiga tunanika barkatai damuwarsa ma rashin daga wayarsa da Abdul yayi




Yarasa waxai kira yaji news gashi sunbabe da Aunty maryam yai mata laifi ga ta gidansa Zannura tayi fushi dashi duk dayasan shi yayi mata laifi ya disgata gaban kanwarta


To amma dai ahakan yakirata awaya kuma akai sa.a tadaga masa kamar ma wani abun bai faru tsakaninsuba


Duk yadda yaso yaji ko akwai wani abu dake faruwa agidan bata yarda tasanar ms ba domin ankwabesu sosai itada Mubina sbd ansan zasu iya kiransa su tsurkunta ms duk da Zannun ce auke very close


Abu daya tagaya masa cewa "Eh to nikam bansan ko meke tafiya ba nidai naji anata zancen za.aje biki kauyen Rogo amma iya maxane zasuje.


Yatambayeta "bikin waye hakan? Ta tabe baki tace masa "oho walh ban saniba may be ckn familyn dadyne na can zasu Aurar da "ya"yansu


Yace "anya kuwa? Ai familyn dady a rogo duk sun kare damafa kakannine acan kuma babusu wataqila dai ko ackn abokansane zasuyi wata hidimar kinsanshi da kara shine harda yin gayyarsa shima.


Ta daga kafada tana murmushi tace "inajin dai hakanne ma amma yaya yakamata kadawo aje dakai kaima tunda aiduk xumuncine.


Yace "Eh zanzo nima aje dani tunda uncle yamatsa wai dole tare dashi zamuje.




Nan sukai sallama tana ms dariyar mugunta tabbas banda tana qule dashi na abinda yai mata da babu abinda zaisa taki gaya masa yanda suke ai babu batun ta iya boye masa wani abun balle damuwarsa tatace to amma yajawa kansa






*****A can bangaren Amarya dijen kauye kuwa batasan wainar da ake toyawaba har ana gobe daurin Aure itadai taga iyayanta maxa sai shige da fice suke ackn gidan sunayin kus kus da Addaji.


Taga kuma yan garinsu Addaji da wasu yan uwan sunxoxxo gidan wai biki sukaxo har ana ce mata amarya! Nan tahau tuhumar kanta wacece amaryar?! To bikin wa akeyi haka da batada masaniya abu har ckin gidansu akeyi?


Da dare ta tisa Addaji a daki ita kadai ta sata agaba da tambaya


"Addaji wai bikin wa akeyi ackn gidan nan dahar ban saniba? Waye adangi ake bikinsa kuma ackn gidanmu?
Addaji takalleta da tausayi tace "Dije Aurenki ne mana kina nufin baki ganeba? Ko bake kk kawo mijin ba??




Da sauri dije ta ja baya tarea dafe kirji idanu awaje ckn rawar jiki tahau fadin "Aurena kuma Addaji!? Dawa za.ai min Aure ban saniba?? Yaushe nakawo mijin walh bansan wani mijiba nikam bansan zancenba dan Allah kiyi min bayanin daxan fahimta.


Nan Addaji ta warware mata magana tace mata Alh mustafha me gidan gonane yaxo dakansa gidan yanemi Aurenta ga dansa kuma iyayanta suka amince kuma ance kina son yaron Ko Abdul sunansa ko miye ma na manta.


Dije ta tsaya cak tunaninta yadawo tahau tunanin wani abu tayi shiru domin tunaninta bata yayi wato dady yaxo yanemawa Abdulhakim Auranta knn har An bashi amma bata saniba to meyasa Abdul yai mata hakan meyaa baizo yasanarta ba har suka tafin. Ita ai dama shi takeso wannan ai abin farin cikin tane.


Ta mike asanyaye tafuta taje dakinta takwanta tana tunanin Abdul


MurmuShi tahau zabgawa tana farin cikin wannan lamari


Wai gobe iwar haka taxama mata agun Abdulhakim tabbas dole tayi godiya ga Allah daya cika mata burinta yabata Abdul A salin Alin batareda tasha wahala wajen bayyana tana sonsa ba.




Kwana tayi tana farin ciki tayi baccin dadi sosai harda makara wajen yin sallah




Allah Allah taringayi axo adaura tayita kasa kunne son taji ana daurin aure amma har hantsi bataji anxo daurin Aurenba tace Allah yasadai bafasawa sukaiba


To acan birni kuwa saida "yan daurin Aure suka fara zuwa Aka dauro Auren Ni,ima sannan Aka rankayo kauyen rogo domin Daura aure na biyu


Ango dai yadawo gidansu Amma baisami zuwa kowanne daurin Aurenba domin rashin lfyr karya yakwanta dasukazo da uncle wai duk don dadynsa yatausaya masa kada yai masa fadan barin gidan dayai hhhmmm shiko dady kallonsa kawai yai ba magana me tsayi sai Allah ya sawwaqe


;
Abdallah yabi ayari zuwa kauyen rogo daurin Aure

Sai shabiyu daidai suka isa


Ba b'ata lokaci aka daura Aure aka kawo musu fura taji nono da sukari suka hau sha suna yin santi harda masu qulla zasuyi guxuri da ita




Kafin sukoma Abdulhakim yasamu kebewa da Amarya asoro


Taxo tasha kwalliya kanta lullube ruf da mayafi kowa yai xaton shine angon ackn gidan domin yasha babbar riga yai kyau ainun


Yarasa da wane lafazi zaiyi mata bayanin komi


Saida tadago idanunta takalleshi da wani kayataccen murmushinta take yaji wani yarrr!
Abinda bai tabaji atattare da itaba sai yau


Tagaidashi tace "Ango na ina wuni.


Jin hakan yasa yadaure yafara mata bayani " khadija ina me bakin cikin sanar miki cewa ba dani aka daura mk Aure ba nasan zakiyi tunanin ko nine mijin naki to bani bane dan,uwana ne Dady shi yayi sha,awar yahada auranki da jininsa sbd kyan halinki da yayi dan haka kiyi hkr kiyi hkr khadija Abdalla ne mijinki baniba ……


Xumbur ta mike tsaye ta yaye gyalen ta jingina da bango jin zata fadi ta nunashi da yatsa tana kuka takasa ma maganar donta makale amakoshinta


Tuno fuskar Abdallah datayi yasa taji wani jiri tareda ganin wani duhu aitake taxube agun


Suma tayi na awa biyu anata shafa mata ruwa don matane suka fito suka dauketa aka kaita dakin Addaji


Shiko duk yarike yashiga damuwa sai alokacin yahau nadamar abinda yayi


Wayyo khadija kada ki mutu baki yafenba.nayi nadamar wannan hadin domin ji yayi xcyrs na mata wani mugun tausayi fiye da yanda xai tausayawa kansa.


Yan taron daurin aure basusan komi daya faru da amaryaba suka hau shirin komawa


Abd dady yace sai sati yazagayo za.a dawo daukar amarya kafin nan aun gama bikin al,adunsu suma na kauye


Jikin Abdulhakim Asanyaye yabisu suka koma birni ransa ba dadi.


Dije tafarka taganta ajikin Addaji jikinta sharkaf da ruwa da alamar shafa mata akai tayi don tafarfado


Subiyune adakin u u


Tana farkawa tahau kuka ckn harshen fillaci tahau fadin " *Wallahi mi yid'a mo Addaji mi wanyi ma lara yeso mako* (walh banasonshi Addaji,natsaneshi bana qaunar inbude ido inganshi)


Addaji tahau bugun bayanta ahankali " *wadu munyal dije, Allah su'bine ko lati khairu* (kiyi hakuri dije kada kibujire Allah yasa hakkane mafi Alkairinki)


Dije tahau kuka tana share kwalla


Addaji tace "kada kinunawa jama.a cewar bamu isa dakeba tunda kuma anriga andaura hkr xakiyi kixama me biyayya don kiga dakyau arayuwa kiyi shiru kinji dijena kixama me bin iyaye da miji.


Maganganun addaji sunshigeta nan tayi lakwas ajikinta tana faman matse kwalla tana fidda numfarfashi


Addaji taci gaba da bata baki cikin fillanci " *jedu accu vojji, d'o on jarabu ma ambo* (kiyi shiru kidaina kuka jarabawarki kenan)


dije ckn sanyin murya tace " to *Addaji wannam do'a, Allah wadu hanjum on khairu me* (addaji kiyimin Addu,a Allah yasa hakan yaxamar min Alkairi Arayuwata)




"Allah yasa dijena.Allah hokkumo sa.a.


Itakanta Addaji saida tayi mata kuka abayan idonta don ta bata tausayi data nuna hkr lokaci guda


Tunani yaiwa dije yawa yaya zatayi da son da takewa Abdulhakim knn?bazata iya cireshi arai ba


Ta wani bangaren kuma ai burinta yacika naxuwa birni


To amma wane irin rayuwa zatayi a birni da wanda bataso baya sonta ????? ………






_muje zuwa_[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:🙆🏼
🐄 *"YAR FILLO…*🐄
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕












*True life story*








*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)












PG 20-25




Cikin kwana guda da yin daurin Aure Dije ta rame ta futa hayyacinta danma tanada garin jiki dama batayo jikin siraran fulanin rugaba




Addaji taringa matsa mata akan saitaci abinci dole ga "yan taron biki basu watseba domin sai anyi sati ana biki ana shad'i dayin bikin mard'on na fulanin kauye wanda "yammata ke hadawa a dandali da daddare


Bikin mard'on bikine nashan damammen gero dafaffe yasha nono da sugari


Kwarya kwarya ake hadoshi daga gidan amare akawo "yammata susha suda samarinsu ana hira ana nishadi me kida nayin kidansa afili wasu na liki


To ita dije dama bawani kawaye take dasu wararruba


Kawayen kara dai sunzo mata "yan unguwa da sa,o,inta "yan uwa ancika anyi bidi,a ta al,ada


Ba laifi ta saki jikinta ackn yan biki wanda ba kowanema yafuskanci tanada damuwa ba


Akwai "yar gidan kawunta sa,ar tace wato indo itace ma tasan abinda ke wakana atare da ita insun kebe takan tausheta da bata baki harda ce mata "aike ki godewa Allah ma da zakiyi rayuwar Aure a birni don wasu hakan suke nema ma kuma mijinki dan gayu ga kudi dan Allah kicire damuwa aranki kiyita Addu,a Allah yasaka mk sonshi kawai.




Dije bata ce mata komi saidai tace mata "hhhhmmmm




Ita kadai tasan me takeji aranta mekuma take hange agaba don ko tayi addu.a Allah yasa mata sonshi aranta to shikumafa yazatayi da tsanar dayai mata, itakam har Abada zuciyarta Abdulhakim take kauna kuma baxata dainaba abinda ma yasa taji hankalinta yadan kwanta tuno kalaman Abdul din datayi nayanda ya bata hkr da kuma nuna mata cewar akullum acan zai kasance tare da ita xaikuma taimaka mata baxai bari Abdallah yacuce taba.


To wadannan kalami inta tuno takanji sanyi aranta.


**** *****
Daga can bangaren ango Abdallah kuwa baitashi saniba sai dare yaji Abokansa ta koina suna masa waya ana masa Allah yasanya Alkairi wasuma harda nuna fushinsu akan bai gaya musu ba




Mamaki yamamaye shi farko yaringa musu dry don yazaci ko zolayace to inbanda tsokanarsa suka shiryi yi yama xa.ai ace yai aure arana guda ya auri mata har biyu kuma daya a kauye daya abirni duk shi kadai


Bai gaskatasu ba saida Uncle dinsa yatashi tfy yakirashi daki agaban mahaifinsa ya shiryasu yai masa fadan gudu yabar gidan dayayi yakumace masa shima yatabbatar yabar maganar Lowerst domin ayanzu shi din me Aure ne akansa Aure ma harna mata biyu.


Ya zabura yarikice yace da uncle "Aure kuma uncle? Ni?!! A,a badai niba walh bansan maganar ba




Uncle din yace dashi "Abdallah kanutsu kazauna inyi maka bayanin yanda akai aka daura maka Aure da "Yammata biyu ayau.




Wato Abdallah kai me hankaline amma kanaso kazama wawa manufa ka girma amma gakanan ne kamar yaro sbd wauta iyayanka na duniya amma kana neman kabata dasu baka son kaxama meyi musu biyayya yanzu abinda kayi na nuna fushi ga mahaifinka daidai ne? Daga gaya maka gaskiya akan yarinya saika gujeshi wannan abu yakona masa rai da baka nuna kabi maganarsa ba kuma yayarka takawo maka magana kasa kafa ka shurs sannan ance akwai yarinyar da a can kauyen rogo kake wulakantawa akan tana nuna maka SO to sune dadynka yadaura maka Aure dasu ita waccen khadija da kanwar mijin maryam ni,imah dan haka inaso kazama jarumi kaxama me hkr da bin iyayae kada kanuna jin haushi ko fushinka kada kace zaka bujire ka kunyatasu tunda anriga andaura maka Aurs dasu.




Wasu zafafan hawaye yaji sun sauko masa akunci dama ashe haka aka shiryi yi masa lallai yau annuna masa rashin kauna kuma saiya nuna shi Abdallah ne


Yakalli mahaifinsa yana kuka kamar wani yaro karami yace "dady Amma wannan matakin da hukuncin naka sunyimin tsauri dayawa walh duka yaran bana sonsu araina kuma baxan iya zama dasu amatsyin matanaba kayiwa Allah dady kasa inwarware wannan Auren Akan nasu walh indai akan yarinyar can dana kawo maka zancen tane to na hkr kabani kowacce ackn "yan uwa amma banda wadancan




Dady yahade rai tamkar bai tab'ayin murmushi ko dariya ba yace da Abdallah


"Kuma ni dasu nake son kazauna kakuma basu babban matsayi ackn gidanka inkuma kanuna min ban isa ba insallama ka


Dan haka kaxaba koni ko ra,ayinka.


Abdallah yayi shiru yana jan ajiyar zuciya ransa na masa quna


Uncle yadafa shi yace masa "Abdallah kaxama namiji gwarxo jarumi mana kadauki wannan tamkar kaddararka knn kayi godiya da Allah dataka jarabawar ma taxo cikin sauki tunda kai da kanka zaka iya daidaita lamarinka wajen karbar taka jarabawar ahannunka manufata karike matanka batare da nunawa ubangijinka cewar baka son zabinsa ba domin zabin Allah ne su kuma zabin mahaifinka dan hk kada kaki amincewa sbd kada kasami sabani akan wannan kaida mahaifinka kaji,


Cikin sanyin jiki yahau gyada kansa da alamar yadauki maganarsa


Dady yadubi uncle da zafin rai da daga murya yace "kasan Allah Alh inhar bai bi wannan abinda na shirya masa ba bai karbi zabin danai masa ba to walh yasani bani bashi bakuma "yan,uwana bashi hakama dangin mahaifiyarsa kada yasa ran xuwansa gunsu dan zan hana su karbeka kuma tsinuwace zata biyo bayanka




Wani abu ne yatsaye axcyrsa lallai dady yadauka da xafi ba dashi xa.ai hakanba ckn kwantar da murya yace da dady




"Allah yahuci zuciyarsa dady na amince zan zauna dasu amatsayin matana


Uncle yace "to aikaji Alh saikasa masa Albarka tunda ya amince da abinda kayi masa.


Dady yasaki rai yace "to naji Allah yayi mk Albarka tashi kaje.


Yatashi asanyaye yafuta




Kai tsaye dakinsu yanufa yatarar da Abdulhakim yafito daga wanka yaxira jallabiya


Da bacin rai yatunkareshi yanunashi da hannu "kai tsohon munafuki ashe Aurena kukaje shine baka gaya minba kuke ta boyaemin kaketa kumbiya kumbiya to walh nasan ma akwai hadin bakinka ack






Abdulhakim yace "hhhmmm koma me zakace kace naji amma kasani cewar kai kaja komi tunda da ace kana daukar shawarata da hakan baxata

Please Login or Register in order to submit comment