Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka bayan nutsuwa tazo yace big gal dama
kina bina bashi yau kam wannan rana nasa ta a cikin
ranakun tarihi sannan duk wanda nake bi bashi ko nawa
ne ranar yana tafe na dubeshi sai dariya nake yace au
dariya ma na baki washe gari har tara na safe muna
manne da juna yaki i tashi wai sai nayi barci jiya banyi
barci sosai ba,zan shiga da kaina in hada miki ke dai
Allah yayi miki albarka me zakici?na dauka wasa ne
ashe da gaske guy shine yayi mana break shi ya min
wanka sannan nayi kwalliya muka fita sai gidanmu,can
muka samu Aunty Mimi ina zaton kara ta kawo,kwana
biu mun sha soyayya dan guy karshe ne ya iya tsantsar
soyyaya, Aunty Mimi ta amshe shi suna tafke rigima
sosai har yayi sanadin dukanta,bata dai tafi ba dan ya
ce kuma in ta sake fita bai sani ba ta tafi kenan yace
yana son ya tafi dani ne yana tunanin Hajiyarshi ,amma
zai gwada yi mata maganar da na ga bai kuma
maganar ba har tazo na san ba sa'a.bayan tafiyar shi
na shiga laulayi kin gaya mishi nayi ko ya yi waya sai
dai na daure mu sha hirarraki, ko asibiti naki yarda
naje, nayi sa'a wannan karon ya dde sosai dan sunyi
wasanni,ga na Nigeria da zasu yi na gasar cin kofin
duniya,ni kaina ban san ko wata nawa bane amma har
ya fito,Anty Mimi tunda taga cikin sai hankalinta ya
tashi,suka shiga shige shige sai ga Aunty Mimi wai tana
iya cin komai tayi ta lallashina naki karba ta rasa
yanda zatayi dani kamar ta min dura can ta aje kwanon
tace ina zuwa bari in aika direba ya kai dady gidan
Haj..
Tana fita na aje mata kwanon a kofar daki na kulle
kofata, ina kallonta ta window tana juya abincin tana
magana ita kadai, tin da naga haka sai da nayi kwana
uku ban fito ba,ina da komai na a kicin dina.Yau
saturday;zaunenake ina kallon wasansu yaynmu na
karshe, kuma wasane tun karfi ,suna wasa ne
Brazil,ganin yanda Nigeria ke musu wasa ai suka shiga
dukan su da wayo,kusa da raga wani dan Brazil ya
sakarma yaynmu kafa a kirji, nan duka haushi ya
kamani nace kai bari yaynmu ya dawo ni dai gara ya
bar kwallo tunda duk abinda yake nema ya samu, sai
kuma ya kama wata harkar tunda yana da kudi, duk da
ture ture da kuma dukan da suke ma su yaynmu sai ga
shi Allah ya basu sa'a sun lashe kofin,murna ba'a
magana. Mutane suka yi ta bugo min waya suna min
murna,Amira ma daga Yola sun kirani ita da
mijinta,Babana ya kira yayi mana murna,bayan minti
talatin na kirashi yace big gal kin kalli wasan mu ne?
nace dole ne guy mun godewa Allah sai dai wanda ya
bige ka a kifjin nan ya bani haushi, yace ka da ki damu
wasa ne.Patyn da aka shirya musu a Abuja nace zanzo
sai yace kar nazo baya son ana kalle mishi ni,yaynmu
akwai kishi.
Da kyar ya bari na bisu Mami zuwa yola gurin
Amira,cikina sai girma yake ko su Mama basu san ina
dashi ba, tunda sanda muka je Yola bai fito ba sai a
bikin Saudatu suka ganshi, Anty Yagana kece min
watan sa nawa ne?nace ban sani ba suka ce banje
Asibiti bane nace sai yaynmu ya iso jibi bikin saudatun
ma mama na ma waya kuma ta mishi waya.
Haj Yaya zaune a gaban boka tace gafarta malam so
nake ka bani maganin da zamuyi amfani dashi yaron
nan da yazo ya saki amaryarshi ya zauna da yar
uwarshi,Boka yace ai Haj aikin gama ya gama dazu yar
uwarki tazo ita da yarta sun amshi maganin da zasu
kasheshi su zubar da cikin Amaryar su ci gado,Haj
Yaya cikin tsoro tace kuma ka basu Malam?yace na
basu ba aikin kudi bane kuma sun bani kudi sosai,Haj
Yaya da tsoro da mamaki suka hanata magana can
tace to ai malam ni ce mamarshi don dana ne shima,
Bokan mamaki ya kamashi yace ai danki ne?tace dana
ne wllh yace shine kike biye masu kuna mashi asiri
lallai baki da hankali in ya mutu wanene da asara?
Yarta zata auri wani kefa zaki haifi kamar shi?to aikin
gama ya gama sai ki tashi in kinci sa'a basu bashi
wani abinci ba ko abin sha, ki samu ki hana shi
karasawa gidan ma don ko gidan ya taka sai yayi wani
mummunan rashin lfy, maryar kuma in ta tsallaka kofar
dakin cikin zai zube,ke kuma in kika amsa sallamar yar
uwarki Haj Laure to zaki mutu, ai bata bari ya karasa
ba ta tashi da gudu da gaggawa ta isa gida ta daga
murya ta kira Kabir tana fadin Kabir kuna ina ynxu?
Yace na dauko yaynmu ne yanzu mun isa gidanshi ta
fasa ihu wayyo Kabir na shiga uku kada ku shiga gidan
hannunta rike da wayan tana fadin kar ku shiga zai
mutu idan kun shiga ko har kun shiga? yace eh,sai ko
ta fadi sumammiya,Mama ta fito tana salati ruwa ta
shafa mata, sauran kishiyoyin suna tsaye ta farko tana
dubansu sai ta ganta a jikin Habiba nan ta soma kuka
tana fadin ya mutu ko? Suka ce wa? tace yaynsu Haj
Laure ta cuceni sannan ta fasa kuka mai karfi ,cikin
kuka take masu bayani tana rufe baki sai akaga
yaynmu da Kabir don har sun kunna kai cikin gidan
sukayi waya da Haj don haka a rude suka shigo tana
ganinsu tace ka shiga gidan? yace a'a menene? nan
tayi musu bayani, tsaki yaynmu ya ja yace ai gara in
mutu in huta da wannan balain,Hajiyata kin bani
mamaki ya juyo ta ruko shi ina zaka? wllh ba zaka
wannan gida ba yace matata can tana cikin hatsari sai
in tsaya,Mama ta dube shi kar kaje itama Allah zai
kareta,yace haba mmn Sagir daina wannan magana,Haj
Yaya tace Kabir jeka zo da Iman gashi ance kar ta
tsallaka kofar dakinta,yaynmu yana min waya ina
babban kicin ya ce kizo gida ynxu ko me kike kar ki
koma daki na ce cikin tsoro lfy yaynmu? yace ba kalau
ba,kar fa ki shiga daki!ki jira Kabir a waje zai zo.Sai da
ana kwashe komai sannan na fita cikin tsoro kun sanni
da rudewa,duk muna dakin Haj Yaya tana mana bayani
cikin kuka ta soma rokon Mama gafara,Mama tace
dama ban rike ki ba,ta dubeni yar nan kiyi hakuri nace
ba komai Haj,kamar daga sama mukaji sallamar Haj
Laure ba wanda ya amsa mata,kowa yayi shiru tace
Murja! Murja!! Murja!!!
Sai ta sa ihu, kafin kace haka hauka tuburan,nan akayi
waje da ita.can sai ga Aunty Mimi da Dady tana jina
abinda ya faru sai kuka,yaynmu yace wa zakiyi ma
kuka? Na sake ki tunda har kin amince ku kasheni sai
a bar mana gida,Ummanki na gidanku sai kije kuyi jinya
bani dana,ya amshi dady,
Ni da yaynmu duk muna gida bamu koma can gidanmu
ba, Haj Yaya anyi nadama tunda ynxu dakinta nake
kwana, ta hanani naje dakin Mama, yaynmu dadi kamar
ya kasheshi.
Na fito wanka ina zaune a bakin gado ina shafa mai
yaynmu ya shigo sai kallona yakeyi,yace Big gal yau fa
zamu fita ina cikin takura fa masu aikin gidannan har
ynxu ba su gama aikin ba duk kudin da nake turawa
dan a takure nake,
Na harareshi ka kara hakuri guy ina jin kunyar su Haj
Yaya da Mama,yace zan tambayar maki nace kaga ina
da ciki ba zan iya maka komi ba yace ai hakan ma kinfi
bani sha'awa bari haj ta shigo nace a'a guy ba
ruwana.... muryar Haj ta hanani karasawa tace menene
naji ana cewa bari inzo?ya sosa keya yace
am..in...dama zamuje unguwa ne tace ina ce yace ba
nisa tayi murmushi kawai,mun fito na leka nace mama
mun fita,ashe daki ya kama a Hamdala Hotel nan da
nan sai gamu,lallai yaynmu yayi missing dina muna nan
har tara nace mu tafi yace ina zuwa,ya fita can sai
gashi da kaya niki niki ya dubeni yace duba kayane
kala uku da takalma nace na menene yace siyowa nayi
a waffa road don kwana uku na biya na zaro ido su
mama fa da Haj? Yace karki damu ai sun san muna
tare kuma tun da suka bani kesun san me zanyi ba
gama cikina nan ba,nayi shiru kawai.munyi soyayya
mai dadi cikin kwanakin bana zuwa ko ina gara shi in
nace ina son wani abu ya kan fita nema min,ranar da
mukaje gida kunya don kunya na kasa sukuni,yaynmu
kam ko a jikinshi ba wanda yace ina muka je dama
wayata ya kashe ta ma.
Wata na biu a gida 'lokacin yaynmu ma ya tafi ' aka
gama gyaran gidanmu komai na cikin gidan babana ya
zuba mana, Yaynmu yazo muka koma sabon gidan
karshen haduwa ya hadu,kwananmu arbain na tashi da
nakuda naso kada yaynmu ya tashi amma ina da ya
kaini asibiti sam yaki fita daga dakin haihuwar duk in da
nace wash nan sai ya rike mun da haihuwa tazo shi da
likita suna rike dani gam na sukuto yar babyna mai
kama da yaynmu tamkar kwabo da kwabo.
Gida aka maidani dakin Haj Yaya,naga gata ganin idona,
ranar suna yarinya taci sunanta Murjanatu!sai muke ce
mata Haj. Amira dasu Mami duk sunzo mana da danta
Ammar, Amira da tsohon ciki.Bayan suna da sati daya
yaynmu ya koma da niyar yin ritaya daga
kwallo,Satinshi uku da tfy ya dawo,tsam ya rungumeni
zamu kasance da juna big gal,ynxu wane abu zan fi mai
da hankali a kai,nace kana da gurin sai da motoci kana
da manyan stores sannan kana da gidan mai sai ka
zaba.Haj ta shigo ganin muna rungume da juna tace
yau naga ikon Allah kai kana da hankali? jego fa take yi
ke kin zauna ya shigo maki da dan labubun jariri ta fita
sai fada takeyi,nace ka gani guy na bani ya zanyi da
kunya,yace dama zata koro mani ke da na huta da
zaman kadaici,kai mata daya matsala ce dole na sake
aure, nace dan Allah kar ka yi min haka guy yace to ba
Haj tace kar ki shige min ba,nace ai a nan ne amma in
mun koma gidanmu ai ka gane..na daga mishi gira
yace naki wayon sai nayi amarya ya fita nace pls guy.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Kasuwanci,shago babana ya bude min kan titin maf
road,kayan dubai nake saida wa yaynmu ne ke sa ana
kawo min don yaki naje,shi kuma kasuwanci ya amsu
ta ko ina,sannan ya fada harkar siyasa abin da ya
karanta, mutane suka matsa sai ya fito takarar dan
majalisar jiha, ni da ban amince ba sai da kyar,cikin
sa'a ya cinye, lokacin Haj Baby nada shekara,Dady ya
shigo mamy kizo papanmu yace kiyi sauri nace yana
ina?dady yace yana dakinshi nace ina baby haj?yace
tayi bacci a falo nace muje ku kwanta bayan mun
kwantar dasu daki na koma na tsuke cikin riga karama
ko cibi bata kai ba gabamta igiyoyin ne dama
albarkatun gasu nan a fili sai gajeran wando ya dameni
na gyara kaina na sa turaruka, yana bakin gado yana
duba wasu takardu yana duba na yayi jifa da takardun
kan durowa ya mike tsaye sai da nazo daf dashi sai
kuma na daure fuska na juya da sauri yace menene big
gal?nace cikin shagwaba ba kace sai kayi aure ba?yace
wasa ne big gal ba zan iya aure ba ke kadai ce na juya
na rungume shi yace yawwa big gal dina zaki kashe ni
da soyayya ya ja igiyar riga ta sai warware ta baya ya
fada katifa nima na bishi.............Pens Uppp,cewar
Auntyn mashi, Alhamdulillhi,Aunty Allah yakara Basira
da Arziki, yakuma raya zuri'a,saikuma ni dana
rubutamuke nakemuku fatan alkhairi,tsawon lokacin
dana daukan kapin kammalashi nasan lallai na batawa
wasu kamar yanda nasan nima wasu sunbatamin,
saidai ta bangarena nayafemuku inna fatan kuma
kuyafemin.
Jinjina gareku Admins namu,Allah yabar zumunci,Allah
yakara hada kawunanmu. Sakon gaisuwa ga dunbin
Masoya dake min magana, inna alfahari damu,sanna
Dan Allah gamasu kallona abai bai Musamman yayin da
sukamin magana ban amsaba Dan Allah kusani inna
sane daku, wasu lokutan abin kefin karfina, nagode
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347






DOCUMENT CREATED BY
ZAHARADEEN SHOMAR
WHATSAPP 08168575100 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment