Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

napkin mai tsafta da riga mai kyau har kamshi yake. Rasuwar Mukhlis da abin da danginsa suka yiwa Asma’u da danta ya taba zuciyar Yohan. Abin da ya kai shi ga yin alkawarin har Khalipha ya mutu ba zai kai musu shi ba, zai rike. A satin suka daga Dublin.
Abin da Yohan ya fara yi domin inganta rayuwar Asma’u da danta shine samar mata gurbi a Jami’ar Trinity, ta fara karatun medicine cikin himma. Ba ta yi nisa da karatu ba Khalipha ya soma wani rashin lafiya, sai hankalinta ya rabu biyu, don ma Marye tana taimaka mata da hidimarsa.
Zama a Turai bai sa Asma’u ta canza daga addinin da ta karba da zuciya daya ba, ba ta son barin danta hannun Marye don ta san ba ta da tsarki. Ta fi so ta kula da danta da kanta, ko ina zata tura shi take cikin keken zaman yara, sai dai dole lokutan daukar darasi take barinsa da Marye.
Likitoci sun sha bincike a kan dalilin da ya hana yaro Khalipha barci kullum cikin dare sai kuka, inda suka gano cewa ciwon hanta ne (Hypertitis B). Allah ne ya yi kawai Khalipha rayayye ne ba maganin asibiti da kwakule-kwakulen likitoci ba.
Asma’u ta ji jiki ta sha wahala da danta Khalipha, Yohan da Marye sun taimaka. Ta yi ta yi su Musulunta sun ki. Rashin lafiyar Khalipha ne yasa ta dauki bangaren likitancin yara paedatric don kawai ta kula da lafiyar Khaliphanta.


Haduwarta da Mansur Balarabe Sardauna, ta samo asali ne a matsayinsa na daya daga cikin malamansu, a lokacin shi ya yi graduating yana aikin da ya zamewa duk wani foreigner dole bayan kammala karatu kamin ya koma kasarsu.
Ya lura in ana darasi tana yawan fita ta je ta shayar da baby a hannun wata dattijiyar Balarabiya da take aikin leburanci a Jami’ar, take rike mata dan saboda Allah, don ta lura Asma’u ce kadai Musulma a bangaren da take kula da shi. Amma abinda yake daukar hankalin Mansur da Khalisah (dattijuwar), basu taba ganin uban dan ba, ga shi Balarabe ziryan ita kuma da ganinta ka ga ‘yar Nigeria.
A al’ada irin ta Bature, mace mai aure kusan koyaushe tare take da mijinta duk inda za su je, balle idan akwai karamin yaro kusan uban ne ke da wannan alhaki na kula da yaron a lokacin zirga-zirga, shi zai tura shi zai dauka, basa barin matansu su sha wahala.
Hazakarta a karatu na ba shi mamaki yadda take yin zarra da manyan maki (marks) a cikin Turawa. Ya damu da al’amarin ta, gata yarinya karama da ko ashirin ba ta rufa ba. Idan yana lacca kusan rabin hankalinsa a kanta yake, idan tambaya ce ita yake jefawa, ba ta yin kasa a gwiwa wajen farke masa zare da abawa.
Tafi-tafi Mansur ya kasa sukuni da tunanin Asma’u da begenta dare da rana. Uncle Yohan shi yake daukar nauyin karatun Asma’u, ba yadda bai yi ba don ya samo mata Nanny din da za ta dinga kula mata da Khalipha a gida ta je ta dawo tunda ba ta son shi a hannun Marye. Asma’u ta ki.
Ya ce, zai dinga kai shi gidan raino na Turawa shima ta ki. Don haka ya yi fushi ya rabu da ita kamar akan ta aka soma haihuwa. Ga shi Allah ya jarrabi zuciyarsa da son Khalipha kasancewar shi Allah bai ba shi haihuwa ba.
Daga shi har Marye kyamarsu take, ko abincinsu ba kowanne take ci ba. Don a Jos Marye murde kan kaza take da ranta ta cizge ta cillar ta fige ta dafa. Ire-iren wadannan yasa Asma’u ta gwammace Yohan ya ba ta kudi ta sayi ‘halaal’ ta dafa da kanta ko ta yi take away daga makaranta a wajen larabawa musulmi ko Pakistani mazauna turai.
Asma’u bata takurawa Yohan da cewa lallai sai ya Musulunta ba, don ta lura tana tufka ne Marye na warware mata, ko yaso ya saduda zigar Marye ke hana shi. Tana nuna masa cewa addinin Musulunci addini ne na takurawa kawai, sannan Musulmin da ya zama kasurgumin Musulmi shine yake zama terrorist (dan ta-adda).
To Allah shi ke hukunta al’amura yadda yaso, idan ya so bawanshi da shiriya ruwa da iska basu isa su hana ba. Marye ta yi mutuwar wulakanci a Dublin inda wani ginin bene ya rubza da ita da jama’a masu dimbin yawa, ko gawarta sai part-part aka tattara, sauran namanta ya zama na ungulu da tsuntsaye.
Asma’u ta ja dan’uwanta a jiki, dare da rana, yini da safiya tana kwadaita masa dadin addini musamman na Islam. Ta kan ce, “Shi Musulunci haske ne kuma guidance ne, wanda zai sada dan Adam ga nutsuwa da kwanciyar hankali, hanya ce kawai dake nuna maka yadda za ka rayu a kan tafarki madaidaici. Tsani ne mai mika mutum kusa da Ubangijinsa yaje ya iske sakamakon abin da ya shuka a rayuwarsa ta duniya.
Ba abin da addinin musulunci bai koya mana ba, hatta shiga bandaki, tsarki, wanka, cin abinci duk Islam ya kawo su a kan hanya sahihiya (to the heaven)” Haka dai, yau da gobe har Allah ya taimaketa ta yi galaba a kan Yohan, ta kai shi wajen Limamai suka musuluntar da shi ya mai da sunanshi Yahya. Hakan bai hana har yau jama’ar da suka san shi kiranshi da Yohan ba.
Yohan (Yahya) ya shiga Islam ne da zuciya daya. A wannan lokacin Yohan ya yi karfi na ban mamaki cikin kasuwancin da yake yi tsakanin Ireland da Nigeria. Ta hanyar Asma’u ya auri wata mutuniyar Somali zaunannun Dublin wai ita Aasiya. Ba ta taba yin aure ba amma ta manyanta domin cikakkiyar likitar mata ce.
Shekara ba ta kai ga fita ba Dr. Aasiya ta haihu da namiji. Ashe matsalar daga Marye ne ita din ta sani likitoci sun gaya mata, wannan ne yasa ta san duk hanyar da ta bi ta hana Yohan zuwa asibiti a bincike su sai karyar bari (miscarriage) take masa.
Har lokacin Asma’u na jinyar Khalipha dake fama da hypertitis B. Zuwan Aasiya gidansu ya kawo sauki mai yawa cikin rayuwarta duk da ita ma Aasiyar ma’aikaciya ce a babban asibitin kasa amma tana taimaka mata sosai wajen rainon Khalipha har Allah ya raya shi, ta kai shi wata Islamic school a London (Al-Muntada Islamic Pri. Sch.) boarding, ita kuma ta koma Dublin. Duka cikin aljihun Uncle Yohan.
A shekarar Dr. Aasiya ta kara haihuwar diya mace, a wannan lokacin shekarun da Mansur zai yi yana aikin wucin-gadi da jami’ar Trinity sun kusa cika, zuwa lokacin ya yi duk binciken da zai iya a kan Asma’u, ya tadda komai, wato ba ta da aure, uban dan ya rasu.
A matsayinshi na Bahaushe Ba-Kano kuma wanda ya fito daga jinin sarautar Takai abin ya zo a karkace, saurayi da auren bazawara mai da. Duk da addininmu bai hana ba, karewa ma hakan sunnah ce, kuma ya san yayansa Abdulkadir ba zai taba ki ba. Shi a kaunar da yakewa Asma’u ma, ko kantin kwari ta haife zai rike mata, kuma in ta amince zai aureta.
Kai tsaye bai doshi Asma’u ba, domin ba fuska, kullum suturce take cikin yalwatacciyar suttura da karamin hijabi iya kafadunta. Sai ya bi ta hanyar da kowacce UWA ba za ta iya kaucewa ba.
Wato yaje ya yi kawance da dattijuwar lebura Khalisa, yake tayata hidimar Khalipha kafin Mamanshi ta kai shi makarantar kwana. In ba shi da lacca wajen Khalipha da Khalisa yake lalacewa. Siyo wannan, siyo wancan duk na Khalipha.
Har Asma’u ta fara mamaki saboda ta san ko shi wane ne a Trinity da tarin iliminsa. A hankali suka soma gaisawa, tunda an ce mai Da wawa. Wani irin so Mansur kewa Khalipha wanda ko shi ya haife shi sai haka, ba kuma don komi ba sai don kamanninsa da mahaifiyarsa. So na hakika shine ka so uwa tare da dan ta.
Sai ga Asma’u na gayar da Mansur Takai kullum, har in ba ta ganshi ba ta hau tambayar Khalisa yau Baban Khalipha bai zo bane? Khalisa kan ce, ya zo ya sumbace shi ya ba shi chaculates ya tafi. Sai Asma’u ta yi murmushi har ta kai Khalipha London a bisa shawarar Mansur a haka suke.
Mansur shi ya lalubo mata makarantar kasancewar ya zauna England kafin Ireland inda ya yi karatun share fagen shiga jami’a. Ya fita sanin UK da Islamic Schools masu yawa dake cikin ta. Sai kuma aka koma kawance har cin abinci take gayyatarsa gidansu wajen Uncle da Dr. Aasiya. Ta kai ta kawo duk wani wanda ya rabi Asma’u, to ya saba da Mansur mai yi mata son kan-uwa-da-wabi, wato sonta yake tare da dukkan ahalinta da duk wanda take tare da shi.
Tare suke zuwa London dubo Khalipha duk wata. Lokacin komawar Mansur gida ya cika, amma ya kara neman visar aiki ya shantake ya ki tafiya saboda Asma’u. Su kuwa gwamnatin Dublin ai gaba ta kai su don dama irin Mansur din suke so su suke gudunsu domin kishin kasa (Patriotism). Irin na ‘yan bokon nijeriyar jiya ba na yau ba.
Sai suka shiga jika shi da kudi, gida cikin gidajen malaman Jami’ar Trinity da Insurance, accommodation and allowances. Da Hakimi ya bi ba’asin fasa dawowar tasa bai boye masa ba, “He cannot live without Asma’uuuuu!!!”


“Wace ce ita?”
Hakimi ya tambaya.
Bai boye komai ba ya warware masa zare da abawa. Satin bai cinye ba, sai ga Hakimi Abdulkadir Balarabe Sardauna da mai dakinsa Kareema a Dublin. Suka karbi auren Asma’u da amincewarta hannun Yohan, suka danganata da dakin mijinta da alkawarin suma din su koma gida. Suka yi musu alkawarin hakan, wato da zarar ita Asma’un ta kare Khalipha ya gama primary.
Mansur da Asma’u cinye junansu ne kawai basu yi ba, saboda so da kauna, a shekararsu ta biyu da aure ne ta haifi IBRAHEEM. Ba ta kara haihuwa ba, ba kuma dalilin tsarin iyali ba, Allah ne bai bata ba, don in ta Asma’u da Mansur ne, duk shekara su haife, suna da halin da za su kula da abinsu, kuma suna so, kamar su hadiye su.
Sanda Khalipha ya gama primary, Ibraheem na primary 3 a Al-Falah Islamic Children School in London. Asma’u ta karbi kwalinta suka tattaro suka dawo gida Nigeria da ‘ya’yansu biyu maza, baki da fari duk kyawawa, kowanne da irin kyan shi mai daukar hankali.
Tun kan su zauna sosai su huta federal ta karbesu aka cillasu asibitin koyarwa na UNILAG Dr. Mansur na aiki yana kuma koyar da medical student. Basu kara haihuwa ba har aka mai dasu Ibadan Teaching Hospital duka tare suke aikin shi da Asma’u.
A can ne Allah ya basu Jawahir, aka mai dasu Jos suka haifi Abida a can bayan shekaru uku. Daga nan haihuwa ta kara dauke mata dif! Har suka dawo Kano, lokacin Gwamna Kabiru Gaya, shi ya dauki kujerar kwamishinan lafiya ya baiwa Dr. Mansur a dalilin wani aiki na koyarwar sa-kai (voluntary) da ya yiwa jami’ar Abdullahi Bayero, wanda shi gwamnan ya neme shi da ya yi.
Wannan ne mafarin zamansu a gidan da suke ciki yanzu a Lamido Crescent, Gwamnatin ce ta bashi ya zauna har ya yi kokarin da ya mallake shi bayan barinsu Gwamnati da komawarsu bakin aiki. A nan ne kuma ta haifi auta Azizah.
Shima Uncle Yohan ya baro Dublin tuni da iyalinsa suna zaune a Jos. Shakuwar dake tsakanin Khalipha da Uncle Yohan ta wuce tunani, don haka yau abin da ta gani ya tabbatar mata da sanya hannun Yohan Khalipha ya nemo dangin ubansa har ya auro jininsa ba da izininta ba.
Ta riga ta yi fushi mai tsanani da dangin Mukhlis shi yasa ko da wasa ba ta taba gaya masa cewa ba Dacta Mansur ne ya haife shi ba kada ya ce zai je ya nemo su. Da ta kawo nan a tunanin da take yi a tsaye a bakin kofa sai hawaye suka tsinke mata.
Yohan da Baba Dacta basu kyauta mata ba, ta fassara hakan da cewa Baba Dacta ya yi hakan ne don ya rama abinda ta yi masa na hana Khalipha auren gallafirar ‘yarsa, me ta yi da zafi, da ta cancanci hakan???!
****


MURFIN LITTAFI NA BIYU!
Tana shirin juyawa ta fita ta ji hannayensu sun rungumeta, sun hanata fitar. Khalipha da Mimtaaz, ke hawayen suma, suna rokonta ta shigo gidansu, ta sa musu albarka, in sun bata mata ne abisa rashin sani ta yafe musu. Domin dukkansu sun tsorata da dogon tunanin da ta afka a tsaye a bakin kofa. Mimtaaz hannun Radhiyyah ta kamo suka shigo dasu cikin falon..
Ita dai Radhiyyah jikinta ya yi sanyi, musamman da Mimtaz ta soma hidimar kawo wannan kawo wancan tana lallaminsu su ci. Tambayar kanta take mececedin Khalipha wannan? Khalipha bedroom ya shiga ya sako cikakkiyar suttura a jikinshi ya dawo.
A baki yake baiwa Mami abinci. Mimtaz na hidimar zuzzubawa. Sai ta ji tausayinsu dukkansu su biyun ya kamata. Hawaye sosai take yi da ta tuna Mukhlis haka yake wannan hidimar da ita wajen cin abinci yadda Mimtaaz ke yi yanzu.
Kawai sai ta rungume Khalipha tana bashi hakuri tana yiwa Mukhlis addu’a. Sai ya jawo Mimtaaz ya kara mata ita cikin hannuwanta. Sun dau lokaci a hakan kafin Mami ta ce,
“Ga Radhiyyah, amma wallahi na daina shishshigi a al’amarin Ubangiji. Na baka zabi ka zauna da ita ko ka sahale mata in baka so tun iddah ba ta hau kanta ba. Babu ruwana, kana naka Allah na nashi, kuma nashin shine gaskiya”.
Ta kai gefen mayafinta tana share ido. Tambayar kanta take tana mamaki wa ya nunawa Khalipha danginsa har suka yi masa aure? Ita kanta duk dadewarta a duniya in za’a kashe ta bata san hanyar Hurghadah ba. Ya ce,
“Na sake ta Mami, Mimtaaz ‘yar uwata kuma kanwata ta isheni, Allah ya bata miji na gari, ba zan iya yin adalci ba.”.


A daren Mami da Radhiyyah suka juyo Kano ko gidanta ba ta shiga ba, sai da ta kai Radhiyyah gaban iyayenta. Ta kawo takardar saki da Khalipha ya rubuta ta bayar. Babu tsoro babu shakka ta gayawa Dr. Halima aure ya kare, Khalipha baya so.
Sai abin ya zama fadi-in-fada a tsakaninsu, aka soma maidawa juna magana ana tonawa juna asiri.
Mami ta ce, “Ai na gane kokari kike ki tarwatsa min gida, ki aure min miji, ko kin dauka ban san kuna neman Dacta har ofishinsa ba tunda naki mijin hoto ne baya amfanuwa, in takurawa Da na ya tsane ni, in kuntata masa ke ki farantawa taki?
Ko kin dauka ban san asirin da kike jifana da shi ba? Ba Rayhanah ba, ko uwarta ce yaje ya auro min zan zauna lafiya da ita, so kike ki fiddani daga addinina kina tura min shaidanu cikin kaina, to ta Allah ba taki ba. Ga ‘yarki nan Umma ta gai da Assha, gobe kuje ku kwashe tarkacenku Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi, amin”.
Ta mike ta nufi kofa Dr. Halima na gyada kai tana fadin
“Za ki gani, in dai Dr. Mansur ne da kike takama da shi haka za ki barshi wutsiya a zage. Tsohuwar arniya tubabba”.
Mami ta ce, a sanda ta murda kofar falon zata fita batareda ta juyo ba
“Na fi wadanda aka haifa cikin Musuluncin, tunda bana zina balle kwartanci”. Da haka ta fice.


Mu Hadu a RAYUWAR RAYHANAH 3&4. Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment