Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[9/7, 10:40] bintaumarabbale: _MAJNUN!_
*'BOYAYYAN -ATTAJIRI*
_NA_
*_BINTA UMAR ABBALE🍒_*

_MANAZARTA WRITES ASSO_
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_


_*DOCTOR MS AGADAS*_
_(MARA'KISIYYA)_
INA GAISUWA🙏🏻🥰
_NA BAKI KYAUTAR WANNAN SHAFIN_💜


*19&20*
Duk da Baban ta amince da abinda takeso hakan bai sanya ta kwantar da hankalinta ba, kullum cikin damuwa take duk saboda rashin sanin takameman gurin da mahaukacin ya sauya da zama, domin ita duk a tunaninta tsokanar da yara ke masa ya sanya ya bar gurin, a rana ta kan je bakin kasuwar sau uku ko fiye da haka tayi ta dube-dube ko Allah zai sanya ta ganshi, babu shi babu dalilinsa sai tarin tarkacensa dake karkashin matacciyar mota (a kori kura) da yake kwanciya a karkashinta.

Da azumin arfa a bakinta daf da za'a sha ruwa ta faki ido ta fita daga gidan kai tsaye bakin kasuwar ta nufa.

Baba Asabe ta fito daga kicin da muburgi a hannunta, Saliha ce kadai a zaune a tsakar gidan tana had'a musu lemo, tace." Ina Shahida ita kuma sai tazo ta soya mana awara kada asha ruwa mu rasa abunda za musa a bakin salati."

Tabe bakinta tayi tace." Yanzu ta fita."

Cike da mamaki tace." Ta fita kamar yaya ina taje."?

Tace." To ni kya tambaye ni, nima ban sani ba, na san dai sa'i da lokaci tana fakar idonki ta fita."

Baba Asabe bata kawo mummunan abu a ranta ba, tafi tunanin cewa Shahidan bakin kasuwa take zuwa gurin mahaukacin data dauki son duniya ta dora masa.

A fili tace." Allah yasa ya tafi kenan ba zai dawo ba domin kuwa na fara zargin mutumin nan idan ba aljani bane to babu shakka maye ne."
Ta daga labulan daki ta shiga tana cigaba da maganar da alama al'amarin yana damunta.


Yau ma ba sa'a domin kuwa gurin zaman nashi ma dabbobi (awakai) ne a kwance a gurin duk sunyi masa kashi ga ruwan saman da akayi jiya ya jika masa wasu kayan nasa, babu shi a gurin sai dabbobin da suka maye gurbinsa.

Wasu zafafan hawaye suka ciko idonta, ko'ina mutumin nan ya shiga? "Watakila ya mutu a wani guri." Zuciyarta ce ke raya mata hakan.

Ta girgiza kai gabanta na wani irin fad'uwa!

"Insha Allahu bai mutu ba."
Ta furta hakan a fili.

Da sauri tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo ta kira wani yaro da hannunta.

Yaro yazo ya tsaya gabanta da ledar kankana da lemo a hannunsa da alama aikensa akayi kuma da azumi a bakinsa yana sauri ya isa gida yace." Gani."

A sanyaye tace." Don Allah ko kasan inda Baban-baba ya koma da zama."

Cike da rashin fahimta yace." Waye Baban-baba."?

Ta nuna masa tsohuwar motar da fadin." Mutumin dake zama a waccan motar."
Ya kalli gurin da take nuna masa ya juyo da tsoro a tare dashi yace." Ni ma ban sani ba.'' bai jira jin abinda za tace ba yayi saurin barin gurin yana waiwayenta.

Ba ta hakura ba ta sake tarar wani yaron tana tambayarsa, yaron irin marasa kunyar nan ne, kawai sai ya fashe da dariya yana gwada irin maganarta ta kurame! "habbbaba! ya nuna ta da yatsa yana kyalkyala dariya ta bishi da kallo tausayin kanta da kanta ya lullubeta, wai shin ita din abar tausayi ce ko kuma Baban-baba!

Hawaye masu zafin gaske suka ciko idonta, tayi namijin kokarin hanasu zuba, da saurin gaske ta bar gurin tana addua a zuciyarta.

Koda ta koma gidan ma 'bacin rai ne! don fad'a ta riska, Baba Asabe ta inda take shiga ba ta nan take fita ba har da cewa idan ba tayi a hankali to za ta kai ta asibitin dawanau a duba kwakwalwarta, to itama a lokacin da Baban ke fadin hakan ba taji haushi ba domin ta fara zargin kanta anya kuwa bata samu matsalar kwakwalwa ba.

Washe gari aka tashi da sallah, jama'a nata walwala da farin ciki mussaman wanda Allah ya hore wa abin layya ciki har da Baba Asabe domin babban (rago) na dubu sittin ta siya tayi layya dashi, wadatar zucci ne da ita tare da kokarin faranta ran jikokinta dake gabanta.


Uku ga sallah ta shirya tsaf fuskarta babu walwala ta fito daga daki da hijab dinta a hannuta.

Baban ta kalleta da fadin." Kin shirya kenan nace Saliha ta shirya kuje tar.....Salihan ta katse ta da fadin." Ni babu in da zani bacci zanyi na huta da yamma Kamalu zai zo muje gidan yayarsa ziyara." Kamalu shine saurayinta wanda akayi musu baiko.

Baban tace." Ayyo! to shikkenan Shahida kinji abinda tace."

Babu damuwa a tare da ita tace." Babu komai.'' Hanyar fita ta nufa da fadin." Sai na dawo."

Tace." Ki gaishe su ba dan halinsu ba, maganar naman sallah kuwa ba zan ce ki tafi musu dashi ba dalili na fi kowa sanin waye Jamilu da burgar tsiya yanzu idan baki take ba yana nan ya kayar da manyan shanu yana neman suna a unguwa."

Bata tsaya taji karshen maganar ba tayi saurin fita daga gidan, a ranta tana jin haushin irin cin mutuncin da Baban ke wa mahaifinta.


Ilai kuwa tana shiga gidan taga zahiri domin kaca-kaca ta same su suna ta aikin suyar nama tare da daka dambu a k'aton turmi Hadiza ce mai wannan aikin.

Can gefe kuma ganda ce tare da kan sah! da rago a babbake akan buhu an shanya k'udaje sai tashi a gurin da wari mara dadi.

Jamila ce kawai ta amsa sallamarta tana fara'a tace." Aunty Shahida ashe kece dama kwana biyu kina raina."

Ta saki fuskarta da fadin." Nima saboda ke nazo gidan."

Hadiza ta kalleta da fadin." 'Yar iska bebiya kawai." da yake a hankali tayi maganar ba ta ji ba ta dai ga bakinta na motsi a lokacin da take maganar amma Talatun da sauran 'ya'yanta duk sun ji."

Babu wani kulli a cikin ranta tace."Talatu ina kwana anyi sallah lafiya."?

A dakile ta amsa ta cigaba da juya zallar sokar naman dake cike da kaskon suya.

Jamila ta shimfida mata tabarba tana zama ya shigo gidan fuskarsa a tur'bune!
kamar koda yaushe yana sanye da tsadaddiyar shadda wacce taji uban aiki irin na manyan mutane, hula da takalmi da agogo duka babu na banza kamshinsa kuwa tuni ya cika gidan.

Gabadaya su kayi masa sannu da zuwa ya amsa babu walwala ya bude dakinsa ya shiga babbar rigar ya cire ya rataye ya zauna kasan kafet zugum! daka gani yana da damuwa.

Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya amsa yana bin ta da kallo har ta samu guri ta zauna tana sake gaishe shi.


Ya amsa yana mata wani irin kallo kafin yayi kwafa da fadin." Sai yau ki kayi ra'ayin zuwa in da nake."?

Shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta.

Ya cigaba da cewa." Maganar aure ce bakya so nayi miki shiyasa ki ka dauke kafarki daga gidan nan ko.''?

Ta kalleshi da fadin." Baba aure nufin Allah ne idan lokaci yayi zanyi aur......ya katse ta, ta hanyar daga mata hannu da fadin." Ni zaki fadawa lokaci? zaman me kike kin zama uwar mata shekara ashirin kanwarki Hadiza saura wata uku bikinta ga Jamila nan itama nayi magana da yaron da yake son auranta mun tattauna da mahaifinsa, ke da kike babbarsu kina zaune to wannan itace magana ta karshe da zanyi miki wata biyu kacal na baki ki fito da mijin aure tunda kin kammala secondary kinyi saukar al'kur'ani to kuma me ake nema."?

Tana shashshekar kuka tace." Wallahi Baba tunda nake babu wanda ya ta'ba cewa yana sona, duk wanda yake so nayi aure ba kamar ni ba, na dai fi tunanin saboda lalurata maza suke gudu na."

Ya girgiza kai da fadin.'' Mace bata kwantai matsalar ki ba zai hana ki auruwa ba, ki na da duk abinda ake bukata saboda haka ni ban yarda da wannan maganar taki ba."

Sai ta kasa ce masa komai domin duk abinda zata fada masa ba zai yarda ba, bahaushe yace." Mai daki shi ya san inda yake masa yoyo, gaskiya ne tunda ta taso babu wani namiji da ya taba cewa yana sonta.

Hannu tasa ta goge hawayen fuskarta, ta kalleshi har yanzu fuskarsa bata sassauta ba."

"Zan tafi Baba." tafada tana kokarin tashi. yace."Ki bari sai yamma idan an kammala soya naman ki tafi da naki."

Ya sosa mata in da yake mata 'kai'kayi cikin fargaba tace."Baba ina ka samu kudi ka yanka *SAH!* har da rago ."

Ya kalleta yana sake tamke fuskarsa." Ke ni kikewa wannan tambayar don ubanki."
Ya fada yana zazzare mata ido!

A sanyaye! tace." Kayi hakuri." Hanyar fita ya nuna mata da hannu cikin tsawa! yace." Tashi ki fita ki bani guri."

Da sauri ta tashi ta fita gabanta na wani irin fad'uwa! akwai dalilin da yasa ta tambaye shi saboda sanin halinsa mugun dan rigima ne zai iya zuwa yaci bashin mutane duk domin yazo yayi bajinta burga! da neman suna a cikin unguwa babban burinsa ace masa ya isa shi mai kudi ne.

Hasashenta ya tabbata domin kuwa bayan fitar ta, ya zurfafa cikin tunanin hanyar da zai bi gurin ganin ya biya mahaucin da ya kar'bi *SAH!* da ragon a gurinsa.

Yayi nazari ya hanga ya hango a yanzu dai bashi da dubu dari uku da hamsin din da zai biya mutumin idan ba gidan da yake ciki a zaune zai daga ya siyar ba.

Dama yasa ran samun wasu kud'i ne sai kuma asara ta same shi, domin hak'ansa bai cimma ruwa ba, a gurin sana'ar tasu shine ya tashi fanko fayau!(ziro) hatta da motarsa bata tsira ba sai da aka kwamushe haka ya dawo gida a motar haya.

Kwabo yanzu babu a cikin account dinsa sai 'yan canjin dake hannunsa, gabadaya tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin hanyar da zai biya mahaucin kud'insa.

Ta shiga dakin tana gyara daurin zanin jikinta da yayi muguwar daud'a sai karni take fuskarta na maiko.

Kerere ta tsaya a kansa da fadin." Babu icce ya 'kare ga kuma uban 'kashi can da za'a soya yanzu dai abunda ake bukata icce da man gyada."

A sakarce ya kalleta yaji wani mugun takaici ya turnuke shi, ta tsaya masa aka kerere! ba ta san halin da yake ciki ba, girgiza kansa yayi yace." Je ki zan fito yanzu na bada kudin."

Ta juya ta fita bagazan-bagazan!

Ya fito tsakar gidan yana nazarinsu. babu Shahida a cikinsu ta tafi, wato da yace ta tsaya ta tafi da nata rabon shine ta kama hanya ta tafi, shikkenan ai tayi wa kanta, waje ya fita minti biyar ya dawo gidan tare da zaratan samari biyu, a yanzu dai bashi da kudin icce ballantana wani man gyada, saboda haka ya yanke shawarar bada sadakar naman da niyya biyu.

Ganin abinda yake shirin faruwa yasa ta fito afujajan! baki na rawa tace." A'a ya haka kuma." ?

Bai saurareta ba ya cigaba da loda tsoka da k'ashi cikin buhu yana fadin gidajan da za'a kai musu.

Talatu kamar ta dora hannu ta kurma ihu! jikinta sai rawa yake tana fadin." Ya haka ina za'a kai kuma."?

Yace." Na bayar sadaka dama haka Allah yace ayi saboda haka wannan na cikin kaskon ya ishe ku."

Idonta ya ciko da ruwan hawaye ta dinga zabga masa harara! wannan ai wulakanci ne! duka na cikin kaskon bai fi ya cika bokin fenti ba.

Su Hadiza ma jikinsu ne duk ya mutu saboda ganin yankan kaunar da mahaifin nasu yake musu.

Kaf ya kwashe naman ya bayar, ya bar musu kadan hatta da kawunan dabbobin da gandar dake shanye a buhu bai bari ba sai da ya bayar, dalili baya bukatar ta sake zuwar masa da wata bukata ta siyan icce ko man gyada da makamantansu.




*LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV*
[9/7, 10:41] bintaumarabbale: _MAJNUN!_
*'BOYAYYAN -ATTAJIRI*
_NA_
*_BINTA UMAR ABBALE🍒_*

_MANAZARTA WRITES ASSO_
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_



*21&22*
Talatu tare dasu Hadiza kamar su mutu saboda takaicin da Hujaj ya k'unsha musu, babu shakka ya cutar dasu, domin naman da ya bar musu bai taka kara ya karya ba, da 'kyar zai kai sati d'aya, gashi sun ci burin ajiyar nama saboda bayan sallah idan kwadayi ya tashi su fito dashi su gyara abinsu, Talatu dai kasa hakuri tayi ta shige daki tana matsar hawayen bakin ciki, tunanin hanyar da zata kuntata masa take.

'Bangaran sa kuwa har ya manta abunda ya aikata domin wanka yayi ya shirya cikin sabon yadi mai tsada anyi aikin kufta a wuyan rigar da hannuwa, ya dora hula zannar bukar a kansa ya fito yana kamshin tsadaddan turaransa.

Yaran ya samu sunyi jugum-jugum! kamar anyi mutuwa.

Ya kallesu na minti biyu kafin ya girgiza kansa ya kama hanyar fita ba tare da yayi musu magana ba, Jamila ce kawai ta iya yi masa a dawo lafiya Hadiza da Amina kuwa harara suka bi shi da ita yana fita Hadiza taja tsaki ta mike tsaye tana kunkuni! daki ta shiga, Jamila ta bita da kallon mamaki! ita kuwa Amina bakin kasko ta nufa ta juya naman dake kan wuta kafin ta tsamo katuwar tsoka tasa a bakinta tana taunawa tare da hure zafin dake barazanar 'kona mata dadashi.

***
Jiki a sabule ta koma gida. Abin duniya yayi mata katutu! matsalar Baban-Baba ita tafi damunta, sai kuma matsalar mahaifinta, sharadin daya gindaya mata na fito da mijin aure cikin wata uku yayi mata tsauri! ba ta da madogara sai Allah domin kuwa babu wani namiji da ya nuna yana sonta ballanatana har su kai ga maganar aure.



Sallah ta wuce da sati biyu da yawa daga cikin wa'inda sukayi layya sun cinye naman su, har sun fara siyan na miya, ita kanta Baba Asabe da ta yanka RAGO a yanzu bata da nama sai diddiga da kakide domin ba tayi son zuciya ba tayi sadaka da naman kamar yanda Ubangiji ya umarta Saliha ma tuntuni ta cinye nata, Shahida ce kawai mai nama a gidan ta kime shi a cikin kakide ta boye a karkashin gado ita bata ci ba, ba kuma ta bawa wani yaci ba yana ajiye.

Tana zaune a tsakar rumfa tana taimakawa Baban da daurin gishiri taji motsi a cikin uwar daki.

Haka kawai jikinta ya bata wani abu, da sauri ta ajiye gishirin dake hannunta ta shiga dakin wanda yayi dai-dai da lokacin da Saliha ta janyo kwanon naman da ta boye a karkashin gado.

Suka had'a ido Saliha ta diriri ce! sai ta wayance da fadin." Ke ni ba naman ki zan ci ba ina neman warin takalmi na ne."

Tsaki taja ta dauke kwanon naman da fadin." Saliha ko kinfi kud'a maita wannan naman yafi karfinki wallahi domin wanda na ajiye wa ya fiki daraja a guri na."

Saliha ta fusata! "Ni ce mayya."

Tace." Me yasa to zaki zo kina min binkice naman nan an raba an baki naki kin cinye, sai kuma ki dinga bibiyar nawa."

Tace." Don Uwarki sharri zakayi min naman banza naman wof.......! Shigowar Baban ya katse maganar tace." Menene wai ? tun daga soro nake jin hayaniyarku."

Cikin yanayin maganar ta tace." Nama na zata satar min shine don na ganta take borin kunya."

Cike da mamaki tace." A ina ki ka samu nama ke kuma."?

Tace." Wanda ki ka bani ne na boye abina."

Tace." Meye amfanin boye wa sai ya lalace yanzu lokacin zafi ne gwara ki fito dashi ki cinye ni bana san neman fitina."

Kai tsaye tace ." Baban-Baba na ajiye wa."

Gabadaya suka zuba mata ido.

Baban ta sake maimaita maganar." Ki kace Baban-Baba ki ka ajiye wa ."?

Ta gyada kai alamun "E."

Ba ta iya cewa komai ba kawai ta kama hanya ta fita daga dakin da tunanin wani abu a ranta, lallai dole ne idan Kawu Musu yazo ta sheda masa abinda ke faruwa domin ta fara zargin wani a cikin ranta.



*ABUJA*
Tun daga bakin Estate din zaka gane lallai mazauna gurin manya mutane ne, gida hudu ne kacal sai tarin sucurites wanda suke kai kawo a gurin, can gefe kuma wasu lafiyayyun karnunaka ne biyu a kwance da alama suna rama bashin baccin da suka ci.

Gida daya a cikin hud'un yafi tsaruwa da burgewa yanayin ginin zai baka sha'awa sosai babu shirman kyale-kyale irin na almubazzaranci.

Daga saman babban gate din da ya katange gidan anyi ado da suna Annabi Muhammad SAW da gold an rufe da wani irin glass mai mutukar daukar ido daga ciki wasu irin fitilu ne da suke bada haske kala-kala sai dare abin yake sake k'ayatuwa da jan hankali.


Ginin tsakiya ne wanda yake dauke da bangare uku sai filin ball dake can gefe da parking spece a in da yake dace, sai kuma gurin hutawa wanda akayi masa ado da wasu irin kujeru masu kyau da daukar hankali.

Suna tsaye sanye da bakaken kaya a bakin kofar suna dakwan fitowarsa, Adamu ne da Sule Escort dinshi.


Yana zaune a gabanta kafafunshi a tankwashe kamar karamin yaro da alama Umarninta yake jira."

Hajiya Saude ce kakarsa wacce ta haifi mahaifinsa ita kadai ce ta rage masa a duniya ita kuma yake gani yayi farin ciki duk mai son yaga walwalarsa ya mutunta ta, mai san ganin dariyarsa ya daraja ta.


"Hajiya lokaci na tafiya." Ya fada yana duba tsadaddan agogon dake daure a hannunsa.

Ta kalleshi tana ya tsine fuska kafin tace." Habu." ita kadai ce take kiransa da wannan suna *HABU* tun yana yaro, Asalin sunansa Abubakar-Assadiq mahaifinsa ne kadai ke kiransa da Assadiq sai kuma abokan karatunsa, amma da yawa daga cikin 'yan uwan mamansa kuwa suna kiransa da *DAN GASKE* wanda mahaifiyarsa ta sanya masa dalilin yaci sunan mahaifinta da kuma alkunya irin ta dan fari, wannan dalilin yasa 'yan uwanta suka boye sunan domin daraja sunan mahaifinsu, sunansa ya 'bace gabadaya a famliy idan zaka kwana kana kiran ainihin sunansa babu wanda zai gane wanda kake nufi mutukar baka kira *DAN GASKE!* ba.

Ta cigaba da cewa." Na ce wai kai ina zaka kai kudi ne? kullum baka gajiya, kai ne can kai ne nan, a duniyar nan babu 'kasar da baka taka ba, wannan kudi dai haka zaka tafi ka bar su, ka naji kana gani Shukura ta zama magajiya tun da ita kadai ka ajiye gemai-gemai da kai da gemu da furfura kana zaune babu aure." Sai ta fashe da kukan bakin ciki ta cigaba da cewa." Ya jama'a ba zasu zarge ka ba, Habu nima na fara zarginka kana neman matan banza a waje."

Ya sunkuyar da kansa yana sauraran kukanta dake mutukar tafarfasa masa zuciya! zubar hawayenta yana nufin abubuwa da yawa a tare dashi, dole ya rarrasheta domin duk irin bayanin da zai mata ba zata yarda ba bahaushe yace (mai daki shi ya san in da yake masa yoyo) duk ta san gwagwarmayar da ya sha a baya, ya tabbatar da cewar ba za tayi masa uzuri ba tunda kullum fadi take ai matan ba duka suka taru su ka zama daya ba."

"Ki kwantar da hankalinki Insha Allahu zanyi aure very soon."

Hanci taja kamar wata karamar yarinya murya na rawa tace." Alhaji Habu ni nafiso ka dawo da Fatima Uwar Shukura domin matar fari itace rufin asiri."

Lokaci guda fuskarsa ta sauya! idonsa yayi jah! kansa ya girgiza da fadin." Hajia kada ki sake min maganar Fatimah idan kina so mu shirya.''

Ta kalle shi ganin yanda kwayar idonsa ta sauya yasa taji tsoro kada ciwonsa ya tashi dama can Fatiman ce *SILA* tace." To yanzu ka samu wacce zaka aura din kuma 'yar wane gari ce? domin wannan karon ba na so ka fita daga Najeria kaje wata kasa neman aure."

A cunkushe yace." Ina dubawa tukkuna tunda nace miki na kusa aure to kisa al'amarin a cikin ranki kuma ki taya ni da addua."

A sanyaye tace ." Allah ya tabbatar da alkairi.'' Ya amsa da "Ameen hankalinsa na kan agogon dake daure a hannunsa.


Tsaye ya mike wanda yayi dai-dai fa fitowar Shukura daga dakinta.

"Daddy yau fa duka kwananmu biyar da dawowa ba zaka zauna ka huta a gida ba."

Hannunta ya ri'ke da fadin.'' Daughter ku kwantar da Hankalinku ba nisa zanyi ba KANO na nufa insha Allah zan duba ma'aikatu na (company's) domin ganin abinda yake gudana."

Ita da Hajiyan suka sauke ajiyar zuciya domin duk a tunaninsu sun d'auka zai bar 'kasar ne kamar yanda ya saba tafiye-tafiye.






*LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV*
[9/7, 10:41] bintaumarabbale: _MAJNUN!_
*'BOYAYYAN -ATTAJIRI*
_NA_
*_BINTA UMAR ABBALE🍒_*

_MANAZARTA WRITES ASSO_
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment