Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a cikin wannan al'amari."

Ta ja dogon tsaki tana surutai kasa-kasa ta juya ta shige kicin domin cigaba da aikin dake gabanta.


A gaggauce ya shigo gidan kawai yayi tozali da ita a zaune tare da yarinyar a kusa da ita, kallo daya yayi mata ya san da abinda ta zo.

A tsaye ya gaishe ta fuska a daure ta amsa, da sauri ya nufi hanyar dakinsa ta dakatar dashi ya tsaya tare da soka hannuwansa a cikin aljihun rigarsa.


Ta ce." Ba wani abu ne ya kawo ni gidan ka ba sai wannan yarinyar domin na zo ne na tafi da ita saboda ba zan ta'ba yarda ka cutar da ita ba."

Ya ce." Kin taba ganin uban da ya cutar da abinda ya haifa."?

Ta ce." Sau nawa kuma sai dai idan ba a sa son zuciya ba."

Ya girgiza kai da fadin "Shikkenan Baba ni ba naso mu dinga jayayya da juna, zan baku dama da lokaci dake da yarinyar domin ni ba mutumin banza bane nayi nufin yi wa 'ya ta aure kin hana to wannan ce dama ta 'karshe a gare ku sati uku kacal ya rage bikin Hadiza kuma so nake na had'asu duka na auran, a cikin wannan satikan nakeso Shahida ta tsayar da miji idan ba ta tsayar ba wallahi tallahi zan had'a ta aure da duk wanda nayi ra'ayi.


Cike da alhani da jajantawa yarinyar Tace." Wai shin Jamilu kai wane irin uba ne mara tausayi da jin kai? shin baka ganin halin da yarinyar nan take ciki ne, bata da koshin lafiya wane namiji ne a wannan zamanin zai iya da lalurarta"

Ya ce." Tunaninki daban da nawa, ni a ganina duk wannan ba matsala ba ce kuma wanda zan bawa auranta zan sheda masa matsalarta cewa kurma ce to sai kuma me? tana da duk abinda da namiji yake bukata a jikin mace matsalar rashin ji ba zai ha na komai ba, saboda haka wannan shine hukuncin dana yanke." yana kai karshen maganarsa yayi gaggawar bude dakinsa ya shiga.



Jiki a sanyaye suka koma gida, duk da cewa ba duka taji komai ba amma ta tsinci wasu maganganun, hawaye kawai take sharewa ta je ta kudindine a kan gado zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta.


Kawu Musa ne ya kai ta chamis aka duba ta tare da bata magani, a wannan lokacin ya tausayawa yarinyar sosai amma ya za suyi da abinda yafi 'karfinsu Jamilu shi yake da iko da 'yarsa ko'ina aka je shiyasa da yaji Baba Asaben tana ikirarin kaishi kotu ya hana ta ya ce tayi hakuri kawai kanta za ta bawa wahala Jamilu yafisu rinjaye da yarinyar.


Kwananta biyar a kwance tana jinyya kafin ta warware ta rame fuskarta tayi haske da tafin kafarta da hannunta alamu sun nuna tana bukatar ruwa a jikinta.

Ta fito da hijabi a wuyan ta.

Ta kalle ta da fadin." Shahida Na ce ." Ki bari yara su kai abincin nan tunda har yanzu jikinki bai gama dawowa daidai ba kiyi hakuri ki koma ki kwanta.

Zumbura baki tayi cikin yanayin da Allah ya halliceta Ta ce." Ni dai idan kin zuba masa kawai ki bani na tafi na kai masa."

Tayi murmushi da fadin." Shahida ko dai wannan mutumin dashi za ayi ne.?

Murmushi tayi tana kawar da fuskarta.

Wani irin tausayin yarinyar ya lullube ta idan ba sharrin zuciya ba mai zai ja hankalinta kan mahaukacin da bashi da asali kawai ganinsa akayi rana tsaka, wannan yana daya daga cikin sharrin *SO!* dole tayi wa yarinyar uzuri.


Ta mika mata kwanon abincin da fadin." To gashi nan amma kada ki ce zaki zauna a gurinsa kamar yanda ki ka saba zaki janyowa kanki jifa da tsokanar yara domin dai duk wanda ya gan ki tare dashi zai dauke kema irinsa ce."

Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Yanzu zan dawo insha Allahu." Hanyar fita ta nufa, sai ta bita da kallon tausayi da jimami!


****

Yana can cikin k'arkashin motar a kwance kafafunsa kawai take hangowa sunyi 'kura sosai amma babu kaushi ko faso! a tafin 'kafar sai dai daud'a.

Da d'an karfi ta kirayi sunansa "Baban-Baba." Jin muryata a cikin kunnansa yasa da sauri ya bude idonsa ya fara kokarin fitowa daga kasan motar.

Ido ya tsira mata yana mata wani irin sihirtaccen kallo, kaunarta yake har cikin kokon ransa.

Murmushi tayi ta dan tsuguna kusa dashi ta ajiye kwanon abincin a gabansa, a nutse Ta ce." Ina wuni."

'Kin amsawa yayi kawai ya kafe ta da kwayoyin idanunsa wanda ta so ta fuskanci wani abu a tare dashi, sai kawai ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannnunta.

Ba zato ta tsinkayi maganarsa." Kin tafi kin barni da tunaninki."

Kallonshi tayi tana so ta tabbatar da maganarsa.

Ya lumshe ido tare da daga mata kai "Nayi kewar ki My dear."

Gabanta ya fad'i ta dinga kallonsa tana mamakin kalaman dake fitowa daga bakinsa kamar ba wannan mai tabin hankalin ba.

A sanyaye Ta ce." Ga abinci nan kayi hakuri nima kwana biyu bani da lafiya shiyasa ban zo ba."


"A jiki na naji hakan domin tare muka kwanta ciwo nima bani da lafiya my dear amma ganinki a yanzu ciwon ya tafi."


A d'an tsorace ta ce ." Don Allah waye kai nifa har yanzu zuciyata bata amince min da cewa kana da tabin hankali ba, haka kawai nake tausayinka.


Shuru yayi bai ce mata komai ba. A lokacin ta fahimci sauyawa daga gare shi, sai ma ya shige 'kasan motar ya bar ta a tsugune a gurin.


Ta mike tsaye tana 'karkade jikinta tana juyawa taga yara sun fara taruwa a gurin, da sauri ta tsallaka titi ta shiga layinsu cikin sassarfa.



Washe gari ma da safe ita ce ta kai masa abin kari, sai dai lokacin da ita isa bakin titin baya nan, sai dabbobi a kwance akan buhun da yake kwanciya duk sunyi kashi da fitsari! gurin sai wari yake ga shara nan birjik da bawon lemo da sauran tarkace! Tsigar jikinta ta tashi! ta tsani ganin kazanta a rayuwarta, wai yanzu a ce mutum mai rai! wanda Allah ya daraja shike kwanciya a gurin, ta girgiza kai tana kokarin mayar da kwallar dake kokarin zubo mata, kofin kunun ta ajiye a can gefe in da babu k'azanta! ta juya gaba da baya tana duba gurin, da yake yanzu garin ya waye babu mutane sosai amma dai wandanda ke sana'a a bakin kasuwar sun fara fitowa yara 'yan makaranta da wanda ke cikin ababan hawa suna ta wuce wa suna kallonta lokacin da take kokarin korar dabbobin dake kwance a kan shimfidar buhun nasa.

Wani almajiri ya zo ya tsaya da roba a hannunsa.

Kallonsa tayi idonsa cike da 'kwansa da alama tashinsa kenan daga bacci ya fito neman abinda zai sa a bakinsa.

Cikin yanayin da Allah ya halliceta take masa magana."

Ya ce." A she baki sani ba ai jiya da daddare wani mutumi ya zo wai ashe shine mai wannan motar." Ya fada yana nuna katuwar akori kurar da ta jima a gurin. ya cigaba da cewa." Ya gargadi Baban-Baba cewa lallai ya kwashe tarkacensa daga gurin zai turo kanikawa su kwance motar ya siyar da ita.

Gabanta ya dinga dukan uku-uku! baki na rawa." Ta ce.'' Yanzu ina yake."?

Cike da rashin fahimta ya ce." Waye."?

Murya a sama ta ce." Baban-Baba."

Wata hanya ya nuna mata da fadin." Ni dai waccan hanyar na ga ya nufa."

A take hawayen da take dannewa suka 'kwace suka fara gudana a saman fuskarta, jikinta sai rawa yake tana bin hanyar da kallo! "Shin ina yake ne a yanzu? wane irin hali yake ciki? wannan tunanin take a zuciyarta idonta kurr! akan hanyar da almajirin ya nuna mata.


A sanyaye Ya ce." Kiyi hakuri ki daina kuka nima nayi nawa kukan na gaji."

Ta kalleshi da ragowar hawaye a fuskarsa ta ce." Saboda me zan daina kuka d'an Malam ina tausayin mutumin nan."

Ya ce." Yana da kirki kullum sai ya bani abinci na ci na 'koshi, shiyasa da aka kore shi daga gurin nan ban san ya zanyi ba."


Hannunta tasa a kafadarsa Ta ce." Kayi hakuri ka ji ko insha Allahu Allah zai sake had'a mu dashi, maganar abinci kuma ni zan cigaba da baka ai kasan gidan Asabe mai abinci ko."?

Da sauri ya daga kai da fadin." Eh na sani." Ta ce." To kullum ka dinga zuwa kana karbar abincin.

Cike da murna da farin ciki Ya ce." Na gode sosai Allah ya shi albarka.

Ta ce." Bude robar abincin naka." Da sauri ya bude ta juye masa kunun da zafinsa da sugar sannan ta bashi fulas da kosai a ciki ta ce." Idan ka gama karyawa sai ka kawo fulas din gida."

Ya dinga godiya kamar zai fashe da kuka.

Cikin mutuwar jiki da muguwar damuwa ta tsallaka titin ta shiga layinsu cike da jimami da fad'uwar gaba.





_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_






*LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment