Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dole ne ya nuna iko akan 'yar sa, babu wani mahaluki da isa yayi masa karan tsaye akan abinda yake da iko dashi, yarinya dai shine ubanta saboda haka zai ga wanda ya isa ya hana shi iko da ita.

"Ka gan........bai bari ya k'arasa abinda yake shirin fada ya sake katse shi a karo na biyu ya ce." Na gaji da wannan yawo da hankali Hujaj nayi hakuri iyakar hakuri saboda haka na rantse da zatin Allah yau ba zaka kwana a gidan nan ba sai ka fito min da kudi na." yana huci! da numfarfashi yake wannan maganar bai kuma jirayi jin ta bakin Hujaj d'in ba fuuuuu! ya bar gurin kamar kububuwa!

Wani zazzafan gumi! ne yake karyo masa! yasa hannu ya share na saman goshinsa hankali a tashe ya shiga gidan!


Talatu ta bishi da kallo a lokacin da yake kokarin shiga dakinsa, duk yanda akayi akwai matsala ganin yanda ya shigo gidan cikin tashin hankali.


Yana 'kokarin fitowa daga dakin ta shiga "Wai lafiya na gan ka duk a hargitse?

Ya ce." Baba Asabe ce take nema ta tona min asiri a gari saboda haka yau zan nuna mata karfin iko na a kan 'ya ta."

Ta ce." Me take nufi to?

Yana kokarin ratse ta ya wuce ya ce." Yanzu bani da lokacin yi miki bayani saboda Saminu ya fusata! komai yana iya faruwa idan ban yi wa tufkar hanci ba saboda haka sai na dawo za muyi magana."


Ta biyo bayansa tana surutai "To ai 'yar ka ce don ka yanke hukunci a kanta sai ya zama laifi gaskiya wannan karan ka nuna mata cewa ba fa ita ce take da iko da yarinyar ba kai ne ubanta dole ne ayi hakuri da hukunci da ka yanke."

Bai ce mata komai ba ya kama hanyar fita yana gyara babbar rigar jikinsa. kai tsaye can gidan Baba Asaben ya nufa.


Dama ta shirya masa koda ya gaishe ta a dakile ta amsa ta cigaba da sabgogin gabanta, ya juya ko'ina bai ga Shahidan ba sai Saliha dake wanke-wanke a bakin rijiya ko kallonsa ba tayi ba ballananta ya samu arzikin gaisuwa.


Fuska a tur'bune ya ce." Kan maganar yarinyar nan ne na zo na tafi da ita domin na yanke hukunci a kanta wanda hakan alkairi ne a gare mu baki daya."


Ta kalle shi a wulakance kafin ta ce." Rufe min baki shakatafe! shashasha wanda bai san ciwon kansa ba, ai dama na shirya zuwanka saboda baka da mutunci shine ka sanya yarinya a cha-cha wato kai abin kunya gaba ka bashi ba baya ba, ka turo wani mummunar hallita da sunan mijin aure kaji kunya Jamilu wallahi kayi faduwar 'bakar tasa."!


Gumi! ya dinga karyo masa! ransa yayi masifar 'baci da irin cin mutuncin da take masa ya ce." Wai shin ke kika haifar min yarinyar nan ne da kike min iko da ita, iya kawaici da kara nayi miki mai zai sanya ki dinga kokarin wuce gona da iri, ki zauna a matsayinki mutukar kina so na cigaba da ganin mutuncinki."


Ta ce." Jamilu cin mutuncin ka ai ba sabo bane a guri na, ka saba dama kai hanyar da mutunci yake baka bi gurin ba, to bari kaji na shirya tsaf wallahi tallahi ba zaka wulakanta yarinyar nan ba sai in da karfi na ya 'kare akan hakan."


Ya ce." Auran da zanyi mata shi ki ke kira tozarci! a tunaninki waye zai aure ta da wannan lalurar? yarinyar fa ba cikakkiyar mutum ba ce wannan ma sa'a aka ci da zai aure ta."


Fashewa tayi da kuka ta nuna shi da ya tsa da fadin." 'Yar cikin ka ce fa Jamilu, saboda Allah ya halliceta a haka sai kake neman kai da ita har ka sanya ta a cha-cha! mai yasa baka sanya daya daga cikin 'ya'yan Talatu ba kada fa ka manta duka kai ka haife su kuma ranar lahira sai Allah yayi muku hisabi."


Ko gezau! ya ce." Ni dai na gama yanke hukunci wannan yarinya ba ta da miji sai wanda na za'ba mata a matsayi na na ubanta yana da kyau a bani hakkina wannan shine magana ta daku ta karshe ku zauna a shirye daga nan zuwa sati biyu komai zai guda na.''


Shuru kawai tayi tana kallonsa hawayen tausayin yarinyar na tsare a saman fuskarta tunda take a duniya bata ta'ba ganin maciyin mutunci irinsa ba, shekara da shekaru yake 'kunsa mata 'bakin ciki har yanzu ta rasa maganinsa.


Shi kuwa rigarsa ya buge! ya fita daga gidan cike da cin alwashi akan abunda ya niyyata.


Saliha na kife kwanuka a kwando ta ce." Wai Baba ina ruwanki ne! don Allah ki kyale shi yayi iko da 'yarsa mutumin nan bai da mutunci wallahi saura kiris na d'ura masa ashar saboda takaici!


Tana goge hawaye ta ce." Saliha har yanzu kuruciya na damunki baki san duniya ba amma mutumin da yake kokarin hada aure da Shahida bai cancanta ba."


Ta ce." To ai gwara shi akan wancan mahaukacin na bakin titi, kamar yanda ya fadi hakane yarinyar nakasashshiya ce da wuya ta samu mijin aure dole sai mara galihu."

Girgiza kanta kawai ta ke hawaye na zuba a saman fuskarta, saboda kawai yarinyar na da matsalar kunne shikkenan ba ta da wani farin ciki da jin dadi a duniya ba za a duba cancanta da abinda ya da ce ba, to ita muddun tana numfashi ba zata bari ayi mata auran tozarci ba.



Tana fitowa daga kantin Shu'aibu ta hango shi ya fito daga gidan.

Gabanta yayi mummunar fad'uwa! sam ganinsa ba alkairi bane mussaman yanda ta hango tsantsar tashin hankali a fuskarsa.


Babu damar guduwa tunda ya riga ya gan ta, fuska a turbene ya k'arasa in da take ta sunkuyar da kanta cikin rawar murya take gaishe shi. bai amsa ba kawai ya rike hannunta ya ja ta sukayi gaba.


Jan ta yake tana bin sa har suka fita bakin titi bai ce mata komai ba gabanta sai faduwa yake tana kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un!


Suna tsaye a bakin titin suna neman abun hawa Baban -Baba ya 'karaso gurin dugujaja! ya tsaye gefen ta. Hujaj din ya razana kad'an! yana kallonsa ita kam ba ta tsoro ta da ganinsa ba, sai ma wani irin kallo da take masa hawaye na sauka a kumatunta tafi jin tausayinsa akan kanta."


Kallo guda yayi masa ya sha jinin jikinsa idan ba mahaifinta ba to wani shakiki ne a gurin ta saboda yanayin kammani da ya gani a fuskokinsu.



Da yake mutum ne mai kyauta sai yasa hannu cikin aljihu ya dauko dari biyu ya bashi domin shi duk a tunaninsa abinda yake bukata kenan.''


Girgiza kansa yayi kafin ya ce." Ina zaka kai min matata?"

Maganar ta dinga yi masa amsa kuwwa! a kunne "Ina zaka kai min matata? ya sake maimaita maganar, itama ta tsorata da jin furucinsa hawayen idonta ya bushe ta dinga kallonsa gabanta na dukan uku-uku!


"Kai ba na son hauka! kar'bi nan ka matsa ka bani guri." abinda ya fad'a masa kenan ya sake mi'ka masa gudar dari biyun.



'Kin 'karba yayi maganar dai ita ya sake maimaitawa "Ina zaka kai min matata."?


Cikin fad'uwar gaba ya ce." Don Ubanki waye wannan maukacin! meye hadin ki dashi.?


Da yake da karfi yayi maganar yasa da sauri ta ce." Ba mahaukaci bane sunansa Baban-Baba a 'karkashin waccan motar yake kwana Baba Asabe tana bashi abinci."


Ya ce." Okey shiyasa kuka k'ulla soyayya a tsakaninku.? ido ta tsura masa tana auna maganarsa. Ya buga mata muguwar tsawa! da fadin." Ba zaki bani amsa ba.? ta ce." Ba soyayya muke ba Allah ne kawai ya hada jininmu nake tausayin........Ya wanke fuskarta da wani azababen mari! yana huci! ya ce." Ni zaki mayar mutumin banza ko? wannan d'an iskan mutumin ban yarda dashi ba kina tausayinsa shi zai iya cutar dake saboda haka aure zanyi miki, kai kuma ka saurare ni da kyau."

Ya tsura masa idanunsa dake cike da tsantsar b'acin ran marin da yayi wa yarinya ya ji ciwon hakan har cikin ransa.

Cikin isa ya cigaba da cewa." Wannan yarinyar tafi 'karfinka ba zan baka auranta ba domin ba ka da komai mahaukaci kawai." yana kai karshen maganar ya ja hannunta suka shiga motar da ta tsaya a gabansu.

Ya jima a tsaye a bakin titin yana nazari da tunani akan al'amarin, can kuma na ga ya tsallaka titin ya bi wata hanya ya mi'ke......



"Ranka ya dad'e ina sauraranka. daya daga cikin yaransa dinshi ne ke wannan maganar yayin da yake tsugune a gabansa.

Ya ajiye jaridar dake hanunsa a nutse ya ce." Sule kai ne kasan gari sosai kasan wata unguwa Ja'in a cikin garin nan.''?


Yayi jim na minti biyu kafin ya ce." Eh ranka ya dade ina dai jin sunan unguwar amma ban ta'ba shigar ta ba amma wani lokaci muna bi ta hanyar tare da kai idan za muje babbban kamfanin ka na sumunti dake sharad'a."


Ya ce." To ai ta kwana gidan sauki tunda ka san hanyar wani aiki za kayi min akan wani mutumi ina so kayi min binkice sosai a kansa.


Ya ce." To ranka ya dad'e babu damuwa ya sunan mutumin."? shuru yayi na minti biyu, sunansa Jamilu idan bai manta ba domin can da dadewa ya taba bugun cikin yarinyar ta fada masa sunansa da kuma unguwar da yake zaune.

"Sunansa Jamilu amma akwai wani suna da jama'a ke kiransa ya kwanta min a rai amma hakan ba zai zama matsala tunda mutumin sananne ne a cikin unguwar binkice a kansa ba zai yi wahala ba."


Ya ce." To babu damuwa ranka ya dade insha Allah zanyi kokari sanin wanene mutumin domin kawo maka cikakken labari a kansa."

Ya ce." To Allah ya taimaka ina tsumayinka daga nan zuwa gobe da safe.

Ya mike da fadin." Insha Allah ranka ya dade .'' da sauri ya nufi parking spece ya fito da mota domin cika umarnin maigidan nasa.


Na jima ina kallonsa ina hango nagarta da dattijantaka a tare dashi, cikakken mutum ne kamili a zahiri da badini domin yanda yake tafiyar da rayuwarsa a nutse shine zai tabbatar maka da cewa ya san abinda yake.






*LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV*
[9/7, 10:45] bintaumarabbale: _MAJNUN!_
*'BOYAYYAN-ATTAJIRI*
_NA_
*_BINTA UMAR ABBALE🍒_*

_MANAZARTA WRITERS ASSO_
__________




*33&34*
Cikin matsatsun kaya ta fito da wani 'karamin mayafi a kafadarta wanda dashi gwara babu. hannunta rike da mukkulin motarta tare da handbag tana wani irin kamshi mai fizgar hankali.

Ganinsa a zaune ya sanya jikinta yayi sanyi sai ta hau duru-duru! ya kalle ta tun daga kasa har sama! yanayin fuskarsa ya sauya da 'bacin rai!

Yarinyar na so ta zubar masa da mutunci a gari domin ya jima yana hana ta shigar kaya irin wannan amma taki ta daina a kullum burinta ta fitar da tsaraicin ta waje.

Cikin 'bacin rai ya ce ." Shukura ba kya jin magana ko ."?

A sanyaye ta ce." Daddy kayi hakuri don Allah."

Ya daga mata hannu da fadin." Koma cikin gida."

Sai ta fashe da kuka tana bubbuga k'afafunta! "Daddy kayi hakuri ka bar ni don Allah." A shagwabe take maganar.

Ya duba a gogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi na yamma daf ake da a kira sallar magariba.


Ya ce." Ina za ki ji."? Hanci ta ja da fadin" Bikin 'kawata a can karkasara."


Girgiza kansa yayi da fadin ." Ki koma gida babu in da za ki je." yanda ya fadi maganar babu wasa ya sanya ta juya a guje! tana kuka!


Ta zube a jikin kakar uban tana gursheken kuka. Hajiya Saude hankalinta ya tashi a duniya ta tsani 'bacin ran yarinyar ta dinga rarrashinta kan tayi shuru ta fada mata abinda yake faruwa


Ta ce." Daddy ne ya ha na ni zuwa kuma kin fi kowa sanin yanda nake da Samira 'kawata ce sosai ai bai kamata Daddy ya hana ni zuwa bikinta ba.


Ta ce." Aikuwa bai kamata ba wallahi, shiyasa wani lokacin bana son zamansa a gida saboda yana matsanta miki da yawa bari ya shigo na ji dalilinsa.

Tana rufe baki ya shigo da niyyar d'aura alwala. ta dakatar shi ta hanyar kiran sunansa "Alhaji Habu."

Ya amsa tare da tsayawa yana sauraranta. "Meye dalilin da ya sa zaka hana yarinyar nan zuwa bikin 'Kawarta kana fa matsantawa yarinyar nan Alhaji Habu."


Babu wasa a fuskrasa ya ce." Hajiya wane irin biki ne wannan ? wanda sai magariba za ayi shi, to ba zan lamunci wannan shashanci ba, bayan haka kuma dubi sutturar da take jikinta tuntuni na hana ta sanya dinkuna irin wannan amma taki ta dai na wannan dalilin ya sanya na hana ta zuwa kowane irin biki ta hakura dashi tunda ba ta jin magana."


Ta kwantar da kai da fadin." Ai ba za ayi haka ba yarinyar nan Samira 'kawarta ce tare sukayi karatu ya kamata ace Shukura ta halarci bikinta kayi hakuri ka bar ta taje ba don halinta ba sai dai ni nake nema mata alfarma."


Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." To shikkenan amma ta sanja kaya lallai kuma ki sanya hijabi a jikinki kafin ki fita."

Da sauri ta daga kanta da fadin." Insha Allah Na gode Daddy." ba tare da yace komai ba ya bar gurin.


Kamar gaske ta fito da k'aton hijab har k'asa tayi wa hajiyar sallama ta fita, tana shiga mota ta cire hijab din tana jan tsaki ! karamin mayafin dake ciki jakarta ta fito dashi ta rataya a kafad'arta sannan ta kunnar motar ta fige ta da karfin gaske.


****
Tashin hankali kenan! tun a bakin titi a ka tare shi aka sheda masa abinda yake faruwa, bai gazgata ba sai da ya karya kwanar layin gidan ya ga zahiri! tun daga nesa yake hango jama'a cike a kofar gidansa ga katakwaye da katifu da sauran abubuwan amfaninsu nan a watse a gurin, tonan silili Saminu ya zo yayi a gidan bayan fitarsa yasa zaratan Samari suka dinga watso musu kayan su waje, Hadiza da sauran 'yan uwanta sai kuka suke, ita kuwa Talatu tana zaune a kofar wani gida abin duniya ya dame ta, ma'kota da 'yan uwanta sai bata baki suke, Saminu yasa k'aton kwado (dan mukkuli) ya kulle gidan yayi tafiyarsa.


Hujaj tunda yake bai ta'ba tozarta irin yau ba, ya rasa da wane ido zai kalli Jama'ar dake gurin, kawai sai ya huce! fushinsa akan Shahida ya dinga gaura mata mari yana fadin." Kin ga irin abinda ki ka janyo min ko? kin ga tozarcin da ki ka janyo min ko."? ya dinga kwashe ta da mari yana haurinta da kafarsa har sai da ta durkushe a gurin tana wani irin kuka! da kyar aka janye shi daga gurin ana bashi hakuri.

Malam Habu makocinsa ya ja shi gefe yana bashi baki da fadin ." Haba Alhaji Jamilu ka nutsu mana ita kuma wannan yarinyar da kake dukanta meye laifinta da zaka huce fushinka a kanta dama tuntuni nake fada maka ka gyara kuskuranka saboda irin wannan rana to yanzu ga abunda ya faru."


Ya cire hular dake kansa yana firfita da ita ya ce." Malam Habu wallahi ban taba tunanin Saminu zai yi min wannan tozarcin ba, amma babu komai tsinanniyar yarinyar can ce ta janyo min domin da ta amince da bukata ta da tuni haka ba ta faru ba kamar ni a ce an tozartani irin haka.''

Malam Habu Ya ce." Yanzu dai mu bar wannan maganar insha Allahu komai zai daidaita, akwai daki da rumfa a cikin gidana zan baka aro ka shiga ka zauna kafin mu ga abunda Allah zai yi."

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke da fadin ." Na gode sosai Malam Habu Allah ya saka da alkairi." Ya ce." Babu komai bari yanzu nasa yara su kwashe kayan su shiga dasu Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba .''

Ya amsa da "Ameen yana bin gurin da kallo, manya da yara sun cika sunyi dafifi a gurin kowa na tofa albarkacin bakinsa.


****
"Ranka ya dade wallahi na dauka binkicen da ka sanya ni zai bani matsala sai gashi cikin hukuncin Allah komai ya zo da sau'ki don lokacin dana shiga Unguwar ban sha wahalar sanin waye Alhaji Jamilu ba."

Zamansa ya gyara a nutse ya ce." Sule nima nayi farin ciki da haka ina fatan zan samu kyakykyawan labari daga gare ka."


Fuskarsa ta sauya da alhani da kuma jajantawa. Ya ce." Yallabai al'amarin mutumin dai babu arziki babu kuma kima da mutunci.''

"Ina sauraranka." Ya fada tare da mayar da hankalinsa gare shi.


Cikin rashin jin dadin abubuwan da ya gani da idonsa ya shiga warware masa abunda ya faru ya kuma dora da bashi labarin da ya samu daka bakunan mutane da sauran jama'ar dake makotaka dashi, domin ya tabbatar masa da gaskiyar binkicensa ya nuna masa hotonan da ya dauka a lokacin da yake ta zazzabgawa yarinyar mari ana ta bashi hakuri.


Ya karbi wayar yana duba hotonan ransa yayi masifar 'baci ganin yanda yake dukan yarinyar har da kafarsa, babu shakka wannan mutumin bashi da mutunci kuma bai san darajar dan adam ba, kuma jahilci shike da damunsa ba wani abu ba, hakika ya ji ciwon yanda ya ke tozarta yarinyar a gaban jama'a amma bai nuna hakan a fuskarsa ba, ya mika masa wayar da fadin." Goge hotonan daga wayarka."

Da sauri ya goge gabadaya kamar yanda ya umarce shi.

Ya kalle shi a nutse ya ce." Da safe idan Allah ya kai mu ka je ka nemi shi mutumin da yayi tozarcin domin jin cikkenan karin bayani daga gare shi, ina so ya tabbatar maka da iya adadin kudin da yake bi daga baya sai mu ga ya za'ayi ."


Ya ce." Insha Allahu zanyi kokarin ganin hakan ya tabbata."

Ya ce." Ma sha Allah ka tashi ka je kawai sai Allah ya kai mu goben ."

Ya mike yana godiya sannan yayi masa sallama ya tafi.


A daran ranar bai kwanta ba sai da yayi Istahara akan al'amarin, ya wayi gari da yarinyar a cikin ransa, yana tausaya mata sosai yana kuma so ya aure ta amma yana tunanin wani abu a cikin ransa, duk da hakan ba haramun bane amma yana ganin kamar yarinyar tayi masa 'kan'kanta da yawa idan anyi duba da matakin shekarunsa, yayi mata girma domin yana kallonta ne kamar 'yar sa Shukura a zahiri shekarunsu na iya zuwa d'aya.


****

Sule ya zo masa da cikakken bayani akan Saminu ya warware masa komai da yanda Hujaj din ya dinga yaudararsa har yayi masa alkawarin bashi auran 'yar sa, daga baya kuma ya dinga yi masa yawo da hankali wannan shine dalilin da ya sa ya yanke wannan hukuncin.


Ba a ja dogon lokaci ba ya Umarci Sulen da kudi dubu dari hudu ya je ya kai wa Saminun domin kashe wutar yace koma lallai ya je ya bude gidan ya kulle. amma ya gargadi Sulen cewa kada ya kuskura ya sheda masa cewa ga wanda ya biya kudin.

Saminu ganin har da riba akan kudinsa yasa da saurin gaske yasa rigarsa ya fito kai tsaye gidan Hujaj din ya nufa, lokacin ya fita yawon Malamai burinsa kawai a daure bakin Saminu sannan ya wulakanta a duniya kamar yanda ya wulakantashi.

Sai Malam Habu ne ya kar'bi mukkulin ba tare da ya bi ba'asin komai ba ya bude gidan, yasa yara suka dinga kwashe kayan suna shiga dasu.


A gari ya ji cewa Saminu ya dawo da mukkuli har iyalinsa sun koma ciki, sai ya sake gazgata karfin aikin malamin da ya taimaka masa, domin duk a ganinsa aikin malamin ne yayi tasiri.



'Bangaran Baba Asabe kuwa da kyar ta wayi gari, domin tunda Sha'aibu mai kanti ya sheda mata cewa Hujaj ya tafi da Shahida hankalinta ya tashi mutu'ka! har tayi niyyar zuwa gidan suyi wacce za suyi Kawu Musa ya hana ta yace a rabu dashi su ga iya gudun ruwansa.


Kasa hakuri tayi washe garin ranar da yamma ta shirya ba tare da tayi shawara da kowa ba ta nufi gidan, domin bata tsammanin zata zubawa mutumin ido yayi abinda ya keso a kan marainiyar Allah, dole sai tayi masa karakare! sannan za su daidaita.





_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_




*LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV*
[9/8, 09:41] bintaumarabbale: _MAJNUN!_
*'BOYAYYAN-ATTAJIRI*
_NA_
*_BINTA UMAR ABBALE🍒_*

_MANAZARTA WRITERS ASSO_
__________






*35&36*
Lokacin da ta isa gidan baya nan, amma kuma daf yake da dawowa domin shiri na mussaman na zuwa mahad'arsu. Babu yabo babu fallasa Talatu ta karbe ta. suka gaisa sama-sama kafin ta bar ta zaune a gurun.

Jamila ta shigo gidan hannunta rik'e da 'bakar ledar dake dauke da kayan miya gwalagwaji. ganin ta yasa ta washe baki da fadin." Baba ke ce a gidanmu."?

Ta saki fuska da fadin." Ni ce Jamila ai na jima da zuwa ina zaune ina jiran dawowar babanku."

Ta ce." Aikuwa yana kan hanya domin lokacin dawowarsa yayi."

Talatu ta fito daga kicin ranta a 'bace ta harare ta da fadin." Sarkin shishshigi da cusa kai a maimakon ki kawo min aiken da nayi miki shine ki ka tsaya kina neman suna ko.'"?

A sanyaye ta ce." Kiyi hakuri." Tsaki taja da karfi ta fizgi ledar dake hannunta aikuwa ta yage kayan miyan suka watse a gurin, sai kawai ta hau d'ura mata ashar! ranta a a bace tayi saurin barin gurin tana turr!! da halin mahaifiyarsu sam bata da d'abia mai kyau.

Shahida ta fito tsakar gidan da alamun bacci a idonta, Jamila ce da ta shiga dakin ta tashe ta daga baccin tana sheda mata zuwan Baba Asaben.

Ganinta yasa zuciyarta karyewa sai kawai ta zube a jikinta ta fashe da wani irin kuka mai sosa zuciya.


Jin kuka ya cika gidan ya sanya tayi gaggawar Fitowa daga kicin da ludayin miya a hannunta nan ta iske Baban na rarrashinta da fadin." Tayi shuru ta share hawayen ta mutukar tana raye babu mahalukin da ya isa yayi mata auran dole.

Karaf ta bude baki ta ce." Wannan fa ba hurumin ki bane Baba kina nema ki wuce gona da iri a akan wannan yarinyar."


Ta daga mata hannu da fadin." Saurara haka kada kiyi min rashin kunya ba gurin ki na zo ba gurin mijinki na zo kuma shi nake zaman jira saboda haka kada ki kuskura ki kara wata magana

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment