Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana rangaji ,horn kawai ake mata ta baya ida rudewa tayi ta zube anan tana rusa ihu tare d kiran sunan jijoz.




Da sauri Furanko ya fito a motar ya rungumeta ,tana ganinsa ta makalkalesa tana huci mota y sakata hankali tashe don tunda Jawad ya daukota yake biye dasu, kai tsaye gida suka nufa.




A rike ya shiga da ita cikin gida da sauri Momy ta taso ta riketa hankali tashe tace"meke damun y'ata Furanko"



"Mama" Sarena ta fada ta fada jikin Momy ta sake fashewa da wani irin razanan kuka mai tsuma zuciya.



Anan take hankalin Momy ya kuma tashi don duk duniya ta tsani bacin ran Sarena itama hawaye taji yana bin kuma tunta.





*ALKALAMIN MARYAMA*✍🏻





Don't for get to



Like
Comment
And share
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA*





NA
*MARYAM ISMAIL*



🌈 *KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*


*united we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers*





Page1⃣9⃣to2⃣0⃣




Da kwarin gwaiwa ta shiga dakin Sarena .
Zaune ta sameta a gefan bed ta zabga uban tagumi ,kiran sunanta ta shigayi amma shiru,hakan yasa ta dafata.

Firgigit ta dago ta goge hawayen idonta tana fadin"Momy n daina fa".
Ganin Nani kas a gabanta yasa ta saki sanyanyar ajiyar zuciya ta zuba mata kyawawan idanuwanta.



Zama kusa da ita Nani tayi sannan ta rike hannayenta duka biyu suna fuskantar juna tace"meke damunki?,ba munyi alkwari ba zaki daina damuwa ba".


Shiru Sarena tayi sannan tace "nima bansan me zanyi ba,kinga Momy bataso kuma banason tayi fushi dani,kuma inaso n rabu dason Jawad amma ba Abu mai sauki bane a gareni".


" karki damu Mamanki bazayi fushi dake ba,nasan tana sonki ,amma kibi a hankali tashi muje waje yazo yana jiranki".


Bude baki tayi zatayi magana,Nani ta rufe mata baki ta kama hannunta suka fito,turata tayi wurinsu ita kuma ta wuce kitchen.


A hankali take tafiyan kanta a kasa sanye take da wando baki rabin cinyarta sai y'ar karamar riga marar hannu wacce ko cibinta bata rufeba gashin kanta kwance a bayanta sai sheki yake, plat shoe ne a kyakyawar kafarta sai faman zuba kamshi take a sanyaye ta iso wurin ta tsaya ba tare data furta komai ba.



Kallonta yayi dakyau dukta fada ta danyi duhu kafin ya kira sunanta"Sarena".


Bata da niyyan ansawa ko dubansa .

Hakan yasa yaci gaba da cewa"yanzu abunda ya faru zaisa ki soma ganin laifina ko kiyi fushi dani?,har yakai bakya son ganin fuskata?".


Da sauri ta dago tare da fadin"pls Jawad stop it".

"To me hakan yake nufi,nidai nasan ina sonki,kuma zan aureki babu abunda zai hana,zakizo ta biyu a gidana bayan nabi zabin iyayena ,shin zaki iya yarda da aurena a haka?".


Langwabe kai tayi tace" addinika ya yarda da hakan wace ni da zance bazan yarda ba zan aureka a haka kodon samuwar farin cikina da kuma naka".




"Never Sarena,ban raineki donki bijire ma umarni na ba,ko kadan banason ki auri Wanda ba addininku daya ba,kuma banaso kisha wahala,Furanko shine mijin daya dace ki aura" cewar Momy ta fada tana ida karasowa inda suke.



Tunda Momy ta fara magana idon Sarena na kanta kwata kwata bata fahimtarta a hankali ta iso gaban Momy tace"what do u say Mommah?"



Gyada kai Momy tayi"nasan kinji mena fada"


"Pls Mommah can we stop this,Furanko baya sona we are just friends, irin haka be taba shiga tsakaninmu ba".



Dariya Momy tayi sannan tace" ko zaki iya yin shiru,kina nufin kicemin bakisan Furanko yana sonki ba,to tun yarinta yake sonki yake kula dake kuma yafi kowa cancantar auranki akan wannan abun"ta ida magana tana nuna Jawad da hannu a wulakance.




Share hawaye Sarena tayi"Momy kina sona?,kinsha fadamun zaki iya sadaukar da komai naki domin farin cikina,zaki bani komai nakeso amma yau gashi da ranar tazo Momy kin kasa bani ko d'aya,ke kike neman rabani da farin cikina,na dauka daga Daddy zan samu matsala,sai gashi shiya goyamun baya fiye dake,Jawad mutumin kirkine auransa baya nufin zan bar addinina a'a zaiyi nashi zanyi nawa, tuni kuka ya kwace mata,cikin kuka taci gaba da fadin pls kiyi wannan domin ni πŸ‘πŸ»".



Yanzu kam zuciyar Momy ta soma karaya daurewa tayi ta dagota daga duken da take tace"meya kawo wannan Sarena?,Mamanki tana sonki kuma zatayi komai domin ke,kawai baki fahimceni bane,zan yarda da auranku domin farin cikinki bawai don inaso ba,a'a saidon banason ganin bacin ranki".



Rungume juna sukayi suna hawaye,amma Momy tana aekawa Jawad da wata iriyar harara dake cike da tsantsar tsana da kiyayya zahiran.



Daurewa yayi sukayi ma Momy bankwana suka tafi.


Yanzu kam no way farin cikin Sarena yasa iyalanta dason auranta da Jawad.




**************"""



Kai tsaye wurin Ammi suka wuce ba bata lokaci sukayi mata bayanin abunda ke faruwa sunyi sa'a ma Abee yana nan yace suje anjima zasuje gidan suka su Abban kada ya damu.



Yanzu kam zuciyar Jawad tadanyi sanyi domin ya fara ganin alamun nasara a cikin tafiyarsa.




Duke hajiya take gaban bokanta tuni ya gama sanin meya kawota,bushewa yayi da dariyar mugunta yace"kinsan idan abu zai yiwu zan fada maki amma idan kika saba babu wani bokan dazai maki aekin saidai kawai yaci kudinki,inaso ku sani auran Sarena da Jawad bazai fasuba don duk a sama gashi anata daura auran, tauraronta nada karfi naga wani abu zagaye da ita a yanzu bamuda nasara a kanta,saidai Ku tsaya ayi auran saimu San yadda zamu bullo mata tabar duniyar baki daya".




Kallon Nabila,Hajiya tayi suka hada ido,wani kululun bakin ciki ya tsayawa Nabila a zuciya tace"Hajiya tashi muje barta ta shigo gidan bala'i ma kadai zaisa tabar gidan,donko tayi bankwana da farin ciki har abada indai zata kasance da Jawad".



Godiya Hajiya tawa boka suka tashi suka wuce.



Tofa ana wata ga wata




Da sallama Abee da Ammi suka shigo tankameman parlon Aminin nashi,cike da farin ciki Umma ta tarbesu suka zauna,kayan ciye ciye aka cika masu gaba dashi.



Kallon Abba,Abee yayi yace"ba wannan ta kawoni ba,nazone akan maganar Dana da kake neman tauyewa hakki kasan kuma ba lafiya ce dashi ba".



Murmushi Abba yayi yace"kayi hakuri ina fatan kasan neke faruwa".



"Kwarai kuwa dama zuba ido nayi,Jawad yabi umarninku na auran Nabila,to meyasa shi zaku tauye masa hakkinshi?,ko kunaso mu rasashi,abunda zaiyi be sabawa addini da shara'a ba,kuka sani idan taji dadin zama dashi kota musulunta,tunda bata da wani mumunan hali ko abunki a tare da ita,to wallahi karkuyiwa Allah shishigi cikin lamurransa idan kuma kun shirya bugawar zuciyarsa ya mutu da bakin cikinku to bismillah".


Haka Abee yaita kwanta masu har jikinsu yayi sanyi suka aminta da shawarar Abee.


Washe gari sukaje Neman auran Sarena a gidansu an masu tarbar arziki sosai anan suka gane ashe y'ar Samol ce kuma sunada sanayya su duka ,aka sanya ranar aure nanda 2weeks rana daya Dana Nabila.



Farin ciki wurin Sarena da Jawad har ba'ae don murna.


Tuni Furanko ya hada kayansa ya koma America.


Nabila kuwa tasha kuka kamar ta kashe kanta don takaici.




*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻


Don't for get to

Comment
Like and
Share
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA*




🌈 *KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*



*united we stand and succed:our ambition is to entartein and motivate the mind of readers*





Page2⃣3⃣to2⃣4⃣






Da huci ta kare maganar tana jin tsantsar bakin ciki a ranta,main parlo suka fito suna surutu da habaici suna sheke ayarsu dukdan su Sarena su jiyosu.



Sarai su Serena na jinsu amma suka share babu abunda takeyi sai tsananin kuka domin rabuwa da Momy yana mata zafi arai sosai.



Ba jimawa gida ya watse aka bar Nabila da Sarena kadai,Manab da Salim suka rako ango dakinshi,suna dauke da manyan ledoji a hannunsu ,ciki ya shiga ya kira Sarena before y kira Nabila,bada bata lokaci ba suka fito tare da dukawa gabansu,sannan Sarena ta gaeshesu,ita kuwa uwar gayyar a chair ta zauna tayi daya kan daya tana taunar gum,kota kanta Jawad bebi bare y tanka mata,haka suka karaci gaesawarsu babu Wanda yabi takan Nabila Wanda hakan kuma ba karamin haushi ya bata ba,kafin sukayi sallama suka tafi.



A shekeke ya kalli Nabila yace"ke ki saurareni kiji,bawai n taraku nan donku maidamin gida dandalin fada bane,don nasan kece fitsararra kece bakyada hakuri,ya kamata ki sani kece karama anan ya zama dole kiwa yar uwarki biyayya,in kinason zama dani,komai tayi maki ki sanarmin zan dauki mataki da kaina amma babu batun rashin kunya tsakaninku"


Baki bude Nabila tabi Jawad da kallo murmushi kawai tayi tace"tab".



"Sarena nasanki da hakuri,inaso ki kara kan Wanda kikeyi Ku zauna lafiya in kuna fada bazanji dadi ba,kuma kinga kece babba duk laifi dole ki dauka kiyi hakuri daduk sharar da kanwar taki ta ebo a kanki"Jawad ya fada.


Numfasawa yayi sannan yace" maganar kwana ya kukeso ayi"



Karaf Nabila tace "ae abun a bayya ne yake,kwana bibiyu zakayi ko ina kawai".



Beko kulata ba yace" Sarena dake nake fa".



A hankali ta dago dara daran idanuwanta tayi murmushi tace"gashi Nabila ta fada hakan yayi ae".



"OK zan fara da dakinki tunda kece babba,Allah yayi maku albarka ya hadamun kawunanku wuri daya".


Saidai shi ya amsa da Amin don Sarena batasan me zata fadaba,itako uwar gayyar bakinci ke damunta wai Jawad zai fara kwana da Sarena dole tasan abunyi,cikin ledojin ya dauka ya mikawa Nabila ya kwashi nasu yaja hannun Sarena,kafin sukawa Nabila saida safe suka wuce daki.wani kululun bakin ciki ya taso mata wani irin rushewa tayi da kuka ta ebe ledojinta tayi daki da gudu ta fada a bed tana kukan bakin ciki.





Shiko suna shiga part din Sarena wanka yace taje tayi shima zaije yayi a part dinsa,kafin ya wuce,toilet ta shiga ta wanke jikinta sosai tazo gaban mirrow ta shafe jikinta da mayuka masu dadin kamshi kafin ta feshe jikinta ko ina da body spray masu dadin shaka sannan ta dauko kayan baccinta mararsa nauyi yan sharashara ta saka ta nannade lallausan gashin kanta ta koma gefan gado ta rakube.



Bangaren Jawad ma wanka yayi ya dauro alwala ya shafe jikinsa d mai sannan ya feshe jikinsa ko ina da turarukansa masu daukar hankali da dadin kamshi jallabiya kawai ya saka ya fito tare da kulle part din nasa.



Da sallama ya shiga part din Sarena isketa yayi inda take ya jawota yana goge mata hawayen da takeyi ,zaunar da ita yayi yace"bari nayi sallah kinji baby na"
Tana kallonsa har yayi sallah raka'a biyu yayi addu'o'in shi ,sannan ya jawota tare da lallabata yana bata gasasshiyar kazar daya siyo tare da fresh milk harta koshi,sannan yaci shima tare sukayi brush kafin yazo ya kama goshinta yayi mata addu'a ,kafin suka haye bed yana dan mata wasanni ,ganin da nayi wasa ya soma canzawa don Sarena harta fara kuka tana magiya yasa na jawo yan matan kafafuna nayo waje,oga ko ya rude bayama sauratonta burinsa kawai ya jefa kwallo a ragaπŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€.




Saida Nabila ta karaci kukanta ta gaji sannan ta tashi taci kazarta ta watsa ruwa ta sheme tana bacci daure da towel.





Sai dab da asuba naga Jawad yayi wanka tare da alwala,itako Sarena sai sharar bacci take,jijiyoyin kanta duksun tashi fuskarnan jajir alamun anci kuka an gaji,sunbatarta yayi sannan ya wuce masallaci.



Koda ya dago kofar dakin Nabila ya tura baccinta take hankali kwance ga ledoji a barbaje gashi tayi daidai a bed tana bacci hankali kwance,tashinta ya somayi ,a galabaice ta bude idanuwanta dake cike da bacci tace"meye yaya".


"Tashi kiyi sallah" ya bata amsa.


"Nayi anjima pls k barni n gaji".

Ganin ya daure fuska yasa ta mike tana guguni ta nufi toilet mintuna kadan ta fito hijab ta zira ta fara sallanta ,ko kadan babu natsuwa a ciki batama iyaba don ita kanta ba zata nuna yaushe rabon da tayi sallah ba harta soma mance karatun sallah.sallama tayi ta zo ta zauna kusa dashi tace " ina kwana".

Beko ansaba yace"Nabila sallah nace kiyi ba wasa ba".



"Wallahi yaya nayi,ita kadai na iya irin wannan Allah kuwa".



Girgiza kai yayi cike da tausayi da jimami ina iyayenta zasu da hakkinta,lallai akwai aeki gabansa," OK zan koya maki don baki iya komai ba".



Murguda baki tayi tace"ba garani ba da wacce bata kallon gabas dinfa nifa ba takurani nazo kayi ba"ta wurgar da hijab din ta haye Bed taja blanket.



Tashi yayi ya wuce part din Sarena ,har yanzu bacci takeyi,zama yayi yana azkar yana jero addu'o'i.



Wurin karfe10:00am Mama tayi knocking kofar Sarena,Jawad ya fito ya bude,ganin Mama yasa ya gaesheta ,itama ta gesheshi tace"an gama shirya abincin karin kumallonku".godiya ya mata ya koma ciki.



Note:Mama itace ke zaune a gidan Jawad tana masa girki,asalinta mai aekin Abba ce,da Jawad yayi aure shine y daukota tana masu girki,gata da kirki da son mutane dama tun suna gida mutuniyar Jawad CE,hakan yasa ya fitar mata da daki a gidan.




Iske Sarena yayi ta tashi ,taimaka mata yayi tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga marar nauyi takai har gwaiwa,sannan ta gyara gashin kanta tayi kyau sosai,har yaja hannunta su fita ta tsaya cak,baya tayi da Dan Saudi taje inda aka ware mata wurin addu' a cikin dakin ta hada hannu biyu ta rufe ido,saida ta gama addu'o'inta sannan ta shafi gunkin dake wurin ta shafa a fuskarta ta fito suka wuce dining.



Anan suka samu Nabila ,Sarena ta gaesheta taki amsawa ,haka sukecin abincin sai aekawa Sarena harare takeyi.




*ZAMAN GIDAN JAWAD*


TURKASHI


*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻



*gaskiya n raina comment dinku a book dinnan,in bakwaso saina daina*



Yawan comment yawan typing.




Luv u all masoyan Asali na.
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA*




NA
*MARYAM ISMAIL*




🌈 *KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*


*United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers*





Page2⃣1⃣to2⃣2⃣





Satin biki ya taho ko wanne bangare shire shire suke musamman bangaren Nabila don tana kudirin yin bikin da duk layinsu va'a tabayi ba dukda cewa kowa a layin yanaji da kudi.




Sarena kuwa babu abunda ta shirya zatayi bayan walimar da zasuyi a coci bayan an gama daura aure,don Momy ta buga kai kasa tace in an daura a masallaci dole azo ayi irin nasu don sai tafi samun natsuwa.





Nabila shagali take ba kama hannun yaro tasha lalle ga uban kitson gashin doki tasha,tunda satin bikinta ya kama take program, yau ya kasance daran biki kuma zasuyi Dinner a dole Umma ta matsawa Jawad akan yaje tunda hada yan uwa.




Badon ransa yasoba,ya shirya cikin maroon din shadda tsadaddiya tasha aeki black hula ya kafa black da takalma d agogo duk black yayi masifar kyau sai zuba kamshi yake.



Manab da Salim suka saka shadda blue colour anko sunyi masifar kyau komai nasu iri daya.



Tsaye Jawad yake yana fesa tirare, da sallama Manab da Salim suka shigo suna fadan Ango kasha kamshi.



Yamutse face yayi kota Kansu bebi ba.



"Wait mlm ,ya za'ae ayi Dinner ace ba dayar amaryar kamata yayi ace Sarena ta halarci wannan taron" Salim ya fada.



Mumfasawa Jawad yayi sannan yace"Bari n kirata".


A waya ya sanar mata akan ta shirya yanzu zasu biyo daukanta.




Still tayi tanabin wayan da kallo,sannan ta dubi Moona ta fada mata me yace.


"OK bari n samu Momy" Moona ta fada tana fita.



Da murmushi Momy tazo dakin ta dafata"OK my Daughter bari naje siyayyan kayan da zaki saka yanzu gamai Makeup nan tayi maki".




Rungume Momy Sarena tayi don Dadi cos ta dauka zata hanata zuwane.



Momy bata jima da fitaba aka soma cancadawa Sarena kwalliya.




Nabila n hango sanye cikin pink din dogon Riga har kasa mai kama da gown tasha make up tayi kyau ba laifi sai blue head da aka nada nata ga yar karamar Jakarta blue itama hills ta saka kayan sun matseta sosai hakan yasa take tafiya kamar tana sanda.



Waje ta fito cikin gate anan ta samu su Jawad ,Salim ne yadan bugo Jawad yace"ango dago kaga kwalliyar Amaryar taka mana"


Tsuka yaja kamar zai tsinke harshensa ya bude mota ya shige tare da kullewa,Manab ne zaija Motar sai Salim a kujerar mai zaman vanza.



A sanyaye ta bude dayan side din ta shiga don taga muguwan hararar da Jawad ke aeka mata.


Gaishesu tayi ,suka amsa but banda Jawad da yaketa faman kallon waya komai yakeyi oho ,tafiya kawai sukeyi ta rasa gane inda suka dosa gashi tana tsoran tambays Jawad y tsinkata.




Kofar wani tankameman gida taga sunyi parking, waya taga Jawad ya kara a kunne ba jimawa taji yace"Baby muna kofar gida".





A hankali take taku zuwa wajen gate din Moona n rike da d'ayan hannunta,sanye take cikin tsadaddiyar weeding gown black colour bata da hannu daga sama ta kamata kasa ya bude wuyanta n kallah goals be zube sai kyalli suke, gashin kanta yasha gyara sai sheki yake an dauresa da bantis sai red net aka rufa mata a kai saidai ka kalli face dinta da tasha make up a ciki ,hannunta rike yake da flowers, masha Allah abun sai Wanda ya gani donko Sarena tayi masifar kyau.




Da sauri Jawad ya bude Motar ya iso gareta da murmushi ya kama hannuwanta ,rungumar juna kadan sukayi .



Murmushi Moona tayi tace"to oga ga bride dinka nan mu zamu taho daga baya".




Gyada kai kawai yayi ya jawo hannunta zuwa motar sun bala'in dacewa da juna musamman da suka jera.




Wani kululun bakin ciki ya tsayawa Nabila a rai,a zuciya tace lallai inada aeki ,marar adalci kawai kun kusa yiwa juna kallon bankwana don vazan taba zama koma baya a cikin gidan aurena ba.




Shine a tsakiya ,kafin Manab yaja Mota sai soli center, wuri yayi wuri taro yayi taro isowar ango da amare kawai ake bukata ,hangosu nayi ya shiga tsakiya sunyi masifar kyau sai dai Sarena tawa Nabila zarra tako ina.




A hankali suke taku sunzo wucewa wurin kawayen Nabila da gangan Aysha ta sakawa Sarena kafa daidai akan idon Jawad,tafiya tayi zata fadi da sauri ya rikota ya dagata sama cak kamar Baby ya kaita sit dinsu kallon juna kawai suke cike da soyayya ,wani irin mahaukacin kishi da kululun bakin ciki suka dira a zuciyar Nabila Jan kafa kawai tayi ta isa ta zauna rakwaf,a dayan Side dinsa.






Casu kawai ake anyi barin nairori musamman Momy da aka fiddo Sarena fili saida kallo ya dawo wurinsu don barin dukiya kawai take mata.
Wuri yayi kyau ba'a tashiba sai wurin 10:30pm sannan kowa ya watse.





Washe gari.




Da misalin karfe 11:00am aka daura Auran Jawad Al'amin da Sarena Samol da Nabila muh'd,akan sadaki ko waccensu dubu Dari.



Daurin auran yayi mutane har wurin 12 sannan suka soma ragewa before ya wuce coci ya karbo auran Amanar Sarena ya saka mata ring itama ta saka masa.



Anata shagali gidansu Nabila sai cashewa takeyi tana takadarci da yamma aka lullubeta cikin hijab Abba ya mata fada sosai before yai shirin daukarta.




Har gidansu Sarena Abee yaje ya karbota wurinsu Momy kuka kawai sukeyi dakyar aka rabasu ya dakkota ya kawota gidansu dake newlowcost .



Gate ne babba saika shiga kaga kofa idan ka shiga babban parlo ne da yasha ado sai part Ukku na tsakiyar ne na Jawad n right side naga Abee ya shiga da Sarena ,fada ya kara mata sannanya fito ya tafi kafin Moona ta iso gidan.




Ba jimawa da zuwansu Abba ya karaso da Nabila a kagare take su shiga ya fito ya tafi donko hijab din jikinta dukta dameta,shima fada ya mata sannan ya tafi .


Kamar jira take ta yakice hijab din ta jefar tace"Aysha Allah yasa BA's kawo shegiyar aljanar yarinyar nanba".



Tsuka Aysha taja tace"na nawa kuma ae kece amarya tun dazu Abee ya kawota".



Ihun haushi Nabila ta daka tace "wlh wannan shirin Jawad ne mugu kawai donta rigani zuwa ya tsaidamu ,to wallahi zatan tayi sallama da farin ciki tunda hartai kuskuren hada miji dani".





*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻



Luv u all
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA*





🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*





Page2⃣5⃣to2⃣6⃣







*zaman gidan jawad*





Zaman gidan Jawad zamane da kokadan bayawa Sarena dadi kowa kansa ya sani musamman yacce take hakuri da halin Nabila da irin izgilancin da take mata,tana goronta mata ita kafura ce.





Wayan dake kusa da ita yayi kara dubanta takai kareta ganin sunan Mom ya bayyana a kan screen din ya sata sakin murmushi da sauri ta dauka tana shaukin jin muryar Mom,saida suka gama gaesawa sannan tace"Sarena kizo muyi bankwana karfe 9:00am jirginmu zai tashi zuwa America ,Daddynki ya gama aekinsa zamu koma kasarmu".



Wata iriyar faduwar gaba ta iske Sarena a hankali tace"Mom zaku tafi Ku barni ni kadai".sai hawaye suka soma bin kuncinta,sallama sukayi ta kashe wayar tana tunanin ina zataga Jawad ta fada masa zataje gida,rabonta da ta saka Jawad a idonta koya kulata tun daran farkon da aka kawota gidan,text ta masa ta waya ta tashi ta fara shiri.



Yana zaune office text dinta ya shigo wayarsa kamar ya duba kamar y bari ,haka kawai ya duba koda yaga me take fada,text ya mata (ki je ae akwai driver kuma kinada mota a gidan kije inda kikaso).



Futowa tayi sanye da dogon Riga iyakarta cinya fara kal gashin kanta yasha kyara dukda ta rame amma hakan besa taki yin kyau ba,ba wata makeup a face dinta amma tayi masifar kyau ,hill shoe ta saka baki ta dauki bag dinta black colour, duba text din da yayi mata tayi,haka kawai taji zuciyarta ba dadi key ta dauka ta fice daga gidan ganin time ya tafi yasa sukayi mahada airport.




Da gudu ta bude motar ta nufi wurin su Mom ganin jirginsu na haramar tashi tun kafin ta isa wurinsu hawaye ke ambaliya a kyakyawar fuskarta,rungume Mom tayi tana fadin"Mommy narh".



Karfin hali Mom tayi tace"a'a Sarena ba kuka yanzufa kin girma,matar aurece,ba yadda za'ayi mu tafi dake, idan kin haihu saiki kaimun Baby na na rike"ta fada tana Jan kumatunta.




Kunya ta kamata ta rufe fuska ta kuma rungume Mom ,sannan ta rungumi Daddy,nan kam Mom ta kasa daurewa haka Daddy yaja Mom suka shige jirgi sukabar Sarena a wurin,tanaji tana gani jirginsu ya tashi,a jirgi Mom kuka take kamar ranta zai fita tana kuma Allah wadai da auran Jawad da Sarena tayi gashi yanzu sun rabu.



Kuka take a haka ta karasa Mota da kyar ta iya shiga mota ta nufi gida ,tana isa da gudu ta fito ta fada part dinta bakinta cike da amai ga wani irin kasala da tashin zuciya dake damunta amai ta zazzaga ba kadan ba da rairahe ta iso a bed ta fada ta rufe jikinta tana kyarmar sanyi har bacci yayi awan gaba da ita.





Tafa hannu Nabila da Hajiya sukayi kafin Hajiya ta sassauta murya tace"waya fada maku barno gabas,take saima tabar gidan kafa zage,yanzu dai ga wannan maganin ki bashi shi a abinci yaci ,dole ya tsaneta ta rika masa warin jaba yaji ko ganinta bayasonyi a gidansa kedai ki dage kiga yaci".




Ansa Nabila tayi tana boyewa a side drower tace"Allah ya barman ke Hajiya ta kin maidani mace na karbe mijina".



Haka sukaita fira marar amfani sai yamma likis Hajiya ta tafi gida.



Bancin Mama ta gama abinci ta jera a dining ,Nabila tazo ta zuba maganin kamar yadda Hajiya ta umarceta,kafin taje tayi wanka,ta shirya cikin atamfa Riga da siket Wanda dasu gwara babu duksun matseta .




Da sallama ya shiga part din Nabila da gudu ta iso wurinsa ya rungumeta yana washe baki yana kara kankameta a jikinsa yana bin wuyanta yana sinsina tare dadan lasarsa.



Zame jikin tayi tace"kaidai baka gajiya muje kayi wanka kaci abinci sannan na baka"ta fada tana kashe ido.



Wanka yayi ya shirya cikin 3kwata da vest ya feshe jikinsa da turare sannan suka iso dining suna makale da juna ,zama yayi ta zuba masa abincin jolluf rice CE da hadadden sobo ,yanaci yana wasa da ita hankalinsu kwance yaci ya koshi yana faman rirriketa.



Sarena dake lekensu ta taga wani irin bakin ciki ya ziyarci zuciyarta ga cikinta dake mata ciwo tanata tashin zuciya zafafan hawayene suka ci gaba da ambaliya a kyakyawar fuskarta da tayi jajir ta sauya launi a kasa ta zauna dishan ta kuma fashewa da kuka tana rike cikinta.







*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻



Share and comment


Luv u all
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA*




🌈kainuwa writers association

United we stand and succed: our ambition is to entatein and

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment