Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

meke dalilin zubarsu,tunani tayi ya zatayi ta sake gujewa Furanko ba mafita dafe kai tayi tana juyi a wurin.







Banko kofar dadin Nabila tayi ta shigo tana taunar gum ta tada daurin kai a sama,kai tsaye jikin Jawad ta nufa ta zauna,jaki yaja ya tureta ya tashi a bed din yana binta da mugun kallo kafin yace"ban hanaki kusantoni ba,karki sakemin haka".





"To my Swt am sorry dama Umma ce tace na fada maka Hajiya tazo ka futo Ku gaesa". Nabila ta fada tana kashe ido.





Sake daure fuska yayi yace" OK fitarmin anan bazanzo ba".Jawad ya fada rai bace.




Bude baki tayi zatayi magana ganin ko kadan bataga alamar wasa a tare dashiba yasa ta mike ta fashe da kuka tayi waje.






Har rigan tambayarta sukeyi meya sameta,jikin Hajiya ta fada tana fadin"Hajiya ya tsaneni wallahi baya sona,ki duba irin cin mutuncin da yakemin da ranku".





Mikewa Hajiya tayi tace"ina wallahi be isaba,bamusan hakaba kuma bazamu taba sani akansaba" taso muje Jan hannun Nabila tayi suka wuce part din Jawad da isarsu ta bankada kofar tana huci bakin cikine ya kara kamata data gansa kwance yanata faman duban wayarsa.





"To Dan iska marar mutunci ,kai harka isa kace zaka juya mana ra'ayi to ba'ayika ba,idan Aminu ne ya turo kiranka zakace baza kajeba ,mai zubin munafukai amma ko kadan albasa batai halin ruwa ba,to bari kaji ko Aminu uban naka be isa ya tsallake maganata ba,ballantana kai,auranka da Nabila ba fashi kama shirya" dungure masa kai tayi ta figi hannun Nabila suka fice.






Tsaki Jawad yaja ya dauki carkey dinsa tare da phone dinsa ya fice daga gidan ta baya kai tsaye gidansu Manab ya nufa yana shiga yayi parking mota ya futo da Amma ya hadu gaesheta yayi cike da ladabi before ya wuce part din Manab.






A zaune yake a lallausar royalchair dinsa yana latsa waya,ko kallonsa Jawad beyiba ya wuce Bed room ya fada a bed yana huci saboda tsabar dacin da zuciyarsa take masa kuma yake kara jin tsanar Nabila a ransa.





Ajiye wayar Manab yayi ya shiga bedroom din murmushi yayi da yaga yarda ya kwanta,karasawa yayi ya soma kwance masa igiyar takalmansa kafin yace "yaron Umma meke damunka haka rai bace".





Shiru kamar bazaiyi magana ba candai yace" Hajiya CE"




"C'mon ka yarda mana me Nabila ta rasa yarinya y'ar gata dalla ka bada kai bori ya hau".cewar Manab.





A firgice Jawad ya juyo yana watsawa Manab mugun kallo ya fizge kafarsa ya tashi ya soma cire kaya saida yaje kofar toilet sannan yace" marar kirki kawai,idan bazaka bawa mutum hakuriba kaja bakinka kayi shiru".







A hankali ta iso dining area din tana binsu da kallo ko kadan babu lakka a jikinta sanye take da maroon din Riga mai hannun Vest iyakarta cinya gashin kanta a sake yake sai plat shoe black colour dake sanye a farar kafarta,da sauri Furanko ya taso ya rungumeta yana mata sannu da futowa,Murmushi kawai tayi ,chair yaja mata ta zauna suka soma zuba mata abinci,ko kadan bata jin dadin abincin wasa kawai takeyi da spoon din tana juyashi.





M'I love u all



Gaskiya na raina comment dinku akan book dinnan.



Fatan alkairi gareku


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜



*ASALI NA*


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜


Na
*MARYAM ISMAIL*



🌈Kainuwa writer's association


United we stand and succed:our ambition is to entartein $ motivate the mind of readers




Page1⃣3⃣






Kallonta Dad yayi yace"meke damunki meyasa ba zakici abinciba?".



"Bakomai Dad karka damu,kawai banason cine,inaso naje saloon ne".




" banda abunki Sarena an taba tafiya da yunwa?"cewar Mom



"Mom kina wani damuwa,nixan wuce". Bata jira cewarsu ba ta wuce daki ta dauko bag dinta da key na mota ta futo ,wucewa zatayi Mom ta rike hannunta ta zuba mata kudi masu yawa a bag dinta tace"ki kulamin da kanki".




Murmushi kawai tayi ta rungumi Mom da Dad sannan ta rungumi Furanko tayi waje,mikewa yayi da sauri Dad ya rike hannunsa yace" kada ka damu ka bari ta dawo inaga wani abu na damunta kwanannan".





Motarta ta shiga kirar corolla ash colour ta figeta tayi waje kai tsaye wurin saloon ta nufa da gyaran jiki ta shiga aka soma gyara mata kanta tare da saka mata kunba ta kafa da hannu red colour.






Tsaye Nabila take tsakar daki tanata kaiwa da komowa a dakin ranta a matukar bace ta fada a fili"bazai yuwuba zaman me nakeyi wacce Sarena daharta fini a wurin Ya Jawad dame ta fini ,ko wacce tayi karya bazan taba bari ta rabi abunda nake soba"Dan figigin gyalenta ta fizga da jaka da key na mota tayi waje tafiya takeyi tana sakesake kai tsaye Companynsu ta nufa da izza ta shiga ciki anan taci sa'ar haduwa da Jamila dake aeki Companyn da farko taso taki bata hadin kai amma da yake Nabila y'ar duniya ce tuni ta siye Jamcy da kudi ta samu duk wasu details da take bukata akan Sarena wata muguwar dariyar mugunta ta saki tana ganin alamun nasara a tare da ita musamman da taji ba Musulma bace tuni sukayi musayar number da Jamcy don da gani y'ar hannu ce tasu zatazo daya, cike da farin ciki ta koma gida tana Allah Allah gobe tayi ta dirarwa Sarena.






Zaune yake a Bed yana shartar lallausar gashin kansa yana daure da towel yana kallon Manab dake damunsa akan yaci abinci.




Daure fuska Manab yayi yace"kana son Sarena har haka harka rayu bayan batan Minad to meyasa son Sarena zai hanaka cin abinci ka shiga damuwa har haka".





Tuni fuskar Jawad ta canza ta rikide zuwa bakinciki marar musaltuwa hawayene suka soma bin kuncinsa yace"amma ka cuci Minad dina ina matukar sonta ,son daba zan taba yiwa wata mace shiba ka daina hadata da ko wacce irin mace".




"Meyasa bazaka mata irin son Minad ba" Manab ya tambaya.




Harararsa Jawad yayi yace"saboda ita ba Minad bace bakuma zata taba zama irin Minad ba,kawai abunda yasa nakeso Sarena wani zubi takan man kama da Minad dina".






"Kayi hakuri zan kira Sarena yanzu nace gobe ta shigo office da wuri sai nida kaina na fada mata gaskiya".






Wayarsa ya zaro ya kira number din Sarena bugu ukku ta dauka tare da fadin" hello Sir,ina wuni"




"Lafiya " bayan sun gama gaisawa yace gobe ta shigo office da wuri yanason ganinta,kamar ta masa musu don ko kadan bata son zuwa amma kuma ta daure ta amsa da too.






Next day



Tsaye take gaban mirrow ta saka Red colour din riga iyakarta rabin cinyarta bata da hannu kuma robace dai dai jikinta gashin kanta a yasha gyara sosai an dauresa da kananun ribom red and black simple makeup tayi but yau ta shafa red janbaki hannunta daure yake da black clock dadaddiya dayan kuma da karamin yan yannu red,shoe dinta hills ne sosai black colour glasses ta saka radow baki me kyau kafin ta dauki black bag ,tayi matukar kau sosai abunka da farin mutum gashi sai fidda sihirtaccen kamshi take.







Saida ta gaishe da kowa na gidan sannan tayi break sama sama ta shiga motarta marcidiz black ta nufi hanyar companynsu.






Ur comments iz needed


Comment
Share





M'I love



πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜



*ASALI NA*


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜



Na
*MARYAM ISMAIL*




🌈kainuwa writer's association



United we stand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of readers




Page1⃣4⃣






A hanzarce Nabila ta fito sanye da dogon riga na atamfa makeup ne sosai a face dinta ga hills ta saka wani Dan karamin gyale ta daura a kanta ga gashin doki baje a tsakiyar baya jakk'a ta dauka da key din mota ta fita, cikin mintoci kadan ta isa companyn a bene ta hangi Jawad da Manab da labe ta iske Jamcy suka buya saitin da zasu iya ganin shigowar kowa a companyn.





Parking tayi amma tadan jima bata fito daga motanba kafin daga bisani ta soma ziro da kyawawan k'afafuwanta da sukasha ado da hadaddun hillsshoe,kafin ta fito gaba dayanta Masha Allah shine abunda na fada domin irin haduwar da tayi ga kayan jikinta sun karbeta,tafiya take a nutse ta nufi office din Manab.




Sosai Nabila ta gane Sarena nan take ta tuno ranar da suka hadu asibiti wasiwasi ta shigayi anya a ranar ba Jawad taje gani ba,nan take tsanar Sarena ta kara d'arsuwa a zuciyarta musamman data lura Sarena ba sa'arta bace ta fita tako wanne fanne,saidai tayi farin ciki da kasancewar Sarena ba musulma ba dominko ta kara samun hujja,anan tabar Jamcy tahawo stairs tana labe dabin bayan Sarena.





Baya ta dawo kadan tare da dafe kai lokaci daya ta furta ashhhhhhh kafin ta dago kyawawan idanuwanta tana kallon fuskar Jawad Wanda shima yake dafe dakai sanadiyar bigewan dasukayi.


Murmushi ya mata kafin yace"see u zaki fashemin kaine ko".


Daurewa tayi tadan wayance tace"kai bakaji tausaina ba,daka bugamin katon kannan naka"ta fada da sigar tsokana.



Zaro ido yayi tahowa yayi da niyyar kamata ta zille ta shige office din Manab.


Gaisawa sukayi kafin Manab ya dubeta yace"Sarena kinada boyfriend? ".


Tambayar tazo mata a bazata a firgice take dubansa tuni hawaye sun soma wanke kyakyawar fuskarta murya dishe ta furta" No".




Kallonta dakyau Manab yayi ya gama fahimtarta yace"to wani friend dina ya ganki yanaso ,zaki soshi?".



Kallonsa tayi kafin tace"idan har yayi daidai da ra'ayina da kuma iyayensa zasu karbi addinina".



"To baki tambayi ko waye ba,kinga sai aji auran rana daya dana Jawad barima na nuna miki matarsa kiga ko tayi".




Gabantane yayi mumunar faduwa idanuwan hawaye kawai suke fitarwa babu tsagaitawa yayinda zuciyarta ke mata zugi ji takeyi kamar ta rusa ihu a wurin saboda tsabar bakin ciki.




Wayarsa yake mika mata ki duba gata,ko kallonsa ta kasayi bare ta karbi wayar,da k'yar ya samu ta karba tana tababar kallon phone din,daurewa tayi ta soma kallon pic din ,zumbur ta mike tana karewa picture din kallo cike da mamaki da tababa shin barcine ko mafarki tana kara goge idanuwanta kodai sun fada mata k'arya ne.



Wani pic dinsune ita da Jawad da sukayi dago ido tayi tana kallon Manab dake mata magana" comedown Baby my friend is in love with u I hope zaki soshi kamar yadda ya soki tsawan lokuta".





Kasa amsa masa tayi tuni kallonta ya koma ga Jawad dake bakin kofa yana daga mata gira,Murmushi yayi ya bude hannuwansa yace"come to ur husband Baby".





Hawayen farin ciki suka zubo mata ta saki kayan hannunta ta ruga suka rungume juna ,dagota yai yana goge mata hawaye yace"l love u Sarena,do u love me?".


Murmushi tayi tace" I love u more than u love me Jawad".



"Ayyye harkun manta dani a nan to yayi kyau,ko kunyata bazakuji ba ko"



Dariya sukayi duka suna makale da juna.




Nabila dake hangensu tuni fuskarta ta jike da hawaye bata gane komai bare ta saurari wanne irin yaraye yake yawa a kanta dafe zuciyarta tayi dake barazabar tarwatsewa da gudunta ta ida shiga office din, iya karfinta ta daga hannu ta kwashe Sarena da mari har biyu kafin ta ingizata kasa ta fadawa chair kafin tace"Mazinaciya kafura harkin isa, ki shigo cikinmu da najasar jikinki,Wanda munafurci bazai taba barin zuciyarku ba makiya Allah to ina fada maki ki fita daga harkar mijina jahila kawai".





Kafin takai k'arshe Jawad ya daka mata tsawa"kima mutane shiru a wurin,me kike tinanin kinyi yanzu ,akwai jahilar data fiki ne,ko a cikin dabbobi sai an tona za'a samu wacce zatayi abunda kikayi"




Wurin Sarena ya karasa ya tasheta tsaye yana goge mata hawaye.



Ihu Nabila ta kumayi kafin tace"akan kafura wacce bata sallah zaka wulakanta jininka,wallahi bazan taba bari kuji dadin rayuwa ba"



Zuciyace ta tunzuro Jawad ya fada da karfi"ko sunanta kikaji dole ki girmama Nabila indai ni jininki ne,ki fita anan tun kafin na bata maki rai".




Tasan halinsa sarai tuni zai iya lakad'a mata duka ,yasa ta fita da gudu ta fada mota ta fita a guje.




Dafe kai Manab yayi yace"kaji yadda take tuki kada wani abu ya sametafa"



Tsaki Jawad yayi kafin yace"to saime damuwarta ce ae"Sarena ya kama yanata bata hakuri.



Rufe masa baki tayi tace"kada ka damu a kanka zan jure fiye da haka"kafin ta dora kanta a kafadarsa






Nabila kuwa a kofar gida tabar Motar ta shigo ta kofa a guje ta shiga parlo ta fada jikin Umma ta fasa ihu tana fadin"Umma ya gujeni kafura yake so,idan ban auresa ba wallahi zan iya mutuwa".




Da sauri Hajiya ta shigo parlon Wanda ta gama jin me suka fada tana fadin"kwantar da hankalinki marar tarbiyar yaronnan marar mutunci be isa ba"






*ALK'ALAMIN MARYAMA*✍🏻





Share and comments
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜


*ASALI NA*



πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜



Na
*MARYAM ISMAIL*




🌈kainuwa writer's association



United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers





Page1⃣5⃣




Huci kawai takeyi tanaso Jawad ya shigo gidan ita kadai tasan me take rayawa a zuciyarta.


Yayinda Nabila ke jikin Umma kwance tana sheshek'ar kuka hawaye nabin fuskarta.Umma kuwa sai faman lallashi take.



Gefe Abba ne yanata kai komo yana tunanin meke damun Jawad dahar yakeso ya wulakantashi yaki y'ar uwarsa.




Sallama sukayi da Sarena cike da k'auna ,Car dinta ta shiga ta tafi gida ranta cike da sakesake tana tunanin ya lamarinsu zai kaya.



Tsaye yayi a wurin yana tunanin mezai iske inyaje gida but yadai San babu abinda zaisa ya rabu da Sarena a wannan lokacin.


Dafasa Manab yayi yace"karka wani damu ka zama jarumi,kasan ya dace ka zabawa kanka macce ta gari,nina tabbata Sarena zata iya musulunta koda bayan auranku ne ka fuskanci kalubalan rayuwarka ".



Murmushi yayi sukayi musabaha ya shiga mota ya tafi gida.



A hankali ta futo daga mota rike da jakkar ta saita laptop a d'ayan hannun da sauri nani ta k'arbi jakkan tana mata sannu,murmushi kawai tayi ta shige cikin gida.



Zaune mutan gidan suke a parlo suna labari ganinta yasa Furanko tasowa da sauri ya kamota ya zaunar da ita a chair sannan yace" meke damunki haka?"



"Babu,kawai na gajine" cewar Sarena.




Daga gefan hannunta Mom ta hango ciwan da taketa boyewa,zaro ido tayi ta taso da sauri ta rike hannun a tsorace tana fadin"meye wannan daga ina kikaji ciwo".



Sorota tsaya tana dubanta sai kuma siraran hawaye suka soma bin kyakyawar fuskarta.



"Kinga kada kiyi kuka ,nasan ba zafin ciwo kikewa kuka ba,watakilla zakiga na takura maki amma komai nakeyi inayi donke kuma nasan zakiji dadi sosai a rayuwarki a gaba,ki kuma gane mamanki na sonki sosai kuma ina zama donke ne".



Murmushi Sarena tayi ta tungume Mom ,kafin ta kira Doctor a waya yazo ya duba hannun nata.




Da sallama Jawad ya shiga parlon babu Wanda ya amsa masa,dama yayi tsammanin haka juyawa yayi zai wuce da sauri Hajiya ta tari gabansa ta fizgosa baya suka tsaya suna duban juna.




" me kuma na maki haka Hajiya?".



"Ubanka kaman shege marar mutunci ". Cewar Hajiya.


Tsakiyar parlon ya dawo ya zauna yana dubansu yasan nufinsu kenan.



Numfasawa Abba yayi yace" yanzu abunda kayi ka kyauta kenan,dubi halin daka saka y'ar uwarka a ciki,Jawad yaushe ka zamo marar tausayi a rayuwarka".



"Abba babu abunda na mata tak'i fahimta ne".

" rufeman baki matsiyacin yaro Wanda baya kishin kansa,to aure babu fashi kokaso ko karkaso".cewar Hajiya.




Tuni launin Jawad ya dade da canzawa donko ya soma gajiya da masifar Hajiya a daure yace"Abba ka bani dama daya, gobe na kawo wacce nakeso Ku ganta,daga nan sainaji me zaku yanke a kai pls Abba na kayi wannan domin ni".




Girgiza kai Abba yayi yace"to kuyi hakuri zuwa gobe muga kan wacce ake abun donsu".



Badon Hajiya tasoba amma sai tayi wani tunani kuma ta hakura taga gobe mezai faru.



Ta waya Jawad ya sanarwa Manab komai ke faruwa ,baki ya bashi da kuma ya zama mai hakuri ya jira yaga abunda Allah zaiyi.






*NEXT DAY AT 4:30PM*



zaune yake a car yasha manyan kaya shadda blue colour ba k'aramin kyau yayi ba,phone dinsa ya ciro ya fada mata isowarsa,mintuna kad'an na hangota.



Sanye take da dogon wando har kasa blue colour sai farar riga iya kugu,kanta a daure batayi makeup ba sai plat shoe din dake k'afarta shoulder dinta rataye take da tsadaddiyar jikka inda wuyanta ke daure da sarkar jinari but me zanan kuroz sai zuba kamshi take tayi masifar kyau.




Da murmushi ta k'araso suka gaesa kai tsaye gidansu suka nufa cikin mintuna kad'an suka iso katafaren gidansu a gate suka samu Manab ya rigasu isowa,gaesawa sukayi daidai zasu shiga taja ta tsaya cak ta rike hannun Jawad tace"ina tsoro fa".



"C'mon babu abunda zai faru muje"



Da sallama suka shiga itako tayi shiru binsu kawai take a baya main parlon gidan suka shiga anan suka samu Umma da Nabila nuna Umma yayi yace"Sarena look at my Mother".



Da sauri ta isa gabanta ta duk'a har k'asa tace cikin gurbatacciyar hausarta"ina wuni Umma na sameku lafiya".



Babu yabo babu fallasa ta amsa mata da lafiya kafin tace Nabila kira Abbanku da Hajiya.




Yamutse fuska tayi kafin ta fita ta kirasu tanabin Sarena da kallon tsana.




Ba jimawa suka shigo yadda Sarena ta gaida Umma haka ta gaeda Abba da Hajiya, shikam Abba ya amsa tsakaninta da Hajiya kuwa sai harara.



"Uhum ina jinka Jawad".


" Abba wannan itace Sarena kuma itace wacce nakeso saboda naga bai sabawa addininmu ba".




"Ina h'ar a bada baka isaba bakuma zaka taba isaba,kafura a familynmu kayi k'arya,makiya Allah zaka aura" cewar Hajiya.



"Kaban Mamaki Jawad yanzu wannan itace abun aure d'ana na ciki ka rasa wacce zaka aura sai kafura wacce bata sallah,indai inada rai babu kai babu wannan auran"Cewar Umma.






*ALK'ALAMIN MARYAMA*✍🏻



Share
Vote
Comment



Love u all
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 🌈kainuwa writer's association

United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers





*ASALI NA*



NA
*MARYAM ISMAIL*




PAGE1⃣7⃣to1⃣8⃣




Kare mata kallo Momy tayi tsab sannan tace"meke damunki?,ki fadamun kinsan duk duniya bakya da wacce ta wuceni kinsan zan iya sadaukar da komai domin farin cikinki,bazan taba jurar hawayenki ba"




"Momy sun rabani dashi,ina sonsa sosai amma sunce bazan auresa ba....." Kuka yaci karfinta tayi shiru.



Cike da tuhuma dason gano meke faruwa Momy tace"wayeshi?,meya fiki gata ko kuwa *ASALI* ".



Girgiza kai kawai tayi sannan ta share hawaye tace"wai donni ba musulma bace...." Daga mata hannun da Momyn tayi shiyasa tayi shiru ta natsu .



Maimaita maganan Momy tayi sannan ta fada rai bace"kin bani mamaki kuma kin bani kunya,yaushe kika fara soyayya?,kuma ki rasa Wanda zakiso sai Wanda ba addininku daya ba,ya kikeso nayi,kema kinsan bazai taba yiwuwa ba,my last word indai na isa dake babu ke babu shi"ta ida nagana rai bace ta wuce part dinta.




Dafe kai kawai Sarena tayi wani bacin ran ya kauda wani tuni ta nemi hawaye ta rasa idanuwanta suka kekashe zafi kawai suke mata wani irin zafine ke ziyartar zuciyarta ta nemi hawaye ta rasa, da gudu ta nufi dakinta tasa key ta sake rushewa da kuka mai tsuma zuciya.





"Kaima kasan abunda bazai taba yiwuwa ba kenan,kafasan *ASALIN* Sarena a kasarnan yake, kuma zanyi duk abunda zanyi don ci gaban boyuwar sirrina,bazata auri musulmi ba final".



" Lissa ki fahimceni bana nufin tonuwar sirrinmu saidai bana so ki matsawa y'arki akan wannan hakan zai iyasa mu rasata Wanda nasan bazakiso hakan ba kibi a hankali kar kisata a damuwa".Samol ya fada da alamar rarrashi.




Numfasawa Lissa tayi sannan tace" zanyi me kace amma bazata taba ganin fuska akan wannan ba,inko haka ta faru zan dauketa mu koma America ta kuma auri Furanko".





**********************



Dab dashi Nabila ta matso tana shirin dafashi,dagowar da yayi ne suka hada ido taga yadda launinsu ya tikide zuwa ja ga hawaye kwance lub a cikinsu,babu abunda take hangowa sai tsantsar tsana da kiyayya wacce Jawad ke mata da sauri ta kauda idonta tabar wurin........Jan hannunsa Manab yayi suka wuce part dinshi sannan ya shiga basa hakuri yace"Jawad ka saurareni babu abunda yafi biyayya ga iyaye dadi,na tabbatar kafi son iyayenka akan Sarena,kayi addu'a Allah zai zaba mana mafita".



Girgiza kai Jawad yayi "bawai biyayyane bazanyi masu ba,ka gane Nabilarta na tsana ko kadan kafi kowa sanin bata cikin jerin matan da nakeso,me akeyi da mace marar aji ballagaza wacce zatasa a tursasawa namiji auranta wallahi n tabbatar Sarena tafita duka wannan abun dana fada,shima wai ko kasan meyasa nakeson Sarena?".


Girgiza kai manab yayi alamar a'a.

Murmushi takaici Jawad yayi kafin yace"iliminta ,natsuwarta ,hankalinta kalinta duk irina Minad ne,kuma kasan ba sauki bane zama kamar Minad komai nasu iri daya at all har kama sunayi son da nakewa Minad shine ya shafi Sarena,pls karku rabani da ita kamar yadda na rasa Minad".



Hakuri Manab yaita bashi yana nuna masa da bashi shawarwari masu inganci sannan sukayi bankwana ya tafi.




Next Day



Kamar kullun cikin suit ya shirya black colour yayi masifar kyau sai zuba kamshi yake dukda yadan fada daga jiya zuwa yau jakarsa da key ya dauka ya fita ta kofar baya ya tafi office.



A sanyaye Momy ta tura kofar dakin Sarena ta shiga cike da tausayin yadda ta isketa take amma saita daure tace"ba zakije office ba?".



Gaesheta tayi sannan ta bata amsa da eh.

"OK inkin shirya ki fito kiyi break nizan fita zuwa office".


Saikin dawo ta mata,Momy na fita hawayen tausayi ya zubo mata ta share fuska donko kadan bataso yanayin data iske y'ar tata ba.




Zaune yake a office din Manab sai tsaki yakeyi kamar zai tsinke harshe yana kallon agogon hannunsa ganin har time ya wuce Sarena bata zoba gashi sai kiran wayarta yake a kashe.



" kayi hakuri,nasan dama bazata iya zuwa yauba,amma Mae zai hana damun tashi office mu wuce gidansu"Manab ya fada.haka suka tsaida shawara don haka 3:00pm a cikin tankameman gidan Mr Samol tayi masu tsaye suke jikin mota a parking space ,ganin baki a wurin yasa Nani kas isowa wurin da murmushi ta kallesu tace"sannu da zuwa,na ganeka Kaine Mr Jawad ina yawan ganin picture dinka a wayan Madam"


Gaesawa sukayi sosai before tace"ka natsu ka jini ka saurari zuciyarka karkayi garaje ka yanke hukunci a hankali kabi maganar zuciyarka da shawara mai amfani amma ka sani babu abu mai mahimmanci a rayuwarka daya wuce iyayenka,zan turo maka Sarena yanzu"bata jira cewarsa ba ta wuce abunta.






*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻




Don't for gate to


Like
Comment
Share



Ga masu bada shawara

09030953294
[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜


*ASALI NA*



πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜


Na
*MARYAM ISMAIL*


🌈kainuwa writer's association



United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers






*HAPPY SALLAH,FATAN ALLAH YA KARBI IBADUNMU*




Page1⃣6⃣




Dago ido Jawad yayi yanabin Umma da kallo Wanda a time din idanuwansa sun rikide sun koma jawur saka makon bacin ran dake kwance luf kyakyawar fuskarshi,kafin ya dauke kallonsa yaji Nabila tace"to mayya y'ar gidan mayu zaki iya tashi ki fita ae kinsan hanyar da kika shigo aurene ba'ayi"




Murmushi Daddy yayi yace"to an sanya ranar auranka da Nabila nanda 2weeks ,n gama magana".



Hawaye ne suka soma fitowa a fuskar Jawad take yaji kafafunsa basa daukarsa anan ya duke kawai y kasa furta komai yana jujjuya kai,da gudu Sarena ta iso ta rikeshi tace"karka damu indan nice zan iya jure komai amma banda ganin kukanka ko bacin ranka pls ka daure".



Cikin sauri Nabila ta fizgeta daga jikin Jawad ta wurgar d ita can gefe kafin ta furta "karuwar banza".




Tsawa Manab ya daka mata yace" ke baki d hankali koko meke damunki sai kinji mata ciwo,ana so dolene?ke yanzu so kike nunawa Jawad ko k'i".




A hankali Sarena ta mike don ta gaji da bakaken maganganun da takeji ana fada mata kuka kawai take kamar zata cire ranta yanzu tanaji tana gani an rabata d Jawad dinta kenan saboda b addininsu daya ba,hanyar fita tayi ,da sauri Jawad y mike zan bita.



Cikin tsawa Umma tace" kana fita binta banice mahaifiyarka ba ,bani bakai"



Da gudu Sarena ta fice daga gidan tafiya kawai take a layin bata gane komai bata ko gani sosai tafiya kawai take

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment