Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mahaifiyar ki tayi mawa mijin ta Alhaji Adamu, kai har uban ki ma ance itace ta kashe shi . Don haka bana son ƙara ganin ki Idan kuma kinƙi ji ba zaki ƙi gani ba”. Ya furta yana rufo ƙofarsa baaaaammmm tare da barin Nasreen anan Wurin tsaye .......Juyawa nayi ina kare mata kallo , gaba ɗaya ta sauya kamanni fuska tayi baƙi tayi kanta na talauci da shiga Masifar rayuwa . Ni kuwa nace dama komai yayi farko zai ƙarshe ,ka ƙulla Alheri sai bayan yayi ƙyau .wannan kenan!
**
Wow Uncle kayi ƙyau sosai ina zamu je da sanyin Safiyar nan? . Ma'eesha ta furta tana kallon Aliyu inda ya yayi shigar Sa ta cikakken bahaushe shadda milk an masa ɗinkin zamani ɗinkin yabi jikin sa yayi ƙyauuuu ƙwarai.


Har wani ɗan ƙiba yayi ƙwana biyu ya aje Ɗan taɓa kaɗan na Hutu da ƙwanciyar hankali . Murmushi yayi yana kashe mata ido ɗaya tare da cewa “ Yau gidan Mami zamu je ”. Wani irin farin ciki ne ya kama ma'eesha da Sauri ta kai hannun ta tana Rungume shi tare da tsallen murna , har yanzu yarintar bai sake ta ba . Murmushin shima yake yi kana yace “ Ai ba daɗewa zamuyi ba . Kawai saboda ina so mu haɗu da mijin Mom Hajara ne , to zamuyi masu kwana biyu , don naji Ance An maida Auren ma nasu yanzu haka tana gidan mijin ta. Kuma nan da Sati Ɗaya za'a daura Auren Khalil da Maryam ”.

“....Hummmm”. Sauke Ajiyar zuciya Ma'eesha tayi kana ta ce “ Yayi ƙyau Uncle , Allah ya kaimu lokacin 💃🏻 ”. Amin ya furta yana riƙe mata hannu tare da nufar Farfajiyar gidan ......! Gidan Mom Hajara zamu fara zuwa .....ya furta yana raɗa mata a kunne . Ita dai kawai taji gaban ta na ta faɗi, musamman yawan sunan Mom Hajara da yake kira , kuma gashi tasan yanda ta tsane ta a rayuwa . Wannan yasa ta yin shiru tana ta tunanin zuciya ita kaɗai don tsoro ne yake kamata.

Bayan sun shiga garin Abuja”.
Ɗaga Wayar sa yayi yana kiran Mom Hajara inda yasa Wayar a amsa kuwa. Hello Mom gamu a hanya zamu zo Ni da Amarya😄🌹matata ”. A lokacin Mom Hajara tana zaune ne a daya daga companin Alhaji Adamu na shinkafa tana gudanar da Wasu Ayyuka tare da bin ƙwaƙƙwafin inda yake da maguɗi don ta yi gyara sosai . Gyara zaman Gilashin ta tayi tana kallon Alhajin nata tare da murmushi, Sai tace “ Alright Kar kazo kuma kayi mun wannan rawar ƙafar akan yarinyar nan , Wacce kake jin ta tamkar ran ka , da tana da iyaye to da tabbas nace An shanye ka ne ba a hayyacin ka ka be .


Ƙaassa ma'eesha tayi da ido ƙwallah na turuwa a cikin su. Ɗan cije laɓɓan sa yayi kana yace ” Mom stop please...ai gaskiya ne....kayya! Wai Da wane kike magana haka Hajara ? Muryar Alhaji Adamu ya katse ta , inda ta furta “ Da yaro na ne Aliyu , ina masa faɗa ne akan matar sa da ya Aura ko nace Yarinyar da ya Raina ....Ammmm kana jina Haidar?. Sauke numfashi Aliyu yayi a ɗan ƙasa ƙasa yace “ Ina jin ki Mom ”. Hunmm na taɓa ƴar zinare ba , dole ka amsa Ni ƙasa ƙasa . To yau akwai event da za'a fara na Maryam , mu haɗu a guest house ɗin Mamin ka duka har dashi yanzu zamu nufa can . Duk da taron sai 4:00pm ne , Amma mu tun yanzu zamu je don a fara komai a idanun mu . Ohk ya furta yana datse wayan tare da danne damuwar sa kar hankalin Ma'eesha ya tashi...........!
[2/1, 3:37 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

88-89
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500 Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409....✍🏻🤍#Mamanteddy#mrsusm.*
Book 3
Kallon ta yayi yana sakin mata murmushi kana yace “ Guest house zamu wuce yanzu ”. Tom ta basa amsa fuskar ta ba tare da ta nuna masa Wani damuwa ba.

**
Wani ƙayataccen gida ne mai ƙyaun gaske , Amma girman sa yayi yawa , Don kamar ba guest house ba . Wannan yasa Idan zasu yi ɗan taro yasu yasu suke zuwa nan. Tun daga Wajen falon take jin Muryar ta cike da izzan nan nata da mulki wanda sai da gaban Ma'eesha ya yanke ya faɗi dammmm” . Saurin kai hannun ta tayi tana riƙo Hannun Aliyu wanda Cike da kulawa yake kallon ta ....idanun ta ne yayi rau-rau , cikin narkakkiyar murya ta furta “ Uncle Bana son shiga ”. Ma'eesha su Mami ne fa a ciki , kar ki damu ko Mom Hajara ba zata yi Miki komai ba , ai yanzu ta rage wasu abubuwan da yawa , taho muje! Ya furta yana kamata tare da riƙe hannun ta suna shiga cikin tsakiyar falon bakin su ɗauke da Sallama .

Haɗa ido Ma'eesha tayi da Mami wacce daganin ta fara'anta ya ƙaru, Ma'eesha na! Ta kira sunan ta tana kare mata kallo . Da sauri Ma'eesha ta nufi mami tana Rungume ta tare da furta “ I miss You mami ”. Rungume ta mami tayi tana shafa bayan ta tamkar jaririya a hannu .....Kana tace “ Lallai Ali ya kula mun dake sosai , kin ga yanda kika yi ƙyau dake Baby na....ko da yake yanzu babyn Haidar ne kar yayi mun iyaka😹 dariya Aliyu yayi yana zama a ɗaya daga kujerun dake zagaye kana ya gaishe dasu Daddy da Alhaji Adamu wanda shima ganin su yake ta sakin Fara'a .

Muryar Jidder ne ya katse su tana cewa “ A'a Momy meke faruwa ne ?”.....duka juyawa suka yi suna kallon inda Mom Hajara take gaba ɗaya bin Ma'eesha take da Wani irin kallo tamkar zata cafke ta ....Hajara wannan kallon da kike mawa Aishatu na menene? Muryar Alhaji Adamu ya katse su. Hummmmm Wani irin Ajiyar zuciya Mom Hajara ta sauke tana miƙewa tare da ƙara ƙare mawa ma'eesha kallo , kawai sai ta juya ga Alhaji Adamu tana furta “ Ka kalle ta da ƙyau ko dai idanuna ne? . Ali wannan itace wannan dai Ma'eeshan ko wata ce daban? .

Aaaahhha'aa! Mami ta furta itama tana miƙewa, yayin da Ma'eesha duk sai taji tasha jinin jikin ta. Yanzu kuma mene zata ce akan ta ? Abun da take Tambayar Zuciyar ta kenan ?. Kaman Wanda Alhaji Adamu ya san Ma'eesha cikin ƙarfin murya yace “ Ita ce dai gata nan menene kuma?”.

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un....ta furta tana kallon su duka , Wasu irin marayun ƙasƙantattun hawaye na zubo ma kuncinta sharrr³. Cikin sauri Jidder ta riƙo Mom Hajara itama tana fara kukan tare da cewa “ Mom don Allah wai menene? Meke faruwa ne Mommy? . Kallon su tayi kana ta kalli Ma'eesha wacce ta maƙale jikin Mami....Jan numfashi Mom hajara tayi tare da cewa “ Wannan ba Ma'eesha Bace! Zahara ce!! Zahara tace!!!

Wani irin kallo su duka suke bin ta dashi , kana Aliyu yace “ Anya Mommy babu matsala kuwa a tare dake ?.

Gaskiya kam! Mami ta furta tana bin ta da wani irin kallo , kana ta cigaba da cewa “ Ya kamata a bincike ƙwaƙwalwar Hajara gaskiya da matsala.

Cikin matsanancin damuwa da rashin sanin hujjar ta , ta kalli mijin nata Alhaji Adamu kana tace “ Ka faɗa musu Wannnan itace Zahra na , ko kai ma ka manta da ƴar da muka haifa ne? Idan su basu san ta ba kai ai ka san ta! Ta furta cikin ɗaga murya wasu hawayen na daɗa ƙwaranya mata ”.


Shiru Alhaji Adamu yayi kaman mai nazari ...Gaban Ma'eesha kuwa wani irin faɗuwa yake yi yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi . Kallon al'amarin take yi kamar a mafarki , Wani irin magana Mom Hajara ke yi wai itace ƴar ta ? Kai gaskiyar Mami ne da tace a bin cike lafiyar ƙwaƙwalwarta ”.


Mtswww!!! Dogon tsaki Mami taja kana tace Shashancin banxa da wofi. Kawai saboda kin dawo hayyacin ki da tunanin ki , shikenan sai ki kalli yarinyar da take nan tsawon shekaru Kice wai ƴar ki? .

Kuka Mom Hajara ta fashe dashi tana furta “ Wallahi ƴa ta ce! Nifa na haife ta tayaya ko tsufa tayi zan gane ta , Ma'eesha Ni ce mahaifiyar ki.

Mom Hajara ke maganan kamar mahaukaciya. Khalil ne ya kalli Alhaji Adamu wanda shima ya faɗa tunanin Abubuwa gami da Ma'eeshan ,tabbas a jikin sa yake jin gaskiyar maganar Mom Hajara . Amma kuma baya da wata ƙwaƙƙwaran shaida.

Ni na san bata mutu ba Wallahi ƴa na ta raye.

To ai sai ki nemo ta , Wannan dai Ba yar ki bace . Mami ta katse ta cike da fushi .

Cikin Muryar dattako Alhaji Adamu ya kalli Mom Hajara kana yace “ Ya isa Hajara mu wuce mu tafi gida yanzu ,zan Miki bayani......Kallon sa tayi tana gani yana tasata tare da yi masu Daddy sallama wanda Duka jikin su yayi sanyi.

Bin ta da kallo Ma'eesha ke yi jikin ta yayi sanyi Qlau. Kawai ji tayi bata jin dadin ganin Mom Hajara a wannan halin , Zuciyar ta na mata babu Daɗi ”.

Har sun kai ƙofa ne Muryar Aliyu ya katse su inda yake cewa “ Abba momy ku dakata! Juyowa suka yi suna kallon shi , inda ya juya yana kallon Ma'eesha dake tare da Mami .

Da gaske ne Ma'eesha diyar Mom Hajara ce babu shakka a ciki , ita ƴar Mommy ce!😲 . Buɗe baki jidder tayi tana faɗin bamu gane ba? . Ita kuwa Mom Hajara saurin fizge hannun ta tayi a hannun Alhaji Adamu tana furta ‘ Kaji ko wallahi na faɗa maka Zahran muce!

Wani irin magana kake yi haka Ali? Mami ta katse shi tana yi masa wani irin duba .

Uncle?
Muryar Ma'eesha ma ya katse shi tana kiran sunan sa , idanun ta na ciko da ƙwallah kana tace “ Wasa kake yi ne ko? Don Allah Uncle ka bari , bance maka ina son ganin Iyaye na ba , bare har ka bani uwar da batawa , ina jin daɗin zama da Mami da kuma Daddy don..... Na taɓa Miki ƙarya? Ina da hujjoji na babu shakka Ma'eesha ɗiyar Mom Hajara ce ta cikin ta . Idan kuna tantama ku muje Asibiti ayi maku gwajin jini . Sannan kar ku manta da Nine fa na tsince Ma'eesha a cikin moton da ke ci da wuta . Kar ku manta su ma hatsari suka yi ......Ya Salam! Furucin da su Daddy suka furta kenan!


Yayin da Alhaji Adamu yayi wani murmushi yana furta “ Alhamdulillah....” Ni tun a ganin farko naga ƴa ta , amma kuma nayi shiru ne ko da tace ƴar muce na nuna mata ba haka ba ,saboda taji zafin tsanar data dingi nuna ma ƴar ta na cikin ta bata sani ba. Yau gashi Wa gari ya waya? Da wani zaki kalli yarinyar ki? Kina ma da bakin yi mata magana?”.

Wani irin kuka mai tsuma zuciya Mom Hajara ke yi ....Itako Ma'eesha ta kasa motsi jin abun take yana juya mata .


Ma'eesha da gaske Ga Abba , ga kuma Momy! Aliyu ya furta yana sakin mata murmushi wanda ta tsaya tana bin sa da kallo cikin Muryar kuka ta furta “ A'a Uncle ka barni da Mami, wannan sam ba mahaifiya ta Bace!
[2/1, 4:16 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: 90
Mmnteddy
Mrs-usm..🤍
#Rainon soja
Started on 02/12/2023
Done and dusted 📚 💃🏻 01/02/2023
“....Kuka Mom Hajara ta saki mai karya zuciya , don jin Furucin Ma'eesha yafi komai ɗaga mata hankali ”. Kiyi Haƙuri Ma'eesha mune iyayen ki , Aliyu yayan ki ne kuma tamkar uba a gare ki ...kiyi mana Alfarma ki amince damu a matsayinmu na iyayen ki duk da bamu tava Miki komai ba a rayuwa , ba muyi Miki ranan komai ba. Alhaji Adamu ya furucin yana kallon Ma'eesha wacce a yanzu shi take kallo . Tausayin sa taji ya kamata , musamman a ƙwayar idanun sa zaka zallar soyayya da buƙatar ƴar tasu. Maxa tafi gare su🥹 ....Mami ta furta tana janye hannun ta daga Ma'eesha, Kallon mami Ma'eesha tayi hawaye na zubo mata tamkar an buɗe fanfo . Ƙwal'ah ne ta gani a idanun Alhaji Adamu wanda cikin sauri ta nufe shi tare ta rungume su da Mom Hajara tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi wanda ko wa na wurin sai da Ƙwallah ya ciko masa . Kusan mintuna biyu ita da Mom Hajara suka ɗauka a wannan yanayin ....kana ta ɗago ta kalli Mom Hajara sai ta juya tana kallon Aliyu kamin cike da sarƙewar murya ta ce “ Uncle Da gaske ne mahaifiya tace!. Girgiza kai jidder tayi , idanun ta sun kaɗa hawayen da take ta dannewa sun gagara mata . Kamin Aliyu ya bata amsa ne , Muryar Jidder ya katse ta tana cewa “ na tayaki farin cikin ganin iyayen ki duka , kiyi Haƙuri duk da nasan ba lallai ki iya yafe mun ba . Amma naji kunya kasantuwar ki ta ƙanwata na daɗe cutar dake ban sani ba🥹 . Hawayen idanun ta ne suka ƙara gudun sauka. Naji ba daɗi amma na tayaki murna , gaki yau da Uwa jajirtacciya kamar Momy , gaki da mahaifi babban mutum ke kadai Allah ya basa kamar Abba , bayan nan gaki da miji Nagartace mai Miki so na hauka na bada rayuwa kamar ya Aliyu...kin zo duniya a Sa'a , a da ina miki kallon mara Sa'a . Ashe kin fi Ni.....Ki yafe mun Ma'eesha ko ba don komai ba ,ko don alaƙar mu ta jini....”

Yanda jidde ke kuka yasa zuciyar Ma'eesha karaya , tabbas ita tana son jidder duk ƙiyayyar da take mata bata taɓa jin kin ta ba .

Janye jikin ta Ma'eesha tayi daga na Mom Hajara tana Rungume jidder tare da murmushi hannun ta tasa tana goge mata hawayen fuskar ta kana tace “ Komai mai wucewa ne Aunty jidder , Ni yar gata ce tun da ina daku . A lokaci duka na ƙara samun ku . Ina sonki sosai🥹😍.

Tuno da maganan nata tayi tun tana yarinya ko ta ɓata mata rai sai dai tace “ Ina sonki Aunty jidder! ”. Gyada kai jidder tayi cikin kuka ta Rungume ma'eesha tana cewa “ Ina sonki Nima Ma'eesha......❤️”#final😲. Ƙirjin wasu ya buga daaammmm🤣🤣🤣 .After some years 🕊️🙌🏻
💃🏻
Ma'eesha! Ma'eesha!!!
Taji Muryar sa na kiran sunan ta cikin barci take ware idanun ta a hankali kana ta sauke su a fuskar sa wanda ya ƙara ƙyau da cikar kamala kai dagani kasan an samu kwanciyar hankali .
Please ki tashi! Ya furta yana kashe mata ido . Ɗan lumshe idanun ta tayi kana ta ware su akan sa tana cuno ƙaramin bakin nan nata tare da cewa “ Uncle Yau fa ka dawo daga....katse ta yayi da cewa “ Don yau na dawo Shikenn sai kar na buƙaci matata? ”. Kallon sa tayi kana tace “ Aaa nayi tunanin zuwa safe.....kaga yanzu fa ka gama da hidimar yara .

Cikin wani irin murya cike da gajiya yace “ Ma'eesha wai yaushe zaki daina gudun sex ne ?

Dariya ta ƙunshe ganin duk guje²n nata ya gano ta , amma sai ta ɗan dake da sauri tana miƙewa tare da hayewa saman shi tana mai cewa “ A'a Uncle ko Ɗaya me zai sa na rinƙa maka guje² , ai yanzu mun zama iyaye yara uku fa ba wasa ba🙌🏻😹 . Murmushi Aliyu yayi yana kai hannun sa tare da shafa ƙasan durinta kana yace “ Har yau kina nan kamar budurwa, shiyasa fa kike guje² saboda Ni nasan sau da yawa kina daurewa ne don nafi ƙarfin ki amma a haka kike ɗauka na ....” kina ƙoƙari sosai .

Murmushi Ma'eesha tayi tana cewa “ Muje daga ciki Are You ready? . Yessss my Doctor . Dariya tasa ka masa tana fara shafa maran sa zuwa ƙasan Twins ɗin sa ,tana wasa dasu kana tace “ Uncle na gode maka sosai daka cika mun mafarkai na da dama . Gashi a yanzu ina matsayin da ban taɓa zato ba , na zama cikakkiyar likita , ka bani jin dadi gani ta sanadiyar ka Allah ya azurta mu da ƴaƴa Hanif Hanifa a lokaci guda Allah yabamu tagwaye sai Bilal .....me zance me Allah da ya wuce godiya da ya bani jajirtaccen namiji mai so na da ƙauna ta.....💋 kissing ɗin Twins ɗin shi tayi yana jan ƙafarsa alamun daɗin ya fara kai masa . A hankali ta fara lasar jijiyar tana shan ta daga ƙasa . Shikam Motsa laɓɓan sa yayi yana cewa “ Yaushe Hanifa zata dawo daga Gidan Jidder ne ?” . Ɗaxu muka gama magana da Areeef kin san tasu Hanifa ta zauna Acan fa...” Ɗagowa Ma'eesha tayi tana kallon sa kana tace “ ai duk gida ne Uncle....” ta dawo ina son ganin ƴata nima🤨. Hummm Shikenan Uncle Haidar gobe inshallah zan saka driver ya ɗaukota”.

Ya kamata ki sauya mun suna , Nima ki kirani da suna me ɗan madara madaran nan😻yayi maganan yana murmushi cike da zolaya yana shafa bayan ta . Dariya Ma'eesha tasa tana cewa “ Ok yanzu zan faɗo maka sai ka zaɓa wanne yafi maka a ciki ?”. uhmmmm barshi ma ai kawai kai Uncle da HERO ya kamata na rinƙa kiranka🫨😹 don na azabtu a hannun ka , wannan exercise ɗin kan shi ........kamin ta ƙare maganan tuni ya fara Dariya yana rungumota tare da fara kissing ɗin ta yana furta “ Duka nayi shine a cikin SO a RAINON SOJA........!



*TAMMAT BI HAMDULILLAH*

______________________

Anan na kawo ƙarshen Wannan littafi na RAINON SOJA...ina godiya ga Allah mai kowa mai komai da ya Bani ikon kammala shi cikin koshin lafiya... na gode ƙwarai da Soyayyar da kuka nuna min a wannan littafi, ƙwarai naga masoya Makaranta da marubuta ina matuƙar godiya ....ba zan rufe wannan littafi ba tare da Nayi godiya a gareku ba Hajiya Nafisat kt tare da ATA🙌🏻😄 kun sayi littafin ga da kuɗi masu yawa ina godiya Sosai 🙏🏻😻 . Anan nake cewa mu huta lafiya....💃🏻

_______________________
*#mmnteddy🤍ga masu buƙatar complete document ₦600 ne via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank shaidar biya ta wannan number 09061466409*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment